Ba ni da gata - Chapter 37
Ba ni da gata Chapter 37: Ba ni da gata Chapter 37. *____________________* ...........lulawa kawai su ke yi cikin sararin samaniya har na wajan sa'o'i uku…
3,274 words
*____________________* ...........lulawa kawai su ke yi cikin sararin samaniya har na wajan sa'o'i uku ka na su na sauk'o k'asa. Babu abunda ke ta shi sai kuka da haniniyar dawakai kuma su ba su ganin koma jin su kawai su ke bisa wani abunda su ba su san ko menene ba, shi ma dai a k'asar sun yi gudu wanda su ke da tabbacin dawakai ne sai dai ba su ganinsu har na tsawon mintuna talatin ka na su ka fara ganin hayak'i daga nesa da su kad'an. Sabrin ta yi fitsari a jikinta ya fi sau babu adadi ya yin da Hamdan ke ta fad'in, "Allahumma inni a'ouzu bika minal khubisi wal kaba isa" kamar wanda zai shiga ba yi. Julaibib kuwa addu'o i kawai ya ke karantawa cikin zuciyarsa, Fu'ad kuwa ya na addu'a ta re da fad'in, "Shikenan Anna mun yi ban kwana". Binty kuwa sai fizgan numfashi ta ke yi kamar mai asthma. Wani dank'areran masarauta su ka hango wanda baki ba zai iya misalta girmansa ba da kuma tsaruwarsa. Domin da zallar d'anyan gwal aka k'era masarautar re da yi mata kwalliya abun sai wanda ya gani. Tun daga nesa daga masarautar dakaru ne sama da guda dubu cikin shigar yak'i fuskansu a rufe amma k'afafuwansu na kofato ne. K'ofofi kuwa sun kai hamsin wanda ko wani k'ofa nan ma dakaru dubu ne masu bud'e shi saboda tsabar girma da nauyinsa. A lokacin ne kuma, Su Julaibib su ka ga wad'anda su ka d'auko su, suma fuskokinsu a rufe ya ke sai k'afafuwansu na kofato. Masarautar nan girmansa da kyawunsa ya fi gaban fad'e. Su ma rayuwa su ke kamar bil'adama. Akwai kasuwa a ciki, ga kuma aljanu nan cikin suffar mutane kowa na hidimansa, kyawunsu kuwa ya fi gaban kwatance, akwai bak'ake amma ba irin bak'in fatar da mutum ya sa ni ba, bak'insu mai masifar kyau ne da d'aukar hankali, gashin kan su kuwa har k'asa ya ke ja saboda yawa da tsawansa. Gaba d'aya yuuuuu aka aljanun nan su ka yi da idanuwa su na kallon su kamar za su cinye su d'anye. Daga k'ofar da za ta sa da su da ainahin fad'ar Oumul Sahwat su ka tsaya, su dai Su Julaibib su na ganin ikon Allah domin su ba'a sama ba, kuma su ba a k'asa ba haka su ke. "Ai mana iso wajan Shugaban mu, na sanar da ita na cika mata alk'awarinta ga bil'adama nan na kawo mata su". Fad'in d'aya daga cikin dakarun nan. Uku daga cikin dakarun kofar da zai sada su cikin fadar Oumul Sahwat su ka shiga ciki don sanar da Oumul Sahwat. Cikin mintuna uku su ka dawo ta re da fad'in, "Sarauniya Oumul Sahwat ta ba da umarni Badakkare Oulbub shi kad'ai ya shigo da bil'adama cikin fad'a". Gaba d'aya sauran darewa su ka yi, ya yin da Su Julaibib su ka ji su a k'asa timm sun fad'o. Sabrin k'ank'ame hannun Binty ta yi ta re da fad'in, "Ki taimake ni Dan girman Allah, wallahi ban so in mutu yanzu". Ta fad'a jikinta na b'ari. Duk da kasancewar Binty cikin gigicewan tsoran da ta ke ji ta ma fi Sabrin d'in amma sai ta ka mo hannunta ta re da fad'in, "Ki yi ta addu'a, in sha Allah za mu koma gida babu abunda zai sa me mu". Gaba d'ayansu kuwa ji su ka yi kamar ana tura su har cikin fadar da sai da gaba d'ayansu numfashin ya d'auke na wucin gadi sakamakon arba da su ka yi da tsaruwar wannan fada da girmansa ya wuce kwatance. Daga bakin kof'ar zuwa can wajan zaman Oumul Sahwat tafiyar kwana uku ce idan aljani ne kuma bai yi amfani da tsafi ba, amma idan mutun ne zai shekara ka min ya isa. Wani tsararran kujeran zinari ne ya ke saukowa daga sama, ga kuma gashin da ya zuba har a gaban su Binty da ke bakin k'ofar fada saboda tsayi da yawansa. Sai da kujeran ya kusa tab'a k'asa ka na ya tsaya cak. Bayan wata farar mace ya bayyana tun daga kan tsakiyar kan ta har kwankwasonta ado ne na zinari. Wasu fararan kayane a jikinta masu stone na gold sai kyalli su ke yi, jelar rigar da ya ke a tsattsage sai da mamaye masarautar nan. Kanta ne kawai ya juya ba ta re da gangan jikinta ya motsa ba. Wani irin ajiyar zuciya Hamdan, Sabrin, Barr Fu'ad su ka saki yayinda Sabrin da Binty da Hamdan su ka zube a sume.
*DAN ALLAH KU YI HAK'URI DA WANNAN ABUBUWA NE SU KA MIN YAWA A SCHOOL* 🌹 *75-76*🌹 ............Fuskanta ne ke kallonsu ya yin da gangan jikinta ke kallon gabanta, kyakkyawace ta wuce misali. Idanuwanta sak irin na mage. Farinta kuwa kamar Snow white. Da hannu ta yi alamar sai ga su su na tahowa har da Sabrin, Binty da Hamdan da ke ya she a sume. Cikin minti d'aya su ka isa gabanta. Ta ke ta jujjuya hannunta ta re da watsa su a kan fuskan su Binty da ke ya she a sume, cikin dak'ik'u su ka farfad'o a matuk'ar razane, don Sabrin k'ank'ame Binty ta yi ta na hawaye cikinta na murd'awa. Oumul Sahwat d'ab yatsanta ta d'aga ta re da jujjuya sa ka na ta tsayar da shi a nan tsakiyar fadar nesa da su k'adan. Ta ke Yousouf ya bayyana a k'uk'k'ulle da wani kaca wanda idan za'a warware kacan mutane dubu ba za su iya ba. Gaba d'aya jikinsa jini ne ke zuba har ta idanuwansa da kunnansa. Daga kan karagar ta mik'e still fuskanta na kallansu kuma gabanta na kallon baya ta re da nufo in da Yousouf ya ke a k'ulle, sai a lokacin ta mai da sauran jikin na ta ya na fuskantar in da fuskanta ya ke ta re da kecewa da wani irin dariyar da ya kusa tsayar da numfashinsu duka ka na ta k'arasa kusa da sarkin k'ofar fada ta re da fad'in, "Ayi shela gaba d'aya aljanun masarautar Daulatul Sira su yi gangami, a kuma shaida mu su da fitowa ta ta re da bil'adama da kuma bak'in mugu jinin adali kuma amintaccan bawan wannan masarauta da ke nai man jefa mu cikin tasku da fuskantar barazana daga azzaluma wato sarauniyar da ke mulkar Daulatul Bahshan da a yanzu haka ta ke tafe da rundunarta domin yak'armu ta kuma had'e harda masarautar nan ta mulka". Cike da girmamawa sarkin k'ofa ya rusuna ta re da juyawa ya nufi fad'awa sarkin shela domin aljanu su yi gangami. Cikin abunda bai fi minti biyu ba, tu ni har kowa da ke cikin masarauta da ma wanda ke wajan gari su ka yi gangami domin amsa kiran Oumul Sahwat. Komawa ta yi gaban Yousouf ta re da d'ago hab'ar shi da d'an yatsar ta ta re da fad'in, "Sai na k'ona zuciyarka kamar yarda ka k'ona tawa zuciyar. Sai na sa ka tafi lahira da tabo mafi muni a zuciyarka na jawo mana fitina da ka yi akan wancan bil'adamar da ba jinsu ku d'aya ba. A cikin wannan Masarauta akai y'antattu da kuma bayin da su ka fi wannan kyawu sau dubu tamanin amma ka k'etare duka jinsinka ka fad'a soyayya da jinsun da ka ke so saboda ka rai na alk'awarin kakana na Uku da ya yi alk'awari da kuma sa hannu da jinin jikinsa akan babu mu ba bil'adama. Ka ci amanar kaka na da kuma na masarautar nan, ka fusata sarauniyar Daulatul Sira wanda a yanzu zan d'and'ana maka azaba wacce ba ka tab'a tunaninsa ba, zan wulak'antaka in kuma tozarta abun k'aunarka da duk wanda ke da alak'a da ita. Sai na saka dakaruna dubu hud'u wanda duk d'ayan su ya na da k'arfin dawakai hamsin su yi mata mummunar fyad'e a gabanka da duk aljanun da ke cikin wannan masarauta, sannan in sadaukar da sauran bil'adaman can wa Sarauniyar Daulatul Bahshan domin fansar masarautata da kuma aljanun da ke cikinsa, kai kuma da Kakan ka mai d'aure maka gindi, zan sa ke baiwa sarauniyar Daulatul Bahshan Ku a matsayin kyauta domin ga na maku azaba a kowacce rana ta na jin sanyi da dad'i har ku shud'e wannan shi zai ragewa zuciyarta rad'ad'in hallakar kakanta na goma sha biyu da bil'adama su ka yi sanadin mutuwarsa". "Allah ba zai tab'a baki wannan damar ba, domin Allah bai ce mu zalinci kowa ba. Ya halicce mu ne don mu bauta masa, kuma mutuwar kakan Sarauniyar Daulatul Bahshan ba laifin bil'adama ba ne, domin Allah ya halicce mu, mu za mu gan su, amma su ba za su gan mu ba, kuma su ne su ka je duniyarsu ba su su ka zo har na su duniyar su ka yi sanadin mutuwarsu ba. Hakan na daga cikin k'addararsu ne. Kuma taimako taimako ne kuma ladarsa na wajan ubangiji. Walau Aljani ka taimaka ko mutum. Ni dai na san ni da Kakana rai muka tseratar". Fad'in Yousouf da ke a k'ulle. Wani kibiya Oumul Sahwat ta zaro daga cikin fatar hannunta ta cakawa Yousouf a cinyarsa sai da ta fito ta baya ta kuma zarowa ta caka masa a d'ayan cinyarsa ta re da mak'ure wuyansa da zara-zaran hannunta wanda ke d'auke da dogayan k'umbuna. Wata tsohuwace ta taho a kan iska a gigice ta zube a k'asa ta re tab'a k'afafuwan Oumul Sahwat ta re da fad'in, "Ki gafarcesa shugawa, a bisa shi ina mai naiman gafararki ki yi hak'uri alfarmar kakansa na goma kuma amintacce bawa a cikin wannan masarauta". Sakin wuyarsa Oumul Sahwat ta yi ta re da nufar kujerarta ta zauna ta re da d'aura k'afa d'aya a kan d'aya. Su Julaibib mutuwar tsaye su ka yi yayin abubuwan ya ke faruwa a gabansu. Ba ki ba zai iya misalta tashin hankalin da su ke ciki ba. Gaba d'aya kowa ya hallara fitowar Sarauniya kawai ake jira. Daga can filin yak'i kuwa, dakaru ne kusan guda million dubu hud'u cikin shigar yak'i. Oumul Sahwat b'acewa ta yi domin komawa cikin d'akinta don kuyanginta su shiryata. Wannan tsohuwa da ta duk'a ta nai man wa Yousouf afuwa a wajan Oumul Sahwat, kallon Yousouf d'in ta yi hawaye na gangaro daga idanuwanta ta re da fad'in, "Ya kai d'ana, ka jajirce kamar yanda ka so ma tun farko to ka kai shi k'arshe. Ka cikasa ladanka, ka da ka tab'a bari a cutar da wad'annan bil'adaman da kai ne sanadiyar shigowarsu duniyar mu. Zan mutu cikin salama tun da har Allah ya sake had'a fuskokin mu. Allah ya yi maka albarka sannan ka warware k'ullin da ka k'ulle ka min ruhinka ya bar gangan jikinka. Ka da ka bari d'an tsokar da ke k'irjinka ya rinjayeka idan har da gakse ka shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah. Allah ya taya ka d'ana". Ta k'arishe maganar da kuka ta re da ta shi sama ta nufi in da Julaibib ya ke. Bud'e tafukan hannunsa ta yi ta re da d'aura masa wani d'an tantabara mai d'auke da sarka. Can kuma ta d'auki sark'an ta re da saka masa a wuyansa ta kuma cusa tantabarar cikin rigar jikinsa. A ta ke ka yan jikinsa su ka canza kala su ka koma Orange, can kuma su ka koma green daga baya kuma su ka koma farare k'al wanda da ainahin kalar su brown ne. Tafin hannun ta kuma rik'ewa ta re da fiddo wani tawada ta yi gajeran rubutu ka na ta kalle shi ta re da fad'in, "Duk rintsi ka da ka yadda wannan sarkar ya bar jikinka, sannan idan kun koma ka samu ruwan zam-zam ka wanke wannan rubutun da na maka a da shi ka baiwa takwaran d'ana wato Yousouf in sha Allah shi da wannan cutar har abada da ma duk wani cutar da aljani ya yi ajiya". Fad'in Wannan aljana ka na ta b'ace b'at. Sabrin dai ta yi fitsari ya fi a k'irga. Ya yin da Binty kuwa cikinta sai katsawa ya ke yi ta na addu'ar Allah ya sa ta tashi daga wannan baccin da ta ke yi haka mai munanan mafarkai. Shikuwa Hamdan sai "Qul ya ayyuhal kafirun" ya ke ambata a fili. Fu'ad kuwa jikinsa karkarwa ya ke yi ta re da uban zufar da ke gangaro masa. Julaibib kuwa kai tsaye ba za ka ga tsoro a fuskanci ba, amma a zahiri ya na cikin firgici amma sai jero addu'o i ya ke yi cikin zuciya. Ganin su kawai su ka yi a waje gaban dandazon jama'a da ke ta ihu wasu na rawa wasu na kid'a wasu kuma na yi kamar za su cafko su. Cikin second biyu ko'ina ya yi tsit hatta tsuntsu da ke wajan saboda bayyanar Oumul Sahwat akan wani k'erarriyar kujeran mulki da aka yi sa da zallar gold, ita kanta saga samanta har k'asanta kwalliyace da gwala-gwalai. Sanye ta ke cikin wani doguwar riga mai wasu irin kyalkyali kalar baki da ja, gashin kanta da ya zuba har ya na tab'a kafafun aljanun da ke k'asa shi kan shi ya sha ado da gwala-gwalai. Wani irin crown ne a kan ta na zallar gold mai d'aukar ido. Gefen hagu da damarta y'an mata ne guda uku-uku kyawawa da fiffike a bayansu su na mata firfita. Sai wasu murtuka-murmukan aljanu cikin shigar yak'i hannunsu rik'e da kaifaffiyar takobi a hannunsu fuskansu a rufe su na jiran umarni. Mahaifiyar Yousouf ce ta bayyana hannayanta rik'e a hannun wasu dakaru bakinta na fitar da jini. Sarauniya Oumul Sahwat ta kalli wani badakkare da ke gefenta ta re da kallon d'unbin aljanun nan. Cikin sauri wannan badakkare ya yi gaba ta re da kallon kafatanin aljanun nan ta re da fad'in, "Sarauniya Oumul Sahwat ta na yi ma ku albishir kukan Ku da fargabarku ya k'are daga yai domin ta samo maganin damuwarku bayan tsawon shekaru sha takwas da wani la'ananne a cikin mu ya nai mi jefa mu cikin masifa. Kuma ta yi alk'awarin zartar da hukunci cikin gaggawa ga dukkanin mai taimakawa wannan d'an iska da ya jawo mana afkuwar yak'in da zai kashe mana masarauta da kuma y'ancin mu. Don haka yanzu za ta fara hukunci ga mahaifiyarsa wacce ta kasance ita ma ta na taimaka masa har a wani karo ta yi mummunar kuskure wajan kwaikwayon halitta da fuskan shugabar mu wajan taimakon bil'adama wanda kowa a nan ya san an rubuta wani yarjejeniya wanda kakan shugabarmu ya saka hannu da jinin jikinsa akan babu mu ba shiga duniyar bil'adama. Sai dai an sa mu mai kunnan k'ashi cikin mu ya karya wannan doka ta re da shi da mahaifiyarsa da kuma mahaifin mahaifiyarsa wanda dukkaninsu sun kasance zuri'ar amintaccan bawan wannan masarauta. Don haka yanzu za su fara fuskantar hukunci". Gaba d'aya aljanun nan su ka shiga ihu su na fad'in, "Hukunci! Hukunci!! Hukunci!!! Sai sun fuskanci hukunci". Kallon wannan badakkare Oumul Sahwat ta yi ta re da jinjina kan ta. Kaifaffiyar doguwar wuk'a ya zaro daga k'ugunsa ya saita k'eyar mahaifiyarsa Yousouf wacce ke hawaye ta na kallon Yousouf d'in ta re da girgiza masa kai ta na kuma furta "kar ka karaya ko sun kashe ni" a leb'anta. Sai da ya d'aga wannan wuk'ar sama ka na ya aza da k'arfi bi sa k'eyar mahaifiyar Yousouf sai da jini ya yi tsartuwa ta re da wanke fuskan Yousouf ka na kan ya fita daga gangan jikinta ya gungura k'asa. Gaba d'aya aljanun nan su ka d'au shewa da ihu ya yin da Sabrin da Binty su ka sa ke zubewa k'asa sumammu karo na biyu. A gigice su ka farfad'o sakamakon wani irin ruwan sanyin da su ka ji a kan fuskokinsu da wannan badakkare ya zuba masu. Yousouf kuwa wani irin zabure-zabure ya fara yi ta re sa fizge-fizge jijiyoyin jikinsa sun yi burd'un burd'un yayin da idanuwansa su ka koma kamar garwashin wuta. Julaibib kuwa ji ya yi gaba d'aya tsoro ya fice a ranshi sai wa ni irin tsana da yaji ya na yi wa Oumul Sahwat na kisan gillar da ta yi wa mahaifiyar Yousouf. "Ke azzaluma ce wacce ba ta tsoran Allah. Muguwa kuwa in Allah ya yarda k'arshan ki ya zo don sai na yi sanadiyar ajalinki". Fad'in Julaibib cikin fusata har jikinsa ya soma rawa. Wani irin d'agowa Oumul Sahwat ta yi ta kalli cikin idanuwarsa ya yin da Badakkare ya yi kan shi don sare wuyansa. Sai da wani tsawa da ta daka masa shi yayi saurin dakatar da shi. Jikinta na b'ari ta mik'e cikin iska ta re da nufar in da Julaibib d'in ya ke babu kwayar zarra na tsoro a fuska da zuciyarsa. "Ciro abunda ke wuyarka ka mik'o shi kan tafin hannu yanzu". Fad'in Oumul Sahwat cikin ba da umarni. Wani k'ask'antaccan kallo ya watsa mata ta re da fad'in, "Ba ki isa ba, domin ni ba kya mulkata. Wad'annan su za ki yiwa umarni su bi ba Julaibib ba". Ya k'arisa maganar ya na nuna aljanun da ke tsattsaye wajan. Saurin dafe saitin zuciyarta ta yi saboda jin alamun k'arasowar Sarauniyar Daulatul Bahshan wato Bak'ayatul Mahruri da tawagarta. Cikin sauri ta juya ta re da nufar in da Yousouf ya ke ta zaro wannan takobi a cikin naman hannunta da ke da tsini da tsawo ta soka shi a gefen cikin Yousouf sai da ya fito ta baya ta re da mik'a tafukan hannunta wanda ya yi dogo gar gaban Julaibib ta re da fad'in d'aura min sarkar nan a nan ko ya bar duniya". Cikin sauri Yousouf ya d'ago su ka had'a idanuwa da Julaibib ta re da fad'in, "Idan har cikin zuciyarka ka na k'aunar Rukhsana ina nufin Binty da gaskiya har zuciyarka to ka da ka ba ta abunda mahaifiyata ta ba ka, shi ne lagonta don da shi ba za ta tab'a iya cin galaba a kan ka ba, kuma ko da ta yi maka barazana da wad'anda su ke ta re da kai, ka da ka ji tsoro domin da wannan abun da ke wuyanka babu abunda za ta iya ma su". Fad'in Yousouf daidai lokacin da ta d'aga mashin nan ta so ke shi ta cikin ramin cibiyarshi sai da gudan jini ya fito daga bakinsa............. 🌹 *77-78*🌹 ...............B'angaran Anna kuwa bayan sun ko ma gida hankali ta she ta re da tunanin halin da Binty ta ke ciki da kuma inda sauran y'ay'anta su ke. Fanan kuwa da Anna ke shaida mata duk abubuwan da su ke faruwa, fitsari ta saki a tsaye ba ta re da sanin ta na yi ba saboda firgici da tsoro. Alhaji Usman kuwa, komawa State CID ya yi don shaidawa DG ko mai za'a yi a yi don ganin y'ay'ansa sun dawo gare sa. Hakan ne ya sa aka tsanantawa dukkannin su azaba mai gigitarwa da fitar hayyaci akan sai sun fad'i in da su ka kai su Julaibib, musamman Junaina wanda a gidanta su ka b'ace. An kira Alhaji Saifullahi ta re da kunna masa wannan video na confessing da matarsa da sauran gaba d'aya su ka yi. Kusan haukace masu ya yi a wajan nan ya na ihu ta re da fad'in duk in da y'ar shi ta ke sai an fito masa da ita. Da kyar aka kwantar da hankalinsa ta re da shaida masa duk in da su ke za'a gan su. Cikin hikima DG da alhaji Usman su ka shiga yi wa alhaji Saifullahi nasiha akan irin nu na banbanci akan y'ay'ansa da ya ke yi wanda haka na iya janyo muguwar rikici da tsana tsakanin y'ay'ansa ko da kuwa mahaifiyarsu d'aya. Sosai nadama ta shigi alhaji Saifullahi domin ya san idan da laifin Junaina to tabbas da laifinsa.