Ba ni da gata - Chapter 38
Ba ni da gata Chapter 38: Ba ni da gata Chapter 38. Abu kamar wasa an yi bincike matuk'a amma ba'a ga in da su Julaibib su ke ba, kuma bincike ya nuna ba…
3,058 words
Abu kamar wasa an yi bincike matuk'a amma ba'a ga in da su Julaibib su ke ba, kuma bincike ya nuna ba su fita daga gidan su Junaina. Wanda hakan ya k'arawa Junaina zargi da su kan su hajiya Mansura da Zuwairah tun da da ma su na cikin k'ungiyar asiri. Tu ni aka tura mota biyar ta re da jagorancin Hajiya Mansura wacce aka ce ta kira meeting d'in gaggawa wanda hakan shi zai ba da umarnin kwamushe duka sauran members d'inta. Sun yi nasarar kwamushe mata ak'alla za su kai guda Hamsin da uku, don motocin da su ka zo da shi ma bai isa ba sai da aka k'aro wasu duk aka watsa su kamar akuyoyi.
Anna alwala ta yi ita da Fanan ta re da yin sallah raka'a biyu su ka shiga yin addu'a akan Allah ya kare su a duk inda su ke.
*_____________________* A matuk'ar razane da mugun tashin hankali Julaibib ya yi wani irin tsalle ta re da isa wajan da Yousouf d'in ya ke a d'aure. Ya na tab'a wannan kaca da aka d'aure Yousouf da shi kacan ya zube k'asa, Yousouf d'in kuma ya taho gaba d'aya jikinsa ya na wani tari mai fidda guda-gudan jini. Tallabosa Julaibib ya yi idanuwansa sun cika da hawaye, jijiyoyin kansa sun yi burd'in-burd'in ya shiga k'ok'arin b'arke rigar jikin Yousouf d'in. Caraf Yousouf ya rik'e hannunsa ta re da fad'in, "Ka da ka yi k'ok'arin ceto na, ka d'auki Binty da sauran mutane ku gudu. Abun da ke wuyanka ba zai kare ka daga tsafi da takobin sarauniya Bak'ayatul Mahruri ba. Don Allah Ku gudu ka min ta shigo cikin masarautar nan". Fad'in Yousouf jini na b'ulb'ulowa daga hancinsa da kuma bakinsa. Mik'ewa ya yi ta re da sab'a Yousouf a kafad'arsa, ka na ya nufi inda su Binty su ke jikinsu na rama, kama hannun Binty ya yi ta re da kallon sauran ya ce ku biyo baya na, kuma ko wanne a cikinku ya rik'a karanta ayatul qursiyu da duk addu'ar da ta zo bakinku. Ka da Ku yadda bakinku ya yi shuru ba ya ambaton Allah". Gaba d'ayansu a tsorace duk su ka tsaya a bayansa. Ya yin da Oumul Sahwat ta tsaya a gaban Julaibib ta re da fad'in, "Za ka ja ni ka yi nasara saboda abun da ke wuyanka, amma ka sani ba za ka tab'a iya ja da Bak'ayatul Mahruri ba". "Allah ya fi ta domin shi ne mahaliccinta". Fad'in Julaibib ta re da yin gaba. Wani irin ihuu Oumul Sahwat ta yi wanda ya yi sanadiyar mutuwar aljanun dubu biyu. Ta shi sama ta yi ta re da rikita ta koma tsuntsuwa, sai da ta yi nisa a sararin samaniya ka na ta b'ace b'at.
Tafiya kawai su ke yi ba ta re da sanin in da su ka nufa ba cikin daji. Wani tsoho ne tukuf ya bayyana a gare su jikinsa duk jini idanuwansa na tsiyayar da hawaye. Nuni ya yi da hannunsa izuwa gangan jikin Yousouf, ta ke Yousouf ya ko ma hannunsa, shimfid'ar da shi ya yi a k'asa ta re da shafa fuskanta. Bud'e idanuwa Yousouf ya yi cike da azaba ya na kallon kakan na sa kuma ya na murmushi kamar bai jin azaba a jikinsa. "Ya kai jika na, ka da ka tafi ka bar ni. Kai ka d'ai ka rage a cikin tsatso na. Y'ata ta mutu ta bar wannan duniyar duk a sanadiyar taimakon bil'adama. Ya Allah ka sa haka ya zama silar shigarta Aljanna". Da gudu Binty ta isa in da Yousouf d'in ya ke a kwance ta na kuka ta re da fad'in, "Ka da ka mutu ka bar ni masoyi, ka manta alk'awarin da mu kai wa junan mu ne? Mun yi alk'awari za mu ra yu da junanmu duk rintsi. Kalla zoben da ka saka min, kalli wanda na saka maka a hannunka". Fad'in Binty ta re da d'aga d'an yatsarsa wanda zoben ke mak'ale. Murmushi ya sakar mata mai cin rai ta re da fad'in, "Mai sona, tabbas ina k'aunarki kuma zan mutu da sonki. Sai dai idan har na kasance da ke Allah ba zai bar ni ba domin na cutar da ke. Wanna na daga cikin wasiyya na k'arshe da mahaifiyata ta bar min akan ka da na bari tsokar da ke k'irjina ta rinjaye ne. Ba zai yu mu rayu ta re ba saboda jinsin mu ba d'aya ba ne. Sai dai ina miki albishir don ki na da wanda ya ke miki k'aunar da na ke miki ko in ce fiye da ni ma". Ya k'arisa maganar ne ta re da kallon fuskan Julaibib ka na ya ce, "Yaya Bibi ga ta nan ka amana, don Allah ka kula da ita fiye da yadda za ka kula da kan ka dan Allah. Ka ba ta soyayya ka da ta yi kuka domin ka". Idanuwan Julaibib ya rine kamar gauta sabida tsabar jan da ya yi. Bai iya cewa ko mai ba sai juya baya da ya yi saboda bai son hawayan da ya ke mak'alewa su zuba. Kuka sosai Binty ta ke yi ta na jijjiga Yousouf ta re da fad'in, "Kar ka bar ni, Yousouf kar ka bar ni dan Allahhhhh". Ta k'arashe maganar da wani irin narkakken kuka mai narka zuciyar mai sauraro. Sabrin ita kan ta kuka ta ke yi sosai ta re da jin tausayin Yousouf d'in da ita kan ta Bintyn. "Su waye iyayena?". Fad'in Binty cikin kuka ta na kallon fuskan Yousouf da shi ma fuskan na ta ya ke kallo. Kallo fuska kaka Yousouf ya yi shikuma ya jinjina masa kai. Dawo da kan shi ya yi wajan Binty wanda a ta re su ka yi haka don Julaibib don jin abunda Binty ta tambaya. Shi kan shi ya na son sanin haka. "Asalin sunan ki Rukhsana wanda haka na gani ajikin showel d'in da aka nannad'e ki da shi, kaka ya tsinci wannan a cikin jikinki". Ya fad'i hakane ta re da yink'uri ya girgiza jikinsa ya fiddo wani k'atotan kwarya wanda a cikinsa akwai kwalliyar d'awisu wanda aka yi sa kamar mafici da kuma wani awarwaro na zinari sai rigan sanyi na yara riga da wando. "Sauran bayani kaka zai miki shi". Hannunta na rawa ta karb'i wannan kwarya idanuwanta na k'ara kwararar da hawaye. Sai da ta d'ad'd'aga kayan ka na ta mai da dubanta izuwa ga kaka, kaka ya bud'e baki zai yi magana barrister Fu'ad ya ce, "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un!". Da mugun k'arfi ya yin da ya yi wani tsalle domin isa wajan da kaka ya ke ya ture sa, sai dai ka min ya har mashin da Bak'ayatul Mahruri ta jefo ya caki bayansa ya kuma b'ullo ta cikinsa har sai da ya tab'a cinyar Barr Fu'ad da ya isa gaban Kakan. Gaba d'ayansu mik'ewa su ka yi a razane ta re da ja da baya don ganin dandazon aljanun da su ka zagaye su. Hamdan rik'e hannun Julaibib ya yi da k'arfi ya na karanta ayatul kursiyyu ya yin da Binty ta sume sakamakon jinin kaka da ya fallatso ya wanke mata fuska. Barr Fu'ad kuwa k'afafuwansa ke wani irin rawa sakamakon tsoro da kuma azabar da ya ke ji a cinyarsa. B'akayatul Mahruri ce ta k'araso wajan ta re da yin kwallo da gawar Kaka sai da ya lula can sama ka na ya fado bisa bishiyoyin da ke dajin. Sai da ta saita takobinta ka na ta d'aga za ta cakawa Binty a zuciyarta, Julaibib ya yi wani irin tsalle don ture Binty takobin ya sa me shi amma sai Barr Fu'ad ya riga sa takobin ya caki k'irjinsa ta ke ya fad'i ko shurawa bai yi ba. K'arar ballewar wuyarta su ka ji wanda tsabar zuciya Julaibib bai san lokacin da ya yi bismillah ta re da murd'e wuyanta ba. Ta ke ta fad'i k'asa ta na shuru-shuren mutuwa. Yousouf gaba d'aya sauran jarumtarsa ya yi amfani da shi ta re da mik'ewa ka na ya d'auki takobin bak'ayatul Mahruri ya datse mata kai wanda ya yi sanadiyar rusunawar gaba d'aya dakarunta wa Yousouf d'in. Cikin azama Oumul Sahwat ta k'ariso wajan ta re da fad'in, "Lallai dole in mayar da kai matsayin kakan kakanka wato amintaccan bawan masarauta kasancewar jarumi wanda ya kashe azzalumar sarauniyar Daukatul Bahshan. Yanzu aljanun masarautar za su kasance cikin salama da.....". Bai bari ta k'arisa ba ya yi amfani da takobin hannunsa ya fille mata kai saboda hango yadda ta fille kan mahaifiyarsa. K'ok'arin fad'uwa ya ke yi Julaibib ya yi saurin taro shi ya fad'o jikinsa. Magana ya ke son yi amma ya kasa saboda jinin da ke kwararowa daga hancinsa, bakinsa da kuma kunnansa. K'ok'ari ya ke ta yi ka da ya kulle idanuwansa amma ya kasa. Jikinsa ne ya yi nauyi sosai har Julaibib ya ji nauyin ya masa yawa sai da ya kwantar da shi a k'asa idanhwansa na tsiyayar da hawaye. Wani irin guguwa ne ya taso mai k'arfi ya lullub'e su na kusan mintuna goma ka na su ka b'ace b'attt. A nan cikin garden su ka tsinci kan su kamar yadda anan aka kwamushe su. Sabrin sakin wani tsumamman kuka ta yi yayin da ta yi kan Binty da ke yashe a k'asa ba ta numfashi. Julaibib kuwa kan Fu'ad da ke zubda jini ta cikinsa ya yi kuma bai numfashi. Daga Hamdan har Sabrin d'in an rasa wa zai bai wa wani hak'uri. Wayarshi da ke aljihunsa ya ji ya na k'ara wacce ya ma mance da ita a jikinsa ya yi saurin fiddowa ta re da picking call d'in kasancewar daddy ne ya sake kira ko Allah zai sa ya dace. "Ku na ina Julaibib?". Fad'in daddy. "Daddy ka yi sauri akwai matsala mu na gidan su Sabrin". Fad'in Julaibib. Kasancewar alhaji Usman su na ta re da alhaji Saifullahi ta re su ka nufo gidan a mota daban-daban. Hankali ta she su ka nufo garden d'in. Sabrin na ganin mahaifinta ta nufesa da gudu ta rungume ya yin da Alhaji Usman ya yi kan Fu'ad da gudu wanda ke zubda jini. Fu'ad d'in ya fara sawa cikin mota ka na ya saka Binty ta re da kwantar da kan ta jikin motar. Sam ba su lura da wani mutum wanda a k'alla zai yi sa'a da alhaji Saifullahi a gefe ba sai wawware idanuwa ya ke yi ya yi wani irin bala'in rama ta re da fita hayyacinsa. Ko bi takansa ba su ba. Alhaji Usman ya shiga gaban mota ya yin da Julaibib ya zauna a baya ta re kwantar da kan Fu'ad a cinyarsa ya na jin tashin hankali cikin ransa. Alhaji Saifullahin ma sai mota ya nufa Sabrin ita ma ta shiga ta re da kayan Binty da Yousouf ya ba ta cikin kwarya. Hamdan bi ye da ita su ka nufi asibiti. Kai tsaye ICU aka nufi da Barr Fu'ad wanda Julaibib ya kasa shiga sai safa da marwa ya ke yi a ciki. Alhaji Saifullahi kuwa jikinsa rawa ya ke yi don idan Julaibib favourite d'in Anna ne, shikuma Fu'ad d'in ne fav d'in sa. Cikin hukuncin ubangiji doctor su ka samu ceto rayuwar Barr bayan sun masa theater don sakamakon wannan wuk'a da ya soke shi ya b'ula masa hanji. Lokacin da su ka fito daga theather nan k'arfe biyu da kwata na dare saboda sun matuk'ar dad'ewa a ciki tun magriba. Binty kuwa dama suma ta yi sakamakon firgici ita ma dai sai da aka k'ara mata ruwa. Sabrin ke zaune da ita. Hamdan kuwa ta re su ke safa da marwa da Julaibib.
............Can wajan Anna kuwa hankalinta ne ya tsananta tashi saboda ganin har biyu amma alhaji Usman bai dawo ba kuma ta kira wayarsa ta k'i shiga. Fanan ta yi kuka har ta na sik'ewa.
Sai da Alhaji Usman su ka yi sallar asuba ta re da tabbatar da farfad'owar Fu'ad ka na ya kira Anna ya shaida mata bayyanar su Binty ta re da fad'a mata Fu'ad na kwance a asibiti. Shi ma dai Alhaji Saifullahi ya kira Hajiya Sakna mahaifiyar Sabrin ta re da shaida mata halin da ake ciki.
*MANAGE PLEASE* 🌹 *79-80*🌹 ................Hajiya Sakna ta fito ne ta ga wannan tsamurarran dattijon ya na tafiya da kyar kamar iska za ta hure shi. "Bawan Allah, daga ina haka?". Fad'in mahaifiyar Sabrin ta na mai k'ara k'are masa kallo. Shi dai da idanuwa kawai ya ke bin ta saboda kamar kwakwalwarsa ya tab'u. "Inna lillahi wa'inna ilaihir raju'un! Shafi'u! Shafi'u!!". Hajiya sakna ta saki salati ta re da kwalawa driver kira wanda ya zo da gudu ta re da d'an rusunawa ya ce, "Ran ki shi dad'e ga ni. Wani wajan za'a kai ki ne? " Fad'in Shafi'u driver. Nu na wannan bawan Allahn ta yi ta re da fad'in, "Daga ina haka wannan? Yaushe ya shigo gidan nan?". Fad'in Hajiya Sakna ta na nuna shi. "Hajiya gaskiya tun jiya bayan fitar alhaji da hajiya k'arama da kuma wani bawan Allah da su ka fita babu wanda ya sake shigowa". Fad'in Shafi'u. Shuru Hajiya Sakna ta yi, can kuma ta d'auko wayarsa cikin jaka ta kira alhaji Saifullahi ta shaida masa komai. Cikin mintuna talatin ya dawo gidan k'urawa wannan bawan Allahn idanuwa ya yi ya na son ya ga ne ko ya san shi, amma Sam bai ga ne sa ba. "Bawan Allah daga ina?". Fad'in alhaji Saifullahi ta re da ware hannayansa ya na kallonsa. Still shuru sai zare idanuwa ya ke yi. "Ku fita da shi daga gidan nan yanzu" Fad'in alhaji Saifullahi. Hannunsa Shafi'u da mai gadi su ka yi ta re da tura k'eyarsa zuwa waje ka na su ka rufo k'ofa. Asibitin su ka koma, in da su ka taras Binty ta farfad'o sai kuka ta ke yi kamar ranta zai fita. Julaibibi ya shiga d'akin har da turo k'ofa. Hanky ya ciro daga aljihun wandonsa ta re da share mata hawayan da ke zubowa ka na ya ce, "Ki dai na kuka please, kukan ki a nan na ke jin sa" ya k'arisa maganar ta re da nu na zuciyarsa. Mai makon ta yi shuru sai ta k'ara sautin kukan na ta. Rungumo kanta ya yi zuwa k'irjinsa ya shiga bubbuga bayanta ya na mata magana cikin kunnanta. Anna ne da Fanan su ka shigo hankali ta she. Cikin sauri Alhaji Saifullahi ya taro su ya na mai kwantar da hankalin su. Sai washa gari aka ba su damar shiga d'akin da Fu'ad ya ke ciki wanda ta farfad'o sai wajan aikin da ke masa ciwo kad'an-kad'an. Su na had'a idanuwa da Binty ya sakar mata murmushi. Da gudu ta k'arisa wajan gadon ta re da fad'in, "Ya Fu'ad". Sai kuma ta fashe da kuka mai sauti Sabrin da ke gefe ita ma ta saki na ta hawayan. Fanan kuwa k'arisawa wajan Binty ta yi ita ma ta shiga tayata kukan. Da kyar Fu'ad ya iya lallashinsu wanda muryansa ke fitowa dakyar. Satinsa biyu a asibiti aka sallamesa, kuma dalilin ciwona ya sa aka aje komai a gefe har da case d'in su hajiya Mansura wanda ake son tura su koti domin ta yanke masu hukunci. Bayan sun dawo gida da kwana uku, mahaifin Sabrin da mahaifiyarta da ita kan ta Sabrin d'in da kuma y'ay'an aunty Junaina duk su ka d'ugunzuma state CID wanda tu ni Alhaji Usman da iyalansa sun isa can. Videon su Kandala aka sa ke kunnawa, hajiya Sakna da y'ay'an Junaina da kuma Sabrin da ba su ga ni ba su ka sa ke gani. Amrah ba ta gigice ba kamar yadda Hanan ta gigice ba sakancewar ita ta san abunda uwar ta su ta ke aikatawa. Hanan kuwa ihun tashin hankali ta rik'a yi har sai da aka fidda ta zuwa mota. Julaibibi kuwa ji ya ke yi kamar ya fiddo su Kandala ya kashe su. Daga nan gaba d'aya gida su ka dawo anan side d'in bak'i da ke gefen side d'in Anna. Barr Fu'ad shi ya zayyane ma su abunda ya faru a can duniyarsu Yousouf. Gaba d'aya al'ajabi da mamaki ya gama kashe su wanda gaba d'aya sun ka sa magana. Kwaryan da Yousouf ya baiwa Binty, Sabrin ta aje a gaban Anna. Anna ce ta d'auki kwaryan ta re da fiddo kayan ciki ta shiga dubawa. Maficin d'awisun ta d'aga ta yi ta jujjuya shi. Murmushi ta yi ta re da mai da kayan cikin kwaryan ka na ta ce, "Allah ya bayyanar da iyayanki a duk in da su ke". Gaba d'aya da amin su ka amsa ka na Anna ta shiga yi wa Binty fad'a akan b'oye mata wasu abubuwan da ta yi. Daga nan ma ta koma kan Sabrin ita ma ta yi mata fad'a akan duk abubuwan da ta ke yi duk da dai sun ji har da sharrin sammu. Sosai ta ke kuka ta re nuna tsantsan nadama da kuma rok'ar gafarar mahaifiyarta. Shi ma alhaji Saifullahi ya rok'i gafarar mahaifiyar Sabrin. Ta na kukan jin dad'in shiryuwar d'iyar tata ta ce, "Na ya fe mu ku duka, Allah ya yafe mana baki d'ayan mu".
Julaibib kuwa hankalinsa ne ya tafi wani waje sabida kallon k'urillan da ya yi ta maficin d'awisun nan da kuma tuno tambarin d'awisun da ya ga ni a k'eyar Binty ranar da ta b'ace ba'a ganta ba. "To wacece wacce na ke ga ni a wonderland?". Fad'in Julaibib cikin zuciyarsa.
Bayan Binty ta kasance ita d'aya a d'aki ta fad'a duniyar tunanin ta yadda za'a yi ta gano iyayanta da kuma dalilin yar da ita a bola.
B'angaran Fu'ad kuwa ya yi k'ok'ari sosai wajan cire Binty daga cikin zuciyarsa kasancewar ganin soyayyar Bintyn b'aro b'aro cikin idanuwar wan na shi. Sai ya shiga avoiding zama kusa da Binty gudun ta da mashi da miki. Gidan ma gaba d'aya ya dai na zaman sa kullum sai bayan isha ga ke shigowa.
............Kallon tafin hannunsa na dama ya yi ta re da k'urawa rubutun da ke hannun na sa don sanin abunda mahaifiyar Yousouf ta rubuta. Sai dai bai fahimci komai ba. Kallan ruwan zam-zam d'in da ke gabansa ya yi ta re da d'auka. Sai da ya yi bismillah ta re da karanto ayatul kursiyyu ka na ya wanke tafin hannun cikin wani k'aramin jug sannan ya tsiyaye a cikin gora.