Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 39

Ba ni da gata - Chapter 39

Ba ni da gata Chapter 39: Ba ni da gata Chapter 39. Aje goran ya yi ta re da shiga cikin bayi don yin kana ya tafi gidan Alhaji Muhammad Ahlam don kai wa…

3,415 words

Aje goran ya yi ta re da shiga cikin bayi don yin kana ya tafi gidan Alhaji Muhammad Ahlam don kai wa Yousouf maganinsa da mahaifiyar Yousouf ta ba shi. Cikin rabin awa ya gama kimtsawa cikin wata gezna dark blue ta re da hula bak'i sai takalminsa halve cover kalar bak'i wanda samansa ya sha stone masu walwali. Kai tsaye fitowa ya yi ya nufi side d'in Anna. Sai da ya kwankwasa sannan ya tura ta re da shiga ciki. Zaune Binty ta ke a kan 1sitter. Riga da straight skirt ne a jikinta irin na y'an kanti. Ba bu d'an kwali a kanta parking d'in gashinta ta yi a tsakiyar kan ta. D'an ramar da ta yi ya k'ara fito da haske da kyawunta earpies mak'ale a kunnanta ta na sauraran wa'azin Yousouf Guruntum mai su na (MAZINACIYA JAKAR GAYU). Har ya iso kan ta ba ta sa ni ba sabida hankalinta gaba d'aya da ta tsayar a wajan wa'azin da ta ke ji. Hannu ya kyasta a fuskanta ta re da zare earpiece d'in kunnanta. Cikin sauri ta d'ago ta kalle shi ta re da saurin mik'ewa tsaye ta na rarraba idanuwa. D'age mata gira ya yi ta re da fad'in, "Mi ye na tsoran to? Ni dodo ne?". Fad'in Julaibib. "Bbb.... Ba komai?". Fad'in Binty cikin in'ina. "Za ki raka ni?". Fad'in Julaibib ya na matsota kamar zai had'e jikinsa da na ta. "A'a". Fad'in Binty had da girgiza kai. "Mai ya sa to?". Julaibib ya sa ke fad'i ta re da kuma matso ta kad'an. "Zan yi aikin a kitchen ne. Zzan yi girki?". Fad'in Binty ta na mai zama jab'ar akan kujeran saboda k'ara matsowa da ya yi. Sabrin da ke mak'ale a bakin k'ofar kitchen sai gimtse dariya ta ke yi sabida kan ya Bibi ya ganta. D'aga k'afarsa ya yi ta re da d'aurawa a kan kujera ta re da fad'in, "Baki ce na yi kyau ba. Na yi kyau??". "Ka yi kyau!". Fad'in Binty da sauri don sabon yanayi da Ya Bibin ke mata kwanan nan. "Ki kula da kan ki, idan na dawo za mu yi hira kin ji". "Ttttt to". Fad'in Binty baki na rawa cike da mamaki. Hura mata iska a fuska ya yi ta re da sauke k'afarsa ya juya ya nufi upstairs don zuwa wajan Anna. Doguwar ajiyar zuciya ta sauke ta re da murgud'a baki ka na ta mai da earpiece d'inta. "Babi!". Fad'in Fanan ta re da nufota da gudu ta rungumeta ta na mai jin dad'i. "Ke dalla menene kuma haka? Menene Babi kuma?". Fad'in Binty. "Au duk kallon Indian ki ba ki san menene Babi ba? To ki je ki yi searching". Fad'in Sabrin ta re da nufar kitchen ta na fad'in, "Kaho na pyar ri heee". Ta fad'i hakane ta re da rungume hannunta a kirjinta.

.............."Ummu Julaibib kin tabbata da abunda ki ke fad'amin kuwa?". Fad'in Alhaji Usman. "Eh to, ban tabbatar ba, shiyasa na ke so na je na yi confirming. Shiyama ko a wancan lokacin ban ce komai ba. Amma gaskiya ban kaso sittin ina ji a jiki na ita ce". Fad'in Anna. "To yaushe za mu tafi kenan?". Fad'in Alhaji Usman. "Nan da sati d'aya idan an gama case d'in su Suhail". Fad'in Anna. "Akwai fa abunda ban fad'a miki ba, na saki Mansura saki uku, domin ba za'a yanke mata hukunci da aure na a kan ta ba. Alhaji Saifullahi shi ma ya saki matarsa saki uku kuma ya hana y'ay'ansa ganinta. Na yi na yi da shi ya bar su su je su ganta ya ce su ma y'ay'an ba su son ganinta". "To Allah ya kyauta". Shi ne abunda Anna ta fad'a dai dai lokacin Julaibib ya yi sallama a k'ofar d'akin.

Amsa masa sallamar su ka yi ta re da ba shi izinin shigowa. Shiga ya yi ta re da mai man waje ya zauna, sai da ya gaishe su ka na ya ce, "Daddy zan je gidan baba Muhammad in kai wa Yousouf maganinsa". "Alhamdulillah! Da na tun tuni na ke son yi maka magana ka hanzarta ka kai masa don yaron na jin jiki sosai. Allah ya sa dai k'arshan wahalar kenan". A ta re Alhaji Usman da Anna su ka amsa da "Ameen". "Julaibib yaushe za ka fito da matar aure? Na gaji da ganin ka haka wallahi". Fad'in Alhaji Usman. Sosa k'eya ya yi ta re sa sunkuyar da kai ka na ya ce, "In sha Allah nan kusa daddy". Fad'in Julaibib. "Ka bar shi ga shinan ai har k'anwar shi za ta yi ta bar shi ai". Fad'in Anna. "Anna wata k'anwar ta wa ce za ta yi aure?" Fad'in Julaibib. "Binty ce ta samu mijin aure". Fad'in Anna. "Binty kuwa? Yaushe? Waye shi wannan mara kunyar? Kuma kun yarda Anna. Ni wallahi ban yarda ba yasin". Fad'in Julaibib hankali ta she. Anna da Alhaji Usman gimtse dariyarsu su ka yi, ya yin da Anna ta ce, "Kai a wa kenan da za ka ce baka yarda ba". "Auranta zan yi, wallahi ina son ta tun ranar da fara ganinta. Anna dan Allah Ku taimake ni ka da in rasa Binty". Anna da Alhaji Usman sun kasa rik'e dariyarsu su ka bushe da dariya. Sai alokacin Julaibib ya ga ne tsokalarsa su ye yi. Saurin mik'ewa ya yi ta re da ficewa daga d'akin.

Kai tsaye gidan Alhaji Muhammad Ahlam ya nufa. Kasancewar ya kira alhaji Muhammad d'in ya shaida masa da zuwansa. Ya na isowa aka shiga da shi d'akin da Yousouf ya ke a kwance kamar gawa. Sai da yi addu'a sosai ka na ya bud'e bakinsa ta re da tsiyaya masa cikin bakinsa dakyar kasancewar ya dates bakinsa. Cikin hukuncin ubangiji ko minti d'aya ba'a yi ba k'afafuwansa su ka fara motsi. Daga bisani ya d'aga hannunsa na dama. Can kuma ya juyo da kansa bakinsa na motsawa ya na karanto salati ta re da mik'ewa ya zauna digirgir. Gaba d'aya gidan nan ya haukace da ihun murnan Yousouf ya dawo cikin hayyacinsa. Ya na mik'ewa ya yi sujjada ta re da fashewa da kukan murna. Nan aka yi ta murna da koke-koke. Sab'ule jikinsa ya yi ta re da guduwa don barin y'an uwa su yi murna da kyau.

A hanyarsa na dawowa wajan traffic kasancewar an dakatar da shi. Juya kansa ya yi ya kalli gefe ta re mayar da kan shi ga titi. Cikin sauri ya k'ara kallon gefen da ya kalla. Tabbas ita ce dai dai lokacin kuma aka ba su umarni su wuce. Da wani irin gudu ta figi motar, shi ma kuwa da gudu ya bi bayan motar kamar. A wani katon gate ta yi horn mai gadi ya wangale mata gate d'in. Ta na danna hancin motar shi ma ya na biye da ita a baya.

*PAID BOOK 08128755583* 🌹 *81-82*🌹 ...............Har zai tura motar cikin gidan sai kuma wani zuciyarsa ta hane sa. Dakatawa ya yi ta re da yin reverse ya yi parking ta re da fitowa daga cikin motar. Wajan driver ya nufa da sauri wanda ke k'ok'arin rufe gate d'in. "Bawan Allah dan Allah minti d'aya". Ya fad'a ya na d'an yin gaba. Washe baki mai gadi ya yi ta re da fad'in, "Ai na san mai ya kawo ki, ai Rauhiyya haka ta ke had'a go-slow a cikin gidan nan. D'aga kai gare ta ga yauk'i kamar kub'ewa. Amma ai na ga kai d'in ka had'u watak'ila kai ka yi da ce". Fad'in mai gadi ba ta re da an tambayesa ba. "Nan ne gidan su kenan?". Fad'in Julaibib ya na kallon cikin gidan cike da tsananin mamakin kenan Binty twins ne. "Eh nan ne gidan iyayanta". Fad'in mai gadi. "Nagode da ma abunda zan tambayeka kenan". Fad'in Julaibib ta re da komawa wajan mota ya shiga.

Kai tsaye gida ya nufa cike da tunanuka cikin ran shi. "Rauhiyyah!" Ya maimaita sunan cikin zuciyarsa ya na mamakin wannan wani irin suna ne. A duniyar aljanu Yousouf ya ce masa ainahin sunan Binty Rukhsana, sai ka ce wasu india, yanzu kuma ya ji wani wai Rauhiyyah. Ya na isa gida ya haura sama. Anna na nan sai dai alhaji Usman bai nan. Knocking bedroom d'inta ya yi, ita kuma ta ba shi izinin shiga. "A'ah, har ka dawo?" Fad'in Anna. "Anna ni fa ina tunanin na ga iyayan Binty na asali". Fad'in Julaibib. Zaro idanuwa Anna ta yi ta na kallonsa ta re da fad'in, "A ina kenan? Ya aka yi ka san su d'in iyayanta ne? Wani alama ka gani?". Fad'in Anna. Nan ya kwashe labarin Rauhiyyah tun ranar da ya fara ganinta a wonderland har zuwa yau da ya bi ta a baya. Anna har ta na watsar da kayan da ke hannunta wajan mik'ewa tsaye. "Maza muje ka kai ni gidan yanzun nan". Ta fad'i hakane ta na lalubar wayarta a kan gado ta dannawa alhaji Usman Kira ta re da shaida masa abunda Julaibib ya fad'a mata. "Ku jira gani nan zuwa yanzu mu tafi ta re". Fad'in Alhaji Usman. Katse wayar Anna ta yi ta re da fitowa daga bedroom d'in Julaibib bi ye da ita a baya. D'akin Binty Anna ta shiga ta re da fad'in, "Binty fito za muje wani waje yanzu". Caraf Fanan ta ce, "Anna ni ma za ni dan Allah". To duk ku fito my tafi. Gaba d'aya parlourn k'asa su ka sauko dai-dai lokacin da Barr Fu'ad ya shigo d'akin shi ma. Nan Anna ta shiga shaida masa an gano iyayan Binty. Sosai ya ji dad'in ya kuma ce ta re da shi za'a je. Fanan ma sai murna ta ke yi an gano iyayan Binty. Binty kuwa ba za ka ce ka yanayin da ta ke ciki ba. Walau farin ciki ko akasin haka. Cikakkiyar mintuna talatin ba'ayi ba Alhaji Usman ya shigo gidan. "Ni fa duk na rud'e Na'ima, ya aka yi hakan to?". Fad'in alhaji Usman ya na kallon Anna. "Shssssss! Muje ka wai" Fad'in Anna. Gimtse sauran maganarsa ya yi, ya yin da Barr Fu'ad ya kalli Julaibib, shi kuma Julaibib ya kalli Anna da Daddy. Anna d'aura fuska ta yi ta re da yin sama ta d'auko wannan kwarya da Yousouf ya baiwa Binty ka na ta fito. Fanan ta rik'o hannun Binty su ka fice. Julaibib shi ne na k'arshan fita ya na son ga no abunda su Anna ke b'oyewa amma ya kasa kuma tabbas ya san da wata a k'asa. Shi ya masu jagora har gidan da ya ga mai kama da Binty wato Rauhiyyah. Horn ya yi mai gadi ya wangale gate su ka shi ga ta re da parking ka na gaba d'ayansu su ka fito. Hannu Julaibib ya d'aga ta re da yafito mai gadi. Cikin sauri ya k'ariso wajansu. "Ahh! Hajiya wallahi ban ga fitarki ba, ta ina ki ka fita to?". Fad'in mai gadi ya na kallon Binty. D'auke kai Binty ta yi ba ta re da ta fahimce abunda mai gadin ya ke nufi ba. "Dan Allah sallama za ka yi mana da mai gidan nan idan ya na nan". Kallon Binty mai gafi ya sake yi ya na son cewa ga Rauhiyyah ai ba sai ya yi masu iso ba. Amma kuwa sai ya juya ta re da nufar cikin gidan. Danna k'ararrawar k'ofar ya yi, second goma wani kyakkyawan yaro ya zo ya bud'e masa k'ofar. "Fakarar yaron kirki kai ne?". Fad'in mai gadi. "Ni ba sunana Fakahar ba Fakhri, understand?". Fad'in kyakkyawan yaron. Washe baki mai gadi ya yi ta re da fad'in, "To fakare, wasu bak'i ne a waje ke sallama da Babanka su na waje, amma fa har da auntynka Rauhiyyah". "Aunty na na d'aki ta na wanka. Ba ita ba ce". Fad'in Fakhri. "To je kira babanka ka ce ya yi bak'i". Fad'in mai gadi ba don ya yarda da abunda Fakri ya fad'a ba. Zai juya kenan ya hango Rauhiyyah sanye da doguwar rigar material pitch colour kan ta sanye da hula mai kunnuwa hannunta rik'e da laptop ta na dannawa. "Wa'innahu sulaimanu!". Fad'in mai gafi ta re da mitsittsike idanuwa ya na k'ara dallarosu ya na kallon Rauhiyyah da har ta zauna a kan kujera ta mai da laptop d'in bi sa cinyarta ta na danne-danne. "Aunty Rauhiy, wai Bala ya ce wasu na nai man daddy kuma har da ke a wajan". Fad'in Fakhri. D'ago da idanuwanta ta yi wanda ke d'auke da zara-zaran gashin idanuwa ta sauke a kan bakin k'ofar ta re da fad'in, "Kai ban san shirme, zo ka wuce ka je ka fad'awa daddy ya yi bak'i awaje". Ta fad'i hakane ta re da mai da kallonta izuwa ga laptop d'in ta. Cikin sauri mai gadi ya juya ta re da nufar wajan da su Binty su ke domin tabbatar wa idanuwansa abunda ya gani. Har ya na tuntub'e saboda tsabar kallon da ya ke wa Binty. "Matsowa kusa ya kamata ka yi sai ka k'are mata kallon da kyau". Fad'in Julaibib fuska a d'aure. "Auu... Ummm amm yanzu zai fito in sha Allah". Mai gadi ya sake fad'i har ya na cin tuntub'e saboda kallon Binty da kuma mamakin kamannin da su ke yi da Rauhiyyah idan akwai abunda ya fi y'an biyu to sun fi haka. Tsayin, hasken fatan, kamannin da yanayin k'iran jikinsu duk iri d'aya ne. Juyawa Binty ta yi ta had'a kai da mota dai-dai lokacin da wani mutum fari tass dogo siriri ya fito hannun shi sab'e da wata kyakkyawan yarinyar da ba za ta wuce 3years ba a kafad'arsa fuskansa fad'ad'e da farara. "Assalamu alaikum, sannunku da zuwa". Ya fad'a ya na mai mik'awa Julaibib da Fu'ad hannu. Daddy ma saurin mik'a masa hannunsa ya yi su ka yi musabaha. Anna ma ta yi saurin gaishe sa, dai-dai lokacin da Binty ta juyo kuma idanuwansu su ka had'u cikin na juna. Yarinyar da ke hannunsa sai da ta kusa sub'ucewa Julaibib ya yi saurin taro ta. Bakinsa na rawa ya ke nuna Binty da ita ma kallon na sa ta ke yi, "Rauhiyyah! Wannan ai Rauhiyyah ce. Amma kuma ai a parlour na baro ta ta na danna laptop". Dafasa Alhaji Usman ya yi ta re da fad'in, "Kwantar da hankalinka, abunda ya kawo mu kenan, wannan ba Rauhiyyah ba ce, kamannin jini ka ke gani". Shuru bawan Allahn nan yi jikinsa na b'ari ya na kuma k'ara kallon Binty da ita ma shi d'in ta ke kallo. Da ky'ar ya iya bud'e baki ya ce, "Muje daga ciki to". Ya fad'i hakane ta re da yin gaba su na biye da shi a baya. Amma duk tafiya sai ya juyo ya kalli Binty. Parlourn bak'i ya kai su ka na ya fito kasancewar yarinyar da ya rik'o a ta na hannun Julaibib. Har da gudu-gudu ya k'arisa gaban k'ofar part d'in cikin gidan ta re da murd'a handle d'in ya shiga. Da gudu ya haura sama. Rauhiyyah da ke danne-danne ta d'ago ta kallesa ta na mamakin mai ya faru ya saka Da-da gudu haka. "Rahima fito fito ki zo muje ki ga abun al'ajabi da mamaki yau". Fad'in Da-da ya na mai ka mo hannun matarsa da ke bakin gado ta na warware wani zani. Sakin zanin ta yi ta re da bin sa a baya. Su na saukowa parlourn ya kamo hannun Rauhiyyah da d'ayan hannunsa. Aje laptop d'in ta yi ta re da bin sa ba ta re da ta ce ko mai ba. Parlourn bak'in su ka isa gaba d'ayansu. Numfashin Rahima kusan tsayawa cak ya yi sakamakon arba da Binty da ta yi. Yayin da Fu'ad, Binty, Fanan, da Anna su ka mik'e cike da zallar mamaki su na kallon Rauhiyyah da ke tsaye a bakin k'ofa. "Inna lillahi!". Fad'in Fu'ad cike da wani irin mamaki kamannin Binty da Rauhiyyah. "Binty! What am I seeing. Subhanallah! Wallahi komai iri d'aya". Fad'in Fanan. Binty kuwa a hankali ta ke takawa har gaban Rauhiyyah ta re da kama hannunta hawaye na zuba daga idanuwanta. Rauhiyyah kuwa kallon zallar mamaki ta ke yi wa Binty ko kyaftawa ba ta yi. "Qalby da ma ba ni kad'ai ki ka haifa ba? Da ma mu twince ne? Ya aka yi haka?". Fad'in Rauhiyyah ta na kallon mahaifiyarta hawaye na ziraro daga idanuwanta. Wani irin rushewa da kuka Rahima ta saki ta re da k'arisawa ta rungumesu duka a jikinta kamar ranta zai bar jikinta. "Shikenan lokacin rabuwarmu ya yi Rauhiyy. Dan Allah ka da ku kwace Rauhiyy ku bar min ita har na aurar da ita". Fad'in Rahima ta na kuka sosai. Kallon kallo aka shiga yi tsakanin Julaibib, Fu'ad da kuma Fanan. Anna da Daddy kuwa wani murmushin da su kad'ai su ka san nufinsa su ka yi. "Qalby mai ki ke fad'i haka? Kamar ya su bar miki ni har ki aurar da ni, mai hakan ya ke nufi? Dan Allah ka da Ku ce min ba Ku kuka haife ni ba". Fad'in Rauhiyy ta na kuka sosai da ya zawo hankalin Mas'ud da fitowarsa kenan daga part d'insa zai shiga main part. Cikin sauri ya k'ariso parlourn don sanin abunda ke faruwa. Cak ya tsaya har ya na wani lilo kamar zai kifa k'asa saboda gigicewa da kuma mamakin ganin Rauhiyyah ta zama biyu. Hannu biyu ya kai ya yi weaving a dai-dai fuskan su duka don ganin idanuwansa ke masa gizo, ko kuwa dagaske ne. "Momma dan Allah idona ne ke da matsala ko kuwa abunda na ke ga ni gaskiya ne?". Fad'in Mas'ud. "Dan Allah duk ku nutsu ku zauna ayi komai dalla-dalla. Ku nutsu dan Allah". Fad'in Alhaji Usman. Kowa samun waje ya yi ya zauna ya yin da Mas'ud d'osana d'uwawunsa ya yi a kan kujeran don ya na cikin mamaki kuma ya na buk'atar a warware masa komai. "Dan Allah bawan Allah mu na san jin ta yadda wannan yarinya ta zo hannunku". Fad'in Alhaji Usman ya na kallon bawan Allahn nan. Ajiyar zuciya ya saki ta re da fad'in, "Mu y'an asalin Adamawa state ne, aiki ne ya dawo damu nan garin shekaru sha bakwai bakwai da su ka wuce. Tun bayan haihuwar Mas'ad Allah bai sa ke ba mu haihuwa ba wanda shi kan shi Mas'ud d'in sai da mu ka shekara Bihar ni da matat ka mun Allah ya ba mu cikinsa. Mas'ud sai da ya cika shekara bakwai sannan matata ta sa ke samun wani cikin. Lokacin da cikinta ya isa haihuwa, cikin dare wajajan sha biyun dare nak'uda ya ka ma ta. A rud'e na d'au mota mu ka nufi asibiti mafi kusa da mu. Muna zuwa cikin ikon Allah ta haihu lafiya sai dai d'iyar ba ta zo da rai ba, matata ta yi kuka sosai saboda ta kwallafa rai musamman ma da ta kasance mace kuma ta na son d'iya mace.. Kasancewar matata ta haihu lafiya sai ta ce a ba mu gawar kawai mu koma gida tun da dai lafiyar ta k'alau. Haka aka yi duk da sun so rik'e mu zuwa safe. To ahanyar mu ta dawowa mota ta tsaya mana dai-dai wajan wani bola, fitowa na yi don duba motar gashi dare ya yi don d'aya ta wuce da minti arba'in. Kukan jariri muka ji wanda ya firgita mu don duk a tunanin mu jaririyarmu ce. Sai dai jin kukan ba daga cikin mota ya ke fitowa ba sai hankalinmu ya k'ara tashi. Ita ta umurce ni da na duba kasancewar shekarar an yi yayin haihuwa a jefar da jariri. Cikin sauri na zagaya na aikuwa na yi arba da jaririya sanye cikin kayan sayin nannad'e da showel da kuma wani mafifici na d'awisu da kuma warwaro na zinari wanda aka rubuta sunan jaririyar a tsakiya. A nan ne muka san asalin sunanta kuma ba mu canza mata ba, yanzu haka ma su na d'aki na zan d'auko su. D'auko jaririyar na yi na kawo wa matata cikin mota. Cikin ikon Allah ina shiga na kunna motar ta ta shi mu ka nufi gida. Cikin daran nan muka yanke hukucin rike ta. Kuma a daran matata Rahima ta so ma shayar da Rauhiyyah wanda haka ya k'ara shak'uwa tsakaninsu. Kuma ba mu shaidawa kowa cewar ba y'ar mu ba ce. Washagari mu ka na sanar da dangi da abokai cewar ta haihu y'an biyu amm d'aya ba ta zo da rai ba. Sosai aka yi shagalin suna, cikin ikon Allah kuwa ba mu cika shekara ba aka canza min wajan aiki zuwa nan garin abuja".

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull