Kenza eBookz

Ba ni da gata - Chapter 40

Ba ni da gata - Chapter 40

Ba ni da gata Chapter 40: Ba ni da gata Chapter 40. ..........Mik'ewa Rauhiyyah ta yi jikinta na rawa, can kuma ta tafi luuuuu ta suma. Cikin sauri…

3,372 words

..........Mik'ewa Rauhiyyah ta yi jikinta na rawa, can kuma ta tafi luuuuu ta suma. Cikin sauri Julaibib ya shiga ba ta taimakon gaggawa. Ba ta jima ba ta farfad'o ta na sakin kuka ta re da k'ank'ame uwar rik'onta ta na wani irin narkakken kuka. "Qalby ki ce mafarki na ke yi dan Allah. Ku ce ku ne ainahin mahaifa na dan girman Allah. Zan mutu idan Ku ka ce ba ki ne iyaye na ba". Fanan da Binty, Anna da mahaifiyar rik'on Rauhiyyah kuwa kuka su ke yi su ma sabida Rauhiyyah ta ba su tausayi sosai. Dakyar aka su daddy su ka lallashe su. Nan Anna ita ma ta kwashe duk labarin Binty ta shaida masu. Sosai su ka shiga tashin hankalin shin su waye aihanin iyayan Binty da Rauhiyyah. "Ina son mu yi magana a keb'ance ni da Ku ban da yara" Fad'in Allah. Mahaifin Rauhiyyah saurin ta shi ya yi ta re da fad'in, "To ku fito muje wancan side d'in sai muyi magana". Duk ta re su ka fice daga d'akin. Sun kai kusan awa d'aya ka na su ka fito daga cikin d'akin.

Sallama Anna su ka masu su ka fice don komawa gida. Kasancewar Anna za ta yi tafiya nan da sati bayan yanke hukunci a kotu.

*KOTU*

*PAID BOOK* : 🌹 *83-84*🌹 *KOTU* .............Cike yake mak'il da jama'a. Daga can gaba kuwa, lauyoyi ne daga ciki kuwa har da Barr Fu'ad da abokan aikinsa. Daga can gefe kuma wajan tsayiwar wad'and'a ake tuhuma, Suhail ne sanye da sark'a, su hajiya Mansura kuma gaba d'aunsu hannunsu sanye da ankwa ta re da dandazon members d'in su. Alk'aline ya shigo gaba d'aya kowa ya tashi. Bayan ya zauna sai ko wa ya zauna, ka na mai karanto k'ara ya karanto k'ara. Daga kan su Hajiya Mansura aka fara, alk'ali ya kalli Hajiya Mansura kasancewar ba su d'auki lauya ba ta re da fad'in, "Shin kun amince da duk abubuwan da aka karanto ko kuwa Ku na da ja, kuma Ku na da lauya ne?". "A'a ya mai girma mai shari'a ba mu da ja, duk abunda aka karanto mun aikata". Fad'in Hajiya Mansura ta na sharar hawaye. D'an rubuce-rubuce mai shari'a ya yi ta re da kallon Suhail ya ce, "Kai kuma fa, ka na da ja da abubuwan da aka kama ka da su a d'aki, kuma mai yasa ka ke aikata ta'addacin a k'asarka?". Kuka Suhail ya soma yi ta re da fad'in, "A gafarce ni ya mai girma mai shari'a, wallahi ban rasa komai ba daga wajan mahaifina ba, sharri shad'an ne da kuma sharrin abokai". Fad'in Suhail ta re da rushewa da kuka. D'an rubuce-rubuce alk'ali ya sake yi ta re da fad'in, "Ke kuma baiwar Allah menene ribar ki na d'aukar y'ay'an mutane Ku na tura su aikatau da kuma jefa su cikin wasu munanan harkan". Alk'ali ya fad'a ta re da kallon Kandala da sai zazzare idanuwa ta ke yi. "Ya mai girma mai shari'a yasin-yasin sabida kud'i ne. Son kud'i ne ya yi min yawa ga shi zai jawo min k'arewa a gidan yari. Don Allah Ku yi min rai". Fad'in Kandala cikin Kuka. Jinjina kai alk'ali ya sa ke yi ka na ya yi y'an rubuce-rubuce ka na ya d'ago ta re da fad'in, "A bisa duba da kuma hujjojin da kotu ta gabatar da kuma amsa laifin da masu laifin su ka yi, kotu ta yankewa Suhail Usman mai rabo hukunci shekara goma sha biyar gidan yari ta re da horo mai tsanani, sannan kuma ta kotu ta sake yankewa Hajiya Mansura da tawagarta shekara goma sha takwas-takwas a gidan yari su ma da horo mai tsanani. Ita kuma Kandala kotu ta yanke mata shekara uku a gidan yari. Alhaji Mudi kuwa wanda Suhail ke kai masa makamai shi kuma ya baiwa y'an ta'adda da muke fama da su a k'asarmu, shi ma kotu ta yanke masa shekara ashirin a gidan yari da horo mai tsanani. Allah ya sa hakan ya zama izina ga wad'anda su ke son aikata irin wannan rayuwa da ma Wanda su ke ciki su tuba su sai da. Courttt". Ya na gama fad'in haka ya bubbuga sandar gabansa ta re da mik'ewa. Gaba d'aya kotun ta hargitse da hayaniya wasu na tsine masu, wasu ba jin tausayi. Yayin da Kandala ke ta sakin zawo a jiki, Suhail kuwa suma ya dunga yi, su Hajiya Mansura kuwa sai kuka su ke yi. Ya yin da Amrah da Hanan ke kuwa kamar ran su zai fita saboda hukunci da aka yankewa mahaifiyarsu domin uwa uwa ce. Alhaji Saifullahi ya rungumesu a jikinsa ya na lallashinsu ta re da alk'awarin kyautata masu da kuma sauke dak wani hak'k'i na su da ya rataya a wuyansa kamar yadda zan yi wa Sabrin. Ya kuma k'ara da alk'awarin yin adalci tsakaninsu da Sabrin. Ita kan ta Sabrin d'in kuka ta ke yi sabida ganin halin da y'an uwanta su ke ciki. Kuma ba ta tab'a sanin haka ta ke jin su cikin zuciyarta ba sai yau da wannan al'amari ya kasance wanda ita Amrah ta na daga cikin sanadin tonuwar asirin mahaifiyarsu duk da ita ta ce ta yi don kub'utar mahaifiyarsu daga halaka ne ganin za ka saka rayuwarta da na su da kuma wacce ba ta ji ba, ba ta gani ba a bala'i.

Julaibib kuwa ya na daga can sama Binty (Rukhsana) na kusa da shi ya hana ta ko motsi, shi kuwa Fu'ad sai satan kallon Rauhiyyah ya ke yi, da sun had'a idanuwa sai ya yi saurin kau da kai. Kasancewar ta na da miskilanci sai ta yi kamar ba ta san ya na kallonta amma kuma ita ma ta na kallonsa da gefen idanuwanta duk motsinsa. Shi dai Fu'ad zai ita cewa idan aka shak'e shi ba zai ce ga hukunci da aka Yankewa su Suhail ba. Duk da ya na gaba, amma idanuwansa na baya wajan Rauhiyyah inda ta ke zaune da Rahima mahaifiyar ruk'onta.

...........Bayan sun baro kotu, gaba d'aya gidan Alhaji Usman mai rabo su ka nufa har da su Rauhiyyah da kuma su Binty nan aka k'ara jajantawa juna. Alhaji Usman ya kira kaf ma'aikatan shashin Hajiya Mansura ya sallame su, ka na ya kira Fasila da Wasila gaban kowa ya nuna masu duk abubuwan da su ke yi a cikin gidan ta re da sallamarsu bayan ya biyasu albashinsu har da k'ari ta re da yi masu dogon nasiha. Wasila da Fasila har da kuka da majina ta kuma kasa had'a idanuwa da Anna. Har gaban Anna ta je ta duk'a ta na kuka majina na bin hancinta ta ce, "Hajiya ki yi wa girman ubangiji ki yafe min duk abubuwan da ba aikata miki wanda ki ka sani da wanda ba ki sani ba dan soyayyar Allah da ke wa manzo SAW". "Ba komai Fasila Allah ya yafe maka baki d'aya ke kuwa Allah ya sa sanadin shiryiwar kenan". Fad'in Anna. Kayansu su ka tattaro daga maid parts su ka fice daga gidan cike da takaicin abunda su ka aikata ga shi ba su ci ribar komai ba sai tarin kunya da takaicin da da na sani.

Bayan sun ci sun sha, Fanan ta zo ta duk'a gaban Maman Rauhiyyah ta re da fad'in, "Mommah dan girman Allah ki bar mana Rauhiyy ta kwana biyu a gidan nan mu sa ba da juna dan Allah". Fad'in Fanan a marairaice. Murmushi ta yi ta re da shafa kan Fanan ta re da fad'in, "Ba komai Fanan ga Rauhiyy nan ta zauna da ku tun da ma Anna tafiya za ta yi jibi sai ta taya Ku hira ta kuma saba da tagwainiyarta". "Anna wai ni da ita wanene babba? Ni ce ko?" Fad'in Rauhiyyah ci ke da son girma". "Ke dallah matsa can, ana ganin mu an san ni ce babba kwarankwatsi". Gaba d'aya dariya su ka fashe dashi saboda tuno masu da Buba mai kwarankwatsi da ta yi kasancewar sun ba su labarin sa. "Allahu masanin gaibu". Fad'in Anna ta na dariya don ta ga alamu daga Rauhiyy har Binty akwai son girma. Sai dai Rauhiyyah ita ta na da kyaliya da kuma rashin son magana idan ba ta ga dama ba, amma Binty ita uwar aku ce sanna ba ta da kyaliya.

Ranar dai a nan gidan aka bar Rauhiyyah, Sabrin, da kuma twince wato Amrah da Hanan. Wuni su ka yi a d'aki su na hiran school da kuma tuno halayan Sabrin d'in a da. Ita kan ta dariya ta ke yi sosai sai ta ji kamar ba ita ba ce ta yi hakan. Sai cin abinci da sallah ke tada su. Barrister Fu'ad da Julaibib ranar wuni su ka yi a parlour su na lek'en upstairs ta inda Rauhiyyah da Binty za su fito su kuma su can sama su na jirarsu ta mata har da shewa don't su na jin muryansu daga nan parlour.

...........Ranar da Anna za su tafi kasancewar jirgi za su bi ita da alhaji Usman d'in, kiran Julaibib ta yi har d'aki. Bayan ya shigo ya zauna ta kallesa ta re da fad'in, "Alhamdulillah zan ta fi yau, kuma kai ne babba na san mahaifinka ya fad'a maka abunda zan je yi, sabida haka daga nan ka min na dawo, ka tabbatar ka fayyace sirrin zuciyarka idan ba haka ba ina dawowa zan ba ka mamaki". Fad'in Anna ba ta re da ta k'ara kallon inda ya ke ba ta sauka k'asa. Gaba d'ayansu su ka raka Anna da daddy zuwa airport. Rauhiyyah, Sabrin, Hanan da Amrah a motar Fu'ad yayin da Anna Binty da daddy a motar Julaibib. Ba su baro Airport d'in nan ba sai da su ka ga tashin jirginsu Annan. Kuma ka min Anna ta wuce sai da ta k'ara jajjadawa Julaibib maganarsu na d'azu. Wajan dawowa Binty ta nufi wajan motar Barr Fu'ad amma ka min ta isa wajan ta ji muryan Julaibib d'in na fad'in, "Hayatiey zonan". Sai da ta waiga dama da hagu ka na ta kalli gabanta ko a kwai wata amma ta ga wayam ka na ta kalli Julaibib ta re da nuna kan ta da d'an yatsa ka na ta ce, "Ya Bibi ni ka ke kira". Ta fad'in hakane ta re da zaro idanuwa. Shi ma waro mata idanuwan ya yi ta re da jinjina mata kai. Kanta ne ya d'aure duk ta daburce. "Hayatiey" Ta maimaita sunan cikin zuciyarta. "Ki zo a motata za mu koma? Ko da ma a wancan motar Ki ka zo airport d'in?". Fad'in Julaibib. Girgiza Kai ta yi ta re da dawowa har in da motar ta ke kanta kuma a d'aure. Bud'e motar ta yi za ta shiga ta ji muryan Fanan da k'arfi ta na fad'in, "Babiiiii". Saurin juyawa Bintyn ta yi ta re da zabga mata harara. Julaibib kuwa da ya san ma'anar babi d'in jinjina ya yi mata da babban d'anyatsarsa wanda ya sa ta zaro idanuwa don ba ta tab'a tunanin zai yi mata hakan ba a yadda ta san ya Bibi mara wasa. "Ba gida mu ka yi ba daga nan mun tafi shan ice-cream". Fanan ta sa ke fad'i ta re da shigewa motar Fu'ad.

Langwab'ar da Kai ta yi ta re da fad'in, "Please yaya Bibi in bi su?". "Please Hayatiey ka da ki bi su ni ma zan kai ki wajan shan ice-cream d'in". Fad'in Julaibib kamar yanda ita ma ta yi maganar. Zaro idanuwa ta yi ta re bud'e baki ta na kallonsa. Hannu ya saka ya rufe mata bakin ta re da nuna mata cikin motar. Shiga ta yi ta na kallonsa har kan ta na buguwa da saman motar. "Aauch!". Su ka fad'a a ta re kamar wani shi ya bige. "Ki yi a hankali ka da ki jimin ciwo ki jawo min aiki Kin ji Nuriyyah". "Biyu kenan". Fad'in Binty cikin zuciya da ba ta san ma ya fito fili ba. "Ai idan dai sunaye ne za ki ji fiye da d'ari ma". Fad'in Julaibib ta re da rufo motar ya zagaya ya shiga mazaunin driver.

Kallonsa ta ke yi ko kyaftawa ba ta yi sabida tsantsan mamakinsa. Hura mata iska a idanuwanta ya yi ta re da fad'in, "Ya dai? Wannan kallon fa Khairiyyah". "Na shiga uku". Fad'in Binty ta re da saurin saka kan ta tsakanin cinyoyinta gabanta na fad'uwa.

Dariya ya yi ta re da jan motar bai tsaya a ko ina ba sai wani park d'in da duk yawonsu da Barr Fu'ad ba su tab'a zuwa ba. Wajan ba hayaniya sosai irin wajan da manyan mutane su ke zuwa ne. Wajen wani shukoki flowers ma su kyau ya kai ta. Sosai wajan ya burgeta har ba ta san lokacin da ta fara murmushi ba. Jin mutum kawai ta yi a bayanta ya na fad'in, "Wajan ya k'ayatar da ke ko? Zan rik'a kawo ki bayan auran duk weekend". Ya fad'i hakane har ta na jin sautin fitar numfashinsa a wuyanta. Wani irin saurin juyowa ta yi ta re da zaro idanuwa sabida kalmar bayan mun yi auran da ya ce har sai da ta bugu da k'irjinsa kasancewar ya na gab da ita sosai. Wayarsa ya yi saurin d'agawa ta re da yi masu salfie a hakan yadda su ke. Saurin ja baya ta yi nan ma ta yi baya da yawa saura kad'an ta kai k'asa ya yi saurin rik'o hannunta ta re da jawota jikinsa gaba d'aya. Waro idanuwa ta ta yi ta re da rasa inda za ta saka kan ta don wani irin kunya, tsoro da mamaki da su ka taru mata lokaci guda. Juyata ya yi ta kalli gabanta yayin da ya rungumo waist d'in ta ta re da d'aura Kansas a kafad'arta sai da ta waro idanuwanta. "Ina son kin tun ranar da na fara ganinki. Ke ce farin ciki na. Ban tab'a son wata mace a rayuwata ba sai ke, ina son ki kasance matata sirrina kuma uwar y'ay'ana. Ki ba ni soyayyar ki dan Allah ba don wanini dalili ba Binty. Ka da ki cuci kan ki, ki soni dan Allah ba don wata alfarma ba kin ji". Ya fad'i hakane ta re da sake mata nauyin Kansa a kafad'arta sai da ta yi kamar za ta zame a hannunsa ya yi saurin k'ara damk'o waist d'in ta. Ita kuwa kunyace mai tsanani ta dabaibayeta ta re da jinta a wani yanayi daban ga kuma wani abu da take ji tun daga kwakwalwar kan ta wanda ba ta tab'a jin sa ba. Sakinta ya yi jin yadda jikinta ke rawa sosai. Aikuwa ya na sakinta ta yi saurin yin gaba ta re da b'oyewa a jikin wata bishiya da ke gabansu kad'an ta re da dafe k'irjinta ta na sauke numfashi. D'an lek'o da kanta ta yi, karaf su ka had'a idanuwa ya na sakin murmushi, saurin komawa ta yi ta na k'ara dafe k'irjinta ta re da zaro idanuwa. "A'a wannan ba yaya Bibi ba ne Allah. Mafarki na ke yi". Ta fad'a k'asa-k'asa. Can kuma ta kai hannu ta re da tsungulin hannunta don tabbatar da mafarki ne ko gaske. "Aauch!" Ta fad'a sabida zafin da ta ji. Saurin isa wajan ya yi ta re don sanin abunda ya sa me ta. Su na had'a idanuwa ta yi sauri rufe idanuwanta ta re da juya baya ta rungume bishiyan. Sosai ta ba shi dariya. K'arasawa wajan ya yi ta re da juyota ka na ya ce, "Ke dan Allah tun 1888 aka dai na wannan gulmar da kinibibi. Idan ki na sona kawai ki fad'a babe". Ba ta san lokacin da ta fad'a k'irjinsa ba don kunya ta rufe fuskanta da k'irjinsa ji ta ke kamar ta nitse. "Mu tafi gida?". Ya rad'a mata a kunne said da ta ji tsigar jikinta ya ta shi har ba ta san lokacin da ta d'aga masa kai ba. Hannunta ya kama ta re da nufar parking space, sai da ya sakata a mota ka na ya zagaya ya shiga. Kanta ta saka tsakanin cinyoyinta ta b'oye fuskanta. Dariya ya yi ta re da reverse su ka bar wajan. Sai da ya hau titi ka na ya kunna wak'ar Umar M Shariff *CIKIN D'AYA*. Hannunta ya rik'o ta yi k'ok'arin kwacewa amma ta kasa, bin wak'ar ya shiga yi kamar haka,

🎻 _Cikin d'aya a cire d'aya, zai zamo ba ko d'aya ni da ke mu zan d'aya ba mu fatan rabuwa. In za ni ba da labari, wa ke saka ni annuri, sunanki zan kira farii, lallai ki da da alkhairi. Kyawun halinki ne ya Jani, ga natsuwa da kyan tsari, auran ki shi na sa buri daga ke ba ni yin k'ari, gun ki kai na sunkuyar, hankali na na tsayar, ke na baiwa ajiyar zuciyata bai d'aya. Ku kalleta kyakkyawa, gu na ta wuce kowa, Idan gaki, idan gani, ni dai ba ni son kowa. Ko da ba ni motsawa, ko da na zamo gawa, da ke zan yi kwantawa ajinina kin ka narkewa. So da k'auna kin shigar, ba bu kowa kin kawar, ke kad'ai ce mallakar zuciyata guda d'ayaaa. O'o'oohh! Lokaci na bak'in ciki, ke ki ka sani na yi darawa, kin sa ni farin ciki duk damuwata na yi mantawa, komai daki-daki na ke a yanzu ba ni rud'ewa, in an yi farmaki gare ki dole na yi karewa. Wajibi in tabbatar, masoyiya na tseratar, ko da rai za na salwatar za na yi maki kariya. Cikin d'aya a cire d'aya, zai zamo ba ko d'aya, ni da ke mun zan d'aya ba mu fatan rabuwa_🎻

Rar cikin jinin jikinta ta ke jin wak'ar, ba ta tab'a tunanin yaya Bibi ya na sauraran wak'ok'in Hausa ba balle ma har ya ita rerata haka ba. Mamaki duk ya gama kasheta. Ta san da za ta baiwa Fanan wannan labarin sam ba za ta yarda ba sai dai ma ta yi mata dariyar k'aryar da ta shararo. Haka ya dunga mata kalaman soyaya cikin wak'ar Umar m shariiff kala-kala ga shi ba gudu ya ke yi kad'an-kad'an ya ke tafiya don ka da su isa gida da wuri.

Bayan sun isa gida ya yi locking motar ta re da fuskantarta ya zuba mata idanuwa ita kuma ta k'udundune cikin cinyoyinta. "Ba ki ce komai ba Ruhiey, kin amince da ni a matsayin mijinki na gobe". Fad'in Julaibib. "Wayyoo dan Allah ka bud'e min in shiga gida dan Allah". Fad'in Binty a marairaice. "Dan Allah ki fad'a min ki na sona". Shi ma ya fad'a kamar yarda ta yi cike da shagwab'a. "Wayyoooo Allah". Binty ta sa ke fad'i. Dariya ya yi sosai saboda ya fahimci kunya ta ke ji sosai. Bud'e lock d'in ya yi. Ai kuwa cikin sauri ta bud'e motar ta fice da gudu saura kad'an ta fad'i har da wani zabura ya yi kamar irin shine zai fad'i.

Da gudu ta wuce su Rauhiyyah da Fanan da ke ciye-ciye har da Fu'ad. Gaba d'aya dariya su ka fashe da shi kasancewar tuni sun harbo jirgin ya Bibi. "Babi!" Fanan ta kwala mata kira cike da tsokana. Ko juyowa ba ta yi ba ta haye sama da gudu. Sai da ta turo k'ofar d'akin ta rufe ta re da jinginar da jikinta a jikin k'ofar ta shiga mai da numfashi.

Tun daga ranar su ka soma wasan b'uya, ba ta yadda ta tsaya in da zai ganta. Shikuwa har ya shiga wani hali na rashin ganinta kwana biyu. Rauhiyyah kuwa ita da Fu'ad kamar da wasa soyayyah ta shiga tsakanin su, tuni Fanan da ma su Sabrin su ka canza masu suna zuwa Babi (matar yaya da yaran Hindi). Mas'ud kuwa tun da ya kyallara idanuwansa akan Sabrin ta tafi da shi, shi ma bai cuci kansa ba ya fito masa da manufarsa, kuma said Allah ya had'a zuciyoyinsu, gidan Anna dai ya koma gidan masoya, don kullum Mas'ud na can su na shan soyayyarsu da Sabrin ya yin da Fu'ad su ke shan na su da Rauhiyy. Mai gayyar ne dai har yanzu ba ta ba shi had'in kai ba.

Ta fito daga kitchen kenan cikin sauri ta na son guduwa zuwa sama ka da ya ganta. Sai da ta isa tsakiyar parlour caraf ta ji an damk'i hannunta.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull