Ba ni da gata - Chapter 41
Ba ni da gata Chapter 41: Ba ni da gata Chapter 41. *PAID BOOK 08128755583* 🌹 *85-86*🌹 ...........Juyawar da za ta yi idanuwansu su ka had'u da na juna.…
2,217 words
*PAID BOOK 08128755583* 🌹 *85-86*🌹 ...........Juyawar da za ta yi idanuwansu su ka had'u da na juna. Ji ta yi kamar ta kurma ihu saboda kunyan da ya lullub'eta. "Mai ya sa ki ke guduna Habibty? Kin san yadda hakan ya ke min zafi ana kuwa?". Ya k'arasa maganar ta re da nuna saitin zuciyarsa. "Dan Allah wallahi kunya na ke ji". Fad'in Binty har da wani karyar da wuya irin marainiyar nan. "Dan Allah wallahi na k'osa in ji kin fad'a da bakin ki kina sona". Fad'in Julaibib cikin shagwab'a shi ma. Kallonsa ta yi na second biyu ba ta san lokacin da ta bushe da dariya ba saboda yadda ya yi da fuska kamar d'an two years. Ka mo hannunta ya yi ta re da matsota kusa da shi ka na ya d'aure idanuwata da hanky ka na ya rik'o hannun su ka fita, can garden su ka nufa. Sai da ya kawota tsakiya ka na ya kwance idanuwan na ta tare da tsayawa a bayanta. A hankali ta fara bud'e idanuwan har ta bud'e su duka. Zaro idanuwa ta yi sakamakon arba da ta yi da wasu flowers multi colours da aka shimfid'a a filin. Ga wasu balloons ma su shape d'in love a jiki kuma an rubuta I love you Rukhsana, wani kuma an rubuta I love you Bintyn Anna, wasu kuma a jiki an rubuta can't live without you. Du ka balloons d'in ba bu wanda ba kalmomin k'auna a jiki. Duk'awa ya yi a gabanta ta re da kamo hannunta ya ce, "Will you be my wife? I mean will you be the one and only mother of my children?". "Yyy.. Yes". Fad'in Binty in a very cool voice ta re da rufe fuskanta da d'aya hannunta". "Na yi alk'awarin zama da ke cikin aminci da soyayya in sha Allah har k'arshan rayuwarmu. Zan kula da ke fiye da yadda zan kula da kai na, zan shayar da ke zallar zuma da madarar soyayyar da ba ki tab'a ga ni ba. Wallahi Salis na son ki irin sosai d'in nan". Gaba d'aya maganganunsa sai su ka tu na mata da Yousouf lokacin da su ke musayar zobe. Kwal-kwal ta yi da idanuwa kamar za ta yi kuka sai ta yi saurin shanye hawayanta.
Fu'ad da Rauhiyyah da ke mak'ale can cikin garden d'in su ma su ma shan na su soyayyar su na kallon su. Rauhiyy ce ta fiddo wayarta k'irar iPhone 13pro max ta soma yi masu video tun sanda ya kwance mata hanky a fuska. "Kin ga love ko?". Fad'in Fu'ad ya na tallabe k'eyar Rauhiyy. Shafa k'eyar ta yi ta na dariya ta re da fad'in, "Kwarankwatsi na ga ni, ni ma ai min irin haka ko inyi rejecting". Fad'in Rauhiyyah. "Ke kin ma isa? Ni da ke ai mun zama hatta da jini". Fad'in Fu'ad.
"Allah ya sa su hango ku yasin". Fad'in Sabrin wacce su ke yowa inda su ke ita da Mas'ud. Dariya su ka yi gaba d'ayan su ta re da nufo in da ya Bibi da Binty su ke su na tafi. Binty na ganin su ta yi ta rud'e ta rasa in da za ta saka kan ta, bayan ya Bibi ta yi da gudu ta b'oye fuskanta a bayansa. Aikuwa nan ma su ka k'ara kwashe da dariya ta re had'a baki su ka soma yi mata wak'a kamar haka, 🎻 _Binty! Ayaya_ _Binty! Aya_ _Binty Binty Binty! Aya_ _Binty mai miji Ayayah_🎻 Balloon d'aya ya d'auka ya bi su da shi da gudu, gaba d'aya su ka dare su na dariya.
Tun daga wannan ranar aka shiga soyayyah ruwa-ruwa tsakanin Binty da Julaibib, abinci daban ta ke dafa masa gidan kuma sai abunda ya zab'a ta ke yi masa ta kai masa har d'aki. Raba dare su ke yi suna waya. Kasancewar idan ya fita tun safe sai dare saboda yanayin aikinsa kuma gashi dama daddy ya sayan masa wani makeken fili ana gina masa asibitinsa a wajan. Yanzu haka asibitin ya kai linta.
..........Kwanansu Anna goma su ka dawo daga bauchi ci ke da farin ciki, sai dai ba su cewa kowa komai ba. Washa garin ranar da su Anna su ka dawo, su Binty su ka d'ugunzuma sai gidan Maman Fakri (uwar rik'on Rauhiyy). Har da su Sabrin da y'an biyu. Sabrin sai duk'ar da kai da sum-sum ta ke yi ita ala dole ta na gidan surukai. Ita kuwa mommah ba ta ma san ta na yi ba duk da Mas'ud d'in ya fad'a mata shi fa ya sa mu matar aure kuma Sabrin d'in ce. Kullum Julaibib da ya dawo daga aiki ya ke tafiya gidan su Rauhiyy dan ganin sahibarshi. Sosai Anna ta ji dad'in ganin sun had'e kawunansu don dama ita burinta kenan. Kwanansu takwas a gidan Mommah su ka dawo gidan Anna, amma ban da Rauhiyy wanda hakan bai yi wa Fu'ad dad'i ba.
Yau bak'o su ke da shi, kuma bak'on ba wani ba ne fa ce Yousouf Muhammad Ahlam don godiya ga Julaibib da ya sa mo masa maganin cutarsa har ya warke garas. Kyakkyawan tarba aka yi ma su shi da abokinsa. Tun da Yousouf ya kyallara idanuwa akan Amrah ya ka mu, kuma ita ma haka ya ke a wajanta. Musamman da ya kasance kyakkyawa kuma mai sanyi. Bai yi k'asa a gwiwa ba ya k'arb'i numbernta ka min ya wuce. Washa gari Hamdan ya taho da akwati nik'i-nik'i ya na ta zuba bala'i kowa ya manta da shi har da bestyn shi da ya yi ta dungurewa kai har sai da ta fad'a kan kujera. Nan su ka shiga mai da yadda aka yi lokacin da su ka tsince su a duniyar aljanu. Fanan da su y'an biyu sun yi dariya don Fanan har da hawa sama da gudu ta shiga toilet ta yi fitsari don tsabar dariyar fitsarin da ta yi ta saki don tsoro. Sabrin ta shak'a ta watsa masa ruwa a fuska ta re da shiga ba su labari shi ma ai ya yi fitsarin har da zawo. Nan ma aka shiga yin dariya. Sai kuma aka koma kwantanta yadda Binty ta dunga suman tsoro da kuma kamannin Oumul Sahwat da ba Bak'ayatul mahruri.
*AFTER TEN DAYS* .............Gaba d'ayan su su ka shiga kintsawa na tafiyar da za su yi zuwa bauchi, don dukkansu za su tafi, tun daga kan daddy, Anna, Julaibib, Fu'ad, Binty, Fanan, Rauhiyy, mommah, mijin mommah, mas'ud, Hamdan, Amrah da Hanan. Kowa sai kimtsa jakarsa ya ke yi don Anna ta ce masu tafiya ce ta kusan wata d'aya. Duk da kasancewar Hamdan ya na final year d'in sa amma hakan bai hana ya k'i bin su ba. Washa gari su ka bi jirgi sai Gombe (Ku yi hak'uri last page na saka Anna sun je bauchi, ba bauchi zan sa ba Gombe ne mistake ne). Kai tsaye gidan sarkin Gombe su ka nufa wanda wa ne a wajan mahaifin Anna. Gaba d'aya tsoro ne ya kama Binty ganin yadda ake karrama su da kuma gaida su duk in da su ka shiga. Rauhiyyah ce dai ko a jikinta don sai d'aga kai ta ke yi ta re da basarwa kamar d'iyar sarauta. Kai tsaye wajan kilishi su ka nufa wato uwar gidan mai martaba. Nan su ka ga mulki ganin yadda kuyangi su ke mata da su kan su. Cikin k'ank'anin lokaci har an cika gabansu da abinci. Julaibib kuwa tuni har an yi masa iso wajan mai martaba. Zaid ya hango cikin alkyabba mai shegen kyau, idan ka gan shi ka ga Julaibib don kamanninsu d'aya tsaf. Cikin sauri ya mik'e ya je ya rungume Julaibib d'in ta re da farin cikin ganin d'an uwan na shi cike da kewarsa. Duk'awa ya yi ta re gaida mai martaba cike da girmamawa. Ka na ya shiga tambayarsa aiki da kuma Canada.
Binty kuwa sai fik'i-fik'i ta ke yi da idanuwa duk da ta na bala'in gidan sarauta sai ta ke jin ta wani iri.
Da daddare misalin isha'i su ka taru a parlour mai martaba gaba d'ayan su. Kallon Binty da rauhiyyah ya yi ta re da sakin murmushi ka na ya ce cike da k'asaita "Masha Allah, har na tuna lokacin da mu ka je Sudan d'auro auran mahaifiyarku. Allah ya muku albarka". Ci ke da mamaki kowa na wajan ya ce ameen. "In sha Allah gobe za mu tafi yola da ku duka wajan mai martaba, mun yi waya da shi na ce masa gobe ina ta fe da manyan bak'i". "Allah uban giji ya kai mu". Fad'in gaba d'aya d'akin. Nan duk aka fita aka bar shi daga shi sai mijin mommah da momma da kuma Anna da daddy.
Washa gari su ka k'ara shiga jirgi dukkansu har da mai martaba sarkin Gombe sai yola. Nan ma uban motoci aka turo masu daga masarautar yola da kuma dogarai su ka zo su ka d'auke su. Masarauta ce mai girma da tsari wanda tsaruwarta ya fi gaban kwantance. Gaba d'aya masarautar an canza masa launi da kuma wasu abubuwan k'awa. Tun daga jama'ar gari da kuma na cikin masarautar a su na wajan masarauta domin tarbar mai martaba sarkin gombe da bak'in sa. Lokacin da su ka shiga cikin masarautar, mai girma sarki na fitowa gaba d'aya fadawa su ka rufesa da rigunarsu har ya isa part d'in sarkin yola shi d'aya, sauran kuma Jakadiya ta yi masu iso zuwa part d'in Fulani uwar gida wajan sarkin yola. Kishingid'e ta ke ta na cin apple cike da is a da Yakama kuyangi na mammatsa mata k'afa. Farar bafulatana ce kyakkyawa sosai kuma mace mara jiki ko kad'an, za ta iya kai wa shekaru hamsin da biyar a duniya. Ta na yin arba da su Binty da Rauhiyyah ta yi wani irin zabura da gigicewa, ita kan ta jakadiyar da ta yi masu iso sai d'igar zufa ta ke yi kamar wacce kunama ya cijeta. "Ina ki ka samo wad'annan?". Fad'in sarauniya Fulani cikin harshan fillanci wanda gaba d'ayan su idan ka cire Amrah da Hanan sun ji abunda ta ce saboda su ma su na jin fillancin. "Mai martaba ya ce in kawo wajanki, bak'i ne daga masarautar Gombe, kuma ta re su ke da mai girma sarkin Gombe d'in". Fad'in Jakadiya wacce ta ke ji ina ma a kwai hanyar ta gudu. Zama Fulani ta yi ta re da korar kuyangin da ke wajan ta shige d'aki ba ta re da tankawa bak'in ko ba su wajan zama ba. Daga can part d'in mai martabar sarkin yola kuwa, bayan gaisuwa ta girmama tsakanin sarakan biyu, sai su ka shi ga mai da magana. Sarkin Gombe ya yi gyaran murya ta re da fad'in, "Ita Na'ima (Anna) ni na rik'e ta, mahaifinsu k'ani na ne uwa d'aya uba d'aya ai ka san shi. To lokacin da aka ta jimamin b'acewar y'an biyun amarya ta san labarin komai kasancewar ta zo mana ziyara daga can abuja gidan mijin ta. Cikin hukuncin ubangiji kuma sai d'aya daga cikin y'ay'an su ka kasance a hannunta. Yanzu dai duk mun tawo da marik'an y'ay'an za su yi maka bayani da kan su". Cike da farin cikin da ya ka sa b'oyiwa a fuskan mai martaba ya ce, "Alhamdulillah! Allah nagode ma ka. Huta idan ya so sai in sa a kawo su nan d'in". Fad'in Mai martana sarkin yola da ke kishingid'e.
*AFTER 3HOURS* ............Tun daga kan Sarauniya Fulani, Sarauniya Zameelah (matar sarki ta biyu), Sarauniya Maimoon wacce ita ce ta uku, sai babban d'an sarki wanda ya kusa sa'a da Julaibib, sai da ba shi da lafiya, irin yaran nan ne da aka haife su abnormal, duk da shi lafiya lau aka haifesa, sai dai ya na kai wa shekara bakwai ya ka mu da wannan lalura. Kyakkyawa ne sosai na gaban kwatance kuma d'a ga gimbiya Zameelah, wanda bayan shi ba ta k'ara haihuwa ba sai da ya shekara goma sha takwas ta haifi y'an biyu kuma washa garin sunan su aka nai me su aka rasa wanda haka ya tada hankali gaba d'aya masarauta. Ya na gefe wanda mai martaba ko kallansa bai son yi saboda wani tsanarsa da ya ke ji wanda hakan ya shafi mahaifiyarsu da ta zama saniyar ware a cikin masarautar wanda Fulani ke juya komai. Sai mahaifiyarsu mai martaba sarkin yola wanda shi kad'ai ne d'a namiji a wajanta. Da kuma waziri da ke ta zazzare idanuwa da kuma Jakadiyar sarki da ta ke ji kamar ta saki zawo don firgici. Shuri d'akin ya yi, ya yin da ko makawo ya kalli Sarauniya Zaheeda ya kuma kalli su Binty ya San daga jikinta su ka fito, ka na ganin ta ka ga cikakkiyar Sudanese wacce kyawunta har yanzu ya na ta re da ita kuma daga wajan ta su ka yi gadon kyau da kuma irin launin fata duk da mai martaba shi ma ba baya ba ne. Sabrin kuwa da su twins mamaki su ke yi wai yau ga su ka sarkin Gombe da na Yola wanda ko a mafarki ba su tab'a kawo hakan ba. Hamdan kuwa cewa ya ke cikin zuciyarsa, "Mummy, uncle Sauban ku zo ku ga asalin Binty ku girgiza ta re da fad'uwa a gabanta don ita d'in jinin sarautace wata muna-munan ce ta kawo ta kan bola.