Ba ni da gata - Chapter 42
Ba ni da gata Chapter 42: Ba ni da gata Chapter 42. *PAID BOOK* 🌹 *87-88*🌹 .............Anna ce ta mik'awa Sarauniya Zameelah wannan kwarya da Yousouf…
3,064 words
*PAID BOOK* 🌹 *87-88*🌹 .............Anna ce ta mik'awa Sarauniya Zameelah wannan kwarya da Yousouf aljani ya bai wa Binty, idanuwanta na zubda hawaye ta karb'a ta re da fiddo kayan da ya ke ciki. Kuka ta saka sosai saboda wannan shi ya k'ara tabbatar da lallai su Binty y'ay'anta. Jakadiya ma kukan ta ke yi domin ita ce da hannunta ta saka masu wad'annan kayan da kuma awarwaron nan a cikin showel d'in su da kuma maficin d'awisu wanda wannan d'in tambarin sarautar Sudan ce, kuma d'in wanda ya had'a jini mai k'arfi da masarautan ana haifansa ne da zanen d'awisu a wuyansa. Ita ma Rauhiyyah duk abunda ke cikin kwaryan Binty haka ya ke cikin na ta. Da kanta jakadiya ta isa zuwa wajen Binty ta duba k'eyarta, ka na ta koma ta duba k'eyar Rauhiyy. Kallon mai martaba ta yi hawaye na gudu a idanuwanta da kuma murmushi ka na ta fad'i a gabansa ta re da fad'in, "Allah shi k'ara maka girma da yawan rai da lafiya, babu tantama wad'annan y'ay'anka ne, domin akwai zanen d'awisu da aka haifesu da shi wanda ke nuni da tambarin masarautar Sudan a wuyansu, sannan ga awarwaro na d'anyan zinari da mai girma Katanga (Mahaifiyarsa) ta ba su". Ta fad'i hakane ta re da mik'awa mai girma Kantanga awarwaron cike da girmamawa. Duk da ta tsufa sosai bai hanata ga ne wad'annan awarwaro ba, domin kyautace da sarakuwarta kakar mai martaba ta ba ta a matsayin kyautar budurci don har da sunan kowannansu a ciki, ita da kan ta ta saka aka yi wannan ka na ta sakawa kowannen su a hannu. Julaibib kuwa gaba d'aya hankalinsa ya na kan Mahensh da ke jirarar da miyau ya na nazartar ciwonsa. Waziri kuwa fitsari ne ke nai man kufce masa domin bai tab'a tunanin wannan ranar za ta zo ba, Sarauniya Fulani kuwa ita har da zawo-zawo ta ke ji. Cike da tak'ama da gadara mai martaba ya yi gyaran muryan ka na ya kalli jakadiya ta re da fad'in, "Ina son sanin ta yadda y'ay'ana su ka b'ata a masarauta washa garin sunan su, idan ki ka yi karya ki sa ni a bakin ran ki ya ke". Jakadiya fad'uwa ta yi a gaban sarki ta na burgima ta re da fad'in, "Wane ni in yi was sarki na k'arya. Wallahi na amince ko kalma d'aya idan ban fad'i ba ayi gangani ka na a fille kai na". Gaba d'aya d'akin zuba mata idanuwa aka yi, Fulani da waziri babu abunda zuciyarsu ke yi sai bugawa kuma k'ani ne ga mai martaba. "Kowa a nan ya San cewa Gimbiya Fulani ita ce matar Sarki ta fari wacce kuma y'ar uwa ce a gare sa don k'anin mahaifin mai martaba ne wanda su ke uba d'aya ya haife ta, auran zumunci aka ma su, kuma lokaci d'aya ya aure su da Sarauniya Zameelah wacce su ka had'u a jami'atul Madina soyayyar da shak'uwa ta k'ullu tsakaninsu. Sosai mai martaba ya ke son gimbiya Zameelah kasancewarta kyakkyawar mace kuma mace wacce ta iya rik'e miji da tarairayarsa. Haka na matuk'ar k'ona zuciyar Sarauniya Fulani kuma ta na mugun kishi da Sarauniya Zameelah musamman yadda ta yi wani irin suna da farin jini a cikin gidan da kuma wajan Sarauniya Katanga. Cikin hukuncin Allah ba ta dad'e ba ta samu ciki wanda ya sa ka mai martaba cikin wani irin farin ciki, don ba zan manta irin kyautar da na samu mai tsoka ba saboda isar da wannan sak'on farin cikin. Sai dai cikin bai yi wata biyu cikakke ba ya zube wanda kowa yaji bak'in cikin haka musamman mai martaba da har ya fara hango an haifa masa magaji. Bayan wannan lokacin gimbiya Zameelah ba ta rufe wata uku ba ta kuma samun wani cikin wanda shi sai da ya kai wata biyar ka na jini ya b'alle mata babu wanda ya yi zaton za ta yi rai haka kuma ya k'ara ta da hankalin mai martaba, an sa mu nasarar ceto ranta sai dai cikin ne ya fita. Duk maganar nan da na ke ma ku gimbiya Fulani ba ta tab'a ko b'atan wata ba kuma haka na damunta sosai ganin ga wata ba re zata haifi magaji a masarautan ta. A tak'aice dai gimbiya Zameelah sai da ta yi b'arin ciki har takwas ka mun ta sa mu cikin Mahensh bawan Allah, lokacin da ta sa mu cikin ba ta fad'awa kowa ba idan ka cire mai martaba da Katanga, kuma sai ta dai na fita har sai da cikinta ya kai wata takwas ka na na san da cikin a wani zuwa shashinta da na yi domin kai sak'o. Sosai na yi mamaki da ganin cikin nan. Na ja baki na na yi shuru kamar yarda ta gargad'e ni. Lokacin da cikin ya isa haihuwa shi ne kowa ya san da zaman ciki wanda ya kusa saka gimbiya Fulani zarewa domin ta yi kondo-kondo na masifa akan b'oye mata cikin da na yi. Cikin ikon Allah gimbiya Zameelah ta haifo d'anta k'atoto kuma kyakkyawan gaske fari tass mai kama da mahaifiyarsa ga gashi. Ranar duk wanda ya ke cikin masarautan ya shaida haihuwan nan domin kyauta mai martaba ya yi na ban mamaki don wani ma sanadin arzikinsa kenan. Ranar su na yaro ya ci suna Ibraheem sunan mahaifin mai martaba sai ake mishi kara da Mahensh. Sosai aka yi shagalin suna wanda aka kashe kud'i da kuma raba kyaututtuka na ban mamaki. Mai martaba idan ya bar Fada bai rabu da Mahensh a wajansa, don ko barci a k'irjin mai martaba ya ke yin sa. Sun shak'u matuka irin shak'uwar da ko mahaifiyarsa ba ta yi da shi ba don tsakaninsu shi ne idan ya buk'aci abinci ta ba shi ya sa a kuma mai da shi wajan mahaifinsa. Mahensh na girma kyawu da wayonsa na dad'a fitowa sosai da kuma basira da wayonsa. Ga wani tak'ama da isa ka na ganinsa ka ga jinin sarauta, sosai ya ke da shiga ran mutane. Sai dai ya na kai wa shekara bakwai a wata safiya ni da Kai na na isa d'akinsa domin shiryasa zuwa makaranta na yi katari da tashin hankali da masifa, domin dai ga shinan kwance cikin fitsari, kwayan idanuwansa ya juye bakinsa ya shagid'e sai zirarar da miyau ya ke yi kamar irin yaran nan da aka haifesu ba dai-dai ba ko kuma wanda su ka kamu da ciwon b'arin jiki sakamakon fad'uwar hawan jini. Da kyar na iya sanar da Sarauniya Zameelah halin da ake ciki wanda ya ta da hankalinta haka ma mai martaba. An kai Mahensh asibitoci da ba za su k'irgu ba, amma bai samu lafiya ba kuma ba'a gano lalurarsa ba, an dawo an yi na gida shi ma dai kamar an shuka duka. A hankali a hankali mai martaba ya fara zame jikinsa daga lamuran Mahensh har bai son ganinsa saboda kyamarsa da ya ke ji hakan har ya shafi mahaifiyarsa. Daga ni sai Sarauniya Zameelah da kuma Katanga mu ke kula da Mahensh. Ba'a a k'ara haihuwa a masarautan nan ba tsawon shekara biyar wanda haka ya sa mai martaba k'ara aure ya auro Sarauniya Maimoon wacce ita m sai da ta yi shekara biyu ta haifi d'iya mace mai suna gimbiya Rufaida wacce a yanzu haka ta na gidan mijinta. Sarauniya ba ta k'ara samun ciki ba sai da Mahensh ya yi shekaru sha takwas, kuma abunda zai ba ku mamaki, duk da lalurar Mahensh ya na kararu kuma ya na ga ne karatu don yanzu haka ma degree d'in sa uku don ma ba'a k'arfafa masa gwiwa ba, don mai martaba ma cewa ya yi ba zai kashewa gawa kud'i ba bai ga amfanin karatun a wajansa ba, Katanga ita ta buga tsalle ta ce mai martaba bai isa ba. Haka kuma ya yaddace Qur'ani. Ranar da Sarauniya Zameelah ta sa mu ciki ta yi matuk'ar mamaki don ta cire rai da haihuwa, sosai hankalin Fulani ya ta shi da sanin cikin nan, sai dai duk abunda su ke k'ullawa ita da waziri sai da y'an biyu su ka ta ka duniya, haihuwarsu ita ta d'an farfad'o da soyayyan Sarauniya Zameelah a wajan mai martaba har ya yi mata gagarumar kyautar takobin zinarin masarauta mai matuk'ar tarihi. Hakan ya bak'anta ran sarauniya Fulani wanda sun dad'e da ma su na y'an k'ulle-k'ullen su a kan haihuwa da ta ke yi, kasancewar Sarauniya Fulani ta san ta na da matsala kuma ba za ta tab'a haihuwa ba. Shi kuma Waziri ba bu abunda ya ke face mulki ganin sarki ya haifi d'a namiji sai hankalinsa ya ta shi tunda ya san hakan na nufin ba zai yi mulki ba, wanda hakan ya sa su ka yi k'ulla k'ulla su ka jefi Mahensh da mummunar asirin da ya koma haka, sannan ni kuma su ka ba ni mak'udan kud'i da zinari akan kashe y'an biyun da Sarauniya ta haifa, hakan ya ta da hankali na sosai na nu na ni bazan iya wannan aiki ba, sai su ka ce to a bakin raina don kuwa za su had'a min makirci wajan sarki da zai yi sanadin mutuwata. Ni na kawo masu tsarin sa ce y'ay'an idan ya so wanda zai fitar da su ya kashe su, sun amince da hakan. Ni da kai na shirya su na kuma saka duk wani shaida da zai nuna su d'in daga nan su ka fito ko da nan gaba an haife su. Ni da sarkin k'ofa mu ka yi hakan, na ce a yi nisa da su daga yola, wanda aka baiwa kwangilan a Adamawa ya aje su, sai dai ni ban san in da ya kai su ba. Amma ya ce min ya raba su ne. Wallahi tallahi wannan shi ne abunda na sa ni". Fad'in Jakadiya ta na kuka sosai. Da waziri da Sarauniya Fulani kuwa zufa ta gama jik'a su sosai. Mai martaba ran shi ya b'aci matuka, shi kan shi bai san dalilin da ya sa ya tsani d'an shi ba, ashe da walakin. Kallon Fulani kawai ya ke wacce ta sunkuyar da kan ta k'asa kuma hakane ya tabbatar masa da abunda Jakadiya ta fad'i gaskiya ne. Cikin b'acin rai ya sallami kowa ba ta re da ya ce komai, mahaifiyarsu ce da shi kawai su ka rage. Masarauta tu ni ta d'auka da zancan gimbiyoyin masarauta sun bayyana.
"Lallai ashe jijji da kai da tak'ama a jinin Rauhiyy ya ke, dole ta yi tak'ama ko ta ina ita d'in jinin sarauta ce". Fad'in Momma wacce ta ke kallon mijinta. Shuru ya yi shi hankalinsa gaba d'aya ya na ko ma wajan muna-munan da ake yi cikin masarauta saboda mulki kawai.
Sosai aka yi zama a tsakaninsu Mai martaba da mahaifiyarsu da nuna Fulani da waziri da kuma wasu manya. In da Fulani ta yi confessing ita da waziri, a take mai martaba ya sake ta saki d'aya ta re da jefa ta cikin kurkukun masarauta haka shi ma waziri bayan cire sa daga muk'amin sa.
Julaibib da kan shi ya sa mu mai martaba ta re da ce masa ya na buk'atar bin jirgi ya ko ma abuja don d'auko maganin da ya ke tunanin zai iya warkar da cutar da Mahensh ke fama da shi.
Mai martaba ya yi na'am, kuma bayan kwana biyu ya tafi Abuja shi da Zain washa gari su ka dawo d'auke da maganin da mahaifiyar Yousouf aljani ta ba shi, don ba zai manta ba ta ce masa duk wani cuta idan dai aljani ya sa ka to zai warke da izinin lillahi. Mai martaba da kan shi ya yi bismillah ya baiwa Mahensh a baki, maganin na wuce mak'ogoransa ya suma, suman da ya ta da hankalinsu domin bai farfad'o ba sai bayan kwana uku. Sai dai cikin hukuncin ubangiji ya farfad'o ne garas kamar bai tab'a kwanciya ciwo. Ko da Mai martaba ya gan shi rungumesa ya yi kuma cikin sauri ya sake sa ta re da nufar part d'in sa ya share kwalla don gudun ka da wani ya gani. Gaba d'aya masarautan ta d'auki murnan dawowa hayyacin yarima Mahensh in da sarakuna daban-daban su ka yi ta zuwa yi wa mai martaban yola murna. Ranar juma'a shi da kan shi ya ja sallah a babban masallacin masarautan in da ya sa mu dubbannin mutane ba matsaka tsinke. Tu ni ya watsu ko ina a media hotonsa kawai ke yawo. Duk budurwan da ta gan shi sai ta ce dama-dama.
(Can naga Darma, Queen Zahra, Haleematou, Farida H, Farida S, maman minal, Oumul da sauran y'an paid group ana turere niya wajan shiga. Aikuwa wani dogari ya bi su da zabgegiyar bulala su na gudu. Darma har da tuntub'e ta fasa baki. Haleematou kuwa jakar kud'inta wacce ke dauke da d'ari takwas da hansin😂😂😂😂😂🤪🤪)
.............Malam Yarima Mahensh fa tun da ya hango Fanan ya ce ya yi mata, kuma tuni ya sanar da mai martaba kuma a gaban Julaibib aka yi haka. Nan mai martaba ya ce was Julaibib shi ma ya fidda matar aure ko ya yi masa auran dole. Sinne-sinne ya shiga yi ya na sosa k'eya ta re da jan yatsun k'afarsa. Zaid kasancewar shi ma ya na wajan shi ya kalli mai martaba ta re da fad'in, "Allah ya k'ara yawan rai ai Julaibib Binty ya ke so, ina nufin Rukhsana". Cikin sauri Juliabib ya fice wai shi kunya wanda ya sa sauran y'an fada fashewa da dariya, shi kan shi mai martaba sai da ya murmusa.
Mai martaba sarkin Gombe sa kan shi takanas ya zo nai ma wa Julaibib auran Binty, Fu'ad kuma Rauhiyy, nan ma mai martaba sarkin Yola ya ke shaidawa sarkin Gomben su ma za su zo nai man auran Fanan. Sarkin Gombe ya ce ai ba sai ya zo ba tin da shi ga shi yazo ya kuma ya baiwa Mahensh auran Fanan. Shi ma sarkin Yola ya ce ya bai wa Julaibib da Fu'ad auran twins.
Lokacin da Julaibib ya sa mu labari, kamar ya zuba ruwa a k'asa ya sha haka yaji.
Gaba d'aya sun dawo abuja ban da Rukhsana (Binty) da kuma Rauhiyy don an bar su da mahaifiyarsu kuma za su je Sudan ne wajan dangin mahaifiyarsu.
Bayan sun dawo ne Mas'ud ya matsa shi ma aje a nai ma masu auran Sabrin, alhaji Usman shi ya je nai ma masa auran wajan alhaji Saifullahi, kasancewar duk an san juna, aka ba shi auranta a tare ya nai ma har da na Amrah kasancewar mahaifin Yousouf shi ya wakilta akan nai man auran saboda shi babban amininsa ne. Ashe daga can gefe Hamdan sun gama d'inkewa da tagwainiyar Amrah wato Hanan shi ma bai yi k'asa a guiwa duk da kuma ya na final year d'in sa ne. Sai dai shi ba'a saka ranar auran ba an bari har sai ya kammala school ya kuma samu aiki.
Julaibib, Fu'ad, Mas'ud, Yousouf an saka ranar auren su nan da wata uku masu zuwa, in da gadan gadan ya shiga k'arisa gininsa dama har an riga an saka kwano sauran k'adan ya rage irin su saka k'ofa da windows da kuma penti da dai sauran abubuwa.
Su Binty kuwa su na can Sudan, su na ganin tsan-tsan mulki da kuma k'awa fiye da sarautar Nigeria. Yadda ake masu kuwa abun sai wanda ya gani. Gyara kuwa da aka shiga yi masu abun ba magana domin duk inda su ka gitta sai sun bar k'amshi a wajan. Al'ada iri-iri sun gan shi awaya. Sai da su ka yi wata biyi cir ka min su dawo shi ma sai da aka had'o su da mai gyaran jikinsu. Rama kuwa Julaibib ya yi shi na rashin ganin Binty ga shi ko ishasshan waya ba sa yi.
Ranar da su ka duro yola, ranar Julaibib da Fu'ad su ma su ka duro. Julaibib ji ya yi kamar ya d'auke Binty su tafi, don wani irin kamshi da sihirtaccan kyau ta k'ara yi masa wanda ya dunga d'ad'dago sha'awarsa na shekaru da ya tara don har ji ya ke kamar ya matso da wata d'ayan da ya rage.
Kwanan su bakwai da dawowa su ka bi jirgi zuwa Abuja su da mai gyaran jikinsu da uban kayan gyara, Rauhiyy ta yi gidan iyayan rik'onsa, Binty kuma ta yi wajan Anna wanda su ka cika gidan da ihu ita da Fanan. Anna kuwa kafad'arta ya kusa cirewa sakamakon daka tsalle da Binty ta yi ta d'are ta.
Washa gari gaba d'aya amaran su ka dawo gidan Anna da zama. Anna kuwa ta yi fankan-fankan ta hana su Julaibib shigo mata side idan ba abinci za su ci ba, shi ma kuma su Binty na sama har su gama su fice. Sosai su ke shan gyara gaba d'ayansu. Sun canza sun yi b'ul-b'ul jikinsu ya yi fresh da santsi da laushi ga kuma sihirtaccen k'amshi da su ke yi.
Bikin ya rage saura kwana goma gaba d'ayan su ka yi Yola amma ban da Anna kasancewar za ta yi taronta ita ma. Tun bikin na saura kwana shidda aka soma shagalin. Al'adu na y'an Sudan kuwa sun gan su kala-kala. Domin ranar lafaya mai matuk'ar tsada su ka sa ka, ga wani kalli da aka masu da ya yi matuk'ar yi masu kyau. Takanas tun daga Sudan aka yi wa shahararriyar mawak'iya jirgi ta zo ta wak'e su. Ranar su Binty sun sha kyau ga kuma b'arin kud'i da aka dunga yi. Ranar d'auri aure kuwa, mai martaba ya ce marik'an su Binty su da kan su za su ba da auran su don su ne iyayansu. Sosai haka ya masu fad'i kuwa. Mai martaba kuwa shi ya yi wakilin auran Yousouf da Mas'ud wanda iyayan su ka wakiltashi kuma shi ma yaji dad'i.
Daga nan aka yo Abuja da su Binty da Rauhiyy ba y'an sun sha kukan rabuwa da Fanan kasancewar ita ta na can masarauta part d'in Yarima Mahensh. Binty gidan Anna Anna ka ta ka min a kai su gidan miji, Rauhiyy ma can wajan iyayan rik'onta aka kai ta. Daga baya dai Anna sai da ta yi danasanin wuto da Binty gidan ta saboda irin kukan da ta yi lokacin da za'a kai ta gidan Julaibib. Domin tsadaddiyar lace d'in jikin Anna sai da ya b'arke don tsabar jan shi da ta dunga yi ta na ihun kukan rabuwa da Annan.