Ba ni da gata - Chapter 43
Ba ni da gata Chapter 43: Ba ni da gata Chapter 43. Shi kuwa Julaibib ya na can ya na zumud'in zuwan amaryan ta shi. Bayan an kai ta an baro ta, Julaibib…
1,108 words
Shi kuwa Julaibib ya na can ya na zumud'in zuwan amaryan ta shi. Bayan an kai ta an baro ta, Julaibib ya shigo da malum-malum a hannu sai washe baki ya ke yi. A tsakiyar gado ya sameta kwance ta na shivering saboda zazzab'in da ke son kamata dalilin kukan da ta yi. Hawa gadon ya yi ta re da jawota jikinsa ta re da so ma yi mata magana a kunne, "Haba Qalby, sai ka ce wacce akai wa auran dole, wannan irin Kuka haka gashi ki na son ki b'ata min dare na, uhmmmiym! Haba masoyiya ki bar kukan haka mana ban jin dad'i kwarankwatsi". Duk da kukan da ta ke yi sai da ta saki murmushi tuno kawu Buban Kandala. "Yauwa ko ke fa". Ya fad'a ya na k'ara rungumeta a jikinsa. "Ta so ki je ki yi alwala ki zo mu yi sallah mu godewa ubangji da ya nuna mana wannan ranar". Fad'in Julaibib ta re da sauko da ita daga kan gadon, ta re su ka shiga bayin ta yi alwala shi ma ya yi, bayan sun gabatar da sallah ya yi mata addu'ar da ko wani Ango ya kamata ya yi wa amaryansa. Ka na ya shiga ciyar da ita kaza da fresh yoghurt wanda ta ci kad'aan (Ta bar zuly da zubar miyau😂). "Ta shi muje d'aki na, don ban yarda da wannan d'akin ba don naga kamar kwayar ido na leke kuma na tabbar Darma ce ko Queen zarah, idan ba su ba to Haleematou ce kuma ba za su ga komai ba". Fad'in Julaibib ta re da ka ma hannunta su ka koma d'akinsa ta re da turo k'ofa dai-dai Darma ta kawo kai aikuwa k'ofar ya bugu a goshinta sai da ya yi k'ulu.😂😂🤪🤪 Daran ranar Binty ta yi kuka, ta yi ihu, ta yi magiya da cizo amma Julaibib bai saurara mata ba sai da fanshe zaman gwagwarcin da ya yi a kanta don har suma sai da ta yi. Washa gari kuwa ya gyara abunsa tasss.
Haka ma a can Yola ya faru, kasancewar har gobe su na al'adar farin kyalle, Jakadiya ta yi shela akan matar yarima ta kawo budurcinta. Sarauniya Zameelah ita ta fara isar da kyautarta na awarwaron zinari guda hud'u, Katanga ma ta ba ta na ta kyautar na sarkan gold ya yin da mai martaba ya saya mata mota ta re ba ta kujeran hajji har na mutun goma ta zab'i wanda zai je a danginta.
..........Sabrin kuwa bakin nan mutuwa ya yi don ita ma ba k'arya ta gurzu sai ta koma owners corner ta yi shuruuuuuuu.
Hajiya Rauhiyyah kuwa kamar jab'a ta fad'a a koko tsabar jigata don har carbi ta d'auko ta na ta jaa, sallah ko ta yi ya kai raka'a goma saboda ka da ya shigo wani tsautsayin ya sa ya ce zai sa ke.
Su Hajiya Amrah ba magana don idanuwanta gaba d'aya sun kumbura.
...........Bayan wata d'aya da auransu, Julaibib ya yi lunching k'atotan asibitin da babu kamar shi a abuja, wanda mai martaba sarkin Yola sirikinsa da kuma sarkin Gombe da ministern Abuja su suka bud'e asibitin. Binty a gida kuwa ta had'a kwarya-kwaryan waliman ta da gaba d'aya amaran sun zo har da Fanan da ke Yola. Kuma gaba d'ayan su su na da shigan k'aramin ciki. Na Binty ya fi nunawa kasancewar laulayi ta ke yi mai zafi don jinin Julaibib na da k'arfi don O'negative ne. Genotype d'in sa kuma AA. O'negative sai ka tara mutane d'ari da kyar ka samu d'aya mai irin jinin.
AFTER 10TH MONTH Sabrin ce ta fara haihuwa, ta haifi d'anta namiji Aahil, bayan kwana uku Rauhiyy ta haifi y'an biyu mace da namiji, su ka ci suna Aayad da Airah, tsakaninsu da Binty kwana d'aya ta haifo mace mai kama da ita sak ta ci sunan Anna Na'ima, su na kiranta da little Anna, Amrah ce k'arshan haihuwa ta haifi mace ita ma ta cire sunan mommah Rahima suna kiranta da khairat. Lokacin an saka bikin Hanan da Hamdan wata takwas masu zuwa don har ya gama service kuma mai martaba sarkin Gombe da kan shi ya karb'i takardunsa ya nai ma masa aiki. Soyayyar ruwa-ruwa ya ke gudana tsakanin Julaibibda da Binty, ba sa fushi mai tsayi da junansu. Sun shimfid'a rayuwarsu cikin fahintar juna, idan d'aya ya yi fushi, d'aya zai sauko ya taushi d'aya.
Ranar bikin Hamdan kuwa sun yi rawa sun cashe ka na su ka mik'a amarya Hanan gidan mijita wanda su ka b'oye su ka yi kuka sosai na rashin mahaifiyarsu akusa ta na can prison ta lalace don duk wata sai sun je ganinta.
Hajiya Kandala an yi shekara uku an fito daga gidan yari ta kod'e ta jeme. Kai tsaye Datu ta fara naima wacce gaba d'aya kud'inta na hannunta da ta k'arba da sunan juya mata kud'in. Sai dai ta yi katari da abunda ya kusan tsayar da numfashinta domin kuwa Datu ta yi aure ta da d'an damfara ya damfareta ya kwashe komai ya gudu zuwa Dubai. Kai tsaye Saminaka ta nufa, in da aka yi mata koran kare domin bayan tafiyanta matar Buba mai kwarankwatsi ta tona asirin komai wa Goggo Shatu.
Wannan tsoho kuma da su ka dawo duniyar aljanu da su Binty ba kowa ba ne fa ce alhaji mai tumbi da mahaifiyar Yousouf ta tafi duniyar aljanuda shi wanda tashin hankali ya sa ka ya yi loosing memory don iyalansa ma sun dad'e da gama Rabin gadon shi ta re sake sure don sun d'auka ya mutu, kuma bayan barin gida na tsawon lokaci su ka Shiga d'akin sirrinsa da bai bari a shiga su ka ga ne ya fad'a k'ungiyar asiri ne.
*TAMMATA BIHAMDULLAHI*
_NAN NA KAWO K'ARSHAN WANNAN LITTAFI WANDA BA HAKA NA SO TAFIYAR TA TSAYA NA, WALLAHI UZURI NE GARE NI BABBA DA FATAN ZA KU MIN AFUWA._ _KUSKURAN DA NA AIKATA YAYIN RUBUTA WANNAN LABARI ALLAH KA YA MIN, ZAN YI AMFANI DA WANNAN DAMAR IN ROK'I YAFIYAR KU WAD'AND'A NA B'ATAWA RAI, NI NA YAFE MAKU HAR CIKIN ZUCIYATA, ZAN TAFI OFFLINE WANDA BAN SAN RANAR DAWOWA TA BA, DAN ALLAH KU YAFE MIN WATAKIL WANNAN SHI NE BOOK D'INA NA K'ARSHE. ALLAH SHI YA SAN GAIBU._
_NAGODE NAGODE NAGODE DON KUN NU NA MIN AMANA, DON BA KU FITAR MIN DA BOOK BA, HAKAN YA TABBAR MIN DA KU D'IN YAN HALAS NE WANDA KU KASAN AMANA DA KUMA HUKUNCIN WANDA YACI AMANA. ALLAH YA K'ARA BA KU IKON RIK'E AMANA YA SA HAKAN SHI ZAI SAMO SILAR SHIGAR KU ALJANNA_
😭😭😭🤧🤧
_SAI MUN SA KE HAD'UWA IDAN DA RABON HAKA_
*MATAR SAYYADEE*🥰