Kenza eBookz

Babban gida takun farko - Chapter 4

Babban gida takun farko - Chapter 4

Babban gida takun farko Chapter 4: Babban gida takun farko Chapter 4. Ba don uncle Suraj ya so ba haka ya haƙura ammah tabbas yarinyar nan zata ci ƙwal…

3,354 words

Ba don uncle Suraj ya so ba haka ya haƙura ammah tabbas yarinyar nan zata ci ƙwal ubanta.

Bayan uncle Hashim ya gama clsss ɗin yace lallai Zahrah taje principal's office yanzu. Bata ma San meh yake nufi ba ta dai ji principal kenan ƙarar ta ya kai. Hmm.

Bin bayan shi tayi har suka isa, sai bayan ya shiga ta shiga,

Gaida principal ɗin tayi da turanci, ya amsa mata. Kneel down ya saka ta a gefe yayin da uncle Hashim ke zaune kan kujera..

“What's that your name miss?” principal ya tambaye ta. “Ohoh wannan ai na sanshi” ta faɗa cikin ranta. “Zahrah Abdulkarim Kuru.” daga haka tayi shiru. Kamar wanda ya gano bata jin turanci sai ya dawo mata magana da Hausa.

“malamah Zahrah MEH yasa malam ya baki umarni kika ƙi bi?" Kanta ta sunkuyar ƙasa “mallam Ni ban san da Ni yake ba, kuma ban ji MEH yace ba”

Kallon baki da wayo ya mata “kina nufin duk maganar da nayi baki ji ba, ƙarya kike” sai a lokacin ta fahimci ashe ya iya Hausa ma kuma shine da tayi shirin bai yi mata ba.

“Wallahi ban ji ba, Ni bana gane turanci da Hausa kayi min ai zan gane, kayi haƙuri”

Haƙurin da ta faɗa yasa ya sauƙo “meh yasa to baki jin turancin?” “makarantar gwamnati nayi makaman namu ma ba iyawa suka yi ba kuma yau na fara zuwa nan ɗin”

Nan da nan suka sake suna ta hira shi dai PC kallon su kawai yake.

“kina don ki koyi Turancin ko kuwa” “ina so sosai, sai dai ban san yadda zanyi ba” “shike nan kada ki damu zan na koya miki kullum ko abu biyu ne, lokacin break kike zama a aji zan ke zuwa. Cikin murna tace “na gode Mallam” “tashi ki koma class".

Haka suka yi second period ammah lokacin uncle ɗin su bai tayar da ita ba. Lokacin da aka tashi kuwa tana fita taga motar yaya Ishaq, da sauri ta ƙarasa ta shiga.

“ƴan makaranta, hope kin ji daɗin makarantar” ɗan yamutsa fuska tayi kafin tace “ga ta nan dai, Ni kam yau abun kunya dai nayi" Zaro ido yayi jin tace abun kunya “faɗa kika yi ko cutie" “aah Yaya, wani malami ne yake ta min turanci Ni kuwa ban san meh yake cewa ba ashe wai cewa yayi na tashi na amsa tambaya.”

MEH yaya Ishaq zai yi in ba dariya ba. Ɓata ran da tayi yasa ya tsagaita. “toh ya kika yi kuma?” Ɗan bakin ta ta turo “ Ni zama na nayi ban kula shi ba shine yace na fita, Ni wallahi ban san da Ni yake ba” “ya zane ki kenan?” “aah ai ban fita ba saboda ban san da Ni yake ba, shine ya ƙira wani mai fuskar shanu ko dariya da baya yi”

“sai kuma shi mai fuskar shanun ya zane ki?” “aah shima cewa yayi na fita to ban san duk a kaina ake ba Ni kuwa nayi zama na, duk sai suka fita tare, shine malamin ya dawo ya ci gaba da darasin, Ni ban ma gane ba”

“shikenan kada ki damu zaki koyi Turanci fiye da malamin in kika sa kanki, mu bi na siya miki wani littafi ki gani” Girgiza kai tayi sannan tace

“baka tambaye Ni ya aka ƙare ba ai" “ina jin ki ai” Shine da ya gama yace muje office ɗin wani ina ga dai headmaster be"

Dariya yaya Ishaq ya saka yace “kai cutie babu headmaster a secondary School sai dai principal" Ranta ta haɗe tamau “toh ai Ni ba sani nayi ba” “shikenan ina jinki, principal ɗin ya duka ki kenan”

“aah shi da Hausa ya min magana shine na ce masa Ni ban fahimci da Ni yake ba kuma bana jin turanci, malamin kuwa yaji tausayi na yace zai je koya min”

Murmushi yayi daidai isowar su wani bookshop. “ki jira Ni ina zuwa”

Ɗauke da littafai a hannun sa ya fito “yauwah karɓi waɗannan cutie, ki riƙe su da iya su zaki ita turanci, sannan ki ƙara maida hankali, duk abun da baki gane ba ki tambaya kinji kar kiji kunyar kowa” “toh"

Ita kaɗai ta shiga gidan shi kuma ya juya. Duk wainar da ake soyawa Kawu bai sani ba.

Bayan ta ci abinci kawai sai taji sha'awar zuwa islamiyya. Wanka tayi ta fito. Ganin yadda uniform ɗin suka cakushe saboda rashin ya sa ta ɓata fuska. “ke kuma lafiya?” Mamah ta tambaye ta Kayan ta nuna mata sai wani tura baki take yi “kiga kaya na kamar daga bakin kura aka amso su” “toh ki shiga gidan su Badi'a ki goge mana kafin lokacin" da kamar bazata je ba sai wata zuciyar ta ce kije.

Sai da tayi nadamar zuwa islamiyya dan kuwa Ustaz Jamil sai da yaci ubanta kan fashi, kuma ya sata duk haddar da yake Binta sai ta biya.

Tun daga ranar kuwa tayi alƙawarin ba zata ƙara zuwa islamiyya ba ko za'a kashe ta, ammah da ta koma gida Mamah tace ai dole sai taje. Tsabagen bakin ciki kamar tayi kuka.

Haka rayuwar Zahrah ta kasance, cikin satin nan kuwa tayi mummunan sabo da ƙawar ta Badi'a yau in suna gidan Mamah to gobe suna gidan su Badi'a.

Ranar Asabat da yammah yaya Ishaq ya zo don yi wa su Mamah sallama. Mamah kam har da kukan ta saboda yace ba lallai ya dawo ba sai bayan shekara biyu ko uku. Uwar gayya Zahrah kuka kamar zata mutu,

“haba cutie, meneneh kuma abun kukan? Ba dai zamu na waya da sabuwar wayar Mamah ba?, Toh kiyi shiru kinji, idan ma kin dage a school in na dawo sai mu tafi tare kema ki shiga jirgi"

Jin yace jirgi nan da nan ta goge hawayen fuskar ta “shikenan yaya zan dage kuma zaka yi alfahari da ni” Murmushi yayi mata sannan yace zo muje ki raka Ni siyayya..

Shopping mall suka je ya siyo mata kayayyaki da mayuka da sauran su. Sandals talkalma duk ya siya mata a cewar shi ko baya nan ba sai ta siya ba. Daga haka suka dawo gida cikin farin ciki. Ranar tare suka yi dinner, sai wajen 9:45pm ya tafi cike da kewar cutie ita ma cutie ya bar ta da kewa. Ko ba komai soyayyar mahaifi da ta rasa tana samun ta wurin yaya Ishaq ga kuma sabuwar ƙawar ta da kuma Ammi har da Abba. Hakan ba ƙaramin daɗi ya mata ba tunda Kawu yanzu ko ya zage ta ba kula shi take ba.

Ƙarfe goma da rabi suka fara shirye-shiryen kwanciya kawai suka ji an banko ƙofar ɗakin.. shaye da mamaki Mamah ke duban Kawu da ya shigo fuskar shi ɗaure kamr kumburarriyar fulawa. Zahrah ko ko kallon yadda yake bata yi ba. Duban Mamah yayi yana wani cika yana batsewa..

“ke Madina, ina so ki share gidan nan gobe tatas kina ji ko?” Caraf Zahrah tace “toh kaga gidan cikin datti ne da zaka yi magana?” Banu yadda ya iya da Zahrah kawai ya ci gaba da muzuran shi “ni dai na faɗa miki, ɗaki na mah a ciro komai na cikin shi don kuwa gobe dalleliyar amarya ta zata zo gidan nan”

Zaro ido Zahrah tayi lokaci ɗaya yanayin fuskar Mamah ya sauya. Bata ce mishi ƙala ba har ya gama surfa bayanan shi ya fice fuu Kamar Mahaukaci.

Daren Mamah bata samu ta rintsa ba, ba wai saboda kishi ba aah sai don bata san waye Kawu zai auro ba.

Washegari tun safiya Mamah ta cika umarnin Baba, da kanta ta gyara gidan tsab gudun kada taƙi yi ma ya ci mata mutunci gaban baƙin amaryar.

Dawowar Zahrah daga school ta kafa rikici ita ala dole ba zata je islamiyya ba tunda za'a yi baƙi a gidan.

“haba Zahrah, yanzu inda kin zauna uban meyeh zaki yi a gidan” Fuskar ta a kwaɓe take kallon Mamah “mamah naga yau za'a kawo amaryar Kawu, Mamah ina tsoro su zo bana nan nasan ko sun miki abu ba zaki rama ba ammah idan ina nan zan tare miki” ta ƙarashe da Muryar tausayi. “ke yarinya ce Zahrah, idan sun yi min ma a banza suka yi tunda ba kula su zan yi ba, maza tashi ki tafi makaranta.”

Ganin da gaske Mamah so take ta hana ta zama kawai ta ɓare baki ɓaaaaaa sai ihu “wallahi Mamah in na fita ba zan dawo ba, tsayawa zanyi mota ta buge ni shikenan ai koh” ta fice a guje. Mamah da ta rasa abun yi sai tabi bayan ta tana ƙwalla ƙira “zahrah, Zahrah ki dawo shikenan na yadda" duk da ta ji me Mamah tace tayi burus ta ƙara wa bujen ta iska, Mamah na biye da ita har suka kawo ƙofar gida tukun ta juyo. Marakraice fuska Mamah tayi hakan yasa ta dawo ta rungume ta duka su biyun suka fashe da kuka mai ban tausayi.

Sai zuwa yamma tawagar amarya suka zo, ihu da shewa ba'a magana. Sai da suka gama jere suka fito tsakar gida su ka fara zage zage.

“Munafika uwar kishi tayi luƙus a ɗaki” Wata daga cikin matan tayi caraf “kin san damah ba zata fito ba ai. Irin matan nan fah sai Saudatu ta dage, don kuwa ko meh kika musu ba zasu ji haushi ba” Ɗayar matar da ta fara magana tace “toh ai babu zuciya kin sani, shi yasa tayi shiru” Hannu suka tafa suna sake guɗa da shewa irin nan matan barikin nan. “ƙawa ta baki da dama, wallahi gaskiya ne maganar ki, kin san ance bata da dangi, kamar ma Idrisun tsinto ta yayi” “Toh Allah dai ya kiyaye, ammah dole Saudatu ta dage” “ke dai lantana kawai ki bari"

______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️

PROLOGUE

𝕻𝕬𝕲𝕰0️⃣7️⃣

Wannan shafi sadaukarwa ne gare ku masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘

SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________

A kunnen Zahrah suka faɗi komai yasa ta ce “Mamah bari naje banɗaki na dawo” Mamah bata ce komai ba saboda bata ji MEH suka ce ba. Zahrah na fita ta Banka musu wani bazan kallo mai ɗauke da ƙasƙanci da tsana kafin ta ja wani tsaki “Mtsssss....daɗin ta ma gidan aka zo ana same ta”

Matar da ɗazu aka ƙira da lantana ce ta zaro idon ganin yarinya ƙarama na mata rasar kunya. A fusace ta yo man Zahrah babu shiri ta goje, wani ice ta gani a gefen ta tayi saurin rarumar shi” Lantana Bata haƙura ba ta ƙara biyo Zahrah ai kuwa bata aune ba taji ice a bayan ta. Ƙarar da tayi ne yasa Mamah da sauran ƴan kawo amarya fitowa.

Tunda ta jinka mata icen ta ja gefe tana sauƙe numfashi, lantana kuwa zube wa ƙasa tayi tsabar azabar da bayan ta yake yi. A hankali Mamah ta tako saboda ta taimakawa Lantana. Hannu ta miƙa mata cike da ƙuluwa ta doke hannun Mamah ta miƙe. Still ta ƙara yin kan Zahrah a fusace

“yau mai hana Ni cin bura uban yarinyar nan shima sai naci uban sa”

Babu alamar tsoro a tattare da ita sai karkaɗa jiki take. A hanzarce Mamah ta taho zata ja hannun Zahrah. Ɗaya daga cikin ƴan kawo amarya kuwa ta bangaje Mamah.

Abu ƙarami dai ya dawo babba. Don kuwa Zahrah janye Mamah tayi zuwa ɗakin ta. Jawo ƙofar tayi ta fito ta fara by bubbuga musu icen nan, ance Sarkin yawa yafi Sarkin ƙarfi ammah wannan karon naga ikon Allah.

Hayaniyar da ta kaurece ga kuma ihun matan ya jawo hankalin ƴan unguwar. Tuni gida ya cika ana ta tambayar ba'asi da ƙyar Ammi ta lallashi Zahrah suka wuce ɗakin Ammi. Labarin ya matuƙar ɓata ran Ammin. Saboda haka ta ja hannayen su duka biyun suka bar gidan.

Dare na yi aka kawo amarya tare da ƙawayen ta wanda shigar su kaɗai kaga kaga ƴan jagaliya, guɗa ce kawai ke tashi sai uban habaici da ake gabzawa wanda wacce suke yi wa bata ma san suna yi ba. Damah tuntuni labari ya isa kunnen Saudatu Kwalba, shi yasa ta tattaro duk ƙawayen ta da niyyar sai sun ci uban uwa da ƴar, sai dai babu yadda zasu yi takaici ya cika su ganin babu kowa a ɗakin, kenan har sun gudu?. Ai kuwa dabara ta zo wa Aunty Amarya kan in ango ya shigo ta haɗa shi da matar. Ai kuwa ta samu na nasarar hakan. Ran kawu ba ƙaramin ɓaci yayi ba “zasu dawo gidan su same Ni ai"

Su Kawu an ci amarci an gaji da amarci. Kwana biyu su Mamah basu dawo ba nan fah Kawu yasa sha jinin jikin sa.

“Fatan na Allah yasa dai ba aikin da nayi bane ya ɓaci, idan kuwa haka ne toh akwai matsala!” “kai bazai yiwu ba!!! Inaaaah! Madina wallahi bayan barki ba!, Dole mu rayu tare kuma dole kiyi rayuwar ƙasƙaci!.

Yanzu dai ina da zaɓi ɗaya ne, dole na fita ko ina na zaga saboda na nemo su!, Ina sun tafi fa komai ya lalace, duk burin da naci zasu ruguje!!! Zan nemo ku duk yadda kuka je ne”.

Ɓangaren yaya Ishaq kuwa ya keta hazo tare da kewar ƙanwar shi.

Wasa wasa sai da su Mamah suka shafe sati guda a gidan Ammi tukun na suka haɗo domin dawowa, Ammi ta bawa Mamah kayayyakin sakawa nata, na Badi'a kuma ta bawa Zahrah. Zuciyar su wasai suka dawo abun su. Lokacin da suka dawo Saudatu Kwalba na zaune akan shimfiɗar tabarma da tayi, gefen ta kuma ƙawar ta ce Asabe Bala'i sai hira suke yi.

Ɗauke da sallama su Zahrah suka shiga, Asabe ce ta ɗago tare da mamakin da ke bayyane akan fuskar ta sai kuma ta sauƙar da kan ta ƙasa. Ƙasa ƙasa gudun kada baƙin su ji ta tace “ke Kwalba waɗannan su waye” “ina kuwa zan san su waye” ta juyo wurin su Mamah. Ganin sun tunkari ɗakin kishiyar yasa ta miƙe zuwa wajen su. Cike da hatsabibancin ta irin na ƴan Iskan matan bariki ta wani riƙe kunkumi. “baiwar Allah uban meh zaki yi kin shigo gidan miji na ba izini kin dashi ɗaki kumah?”

Murmushi mamah ta cilla mata wanda yasa zuciyar ta ƙara tafasa. “kut!!!! Ina miki magana, toh don Ubanki jawo hannun ƴar ku mai zubin aljanun nan ki fita min gida” “a'ah!, Shi mai gidan bai faɗa miki cewa mata biyu gare shi ba?”

Amsar da mamah ta bata ne ya tabbatar mata da cewa ita ce Madina matar Idrisu. Lokaci ɗaya ta shiga ruɗu. Mamah kuwa ta ciro key ta buɗe ɗaki suka shige ita da Zahrah.

Mamaki ya matuƙar kama Saudatu har sai da Asabe ta zo ta ja ta suka wuce ɗaki.. “ke Bala'i ammah idrisu ya raina Ni, irin wannan yaudara haka” “wai MEH ya faru ne?" “ke da kike gani wannan tsuleliyar matar da kika gani da yarinya mai shegen kyau kamar ɗiyar Mayu matar sa ce fah!!” Shaye da mamaki Asabe ke kallon ƙawar ta. “lallai in dai haka ne toh bamu ga ta zama ba” “ai kuwa, yanzu meyeh abun yi?” “rabu da ita kawai, zan bata shekara biyu zuwa uku ta sarara sannan na aika ta lahira shikenan, ɗiyar ta kuma ta zama jaka ta” “Ammah Kwalba bakya tunanin a samu matsala kafin lokacin da kika bata?” “A'ah Bala'i, ba a so a fahimci komai game da mutuwar ta, yanzu haka zan aika a kawo min Bibalo ta dawo waje na da zama ko dan saboda cikar buri na. Idan Bibalo ta dawo nan kinga ai Sa'ar yarinyar ce, xan sa take cin zalin ta kuma na hana ayi magana har baƙin ciki ya kama uwar, daga ƙarshe cikin shekaru ukun da na ɗebar mata ciwon damuwa yayi mata mummunan kamu, sai na sa boka Bulebule ya ƙarasa min ita, daga nan kuma ɗiyar ta ta zama tawa, sai yadda nayi”

Dariya suka kwashe da ita suna tafa hannu “kai ƙawa ta baki da dama!, Ƙwaƙwalwar ki tana mugun ja” “ke dai ki bari, ko kin manta suna na ne ‘kwalba’?” “hhhhhh haka ne fah, shiyasa nake daɗa ƙaunar ki”

(TOH KUN JI FA KUDIRIN AMARYAR KAWU, KO YA ZA'A KAYA?

Ɓangaren Mamah kuwa suna shiga ta ƙara kaɗe ɗakin ta, ta gyara zaman kayan abincin su da kyau, sai lokacin ta tuna yau da Ishaq ya tafi. Addu'a da fatan alkhairi tayi ta jera masa. Daga nan suka yi zaman su a ɗakin..

“zahrah” jin mamah ta ambaci sunan ta yasa gaban ta faɗuwa don ta San in tayi mata irin kiran nan toh abun is serious. “na'am Mamah ta” “kina ji na koh” “eh Mamah ina jin ki” “ko da wasa ban amince kiyi wa matar kawun ki tsiwa ba, kinga idan kika yi mata zaki jawo mana kawun ki ne shiga rayuwar mu, don Allah Zahrah ki mata biyayya kin ji" Cikin sanyin jiki ta ce “toh mamah naji ammah wallahi idan ta shiga harƙa ta ba zan ƙyale ta ba” “zahrah kenan! Ba zaki taɓa sauya wa ba, baki tunanin gaba ne kam? Yanzu in aka ce bana nan rai yayi halin sa gashi kuma baki da kowa a duniyar nan fah? Su ɗin dai sune dolen ki a lokacin, kuma baki da wanda suka fisu, ya kamata zuwa yanzu ac kinyi koyi da hali na” “haba Mamah Allah ma ya sauwaƙe, Ni zan riga ki mutuwa ma kuma mamah ai ko kin mutu akwai ahalin ki, shiyasa nake cewa Ni ki haɗa Ni da su ko da ace ke ba zaki je gare su ba”

Lokaci ɗaya yanayin Mamah y sauya, abun da take ji a ƙirjin ta Allah kaɗai ya sani, hawaye ne kawai ke zuba daga idon ta. Nan hankalin Zahrah ya tashi don. Ko kaɗan bata son ɓacin ran Mamah. “mamah ta don Allah kiyi haƙuri Ni nayi miki laifi ko" Jijjiga kai tayi don a halin yanzu ko kaɗan ba zata iya magana ba. “shikenan kiyi haƙuri ba zan ƙara tambayar ki ahalin ki ba tunda na fahimci ba kyaso, kiyi shiru haka don Allah” ta ƙarasa itama hawaye na zuba daga idanuwan ta yayin da take goge wa Mamah nata hawayen.

Da ƙyar Mamah tayi shiru sannan ta kamo hannun Zahrah ta ƙanƙame cikin nata tamkar za'a ƙwace mata ita. “ɗiya ta Zahrah, ba wai bana so ki san ahali na baneh sai dai kawai in anyi maganar ina shiga wani yanayi, kada ki damu wata rana da yardar Allah zaki gan su har ki rayu da su” “shikenan Mamah na ta kaina na daina ba zan ƙara tambayar ki ba, to yi murmushi muga" Ta faɗa tana lakuce kumatun Mamah. Nan da nan kuwa suka ware suka ci gaba da hidimar su.

Wajen azahar Ammi ta aiko Badi'ah da basket ɗin abinci ta kawowa Mamah. Sun daɗe suna hira da ƙawar tata kafin ta tafi. Suka ci abincin su kafin su fitar da kayan Masar Mamah su ka ƙara tsaftace su.

Da yamma Mamah ta wuce kasuwa wurin kasuwancin ta, alhamdulillah yau kam da wuri ta gama har aka zo ana neman masa. Da taimakon Lauwali suka dawo. Bayan ta sallame shi ya tafi. Duk abun da yake faruwa akan idon amaryar Kawu, jira kawai take mai gidan ya dawo ta zuba mishi yasha.

Ana yin Sallah sai ga Badi'ah da basket ɗin abinci, Mamah ta amsa tayi godiya sannan ta bata wancan na ranan because it's already washed. Badi'a na shirin fita taji an riƙe kafaɗarta, a tsorace ta ɗago ɗin ganin waye. Murmushi mai ɗauke da ma'anoni ta ke zuba mata.

“ƴan mata nace waye yake aiko ki kawo abinci?” tun da ga nan ta harbo matar, “kenan wannan ce auntyn Zahrah, tab, tallai akwai matsala dole na sanar da Ammi" jin bata bata amsa ba yasa ta ƙara maimaita mata “ƴan mata wai waye ke aiko ki kawo abinci ne” “nimah ban sani ba, sake Ni na tafi gidan kada a neme ni” “kenan ba aiko ki ake yi ba” “eh Ni nake kawowa da kaina, sake Ni" Banu yadda Saudatu ta iya ta sake Badi'a, a tsorace ta isa gida.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull