Babban gida takun farko - Chapter 6
Babban gida takun farko Chapter 6: Babban gida takun farko Chapter 6. Daga haka ƙiran ya katse. Principal ne ya shigo tare da uncle Hashim da uncle Suraj.…
3,294 words
Daga haka ƙiran ya katse. Principal ne ya shigo tare da uncle Hashim da uncle Suraj. A nan kowa ya yabe ta tare da faɗin irin alkhairin da makarantar ta samu sanadiyyar drama show ɗin su, Governor daga baya da kanshi ya aiko wa makarantar saƙo kuɗaɗe masu yawa haka manyan mutane suka bada kuɗaɗe su mah. She's totally speechless on how victorious she's, and she promised to do better than this. Daga ƙarshe yace ta turo baban ta domin karɓa mata kyaututtukan da ta samu, in ta fita ta kira mishi Badi'a. “ohk sir" daga haka ta fice zuwa class. Badi'a ma same message aka yi passing mata. Finally they decided to send Abba, don ita ko karen huka ne ya cije ta ba zata taɓa turo Kawu matsayin wani nata ba. Toh me mah ya kai ta? Mutumin da bai san ci ko shan ta ita da mahaifiyar ta ba a matsayin shi na wadda hakƙin su ke a wuyan shi, bai don ko da lafiyar su da rashin ta ba. Inaaaah ba zata taɓa ba ko da kuwa alkhairi zai wuce ta ne.
Haka har lokacin tashi suka koma gida daga nan suka tafi islamiyya. Bayan sun dawo kowa ya wuce gidan su.
★★★★★★★
Tafiya suke ita da Asabe Bala'i cikin wani ƙungurmin daji wanda ke da matuƙar duhun tsiya suna tafiya suna sare ice saboda irin bishiyoyi masu canopy ɗin an ne a ciki. Sunyi tafiyar da ta kai kimanin 2hours kafin su iso wajen wani old building Wanda ke zagaye da wasu bishiyoyi masu baƙaƙen leaves. Daidai ƙofar wajen suka nufa.
Tsawa aka buga musu “kai!!! ba'a shigowa nan da ƙafar damah! Ku fice” A tsorace dukan su suka juyo don irin yadda Muryar ta kasance maras daɗin sauraro da kuma mugun tsoratarwa...
“zaku iya shigowa yanzu ammah kada ku kuskura ku shigo min da ƙafafun dama” A ruɗe suka shiga kamar dole. Wani irin gini ne maras kyawun fasali, jikin ginin baƙi ƙirin ga wasu ƙwari baƙaƙe dake yawo jikin ginin, duhu ne ya mamaye wajen lokacin ɗaya suka rasa inda da zasu sanya kansu yayin da suka ji wata guguwa ta tashi, rumtse idanuwan su suka yi sannan suka ji iskar ta janye su zuwa wani sashe. Lokaci ɗaya haske ya bayyana a wajen, suna buɗe idanuwan su suka gansu zube gaban wani mutum mummuna..
Idan nace muni to fah munin ya wuce misali, fuskar shi ne baƙa ƙirin ta yamutse ga uban gashin kai kamar na wata baindiya sai dai nashi babu alamun gyara, gemun shi ya kai saitin guiwar shi Tsayin sa kuwa ba'a magana haka girman jikin sa ya wuce misali. Sam ba shi da daɗin gani. Dariyar shi ce ta ƙara tsoratar da su suka fara zazzare idanuwan su kamar waɗanda suka yi wa sarki ƙarya.
“Hhhhhhh.....Saudatu Kwalba tare da ƙawar ta Asabe Bala'i. Hhhhh...hhhhhhh.....barkan ku da zuwa fadar Bulebule Bokan kowa hhhhhhh....hhhhhhh....” “mun go....de...ran....ka..shi...daɗe....”
Lokaci ɗaya ya haɗe fuskar shi ya fara duban su. “Kwalba kin zo akan kishiyar ki ko?" Cike da mamaki ta ɗan kalli boka Bulebule. “kin zo ne akan ta mutu ammah ba yanzu ba sai nan da shekara biyu sannan ki mallake mijin ki da kuma ƴar ɗan uwan sa zahrah”
“eh haka ne ranka shi daɗe ka taimaka min” “shikenan kada ki damu"
Wata ƙwarya ce ta bayyana a gaban shi, cikin ta ya fara surkulle yana furta wasu maganganu. Can ya buga kwaryar nan da nan ta ɓace
“Akwai matsala! Matar nan ba zata mutu ba sai dai zanyi miki wani aiki da zata haukace, idan ta haukace ita da kanta zata fara jinya sai ta gudu ta bar gidan. Ita kuma ɗiyar ta zaki mallake ta ammah akwai babbar matsala don kuwa akwai manya manyan sheɗanu a tattare da ita wanda Ni kaina tsoron taɓo su nake. Mijin ki ki sa a ranki kin mallake shi. Hhhhh....hhhhhhh...hhhhhhh..”
“yauwah ranka shi daɗe na gode sai kuma kuɗin aikin" Dariya yayi sannan yace “bulebule baya karɓar kuɗi kasafai sai dai ladan aiki da zaki bashi wanda ya kasance mai sauƙi. Zaki zauna a tare da ni na kwana biyu, zan yi amfani da ke sau biyar” Ba tare da ta damu ba tace “shikenan ranka shi daɗe na gode”
“ke Asabe zaki iya tafiya ita sai nan da kwana biyu ammah in kina so zaki iya zama zan baki ɗaki kema anan” “shikenan ranka shi daɗe zan kwana a nan ɗin”
(Authubillah!!! Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama yace :duk wanda yake wurin ɗan duba, ko kuma boka, kuma ya aminta da abun da ɗan duban ya faɗa masa toh haƙiƙa ya kauracewa abun da aka sauƙin min”
Mata muji tsoron Allah mu sani mutuwa tana nan tana jiran mu, MEH yasa in muna da bukata bazamu riƙa wurin Allah ba? Shi fah in ka roƙe shi zai amsa maka kuma baya gori dan ya baki. Saboda haka ki kiyaye in son mallake mijin ki toh ki kyautata masa da haka zaki sace zuciyar sa kai har ma da ta dangin sa matsawar kina kyautata musu.
Allah ya tsare).
★★★★★★★
Abba da kan shi ya amso musu kyaututtukan su. Cike da farin ciki ya dawo yana nunawa Ammi. Sunyi farin ciki da nasarar yaran musamman Zahrah da ta kasance babu mai tsaya mata damah. Sai da yammah dab da dawowar su daga islamiyya suka wuce zuwa gidan Mamah.
Tabarma ta shimfiɗa musu “sannun ku da zuwa maraba lale” “sannun mu Maman zahrah” Bayan sun zauna ta ɗebo musu ruwa. Ba tare da nuna ƙyama ba Ammi ta kurɓi ruwan. “ina wunin ku ina gajiya” “lafiya ƙalau Maman Zahrah" “ya hidima kumah, Allah dai ya saka muku da alkhairi Abban Badi'a" “amin babu komai Maman Zahrah ai yiwa kai ne," Murmushi mamah tayi. Abba ya gyara murya sannan ya fara magana “toh kamar dai yadda kika ganmu a nan mun zo ne don taya ki murna bisa nasarar da Zahrah ke samu a makarantar su ta boko. Shekaranjiya anyi tarin yaye ɗalibai a makarantar tasu, toh a nan ta samu kyaututtuka da dama, akwai kuɗaɗen ta kimanin Naira Dubu ɗari biyu (200k) Wanda ta samu daga wurin manyan mutane a faɗin jahar da kuma wajen ta. Saboda haka ne ma na amso musu saƙon ita da ƴar waje na Badi'a.”
Cike da farin ciki Mamah tace “madallah Allah ya saka da alkhairi Allah yasa mai amfani ne” Ammi ta amsa da “Ameen” “toh saboda haka ne nake ganin MEH zai hana kije ki buɗe account sai a zuba miki kuɗin a ciki” girgiza kai mama tayi “Aah Abban Badi'a ba za'a yi haka ba, kawai ka riƙe kuɗin a wajen ka ina ga zaifi. Idan a waje na ne zai iya salwanta a banza ammah idan a wajen ka ɗin ne kamar zai fi. In yaso in an tashi amfani da shi sai ayi nan gaba"
Abba bai Musa da shawarar Mamah ba haka Ammi. Girman ta kuwa a idon su ya ƙara ƙaruwa. Daga nan suka yi sallama suka wuce gida.
TOH GA FA BABA AMARYA DA KUMA TUGGUN TA GA MAMAH DA ƊIYAR TA GA KUMA YA ISHAQ SHIMA ASHE YANA NAN.
KU CI GABA DA BIBIYAR ALƘALAMIN DIAMOND LADY DON JIN YADDA ZATA KAYA COMMENTS DIN KU KAWAI NAKE SO SABODA SHINE ƙWARIN GUIWA TA. DIAMOND LADY CE 💎🤟 Oum Zainab.
______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣0️⃣
Bazan manta da ku ba ƴan uwa na kuma rabin jiki na Aminatouh Adamu Hassan (Dr. Meenal) Sa'adatu Adamu Hassan (Shaheedah) A'ishah Saleh Uthman da kuma Safiyya Saleh Uthman (Autar Umma)
SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, yau daɗi gobe akasin haka. Tun ranar da BABA AMARYA ta dawo daga wurin boka Bulebule komai ya sauya a gidan nan. Cikin sati guda ta fara shimfiɗawa Kawu sarautar mulkin ta a gidan, tana cewa abu har rawar ƙafa yake don yayi mata. Wannan shine mafarin zancen.
Zaune take akan taburmar da ta shimfiɗa yayin da Kawu ke mata tausa a tsakar gidan. “mai gida tashi ka ɗaura mana sanwar nan manah don Ni na riga da na gaji” Da sauri ya miƙe kamar mai cika umarnin mahaifiyar sa ya fara haɗa ice cikin murhu. Ba don komai ta sashi ba sai don kawai haka tayi ra'ayi. Da ƙyar wutar nan ta kama ammah haka tace ya daure yayi musu girkin nan. Tun bai wuce 11:20am aka fara girkin ba har 1:00pm da ɗori ba a saka shinkafa ba.
Lokacin da Zahrah ta dawo daga school tayi arba da Kawu na girki. Shewa ta buga sannan tayi hanyar ɗakin Mamah tana dariya. Batayi tsammani ba sai jin Muryar shi tayi yana ƙwalla mata ƙira..
“Zahra'u zahrah'u”.....babu alamun zata tsaya ballantana na ta amsa ta wuce ciki abun ta. Kamar yayi kuka haka ya tasa tukunya da murhu a gaba, gashi babu yadda ya iya tunda gimbiya ce ta bashi girkin.
Ana cikin haka Badi'a tayi sallama da basket ɗin abinci a hannun ta, a hanzarce ya miƙa ya zo gaban ta yana miƙa mata hannu. “ɗan matsa zan wuce” “kawo na shiga da shi” da ƙyar Badi'a ta danne dariyar da ta kama ta sannan tace “gyara na wuce ko sai na yi wa bodyguards ɗina magana” kasancewar bai san ta ba kuma yaga ƴar gayu yasa yayi tunanin da gaske ne. Direct ɗakin Mamah ta miƙa abincin sannan ta fita.
Kawu da ya gama galabaita ga rana, ga zafi ga hayaƙi in Banda zufa babu abun da ke ketowa daga jikin shi. Bana amarya kuwa ta tsare ina bai dafa ba ko ta dafa ba zai ci ba don ba bashi zata yi ba.
“kiyi haƙuri kizo ki amshi girkin nan, Ni babu abunda zan iya wallahi yanzu haka na wahala” Hararar shi tayi ta gatsina hanci tukun tace “ita waccar ta ɗakin uban meh take yi a gidan da bazara dafa ba, maza je ka taso ta”
Zungui zungui babu kunya ya ja ƙaton kanshi zuwa ɗakin Mamah. Lokacin kuwa sun zuba fried rice da kuma papper meat da aka kawo daga gidan Ammi suna ci. Yawun Kawu duk ya tsinke ammah ya dake. “madina ki fito in ji amarya kiyi girki” Idan gini na magana toh, Mamah ko kallon shi bata yi ba gashi yanzu duk jin zuciyar sa yake yi a mace ba zai ma iya dukan ta ba. Ya fi 10minutes yana jira ko zata fito ammah shiru, hakan yasa ya ja dogon kafar shi ya koma wajen bana amarya. Marairaice mata fuska yayi “don Allah gimbiya kiyi haƙuri ki zo ki ƙarasa, gaba ɗaya sun ƙi kula Ni su ma.
(Nace ah su Kawu anyi luƙus kenan”
Harara ta ƙara banka mishi “toh ita ɗin uwar ka ce da ba zaka ce ta fito ba, koma kace ta fito” haka ya ƙara komawa kamar ɗan ta. “tace wai ki fito" banza Mamah ta ƙara yi mishi. Babu yadda ya iya ya ƙara dawowa. Wasa wasa abinci har 3:00pm ba'a zuba shinkafa ba. Da ya gaji kawai ya fice shagon gyaran babur da yake ya zauna Allah ya taimake shi wani ya kawo gyara sannan ya samu ya ci abinci.
Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, duk shekara sai lashe kyaututtuka masu yawa daga makaranta da kuma wajen makaranta. Yanzu har su Zahrah suka shiga aji uku (jss 3) kwacakwam hankalin su ya koma kan karatun su, gashi Badi'a na shirin yin sauƙa saboda damah can tayi wa Zahrah nisa.
An samu sauyi cikin gidan Kawu sosai don kuwa yanzu Kawu ya zama dolo, babu abun da ya isa yayi sai da umarnin baba amarya. Ya bi ya rame har abun tausayi ammah hakan bai taɓa zuciyar Zahrah ba.
Yaya Ishaq har yau shiru babu shi, sai dai wasu lokutan ya kan kira wani staff ya haɗa shi da Zahrah. Su Zahrah an girma,duk ƙiriniya irin ta Zahrah yanzu babu, ko dan ance zama da maɗaukin kanwa wai shi ke kawo farin Kai. Toh Zahrah ma dai ta sauya. Ga wani irin kyau da take yi yanzu wanda ake kira da ƙyalƙyalin ƴan matanci....ta ko ina Zahrah batada makusa. Idan kyan fuska ne toh Zahrah ƙarshe ce, kana ganin ta kaga fuskar Mamah kamar anyi copy sai dai Mamah da yake wahala ta dafar da ita yasa Zahrah ta fita haske sosai. Uwa uba wani rashin don magana da Zahrah ta ɗauko abun mamaki idan har kaga tana magana toh an taɓo ta ne. Hakan ba ƙaramin ƙara mata kwarjini a idon ƙawayen ta yayi ba don kuwa kowa shakkar ta yake.
Zahrah ce zaune a class yayin da mates ɗin ta suka kewaye ta tana kwatanta musu yadda ake solving wani equation a maths, da ƙyar suka samu suka fitar da amsar. Bayan sun gama ne ta ci gaba da koya musu sauran abubuwan da suka kamata. Aikin su kenan kullum a school yanzu idan sun je saboda an ma daina shiga clsss ɗin su.
A lokacin exams kuwa Zahra ta nutsu ta rubuta abun ta. Bayan an kammala aka sallame su har sai result ya fito za'a neme su don yin registration na senior class, ranar sunyi kuka iya kuka saboda wasu ba a nan zasu ci gaba da karatu ba. Zahrah na ɗaya daga cikin waɗanda suka cire tsammanin dawowa ALMUNAUWARA don ci gaba da karatu duba da sponsor nata baya nan kuma babu alamun zai dawo, kuɗin kuma yafi ƙarfin mahaifiyar ta. “Dole zan koma government school ne na sani ammah Alhamdulillah for these three good years I've learned a lot” Da haka ta lallaɓa zuciyar ta tare da fauwalsws Ubangiji komai. Yanzu iya islamiyya suke zuwa. Zahrah ta maida hankalinta sosai kan karatun addinin ta, wanda ya kawo sauyi mai kyau cikin rayuwar ta.
Rayuwar ta haskaka sosai, a da Zahrah bata iya riƙe bakin ta duk maganar da ta zo mata ko a waye kwaɓa mata take yi ammah yanzu Alhamdulillah an samu great improvement don kuwa a rana maganganun Zahrah ƙirgaggu ne, sanadiyyar islamiyya yanzu Kawu yana cin arziƙin gaisuwa daga gare ta, haka baba amarya ma idan ta ganta takan gaishe ta. Sana'ar Mamah ta ja baya sakamakon jinya da take yawan yi yanzu sauƙin ta ma suna samun abinci ko da yaushe ga kuma kyakkyawar kulawa daga sabon ahalin su. Jinya abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, an je asibiti abu yaƙi yiwuwa. Duk san ɗin da za'a yi sai ya nuna normal hankalin Zahrah duk ya tashi. Damuwa ce fal a ranta ga wata dama da ta fara yi.
Fahimtar haka da Ammi tayi yasa ta yanke wata shawara ita da mai gidan ta. “Ni wallahi Abban Badi'a abun ya ɗaure mun kai, mutum mai lafiya lokaci ɗaya sai jinya, duk da cewa ba abun mamaki baneh kaɗan daga hikimar Ubangiji ammah jinyar Maman Zahrah akwai sa hannu astaghfirullah, a ce duk wani investigation da aka yi sai ya nuna normal bayan kuma gata nan tana jin jiki” “ni kaina nayi tunanin hakan, ita wannan mata gaskiya tana ganin jarrabawar rayuwa, kiga fa mijin ko sau ɗaya ban taɓa ganin an zo da shi ba” “wallahi kuwa Ni haushi yake bani daga shi har amaryar tasa mai zubin karuwai. Wallahi haƙƙin Madina da ɗiyarta kaɗai ya ishe shi, da sannu zai fahimci hakan tun anan duniya. “Allah zai saka musu kam” “Ammah Ni ina da wata shawara fah, ko za'a gwada ISLAMIC medicine me?" “shawara Mai kyau sai mu gwada ai.”
Tun da aka fara ISLAMIC medicine ta ɗan fara samun sauƙi, sai dai yanzu ta fara wasu irin surutai musamman ina tana bacci. Wani lokacin Zahrah sai dai ta zauna tayi ta sharar kukan ta daga ƙarshe ta ɗaura da yiwa Mamah addu'a.
Yau da safe Zahrah na zaune gefen Mamah yayin da take bacci kawai taji Muryar Mamah na magana. “Tabbas na riga na cuci rayuwa ta da na gudu na bar dangi na wanda bana jin har abada zan ƙara ganin su, Alhaji Baba da kuma Hajjaty ina roƙon ku yafe min bana jin zan iso gare ku mutuwa zata riske ni.... Nan da nan jikin Mamah ya ji ƙera da zufa sai wani karkarwa take yi. Addu'a ta tofa mata nan da nan taci gaba da bacci ta.
“Tabbas akwai ɓoyayyen al'amari game da rayuwar Mamah na, ya Ubangiji kafi kowa sanin ɓoyayyen al'amari da kuma bayyananne, ya Rabb! Ka bawa mahaifiya ta lafiya ka kuma bani ikon haɗa ta da dangin ta” ta ƙarasa hawaye na zubowa daga idanuwan ta.
Kwanci tashi asarar mai rai Mamah ta shafe wata guda tana jinyar da aka gagara gano wace iri ce, a lokacin kuma baba amarya ta fara shiga tana gaishe ta kullum. Ita dai Zahrah bata kawo komai a ranta ba don yanzu babu laifi suna gaisuwar mutunci da BABA AMARYA ɗin.
Ana cikin haka result ɗin su ya fito, a ranar kuwa suka dukufa zuwa school bisa tursasawar Ammi. “Zahrah ki tashi kije ki shirya a can tare da Badi'a kuje school za'a buɗe muku result” cikin fuskar dake bayyana tsantsar damuwa tace “Ammi don Allah ki barni na zauna a nan tare da Mamah, Badi'a sai ta duba min" “Aah Zahrah tashi zaki yi ku tafi, ina nan zan kuka da mamah”
Babu yadda ya iya ta wuce gidan Ammi a can suka shirya suka shiga adaidaita saboda Abba ya tafi Kaduna. Suna isa ganin classmates ɗin su Zahrah ta ɗan ware, ihun murna suka yi da suka hango Zahrah da Badi'a. Da gudu suka rungume su tamkar zasu faɗi ƙasa.
Murya uncle Hashim me ta dakatar da su “Hey! Are You alright?” waskewa suka yi suka ce “yes sir” Yace “Alright You guys should FOLLOW me to the computer library so that your results will be checked”
Yana tafe suna bin bayan shi har suka iso. Ɗaya bayan ɗaya ake dubawa kuma Alhamdulillah duk duk sun samu abun da ake so na tafiya senior class. Badi'a ce second to the last, Tana fitowa tayi hugging Zahrah “best frightful and colourful result” Tsalle Zahrah tayi “Alhamdulillah, bari na dubo nawa ki jira ni”
Kamar yadda Badi'a ta fito da gudu haka Zahrah ta fito da gudu “Awful and marvelous result" Farin ciki tamkar su yi yaya.
______________★★★_______________ Typing 📲 🏡𝙱𝙰𝙱𝙱𝙰𝙽 𝙶𝙸𝙳𝙰🏡 (𝔗𝔥𝔢 𝔟𝔦𝔤 𝔥𝔬𝔲𝔰𝔢🏠) ★TAKUN FARKO★ [Labari/Rubutawa] 🄳🄸🄰🄼🄾🄽🄳 🄻🄰🄳🅈 𝑂𝑢𝑚 𝑍𝑎𝑖𝑛𝑎𝑏🖊️
﷽
PROLOGUE
𝕻𝕬𝕲𝕰 1️⃣1️⃣
Wannan shafi naku ne masoya littafin babban gida. Ku ci gaba da bibiyar alƙalamin DIAMOND LADY. Much ƙauna🤩😘
SHARE AND COMMENT PLEASE! _______________★★★________________
Bayan an duba wa kowa PC ya haɗa musu assembly.
“Good day to you all our graduating junior students, you indeed deserved to be honored because you all perform well an fantastic.” Tap tap tap sukafara tafi “The most amazing part of your success is that three students from this school were honored with money 💰.” Tap tap tap “I'll like to see Mayam Muhammad on the stage” M² ta fito a natse, “the state's board of junior secondary School examination awarded 100k to you for your wonderful performance and this school specifically honored you scholarship in to the senior class.”
Nan da nan ihu ya kacame sai tafi Tap tap tap A hankali ta koma tana murmushi.
“Badi'ah Kabir Umar, shi also perform wonderfully in this exams the board awarded 300k to you, congratulations Badi'a, and to you also the school management awarded a scholarship to you in to the senior class”
Ihu ta ka ina da ƙyar suka yi shiru.
“The champion, Zahrah Abdulkarim Kuru being the overall best student to write this JSSE in this state at large was awarded the sum total of 500k and sane, management of the school awarded a scholarship to you"
Murna ta ko ina sai da PC ya tsawatar musu suka yi shiru.