Kenza eBookz

Babban goro complete novel - Chapter 18

Babban goro complete novel - Chapter 18

Babban goro complete novel Chapter 18: Babban goro complete novel Chapter 18. **** To haka rayuwarsu ke garawa, cikin nasarori da falalar Ubangiji iri-iri.…

3,249 words

**** To haka rayuwarsu ke garawa, cikin nasarori da falalar Ubangiji iri-iri. Shekara kwana ga mai yawan rai, a yau ne ake yaye daliban Jami'ar Ahmadu Bello na wannan shekarar, ciki har da Safah Aliko Dan kasa, wadda ta karbi kwalin MBBS mai daraja ta farko, tuni ita Marwah ta karbi kwalinta tun shekaru biyu da suka wuce, don nata karatun bai kai tsayin na Safah ba. Ita ta fito da kwali mai matsayi na biyu. Cikin farin ciki Hajiya Zainab ta rungume 'yar ta, Zahraddeen na daukar su a hoto da digital. Har suka zo gida farin cikin da suke ciki a yau ba zai fasaltu ba. A daren ranar suka juyo Zaria wato shi da tashi matar, duk yadda Marwah ke so ya barta ta kwana dasu Mami ya ki amincewa, tana ta kumburi kamar ta fashe da kuka, ya bude mata kofar gidan gaban motar ta shiga ta zauna. Ya yi murmushi ya ce, "Kwanan ne ba zan iya ba Marwah, ni sai ki barni in ragaita?" Ta zumbura baki ta harare shi yana dariya ya ja motar aguje suka harba kan titi. Karfe goma na dare suna cikin gida, sun dade a dakin Inna ana hirar yadda taron ya kasance, sai da Inna Binta ta kore su ta ce suje su kwanta. *** Likitar hakorin Dr. Safah Dan Kasa da mai harhada magungunan (Pharmacist) Marwah Aliko Dan Kasa sun zauna sunyi shawara a tsakaninsu cewa, za su sayar da wani kaso na gadonsu su bude babban asibitin hakori (pribate). Kuma Zahraddeen ya goya musu baya. Bayan kammala karatunsu a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Zaria (ABUTH). Da taimakon malamansu da sauran manyan likitoci 'yan'uwansu. Dan Kasa Dental Hospital ya samu kafuwa cikin dan lokaci kalilan, a garin Kaduna. A lokacin sun bar Zaria, sun bar Inna da Rabi'a wadda ta fitar da miji a wannan watan, an sanya kwanakin bikin watanni biyu cif! Nura yana tare dasu a Kaduna, domin ya gama sakandire ya fara karatu a Kaduna State Unibersity. Zahraddeen na cigaba da sauke wannan nauyi da Alh. Aliko ya aza masa, dukiyoyinsu suna hannun sa har kawo wannan lokacin cikin AMANA sai bunkasa suke, abin kamar a jinin sa yake, komai kara hauhawa yake. Kuma baya wasa da hakkin Allah cikin dukiyarsu. Su kansu bazasu iya iyakance abinda suka mallaka a duniya ba. Saidai fa daya alkawarin da yayiwa Daddy har yau yana nan yana yawo a kwanyarsa, yana masa kuda a kunnuwansa, wa zai aura, don ya cika wannan alkawari? Matarshi ta ishe shi ta kowanne bangare, tun bayan da suka shirya baya ko iya daga ido yayiwa wata diya mace koda kallon kirki. Matsalarsu daya ce wadda Zahraddeen din shikadai ya santa, matsalace wadda ta shafi auratayya, ba kuma wata gagarumar matsala bace da ta gagari a yi solbing dinta, tunda babu yadda za'ayi ace dan adam ya rayu ba tareda wani nakasu ba. Kowanne dan-adan tara ne bai cika goma ba . Ga Matar tashi da bala'in kishi, duk sakatarorin shi mata da abokan aiki saida ta san yadda tayi ta raba masu wajen aiki. Ta maye gurbinsu da karti. A lokacin ne suka kara bude DAN-KASA INDUSTRIES na sakar tufafin auduga wanda ke da reshe a Geneba, wanda suka bude da sunan Zahraddeen halak-malak ba tareda shi din ya sani ba. Har sai lokacinda ribar da kamfanin ke samu gabadaya ta soma tittida cikin account dinsa, ya yi kokarin yin musu, amma 'yan biyun suka fashe mai da kuka, wai in Daddy ne yayi masa kyauta domin nuna godiyarsa abisa wani kokari ko taimako da yayi masa ya ji dadi, ya amfana har fiyeda yadda yayi zato, yayi masa dan ihsani domin domin ya nuna jin dadinsa ko godiyarsa, zai maida masa ne yace ba za ya karba ba? Sai albashi kawai? Da haka suka rufe bakin sa domin ya kasa cewa komai. Shi kuma ya yi amfani da wannan damar ya koma karo karatun PhD dinsa a babbar Jami'ar garin Geneba. Wanda ke karkashin kasar Switzerland. A lokaci guda kuma tareda bunkasa ayyukan kamfanin DAN-KASA INDUSTRIES. Zuwa rassa guda biyu daya a Munich (Germany) daya a Zurich (the greatest city of Switzerland).

Likitar, (Safah) ta dauki kwararrun likitocin hakori, musamman abokan karatunsu na jami'ar Ahmadu Bello. A gefe guda na 'Dan-Kasa Dental Hospital' tankareren dakin shan magani ne (pharmacy) wanda ke dauke da duk wani nau'in magani na gida da waje, wanda ake shigo dasu kai tsaye daga kasar India, mallakin Marwah Aliko Dan-kasa. Zuwa wannan lokacin Marwah ta gama mallake zuciyar mijinta da kyawawan halaye, biyayya, soyayya da kyautatawa. Ta yadda har ya zamo cikin nadamar alkawarin da ya yiwa Alh. Aliko na cewa zai kara aure, wai aure na soyayya a cewar Alhajin, domin matarshi ta ishe shi, ba shi da gurbin da zai iya jogana soyayyar wata diya mace. To shi yanzu wajen wa zai je yace yana son ta? Kallon mata yake a dage, a kaikaice (basu da abinda za su ja hankalinsa kansu). Har ya ke tambayar kansa ashe dama 'your first lub might not necessarily be your true lub???' Marwah bata bi Zahraddeen Geneba ba, sakamakon tsohon cikin da take da shi na haihuwa yau ko gobe. Suna gidansu na Malali a Kaduna. A lokacin Zahraddeen yana can sai Inna Binta ce ta dawo gidan dan kula da ita. Duk wata kulawa da ya kamata uwa ta gari ta yiwa diyarta Inna Binta na yiwa surukarta. Ranar wata litinin a lokacin watanni Zahraddeen biyar a Geneba, nakuda ta tashi gadan-gadan, Inna ta kira Nura a waya ta ce maza ya zo ya fiddo mota su tafi asibiti. Ko kamin Nura ya zo faya ta fashe, kan kyakkyawan yaro mai kama da ubansa a komai ya sako kai. Haihuwa mai matukar sauki Allah Ya bata, sai Inna ta shiga hamdalah, ta yanke cibi ta zaro mahaifa ta kunshe. Duk wani taimako da ya dace ita tayi mata, sanda Nura ya fiddo mota suka je asibiti an tabbatar da koshin lafiyarsu ne kawai itada jaririn. Tareda basu magunguna na karin lafiyarsu. Inna ta yi mata wanka da tawul ta wanke jariri, ta shirya shi cikin kayan sanyi. Nan da nan ta hau damun kunun kanwa, gasa nama da farfesu don maijegon ta samu ruwan nono da karfin jikinta. Ta aika aka samo runhu daga Zaria don fara wankan jego. Mami da iyalanta tare da Hajiya Mama sai zuwa suka yi suka tarar da maijego da jaririnta fes dasu, su kansu sun gamsu da kulawar da Inna ke mata babu wanda ya ce zata koma gida wanka. Mami don kunya ba ta dauki jaririn ba, sai Aunty Shahidah da Safah ke rige-rigen dauka. Suka sunkuto shi suka kawo shi cinyar Mami. Hajiya Mama ta ce, "A'a, ku yi a hankali kada ku karya shi ko ubansa bai ganshi ba, sun san zafin abinsu, kun san kuna son dan kuka zauna a gabanmu har yanzu gotai-gotai da ku kuna gantalin aiki da karatunda bashi da karshe?" Suka sa dariya, Safah ta ce, "Here comes Daddy!". Wato ga Daddy ya zo. Mami ta ce, "Da yake ke kika haifar musu dan da za ki sa masa suna? Ni matsa nan kada ki taka ni". Marwah ta yi murmushi ta ce, "Allah Mami sunan Daddy za a sa, Deen ba zai ki ba. Kullum addu'arshi kenan Allah Ya sa namiji ne mu samu mai sunan Daddy".

Yana tsaka da daukar lacca ya ji shigowar sako ta hanyar blackberry messenger cikin wayarsa, ya duba sai ya ga image ne ya shigo. Ya bude yana kallon photocopy dinsa cikin mamaki, wani kosashshe kuma lafiyayyen jariri kamar yayi kaki ya tofar, ya tabbatar 'Aliko' ya zo. Ya lumshe ido ya yi murmushi ya sumbaci hoton jaririn. Karfe shidda na asubahin washegari shine mutum na farko da ya doka musu kofa. Inna da ke lazimi bisa sallaya ta mike ta nufo kofar cike da mamakin wane ne zai zo musu a daidai wannan lokacin. Sai ta ga Zahraddeen rataye da falmaran din bakaken 'suit' da yake sanye dasu, a daya hannun kuma karamar jaka ce ta matafiya da jibgegiyar rigar sanyi wadda daga ganinta kasan daga cikin kankara ya fito. Kai kace wani haifaffen Afro-American ne. Wato irin bakaken fatar nan haifaffun Amurka wadanda iyayensu haifaffun can ne tun lokacin cinikin bayi. Wadannan bakaken sun fi turawa kyau, sun fisu daukar hankalin mata, ga tsayi ga zati, ga koshin lafiya ta ko'ina. Sannan ga hutu a jikinsu kamar basa taka burbushin kasa. Ta kama baki tana murmushi domin ba ta zace shi ba, don ko jiya da dare sunyi waya da shi bai ce da kowa zai zo ba. Ta bashi hanya ya wuce ciki ta rufe kofar, ta dube shi suka yi dariya irin ta Uwa da danta. Ya zube yana gaishe ta, ta wuce daki ta barshi tana cewa. "Kai! Yaran zamani da son 'ya'ya sai a barku". Shi kam murmushi yake ya matsu ya ga kyautar da Allah Ya bashi.

Tana shayar da Babyn ya murda kofar ya shiga, idanuwa shi fes a kansu. Abinda ya fara ce da ita shine; BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE……takawarki lafiya matar Zahradddeeeeeniiiii…" Har da dan rankwafawa, da jinjina ta girmamawa. Zumbura mishi baki tayi "ka ga Allah ka bari bana so!" Sai ya tafi da sassarfa yana dariya ya hada su ita da bebin ya rungume su. Tsayin minti goma Zahraddeen ya kasa sakin iyalinsa, idon sa kawai ya rufe yana sakin ajiyar zuciya akai-kai, yana yiwa Alhaji Aliko addu'a ne batareda ita din ta sani ba. Saida babyn ya soma motsin matsar da akai masa sannan ya sake su. Ya ce, "na bari, bazan kuma TUNA BAYA ba. To amma Takori tace TUNA BAYA SHINE ROKO. Shiyasa na tuna din. Anyway kin biya ni Marwahhh..... (rana ta farko daya kirayi sunanta deeeeeeply a tsayin rayuwarsu) irin wannan 'bouncing baby' haka? (Ya fadi hakan cikin kokarin shigar da kwayar idanunshi cikin nata). Har ban san da wace kalma zan nuna godiya ta ba". Ya sake fada, yana kokarin su hada idanun amma ta ki. Ta mike zata fita, don ita kadai ta san me ta gano cikin kwayan idanunnan nashi, wadanda daga cikin su yake fara sauya tasha a salon soyayyarsa, amma sai ya riko hannunta don ya gane tafiyar zata yi, ba tareda ta juyo ba ya cigaba da Magana "Marwanatouh Allah Ya barmu tare cikin ALHERInsa, har zuwa ranar da muka daina numfashi". Ta daga mishi kai, yace "ban ji kin ce amin ba" Murmushi ta yi, ta juyo ahankali ta kwantar da kanta a kafafunsa. Jaririn na bisa cinyoyinsa. Ya zuba mishi ido kamar zai hadiye shi. Still hannunta cikin nashi bai cika ba. "Guduwa zaki yi ki barni ko Marwanatuh? Alhalin tsallake komai nayi, nazo don muyi celebrating farin cikin mu mu ukku? Dubi nan…" ya nuna mata babyn, "me ya fishi dadi a rayuwa? He's a life-time companion 2 his Dad (Zahraddeeni), his pet, his friend and a Dad's pride. In ban kare yinin yau da darensa da Uwarsa a gefe na ba, cikin sanyata farin-ciki, na wahalar dana bata wajen daukar cikinsa, rainon cikin sa da nakudar haifeshi…., celebration din will be incomplete, …..yet meaningless…….. !!! Ya fadi cikin murmushi, cikin wata irin murya mai taushi dake nuna yana yin maganar ne tun daga karkashin zuciyarsa. "Wata ukku, ban gan ki ba, ban ji dumin jikin ki ba 'apple of my eyes….(the one I lobe most) " ya fadi yana kokaerin dago habarta dake sunkuye, "ga Da na yau a hannu na jikan Alh. Aliko, wanda zan dora a kujerar Aliko….., in gaya masa kowanene Aliko….., in sa masa suna Aliko…., inyi ta addu'a ya debo halayen Aliko…. If u did not join me in my celebration you might not run away from me……. Banda Allah wa zai maka wannan kyauta? Farin cikin dana ke ciki a yau Marwanatouhhh, ban taba tsintar kaina acikin irinsa a tarihin rayuwata ba….. so plz join me…..!!!". Ya fada kasa-kasa, tareda aje Dan a gefe, ya mikar da ita tsaye ya rungume sosai, kamar ya maida ita cikin jikinsa su zama mutum daya, ya soma 'kissing deeply' irin yadda bai taba yi ba.

Cike take da kunyar iya shegen da ta rinka yi masa a baya, shine abinda ya sa ta kasa kallon idanun sa, yau ga dan sa ya fito daga jikinta tana shayarwa daga jikinta, domin cikin fadin duniyar nan a halin yanzu ba abinda take so sama da mijinta, da rabon da Allah Ya basu. Shiyasa aka ce in zaka yi kiyayya ka yi ta saisa-saisa, haka in zakayi soyayya itama kayi ta tsaka-tsaki, don baka san me gobe zata haifar ba. Ta tabbata Daddy gata ya yi mata, ta yarda ta amince da hakan yanzu, hakan da Aunty Shahidah tayi ta gayamata, amma ta ki sauraronta da gangan, da ina za ta samo miji irin Zahraddeen a wannan zamanin?

Babu shaye-shaye, babu neman mata, mai amana da gaskiya, wanda ke motsi cikin biliyoyin kudi, amma babu kobo da ya taba bata cikin lissafinsu, har ya samu ya maida 'Dan Kasa Holdings' abinda ta zama a yau. Ya koma gefe matsayin babban director mai bada shawara cikin hikima da baiwar da Allah Ya bashi wajen iya juya kobo ta koma dari. Bayan ya cika kamfanonin Dan-Kasa da hazikan ma'aikata ma'abota zuzzurfan ilmi da suka san abinda suke yi. Jarumi kuma haziki a fannin komai, sadauki a fannin soyayyah. Hakan bai hana shi daukar nauyin ci da shansu da sutura da Allah Ya dora masa ba, kuma miji mafi kusanci wanda baya la'akari da abinda take dashi wajen sauke hakkokin ta da ke kansa, sai tunanin abinda shi zai bata. A kullum tunaninsa ya kare ne a abinda zai mata ya sata farin ciki ya kara inganta rayuwarsu, tunda itama bata rageshi da komai ba, kokarinta kullum a inganta aurenta ne da kokarin ganin ta dauke hankalin Zahraddeen daga sauran matan da ke farautarsa kamar su fyade shi, duk da dan-adam tara yake bai cika goma ba. Wanda baya waiwaye cikin abinda ta mallaka cikin rayuwar aurensu. Bata da abin da za ta ce da mahaifinta day a zaba mata Zahraddeen a matsayin miji sai fatan Allah Ya haskaka kabarin sa, ya yi masa rahma da gafara.Aliyu, da suke kira Daddy yana da shekara biyu Zahraddeen ya kammala PhD dinsa, ya dawo gida Najeriya cike da dimbin nasara, ya koma ofis aka cigaba da gudanar da komai cikin nasara da karin ilmi mai tafiya da zamani. . Don haka duk suka tattara suka koma birnin Tarayyah inda 'main-branch' na DAN-KASA HOLDINGS' ya koma. Sai Dr. Safah ce ke kula da asibitinsu, kullum she is busy... don asibitin ya samu karbuwa yadda ba a zato, har daga sauran jihohi ana kawo patient masu fama da matsalolin hakori, dadashi da makogwaro daban-daban. Cikin dan lokaci kankani DAN KASA DENTAL HOSPITAL ya soma gogawa da sauran manyan Pribate asibitocin hakori na garin na Gwamna. Musamman da aka ji cewa na 'ya'yan Dan Kasa ne. Don haka Dr. Safah ta zamo ba ta da lokacin kanta, wannan ya kawar da hankalinta daga halin damuwar da take ciki na rashin yin aure, wanda daga ita sai Ubangijinta suka sani. Tun Mami da Hajiya Maama na fada da kumfar baki a kan ta fito da miji ta yi aure, don sun gaji da wannan gantalin asibitin har sun gaji sun zuba mata ido, don a duk lokacin da suka ta da zancen aure kuka kawai take sanya musu. Almustapha Zubair Dan Kasa kadai zuciyarta ke yimawa kwakwa, take nema ruwa a jallo. Duk da tasan ko Allah Ya nufa ta kara ganinsa ko ya dawo don kansa, babu maganar aure a tsakanin su sai ta 'yan uwantaka kamar yadda zuciyar ta mai kimsa mata komai ta zaba. Kaico da aikin zuciya musamman idan ka bata linzami da ragamar kanta. Ya tafi da duk wata soyayyar da Allah Ya halitta a zuciyarta, bai bar ko sako daya da take jin za ta iya jogana soyayyar wani da namiji a duniya a zuciyarta ba. Tun daga lokacin da zuciyartata da kuruciyarta suka hadu suka janyo mata asarar wannan BABBAN GORON da Allah Ya bata, in ba shi ba kowanne GORO karami ne a idonta, daci da bauri yake a bakinta. ****

Yau litinin babbar rana. Dr. Safah ce ke kokarin daura lab-coat cikin hanzari a kan shudiyar atamfa (super) mai hasken sararin samaniya dake jikinta, dinkin riga da babban sikit wanda ya bude sosai daga gwiwarta zuwa kasa, dinkin rigar kuma dan karami ne daidai jikinta ya bi surar jikin ta ya kwanta, , ta kawo farin gilashinta ta dora ta nade kanta da siririn shudin mayafi (pashmina). Ta bude bed-side fridge dinta ta dauko gorar fresh milk mara sanyi ta bincire hancin ta kafa kai tana sha, sai da ta koshi sannan ta jawo kofar dakinta ta rufe rungume da jakarta, da alama cikin sauri take. Ta leka dakin Mami ba ta ciki, ta nufo kicin inda take jin motsin kwanuka, nan ta cimma Mami tana suyar chips da plantain (agada). Daga bakin kofa ta dakata, "Mami ni zan wuce...." Mami ta juyo ta kalle ta, sai 'yar tata ta bata sha'awa, ta zama cikakkiyar matashiya 'yar kimanin shekaru (27) da haihuwa, amma sai ka rantse da Allah shekarun ta goma sha bakwai. Ta yi mata murmushi ta ce, "Haka za ki fita baki ci komai ba Safah? Kin fi kowa sanin illar rashin cin abinci a kan lokaci, amma kin fi kowa sakaci da cin abincin. Shi yasa gaki nan kullum kamar a hureki ki fadi. Ungo wannan maza cinye ki bani farantin". Ta narke fuska kamar karamar yarinya, "Allah Mami na yi break fast da fresh milk, in ba so kike na yi amai ba, to ki barni". Mami ta maida plate gefe ta ajiye, "Na barki, cikin ki ko nawa?" Ta yi murmushi, tana karanto damuwar Mamin akan rashin cin abincin nata cikin kwayar idon Mamin, amma kawaici da fulatanci ya danne komai, ta ce "To na tafi asibiti Mami, baki yi min addu'a ba". "Allah Ya bada sa'a, a dinga aikin da kula. Zancen da bakya so kuma dole in yi miki, duk wannan gantalin da kike duk da cewa aikin lada ne, to ladan aure YA FISHI". Ta zumbura baki ba tare da ta ce komai ba, ta juya ta fice, a ranta tana cewa, "Wa zan aura ne Mami? Duk masu so na masu iyali ne. Tukunna ma Mami har yau ban fidda rai da cewa WATARANA zai dawo ya maida ni ba, zai yi min uzri cikin kowanne hali". Shigarta 'office' ke da wuya aka shigo mata da 'file-file' na marasa lafiya da za ta duba a safiyar yau. Haka nan ta samu kanta da kallon sunan mutum na biyu da za ta duba, domin suna ne ba boyayye ba. "NASEER ABDULKARIM (LAMIDO)". Ta maimaita ta sake maimaitawa cikin zuciyarta. In bata yi kuskure ba, Nasir Abdulkarim shi ke rike da matsayin kujerar shugaban EFCC a halin yanzu, wanda ko baka san shi a rediyo ba, to za ka san kyakkyawar bafulatanar fuskarshi a talabijin, jaridu da mujallu, saboda matukar kwarewarsa wajen tsamo masu handame mana dukiyoyi da albarkatun kasarmu mai dimbin albarka. Idan har kana duba manyan journals da news-papers na gida Nigeria, akan duk wani abu da ya shafi tagomashin tattalin arziki, ayyukan ECOWAS, International Monetary Fund (IMF), Bureau of Public Enterprises (BPE) FMBN, NCP, NEPZA (Nigeria Edport Processing Zones), CAC (Corporate Affairs Commission), NEPC, NEDIM BANK, (Federal Mortgage Bank), dole kasan waye Naseer Lamido?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull