Kenza eBookz

Babban goro complete novel - Chapter 23

Babban goro complete novel - Chapter 23

Babban goro complete novel Chapter 23: Babban goro complete novel Chapter 23. Yau da dare Rugar Ardo ta yi tsit, duk al'ummar rugar sun ya da hakarkarinsu…

1,446 words

Yau da dare Rugar Ardo ta yi tsit, duk al'ummar rugar sun ya da hakarkarinsu kasa, shakuwa ta damu Badijo. Har ta tashi Inna ta bude randa ta debo ruwa ta kawo mata shimfidarta, ta tallafo ta tana ba ta ruwan, sakamakon aci bal-bal din an rage ta, ba ta ankara da cewa ruwan dawowa yake yi ba. Tuni Mai kowa da komai Ya amshi abinSa. Da ta ji shiru tsammani ta yi ta koma barci, sai ta kwantar da ita ta koma shimfidarta. Anisa ma ta tashi tana zaune dungurgur ta rasa me ke damun ta? Ta rasa inda za ta sa kanta da soyayyar dan'uwanta. Ita ma Inna kasa komawa baccin ta yi, ta dauro alwala ta zo ta soma nafilfili tana rokawa 'yar'uwarta sauki wajen rabbil izzati. Asuba ta yi sannan ne Anisa ta yo alwala ita ma ta fara bada farali. Ita kuma Inna Binta sai kawai ta dora sallar asubahi. Gari ya soma haske ya yi dan shaaaa! Haka, basu ji maganar Badijo ba ko gyaran muryarta. A ka'ida kuma duk asubah sai ta tashi kowa ya yi sallah, har karfe shida na safe. Inna Binta ta yanke shawarar tashin ta. Kallo daya ta yiwa 'yar'uwarta ta tabbatar mai kowa da komai ya amshi abinsa. Ta ce, "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Sai ta janyo mayafinta jikin kofar bukkar ta yafa tana hawaye ta nufi gidan Liman ta sanar da shi. Sannan ta dawo kofar bukkar su Marwa, "Dini kun tashi ne?" Zahraddeen dake sanye da short - nicker din (Adidas) da farar singileti fara sol saboda zafi, ya yayibi zanin matarsa ya rufa sannan ya ce, "Ni ne dai na tashi". Ta ce, "To ita ma tashe ta ku fito jana'izar Badijo wa'adi ya cika". "Daga Allah muke kuma gare shi zamu koma". In ji Zahraddeen. Ya yi hanzarin zura kaftanin shadda a jikinshi da dogon wando, sannan ya soma jan yatsun matarsa. Cikin barci ta ce, "Na fa yi sallah, don Allah ka barni in dan runtsa". Ya ce, "Watarana dukkanmu haka zamu tsinci kanmu a kabari daga barcin safe". Ta girgije ta ce, "Me kuma ya kawo zancen kabari saboda Allah?" Ya ce, "Badijo ta rasu....' Kafin ya rufe bakinsa ta kai kanta bukkar Badijo daga ita sai rigar barci ko kallabi babu a kanta. Ta tarar Inna Binta da Abuwa matar Liman suna yi mata wanka, sai ta sulale a gefe za ta fara kuka. Inna ta ce, "Kul! Tashi maza ki je ki kintsa ki zo mu yi mata karatu kafin maza su taru". Anisa tana ta suma ana yayyafa mata ruwa tana farfadowa, amma in ta ga gawar Badijo sai ta sake sumewa. Don haka aka fita bukkar da ita.

Ta taso ba ta san iyayenta ba sai Badijo, wajen haihuwarta uwarta ta rasu, babanta shine da daya kwal da Allah ya baiwa Badijo. Ita ta raine ta da madarar shanu har Allah ya kawo ta yau inda ta ke. Ba ta san dangin mahaifiyarta ba saboda Fulanin tashi ne ba zaunannu ba. lokacin da suka aurar da mahaifiyarta gaba suka yi basu tsaya ba tunda ta tubure tana son Haruna, alhalin ba dan rugarsu bane. Sai da ta yi wayo babanta shima ya rasu, sakamakon wata saniya da ta soka masa kaho a ciki wajen kiwo. A haka Anisa da kakarta suka rayu, basu da kowa sai Inna Binta, ita ta sata a makaranta tare da Rabi'a, akwai shakuwa ta 'yan'uwantaka tsakanin Rabi'a da Anisa. Tun bayan auren Rabi'a Anisa ta dauke kafarta daga Zaria, tana nan tana jinyar Badijo. To yau hukuncin Allah ya cika a kan Badijo. Jama'a sosai suka halarci jana'idar ta, bayan an kaita makwancinta suka ci gaba da karbar gaisuwa har kwana uku. A ranar sadakar bakwai Inna Binta ta yi umarni ga dattijan rugar Ardo suka daura auren Zahraddeen da Anisa. A kuma ranar ne suka hada kayansu domin barin rugar. Motar Zahraddeen dake rufe cikin tamfol ta yi kura futuk, yashi ya rufe rabin tayoyinta. Haka ya zage yake wanke motar da kansa ciki da bai dinta, yasa karfi ya banbarota daga cikin yashi da kwanjinsa, ya yi mata ful tank da fetir din da tuni yayo guzurinsa a but din motar ya soma diban kayan amfaninsu marasa nauyi yana zubawa a boot, irin su mujallu da computer (Ipad), da makullan gidansu, amma ko kayan sakawar da suka yi amfani dasu a bukkokin basu dauka ba. Zannuwan gado, filallika, barguna da takalmansu duk basu dauka ba sadaka suka barwa iyalan Liman. Sai da ya gama zuba dukkan kayansu ya dubi Anisa dake gefe kan kunkuru tana mike da kafafu wadda ke nuna babu abin da ya dameta yanzu. Ya harareta ya ce, "Ke ba za ki dauki komai ba?" Ta ce, "Komai kai". Ta mike ta je ta kinkimo katuwar akwatin karfenta da take amfani da ita tun a makaranta da Ghana Must Go shake da sutturunta ta dire a gabansa. Sannan ta kinkimo katon kunkurunta shima ta dora a kan akwatin, ta ce, "Suke nan basu da yawa". Zahraddeen don haushi bai san sanda ya ce, "Kin ci ubanki bakauyar banza!" Ta ce, "A'a-a'a! Ubana yana kabarinsa ban san halin da yake ciki ba ka daina zagar min shi". Ya kama baki, "To ki rama mana". Ta zumbura baki ta turo dankwalinta goshi dogon gashi ya zubo kamar na Larabawa, amma wallahi bai burge shi ba, ganinta ma ya yi ta koma kamar tunkiya. Daidai sanda Inna da Marwah suka fito yafe da mayafansu, Inna rike da hannun Daddy, suka tadda diramar da ake tsakanin Zahraddeen da amaryarsa. Ya ce, "Wallahi Inna ba zan saka wannan akwatin karfen mai kama da akwatin ajiyar gawa a boot din motata ba, balle wannan jakar buhun cike da tsummokara, bare kuma kunkuru da ransa". Ai kuwa Anisa ta balle da kuka, "Ni wallahi ko ba za a dauki komai ba, ba zan bar kunkuruna ba. Ni na raine shi tun yana karami, na ci da shi na sha da shi har ya zamo abin da nake zama a kai in ji dadi, in dube shi in ga kamar na ga wani dan'uwana a raye". Gaba dayansu sai jikkunansu suka yi sanyi, Marwah ta ce, "Don Allah ka barta da abinta". Ya ce, "Na ji, amma wadannan shirgin ba zan dauka ba, za su sa motata makalewa cikin yashi da kwazazzabo". Inna ta dube ta (Anisar) "Kwashe su ki mayar dasu". Ta kwasa ta mayar. Ya ce, "Dauke shi da kanki ki sa shi a boot din ni ba zan iya ba". Ta ce, "Tab! Wallahi ba zan sa shi a boot ya kasa numfashi ya mutu ba". Ya ce a ransa, "Wannan ba karamar 'yar iska ba ce". A fili kuma ya ce, "To ya za a yi kenan? Look ina da abin yi, I'm not tolarating nonesense, sai ki san yadda za ki yi da shi kuma". Inna ta ce, "Sai ki dora a kan cinyarki". Ta ce, "A'a, kafafuna zan dora a kanshi har muje". Zahraddeen sai ya bude mota ya fada bai kara bi ta kanta ba, ya dauki dansa ya aza a tsakanin cinyoyinsa ya tada mota. Marwah ta shiga gaba, Anisa da (tortoise) dinta da Inna suka shiga baya, yaja motar a hankali ya kure A.C din day a dade bai sha ba. Suka bar Rugar Ardo, jama'arta na daga musu hannu. Kowa jikinsa na sanyaye, 'yar takaitacciyar rayuwar da suka yi a wannan waje will foreber remain fresh in their memory. Sun dandana rayuwa mai dadi, mai sauki da ada basu san da ita ba. Wannan ya kara musu imani da wadatar zuci, hadi da godiya ga Allah a bisa baiwar da ya yi musu wadda bai yiwa sauran 'yan Adam ba. "Wannan shine hierarchy of social class….". In ji Marwah. 'Yan Adam ba daya muke ba, kamar jerin 'yan yatsu ne wani ya fi wani, kowa da yadda Ubangiji yake son ganinsa. Ga shi zaman ya kara musu shauki da kaunar juna, ya kuma kawo sauyi cikin rayuwarsu wato karuwar Anisa cikinsu. Marwah ta dauki hakan a matsayin daya daga cikin kaddarorin da Allah ya rubutawa Zahraddeen, ba don baya sonta ba ko ya gaji da ita ba, ko Inna ba ta sonta ba. Babu daya. Ita ma mai taya su ce su kula da rayuwar 'yar'uwarsu da ta zamo dolensu, in dai Zahraddeen zai cika alkawarin da ya dauka na cewa ko farcenta ba zai kama ba. (Dariya) ku taya ni ji makarantan Takori, anya? (Murmushi). Marwah Dan Kasa ta cira kai tana kallon kwazazzabai da shanu na kiwo, wasu na cin ciyawa, wasu na shan ruwa a korama. "Fondest thought!" In ji Marwah. Tana mai kara dayanta Allah a zuciyarta. ****

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull