Kenza eBookz

Babban goro complete novel - Chapter 24

Babban goro complete novel - Chapter 24

Babban goro complete novel Chapter 24: Babban goro complete novel Chapter 24. A ZARIA S un iso yamma likis, kafafun Marwah sun kara kumbura, jikinta ya yi…

3,530 words

A ZARIA S un iso yamma likis, kafafun Marwah sun kara kumbura, jikinta ya yi tsami matuka, ta gaji iyaka. Don haka suna isowa Nura ya tarbesu, ya bude musu gate. Amma da ya hango budurwarsa Anisa sai ya hangame baki yana dariya yana tafa hannuwa. Ya ce, "Yayi-yayi sarauniyar". Ta balla mai harara, "Ji ka don Allah kullum cikin kananan kaya, kai baka yadda ba Bature, ai duk iya sa kaya abi bayan Yaya Deeni….". Zahraddeen ya dago a birkice jin abin da ta fada, ya yi saurin taka totur da ya kusa yin gaba dasu yasa giya baya, saura kadan su daki bango saboda firgitar da tasa shi suka yunkuro kamar zasu ci da baka. Itama Marwah ta yi dummmmm….., ba su ce komai ba. Nura ya bude mata mota ta fito ta kinkimo kunkurunta, tsalle ya yi yai baya, ita ko ta ce me za ta yi ba dariya ba. Ta ce, "Matsoracin banza, a haka zan aureka kana jin tsoron kunkuru kamar wani mace?" Ta fada tana mere baki tana kallon shi sama da kasa a raine. Ya ce, "Oho dai! In ma Yaya Dinin kike hari da matarsa har da dansa, kuma ya fi karfinki wallahi, ni din dai da kika raina nine zan aure ki, don nine daidai ke". Ta kada masa cinya, "Sai abi wani sarkin ba Ado ba, ni nan amaryar Yaya Deeni ce, ko Inna?" Ta juya ga Inna don ta tabbatarwa Yaya Nura ita amaryar Yaya Dini ce. Ita dai Inna ko kallon su ba ta tsaya yi ba ta shige cikin gida rungume da Daddy a kafadunta wanda ke ta sharar barci. Zahraddeen ya fito daga mota ya zagaya ya fito da mai dakinsa, Nura ya karaso yana gaishe shi, ya jarbi jakar Marwah da wayoyin Dinin dake hannun shi ya bi bayansu, hannayensa rungume da kugun matarsa wadda ke cira kafa da kyar saboda kumburi. A haka suka karasa har kofar falonsu. Nura ya yi azamar bude musu kofar gilashin suka shiga, bai bi ta kan mahaukaciya Anisa ba. Yadda yake kiranta a ransa. Ta bisu da kallo ta kyabe baki ta wuce wajen Inna rungume da kunkurunta, ta ajiye shi a tsakar gida, ta samo masa ruwa ta ajiye masa, ta bude jakarta ta fiddo cake din da suka ci a mota ta rago masa ta gutsittsira masa, sannan ta shige bandaki ta yi wanka, ta yi alwala ta samu Inna a falo ita da Daddy tana fifita masa shayi, shi kuma yana ta mutsittsika ido alamun barci ya tashi. Ko kallon yaron ba ta yi ba cike da takaici ta dubi Inna ta ce, "Saboda Allah Inna kin gani ko? Ya sani na baro kayana yanzu ga shi na yi wanka bani da wanda zan canza dasu". Inna ta ce, "Bari Nura ya karbo miki wurin Maman Daddy kafin a hada miki lefenki". Ta fiddo ido, "Me kika ce Inna? Kayan kishiya zan saka? Tab! Wuce nan wallahi". Inna ta dunkule hannu ta sakar mata, "Ungo naki, shashashar banza, ba zan dauki wannan haukan da kike shirin kawo min cikin gida ba. Tun dazu ina jinki kina ta hauka na yi miki shiru. To wallahi ki kama kanki, ki yiwa bakin ki linzami. Wadannan masu ilimi ne, in kika ishesu za su yi barin mahaukaciya dake su kalle ki a dabba, don haka ki nutsu ki san me kike ciki. Wannan surutun ki daina shi, ki yi biyayya ga wadanda kika taras, don ba sa'o'in wasanki bane ba". Ai kuwa sai Anisa ta balle da kuka har da ihu. "Ni dama na san rayuwata sai Allah yanzu, babu uwa babu uba, babu Badijo waye zai so ni? Na san ni ba kowa ba ce Inna, tunda ubana bai bar min gadon arziki ba. Dadin abin dai bani na ce ina son Yaya Dini ba Badijo ce, Allah ya ji kanta". Ta zube a nan tana ta shirga kuka. Inna ta bude baki ta kasa magana, ta kwasowa kanta abin da zai dagula mata lissafi, ya kawo rashin kwanciyar hankali cikin iyalinta, ya lalata zumuncinta da 'yar'uwarta dake kabari da babu abin da ba ta yi mata a rayuwarta ba. Nura ne ya jiyo kukan ya ki karewa ya shigo yana cewa, "Wa ya taba min matata ne?" Ya zube a gabanta ya dafa kafadunta, da gudu Inna ta rarumo ludayi ta rafka masa a hannu. "Matar auren kake dafawa?" Har ga Allah shi Nura firgita ya yi, sannan ya soma ja da baya. Da zuciya daya yake son Anisa, tun tana karama, amma ya yi nauyin baki bai fadi ba sai dai cikin tsokana. Ya ce, "Inna wa ta aura?" Ta ce, "Abban Daddy". Tunda ya sulale a kan kafafunsa ya dukar da kai bai dago ba, haka zalika ita ma Anisan ba ta daina kukan Inna ba ta sonta ba. Wani tunani Inna ta yi, wannan yarinya fa taki ce, amana ce a hannunki, duk wani matsayi da za ki ba matar Dini a zuciyarki bai kai nata ba. Sai ta matso gabanta ta dagota tana lallashinta. Nura ya ce, "Idan auren ne ba ta so Inna to ni a kwance ayi dani mana? Inna na dade ina son Anisa, wallahi Yaya Dini ba zai taba sonta ba, don ba class dinsa ba ce. Ai BABBAN GORO sai magogin karfe". Inna ta yi mishi dakuwa, "Don kabarin ubanka ka fitar min daga daki, kada ku hadu ku sa min hawan jini. Yi hakuri Anisa daina kukan, yanzu me kike so ai miki?" Ta ce, "A dinka min kaya, nima in yi masa kwalliya, ba kayan matarsa ba". Duk halin da Nura yake ciki bai san sanda ya fashe da dariya ba. Ya ce, "Au! Ke kina son sa kenan?" Ta galla masa harara ta ce, "Wallahi in baka rabu dani ba zan danna maka ashariya. Ni matar yayanka ce, don haka duk shekarun ka na zama yayarka". Inna ta ce, "Kin fadi gaskiya Anisa, tashi ka bar mana dakin mu". Anisa da ba a iya mata ta ce, "Ina! Ai ni ba a dakin ki zan zauna ba Inna, gidan mijina za ni, wanda nake zamansa ba ruwana da wata matarsa, yadda take fankama ita matar shi ce, haka nima. Ba ta fini matsayin komai ba, in ta fini arziki, ni kuma na fita kusanci da Yaya Dini, kin san an ce kuma wata kusan ta fi wata. In ta fini ilimi, ba ta fini zuciya mai So da Kaunar Yaya Dini ba.!!! Ke dai Inna dinka min kaya in koma gidan ki yi gefe ki zuba ido ki sha kallo". Ta tafa cinya. Nura na ta dariya har da tuntsurawa. Inna ta sassauta murya ta zauna sosai a gabanta. Ta ce, "Anisa don Allah ki daina irin wadannan maganganun da kike yi, ki daina wannan zakewar, namiji ba a yi mishi haka, wanda yake sonka ma, balle wanda a kan dole ya aure ka. Mene ne damuwarki da matarsa da kike son lallai sai kin yi kunnen doki da ita? Ki tsaya a matsayinki, ki nutsu in fa har kina son in ci gaba da shiri dake. Komai dan a hankali ne, kaifin bakinki da wautarki ba su za su baki soyayyar Dini ba, face ya yi miki kallon mahaukaciya, don Allah ki nutsu. Yadda kike marainiya haka itama take, yadda kike amana a hannuna, haka ita ma take. Ubanta ya fi karfin komai a wajena tunda shi ya maida Dinin mutum din da har ya baki sha'awa kika so shi. Ya yi masa kaunar da ko mahaifinshi na raye iyakar kaunar da zai nuna masa kenan. Ki barni in ji da yadda za ku zauna lafiya ya so ki a hankali kada kisa jinina ya hau. Ga daki nan na baki kusa da nawa shiga ciki ki kwanta ki huta, akwai sabbin atamfofina da ban daura ba bari in dauko miki". Ta mike ta yi daki. Anisa ta ce, "Tab! Ba zan sa dinkin tsofaffi ba ya kara raina min wayo". Inna ta yi salati ta ce, "Wato duk abin da na gaya miki ta bayan kunnenki ya wuce ko? To shi kenan kada ki saka, debo naki masu daudar ki saka yadda za ki fi burge shi. In dai Dini ne wallahi gaki nan ga shi, na daina magana Allah Ya baki sa'a". Nura ya ce, "Wallahi kuwa, Inna kin ga da anyi sakin sai a daura da ni". Anisa ta kai mai duka da ludayin Inna ya fice da gudu. Haka Inna ta kwana da Anisa tana lallashi da ban baki, idan ta bullo ta nan, ita kuma sai ta bullo ta can. Da Inna ta gaji ta rabu da ita ta hau kulla gidan sauro (net), don ita da jikanta su kwanta lafiya, don ko ya ya sauro ya ciji Daddy sai ya yi zazzabin cizon sauro kamar wanda ya tashi a Turai. A nasu bangaren, kwana suka yi Zahraddeen yana messeging kafafun ta da suka kumbura. Da asubah bayan sun idar da sallah ta yanar gizo ya yi booking jirgi da yake da bizarsu a hannu zuwa Paris, inda yake so Marwah ta haihu domin EDD dinta ya nuna saura sati biyu. Shi kuma hutunsa na wata uku ne sun ci wata biyu a Rugar Ardo. Sunyi sa'a akwai jirgi mai zuwa direct (kai tsaye) Suisra wanda zai tashi karfe goma sha biyun dare na yau, amma ta Abuja zai tashi. Don haka ya soma shirin ba tare da ya yiwa Marwah bayanin komai ba, ta dai ga yana ta shirya Trolly, ya kwashi na Daddy ya kai dakin Inna, lokacin ita Innar tana sallar asubahi. Sai da ya gama komai ya wuce wajen Inna ya tadda tana wuridin da ta saba duk safiya, sai ya samu kujera ya kwanta ya dan mike yana jiran ta karasa. Anisa ta fito cikin atamfar Inna, ba ta san yana falon ba da brush da makilin din Nura a hannunta ta wuce toilet. Ta dade tana wanke bakin yana jinta sannan ta fito da alwalarta. Nan ta ganshi a kwance, dadi kamar ta yi ya ya. Ta ce, "Ya Dini yaushe ka shigo?" Ya dan dago ido yana kallon ta cikin kayan Inna tana ta yawo a ciki, kafadar rigar na sabulewa yana dariya ya amsa. "Tun dazu". Ta ce, "Ka kwana lafiya?" Ya ce, "Lafiya lau". Ta ce, "To bari in yi sallah sai in yi wanka in yi maka kwalliya". Ya ce, "To". Inna ta aje carbinta ta shafa fatiha, haushi da takaicin Anisa yasa ta kasa tuna me take karantawa a wuridin. Da sauri Anisa ta wuce daki ganin kallon gargadin da Inna ke mata. Ta juya ga Dinin wanda ya taso ya ciro Daddy daga cikin net ya rungume shi a jikinsa yana cewa da Daddy, "It is morning my darling Daddy, Gud morning....open your sparkling eyes and say bye to Dad, he is gonna trabel without you.....kiss me my durling Dad, I'll miss you.....so much….." Daga can dakin Anisa ta kasa shiru don haushi ta ce cikin kunkuni. "Allah dai Ya sa mun je makaranta balle ayi zaton bamu san me ake cewa ba". Inna ta daga murya tana cewa, "Magana kike yi ne Anisa?" Ta kyabe baki kamar Innar na kallon ta, ta ce, "A'a, tadin zuci ne". Zahraddeen ya jita sarai ya dauki Daddy ya shiga bandakin Inna don ya yi mishi brush ya ci karo da audugar always a cikin masai, da alama an so ayi floshing dinta ne ta ki tafiya. Ai da sauri ya fito, ya leka dakin da take sai ya ga wai kuma tana sallah. To ko Inna ce? Ya ce a ransa. Kai! Inna ta wuce yin jinin al'ada. Ya kasa shiru ya ce, "Inna a daina sa miki auduga cikin masai, a dinga samun bakar leda ana kullewa ana sawa a shara, in ba haka ba masanki za ta toshe yadda ko anyi floshing ba zai tafi ba. Sannan a raba toilet, kazami ya dinga shiga na tsakar gida kar a watsa miki kwayoyin cutar bandaki. Sannan jahili shine wanda bai san in ana jinin al'ada ba a sallah ba". Kunya duk ta kama Inna kamar ba danta ne na cikinta ba. Anisa kuwa baki bai mutu ba, ta ce, "Oho dai! In ma mun yi kazantar babu yadda za a yi damu mun zama dolen mutum, mun zama duwawunsa dole ya zauna damu. Ilimin addini kuma ba a fimu ba, domin shi ya gaya mana cewa idan jinin al'ada ya wuce kwana goma sha biyar ayi kunzugu a ci gaba da sallah, ya zama jinin cuta......" Inna ta daga murya da karfi, "Anisa! Anisa!! Ki shiga hankalinki, waye abokin wasanki a nan da mutane suna magana za ki sako musu carkwadeden bakin ki". Shi kam Zahraddeen sai ya fice ya yi dariyarsa mai isarsa, sannan ya dawo dakin ya zauna ya yiwa Inna sallama. Ya ce, yanzun nan za su wuce Abuja, a daren yau za su tashi zuwa Paris, za suyi wata guda sai Maman Daddy ta haihu za su dawo da Babyn. Inna ta yi fatan alheri da fatan zuwa da dawowa lafiya. Allah ya so wannan karon Anisa ba ta ce komai ba. Da Marwah ta kintsa a nan ta same su, ita ma a nan ne ta ji zancen tafiyar. Daddy ya makale babanshi shi sai an tafi da shi. Daga uwar daka suka ji Anisa ta fashe da kuka, gaba dayansu suka yi dakin ban da Zahraddeen, domin sunyi zaton wani abune ya same ta. Amma me? Da suka dame ta da lallashin me ya same ta, sai ta bude ido jawur ta dubi Marwah, "Ki gayawa mijinki, ban taba yin ZINA ba, ban taba yin MADIGO ba, ina rokon Allah Ya kare ni, da duk zuri'a tad a masu kaunata, ina rokonSa kada Ya sa na yi idan ya tafi ya barni ban san ranar dawowarsa ba………..". "La'ilaha illallahu!" In ji Inna. "Muhammadur rasulillahi....." In ji Zahraddeen dake falo. (Sallallahu Alayhi Wasallama) inji Marwah. Sim-sim-sim ya ja dogayen kafafunshi ya gudu, don ba zai iya hada ido da Inna ba. Ya fiddo mota ya bata wuta jikinshi yana rawa saboda firgita da mamakin wannan magana ta 'yar yarinya Anisa. Ya soma jera horn don Marwah ta fito amma shiru. Marwah da Inna kuwa ko duban juna sun kasa yi, yarinya da gaskiyarta, ciwon 'ya mace na 'ya mace ne (In ji Marwah) wadda ke tadin zuci, ba ta san cewa a fili take yi ba. Ba ta iya hada ido da Inna ba wadda har zuwa lokacin take tafa hannuwa tana salati, ta sunkuyar da kai ta ce da Anisa. "Ki daina kuka, ki kwantar da hankalinki, anyi mai wuyar tunda kin zama matarsa halalinsa wadda Allah Ya dora hakkin duk wadannan abubuwa da kika lissafo a kansa. Amma yanzu baki da passport da biza, balle kuma ba dadewa zamu yi ba asibiti za ni. Na yi miki alkawarin da zarar mun dawo tare dake zamu wuce Abuja". Ta dan tsurawa Marwah ido jawur tana kallon ta, ashe tana da kirki? Take fadi cikin ranta. A sanyaye ta yi kasa da idonta ta ce, "Ba komai, ku je Allah Ya kai ku lafiya Ya kuma sauke ki lafiya". Haka suka kamo hanya ma'auratan, ba mai kallon dan uwansa ba mai ce da dan'uwansa komai, har suka shigo Kaduna. Suka shiga a gurguje suka gaisa da Mami da Hajiya Maama, ko zama basu yi ba, Mami ta hada musu abin karin kumallo a kwandon abinci, aka sa a kujerun bayan motar suka mika basu tsaya ba sai a Abuja. Haka ta ci abincinta ba ta kula shi ba, shima bai tanka mata ba, domin ya hango rikici mai yawa a cikin kwayar idanunta. A gidansu Safah suka yada zango, suka yi sallolin da basu yi ba a guest room, suka yi wanka suka ci abinci, a lokacin ne suka samu nutsuwa. Lamido da amaryarsa suka same su a guest room din ake ta hira, amma fuskar Marwah babu walwala babu bakinta cikin hirar, har Lamido ya gane. Ya ce, "Yar gidana ya aka yi ne? Garin ko jikin?" Tana girgiza kai cikin takaici. Ta ce, "Babu ko daya". Ya ce, "Na ganki ne rather-moody???". Ta ce, "Yau da gobe ba ta bar komai ba". Ya ce, "Brother na ne ko? Yau bai yi messaging kafar ba halan? Gata nan ta suntume". Ta kyabe baki, "Yaushe ka zama dan'uwannasa? Ga dai 'yar'uwarsa can amaryarsa ya baro a Zaria tana jiran shi mu dawo su barje amarci, har tana gaya min magana zan dauke mata miji, amma ku ya yi shiru ya ki fada muku". Safah ta zaburo, "Yaya Deen da gaske aure ka yi?" Idanunshi na kan labarun CNN ya ce, "Daurowa ta yi". Sai Lamido ya zungure shi, "Ka ce mun yi ekual, me ya kai cancada-cancadan mata dadi a duniya?" Ba tare da ya dauke idonsa a kan 'Mu'azzam Kanti' ba ya ce, "Babu abokina, tunda an hanani 'yan'uwantakar ka. Sai na abotake ka. Tana nan (sweet 16) kamar za ta mutu don soyayya". Suka tafa suka tintsire da dariya. 'Yan biyun suka fusata kowacce ta soma huci kamar mesa, mai cikin saura kadan ta fadi saboda mikewar bazata da ta yi. "Idan baka koma ka daukota ka tafi da ita ba baka cika namijin ba. Ai ina lura da kai kana sonta kake mata wani muzuran banza. Ni dai na gaya maka, daga ranar da ka kama farcenta da sunan auratayya wallahi-wallahi na bar gidanka kenan". Mikewa ya yi ya riketa a gabansu ya toshe masifaffen bakinta da nasa. Kissing yake passionately kamar babu wani mahaluki awajen bayan su. Lamido ya rufe ido da tafukansa, cikin lalube ya lalubo hannun matarsa dake kusa dashi ya finciki hannun ta suka tafi. Tuni bakin masifa ya mutu, sai dai Allah ya jikansa, ya koma sambatu na soyayya mai ban mamaki a tsakanin ma'auratan. Daga karshe sai ta koma kuka tana rokonsa kada ya karya zuciyarta, kada ya hada jiki da kowacce mace a duniya bayan ita, zai karya mata zuciya daga ranar da hakan ta faru. Ya taimake ta ya bar Anisa ta ci gaba da zama kamar Rabi'a, don za ta yi mata raini na karshe duk ranar da ta ga gadon barcinta. (Anya uwargida baki so kanki ba)? Takori. Basu dawo cikin hayyacinsu ba sai karfe goma da rabi na dare. Wata irin sassanyar kaunace suka gudanar a yau mai tsayawa a zuci. Sun yarda, sun amince, rabuwarsu ko na minti daya na nufin shigar rayuwar kowannensu cikin garari. Alkawuran da Zahraddeen yai mata a yau ba za ta taba mantawa dasu ba. Shin wane irin miji ne cikin dubu ubanta ya zabo ya ba ta? Son da take masa, sai dai ya bi bayan wanda mahaifiyarsa da Ubangidansa ke masa. Shi kuma son da yake mata, ya zarta wanda ya yiwa Safah tun daga ranar da ya dora hannu a jikinta, ya dauki budurcinta cikin GIRMA da girmamawa. Safah da Lamido su suka kaisu har Airport, basu dawo gida ba sai da suka ga tashin jirgin su. Suna tafe a hanya Lamido na tunanin nashi borin dake jiransa wanda ya zarta na Marwah mai karamin kishi. Domin dai gobe ne Danejo za ta dawo daga boyon da ya yi mata a Sydney (Australia) ya yi auren sa ya barje amarcinsa. Yara dama suna makarantar kwana (Nigerian Turkish) da ke Kano, anguwar Tarauni. Itama Safah ya gaya mata gobe ne Maman Fahad za ta dawo. Sai ta samu kanta cikin rashin sukunin zuciya tun daga lokacin. Har suka iso gida daga Airport bai ga fara'ar amaryar tasa ba. Ya girgiza kai, "Mata! Mata!! Mata!!! Sai a barsu, tunda burinsu su haramta maka abin da Allah Ya halatta maka saboda son kansu. (Don Allah mu dinga tunani, ko zamu yi kishin kada mu yi wanda zai dagula nutsuwar mazajenmu, haka Allah ya ce suyi, don su tserar da kansu daga dattin zina da cikar kamalarsu da mazantakar su, ba yin kansu bane, ba kuma umarnin kansu bane, na UBANGIJI ne). Yana shan tea a gefen gado yana satar kallon ta, sai wani ciccin magani take tana doddojewa. Ta dauki filo ta jefa a sofa ta yi kwanciyarta, wato (yau tunda matarka za ta dawo ba zan hada makwanci da kai ba). Sai ya girgiza kai, ya aje kofin, bai bita yana lallashinta ba sai ya zuba mata ido. Ya yi wanka yai sallah, ya yi lazimi yana sauraron kira'ar Abdurrahaman Sudaith cikin 'yar kankanuwar na'ura cikin Suratul Nisa'i. Yana jin umarnin da Ubangiji yake yiwa mata da alfarmomin da yai musu, da umarnin da Ubangiji ya yi a kansu wajen rabon gado. Amma sun ki hankalta. Da ta san tashin hankalin da zai shiga a gun Danejo da ta sassautawa tata zuciyar ta tallafe shi. Ya koma ya kwanta shi kadai a gadon ya yi light up, amma ya kasa barcin. Yaya ga mata cancadediya Allah Ya bani zan kwana gwauro? Barcin nata ma ai na karya ne don ta kasa. He is someone she lobe and respect most! Idan zuciyarta ta jure gangar jikin ba za ta iya jurewa ba. Don haka ne da ta ji ta a hannunsa ya maida ta gadon sai ta mika wuya ga bautar Ubangiji.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull