Kenza eBookz

Babban goro complete novel - Chapter 25

Babban goro complete novel - Chapter 25

Babban goro complete novel Chapter 25: Babban goro complete novel Chapter 25. Da safe tana cikin bargo tana rama barcin da Nasir bai barta ta yi ba a daren…

3,094 words

Da safe tana cikin bargo tana rama barcin da Nasir bai barta ta yi ba a daren jiya baki dayansa (throughout), ta ji alamar shigowar sako (tedt) cikin wayarta. Lokacin Lamido ya tsufa a office, domin 8 o'clock a cikin office take mishi kafin ya rage ayyuka ya tafi taren Danejo wadda za ta sauka karfe hudu na yamma. Ta mika hannu ta dauki wayar ta duba.

"We are in a train between Suisra and Paris, lub you ma Sis….".

Nan ta gane sun sauka lafiya. Ta mayar mata amsa da

"Lub you too sissy….… Allah Ya sauke ki lafiya".

Sannan ta mike ta shiga wanka.

****

L amido da Danejonsa kwance a bayan mota 'Ferrari has come' Isaac direbansa na kwarara gudu dasu a kan manyan titunan Abuja. Lamido rike da hannun Danejo, ita kuma ta kwace hannunta kada su Isaac su ce miji ya kama hannunta. Ire-iren wadannan kauyancin na Danejo ko shekara sittin ta yi a birni irin haka ba za ta daina su ba. Da zumudinsa yake mata barka da zuwa, ya ta baro Sydney? How does it look like? How does she feel libing there? Don shi bai taba zuwa Australia ba. Ire-iren tambayoyin da yake mata kenan cikin Turanci tana mayar mishi da Fulatanci, don ba ta so ya ci gyaranta ko ya yi mata muguwar dariya in tana kwabo Turanci. Sai magariba suka iso gida. Safah ta daga labulen dakinta dake saman bene sakamakon horn din Isaac da ta jiyo. Gumsu kurtun soja ne shi ke kula da gidan Lamido, shi ya bude get Isaac ya sanyo hancin motar cikin gidan Ya kame ya yiwa oga barka da zuwa, ya amsa. Kasancewar harabar gidan tarwai take da fitilu masu tsananin haske kamar kana Dubai, ya sanya ta ga fitowar Danejo da Lamido. Fara sol mai kyau gajeriya mai dan jiki. Ta ce, Lamido na da mace mai kyau haka me ya gani a jikinta ita baka ya kasa sukuni sai da ya same ta? Ta yi saurin sakin labulen a lokacin da Nasir ya dago suka hada ido. Ta fada a gado tana numfarfashi kamar wadda ta yi gudun famfalakin mita goma. Kai kishi bala'i ne, ya Allah Ka rage mana. A can side din kuwa Lamido sai nan-nan ake da Danejo, sai da ta ci abinci ta koshi, sai dai babu alamar Daddy (yadda take kiran shi saboda su Fahad dake kiranshi da hakan). Ya yi missing din ta, dan ko rungumarta bai yi ba sai tadi yake ta zuba mata na mutanen Taraba. A yadda ta san Daddy in ta yi tafiya irin wannan ta dawo ya fara barin jiki kenan kamar wanda ake kadawa gangi. Yau dai Daddy hirar su Fahad kawai yake yi, ita ta sauke kunya ta soma mishi abin da ta san yana so, amma Daddy ko gezau. Cewa ma ya yi, "Bari Dijah, am not in the mood wallahi". Ta ce, "In baka cikin mudun ni ina ciki, watanni biyu ba kwana biyu bane. Na yi kewarka Daddy, na yi kewar soyayyarka yadda baka zato, don Allah Daddy". Tausayi ya kama shi ya rungume matarsa don sauke hakkinta da Allah ya dora masa, amma ba don yana cikin sha'awa ba. Wayyo! Dole mata su ki kishiya, ba kishiyar suke gudu ba, wacce iri za a kawo musu shine abin tambayar. Ya take? Kowacce mace da irin baiwar da Allah ya yi mata. A yau EFCC Lamido ya tabbatar mata masu sunan mata Allah ne kawai yake halittarsu, ba za ka taba bambancewa a fuska ko a launin fatar jiki ba. Ji yake kamar yana cin tuwon tsaki (biski) ba tareda miya ba, ashe shi da, (prebiously) maza ya rako duniya bai san wace ce diya mace ba. A daddafe aka daddage aka farantawa Danejo saboda kyakkyawar zuciya irin tasa. Hakan bai sa zuciyarsa ta yi kudurin wulakanta Danejo ba. Tausayinta ma ya ji sosai. Sai da ta nutsu take nazarinsa, gaba daya ya canza kamar ba shi ba ya daina dokin ta. A lokacin ma shi hankalinsa ya koma ga amaryarsa wadda ya baro tun safe tana barci, wunin yau zungur bai ganta ba, bai neme ta a waya ba, ko bangajiya ya yi mata da wujijjigata da ya yi a daren jiya bakidayansa. Danejo ta taso ta dawo jikinsa ta zauna ta yi shiru. Ya juyo ya dube ta tausayi ya rufe shi, nata da nashi baki daya. A haka ya karar da samartakarsa ta shekaru goma a baya da macen da ba ta isa ba a sanyata a jerin mata, bai taba yin zina ba, balle ya san bambanci sai 'yan abubuwan da ba a rasa ba, wadanda sharrin kudi da mukami ke sawa. Ya ce, "Danejo ki saurareni, na yi aure bayan tafiyarki". Sai ta kyalkyale da dariya, "Daddy ho! Yau kuma da wannan za a tsokane ni?" Fuskarshi serious ya ce, "Am not teasing you Madam, and I'm not joking. Abin da nake so shine, ki zama uwargida ta gari abin koyi ga na kasa dake. Sai kin rike girmanki zan samu kwanciyar hankali madawwami. Kinga dai ban hada ku ba, kowacce na side dinta balle ta yi kukan daya ta yi mata ba daidai ba. Safah ba ta da matsala, am sure za ta zauna dake lafiya ta baki girmanki, ke kuma ki rike girman don Allah". Danejo ta yi kukan kura ta wawuro fitilar jikin gado ta maka masa a baya. Ta sake yin wani kukan kuran ta bishi ta shake. "Daddy sai dai mu kashe juna kafin daya ya kashe daya........" Ya kama hannuwanta ya rike gam-gam, sannan ya zuba mata wani lafiyayyen mari a hagu da dama, sakamakon wata azaba da ya ji a kwakwalwarsa a dalilin takalminta mai tsini da ta kantara masa a tsakar ka. Marin ya shigeta sosai, don daina ji da gani ta yi na wucin gadi. Ya mike ya fita bayan ya kulleta a dakin ba tare da ya zare mukullin ba. Sassan Safah ya nufa jini na diga daga kansa. Tana kwance a falo ta rungume filo ta kashe fitilar falon sai hasken talabijin dake aiki, sai danjar A.C dake dan haskaka falon. Don haka ba ta ga halin da yake ciki ba, ita ma bai yi mata magana ba kai tsaye ya wuce toilet ya saki shower a kansa, yana ganin jinin jikinshi na bin ruwa. Jiri ya ji yana kokarin kama shi don haka dole ya nemi taimakon ta, duk da ya lura ita ma nata buhun bala'in yana nan yana jiransa, sai dai ya san ba na hauka da rashin imani irin na Danejo ba. Ita iyakar nata fushin shine ta ki yi masa magana ko ta raba makwanci da shi. Yana dafe da bangon bandakin ya ce, "Ki zo ki taimaka mini ina bleeding……..". A sukwane ta mike ta kunna fitila, ta ga Lamido tsamo-tsamo cikin jini. Ta ce, "Subhanallahi! Nasir (karo na farko da ta kira sunansa na ainihi) 'yan fashi ne suka shigo?" Girgiza mata kai ya yi kwayar idonshi na shagidewa za ta bace daga cikin idanunsa. Akwatin taimakon farko (First Aid Bod) dinta ta nufa da gudu ta kungiyar (red cross). Kafin ta iso har ya kai kasa. Ta yi azamar tallafo shi ta rungume a kirjinta ta fashe da kuka. Kokarin tsaida jinin ta fara yi, yana bukatar dinki a kan domin ya yi rami sosai na dunduniyar takalmin mace. Kana iya hango kwakwalwarsa da jinni ya lullube. Don haka dole a dangana da asibiti. Bata taba shiga tashin hankali irin na yau ba. Taga (window) ta nufa tana kiran "Isaac...! Isaac...!! Gumsu". Isaac wanda ke kasan benen yana shan taba ya jiyo ta, amma Gumsu bai ji ba don yana can yana baiwa karensa abinci. Sai ya haura da gudu yana fadin "Madam....Madamm, gani nan what happen?" Da ya shigo falon kara yayi, "aaaah! Oga!!! Sai ya kinkime shi ya yi kasa yana nishi kamar zai kifa, don ma yana da karfi. Bayan mota ya yi, kan ka ce meye wannan ma'aikatan gidan duk sun fito suna neman ba'asi, wasu sun ce saidai in bullet ne ya huda masa kai, to amma waye mai pistol a cikin su? Cikin kowannensu ya duri ruwa. Isaaac bai bi ta kansu ba, yayi asibiti da ubangidansa shida escourt dinsa yana tafe yana ta kiraye kirayen wayar Likitan Lamido yana kuka riris yayi asibiti da shi ba tareda yasan bayanin da zai yiwa likita ba. Haka likitoci suka rufu a kanshi don ceto lafiyar shi data kwakwalwarsa. Mu karasa a littafi na 3. Kuma na karshe insha-allahu. Maman khazrajy.BABBAN GOR…3 A llah ne ya kai Susan mai aikin Danejo dakin uwargijiyarta don ta gaya mata an harbi Oga tun dazu babu wanda ya ganta ta fito, ta duba falon ba ta nan sai ta nufi bedroom, nan ta jiyo muryar Danejo na cewa. "Waye a nan? Bude ni don Allah". Ta bude ta, ta ganta wujiga-wujiga dakinta kamar an sha dambe a cikinsa, nan da nan ta gane abinda ya faru. May be Oga ya gaya mata ya yi aure daga dawowarta shine ta nemi kashe shi. Don ko su barorin gidan sun santa farin sani kan kishi, cikinsu babu wadda ta isa ta shigo in yana gidan sai in ya fita ta neme su. Sai ta kasa gaya mata komai ta ce dai an wuce da Oga asibiti basu ganta ba. Tsaki ta yi ta koreta. Tana kwafa ta ce, "Ai mutuwar kasko zamu yi, kar ka barni da rai, kamar yadda nima ba zan barka da rai ba". Safah na cikin likitocin dake kula da Lamido, domin dai MBBS ta yi ( specialization dinta kawai shine dental surgery/dentistry). Sai da aka kwana uku ya samu kansa. Anyi dinki sosai an rufe wajen, kafadarshi ta dama ma ta kumbura sakamakon fitilar barcin da ta sauke masa a kafadar. Tun daga asibiti ya sai mata tikiti ya aika mata, sannan ya kirata a waya ya ce ta tattara ta tafi Yola shi ba zai iya wannan bala'in ba kafin ta kai shi kabari kwananshi bai kare ba, idan ta sake ya zo ya taddata a gidan zai sake ta. Wannan shine weakness din Danejo (saki daga Lamido). Don haka tana kuka ta debi wasu daga cikin kayanta ta tafi. Ta je ta shiryawa 'yan'uwa da iyayensu karya da gaskiya ya ce in ba ta tafi ba zai saketa. Ya yi aure bata sani ba, don ta yi magana ya yi mata dukan tsiya ya koro ta. Hankalin Hajiya Nadeeya ya tashi kwarai, Malam kuwa bai yarda da ita ba, cewa ya yi sai ya ji ta bakin Lamidon. Ya yi ta kiranshi a waya amma dukkan wayoyinshi a kashe. Hajiya Nadeeya ta ce, "Ka ga abinda nake gudu ko Malam? Shi yasa raina bai kwanta da karin auren nan na Lamido ba, amma ka yi uwa ka yi makarbiya kai ga mai 'yar'uwa. 'Yar'uwar da saboda daular da take ciki ta daina neman ku, ta daina zumunci daku. Yarinyar da aka tabbatar tun kan ta je gidan miji ya saketa saboda sun gama watsewa da saurayin tun a titi, shekaru bakwai da rabuwarsu ba ta samu miji ba ya je ya kwaso ta, kai kuma ka goya mishi baya. Ga shi nan ai tun ba a je ko'ina ba ya koro uwar 'ya'yanshi. To wallahi mu ba zamu yarda ba. Idan har Danejo bazata zauna tare da shi a Abujar ba, sai dai in ita ma Sakina take ko wa? Ta dawo nan su zauna tare da Danejo muna kallon takun kowaccensu, ba za a mallake min da ba, kamar yadda suke mulkar maza! Labarinsu kwando-kwando babu wanda bani da shi". Malam Abdulkarim bai katseta ba sai da ta dasa aya. Ya ce, "Nadiya! Nadiya!! Nadiya!!!" Har sau uku. "Ke ce ko ba ke ba ce? Ko wata me kama dake ce take yi min gizo da kamannin ki?" Ta karkace kai, "Gaskiya ai daci ne da ita". Malam ya yi murmushi ya ce, "To yanzu in ya tattaro matan nasa ya kawo miki shi ya tafi shi kadai me za ki yiwa matan nashi? Za ki ije musu larurar aure ne ko za ki dauki nauyin su?" Ta yi shiru, don ta rasa amsar da za ta bashi. Ya ce, "Da girmanki, da mutuncinki kika share mazauna kika zauna ana gaya miki gulma a kan mutanen da basu da hakkin ki. Wallahi ki ji tsoron Allah, Allah ba azzalumin kowa bane. In kin ki ji ba kya ki gani ba". Ya karkade babbar rigarsa ya fita. Kwana bakwai din da suka biyo baya, babu waya daga Lamido ko ji daga gare shi. Don haka Malam Abdulkarim ya yi shiri ya bi dansa don hankalinsa ya gaza kwanciya. Ta jirgi ya taho, dan haka cikin dan lokaci ya isa Abuja, ya yiwa Isaac waya ya je filin jirgi ya dauko shi. Suna tafe a hanya Isaac yake gaya mishi ai Oga yana asibiti yau sati guda, mai yiwuwa ma yau a sallamo shi. Malam jiki a sanyaye ya ce, "Me ya same shi?" Isaac ya ce, "Mu kanmu ba zamu ce ba, lafiya na dauko su a filin jirgi shi da Maman su Fa'ik, muka shigo gida lafiya. Ta dade a Sydney sai ranar ta dawo. Ba a fi awanni biyu da shigarsa gida ba sai Madam karama ta soma ihun kirana. Wallahi wani abu aka luma masa a tsakar ka kamar bullet saboda zurfin da ya yi. Dan Allah ya rubuta yana da sauran shan ruwa a gaba da ba za a same shi ba. Har yanzu likitoci suna hasashen Allah yasa kwakwalwarsa ba ta samu matsala ba, za su tura shi wani asibitin a Miami, likitan kwakwalwar da babu kamarsa a Africa da Turai ya duba shi sosai, Dr. Al-ameen Bello Makarfi (Siradin Rayuwa). Don haka duk da bai fada ba, sai dai in a tsakanin Madam babba da karama ne wata ta yi mishi wannan aika-aika wallahi, don mu dai bamu ga kowa ya zo ba, kuma babu wanda ya shiga, don babu wanda ya isa ya karya security din gidan nan kwamfuta bata nuna shi ba". Malam ya girgiza kai, tuni ya gano bakin zaren al'amarin. Ya samu Lamido ya ji sauki sosai, sai dai asibitin cike yake da ma'aikatansa da abokan arziki har da mataimakin shugaban kasa. Lamido ya ji dadin ganin mahaifinshi. A lokacin aka sallame su suka nufi gida motoci bila'adadin biye dasu. Lamido mutum ne na jama'a, kowa son shi yake. Shi ba dan siyasa bane amma yanada siyasar sa akan- karan kansa, wadda ke sayo mishi kauna daga al'ummar Nigeria kabilu da hausawa. Yana rike da hannun Malam, Safah na biye dasu rike da jakar Malam din karama, basu tsaya ba sai falonta na kasa. Lamido bai ambato Danejo ba balle ya ce ita ta yi mishi wannan aika-aika, cewa ya yi tsautsayi ne wanda ba a sa mishi rana. Malam din ma bai takura sai ya kure shi ba, shi dadi ma ya ji Lamido zuciyar 'yan Aljannah gare shi, ya rufawa iyalinsa asiri shima Allah Zai rufa masa. Malam don haushin Danejo ko zancen zuwanta Taraba bai masa ba. Ita tana can ta hada shi da mahaifiyarsa da 'yan'uwansa, shi ga shi yana rufa mata asiri, don ya tabbatar bai yi aure don baya son Danejo ba, ko don ya wulakanta ta ba. Washegari Malam ya yi sammako ya yi komawarsa. Bayan ya saka musu albarkar hidimar da suka kwana suka yini yi da shi kamar sun hadiyeshi shi da Safah. Da ya dawo gida ma bakinshi ya ja ya yi gum bai ce dasu komai ba. Ta zauna gidan in ta zama 'yar ta'adda kar ta kashe masa rabin zuciyarshi Lamido. Tambayar duniya Haj. Nadeeya ta yi Malam ya ki ce da ita komai. Da ta dame shi da tambaya sai ya ce. "Dana bai ce min ga laifin da Danejo ta yi masa ba". Ta ce, "Rashin arziki ne kenan ka gani ko? Don haka gobe a sai mata tikiti ta koma dakinta". Ya ce, "Bani da hali". Ta ce, "Ni ina da shi zan bata". Ta shuri kwanukan abinci ta fita.

Zahra'u ta shigo ta tadda mahaifinsu cikin tagumi, Zahra'u ita ce autar su Lamido. Akwai shiri sosai tsakaninta da dan'uwanta da take so fiye da kowa a gidan. Shekarunta sha bakwai ta gama sakandire tana jiran fitowar jarabawa, don Lamido ya ce Malaysia zai kaita ba yanzu zai yi mata aure ba. Ta gaida Malam, ta yi masa barka da dawowa. Sai ta koma gefe ta takure ta yi shiru, idanunta suka ciko da kwalla. Malam ya maido hankalinsa kanta da ya gane cikin damuwa take, ya ce, "Fadima (sunan da yake kiranta) me ya faru ne?" Hawaye ya zubo mata ta matsa kusa da shi sosai, kamar zata shige jikinsa jikinta yana rawa, "Baba tun muna yara ka hane mu da yin labe (sauraron maganar mutane), kuma wallahi ban taba yi ba". Ya girgiza kai alamar ya yarda ba ta yi din. Ta ci gaba da cewa. "To jiya Hajiyarmu ta fita Inna Shatu (mahaifiyar Danejo) ta zo, lokacin ina barci a uwar daka tashina kenan, amma ban fito ba sai na ci gaba da kwanciya. Sai na ji Aunty Danejo na gayawa Inna Shatu fasa kan Yaya Lamido ta yi da tsinin takalminta". Ta share idonta da hanci. Ta ci gaba da cewa. "Ta gayawa Inna Shatu wallahi sai ta karasa shi in dai bai rabu da matar da ya aura ba. Ita ba gado take so ta ci ba, don ita ma ta shirya tafiya lahirar suje can su zauna su biyu, ko hurul'ini Allah ya ba shi sai ta rabata da numfashinta". Malam ya kadu sosai ya firgita. Zahra'u ta ci gaba da cewa, "Sai Inna Shatu ta hau yin dariya, ta ce mata ai a lahira ba a mutuwa. Ta yi hakuri ta zauna su ci gado, ta danne shi da filo kawai ko ta zuba mishi abin da zai tsitstsinka mishi hanji bakinsu alaikum, ba kishiya kuma ga gado daga ita sai 'ya'yanta, karkari a bawa amarya tumunin takaba, su Malam da Nadiya ma dan abin da za a tsakura musu a ciki bai taka kara ya karya ba…..". Zuwa wannan lokacin Malam ya mike tsaye. "Tsakanin ki da wa kike magana Fadima? Mai sunanki ba ta karya". Ta ce, "Idan na yi musu karya kada Allah ya sunsuna min kamshin Aljanna". Ya ce, "Jeki, ki kwantar da hankalinki barni dasu, ba abinda zai samu dan'uwanki da yardar Ubangiji. Mutane na gari Allah yana kare abinsa a ko'ina. Balle wadanda albarka da addu'ar iyaye ta yi musu lullubi". ***

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull