Kenza eBookz

Babban goro complete novel - Chapter 26

Babban goro complete novel - Chapter 26

Babban goro complete novel Chapter 26: Babban goro complete novel Chapter 26. T un daga ranar Malam ya daukewa Hajiya Nadeeya wuta a kan zancen komen…

2,759 words

T un daga ranar Malam ya daukewa Hajiya Nadeeya wuta a kan zancen komen Danejo. Gargadi ya yi mata mai zafi cewa kada ta sake ya ji ta maida Danejo dakinta sai mijinta ya bukaci hakan, ya kuma zo da kansa daukan nata. Wannan ba karamin tada ma Hajiya da Danejo hankali ya yi ba, sai dai ita Danejo ta fita tashin hankali, musamman idan ta tuna Lamido na can yana barje amarcinsa da watanta. Wannan tunanin ba karamin tada mata hankali yake yi ba. Aka debi sati biyu babu Lamido babu wayarsa. Sai ta soma hada kayanta kawai kamar mahaukaciya a hantsin safiyar lahadi ta fito jaye da trolley, ta samu Hajiya a madafi ta ce. "Ni zan wuce Abuja Hajiya, jikina na bani Daddy ba lafiya ba, don bai taba yin irin wannan fushin dani ba". Hajiya ta yi dan jum! Ta ce a ranta, "Danejo kishi ya maida ta mahaukaciya". Kamin ta ankara Danejo ta fice. A zaure ta hadu da Abubakar, ta ce, "Yauwa Bukar, dauki akwatin nan ka rakani Airport". Abubakar ya cika da mamaki, ya ce, "Aunty Danejo babu mukullin motar Malam a hannuna, kin san kuma ba zan goye ki a babur ba". Ta ce, "Tasi zamu hau". Ya kama baki yana mata kallon wani abu na motsi a kwakwalwarki, sannan ya ce, "Da izinin Yaya Lamido zan dauke ki a tasi in kai ki filin jirgi?" Ta lailayo wani ubansu ashar ta mirgina masa, ta ce, "Shi da Yaya Lamidon su raba, zai rakata ko ba zai raka ta ba?" Da gudu Abubakar ya yi cikin gida ya shige kuryar dakin Hajiyarsu yana cewa, "Hajiya! Hajiya!!" Ta aje ludayin da take damun kunun gyada da shi ta bishi dakin zaninta na kwancewa, ta ce, "Lafiya Abkar". Ya ce, "Wallahi Aunty Danejo kanta da motsi". Ta ce, "Nima na ga alama". Suka dunguma soron suka kama jakar suna lallaminta ta koma gida ta jira Malam ya dawo ya ba da mota sai a kaita. Sai ta fashe musu da kuka, daidai lokacin Inna Shatu ta sawo kai soron. Ta ce, "Lafiya?" Hajiya ta ce, "To da sauki dai, Danejo ba ta jin magana, har yau matar Lamido take ba ta gama sanin halinsa ba". Da kyar suka lallabe ta da taimakon uwar suka koma cikin gida. Hajiya Nadeeya ta ce, "Ki bar ni in bai zo ba karshen satin nan ni da kaina zan maida ke dakinki. Bai isa ba wallahi, har yau ba a haifi diyar da za ta rabaki da Lamido ba. Ba 'yar'uwar Malam ba, ko 'yarsa ce ta cikinsa".

**** A nasu bangaren, komawar Lamido gida daga asibiti ta zo da sabon sauyi wanda ke nuna lallai Lamido na bukatar ganin likitan kwakwalwa. Da farko al'amuran basu damu Safah ba, don tana danganta hakan da zafin ciwo, tunda raunin bai gama warkewa ba. Abu na farko, idan Lamido ya shiga wanka baya fitowa sai ya yi awa biyar. Tana mamakin me yake zama yana yi haka? Rannan dai ta ga zaman jiranshi a bakin gado ba zai yi mata ba, sai ta bishi bandakin ta ga me yake yi kwanan nan a bandaki? Sanda ta murda kofar ta shiga sai ta ganshi yana matsa (gilette shabing cream) a kan burushinsa, ya hau wanke baki da shi. A gefe kuma ya tara kumfa a baf ta omon Ariel ya shiga ciki ya soma bathing. Yana ninkaya cikin rowan. Yana mai yin soso da hularsa. As a proffessional medical Doctor, sai ta soma obserbing kwayar idanunsa, a juye take gaba daya. Sanda ta fito, zama tayi kan duwawunta a gefen bandakin a dandaryar tayal tasa hannuwanta cikin gashin kanta kamar ta kurma ihu, ta rasa inda za ta sa ranta. Sai ta ga ya fito daure da tawul ya nufi ma'adanar kayanta ya fiddo best dinta fara sol ya soma kici-kicin sakawa amma ta ki shiga jikinsa. Da ya takura sai ta tsage gida biyu, ya yi ta tsaki ya yar da ita ya dauki wandon farin boyel ya saka, tazugen na reto har kusa da gwiwarsa. sai ya kawo suit baka ya dora. Ya kawo hula zanna-bukar ya saitata a goshinsa. Ta mike da gudu ta rungume shi ta baya,

"Lamido kada ka karya min zuciya, bayan ta mika wuya ga kaunarka!!!".

Kokarin rabata yake da jikinsa, bayan ya bata kyawawan mari guda biyu a kuncinta na dama. Zafin marin ne yasa ta yi baya ta yi taga-taga ta fada gado. Ya fice yana ce da ita, "Ki yi maza ki dama min koko da 'yar tsala, irin wadda Hajiyata ke mini ina tafiya dasu makaranta".

Fitowarsa ke da wuya Isaac ya jawo mota har gabansa, haka mai tsaron lafiyarshi na tare da shi suka nufi office, kowannensu fuska muzance da shigar da Ubangidansa ya yi. Amma wa ya isa yayi Magana? Isaac na tuki yana sharar hawaye, lallai maganar likitocin sa ta tabbata. A cikin office abubuwa suka ci gaba da gudana abnormally, a fuska dai Oga lafiyarsa kalau, amma abubuwan da yake yi sun sha bamban da wadanda yake yi a baya. Abu na farko da ya fara yi shine, transferring gaba daya kudin dake cikin account dinsa zuwa account din Safah (na bankin GT kenan). Na First bank zuwa account din Malam Abdulkarim. Na kadarorinsa kuwa zuwa account din Fahad da Fa'ik. Sannan ya rubuta wata latter ya tura ta zuwa email din mataimakin shugaban kasa mai dauke da cewa a sauke shi daga mukaminsa zai koma kasar Saudiyya da zama, a nemi wani a bashi kujerar shi ya yi retire.

Sako ya shigo 'Economic and Financial Crime Commission' cewa ga mai girma Deputy zai shigo ma'aikatar yanzu. Nan da nan kowa ya mike tsaye aka karbi mai girma Deputy. Bai tsaya ba kai tsaye ofishin Lamido ya nufa. A lokacin Lamido kuka yake yi, ya kifa kai a teburinsa. Har mai girma ya shigo bai san ya shigo ba, sai da ya fiddo waya yana magana da Mr. President sannan ne Lamido ya dago. Ko gurin zama bai bashi ba, shi ya yiwa kansa mazauni a kujerar dake fuskantar Lamidon. Ko gaishe shi Lamido bai yi ba balle ya mike tsaye don girmamawa. Kallonsa kawai yake da juyayyun kwayar idonsa, shine ya sassauta murya ya ce. "Lamido baka gane ni bane?" Ya ce, "Idan na sanka sai me za a yi? Aikinku ne na ce bana yi, to me ka zo ka yi min?" A daidai lokacin da jiniyar sojoji ta cika ma'aikatar, sai ga mai girma Mr. President ya zo da kansa. Suka kulle kansu su uku a office. A Turance suke magana a tsakaninsu da mai girman da mataimakinsa. Nasir sai harararsu yake, ya soma tunanin ma bari kawai ya gwara kansu dukkansu munafukai ne. Ai da suka ga ya mike ya nufo su a fusace daya ne ya bi ta kan daya ya cimma kofa. A nan ne kuma likitan Lamido ya danno kai, sai Mr. President ya bi ta kansa ya yi gefe guda shi da jakar aikinsa, bai tsaya ba ya tsallake shi ya cimma jama'arsa a kofar ofishin yana haki yana zazzare ido da kokarin nuna komai is normal. Don haka Lamido kan Mr. Deputy da Dr. Mohammed ya hada ya gwara da bango, sannan ya nuna musu kofa ya ce, "Habe your way here". (Ku bi nan). Deputy bai tsorata ba, haka Dr. Mohammed, sai ya rungume Lamido yana kuka sosai, goshinsa yah aye yayi suntum, ba tare kuma da ya damu da naushin da Lamido ke kai mishi ta ko ina ba. Shi kuma likita yayi gefe bisa tebir yana ta rubuce-rubuce cikin file din shugaban EFCC Nasir Lamido Taraba. Da lallashi da ban baki Deputy ya ciyo kansa ya yarda ya shiga mota suka maida shi gida, suka samu Amarya abin tausayi, ta ci kuka har ta gode Allah. Ko kayan barcin jikinta ba ta cire ba, tana zaune cikin kujerun falonta ta yi tagumi, fuskar nan data sha mari ta kumbura duk da ta mulketa da manthaleta. Da saurinta ta mike ganin sun shigo da shi a rirrike. Yau ce rana ta farko da ta taba yin ido da ido da Deputy Sulaiman Yakasai, sai dai ta ji shi a bakin Lamido ko hirarsu in suna waya. Ba wannan ne a gabanta ba, ta ce da Dr. Mohammed "Am sure Lamido is not well". Ta gaya mishi abubuwan da ya yi a yau. Allurar barci Dr. Mohammed yai mishi, bai kai minti biyar ba ya yi barci. Cikin dan lokaci manyan Psychiatrists sun cika gidan, har da jar fata. A can bangaren Deputy da Mr. President tuni sun kammalawa Lamido da Safah shirin tafiya MIAMI. An dora wani a kan kujerarsa an kuma tafi dauko Malam Abdulkarim daga Taraba. Wanda ke can yana mamakin alert din da ya samu cikin wayarsa mai nuna cewa Lamido ya yi masa kyautar kudin da bai taba jin adadinsu a rayuwarsa ba. Sai ga sako ya cimmasa Isaac ya zo, aka bude mishi dakin ganawa da bakin Malam. Can Malam ya je suka gaisa, ya gaya mishi an turo shi ne ya dauke shi. Bayan wannan bai ce da shi komai ba. A daren suka tashi zuwa Abuja. Hankalin Malam Abdulkarim ya kai kololuwar tashi da ganin wai Lamidon shi ne riga daban wando daban, yana kallonshi cikin ido amma bai gaishe shi ba. Safah na gefe dukunkune cikin lafayya tana ta kuka mai ratsa zuciya. Addu'a malam ya soma karantowa yana tofa mishi, sai ya soma kunkuni yana cewa, "Gaskiya ni ka daina tofa min miyau".

A wannan dare da ya zowa Safah da sauyika da dama a rayuwarta, har garin Allah ya waye ba ta daina kuka ba, ba ta san tana son Lamido har haka ba sai yau da rayuwa ta juya masa baya. An sauke Lamido daga kujerarsa an mayar da wani a gurbinsa. A cewarsu, dakatarwa ce ta rashin lafiya a bisa shaidar motsuwar kwakwalwa da likitocinsa suka bayar. A washegari suka tashi zuwa MIAMI su hudu, Malam Abdulkarim, Safah da Lamido, sai Dr. Mohammed (personal Doctor ) dinsa da iyalinsa.

****S MUTANEN PARIS un sauka a Paris karfe goma sha biyun dare, motar Hotel din da Zahraddeen ya yi booking tun kamin su taso tana tsimayen saukarsu, suna sauka chauffer din ya kwashesu. Babu komi cikin wannan zama na Zahraddeen da mai dakinsa sai so da kauna zallah. Hutu suke mai suna hutu da tsimayen isowar jaririnsu ko jaririyarsu. Sun manta da wata Anisa da al'amarinta wadda suke kallo a matsayin wata wadda ta yi musu karan tsaye a cikin rayuwarsu. Sai dai Marwah zuciyarta babu mugunta. Da ta samu nutsuwa ne ma ta soma tunanin hanyoyin da za tabi ta janyo hankalin Zahraddeen da su ya kaunaci amaryarsa, in dai ba zai kusance ta ba ita bata damu ba, ko duniyar ne ya tattara ya bata. A ranar da suka yi kwana uku ta kira Inna ta sanar da ita sun sauka lafiya, kuma tana samun kyakkyawar kulawa daga likitocin ta. Inna ta baiwa Daddy, ta sha surutu. Sai ta ce, "Inna Anisa ba ta kusa ne?" Inna ta yi shiru, domin dai ita tun jiya ba ta ga Anisa ba. Ta dauki makullan sassan Zahraddeen da suka ba ta ajiya ta ajiye a kan talabijin ta je ta zabi daki ta yi zaman ta. In ta ji yunwa can take dafa abin da take so ta ci don babu abinda babu a store da freezer. Jin Inna ta yi shiru sai ta ji gabanta ya fadi, ta cika da taraddadin kada dai wani abu ne ya samu Anisan saboda son Zahraddeen. Ta ce, "Inna wani abu ya faru da ita ne?" Inna ta ce, "A'a, babu komai. Ta dai tattara ne ta koma sassanku. Kin santa ba kan gado ne da ita ba". Maimakon Marwah ta ji haushi sai abin ya yi bala'in bata dariya. Wannan tusa kai ga miji har ina? Tana dariya ta cewa Inna, "A kyale ta Inna ta yi zamanta a tayamu addu'ar sauka lafiya, da na sauka zamu dawo". Inna ta ce, "Allah ya yi miki albarka Marwah, ya baki 'ya'ya masu kyakkyawar zuciya irin taki. Ya tallafi maraicin ki kamar yadda kika tayani tallafar nata maraicin. Shi kuma Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakaninku". Cike da jin dadin addu'ar Inna Binta ta ce, "Ameen Inna, Inna Allah Ya kara girma". Ko kusa ba ta gayawa Zahraddeen ba, ta ci gaba da hidimomin gabanta. A cikin tsarin da likitarta ta yi mata har da na yawan motsa jiki da yawan tafiyar kafa. Karfe hudu na yamma agogon su n a can ta idar da sallar la'asar kenan Zahradden ya fito cikin shiri na red trouser din jeens da farar shirt samfurin BBulgari. Ta daga kai tana kallon shi yana tazar sumarshi kamar ta hadiye shi, "You are looking takeaway….". Ta fada cikin ranta, ba ta san cewa furucin ya subuto ya shiga kunnensa ba. Dariya ya yi ya girgiza kai amma bai juyo ba, kada ta fahimci ya ji ta. Ta ci gaba da cewa. "To yanzu haka zai je yana romancing yarinyar nan, na shiga uku na lalace......." sai kuka. Zahraddeen ya ce, "Uh Allah!" Sai ya hau cire kayan ya janyo dakakkiyar shadda har da babbar riga ya zurma. Ya kawo hula kube ya dora kamar angon da za'a daurawa aure. Ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye. Ya rada mata cikin kunnuwanta "Idan ta ganni a haka itama ta san ko kusa dani bata isa ta zo ba". Ba ta san sanda ta yi dariya ba, dariya sosai, ta dunkule hannu ta buga mai a kirji, shi kuma sai ya yi azamar rungumeta. Wata irin soyayya suke gudanarwa a tsaye, ba tare da zungureren cikin ya hana komai ba. Ta yarda ta amince Zahraddeen nata ne ita kadai. A cikin wannan halin dai da yake ciki ko cewa ta yi ya saki Anisa wallahi zai saki ko saki hamsin ne in akwai. Kawai dai abin ya zo mishi a kaddara ne, wadda ba shi da ikon kauce mata. Fitar da aka shirya yinta karfe hudu ba a yi ta ba sai bayan magariba. Yana rike da hannunta suke zagayawa wani dankareren shagon jarirai a tsakiyar birnin Suisra. Dauki wannan jefa cikin kwando, dauki wancan haka suka yi ta yi. Kayan jarirai ne suka hada masu ban sha'awa, sannan ta dibarwa Daddy, da Anas da Malik 'ya'yan Rabi'a kanwar Zahraddeen. Basu koma masaukinsu ba sai karfe daya na dare. Zahraddeen na bisa Ipad dinsa yana tura sakonni. Ni'imar birnin Suisra na ratsa kowacce gaba a jikinsu. Sai Marwah ta mike ta shige toilet da kyar don rage mara da wani mugun fitsari da ya kulle ta a marar. Amma me? Da ta tsuguna ta yi fitsarin sai ga jini ya biyo baya hade da wani azababben ciwo mai gigitarwa. Sai kuma ga kan kyakkyawar jaririya ya danno, ji kake suluf! 'Yar baby a cikin masai. Da karfinta ta ce, "Abban Daddy........" Ya sheko da gudu ya tsamo 'yar dake ta wutsil-wutsil.....cikin masai, sai kuma ta canyara kuka mai karfi. Da jinin dake jikinta da cibi ya hada a kirjinsa ya rungume. Marwah da kanta ta yanke cibin ta goge mata jiki da olibe oil. Cikin kayan da suka sayo ta ce ya je ya sa mata masu kauri ya lullube ta. Fadi yake, "Kin san nakuda kike kika yi shiru? Saboda Allah da wani abu ya faru fa? Baki taba bani haushi irin yau ba. Wannan wane irin gangancine?". Ita dai ba ta kula shi ba ta ci gaba da kokarin gyara kanta. Ba ta fito ba sai da ta gasa kanta cikin ruwan zafi da tawul, ta tabbatar ba ta samu kari ba. Ta sha magungunan da suka dace sannan suka wuce asibiti. Lokacin asubah ta yi. Rungume yake da babyn mai mugun kama da Rabi'a. A asibitin ya yi sallah sannan suka wuce ofishin likita. Su ma fada suka yi ta yi. Ta ce su yi hakuri ita ba ta ji wani ciwo ba sai a toilet. Nan suka rike su suka ci gaba da basu kulawa. Basu sallamesu ba sai bayan sati daya. A ranar ne kuma suka biyo jirgi zuwa Nigeria. A airport din Abuja suka sauka. Duk kokarinsu na samun layin Safah ko maigidanta hakan ya faskara. Don haka kai tsaye Saifullahi abokin Zahraddeen da ya taho dasu daga filin jirgi ya wuce da su Asokoro, wajen Gumsu da Isaac dake bakin get, suka samu labarin cewa suna Amurka, Oga babu lafiya. Har suka zo Kaduna tambayar junansu suke ko me ya faru da Lamido?

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull