Kenza eBookz

Babban goro complete novel - Chapter 27

Babban goro complete novel - Chapter 27

Babban goro complete novel Chapter 27: Babban goro complete novel Chapter 27. Inna na yankan ganyen shuwaka da za ta yi musu miya da ita sai jin shigowar…

2,612 words

Inna na yankan ganyen shuwaka da za ta yi musu miya da ita sai jin shigowar mota ta yi gidansu. Kamin ta gama sakar zucin waye ya zo ta jiyo jaririya tana ta tsala kuka, ga kamshin iyayenta ya fara sirnana cikin hancinta. Ai sakin wukar hannunta ta yi ta tsallake ganyen dake jibge a gabanta ta taresu ta karbi 'yar tana hamdala ga Allah har da hawayenta. Sai ga Daddy ya shigo da gare-garensa ya yi fututu da ka ganshi ka ga dan unguwar Tukur-Tukur. Ya watsar da gare-garen ya sheko da gudu, "Momi! Daddy!!" Ya rungume uwar, sannan ya juya ya rungume uban. Shi kuma ya sure shi ba tare da ya damu da fututun kafarsa da laimar hancinsa ba ya soma juyi da shi a tsakar gidan..... hugging him, kissing him…….."I cannot edpress how much I missed my darling Daddy…….!". Hayaniya ta hana Anisa barci, wacce ke narke cikin lallausar bargon bed room din Zahraddeen.. Ta leko ta taga, nan ta ga abin da ta gani, ta dafe kirji tana numfarfashi ta ce, "Wayyo madarar raina….. ya dawo". Da gudu ta dirgo daga gadon ta soma kokarin canza kaya, ta zare siket da riga cikin wadanda Nura ya dinka mata ne na atamfar super shudiya za ta saka leshi, sai ga Zahraddeen ya shigo. Salati ya yi sannan ya ja da baya, don shi bai san tana sassan ba, ya dai sha mamakin ganin kofofin a bude. Marwa ba ta gaya mishi hirarsu da Inna ba. Yarinya kamar aljana, ya fusata matuka don ya ga karambanin nata ya yi yawa. Ya daka mata tsawar da ta gigita ta ya ce, "Wa ya baki makullina? Da izinin wa kika shigo mini daki?" Jikinta ya hau mazari don ba ta taba ganinshi cikin matsanancin fushi irin wannan ba. Amma bakinta bai mutu ba, amsar da ta ba shi ta sanya jikinsa yin sanyi. Idonta cike da kwalla ta ce, "ALLAH!" (wato Allah shi Ya ba ta izinin shigo masa daki a matsayinta na matarsa). Ta juya ta soma hada tarkacenta tana kuka tana shessheka tana sharce majina da hawaye. Ta mayar da kayan jikinta da ta cire don ta yi masa kwalliya, ta hada sauran tana kullewa cikin zanin atamfarta. Ta bi ta gefensa bayan ta daura kullin kayanta a kanta ta fita. Ya zauna a gefen gado, ya kai hannuwansa biyu ya dafe kai, ya rasa abin da ke mishi dadi. Daga nan inda yake ya jiyo ihunta a dakin Inna tana birgima a kasa wai Yaya Dini ya korota. Inna wadda ke kici-kicin daura garwar wankan jego ko juyowa ba ta yi ba balle ta rarrasheta, don ta san dama za ai haka tunda ita ba hankali ne da ita ba. Nura da Marwah da dan yaro Daddy sune 'yan lallshi. Daddy ya ce, "Aunty Anisa ki daina kuka". Ta zazzaro masa ido ta ce, "Kai tafi can, ba saboda uwarka ake wulakanta ni ba?" Nura ya yi baya yana ta dariya, ya janye Daddy suka yi waje yana cewa, "Zo muje my son rabu da ita, ba mu muka kar zomon ba balle a bamu ratayarsa. alhakin soyayyata ne yake dawainiya da ita". Wannan karon ne Inna ta yi magana, ta ce, "Nura!" Ya dakata ba tare da ya juyo ba. Ta ce, "Kada in kara jin maganar nan a bakinka. Anisa matar aure ce karewa ma matar Yayanka, ka ji na gaya maka". Ya sa kai ya fice yana ta dariya cikin ransa, shi dai ba zai daina son Anisa ba sai ranar da ya daina numfashi. Don haka yake jin dadin dizgin da Zahraddeen ke mata. Ita ma Marwan Inna tsawa ta yi mata, ta ce ta rabu da ita ta taho ta yi wanka. Inna ta salle jikarta tsaf da sabulun salo da dama ta tanada don haihuwar. Ta shafe ta da zaitun, ta sa mata farin kwalli har da fashin goshi (dan dirimi). Ta shiryata tsaf ta goye ta shiga harkokinta. Nan da nan ta hada tuwon shinkafarta da miyar shuwaka, ta dauki kaji a frezer ta gasa daya, ta yi farfesu da daya, duk ta dire a gaban surukarta. Marwah cike da tausayin hidimar da dattijuwar take da iyalanta ta ce, "Sannu Inna, Inna Allah Ya bar mana ke". Har ranta ta ji dadin furucin Marwah, ta yi murmushi kawai. Ta kara da cewa, "Inna nan dakinki ai zan zauna sai na yi arba'in". Inna ta ce, "Sai ka ce wata haihuwar fari? A'a, ki gama hutawa ki ci abinci ki tafi dakin ki zan ke shigowa ina ma baby wanka tunda kuna da ruwan zafi na lantarki. Dini ma zai fi son haka". Ta dan ji kunya, ta ce, "Haba Inna? Shi mai amarya? Ai zai fi son a barshi da amaryarshi". Inna ta yi dariya, domin dai ko gashin idonta ka kalla ba ma kwayar idanunta ba, sai ka ga yadda suke russunawa suna rankwafa kansu saboda KISHI. Ta koma tana lallashin Anisa ta yi hakuri ta ci abinci, amma fur! Ta ki sai jiniya take yi wai ita ba Inna take aure ba, idan Zahraddeen ba zai barta a dakin aure ba, to za ta shiga duniya kowa ya huta tunda baya sonta. Marwah na baiwa baby nono tana jiyo danger girl (sunan da ta sa mata). Ta yarda yarinyar da zuciyarta daya son Zahraddeen take, kuma frank ce bata da munafunci, shi din ne dai bata sani ba ko yana sonta ko baya sonta??? Kasancewarsa jajirtaccen namiji da mace ba ta juya shi, ko ya zauna yana yin zancen wani. Bai taba yi mata zancen Anisa ba tunda suka tafi har suka dawo. Sai ta ji wani bangare na zuciyarta ya soma tausayin Anisa. Kawai ba za ta iya juriyar Zahradden ya yi gamayyar jiki da ta zuciya da wata diya mace ba. Saboda tsoron halin maza, masu canzawa kamar wahainiya. Sabida dai kowacce mace komi muninta da baiwar da Allah Yayi mata, balle danyar kyakkyawar bafulatanar yarinya irin wannan. Ba ta sani ba shi Zahraddeen ko da sadaka bai jin zai iya auratayya da Anisa, ko don tattalin martaba da manyantakarsa a idanun kanwar tasa. Shi kansa bai sani ba, yana sonta ko baya sonta? Da kyar Inna ta samu ta shawo kanta ta dawo daki, nan ta ga Maman Daddy na shayar da Baby. Ta yi turus! Don dai ita ba ta san anyi haihuwa ba. Sai kuma jikinta ya yi sanyi don ko Allah Ya raya bata ce ba. Ta koma gefe ta zauna tana satar kallonsu, an ce "Naka sai naka". Sai ta mika hannu wai a bata 'yar. Marwah ta yi murmushi ta cireta a nono ta bata. Ta kurawa jaririyar ido ta ce, "Inna kamar Rabi'a". Inna ta yi murmushi ta ce, "A'a, Anisa dai, musamman wannan bakin rigimar". Ta yi dariya ta ce, "Kai Inna, wannan ai ta fini kyau, 'yar 'yan gayu, wadda haihuwarta ma ba za a yi ta a Nigeria ba sai cikin Turawa 'yan'uwansu". Marwah na ta dariya Inna ta ce, "Kema in kin yi hankali kin kwantar da hankalinki Allah kadai ya san iya adadin da zaku yi ta haifa kuna kawo mini ina goyawa kafin ta Allah ta kasance a gare ni. Koda duk shekara ne, domin na sadaukar da sauran rayuwa ta ga jikokina da zaman lafiyar ku. Amma idan kina ta yin wannan haukan da kike, yaushe mijin zai yi miki duban arziki?" Ta ce, "Bari ke dai Inna, ai ni ko mayya ce daga yau na hakura da Yaya Dini. Mugun dan wulakanci ake gaya miki, baki ga tsawar da ya yi min ba kamar wata dabba, nima makaranta zan koma......." Kalmar da ta shiga kunnen Zahraddeen kenan a sanda ya sanyo kai cikin dakin. Ya ce daga bakin kofa. "Da auren wa za ki koma makarantar? Ba dai da aurena ba, in je ki je ki lalace alhaki ya dawo kaina, tunda har za ki iya bude baki ki ce za ki yi zina idan miji bai tafi dake ba. Kin dauka na manta ne? Babu inda za ki, kuma mijin ba zai dauke kin ba sai kin gaya min inda kika san meye amfanin miji ga mata, tunda ba karance-karance kike yi ba amma wai har 'yan madigo kin sani, a gidan uban wa kika sani?" Ya zazzaro mata manyan idanunsa masu maiko (oily eyes), fiye da tsawar baya, ta gigice ta kidime ta soma inda-inda. Kunya kamar ta kashe Inna da Marwah, basu yi aune ba sai gani su kai ya zare belt din jikinshi ya zuba mata a baya. Ta bankare ta zabura ta yi kan Marwah, wata tsawar ya kara zubo mata, "Kika karya min Baby karyaki zan yi barambas, kuma wallahi sai kin gaya mini ko in kara zuba miki. Ki yi ta yiwa mutane hauka, idan anyi magana kice ke marainiya ce, kowa ma marayan ne, kuma baya amfani da marayantakar wajen hauka da yiwa bayin Allah tijara. Za ki gaya min ko sai na kara zuba miki?" Tana kuka sosai ta ce, "Wallahi ni ban taba yi ba". Ya ce, "To a ina kika sani?" Ta ce, "Ai Rabi'a ta gaya mini mata da miji soyayya suke yi in aka yi musu aure". Juyawa ya yi dariya kamar ta kashe shi. Inna ban da salati da sallallami babu abinda take yi. Marwah kuma ajiye Baby ta yi a cinyar Inna ta shiga bandakin Inna ta sunkuya ta yi dariyarta mai isarta. Tana jiyo Inna na cewa, "Kai kuwa Dini baka da mutunci wallahi". Anisa ta ce, "Rabu da shi Inna, ko shine autan maza daga yau na hakura da shi. Ka sake ni in samu miji inyi aurena". Inna ta bige mata baki, ta ce, "Kul! Kika kara furucin mijinki ya sake ki. Ba karamin batawa Ubangiji bane". Ya ce, "Rabu da ita Inna, sunan aurenmu auren zobe, ba saki ba yaji. Amma fa babu miji a hannu. Ita ma Rabi'a za ta ci ubanta". Kai yau Marwah ta ci dariya, duk sanda ta dago ido ta dubi Anisa wadda ke ta hidima da Baby sai dariya ta kama ta. Ita kuwa Anisa sai tsuke baki take tana sakin tsaki, can kuma ta ce, "Inna Yaya Dini dan rainin hankali ne. Ban da ya rainani shekarata shida a primary, shida a sakandire. Amma wai ban san me suke yi suke haifar 'ya'ya ba. Yo ko yaro dan shekara goma zai ba da wannan amsar balle ni mai sha shida". Inna ta dunkule hannu ta sakar mata, "Kin ci ubanki, na ce kin ci uwarki. Kika kara yi min zancen nan sai na fasa miki baki wallahi". Da haka Inna ta samu ta kashe zancen, ita dai Marwah bata uffan, amma har garin Allah ya waye ba ta daina dariya ba. Yarinyar na kara shiga ranta.

Washegari karfe bakwai na safe, Inna na kicin Marwah na gasa jikinta a toilet, Anisa ce ke damawa Baby madara wadda ke ta tsala ihun neman uwarta. Anisa ta goyeta tana ta jijjigata tana hada madara cikin feeder ya sanyo kai dakin Inna cikin shirin suit da sallama. Tun kan ya karaso kamshin Dior Addict ya gayawa mutanen dakin shigowarsa. Ga mamakinsa ba ta amsa sallamar shi ba, kuma ba ta juyo ba balle ta kalle shi sai girgiza fidarta take. Mamaki ya kama shi, ranshi ya dan tabu. Ya ce, "Ke kina jin mutane suna sallama kika yi kunnen uwar shegu dasu?" Ta juyo a slow ta yi masa kallon sama da kasa, sannan ta kyabe baki ta juya masa keya har da turo dankwali gaba. Zahraddeen sai ya sandare a tsaye, daidai sanda Inna ta shigo tana cewa, "Bani hanya in wuce ka tokare min a bakin kofa". Ya ba ta hanya ta wuce, amma hankalinshi na kan Anisa wadda ta sauko Baby tasa mata feeder a baki, nan da nan ta kama ta yi shiru tana ajiyar zuciya. An ce mai Da wawa......sai ya ce, "Inna ina Maman Daddy ne? Lagos zan wuce yanzun nan sai sun kwana biyu zan dawo". Ya fadi yana kallon Anisa wadda ke ta baiwa Baby madara ba ta ko kara bi ta kanshi ba. Shi kuma so yake su hada ido ya kara gasgata wannan kallon ko in kula din da ya gani cikin kwayar idanunta, amma ta ki dagowa. Sai dai fa da za ka tona zuciyar Anisa a wannan lokacin, ta fi duhun dare duhu, da jin cewa mijinta Dini zai tafi, wanda take gani ta ji dadi, ya yi mata tsawa ta yi kukan dadi, ba kukan bakin ciki ba. Kawai sai ga hawaye suna biyo fararen kuncinta suna sauka a fuskar Baby. Inna ba ta gani ba, amma shi ya gani. Sai ya ta'allaka zubar hawayen da tozarcin da yai mata jiya a gaban kishiyarta. Sai ya ji ransa babu dadi, tunda ga shi ita hakan bai sa ta yi fushi da jininsa ba (Baby), ga shi nan tana ta rainonta. Marwah ta fito daure da tawul mai fadi, ta kuma rufo wani a kanta, gashin kanta na digar da ruwa tana tsaneshi da wani karamin tawul din dake hannunta. Suka yi magana cikin harshen Turanci ba tare da sun karbi 'yar daga hannun Anisa ba, suka shiga uwar dakin Inna inda ta kwana. Doguwar riga ta fara sakawa sannan ta janyo manyan jakunkunansu ta zuge ta soma ware mishi kayan da zai tafi dasu tana shiryawa a jakar da babu komai. Zahraddeen ya matso jikinta sosai cikin murya mai rauni ya ce, "Yaushe zan zo in ta fi daku?" Ta ce, "Ka yi hakuri Abban Daddy mu yi ko da wata guda ne Baby ta yi kwari". Ya ce, "Tab! Kema wasa kike, sai kun ganni kawai". Ya kwantar da kai a bayanta, "Marwah kiss me plzzz...." Ai kuwa ta soma manna mishi deep-kisses a goshi, idanu da karan hancin sa. Ta dire a bakinsa. Anan ne Zahraddeen din ya kankameta. Daidai lokacin da Anisa ta sawo kai rungume da Baby da ta yi barci don ta kwantar da ita cikin net dinta. Zahraddeen ya tafi da yawa fiye da Maman Daddyn, wadda ita ce ke aikin ladan. Don haka bai san da shigowar Anisa ba, don a lokacin ma kalaman da yake furtawa matarsa cikin turanci bai san su ba. Saura kadan ta saki jaririyar a kasa, ta juya da sauri cikin gigicewa ta dangwarawa Inna jaririyar a bayanta. Inna dake durkushe tana hadawa Daddy tapioca ta yi maza ta rike jaririyar saura kadan ta fado daga bayanta. Ta ce, " subhanallahi. Ke kam ban san yaushe za ki yi hankali ba". Ta so ta baiwa Inna amsa ko don Zahraddeen ya jiyo, sai kuma ta fasa, a sabili da sabon kudurinta na yakice Zahraddeen daga zuciyarta ko tana so ko ba ta so. Don haka ba ta ga me ya yi mata zafi da rayuwarshi ba. Sai ta shige kicin don ta yi kalaci, ta debi soyayyar Agada (plantain) mai yawa, da soyayyen dankalin Turawa, da kunun alkama, ta ja kujera ta zauna ta sa musu ido. Ga mamakinta duk da yunwar da take masifar ji ta kasa cin ko loma daya. Sai ta sa kanta cikin cinyoyinta ta fashe da kuka Karfe takwas da rabi Zahraddeen ya yi musu sallama zai wuce, bayan ya barwa Inna komai da za a nema. Tuni ya yiwa jaririyarshi huduba da sunan Inna. Inna har kukan dadi ta yi tana shi masa albarka. Daddy na ta kuka sai ya bishi. Yau ma kamar kullum kalaman nan ya gaya masa, wadanda inda sabo to yaron ya saba jinsu daga bakin mahaifin nasa. "I'm bery sorry my darling Daddy, I'll be back to you soon......" Da kyar Inna ta rike shi yana kuka yana birgima kamar ransa zai fita.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull