Baccin so complete by m shakur - Chapter 10
Baccin so complete by m shakur Chapter 10: Baccin so complete by m shakur Chapter 10. Tayi bacci sosai maybe harda magungunan datakesha wuraren 6 na yamma…
3,807 words
Tayi bacci sosai maybe harda magungunan datakesha wuraren 6 na yamma ta farka yana bude idanu ahankali har idanunta suka budu tarrr shiru tayi tana kallon kofa Ammi take tunawa da Miemie she's really really missing Ammie da batamasan yaya zatayi ba saita tashi zaune da tana kallon kofa Ammi ta tuna tana wani nishi sama sama tana tunanin one of the measure thing dabata iyaba is expressing abu rashin iyawan da bata iyaba saisa duk lokacin da abu yataso mata saidai kanta yadinga mata kaman zai fashe tarasa sukuni tana numfashi wani iri, she feels suffocated acikin dakin nan, mikewa tayi tana tafiya wajen kofa tanaji kaman ana rike mata numfashi da wuya ta taba kofan saitai knocking kofan bakinta na furta Ammi ahankali, buga kofan tafarayi Ammi Ammi, saita shiga jijjiga kofan tana bugawa da karfin gaske kaman zata balla kofan daidai wata nurse tazo zata wuce jin yanda take buga kofan saita tsaya ta kalli room number saitace "stop banging kofan man haka you are disturbing other patients" Amirah taki denawa hakan yasa tashiga bude kofan tana budewa Amirah tazo zata fito nurse din tace "ina zak?" Ihu Amirah ta kurma ta turata saita shiga tafiya nurse din na danna wani bell Amirah tashiga tafiya da sauri kanta akasa hannunta daya takai baki tana ciza tana fadin Ammi murya kasa kasa kana ga gashinta na lilo, Iyawo ne tasha gabanta tace "ina zaki" tsayawa Amirah tayi jikinta nawani kalan bari saita kurma ihuu patients dake lobby duk aka juyo Amirah tawani juya ta kwasa da gudu Iyawo tabita, hanyar kofa data gani dake kai mutane compound tayi daidai zata fita Saleem na kokarin shigowa Iyawo na biyota Amirah na ihu tana gudu towards him gashinta nawani irin lilo kirjinta na bouncing sosai dudda free kaya ke jikinta amman kana gani, numfashin Saleem tsayawa yayi chak yanajin wasu kwari masu danyi dake motsi na yawo acikinsa ganin fuskanta ko kadan Amirah ma bata lurada shi ba she's just running screaming tana waigawa baya tana kallon Iyawo dake biyota da gudu ga all patients na wajen dake sanye da uniform sun taso ana dariya ana ihu harda clapping abunka da mahaukata Saleem ya tsaya chak gaban kofan bai koyi motsi ba yanaji numfashinsa na neman fita daga kirjinsa cus he just realize he's inlove with this mad girl dako sunanta bai sani ba! Daidai Amirah na taka lace na canvas dake kafanta tai wani gaba zatai tumble tafadi Saleem yataho da sauri dan yakamata yana gab da isowa aka bude kofan wani daki dake next to door din Marwan yafito da hannu daya ya tallabota tafado jikinsa gabaki daya chak Saleem ya tsaya Amirah tawani irin kankame Marwan tana manna kanta a kirjinsa sosai tasa hannayenta biyu ta rirrike lab coat nasa tana wani irin numfashi sama sama bakinta na kiran Ammi Ammi Ammi saikuma ahankali kafafunta suka lankwashe tasume ajikinsa!.
GUYS WHAT IS HAPPENING?
WANI SADAUKARWA YAFI SALEEM YASA AN KWANTAR DASHI A ASIBITI SABIDA KAWAI YASAMU YAGA AMIRAH!
MARWAN IS JUST BEING A DOCTOR!
A GANINKU WAYAFI DACEWA DA AMIRAH CIKINSU??? EPISODE 1️⃣8️⃣
Dawani kalan sauri Saleem yazo wajen yaduka yana kallon yanda take a sume jikin Marwan kirjinsa kawai yaji yanamai kaman yakama da wuta, duk yanda yaso ya danne yakasa baimasan ya akayi ba kawai yaga yamika hannunsa yakai zai tabata more like yataya Marwan riketa wani tsawa Marwan yadakamai da saida lobby gabaki daya ya amsa. "Do not touch her!" Jikake tsit kaman anyi ruwa an dauke, Marwan nayin maganan yatashi tsaf rikeda ita kaman yarike yar paper, Saleem yaci abu yatabamai zuciya yakalli chocholate dinta that was on the floor awajen saiyakai hannunsa ahankali yadauka zuciyansa kawai sai bugawa yake ba kakkautawa kafin yatashi tsaye, saiya wuce yatafi hanyar dayaga Marwan yabi. Bude dakinta Marwan yayi ya kwantar da ita akan gadon, she just had a panic attack, he felt bad somehow he felt responsible cus dazu yamata ihu da fada, saiya tsaya yadafe karfen gadon, she needs her mother, saiya dauki bottle water dake wajen yabude ruwan kadan yadeba ya yayyafa akan fuskanta ahankali Amirah tashiga bude idanunta tana kalle kalle, kafin tadaura manyan idanunta akansa suka hada idanu dasauri tawani lumshe idanu tai lamooo, she seems very scared dudda bawai ya nuna a fuskanta bane, but he could see it, cikin sanyin murya yar karama cike da lallashi yace "I am sorry!" Yana kallonta still bata bude idanunta ba, kaman yanama yar yarinya magana yace "namiki ihu dazu ko?" Gyadamai kai tayi alamu eh ahankali kaman yar karaman yarinya, Marwan yace "bazan karaba toh sit up" tasowa Amirah tayi ahankali tana bude idanunta kadan kadan tadan kallesa saitakai hannunta baki tazauna, Marwan yace "zan kawo miki Ammi gobe okay"? Gyadamai kai tayi saita daga hannunta dayan ta kalla chocholate nata take nema, saita juya ta kakkalli gadon Marwan na kallonta dasauri ta sauka daga gadon tamike taduka Marwan yace "me kike nema?" Shiru tayi batai magana ba, saita mike tajuyo ta tsaya dab dashi agabansa takai duka hannayenta bakinta, Marwan dake kallonta sosai yace "me kikeso"? Hannunta dayan taciro daga bakinta sai kawai takai aljihun lab coat nasa tasa aciki na side Marwan dake kallonta yace "you want chocholate"? Gyadamai kai tayi kanta akasa, yace "abinda kike nema kenan?" Gyadamai kai tayi, ahankali yace "okay muje nabaki" sai yayi gaba yabude kofan ya tsaya jikin kofa yace "muje" ita tafara fita daga dakin, tana fitowa taga Saleem tsaye a corridor rike da chocholate yana kalle kalle daga gani kasan dakin nata yake nema chak ya tsaya ganinta tafito kanta akasa kaman bata gansa ba daidai nan Marwan yafito kallo daya yama Saleem yadauke kai saiya tsaya agaban Amirah da kanta ke kasa, Saleem yataho da sauri harwani leka Amirah dake bayan Marwan yake yayi murmushi tsabagen how nervous he's yace "Hello Pretty girl!" Maheer jiyayi kaman ya watsamai barkono a zuciya, one thing with Saleem he's straight forward baida gulma ko munafinci, he's straightforward, saiya wani leko bayan Marwan dan yaganta da kyau, dawani irin sauri Amirah ta manna fuskanta a bayan Marwan tasa hannunta tana kama masa rigansa kaman taga dodo, da kyar Marwan ya iya daidaita muryansa yace "can you stop this Saleem"? Saleem yadan dawo baya yakalli Marwan ido cikin ido yace "stop what?" Dannewa Marwan yakarayi calmly yace "stop scaring her, she's uncomfortable" tabe baki Saleem yayi yadaga chocolate na hannunsa yace "I'm here to give her this chocholate" dasauri Amirah ta dago kanta saita leko ganin chocholate nata ne a hannunsa saita fito tasa hannunta akan chocholate din zata amshe Saleem yarike yamata wani cute smile cikeda kauna yace "Hey my name is Saleem ni yayan this your Dr ne Marwan, I'm his bro…." Wucewa kawai Marwan yayi fuuu duk yanda yaso yadaure ya tsaya yakasa jiyayi kaman zai kama da wuta, yanada wani irin zuciya sometimes mara kyau, Amirah tadago kanta dasauri takalli Marwan daya wuce jin yawuce, this is the second time Saleem ke ganin kwayan idanunta, tunda yake aduniya baitaba ganin yarinya that is as fine as this girl ba, sannan takeda shiga rai kaman new born baby ba, sakinmai chocholate din tayi saita bi Marwan da sauri sauri gudu gudu Saleem yajuyo yana kallonta batama iya sauri da gudu ba and she has shape what! Marwan na fitowa lobby yasa male nurse a maida kowani patient ward nasa, yasa Umma ta maida Amirah daki dudda yana gani tana kokarin zuwa wajensu but yaki ganinta kawai ransa yabaci yawuce yashiga wani ward abinsa yayi banza da ita. Wuraren magrib yasa akaimata magani da abinci lafiyaye yawuce yatafi batare daya ganta ko yaje yaga Saleem ba. **
Ammi na zaune bayan sallan isha'i tabuga taguma tai shiru daga ita har Yaya babu wanda yasami Daddy dan wayansa a kashe har lokacin, Miemie tai girki takawo mata amman takasa ci, saida yayi parking a compound dinsu sannan yayi jimmm batare daya fito daga motan ba saiya kalli folder nata dake dayan seat din yakai hannu yadauka ahankali yabude yayi shiru yana kallon details na next of kin nata da details na mother wanda duk info daya ne awajen Zainabu Auwalu same phone number wayansa yadauka saiya kwashi number yasa ya ijiye folder gefe yayi shiru, contacting family patients is a normal thing a asibitin mahaukata da akeyi dan tambayoyi kam patient da sauransu amman baitaba yo dakansa ba receptionist ake sawa suyi aikin but baisan mesa shiyakeso yayi na Amirah da kansa ba, they is this urge dayake feeling na he wants her to get better he believe he can help her get better he knows it she's to young and too innocent tafara suffering from all this matsala at a young age haka, jiyan zuciya yasauke sai yayi dialing number yasa wayan a kunne Ammi na zaune wayan yafara ringing dasauri tasa hannu tadauki wayan dan taja expecting wayan Yayanta amman saitaga number da bata sani ba kaman bazata dauka ba saikuma tadauka takai wayan kunne ahankali da muryanta da duk ya shake sabida kuka tace "Assalamu Alaykum" Shiru Marwan yayi kaman mai nazarin muryanta saiya amsa sallaman anatse yace "ahmmm kece mahaifiyar Ameenah?"Wani zabura Ammi tayi tamike tsaye dasauri Mimie tamike itama tana kallon Ammi, Ammi tace "eh eh nice nice, kaga diyata ne? Nemanta mike tun jiya? Waye Kai bawan Allah? Kagan mini Amirah na ne?" Muryan Ammi yakoma karami cus she was getting emotional calmly Marwan yace "sunana Dr Marwan and your Daughter na asibitin mu I called to tell you inason ganinki gobe by 10"hawaye Ammi tagoge tace "Alhamdulillah, Alhamdulillah Doctor lafiyanta kalau ko? Gani nan zuwa ma yanzu basai gobe ba wani asibiti ne" Dan bata dauki muryan Marwan bama, a nutse yace "kokinje yanzu baza'a barki ki shiga ba dan ba'a zuwa da daddare, and Ameenah is fine, just come tomorrow general asibiti ne but asalin ward din psychiatric zakizo building dinmu daban da general" Ammi tana goge kwalla tace "Doctor nagode nagode daka kirani ka sanar dani inda Amirah take, kaine Dr damuka ganinrannan nan ko"? Ahankali Marwan yace "uhn" Ammi tace "nagode nagode nagode" katse wayan Marwan yayi kawai yana sauke ijiyan zuciya yayi shiru sannan yabude mota yafita yana tafiya ahankali. Yana bude kofa yaga wutan falon akashe ahankali yakai hannu ya kunna wutan falon "suprise!" Akai ihu yaga anyi decorating falon sosai ga Mami, ga Farida da Faiza, saikuma gawasu mata guda uku wanda duk manya ne Ya Ammah, Ya Maryam da Ya Fadila, kap gabaki dayansu suna kama, kana ganinsu kasan yayyinsa ne especially Fadila wanda ita Marwan kebi tabasa 2yrs, ita ke rike da cake da akwai candles na 34yrs ajiki, suka hau waka. "Happy birthday to you, Happy Birthday to you Happy birthday, happy birthday to Marwan, happy birthday kid bro" kansa yadan shafakai cikeda takaici zai juya Ya Fadila tace "zai gudu" dasauri Ya Ammah tazo ta jawosa tace "zan cimaka mutunci fa Marwan" kaman zaiyi kuka yadan kalli Mami dake dariya na manya tana kallonsu yace "Mami" Mami tace "don't call me, kasan how long they've been planning this? Kowacce tazo gidan nan sabida kai kana wani Mami awajen, menene problem dinka da birthday naka"? Ya Maryam tace "zaunar dashi Ya Ammah ya hura candles nasa" zaunar dashi Ya Ammah tayi tana karban folder hannunsa da labcoat, tace "Faiza take this folder to your Uncle's room" dasauri Faiza ta amsa tawuce sama, Ya Fadila takawo cake din tana murmushi sosai tace "Happy Birthday Kiddo" wani kallo yamata yace "waye Kiddo"? Ya Maryam wacce Fadila ke bi tace "kahura candle kadena wahalar damu" Mami ya kalla gyadamai kai tayi alamun yayi, baiyi musu ba, ahankali ya hura candle din, sukahau tafi, Ya Fadila ta lakato icing sugar ta shafa masa a fuska tana dariya, Marwan yace "Mami" zuwa wajen Mami tayi kaman zata mata fada sai itama ta lakata ta shafa mai a kumatu tace "happy birthday Son, Allah maka albarka" saita mannamai kiss a goshi, lumshe idanu yayi, Ya Ammah ta rungumesa tace "I love my only brother" Ya Maryam itama ta zauna tace "I love him even more, Faiza kumana hoto" dasauri Marwan ya yunkura zai tashi suka rikesa, Ya Fadila tace "Wlh saika dauki hoto" yahade fuska twins na dariya suka mummusu hotuna, Ya Ammah takama fuskansa tace "smile dan Baby this is what you get idan all yayyinka mata ne" kaman zaiyi kuka yamike zai wuce Fadila tai hugging nashi tace "tsaya kaji ina zaka sabida kai aka hada meeting dinnan fa" dan tsayawa yayi ya kalleta yace "meeting na mene"? Mami ganin yagaji and tasan bazasu barsa yahuta ba tace "sai gobe za'ayi go and get changed yanzu ka sauko let's do dinner" dan kallonsu yayi duk suna kallonsa, understanding mata is so hard yakasa gane anything, sai kawai yajuya yana magana kasa kasa yace "why do i have to be their younger brother not elder please, i hate this!" Ya Maryam tace "Allah ne yakeso yakama ka kuma ba yanda zakayi"bai kara magana ba yawuce abinsa. Ya Ammah wacce kebin Mami tace "but how's the girl like Mami?" Duk Mami suke cemata kap dinsu, Ya Maryam tace "banson yarinya mara tarbiya fa wacce zatazo tarabamu da kanninmu, we raised kaninmu together zumuncin mu is thriving so she has to be good and from a good home" ahankali Mami tace "kawai namai sha'awabta ne, tanada hankali sosai, ga kirki, she called me jiya taji ya kafan nawa, kawai ni namai kwadayin yarinyar sabida nasan baida budurwa, kuma naga itama sai Satan kallonsa take, zanso ahada bikinsa dana Saleem suyi aure, he's 34 why is he still single yakamata yanada yara by now"Ya Ammah tace "ai haka likitoci suke wlh idan bamu tsaya akansa ba auren ma bazaiyi ba dayayi aure zaiyi gwara yaje yakaro course kan wani abu daban karatun likitoci baya taba karewa fa aduniya" duk sukai dariya, Fadila tamike tace "lemme go and bring him down". EPISODE 1️⃣9️⃣
Sama Ya Fadila tawuce knocking dakinsa tayi batare data bude ta shiga ba, he might be kanninsu but all of them even Mami wacce take matsayin mamansa da mamansu duka respect him, sabida Marwan nada natsuwa, da hankali, they all play and crack jokes but they respect his privacy sosai, sake knocking tayi tace "idan bakace na shigo ba Allah zan shigo abu…" bude kofan Marwan yayi yana sanye da 3qauater wando na common flag dawani dari green sleeve daya kamasa hakan yasa muscles dinsa suka bayyana na hannunsa a mummurde yama baza kamshi da farin glasses din a idanunsa yahade fuska sosai itama Fadila tahade fuska tana kallonsa tace "wai sabida kaga kafimu girma shine you are feeling kaman kaine babba" hararanta yayi kawai yajuya baiyi magana ba, shigowa dakin tayi tanabin ko'ina da kallo dakinsa kamshi sosai everywhere looks clean tawuce bakin gadonsa ta zauna shikuma tana kallon wani English novel dake wajen babba masu irin thousand plus pages dinan mai suna love wreck, tadauka tabude tana murmushi tace "you book warm" Marwan ya wuce closet nasa dan Saleem ya hargitsamai kaya aikin yakeyi, ahankali Fadila tamaida novel din ta ijiye tanabin ko'ina da kallo tace "Doc kasan mene"? Shiru yamata still hakan yasa tamike tashigo closet din ta tsaye gefensa tana kallon yanda yake arranging kayansa tace "Mami wants that girl for you" dan tsayawa yayi chak saiya juyo ya kalleta looking very confuse yace "which girl?" Ya Fadila tace "wacce ta taimaketa a airport" dan gajeren tsaki yayi yajuya yacigaba da abinda yakeyi bai magana ba, sai Fadila tazo gaban closet din ta tsaya gabansa tana kallonsa sosai, ahankali yace "what?" Hannu tasa ta karbi hannunsa tarike cikeda dan damuwa tace "Marwannnnnn" dan rage murya tayi tace "please get married kaji kodan hankalin mu ya kwanta gabaki daya, kagama school you are doing well for yourself, to what is stopping you from getting married? Kobakayi dan mu ba do it for Mami kaji, you know batason takuraka tana sonka da yawa amman batada burin daya wuce kai aure kasami yarinya daga gidan arziki ka aura kaji" shiru yayi baice komiba, Fadila tace "Kanada anyone yet dakakeso tunda bakason wacce Mami keso"? Ahankali yawuce yana tattara kayan laundry kaman bazaiyi magana ba yace "I don't know" dasauri Ya Fadila tace "I don't know? What does I don't know mean? Is that a yes ko no" saitai shiru kaman mai tunani saita zaro idanu tace "akwai wacce kakeso amman baka riga kafada mata ba kenan Marwan is that abinda kake nufi"? Wucewa yayi yashiga restroom abinsa Fadila tai wani tsalle tace "yesss, yessss" saita wuce tabar closet din dasauri tasauka kasa. Around 9 ya sauko yau duk agaidan Mami yau yayyinsa suka kwana, kitchen yawuce yasami Mami na bama Faiza cereal tace "morning Best Uncle" kanta yashafa yace "how are you" tace "fine" ta karbi cereal tafita yace "Mami ina kwana" Mami tace "nace maka we have meeting yau ina zaka kuma"? Ahankali yace "I have patients now anjima idan zaku fara calll me zan dawo" dan jim Mami tayi saita gyadamai kai tace "muje kai breakfast toh" dasauri yace "Mami nadawo zanyi I don't want to eat this early, or pack for me" yayi magana tuna Amirah dayayi…..
Wuraren 10 yakai asibitin parking yayi yafito as usual yana tafiya a nutse dayake yau Friday, wani soft yadi ne ajikinsa dark blue anyi wani simple karamin aiki a wuyan Ya Rabbi yayi wani irin kyau kaman ango, baisa hulaba gashin kansa sun kwanta suna kyalli glasses na idanunsa sunmai kyau, hardly yake rike kulan amman yau yadauki kulan abincin da Mami tasamai da kansa yawuce ciki yana shiga reception yaga Ammi zaune da hijabi har kasa tareda wata yarinya da kusan kansu daya da Amirah zamatafi Amirah kiba saidai Amirah tafisu haske sosai but suna kama tana sanye da black hijab, yana ganinta yagane itane Miemie da Amirah ta rubuta, tunda ya shigo reception din Miemie takafesa da idanu tunda take arayuwanta bata taba ganin namiji kyakkyawa dan gayu irinsa ba ba lab coat ajikinsa so he doesn't look like a Dr, yana shigowa reception din yadauki kamshi, kallo daya yama Ammi yaganeta batama ganesa ba saiya taho wajen kai tsaye alamun mutum na zuwa towards them yasa Ammi tadago kai itama bata ganesa ba danba lab coat a idanunsa amman glasses na idanunsa yasa tadan dauki fuskan tamike da sauri tace "Doctor ina kwanan mu" anatse Marwan yace "Assalamu Alaykum, ina kwana Ammi" ahankali Ammi tace "lafiya lau" ta taba Miemie dake kallonsa tace "baki iya gaisuwa ba" dasauri Miemie tace "ina kwana" Gyadamata kai yayi batare daya amsa koya kalleta ba yajuya yace "let's go" dasauri Ammi tace "to" suka bisa abaya har zuwa office nasa Ammi sai kallon wajen take yanda wajen yakeda kyau kaman ba'a Nigeria ba ga patients da uniform suna breakfast mai kyau shayi da bread da egg, ga ma'aikata ana kula dasu, suna ganin Marwan suka fara ihu. "Dr M good morning" hannu yadaga musu yace "morning friends" yabude office ya shiga yace "bismillah" shigowa su Ammi sukayi suka yanuna musu couch Ammi gabanta faduwa kawai yake ta kosa taga Amirah, labcoat dake hanger Marwan yadauka yasaka tareda daukan sthethoscope nasa yace "bari nakawota" Ammi tace "tom" yawuce yafita Miemie tabisa da kallo Ammi ta daka mata duka tace "baki taba ganin likita namiji bane kike binsa da idanu haka" dasauri Miemie tace "Ammi wlh bantaba ganin Dr dan gayu kyakkyawa kaman balarabe ga charisma irinsa ba, Ammi inama ya auri ya Amirah, yaransu will be very fine" Baki Ammi tabude tana kallon Miemie, sai kawai takai hannu ta dan bugi bakinta tace "shirmammiya yimin shiru" Miemie tadan turo baki bata kara magana ba. Ahankali yabude kofan dakin Amirah na zaune bakin gado an gyara dakin tsaf Umma na tareda ita tayi wanka ta chanza uniform Umma na bata abincin data kawo mata taki karba yana bude kofa Amirah tajuyo da sauri ta kallesa sabida kamshin dataji, yana sanye da lab coat baisa botura ba kana ganin blue yadi dake jikinsa wani irin sanyi Amirah taji da batasan sanda tadaga hannunta takai baki ba tana bitting nails nata kafafunta farare tasss dan ba'a Riga an maida mata black sock dinba, Umma tace "barka da zuwa Doctor" karasowa wajen yayi anatse yace "sannu da aiki Umma"Umma tace "takicin abincin" hannunsa yamika yadauki chat na Amirah yana dubawa dan yaga abubuwan da nurses sukai logging in yace "barta zaki iya tafiya" wucewa Umma tayi ta bar dakik yana tsaye wajen yana duba chat nata Amirah da hannunta ke baki tasake dago kanta kaman yar Baby ta kallesa wlh yamata kyau genunaa da sajensa akwance suna shinning yana kamshi sosai wani irin haske taji azuciyanta tareda sanyi juyowa Marwan yayi yadaura kwayan idanunsa cikin nata wani kalan kwarewa tayi da tari sabida tsabagen sanyin dataji sabida yanda ya kalleta cire idanunta tayi tana tarin maida folder yayi yarufe saiya taho ya tsaya gaban gadon daidai tarin na tsayawa hannunsa yasa yadauki black sock dinta dake gefen gadon batare daya kalleta ba yace "baki iya gaisuwa ba sai kallon mutane" dayan hannunta takai tasa abakin tahada duka biyun ko tadanji dama daman abinda takeji cikin yar karaman very tiny bedroom voice din tace "ina kwana" "how are you Ameenah?" Ya amsa da very husky manly voice yana kallon fuskanta ganin wani katon pimple guda daya daya fito mata a kumatu wanda babushi jiya yana gani yasan kuma na menene, shiru tayi takasa magana, saiya sa mata safa a kafa without touching her skin juyowa tayi ta kallesa dukawa yayi saiya dauki canvas nata ya zazzage datti dake ciki yashiga samata yana kulle igiyan yasa mata Second one din saiya mike yakalleta dasauri tadena kallonsa yace "kinaso kiga Ammin ki?" Dasauri tajuyo ta kallesa lumshe idanu yayi yabude yace "let's go" dasauri tawani sauko daga gadon jikinta har wani tsuma yake dudda fuskanta is normal ba farin ciki nor bakin ciki saiya juya yayi gaba tabisa da sauri yabude kofa yajuyo yana jiranta danya lura bata iya tafiya da sauri ba ficewa tayi yafito yarufe kofan yawuce tana biye dashi har zuwa office nasa, bude kofan yayi Ammi tamike dasauri hakama Miemie Marwan ya matsa yana kallon Amirah yamata alamu data shiga dawani irin sauri ta shiga ganin Ammin wani tsuma jikinta yafara kaman tai shekara bataga Mamanta ba kawai saita wani irin kwasa da gudu tai wani tsalle kaman yarinya tawani rungume Ammi ta kankame Ammi gamgam tana manna fuskanta sosai a kirjin Ammi kaman zatasha nono, batace anything but kalan hugging Mamanta datayi says morethan enough, she misses mahaifiyarta, kankameta Ammi tayi idanunta na ciko da hawaye sosai duk yanda Ammi taso kartai kuka amman takasa sai hawaye tana shafa bayanta tace "Amirahhhhh" Miemie ta share hawaye tana kallonsu she's so happy taga sister ta, Marwan yadade yana kallonsu dazai shigo office dinne amman saiya maida musu kofan yarufe yawuce they need the time. EPISODE 2️⃣0️⃣