Kenza eBookz

Baccin so complete by m shakur - Chapter 9

Baccin so complete by m shakur - Chapter 9

Baccin so complete by m shakur Chapter 9: Baccin so complete by m shakur Chapter 9. ** Wuraren 1:30PM Saleem yashiga bude idanu shima sabida knocking kofan…

4,427 words

** Wuraren 1:30PM Saleem yashiga bude idanu shima sabida knocking kofan dakin da Mami tazo tanayi da kanta ne, "Saleem maza atashi lokacin sallan zuhur yayi" da kyar kaman zaiyi ihu ya juya, sai kawai Mami tashigo dakin labulen windows daki tabude dakin yayi haske abinda baiso kenan yabude idanu yatashi zaune kaman zai mata kuka yace "Mamsssss" dakuwa Mami tamai tace "wuce kaje kayi salla Saleem kafito ina jiranka magana zamuyi" dan kallonta yayi kadan saiya tashi ahankali yawuce bayi Mami tawuce tafita daga dakin. Wanka yayi yafito da gangan yakara shiga closet na Marwan yanabin kananun kayansa da kallo, they're to decent for his liking hakanan dai yazaro wani Zara jean blue da farin shirt na H&M yasaka, yadauki p-cap yarike a hannu yafito yana baza kamshi saiya shimfida dadduma yayi salla yawuce gadon yadauki wayansa yana dubawa miss calls ne dayawa kuma duk na abokan sa ne, message din David yaduba a watsapp yace "Johnson street" yasan abinda abin ke nufi hakan yasa yawuce yafita daga dakin tundaga staircase yake kwalama Mami kira. "Mams, Mams" Mami dake kitchen tare da masu aiki tace "oh ni jama'a Saleem gani nan fa" fitowa tayi daga kitchen takallesa tace "zokai breakfast" baiyi musu ba yawuce yazauna kan dinning wayansa na ringing yasa a kunne yana magana Mami na zubamasa abinci, fried rice tasamai da tea da kaji sauke wayan yayi daga kunnensa yace "you are the best cook Mams" zuwa bayansa Mami tayi kai tsaye yaji hannunta akan kunnuwansa dasauri yakalleta Mami tahararesa tace "kace wani abu wlh saina rankwashi kanka bani dan kunnen nan, ko su Faiza naba suna sawa zaka sami lada, these don't belong a kunnenka eh Saleem" yanajin nauyin Mami sosai sama da yayan nasa ma, cire an kunnayen tayi takai hannunta ta kwance sarkan shima ta cire kaman zaiyi kuka yace "Mamssssss" zama kusada shi tayi ta tsaresa da kallo tace "Saleem!" Kin magana yayi yaturo baki yana jan abincinsa yafara ci, Mami ta tsaresa da kallo, tace "Saleem wai bakaga mutuwa ake ba yau mune gobe bamu bane, menene amfanin muna sabama Allah da gangan with the little time we have left? Kayi islamiyya kayi boko, d same school dakayi shi Marwan yayi, amman baka aiki da abinda aka koyar daku a islamiyya, we all love you so much we want the best for you mesa kake haka"? Muryan Mami yadanyi sanyi, saiyadan kalleta yace "Mami don't do the sad voice here please just tell me mekikeso"? Shiru Mami tayi tana nazarinsa, all magananganunn data gamayi ko tabasa basuyi ba wlh kawai dan muryan data chanza ne bai so Abinci ma yakeci abinsa, ahankali Mami tace "aure nakeso kayi Saleem!" Ruwa yakai bakinsa amman saida ya kware yahau tari yana buga kirjinsa yakalli Mami yace "wait wat? Mams mene? Aure? Me?"Ya yunkura zai mike Mami takamasa ta zaunar tace "zauna ban gama magana dakai ba" kaman zaiyi kuka mata dan jiransa ake yace "Mamii please jirana akeyi fa"Mami tace "fitanma saina hanaka" dasauri yace "woh woh woh nooo Mams please my friends are waiting for me" Mami tace "inaso kafito da mata kai aure kaji Saleem" dan dariya yayi yace "seriously Mami"? Sai yayi dariya daya lobar da dimples nasa ciki yace "Mami I hate marriage aure damuwa ne please banso there's nothing a aure" Mami tace "okay shikenan zanko bar yayanka ya auro maka kowace mata ne yaga dama" zaro idanu Saleem yayi yace "wat? Mams what's going on"? Cikeda hikima Mami tace "yayanka yace zai samo kowa yaga dama yamaka aure, it took me the whole night to convince him karya maka haka ya banni nizan maka magana kafito da wacce kakeso da kanka dan zamanın nan ba'a yima yaro auren dole saisa na kiraka ina maka maganan amman tunda nima baka daukeni serious ba zan barsa yamaka kome yaga dama" dasauri Saleem yace "no no nooo Mams please, you know how that old man can be trouble ni zaije ya zaboma mata yanda yake jik haushin nan nawama ai wata chan zai dauko a kauye ya auromin"Mami tace "ashe kasan yayanka" dan shiru Saleem yayi yarasa mezaice, Mami ahankali tace "baka da budurwa duk yammatan ka Saleem" wata yar dariyan iskanci yayi Mami batasan tsakaninsa da su ci bane kawai yace "banda shi" Mami tace "to kafara nema zan rokesa na lallabasa yabaka nan da one month" Shiru yayi baitaba sanin zancen aure can make kansa yaji yayi so blank ba sai kawai ya gyadama Mami kai daidai ana sake kiransa yamike da sauri yace "bye Mami I'm taking your car keys" yadauki key motanta yafice harda dan gudu Mami tabisa sa kallo tana karamai addu'an shiriya.

Motan Mami yashiga duk iskancinsa hakanan yana tsoron Abba yayomai aure dan yasan karamin aikin yayansa ne wlh ayanda yakejin haushin nan nasa, shi kawai akyalesa abarsa yayi rayuwansa abinsa, taka motan yayi da gudu dan sauri yake he needs to make a quick stop before yaje wajensu David…..

Takai kusan 30min ahaka sai tadago ta kalli paper drawing din, saiya dauki pencil tashiga zane, tanatayi ita kadai, Malaman su ne tazo wajen ta tsaya takalli abinda Amirah ke zanawa saitai jim saita wuce cus zata iyama Amirah magana taki cigaba, chan saiga Marwan yataho wajen, kamshinsa kawai Amirah taji saita dakatar da abinda takeyi takai pencil din ahankali bakinta batare data dago kanta ba, kirjinta sai bugawa yake, tahowa yayi wajen kai tsaye yasa hannu yadauki paper datai zane aciki yakai one minute yana kallon abinda ta zana saiya nannade yarike a hannu yace "let's go" dasauri Amirah ta tashi sai yayi gaba tana binsa abaya da sauri kanta akasa da pencil da hannu duka abakinta tana binsa yabude office nasa yajuyo kalleta yace "shiga ki zauna ki jirani" shiga tayi ahankali ta tsaya yace "zauna" zama tayi sannan yakulle kofan yawuce……

Saleem bai tsaya ko'inaba sai hospital din su Marwan yawuce yayi parking yanadan gajeren tsaki cus he hates coming to the hospital it always remind him of sanda Babansu ya rasu he dies in the hospital, parking yayi yaciro wayansa yanabin wakan dake tashi a motan na Akon yayi dialing number Marwan yanasa wayan a speaker amman harta gama ringing bai dagaba he knew this might happen sai kawai ya kashe wakan yabude motan yafito yawuce ciki yana zuba kamshi yashiga cikin psychiatric ward din yana tafiya da dan sauri, yawanci nurses ne wajen direct hanyar office na Marwan yayi kai tsaye yabude office din yashiga yana maida kofan yarufe daidai yaji ana rike masa gefen riga gam dawani irin sauri yajuyo yakalli side nasa adan firgice, Amirah ce gefen kofan kanta akasa hannayenta na baki da pencil dayan hannun kuma ta rike masa gefen rigansa dashi, ga pink lips dinta dake motsi sosai tana kallon kasa, at first ya bala'in tsorata daga shigansa office out of nowhere wata tarike masa riga saura kadan yayi ihu cus yadauka aljana ce, but sai baiyiba ya tsare fuskanta da kallo especially long eye lashes nata dasuke nan kaman tai fixing da giranta dayake aciki dan idanunta na kasa da pink lips nata dan karami irin na jarirai, ga gashi a goshinta a kwance lublub kaman buzuwa, dan dukawa Saleem yayi yawani leka fuskan Amirah daidai tana tauna fingers nata suka hada idanu, idanuwanta kaman an wanke da madara sabida tsabagen haske baisan sanda gabansa yawani kalan fadi ba rassss! Amirah tadan dakatar da bitting fingers dinta datakeyi ganin fuskan wani daban daba Dr ba but he smells exactly like him dan turaren Marwan Saleem yasaka yafito abinsa, ahankali tasaki gefen rigansa while Saleem cikin wannan care free attitude din nasa yamata wani irin murmushi dayasa dimples dinsa suka lotsa sosai so deep yace "Hi, Hey, Hello Pretty!" Runtse idanunta Amirah tayi da sauri gabanta na faduwa muryansa zaki and so husky saita shiga komawa baya idanunta a kulle ganin wanda bata saniba at all, daidai ana bude kofan office din dawani irin sauri akuma tsorace Amirah ta juyo tana bude idanunta Marwan ne ya shigo da lab coat a jikinsa stethoscope a hannunsa dan wani patient dake having seizure yaje yaduba, ganin Saleem a office nasa yana kallon Amirah da batada wani tazara dashi sosai saiya tsaya chak itakuma Amirah data rude saitayo kansa kaman zata fado kansa looking confuse, cikin very harsh tone ganin zata shiga jikinsa yace "ke!" Tsayawa Amirah tayi chak amman dab dashi har iskan numfashin datakeyi yanaji akan fuskansa, hannunta daya na bakinta saitakai na biyun shima tasa a duka bakinta tana taunawa nervously, Saleem dake binta da kallo bayako kyafta idanu yace "wowwwww!" Cus tayimai wani irin bala'in kyau, yazuba hannu a aljihun wandonsa yana kallonta ko kadan Marwan bai kalli Saleem ba amman yaji yanda Saleem ke kallonta and yaji yanda yafurta wow, wani abu kawai yaji yayi brushing mind nasa sai ya matsa gefe yana kallonta yabude kofa murya ciki ciki yace "let's go" sum sum sum duka hannun nata na baki tawuce tafita, Marwan yajuya batare daya kallesa ba yace "ina zuwa" baima jira amsan Saleem ba yafice tareda rufo kofan. EPISODE 1️⃣7️⃣

Amirah na tsaye gefen kofan yarufe yafito kawai yawuce yafara tafiya baima kulata ba Amirah tana binsa kaman bindi da sauri sauri dan dasauri yake tafiya, one step nasa shine like 2steps nata, kuma ba ahaka yasaba tafiya da ita ba ahankali yake tafiya but yau dasauri yakeyi har zuwa dakinta, yabude ya tsaya gefe batare daya shiga ba yakalleta yace "get in" zuwa tayi ahankali ta shiga hannayenta na baki, sai yashigo direct ya dauki maganin ta na rana yabata, batai musu ba dan taga kaman he's angry ta amsa ruwan,ahankali yace "open" bude bakin tayi yazuba ta hadiye da kyar tanashan tuwa, saiyadan kalleta ko kadan batason magani yace "haaa" bude bakin tayi yaduba, yace "stay here, ina zuwa" yajuya zai wuce dawani sauri Amirah ta taso. "I said stay here!" Marwan yadaka mata tsawa da batasan sanda takoma gado da sauri saitama kwanta agadon ahankali ta runtse idanunta takai hannunta baki dasauri tanasha tana numfashi da sauri sauri, Marwan yayi shiru baiji dadin yanda yamata ihu ba at all, but hakanan har cikin ransa baiso Saleem yaganta, there's nothing arayuwansa dazai taba iyama Saleem shamaki but wannan yarinyar sai yaji kawai he doesn't want her in Saleem's space sabida yasan waye Saleem, lumshe idanu yayi yabude saiya juya yayi wajen kofan yabude yafito yamaida yarufe yadan tsaya yayi jinmm saiya shiga tafiya, yana fitowa daga corridor saiyaga Saleem tsaye gaban office dinsa yana kallonsa yanadan murmushi ga waya a hannunsa yanajan gemunsa da dayan hannunsa, Marwan yakarasa wajen yace "why are you here? I'm very busy with patients" bude office nasa Saleem yayi yakoma ciki direct yaje yazauna kan kujeran Dr yayi wani rotating akai Marwan na shigowa yamaida kofan yarufe yana kallonsa sai bai kara magana ba yawuce fridge din yabude yadauki karamin bottle water yadawo yazauna yabude yakai baki yadan kurba Saleem yace "I want your ATM card" kallonsa Marwan yayi wani mugun kallo ma, Saleem yace "kadaisan I'm broke ko kuma bazan iya karban kudi a hannun Mami ba ko dan haka kabani kati nawuce" kai tsaye Marwan yace "anki abayar din kudina bana zuwa club bane"kai tsaye Saleem yace "why am I even wasting my time asking you" drawer table din yajawo yadauki wallet din Marwan, black card dinsa yazara yamike tsaye ya ijiye car key Mami yadauki na Marwan yace "Mami's car sucks ba waka so ama use your own" yazagayo yawuce yayi kofa yana nunamai card yace "t for thanks, I know the pin don't worry" yasa hannu zai bude kofan gently Marwan yace "Saleem must you club? Can't you go just a day without clubbing? What is fun in shaye shaye and the rest? Do you know how many patients are in this facility sabida shaye shaye ya juyar musu dakai"? Dan shiruuuu Saleem yayi sai yajuyo dasauri yadawo cikin office din yajawo kujera yazauna gaban Marwan dake kallonsa yace "actually kasan wani abu little brother"?Marwan yayi shiru yana kallonsa baice komiba, Saleem yace "admit me to this hospital" wani kallo Marwan yamasa Saleem yace "yesss I mean it, listen I'm adicted to shaye shaye zuwa club u know girls" yadan kannemai idanu alamun sex, yace "amman kaga idan kai admitting dina i will be here bazan dinga zuwa ba with 1,2 ko 3weeks maybe na manta da shaye shaye duk kuhuta da wahala ta, the old man shima yadena fushi dani right, yadena rashin lafiya, problem fix, so admit me" yamikama Marwan hannu yace "samin drip do your Doctor thing" dan shiru Marwan yayi sai yace "do you think this is funny kai komi saika maida wasa and fun"? Dasauri Saleem yace "do you think wasa nake? Dude I want to be admitted here, this is me willingly nake baka kaina kai admitting dina ka mannani bangaren yan shaye shaye you guys should help me cus ni on my own can't help my self, so help me help myself little brother Dr Marwan"Marwan yayi shiru yana kallonsa shima Saleem yana kallonsa, Saleem yace "bazakai magana ba?" Lumshe idanu Marwan yayi yabude yace "why here? I can take you to another hospital?" Kai tsaye Saleem yace "kanada wata budurwa anan ne dakake tsoron karna kwace maka?!" Wani mugun kallo Marwan yamasa, Saleem yayi wani cute smile yace "just joking, I know bakada shi, and you know me I'm not a rapist ko wani monster I will never attempt to touch or sleep with any patient naka that's idan ma abinda kake tsoro kenan ko koyama patients naka bad abu, no Marwan I will never do that so feel free wait one minutes"Marwan yaki magana still kawai kallonsa yake, wayansa Saleem yadaga, Marwan duk na kallonsa daddanna wayan yayi sai wayan yashiga ringing Marwan baisan wayake kiraba chan aka daga wayan ba'ai magana ba Saleem yadan shafa kai yana murmushi kasa kasa yace "Hi Yays" cikin fushi Abba yace "ka kara kirana da sunan nan saina cikama mutunci Saleem" murmushi yayi yace "Yaya nifa ba kira nayi muyi fada ba I call you to say sorry saikuma ammm" Abba yace "ina jinka saikuma me"? Dan gyaran murya yayi yace "Abba inaso Marwan yayi admitting dina a hospital nasu ne, kawai nazauna nai dogon tunani nima inaso na chanza dabi'una, shaye shaye na yayi yawa so inaso a kwantar dani naga professional, nayi undergoing therapy bayan kwanaki dazaisa na mance da shaye shaye Yaya, I need help I can't do it alone"shiru Abba yayi sai chan muryansa asanyaye yace "Saleem kaike magana haka da kanka?" Saleem yace "eh Yaya nine"cikin tsananin farin ciki Abba yace "Alhamdulillah, Alhamdulillah" Saleem ya juya idanu cikide iskanci yanadan tabe baki, Abba yace "bari nakira Marwan din da kaina naji yaya za'ayi abin" Saleem yace "ai gani nan tareda shi Yaya nazo asibitin wajensa" cikeda mamaki Abba yace "da kanka kaje asibitin Saleem"? Saleem yace "eh Yaya I really want to change" Abba farin cikinsa yakasa boyuwa yace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, ba Marwan wayan" zare wayan Saleem yayi yana murmushi yamika ma Marwan dake kallonsa wayan yace "Yaya gasanan, ga Yaya Marwan" yayi maganan haka da gangan sabida ya karbi wayan, ahankali Marwan yasa hannu ya amsa yace "Assalamu Alaykum Abba" Abba yace "wslm Marwan Alhamdulillah Alhamdulillah, banda abinda zan cemaka Marwan sai Allah yamaka Albarka, Allah yatayaka gyara naka, thank you for taking care of dan uwanka, Allah yacigaba da hada kamku kaji, thank you Son, please ku rikesa a asibitin amai abubuwan dake fitar da shaye shaye Allah yasa shiriyan kenan" Saleem dakejin komi ya yatsine fuska abinsa yana juyar da kansa yakalli kofa daidai inda yaga Amirah dazu kamanninta nadawo wa ransa sosai.

Abba yayi sallama da Marwan, Marwan yayi shiru yanadan tunani he doesn't know why but he's not just happy about admitting Saleem dudda idan you look at abin is a good thing, in reality for someone like Saleem to willingly bring himself yace a kwantar dashi abasa taimakon dena shaye shaye, is a good thing and he should be happy but he's not and he's a bit scared kuma yarasa mesa he's feeling that way, yasan Saleem bazai taba attempting iskanci da wata patient nasa ba ko nurses ba, and he's not a rapist, duk Iskancin sa bazai taba shaye shaye a hospital ba to why is he scared? What is he so afraid of instead of him to be happy Saleem yace ayi admitting nasa? Yasake tambayan kansa amman yarasa amsa, tashi yayi saiya wuce kan kujeransa yabude wani file yazaro wata paper yamikama Saleem yace "I need you to feel in this form but akwai something da I need to tell you before kayi signning in"Saleem ya gyara zama yace "I'm listening Dr" Marwan na kallonsa yace "I will not favor you ko give you special treatment sabida kai dan uwana ne, in this building all my patients are dsame to us" Saleem yace "agreed" Marwan yace "you will not be coming to my office without permission aduk sanda kaga dama unless nina kiraka" Saleem yace "agreed"Marwan yace "current condition naka doesn't required a single private room we will admit you in ward na male patient each ward 10 patients ne awajen akwai 9 already you will be the 10th one" Saleem yace "agreed" dan shiru Marwan yayi yasake tsaresa da idanu akwai something dayakeso ya fahimta ya gano game da Saleem but yakasa ganin komi a fuskan sa, Saleem ne ya yarda easily ya zauna a ward da patient mahaukata dayawa haka ciki?, Marwan yace "patient namu are not allowed to use phone so you will submit your phone along side your flashy items, visitation is 2times a week sai anyi searching guest naka kafin su ganka idan sun kawo abu mara kyau bazasu ganka ba and they will be ban from visisying you ever again"Saleem yace "agreed" Marwan yace "lastly I will not be your Dr, Doctors aren't allowed to treat family so I will be assigning a different Doctor to you" kai tsaye Saleem yace "agreed" Marwan yace "then fill in the form, you will be in this facility har sai sanda muka yarda cewa kabar shaye shaye" murmushi yayi yashiga rubuce rubuce abinsa, Marwan ya tsaresa da idanu bayako kyaftawa daidai wayansa na ringing yadaga wayan ya kalla saiya amsa yanasaka speaker David ne yace "yoh where are you?" Dan shiru Saleem yayi sai chan yace "you know what Abba just sent me to you Cairo I will be there for 2weeks, will call you when I get back, you guys should go ahead without me" baima jira amsan David ba yakatse wayan saiya kashe wayan gabaki daya ya ijiye gaban Marwan yacigaba da filling in form din, yagama tass yayi signning saiya mikama Marwan yace "here" Marwan yasa hannu ya karba yakalli komi saiya kalleshi yace "are you sure you can do this Saleem? Rayuwa in a confined space tare da mutane da basu da lafiya, ba waya ba social media duk wani abu that makes you happy will be on stop this coming weeeks are you sure you can do this?" ahankali Saleem yace "yessss I can" tashi Marwan yayi yace "ina zuwa" yawuce yafita, sake juyowa Saleem yayi yana kallon exact spot da Amirah was standing dazu kafin yamaida idanunsa zuwa gefen rigansa inda tarike da har lokacin yake nuna alamun tamukewa na hannunta, shafa wajen yayi yana mamakin menene dalilin dayake tunanin wacce duka duka yaganta acikin 5secs ne amman shine harya ke commuting kansa in this hospital just sabida yasami access na ya dinga ganinta what is wrong with him? Ya tambayi kansa dan baitaba yin abu kalan haka in his life ba wlh wlh, shifa mata basa gabansa he just like sex dazaran yasami kuma he's s fine saisa ko matan dayakeci ma yawanci karuwai ne yasaka CD yaci yabiyasu yayi gaba no emotions nor feelings attach kawai urge dinsa yake feeding, but yanda yarinyar nan tarikeshi just now da yanda ya duka ya kalli kwayar idanunta daidai tana bude idanunta suka hada ido wani kalan hasken sparks kwayan idanunta sukamai a zuciya har yanzu zuciyansa bugawa yake, bawai yanason yarinyar nan bane, shi he doesn't know but kawai he wants to see her again, her mouth, d way she acts, she looks so adorable and sweet like a baby he just wants to be seeing her koda bazata mai magana ba, shigowa Marwan yayi yakallesa yana maida kofan yarufe amman Saleem bai gansa ba tunani yake tsayawa yayi agabansa rikeda uniform nasa da canvas nasa ijiye kayan yayi akan cinyansa hakan yasa Saleem yayi firgigit ya farga ya kalli kayan da Marwan ya ijiye a gabansa, ahankali Marwan yace "wat is wrong tell me, tunanin me kake"? You can back out idan you don't want to, girgizamai kai Saleem yayi yace "no, I'm just thinking of having one last drink kafin ka kwantar dani" wani kallo Marwan yamasa hakan yasa Saleem ya kwashe da dariya yace "just joking maida wukan" Marwan yace "change I have to check on my patients" gyadamai kai yayi saiya mike Marwan yawuce yana hada file na patients dazai gani Saleem ya chanza tsaf, blue uniform din sunmai kyau sosai sun fito da muscles dinsa da murdadden hannunsa, Marwan yadan sauke ijiyan zuciya yace "let's go" yayi gaba biyosa Saleem yayi suka fito tare yanabin ko'ina da kallo suka wuce asalin ward ga patient dayawa dake falo wasu na games wasu ana basu magana wasu na kallo ga nurses da care takers dake kula dasu, yanzu shine yake willing ya kwantar da kansa a asibitin mahaukata just because he's curious about a particular person dayagani acikin sakan biyar? Is he okay? Kodai yarinyar aljana ce? Why is he doing this to kansa? Ward na maza Marwan yabude patients na wajen na ganinsa sukahau clapping Dr M, Dr M, murmushi Marwan yayi yace "hello boys I have new mate for you" sai sukahau dariyan mahaukata Saleem yana kallonsu gado ya nuna masa yace "come sit" ahankali Saleem yazo yazauna yana kallon mahaukatan dake kallonsa kaman zasu hadiyesa da idanu cikin whispering yace "Marwan must I stay with them what if sukamin wani abu" murmushi yayi yana karban hannunsa dan duba pulse nasa yace "we keep our dangerous patient out of sight anyone you see nan is chill so calm down" Dan ijiyan zuciya yayi yace "where is your Dr he should be here my now"daidai nan wani Dattijo Dr ya shigo ward din, Dr zaikai 40 yazo yace "Hi Dr Marwan Assalamu Alaykum" suka gaisa yace "this must be my new patient" yabude folder Saleem yace "Hello Mr Saleem sunana Dr Dattijo but you can call me Dr D and I handle chronic drug addicts like you"Patient na dakin suka kwashe da dariya Saleem na hade fuska ganin yanda Dr yakirasa da drug addict, Marwan dake kallonsa yahadiye murmushin dayake shirin yi, Dr yace "the boys are laughing sabida duk yan hannu ne suma nan dakin shi ake kira da dakin yan shaye shaye" haba zokaga dariya wajen patients din, Marwan yadanyi murmushi dan yawancin su likitocin mahaukata the reality is suma din mahaukata ne cus they always act like one idan sunason mahaukacin ya fahimcesu, ai treatment na dan shaye shaye shine ka nunamai kama fishi sanin kan shaye shaye, Dr D yace "yau me kasha budemin bakin ka haaaaa" Saleem afusace zai bude baki yayi magana kawai Dr Dattijo ya wangale masa baki unexpectedly yace "good boy haaaaa da kyau nagani" yayi maganan yana leka bakin Saleem daya bude Marwan yajuya yana daura hannu akan bakinsa yayi dan tari na tsabagen dariya dake cinsa, ture Dr Saleem yashiga yi Dr Dattijo yace "no no, no pushing no pushing, do you want me nasa a daddaureka eh handsome boy, be a good boy you are doing a great job, bakin nan yasha shisha, 25% alcahol, wizo da maruwana last night" tsaresa da idanu Saleem yayi jin duka abinda yafadi yashasu jiya Dr D yasake sa sai ya ciro wasu allurai yana injecting a drip yakama hannunsa gaban Saleem yadan fadi shida lafiyansa kalau jibi inda yakawo kansa yanzu me za'a masa kallon Marwan yayi idanunsa Marwan ya kalla kawai yasan he's scared, he don't think tunda suka taso Saleem yataba rashin lafiyan da akai admitting nada a hospital ko drip ba'a taba samai ba, sai yaji yabasa tausayi kuma kaman yafasa kar ayi, ahankali ya matso dab dashi Saleem yadan kallesa anatse Marwan yace "I'm right here and I'm proud of you" tsaresa da idanu Saleem yayi, murya chan kasa Marwan yace "thank you for doing this" lumshe idanu yayi yana samai alluran canula saida aka gama yabude idanunsa, Dr ya saita komi yace "I will be back in the next 30min" Marwan yace "thanks Dr" Saleem ahankali yace "I don't like him" ahankali Saleem yace "he's the best Dr for you trust me" yayi shiru shima Saleem haka, sai ahankali yace "do you really think I can change?" Gyadamai kai Marwan yayi yace "yes" Saleem yace "why? Baka tunanin I will do all this rannan da aka sallameni nacigaba" Shiru Marwan yayi yakallesa sai chan yace "Saleem you're a good person much more than yanda ka dauka, I believe in you shiru Saleem yayi saiya sake lumshe idanu baice komiba, Marwan yace "nurses zasu dinga zuwa suna dubaka idan you need me zaka iya cema any of them su kira maka ni, akwai tendency na treatment dinnan zai dinga saka feeling nuasuw da sauran su don't be scared is a normal think yana flushing toxins daga jikinka ne so akwai da nueasa feeling attach to it, I have other patients zan gansu kafin natafi gıda I will come check on you" ahankali Marwan yace "when is break, As a Muslim lokacin salla you can request for acire maka drip kaje kai salla we have mosque anan cikin lobby, saikuma every inhar babu wani treatment da akeyi 8-9 ana fito da all patient suyi little minor exercise then breakfast therapy class, health education class, piano class etc depend on wanda aka saka you are free to walk around the premises garden as long as lafiyanka kalau"Gyadamata kai yayi Marwan yayi shiru yana kallonsa yace "lemme go" gyadamasa kai yayi tashi Marwan yayi yace "later boys" yawuce yafita Saleem yabusa da kallo.

Baije office nasa ba dakin da Amirah ke ciki yawuce yabude kofan ahankali ayanda ta kwanta dazu ahaka yazo ya sameta amman tayi bacci hulan kanta ya zame gashinta yafitoo tsayawa yayi yana kallonta gabansa kawai yashiga bugawa non stop sai yajuya dasauri yabude kofan yafita daga dakin yarufo mata, yashiga ward.

Readers Also Read