Baccin so complete by m shakur - Chapter 8
Baccin so complete by m shakur Chapter 8: Baccin so complete by m shakur Chapter 8. Batasan metakeba kawai kankamesa sosai Miemie tayi back, Umar yafara…
4,500 words
Batasan metakeba kawai kankamesa sosai Miemie tayi back, Umar yafara patting bayanta yana mata magana a kunne, "Maryam do you also want to loose me too? Cus kukan ki zai iya halakani kinga saiki zama ke kadai aduniya uhn" kankamesa Miemie tayi tana girgiza masa kai, ahankali yace "komi yayi zafi maganinsa Allah, rayuwan nan babu wanda baya cikin wata jarabawa, I just want you kisan cewa Allah baya bacci, ki karfafa imaninki, kome ke damunki ki fuskancesa kiyi addu'a, kima Amirah addu'a wherever she's Allah ya tsareta ya kareta yakuma bata lpy, yadawo da ita lpy, sannan Allah yabama Ammi lafiya, everything is going to be okay I promise you, kinji, I'm right here fa, I will always support you and be there for you no matter what kinji"?Gyadamai kai tayi tanajin wani natsuwa da karfi a zuciyanta, ahankali Umar yace "I love you so much be strong for me okay" gyadamai kai tayi, cirota yayi daga jikinsa saita kasa kallonsa kuma ta sauke kanta kasa shima yatashi yakoma gefenta ya zauna saukai shiru sai chan ya kalleta yace "bari natafi uhm, saida safe tashi ki koma ciki" tashi Miemie tayi da sauri kanta akasa tace "saida safe uhm nagode Ya Umar" tawuce dasauri yabita da kallo yadanyi murmushi dan hug dasukai sharing nadawomai greasy azuciya yashafa kansa yamike ahankali yawuce yahau machine dinsa yabar asibitin. **
Wuraren 10 na safiya Ammi tashiga bude idanunta ahankali, dasauri Miemie dake gwfenta tawani zabura tace "Ammi kin tashi, gani nan Ammi kina ganina"? Bude idanunta Ammi tayi ahankali tana bin ko'ina da kallo kafin tasauke idanunta akan Miemie dake kanta, Miemie tace "Ammi" murya chan kasa mara karfi Ammi tace "ina ne nan Miemie? Meya kawoni nan"? Ahankali Miemie tace "kanki ne yadan fashe tun jiya kike nan" shiru Ammi tayi nan da nan abinda yafaru jiya yadawo mata dawani irin sauri tazabura ta mike zaune zata sauka daga gado Miemie tariketa tace "Ammi tsaya kinji dan Allah" Ammi da zuciyanta yashiga bugawa dumdumdum tace "Miemie ina Amirah? Babanki yasa mazan nan sun tafi da ita?" Ahankali Miemie ta gyadama Ammi kai, gaban Ammi yayi wani mummunan faduwa sai kawai ta kalleta tace "kira Dr a sallameni, bazan iya zaman asibiti bansan wace duniya Amirah take ba, kome zai samen ya samen" gyadama Ammi kai Amirah tayi batare datai gardama ba tawuce tafita takira Dr sai gasu, Dr yace "Hajiya kibari agama miki treatment BP ki is very high maisa kikeso a sallameki" cikin dauriya dan daurewa kawai Ammi take tace "nabar diya mara lafiya agida, lafiyanta shine gabana likita banawa ba" dan Allah ka sallameni sauri nake, ganin yanda Ammi take magana sai kawai Dr yaji tabasa tausayi yace "okay amman ki dinga zuwa duk sayı sati dan mu dinga managing BP naki sannan you need to sign this discharge against medical advice form" gyadamai kai Ammi tayi tai signing komi, Miemie tashiga hada kaya tass Mamie tazira hijabi ance subiya 5k suka biya suka fito Ammi bamatajin karfi jikinta amman tafiya kawai take har titi suka tare keke sai gida.
Shiga gidan sukayi bakowa agidan babu motan Daddy bangaren Maman Baby ma a kulle alamun batanan, Ammi kawai tafiya take tana shiga flat nasu koina tabi da kallo kafin tafada ban daki ta dauro alwala tai sallolin da ake binta dan Allah ne farkı before anything saita shiga kiran Daddy wayansa na ringing baya dagawa, da kyar tasamu akaro na kusan 20th call aka dauka, muryan Maman Baby taji tadauka tace "dan Allah kadauki wayanta kar bakin ciki ya kasheta sweetheart" muryan Daddy Ammi taji yace "tunda kin rokan mata ai hikenan" yasa wayan a kunne yace "yi maganan ki da sauri dan tuki nake Zainabu" dakewa Ammi tayi tana rike abinda ke zuciyanta saita kalli Miemie dake gwfebta tace "bani wuri Miemie ki rufomin kofa"ta ashi Miemie tayi jikinta asanyaye tafita daga dakin tarufo kofa amman saita kasa wucewa ta tsaya tareda jingina kanta jikin kofan.
Da kyar Ammi tadaure tace "Baban Baby ina Amirah?" Wani dan dariyan shakiyanci yayi harda shewa yace "har abada bazaki san inda Amirah takeba idanma abinda yasa kike kirana kenan gwara ki kashe dan bazan gayamiki ba"wani abu Ammi taji yazo mata wuya ahankali tace "Baban Baby dan Allah dan darajan sa, kaduba girman Allah kagayamin inaka kai mini Amirah, karaman yarinya ce dabai kamata tana inda maza sukeba, idan suka keta mata haddi fa, ba hijabi ba takalmi ba hula jikinta, Amirah batasan komi akan rayuwa ba batada wayan kara kanta idan suka mata wani abu fa, katuna akwai Allah yarinyar nan marainiya ce, kafadamin ina ka kaita" tsaki Daddy yaja yace "ai saikuma kiyi keda ganinta har abada dan wlh wlh wlh kinji na rantse miki mahaukaciyan nan bazata kara dawowa cikin gidana ba har abada wlh kuwa ki mutu idan zaki mutu munyi tafiya sai nan da yan kwanaki zamu dawo" ya katse wayan Ammi tace "Baban Baby Babban Baby" tai maza tasake dialing number taji akashe takira Number Maman Baby shima akashe duk dauriya irin na Ammi kawai saitaji kuka yazo mata tafashe da kuka sosai dayasa Miemie tadaura hannunta akan bakinta tana rushewa da kuka itama. Takai morethan 20mins ahaka saita daga wayanta tai dialing wani number ringing daya aka daga wani dattijon namiji ne yace "Zainabu Abu" muryanta adan shake tace "Yaya ina yini" kai tsaye jin muryanta yace "meyasameki muryanki yake haka" ahankali cikin sheshekan kuka tace "Yaya zankai Abban yaran nan kara a police station" one thing he knows about his sister is she's a very very peaceful person ga hakuri hakan yasa yace "Subhanallahi meya faru haka Zainabu? Ina zuwa tsaya nasa kati na kiraki" katse wayan yayi within one minute sai gashi yakira Ammi back tadaga yace "what happened Zainabu? Meya batamiki rai haka dahar zakikai mijinki kara police station eh"? Duk yanda Ammi taso ta daure takasa sai kawai tafashe da kuka tahau gayamai komi tace "idan wani abu yasameta fa? Wlh batada lpy, jikinta zafi kaman wuta, me mukamai ya tsaneta haka? Nagaya maka batun yau ba mutumin nan ba kaunata yakeba gadon yakeso yaci yasa ya aureni sabida komi yadawo hannunsa, zan kaisa kara yafito min da yata yasakeni yabata gadonta mubarmai gidansa"anatse Yaya yace "Zainabu inaso kibani hankalinki nan, first of all nasan duk bakin hali irin nasa bazai kai Zainabu inda za'a kasheta ba wani asibitin dai zai kaita bazai tabar barma gardawan nan yarki ba ko yaje ya zubar da ita kasan gada ko kan bola zan kirasa nayi magana dashi" cikin kuka Ammi tace "ko ka kira baraka samesa ba yayi tafiya yakashe wayansa Yaya, ni ta Amirah nake kabarni na kaisa police station"ahankali Yaya yace "Zainabu kome zamuyi aduniya dole fa zamu dinga sara muna duban bakin gatari, ni da ke munci zamanin mu kome zamuyi yanzu a matsayin mu na iyaye yaran damuka haifa zamu dinga kallo, Alhamdulillah diyarki daya miji yafito ana maganan aurenta nan da yan watanni aji kina case da mahaifinta a police station kin rabu da Babanta ba abin kunya bane, bar wannan gefe kika rabu dashi kinada tabbacin zaki karbe gadon naku? Gadon musulmai fa ba irin na kiristovi bane da ake rubuta will ba tsaf zai iya cewa yabaku kuma ya zauna, ni kina ganin banda wani karfi kika rabu da mahaifinsu kije ina gaki da yara mata dasuka dan tasa daya mai lallura daya lafiya kalau? Eh Zainabu? Lamarin aure hakuri ake wannan shine kalman danasha gayamiki shekara da shekaru wata rana sai labari duk abinda zaman lafiya bai kawoba tashin hankali bazai taba kawosa ba kaisa police station bazai amfaneki da komi ba saidai ya tarwatsa komi naki maybe ma har auren diyarki Maryama haka kikeso" cikin kuka tace "to yazanyi Yaya" cikin muryan lallashi yace "Zainabu hakurin nan kinsha yinsa banso ki gaza, ki daure ko Maryam ne ki zauna ku aurar da ita tare daganan idan abun ba chanji sai asan yanda za'ayi kinji, inaso kibani nan da zuwa dare zan nemesa zamusan inda Amirah take, addu'an mahaifiya bata fadi kasa wlh babu abinda zai samiAmirah sai Alkhairi inhar kin mata addua, everything will be fine Amirah zata dawo wajwnki kinji?Banso kiyi komi kinji, kiyakuri kinji Zainabu na nafa sanki da hakuri ina ke ina zuwa police station dan Allah kiyakuri duk shedan ne kemiki huduba kibani zuwa dare kinji" ahankali tana goge fuska tace "toh naji Yaya nagode" Yaya yace "to zan kara kira anjima" ya katse wayan Ammi tai tagumi saikuma takara fashewa da kuka bata tabajin tanajin bakin ciki da kunci kalan wanda takeji yauba in her life.
Bude kofan Miemie tayi ahankali tashigo tana kallon Ammi data shiga goge fuskanta dasauri ta kakalo murmushi tace "zonan yammata na" tahowa Miemie tayi sai kawai ta zauna gaban Ammi, Ammi ta tsareta da idanu saitakai hannunta kan fuskanta tace "kuka kikayi ko?" Hawayene suka zubo suna sauka tace "Ammi kiyakuri kinji karki sake kuka" rungume ta Ammi tayi tace "maza dena kukan nan banso" dataga yaranta na kunci gwara ita kadai ta shiga, burinta a duniya is to always see yaranta are happy, da kyar tai shiru Ammi tace "a ina kika sami kudin kaini asibiti?" Murya chan kasa tace "Ya Umar ne" tsareta da idanu Ammi tayi hakan yasa tashiga fadama Ammi all abinda yafaru sai kawai ta sauke ijiyan zuciya tace "anjima zaki kirasa saina masa godiya". EPISODE 1️⃣4️⃣
Wuraren 9 nasafe Amirah ke bude idanunta ahankali kadan kadan, jikinta feels so relax, kanta feels so light, wannan rashin dadin da jikinta keyi mata baya mata yau, sake lumshe idanu tayi tabude bakinta yayi motsi murya chan kasa tace "Ammi!" Kaman ta tuna wani abu a firgice ta tashi zaune tanabin ko'ina na dakin da kallo da hannunta da drip ke kai tana tuna duka abinda yafaru da ita cisge kanulan tayi saiga jini ga zafi dataji tahau yarfe hannunta tana goge jinin a riganta ganin yaki dena fita tabarshi tamike tasauka daga gadon kafafunta ba takalmi kafanta fari tasss da dogayen kumbunanta masu kyau, uniform ne ajikinta ko hulan yafita akanta ribon din shima yafita akanta tai wajen kofa datagani, so kawai take ta tafi wajen Ammin ta, saita shiga kokarin bude kofan amman kofan baya buduwa, tahau buga kofan sosai tana girgizawa sai jikinta yafara bari tafara kiran Ammi muryanta kasa kasa tana buga kofan da duka karfinta ga fitsari tanaji sosai rabonta da fitsari tun jiya maybe ma sabida bataci wani abu bane yasama bata fitsari tun jiyan ba. Zuwa wajen kofan Iyawo tayi tabude kafinma takarasa budewa Amirah tabi da gefenta zata wuce dagudu kamata Iyawo tayi ta dagata sama Amirah takwada ihu fitsari na kufce mata, jin fitsari ajikinta yasa Iyawo tasaketa cikeda fada tace "ni kikema fitsari"? Ta dakamata tsawa dayasa Amirah takoma baya dasauri nurses na shigowa su uku, Iyawo tanuna musu jikinta tace "jibi yanda tamin fitsari ajiki? Bari nazo nacire miki kaya namiki wanka" dasauri Amirah tawuce gadon ta kwanta tai lamo kawai tsoron matan take she's so big and strong kuma bataso kowa yamata wanka.
Bude dakin yayi yashigo anatse hannunta da yanda yayi jini yabi drip din da kallo, yanda tajuya tana kallon bangon gadon ta kifa kanta jikin gadon jikinta nadan bari ya kalla, dan gyaran murya yayi duk aka kallesa suna gaidasa anatse yace "what is going on here?" Dasauri Iyawo tace "fada take dani kuma tayi fitsari ajikinta taki bari nacire mata kaya, taki bari natabata kuma takicin abinci" strictly Marwan yace "why will you remove her clothes gaban everyone dake nan, part of your job is to understand the nature na patient and respect his privacy, just because she's like this doesn't mean you should naked her in front of all the nurses" yayi maganan strictly dasauri Iyawao tace "ayakuri Dr"strictly Marwan yace "Excuse me and page Baaba, kuma zaku iya barin dakin" ya sallami all nurses din suka fice daga dakin aka maida kofan aka rufe, ahankali yasa hannu yadauki blanket dinsa dake kasan dakin yamike tsaye yataho gently ya warware yadaura akan jikinta dasauri Amirah takama bargon ta kankame tai lamooo like a helpless orphan, Marwan ya kalleta, ahankali yace "good morning Ameenah!" bugawa kirjinta yayi tai shiru jin yanda yakira sunanta, hannunsa yazuba a aljihun labcoat dinsa yace "kinaso nakawo miki Ammi"? Dawani irin sauri Amirah tajuyo ta tashi zaune tajuyo gabaki daya bawai akwai farin ciki ko murna a fuskanta bane babu kodaya, amman gesture datasa na tashi tazauna datayi means this is the greatest news he has ever given her, saitakai hannunta tasa abakinta tana tauna yan fingers nata tana motsi da fararan kafafunta tar da babu slippers ko safa ajikinsu abakin gadon, ahankali Marwan yazo ya tsaya gaban gadon directly opposite her yana kallonta, bitting fingers nata take sosai, murya chan kasa yace "idan kinaso nakawo miki Ammi akwai rules dazansa miki inhar kinyi zan kawo miki Ammi, kinaso ki ganta"? Dan gyadamai kai kadan tayi tana kallon waje daya tana cizan hannunta, Ya Allah she looks so adorable and charming, yadan sauke gajeren ijiyan zuciya yace "stop fighting my nurses they're all here to take of you, yanzu za'a miki wanka kisa kaya then I will come back muyi maganan"Kaganta this time bazakace da ita ake magana ba daidai Umma ta shigo wata yar dattijuwa ce sanye da uniform na ma'aikata tace "sannu Dr M" Gyadamata kai yayi yace "yauwa Umma, please ki taimaka mata tai wanka ta chanza kayan nan" Umma tace "tom shikenan yammata tashi muje" sai kawai Amirah ta sauko daga gadon ahankali har lokacin hannunta na baki tana cin kumba ga fitsari duk a wandonta tasauke kanta kasa kaman tanadan jin kunya tafiya agabansa ahaka, juyawa Marwan yayi yafita daga dakin batare daya karaba jikinta second look ba cus uniform din sundan kama jikinta shape nata yafito sosai hips dinta da boobs nata, yace "Baaba adinga samata uniform dasuka danfi wannan girma" part of job nasu is protecting features na patients nasu ta yanda suransu bazai wani fito sosai dahar zaisa wani patient ko Dr ko worker yaganka yayi sha'awanka ba,
Wucewa yayi yashiga duba other patients nasa, bayi suka shiga Baaba tahada mata ruwan wanka tace "yauwa zo ayi wankan toh" make mata wuya Amirah tayi saita shiga tafiya ahankali ta duka ta rungume buket din irin kaman kunya takeji, Umma tace "ohh kunya akeji to maza yi wankan, ni bari na gyara gadon" fita Umma tayi hakan yasa Amirah tacire kaya ahankali tashiga watsa ruwan ta shafa sabulu batason soso dama gamawa tayi tadaura towel tafito taga Umma ta ijiye mata uniform tace "masha Allah angama ka kaya saka" daukan kayan Amirah tayi saita kara juyawa takoma bayi tasa kayan tafito tazauna abakin gado tana murza hannunta a cinya Baaba takawo wani black cap tace "a sa wannan ko" takawo tasa mata black cap din aka ta tattare gashinta tasa aciki ahankali sannan tawuce tafita dan dago kanta Amirah tayi tawuce kofa chan sai gasa yazo wajen yarataya sthethoscope a wuyansa hannunsa daya rike da folder da iPad dayan hannun rike da wani small bottle of water da karamin container da kwayoyin magunguna guda biyu rak keciki, ahankali yabude kofan yana kallon gadon baiganta akai ba, lurada mutum dayayi a gefen kofan yasa yajuyo da kansa yakalli gefen kofan tsaye yaganta kanta akasa tana wasa da yatsunta, tundaga kai yake kallonta an samata hula black, zuwa uniform na jikinta yanzu that are a bit free compare to na dazu kafanta ba takalmi ba safa haka take taka tiles din, sosai tashiga murza hannayenta sai kuma tadaga hannu daya takai tasa fingers nata a baki bata dago kanta ba dake kasa, ahankali Marwan yamaida kofan yarufe calmly yace "jeki zauna" juyawa tayi tawuce taje ta zauna abakin gadon like a very obidient girl saiya taho wajen yajawo wata kujera yazauna yana facing nata saiya ijiye bottle of water da container na maganin daidai anyi knocking Umma ce takawo tray na breakfast da akama patients yau tea ne da bread da egg abincin is not bad for government hospital o, hannu yasa ya karba da kansa ya kalli abincin saiya bata yace "take this" kin cire hannunta daga baki Amirah tayi takima kallonsa sai cin yatsu datakeyi tana wasa da kafafunta, he knows bazataci ba bataso, saiya juya yaba Baaba yace "Baaba akwai flask na abinci a office dina za'adan taimakamin dashi" Umma tace "toh Dr"tawuce tafita. Ahankali Marwan yasa hannu a aljihun lab coat nasa saiya ciro leda na new dogon black socks mai dan kauri yabude yacire safan tareda mikemata yace "take put this on a kafanki, always wear sock daga yanzu" left hand nata wanda shine akan cinyanta takai tamikamai still bata kallesa ba, Marwan yace "no bani hannun dama not left" cire hannunta tayi daga bakin tamikamai duk saliva a jiki, tsare hannun yayi da idanu saiya saka hannunsa a aljihun yaciro handkerchief dinsa, ahankali batare da skin na hannunsa yataba fatar hannunta ba yashiga share mata yawun daga hannunta, gently Amirah tadago kanta tadan kallesa da fararen manya manyan idanunta, kawai Ammi ta tuna anytime taba Ammi hannu idan akwai datti ko ruwa ko kasa ko yawu a hannunta sai Ammi tafara sa tsuma ko wani abu ta share hannun tass kafin tabata abinda zata bata, sosai take kallonsa especially glasses dake idanunsa, da lips dinsa dasuke pink yirrr ga kamshi mai bala'in dadi dayakeyi dake kwantar mata da hankali.
Tass Marwan ya goge mata hannun saiya saka safan akai tareda dago kansa karaf hada ido yayi da Amirah dasauri Amirah ta maida kanta kasa abin yadan basa mamaki ganin takallesa, bude safan tayi saita shiga sawa a birkice wajen diddige na saman kafa instead of yazauna a kasa zata saka dayan, cikin tattausan murya Marwan yace "wait!" Tsayawa Amirah tayi batare data kallesa ba, hannunsa biyu yakai kan kafan data saka safan, ahankali yakama fatar safan without touching her sai yayi adjusting ya daidaita safan, kaman yana magana da Baby sabida how soft he's da ita yace "jashi sama toh" ahankali Amirah taja safan sama, Marwan yace "sa dayan" saka dayan tayi same way, yasake gyara mata saiya koma yazauna yabude file nata sai yayi rubutu awani fresh paper, saiya dago yakallate tamaida hannunta baki, a hankali yace "I will ask you some questions inhar kin bani amsa kinyi duk abinda nace baki mana rashin ji ba zan kawo miki Ammi gobe kin yarda zakiyi"? Gydamai kai tayi tana cin hannu tana kallon waje daya, gently yace "stop eating your fingers" ciro da hannun tayi daga baki ta ijiye akan cinyanta, saita shiga ninninke yatsun nata all together Marwan na kallonta saiyayi rubutu ahankali yace "kinsan sunanki"? Gyadamai kai tayi, his eyes fixed on her yace "gayamin sunanki naji" dan bata lokaci tayi kaman mai tunani idan zatai magana murya chan kasa that's very tiny and slow suna kiran term din a psychiatrict world da bedroom voice idan baka natsu bama bazakaji me zatace ba, murya very very kasa Amirah tace "A…..mirah!". EPISODE 1️⃣5️⃣
She speaks very low with a very gentle tone da zaka dauka a year old baby ne tai magana, muryanta bala'in dadi, soft charming and adorable da baby yanda zatai magana da zuciyanka bazai amsa ba, sosai Marwan ke kallonta tai maganan tana wasu wired wasanni da yatsunta bazama kace itane tai magana ba, kaman badaga bakinta maganan yafito ba, rubutu yayi yacigaba da kallon gesture datake making, calmly yace "Amirah sunanki but rannan Ammin ki tafadamin asalin sunanki, kinsan asalin Sunanki?" Shima magana yake mata calmly and very gentle baiso yadaurama kanta abubuwa dayawa, gyadamai kai Amirah tayi alamun eh batare data kallesa ba, Marwan daya kafeta da idanu bayako kyaftawa yace "gayamin, menene asalin sunanki" wannan karan maganan ma fitowa yayi daga bakinta like whispering, kaman irin tafadi ma mutum magana a kunne dinnan, tace "Ameenatu!" Wlh bugawa kirjin Marwan yayi dum! Dan shiru yayi ya lumshe idanu kadan taredakai hannunsa yadaura kan goshinsa sannan yazare tareda bude idanun, why is he feeling like this towards this patient? Yasake dago idanunsa yadaura akan fuskanta yana kallonta, wasa take da hannayenta tanadan motsi da kafafunta suma, dakewa Marwan yayi ya danne duk wani abu da zuciyansa kemai yace "dake da waye da waye agidanku"? Tafin hannunta daya shiga zufa ta share a cinyanta saita daga duka hannunta biyu zatakai baki saita tuna abinda yace dazu yahanata wasa da yatsunta tashiga yi saita kalli gefe kaman bada ita akai magana ba, chan da yar kankanuwan muryan tace "Ammi, Miemie da Amirah ne agidan muuu" taja muu din like a baby tai shiru sai kawai this time takai hannun nata baki tafara ci tana kallon gefe, Marwan ya tsaya yana kallonta kirjinsa na bugawa dum dum dum yana maimaita kalan sigan yanda tajero sunansu Ammi, Miemie da Amirah ne agidan mu, irin yanda yara ke gayamaka waya da waye gidansu dinnan sai Marwan yayi circling Babanta cus bata ambato mahaifinta ba, daidai lokacin akai knocking akan shigo Baaba ce da flask dayace takawo mai tace "gashi Dr" nuna mata inda ya ijiye ruwa da magani yayi saita wuce ta ijiye tajuya tafita, sai yadauki wani empty blank paper yarubuta Ameena boldly saiya daga paper yabata yace "take" hannunta datake wasa dashi tazare zata bashi na haggu batare data juyoba saita basa na dama yasa mata takardan ta amshi paper tana kallo yace "mena rubuta anan?" He wants to know idan ta iya karatu koda kadan ne, ahankali Amirah tace "Ameenah" murmushi Marwan yayi yace "good job Ameenah" wani sanyi taji a zuciyanta kaman an goga da kankara yanda yace good job Ameenah, saiya mikamata hannu alamun tabasa yace "kawo" basa tayi ahankali tana kallon agogon hannunsa, saiyasa hannunsa a aljihu yaciro chocolate na cabry diary milk yamika mata yace "that's all for today take your reward" chocholate din ta kalla sai dawani irin sauri tasa hannu ta amshe, zata bude yace "wait, wait kisha magani kici abinci then chocholate" maganin yakawo yana bude ruwa, yawanci su ne suka ba patient magani da kansu a gidan mahaukata wannan ka'ida ne dan patients akwai wayau basashan magani, gently Marwan yace "haaaa" kin bude baki Amirah tayi dan batason magani ko kadan takai hannuwanta biyu tadaura akan fuskanta tarufe, abin yaso basa dariya, saiya mika mata hannu yace "bani chocholate dina tunda bazaki sha magani ba" dasauri tacire hannayenta dake kan fuskanta da chocholate din ke jiki taboye chocholate din abayanta tana makemai kafada batare data kallesa ba, Marwan yamata wani kallon mamaki da ace this girl is very fine kalan tsiwan dazatayi ko, ataushashe kaman mai lallashinta yace "okay tunda bakiso na amsa chocolate din open your mouth kisha magani, ko bakiso nakawo miki Ammi"? Ahankali tabude baki jin maganan Ammi, dan bugawa zuciyansa yayi sabida yanda tabudemai bakinta that is very clean, hakoranta yan kananu with her very pinkish lips and tongue, maganin guda biyu yasamata abaki tareda samata ruwa ta zuka ta hadiye tana lumshe idanu tai ahhhh, ahankali yace "karkimin amai" yadan kalleta to be honest bata iya expressing happiness ko sadness ko tsana ba, she hates magani tasha taji ba dadi but fuskanta is just d way it is, rufe goran ruwan yayi yace "open your mouth nagani cus you patient are kinda sneaky now adays" bude bakinta tayi ya kalla saiya wuce wajen warmer da Mami tabasa abinci saiya bude, chips ne da eggs da pepped chicken and plantain saiyasaka spoon yazo wajen yabata yace "ea…." Kafin yama karasa magana yaga takawo hannunta takarbi kulan hannunta nataba nasa takarba da sauri tadaura akan cinyanta saitasa hannu tafara cin chips din da egg da plantain, tsayawa Marwan yayi yana kallonta saiya sa hannu yadauki bottle water din yabude yazo wajen ya ijiye mata a gefenta, sai kawai yadena kallonta yabude folder yashiga rubuce rubuce saiya rufe yasake kallonta she's still eating comfortably kaman batasan da mutum awajen ba, sai yadan sauke ijiyan zuciya since she's eating today unlike jiya, and yau she's not running temperature, yajuya zaiyi kofa dawani irin sauri Amirah tamike tabiyosa hannunta daya rikeda chocholate dinta dayan rike da kulan abinci gabanta na faduwa hankalinta natashi bataso yabar inda take, dakatawa Marwan yayi ya tsaya jin tabiyosa yajuyo da sauri yakalleta tana tsaya dab dashi kanta akasa ga kulan a hannunta da chocholate, kaman zata shiga jikinsa ayanda take dab dashi yayi dan jim saiya juya yawuce yace "muje kici abinci" juyawa tayi itama sum sum yanuna mata gadon taje ta zauna tasake tacigaba da cin abincin yana tsaye yana kallonta, she has a very very good appetite dudda bada sauri takecin abincin ba but she's eating well, tagama takama naman duk tanaci, abinma dariya yaso basa saiya dauke kai yaciro wayansa yana dannawa dan ita kawai yake jira, kadan tarage a abincin tadauki ruwan tasha ta ijiye saiya dago kansa yakalleta ganin tagama kanta akasa saiya maida wayansa aljihu ya matso dab da gadon yasa hannu yadauki gora sai yarufe ya ijiye a gefe yadauki flask din yakalli dan naman karamin data rage, saiya sa hannu yashiga picking abincin data zuzzubar a gadon, ahankali Amirah tadan dago idanunta ta kallesa yana wani irin sanyi takaraji acikin zuciyanta kaman an zuba kankara, rufe flask din yayi ya ijiye ya kalleta hada idanu sukayi dasauri Amirah tadauke kai, baice mata komiba yawuce wajen bayi dasauri tamike tabiyosa yana bude kofa tabisa yajuyo ya kalleta saiya kunna tap yace "come wash your hand" bude tap yayi saitazo tasa hannunta akasa tana wanke hannunta saita bude baki hakoranta suka fito tai wani clapping hannunta under the running tap ruwan yawani tawarwatsa har fuskan Marwan ya tsareta da idanu ahankali yace "wasa da ruwa nace kiyi" dasauri tajuyo ta kallesa sai takai hannun data wanke zatasa abaki yace "don't, clean your mouth" goge bakinta tayi, yace "wash your hand again" wanke hannun tayi, saiya bude kofa yace "let's go" ahankali tafita yafito shima, wani takalmi canvas ne wanda shine general shoes dasuke bama patient nasu fari ya dauko a drawer dakin, saiya duka ahankali gabanta agaban gadon, Amirah ta kallesa, bude takalmin yayi yace "put your leg" sa kafanta Amirah tayi saiya samata takalmi da kyau ya kulle igiyan sai kallonsa take kanta trying to put things together, he's just like Ammi, he is her second Ammi sabida yanda yake kula da ita, same thing da dayan kafan yayi ya kulle, yakalli hulanta ya zauna akanta sosai, yace "let's go" saukowa tayi yadan tsaya ya kalleta fully kayan looks free ajikinta sai yajuya kawai yawuce yayi kofa tana biye da shi abaya suka fito, lobby yakaita yau drawing a painting ake koya musu, chair yanuna mata yace "sit" zama tayi Malaman na kallonsu da other patients, Malaman takawo mata new board da pen ta ijiye tace "here you go" anatse Marwan yace "I want you to draw anything dakika tuna, stay here I will come back anjima kadan karki biyoni" yafada strictly saiya juya binsa Amirah tayi da kallo zuciyanta yashiga rawa sosai har saida tadaina ganinsa sai kawai takifa kanta a table din tai lamo kaman marainiya tareda lumshe idanu. EPISODE 1️⃣6️⃣