Baccin so complete by m shakur - Chapter 7
Baccin so complete by m shakur Chapter 7: Baccin so complete by m shakur Chapter 7. Daga labulen dakin akayi dasauri security suka juyo suka kalleshi but…
4,382 words
Daga labulen dakin akayi dasauri security suka juyo suka kalleshi but ganin band na hannunsa sai basuce komiba bin mutanen dakin yayi da kallo idanunsa suka sauka kan David a UK suka hadu da yaron a university dsame major David yayi da Saleem Law dasauri yashigo dakin kai tsaye yayi kan David yawani fizgosa yace "where's Saleem?" Dan bude idanunsa kadan yayi yace "restroom" sakinsa yayi batare daya kalli matan dake tsirara awajen ba sukuma sai kallonsa suke ganin hadadden guy ya shigo very class yana kamshi, Marwan yayi wajen door dayana kyautata zaton bayi ne zai shiga bodyguard yatare kofan yace "no one disturbs Sam when he's in cloud X" daidai lokacin kukan macen yakaru gawani kara da kofan yayi kaman yabugata da kofa ne, takaici kaman zai kashe Marwan ga hayakin dake tashi awurin dasuke busawa yadamesa sosai yana clouding glasses dinsa ma dan babu cikakken haske he can't wait yafita daga club din, yadaga murya yace "Saleem, Saleem" cin yarinyar ahaukace Saleem yake but jin yanda aka kira full name dinsa saida yadanyi slowing down cus kap duniya nan yan uwansa ne only family calls his full name Saleem, friends and ko'ina da Sam aka sansa ake kuma kiransa, Marwan yadaga murya yace "Saleem!" Daidai lokacin yagane kowaye ahankali yace "fuck!" Yacigaba abinsa, azuciye Marwan yace "Saleem" bodyguard cikin fushi yace "lower your voice kana damun activity dake going on" azuciye Marwan ya tsaya dab dashi yace "anki ayi lowering mezakayi? Saleem" yasake daga murya with anger, bodyguard din ya matso dab dashi with annoyance daidai ana bude kofan karuwan tazube akasa tsirara ga leda condom da Saleem ya wurga kanta dake zubar da sperm nasa, Saleem yafito yanajan zip na wandonsa yana kallon Marwan dake kallonsa da takaici sosai, with a straight face yataho kai tsaye yadauki glass cup na giya akan table dan yabar dayan a bayi zaikai baki tashi daya Marwan ya fizge cup din yace "you've had enough let's go" dan kallonsa Saleem yayi yakalli cup na giyan dake hannunsa sai yayi murmushi daya bayyanar dawasu cute dimples dake fuskansa dasauka kara mai kyau cikin slow voice dan abuge yake yace "yohhh when did you start drinking"? Ijiye cup din Marwan yayi yakai hannunsa kai tsaye yakama hannunsa yace "let's go" kaman daga sama Bodyguard din yazo azuciye yakai hannunsa zai tura Marwan yace "how dare you touch Sa……" chak yaji anrike masa hannu dasauri yajuyo Saleem ne cikin kakkausan murya yace "did you just try touching my brother"? Duka yazo zai kaimai Marwan yashiga gabansa yace "let's just g…." Kasa karasa maganan yayi sabida tari daya kamasa, hayakin shaye shaye yamai yawa tun yana yaro bayaso hayaki baida athsma but yafara tari nunfashinsa har neman daukewa yake due to smoke, dan kallonsa Saleem yayi ganin yanda yake tari yana kokarin magana ma yakasa Saleem ya tsaya chak yana kallonsa tsaki yayi kawai saiyasa hannunsa shiya fizge Marwan din dake tari suka fice daga wajen yace "ubanme yakawo ka nan wajen when you clearly know this is not your type of environment now look" harsukakai waje tari Marwan yake, wani plastic chair na security dake gaban club din yadauka yakai gefe sannan ya zaunar da Marwan akai dake tare sannan yadan koma baya yayi folding hannayensa a kirji yana kallonsa, ahankali tarin da Marwan yake yasoma raguwa dan hayakin da smell na watever it is dasuke shaye shaye dashi was choking his throat, tsayawa tarin yayi idanunsa sunyi ja, strictly Saleem yace "why are you here?" Mikewa Marwan yayi yakalli inda suke akwai mutane ga bodyguards yace "let's talk in the car" "I'm not going anywhere, why are you here?" Anatse Marwan yace "why didn't you tell me you were in Nigeria?" Dan tsaresa da idanu Saleem yayi saikuma ahankali yace "dole ne saina fada maka inda nake when we clearly live different lives and live in different worlds" Ahankali Marwan yace "I've known your world Saleem dudda I don't live in it, atleast you should have told me ba inda kaje, we are brothers" "we are not brothers!" Saleem yafada azafafe yace "and stay away from me you see what you get just now by coming to inda nake right, don't ever look for me" yawuce zai koma ciki karaf Marwan yarike hannunsa, chak Saleem ya tsaya batare daya juyoba murya chan kasa yace "why are you doing this Saleem? I don't care if you don't take me as your brother I take you as one and you will always be one, and I will never leave you alone ko stop coming to look for you or stop trying to change you and make you a better person than you are now just like d way I've always done tun muna yara har mukaje university" Marwan yadanyi shiru ahankali yace "Abba almost had a stroke yau he fainted is BP is not doing good please come back home" Kin magana Saleem yayi sai Marwan yasaki hannunsa yazagayo ta gabansa ya kalli fuskansa yace "family is everything not club not club mate, all this are worldly thing, do you want to loose the only person daya rage maka a duniya?" Saleem yadade yana kallon kwayar idanunsa sannan yace "do you really think I care?" Marwan yayi shiru yana kallonsa Saleem yace "as long as mahaifina da mahaifiyata sun rasu kowama yarasu I don't care the world doesn't stop for no one, mutumin dayasa akai freezing account dina" Saleem yadanyi murmushi yace "dude that old nigga just turned me into a broke ass nigga ko biyar banda ita shine kuma you want me to go back home inmai uban mene ya mutu mana saime waye bazai mutu ba, dalla ka kyaleni zan koma cikin club" yawuce ciki abinsa Marwan na kiransa Saleem Saleem kaman badashi akeba, Marwan ya tsaya yayi shiru kobadan maganan Abba ba is high time someone step up gadangadan and save Saleem and Saleem is super stubborn da maganganu hardly pierce iron heart dinsa so he also needs to act stubborn, hannunsa yakalla har lokacin yanada tag kawai saiya wuce yashiga ciki ba'a hanasa ba yawuce saman batare daya kalli kowa ba Saleem harya zauna yaga Marwan yashigo takaici yakamasa zaiyi magana saiya fasa yaja pipe na shisha yanasha yana busarwa azuciye ta hanci da baki, Marwan yasami waje yazauna bangare daya wata karuwa tazo zata zauna kusa dashi yamata wani kallo takoma dasauri yadanyi tari kadan dan hayakin yafara damunsa amman yaki tashi Saleem ya lumshe idanu yana shan shisha mata biyu sukahau jikinsa suna shafasa ko ina, dayan na murza dick dinsa ta saman wando normally anamai haka yana jin dadi sosai amman Marwan dukya lalatamai mood babu abinda yakeji gashi sai tari yake every tari dayakeyi yanajinsa har kasan ransa amman yadake yanaso yagaji da tarin yawuce yafita da kansa yatafi.
Tarin dayakeyi is not normal is like he's allergic to some substances dasuke smoking cus lungs dinsa were getting very tight yanaji, tari tari tari yafara kowa na dakin yajuyo yana kallonsa banda Saleem daya lumshe idanu but yadena shan shishan, chan Marwan yayi wani irin nishi kaman zaiyi amai yana fadowa daga kujeran bude idanunsa dasauri Saleem yayi yawani irin jefar da shishan dake hannunsa yataho da gudu baima tsaya wani abu ba dagasa yayi yakamasa bodyguard yatayasa suka fice har waje, Saleem yataba aljihunsa yana zaro key mota ya danna yana waige waige baiga motan daya kawoba kuma shi a motan David yazo dan baida ma kudin fuel body guard dake wajen ne yace "abakin titi chan yayi parking" kallon fuskansa Saleem yayi yace "seriously! What a stingy nigga, 1m dinne bazaka iya biya a club ba"? suka shiga tafiya zuwa chan bakin titi Saleem yaga motan suka bude gaba suka sashi Saleem ya tsaya yana kallonsa a sume yake tarin ya tsaya but idanunsa a lumshe glasses dinsa ya zazzago, hannu yasa yazare glasses din ya ijiye gefensa ya tsare fuskansa da kallo yace "look at who come to get me da just hayakin shisha ya bugar dashi haka, Lazy weak ass nigga" yakama seat belt yasamai kawai ya rufe motan yazagaya ta dayan bangaren yashiga yazauna yarufe kofan ya kunna motan yana kokarin sa waka motan Mami ba waka yawani daki sitare yace "what kind of car is this" wayansa yadauka yayi connecting to motan yayi wani blasting waka ya kure volume sannan yaja motan da mahaukacin gudu yanabin wakan a buge yake fa but yasaba da shaye shaye da komin yanda yabugu idan yanaso yayi abu yana iyayi.
Karan uban music yasa Marwan yashiga motsi ahankali saiya bude idanunsa dishi dishi yake ganin yashiga motsi hakan yasa Saleem yajuyo yakallesa yasa hannu yadauki glasses nasa yamika masa yace "Hey blindy have your glasses" hannu Marwan ya mika masa saitin inda yake ganin dishi dishin hannunsa, amman ba direction din bane, cire hannunsa Saleem yayi a sitari yajuyo yakama hannunsa yasamai glasses din, dasauri Marwan yasaka a idanunsa yakai hannunsa ya kashe music din dan kunnensa kaman zasu fita, Saleem yace "wlh ko ka barmin wakana kona fasa komawa gidan" yasa hannu ya kunna music din back, Marwan kawai ya kallesa da takaici ya kyalesa, Saleem yanabin waka yana rawa yana tuki, da ace Marwan matroracine da sai yayi kuka sabida matsiyacin tukin da Saleem keyi haka cikin ikon Allah suka kawo gida.
Yawani danna mahaukacin horn Marwan yasauka zai bude gate amman gateman Musa harya fara budewa yasa masa hannu suka bude tare Saleem yayi ciki da motan wuraren 1:30 nadare, Mami da Abba na zaune a falon daganan sunajin kidan motan, maida gate sukayi suka rufe, Saleem yakashe motan yasauko abinsa yadan bi jikinsa da kallo 3 quarter ne ajikinsa da bakar singlet da sarka da dan kunne, Marwan yazo yadan kallesa saiya zare t shirt na jikinsa ya mika masa yace "put this on" cikeda Iskanci Saleem yace "why? Kana tsoro bakaso nai breaking heart din Abbanka?" Yana maganan yawuce abinsa yabar Marwan da riga a hannunsa maida rigan Marwan yayi yasaka yabi bayansa su Mami na zaune aka bude kofa Saleem yafara shigowa Marwan biye dashi Abba yabi Saleem da kallo tundaga kan wani dundumemen canvas dake kafansa da gajeren wando crazy ayayyage dawani shegen dan iskan singeleti da sarka a wuyansa da dan kunne, Saleem yakalli Mami da itama ke kallonsa jikinta ba karfi yace "Hi Mams" Mami tama kasa magana jikinta yayi la'asar wlh ganin Saleem yakoma gogaggen maraji, Abba yamike cikeda fada yanuna Saleem from head to toe yace "what is this Saleem? What is this? Me wannan a wuyanka? Mace kakeso ka koma? Kasan cewa Allah ya tsinewa namiji maisa kayan mata? Meya hadaka da sarka da dankunne, jibi yanda kake warin giya eh Saleem?" Irin yanda niggas ke behaving yawani bude hannu yajuyo yakalli Marwan dake bayansa yace "yooo! You see why I don't wanna come back, you see now"? Cikin tsananin fushi da bacin rai Abba yawani fizgosa ya juyo dashi yace "ba magana nake maka ba wai kana dan musulmi gaba da baya kake shiga haka kaman kafiri?" Cikeda takaici Saleem yace "yooh wai menene aibun dressing dina Yays eh" Wlh wlh Abba try his best to control his anger amman yakasa wai wato Yaya ne ma Yays yanzu, hannu yadaga a fusace zai dauramai mari dasauri Marwan yashiga gabansa Marin yasauka akan gefen wuyansa da side na kunnensa, Saleem ya kalli Marwan idanunsa sunyi ja Mami tace "Alhaji dan Allah calm down ba'a gyara kuskure da fushi" takalli Saleem tace "kuwuce kuje ku kwanta Saleem gobe zamuyi magana" wucewa azuciye Saleem yayi yace "okay Mams" Marwan yabi bayansa, sukai sama instead of Saleem yashiga dakinsa dake gaban na Marwan kawai yabude na Marwan ya shiga Marwan yayi dan jimm saiya shigo baice komiba, yamaida kofan tarufe Saleem yashiga cire kayan jikinsa yana jefarwa duk inda yaga dama yarage dagashi sai boxer yafada bayi, dukawa Marwan yayi ya kwashe kayan nasa tass dake wari shaye shaye ya tattara yakai Landry basket yazuba sannan yawuce yafita daga dakin koda yakoma kasa su Mami basanan anma kashe wuta sunje sun kwanta kitchen ya shiga yahada lemon tea yana warware hangover nasu giya da shaye shaye, sai yayi frying egg guda 4 Yayi toasting bread yadauki karamin bottle water duka yahada a tray sannan yakashe komi yafito yataho sama har dakinsa yabude kofa har lokacin wanka yake normally yana dadewa a bayi, ijiyemai abincin yayi kan study desk dinsa inda ka top nasa yake da folders daya kawo daga hospital na patient, ya ijiye wani kati na kwayan magani guda daya shima yana kara flushing toxins daga jiki, yadauki pen yarubuta eat and drink this, yakashe wutan dakin ya kunna mai wutan study desk din dake haska abincin sannan yakunna mai wutan closet kafin yajuya yawuce gado ya bala'in gaji ya kwanta yana cire glasses nasa ya ijiye kan side drawer dake gefensa yayi addu'a yashafa ajiki ya kwanta ko 2min ba'a dauka ba yayi bacci dan yagaji sosai lokaci was already 2 nadare. Wuraren 2:15 Saleem yafito ya tsaya yana kallon abincin daya hadamai a study desk yakallesa yana gado yarufa da bargo sai kawai yawuce closet, pajamas dinsa yadauka yasaka yafito ya shinfida dadduma yayi magrib da isha'i yatashi yazauna akan kujera yana kallon rubutun dayamai yakalli kwayar maganin wanda baisan na menene ha amman yabude kawai ya jefa abaki yasha yana daukan tea ya kurba, yadauki spoon yadebi egg yakai baki saiya tsaya yayi wani dan tsuki yana murmushi daya wani irin karamai kyau yace "what a terrible cook" saikuma ahankali yace "is after 2 I'm hungry I have to eat it like that" shaye shaye nasa kaji yunwa, he knows Marwan yasan da hakan saisa ya ijiyemai abinci tass ya cinye komi dan shi yanada cin abinci, yadauki tea yashiga sha idanunsa suka sauka kan folder ahankali yakai hannunsa yace "let's see wani case kebama yaron nan headache cus any folder daya kawo gıda means one thing the case is intriguing and he needs to study more or dig more" yabude file din yanabi da kallo yanashan tea, Aminatu Adamu, born 2004, an kawota akace autism….. saida yabi komi ya karanta down to treatment da Marwan yamata yau zuwa sanin Babanta ne yakawota asibiti she was agrressive ta cije baban"dariya yayi yace "woww wat a fiesty little girl, inason yara haka, aida kin yayyaga old man dinki da kumba, if I ever see you I will tell you how to handle all this trouble some old niggas, mine too is disturbing my life" Yayi maganan yana rufe folder kawai ya ijiye. Yamike tsaye ahankali yayi murmushi yace "Aminatu Adamu Daddy's biter" yadauki wayansa yawuce zuwa gado yahau gadon ahankali harzai kwanta saiya kunna touch nasa ya haska Marwan dake bacci ya kalli wuyansa dayayi ja sai yadanji wani iri yace "bakasan yanzu mun girma ba when will you stop taking beating for me foolish boy, he's just too caring, i thought by now he will realize not everyone deserves it especially me cus gobe still sainaje club" ya kwanta yanandago bargo yarufa sai bacci.
Wuraren 5 Marwan yabude idanu da kyar shima kawai dan jikinsa yariga yasaba da tashi around that time ne for subhi, ahankali yamika hannu yadauki glasses naaa yasaka sannan ya yaye bargo yatashi zaune yana addu'an safiya kafin yamike yawuce yafada bayi saida ya gyara bayin sannan yayi wanka yafito yashiga closet nashi ya shirya yafito cikin wata milk jallabiya yasa faran hula yana kamshi yazo gadon ya bubbuga Salim yace "Saleem, Saleem, Saleem" da kyar Saleem yayi motsi yace "if I have the chance stitches your mouth Marwan" ahankali yace "tashi muje muyi salla saika dawo ka koma bacci, tashi tashi kafin Abba yazo" Sarai yasan yayansa ruwan sanyi zai zuba masa hakan yasa yabude idanu da kyar yaki motsi yace "I can't feel my body" dagasa Marwan yayi yawuce yashiga bayi yadauro alwala yafito jallabiyan Marwan yadauka daga closet yasaka yafito yana hamma ya ballama Marwan harara dake kallonsa yace "mugu" murmushi Marwan yayi suka fito suka wuce mosque.
JAMA'A GA SALEEM GA MARWAN!!!
ME KUKE GANI ZAI FARU??
KUN TABA GANİN KANIN DA SHIKE KULA DA YAYA?
AGANIN KU WA AMIRAH ZATA AURA?? EPISODE 1️⃣2️⃣
Miemie sosai take buga kofa tana kuka sosai tana kwalama Ammi kira amman shiru kuma babu yanda za'ayi ace kap gidan nan ba'aji ihunta ba dan harta window taje ta tsaya tana ihu tana kiran su Maman Baby amman shiru, dasauri tai wajen wayanta dake kan gado tadauka jikinta har rawa yake tashiga dialing number Umar, a ringing na farko bai dagaba ana biyune ya daga, cikin kuka sosai tace "Ya Umar kana ina?" Dadan damuwa yace "menene kike kuka meya sameki? Gani a gareji" cikin kuka Miemie tace "dan Allah kazo gidanmu yanzu ka shigo har side namu" dadan tashin hankali yace "wait why are you crying like this?" Dasauri tace "zan fadamaka kazo kashigo ciki" ahankali yace "ya za'ayi na shigo cikin gidanku babu izini" tasan gaskiya yafada hakan yasa tace "Ammi ta sume ne kuma kanta yabugu ni ina daki a kulle kuma babu kowa dazai budeni nabata taimako you are the only one I could think of, dan Allah kazo Ammi first we will deal with koma menene later" ahankali yace "okay gani nan zuwa" tana tsaye awajen jikinta rawa kawai yake bini bini tana share hawayen dayake saukowa daga idanunta hankalinta atashe batamasan meke mata dadi aduniya ba ina yakai Amirah?
Wani matashin saurayine dazaikai shekaru 30 haka aduniya kakkarfa bafulatani yayi parking Wayyo kudina a kofar gidan yana sanye da kayan gajere dan bakaniken mota ne yaciro wayansa yayi dialing number dayasa my wife ajiki ringing daya Miemie tadaga jin tana kuka har lokacin yace "waiba nace kidena kuka ba, nothing will happen to Ammi, gani awaje" cikin kuka tace "to kashigo flat dinmu ne na karshe ai kasan flat din ko rannan dakuka zo ganin Daddy" ahankali yace "eh nasani" katse wayan yayi ya kalli gate din dudda he's feeling uncomfortable amman haka yabude gate din yashiga luckily babu kowa a tsakar gidan yawuce flat nasu sallama yayi yadaga labule yashiga yana hango Ammi akasa flat ga jini agoshinta daya kumbura yace "Subhanallahi" yayi wajen jin muryansa yasa Miemie ta jijjiga kofan tace "Ya Umar ina nan budeni" kofan ya kalla sai yayi wajen ya murza key dake jikin kofan yabude Miemie data saka hijab dinta har kasa tayi wajen Ammi da gudu tarushe da kuka tana dagota tana jijjigata. "Ammi, Ammi Ammi, Ya Umar Ammi na ta mutu ne"? Dasauri yace "don't say that" yamike cup ja ruwa daya gani akan table yadauka yazo wajen yadan debi kadan ya yayyafa ma Ammi a fuska amman ko gezau batayiba Miemie tarude jijjiga Ammi kawai take kaman mahaukaciya duk takara daburta Ya Umar the only thing dayazo kansa is. "Bari nakira keke mukaita asibiti" Miemie tace "kafadamin gaske ta mutu ko shine bazaka fadamin ba" Ya Umar yace "waiba nace kidena magana hakaba" cikin tashin hankali tace "to maisa bata farfadowa bayan mun watsa mata ruwa inba mutuwa bane, idan Ammi na ta mutu nima saina bita Ya Umar"ganin yanda kaman ta haukace saiya duka kusa da ita abinda baitabayi ba yayi yakai hannunsa yakama kuncinta yace "Maryam put yourself together babu abinda yaşamı Ammi we will take her to hospital dole ke zaki tsaya mata so kudawo hayyacinki kina jina" gyadamai kai tayi yamike dasauri yafita.
Ko 3min bai bataba yadawo suka shigo da keke yabudema Keke gate aka shigo Miemie tasama Ammi hijabi yashigo dakin shida Miemie suka kamata suka fito da ita daidai Maman Baby na zuwa wajen tace "Au karuwanci kika fara kike kiran saurayin naki har gida" dukansu biyu babu wanda yabi ta kanta sukasa Ammi a keke keke yafice Unar ya sauka a waje yahau machine nasa yabisu abaya.
Wani karamin primary health care center sukaje suna zuwa aka karbi Ammi dasauri Miemie tazauna tana kuka shiya biya kudin komi da yan kudaden dayake dashi sannan yadawo yazauna gefenta yayi shiru yana kallonta tabasa tausayi wlh yanason Maryam sosai bata taba fadamai anything akan family ta ba but zaman tare yadan lura da yan abubuwa from rannan dayazo tambayan aurenta Babansu baice komi akan Miemie ba amman yanda yadinga kiran Amirah da mahaukaciya dakuma yanda yadinga kaskantar da Ammi agabansu he knew something is going on just like that yasan Ammi bazata fadi hakaba Miemie kuma a kulleta adaki ba sannan baiga Amira ba, he knows something is going on ahankali yace "Maryam" dago rinannun idanunta tayi tace "uhm" ahankali yace "ina Amirah?" Tsare Umar tayi da kallo wani kuka nataso mata kawai saita shiga rerama Umar kuka tama kasa magana but kukanta said a lot tace "bamusan inda Daddy yakaita ba Ya Umar" yayi shiru saikuma cike da tausayi yace "ya isa stop crying kar zazzabi yakamaki, kika fara zazzabi ina zansa kaina eh kinaso nakasa aiki ne?" Girgizamai kai tayi yace "okay we will do this first thing first, muji da Ammi yanzu dake gabanmu muji ta farfado, tunda Amirah natare da Abba zamu nemeta okay" gyadamasa kai tayi ahankali, yazaro handkerchief mai kyau daga aljihu yabata yace "wipe your friends mujira Dr I'm here for you okay, you are not alone Wifey"wani sanyi Miemie taji aranta Umar nada kirki sosai baida wani kudi tasan kwanan nan he's working times 3 sabida yahada kudin aurensu yana hada akwati akwai dan karamin filin dayake dashi daya daha ginin gadan gadan dan awajen yakeso su zauna gashi duk yakashe kudi anan sai yabata tausayi ahankali tace "nagode Ya Umar Allah kara buda maka" dasauri yace "inhar zaki godemin da gaske godiyan danakeso is kidena kuka sabida dagamin hankali yake" share fuskanta tayi tass yace "to yima mijinki murmushi kadan" murmushi tayi tadanja hijabinta tana boye fuskanta yayi murmushi yace "Alhamdulillah" baison abinda sai taba Miemie ko kadan, suna zaune awajen Dr yafito dasauri Umar yatashi yace "stay here" zama tayi yawuce wajen Dr dasauri, Dr yace "jikinta yahau sosai that's abinda yayi contributing dayasa takasa farfadowa amman she's out of danger mun mata allurai mun dinka mata kan, tana bukatan full circle na sleep so bazata tashi ba sai zuwa gobe da safe zuwa rana haka amman Alhamdulillah no need to worry again" Dasauri Umar yace "Alhamdulillah Alhamdulillah thank you Dr thank you" Dr yace "zaku iya shiga ku ganta yanzu za'a maidata ward"tahowa wajen Miemie yayi data tsaya tana kallonsa murmushin dataga yanayi yadan kwantar mata da hankali yace "Ammi is fine yanzu amman Dr wai yamata alluran bacci sai zuwa gobe zata farfado muje ki ganta zasu maidata ward daga emaergwncy room din" Gyadamai kai tayi tabisa sukaje har ward ne inda kusan patient goma suke kowa akan gadonsa suka gaida mutane sannan sukaje gadon Ammi dake bacci ga drip nabin jikinta da gudu Miemie tawani rungumeta ta kankameta Umar yabita da idanu, da yanada kudi dabazai jira 4 months da aka deba musu ba kawai aurenta zaiyi yahuta da wutan sonta dake damunsa sai yanzu hankalinsa ya kwanta ganin tadena kuka dazu world dinsa was crumbling because of yanda take kuka. Ahankali yazo wajen 10k ya dunkule ya ijiye kusa da ita yace "ga wannan incase wani abu come up, bari nakoma gareji anjima zan dawo da yan abubuwan da kuke bukata" dago kanta tayi takallesa saita gydamai kai akunyace tace "thank you Ya Umar Allah kara budi da arziki" ahankali yace "promise bazaki kara kuka ba" sauke kanta kasa tayi tana wasa da yatsunta ahankali tace "tom" murmushi yayi yace "take care and take care of Ammi bye" yawuce yafita yan ware din na kallonsu machine dinsa yahau yabuga sai gareji.
Miemie na asibitin har magrib ta ari dadduman wacce ke next to bed nasu tai salla har akai isha'i ma haka 8 daidai Umar yayi sallama yashigo Miemie tadan dagokai ta kallesa yana gaida marasa lafiyan yan dakin yana sanye da shadda blue mai kyau yasa hula sai kanshi yake hannunsa duka biyun rike da abubuwa sannan yazo wajen gadon ya ijiye basket din yace "Umma tace akawo miki Allah kara sauki gobe zasuzo dubiya" ya ijiye dayan ledan wanda yan shopping ne yamata, Miemie da kanta ke kasa tace "an gode Allah amfana" zama yayi akujeran daya bata yakalleta yace "bude kula ki debi abinci kici" Dan kallonsa kadan tayi ganin ba wasa fuskansa saita sauka saga bakin gadon tabude kulan dafadukan shinkafa aka dafa musu da nama da zobo mai sanyi tadauki spoon da plate ta deba tadan kalli matan dake bata Aron dadduma ta kusa da su tace "ga abinci muna kwarya" matan tace "ahh Alhamdulillah an gode" dawowa tayi tazauna tafara ci duk kanta akasa Umar sai kallonta yake, haka take ta gansa taita kunya ko yazo zance awaya ne take bude baki tamai magana, today is the first day datake ganinsa in reality tayi magana shima sabida rudewan Ammi ne, cinyewa tayi tasha ruwa sannan ta ijiye plate din, Umar yamike yace "bari naje to gud night akwai sock da zanin gado kisa ki rufa da kyau sabida sauro" gyadamai kai tayi tace "nagode agaida Umma" dan kallonta yayi yace "muje kirakani" akunyace ta sauke kanta kasa wucewa yayi yay gaba sannan tasauka tasa takalmi tafito awaje ta samesa wajen wani bishiya inda akasa kujeran zama haka tawuce wajen tana tafiya ahankali ya tsareta da kallo taje saita zauna amman tabar dan gab between them, sukayi shiru sai chan yace "Maryam" dago kanta tayi takallesa, ahankali yace "how are you?" Tambayan ya sosa zuciyanta sosai baki tabude zatai magana kawai saita daura hannayenta akan fuskanta kaman yar yarinya tafashe da kuka, she just feel alone, she feels ayanzu right in this moment batada kowa sai Umar, ba Ammi ba Amirah, mikewa Umar yayi saiyazo ya tsaya agabanta kafin yaduka gabanta ahankali yace "Miemie is this the promise dakika min? Yakikeso nayi da raina? Do you want to kill me eh Miemie, bakiso na ko?" Girgixamai kai takeyi tana shesheka irin yanda yara sukeyi hancinta harda majina tace "Ya Amirah batada lafiya, bataci abinci ba nasan har yanzu dare yayi bazataci ba tunda bataganmu ba, jikinta was hot, bansan wani hali yar uwata ke ciki ba, Ammi gata itama a hospital banda kowaaa" tana kuka numfashinta har neman daukewa yake Umar baimasan mezaiyiba sai kawai ahankali yajawota for the first time tunda suka san juna yayi hugging nata. EPISODE 1️⃣3️⃣