Baccin so complete by m shakur - Chapter 28
Baccin so complete by m shakur Chapter 28: Baccin so complete by m shakur Chapter 28. Wuraren 12 Amirah tashiga bude idanunta tana bin dakin da kallo kadan…
4,279 words
Wuraren 12 Amirah tashiga bude idanunta tana bin dakin da kallo kadan kadan take bude idanunta kafin ta idasa bude idanunta gabaki daya dan zafi taji a tsakiyan kanta hakan yasa tadaga hannunta takai tsakiyan kanta taji bandage tai shiru saita sake lumshe idanunta sai kawai rayuwanta yashiga dawo mata tun tana yar yarinya da yanda batason mutane da yanda take makale da Ammi da yanda ta tsani Daddy sabida yanda yake dukan Amminta, haduwanta da Marwan da yanda take sonshi da yanda take farin ciki tagansa abinda yamata da daddare komi kawai yashiga dawo mata tanajin wani kalan perfect feeling wanda bata tabaji arayuwanta ba na natsuwa, wajen farinciki she feels it, bakin ciki she feels it, tajaici taji, komi haka, just like that saitaji jikinta da kanta yamata daban da yanda takejin kanta ada dudda bata gane ba amman kaman something in her change sake bude idanunta tayi jin an taba kofa Mami tashigo dasauri tana kallonta tana murmushi tace "Amirah kin tashi?" Gyadamata kai Amirah taso tayi amman kanta zafi dasauri ta yatsine fuska Mami tace "sannu sannu inda kika buge ne sannu kinji, bari nakira Dr adubaki, ance kika tashi zamu iya tafiya but saisun dubaki" dasauri Mami ta danna bell na kiran Dr duk Amirah na kallonta saiga wata mata baturiya Dr tashigo tazo wajen Amirah takama habanta taciro haske tana haska idanun Amirah tace "follow this light"Bin wutan Amirah tayi da kallo, Dr tace "good" takashe wutan tana kama Amirah tace "sit up" tashi Amirah tayi ahankali tazauna, Dr tace "tell me do you feel pains anywhere"? Shiru Amirah tayi tana kallonta kaman mai waswasin magana kawai mamaki take to meke hanata magana ada, Mami zatai magana tacema Dr bata magana sosai ga mamakinta cikin normal kamilallen voice cikin kuma harshen turenci Amirah tace "I just feel pains here I don't know why"Ware idanu Mami tayi tana kallonta cus akwai yanda Amirah ke magana ada her speech is not clear is like a little girls speech tunda tasan Amirah bata tabajin ta tai clear direct speech hakaba, Dr tace "ohh is where you hit your head it will go away soon okay pretty" lumshe idanu Amirah tayi tabude ahankali tace "thank you Dr", Dr takalli Mami dake kallon Amirah batako kyafta idanu tace "you guys can go home she's fine now" gyadamata kai Mami tayi batama kallon fuskan Dr tace "thank you so much Dr" Dr tawuce tafita dasauri Mami tazo kusada ita tana kara kallon fuskanta tace "Amirah na, lafiyanki kalau" Mami ga kalla ahankali tace "Mami kaina namin wani irin kaman bani ba" dasauri Mami tace "Alhamdulillah kaman buge kan dakikayi yaşa kin sami lafiya"tashi muje gida ga kayanan chanza kisaka hijabinki muje, Gyadamata kai Amirah tayi kayan ta kalla saitaji tana kunyan ta chanza kaya gaban Mami kaman yanda take da sai tawuce bayi ahankali take tafiya dan any motsi sa kanta ciwo yake Mami tabita da kallo saikuma tace "Ya Allah kasa lafiyan tasamu kenan mai daurewa daman ance wani abun Alkhairi ne, idan wannan fadan shine sanadin warkewanki Amirah Alhamdulillah Allah mun gode maka" fitowa tayi ta maida rigan baccin tasaka maroon hijabi har kasa mai hula yamata yau sai Mami takama hannunta tace muje, ahankali take tafiya kadan kadan every step tanaji akanta suka fito ga su Ya Ammah dasu Ya Maryam wani kunyansu Amirah taji tanaji saita sauke kanta akasa ahankali tace "ina yininku" ahhh suma mamaki ne yakamsu sunm kasa magan Mami tace "kumuje" suna fita compound na asibitin daidai ℳ𝒶𝓉𝒶𝓇 Marwan na shigowa asibitin shida Abba yayi wanka yana sanye da faran riga kal zai shiga parking space Abba yace "muje gaban reception ka dauki matarka.
Baice komiba yawuce direct wajen duk suna tsaye amman yaki kallon kowa yayi parking wajen tunda motan ke dumfarosu gaban Amirah yashiga faduwa dudda bama tasan waye a motan ba daidai Saleem na fitowa daga asibitin kowa yajuyo yakallesa banda Amirah daidai Abba na fitowa daga motan yace "daughter Amirah wuce mota mijinki na jiranki kutafi gidanku" Saleem ya tsaya chak yakalli Abba dako kallonsa bayayi, jikin Amirah yahau rawa tadan kalli Mami wani irin shakka da tsoron Marwan take azuciyanta sosai, Mami na ganin idanunta tasan tsoron Marwan take ahankali tace "jeki zan aiko miki da wayanki gidan kome yamiki ki kirani ki sanar dani zanzo ja cimasa mutunci kinji, wuce kuje" gyadama Ammi kai tayi tashiga tafiya ahankali wani abu Saleem yaji kaman zai mutu bazaima iya kallo Amirah na shiga motan ba gashi babu Wanda yaga Marwan dan bai sauke glass kasa ba motan tinted ce kawai Saleem yawuce fuuuu da kafa Mami dasauri tace "Saleem" ko alamun yaji takirasa baiyiba yawuce abinsa Abba yayi kaman bai gansa ba yana tsaye wajen kofa yana jiran Amirah yace "maza" tahowa tayi ahankali tashiga gaban motan ko gigin kallon Marwan batayiba ta zauna Abba yace "yauwaaaa Allah miki albarka"Yakalli Marwan yace "son take care of my daughter" gyadamasa kai kawai Marwan yayi bai magana ba Abba ya rufe kofan motan Marwan yaja motan yayi reverse yawuce.
TOH YAKUKE GANIN ZAMAN SU ZAI KASANCE???
MAISA MARWAN KE FUSHI DA AMIRAH???
KUNA GANIN SALEEM ZAI HAKURA KUWA???
AGANINKU YANZU DA AMIRAH TASAMI LAFIYA WANI SHAWARA ZAKU BATA NA SHAWO KAN MIJINTA DAYA DAU ZAFI??? EPISODE 7️⃣8️⃣
Keke Saleem yatare yashiga, bakin ciki kaman zai mutu, direct gidansa da Precious ke ciki yawuce, yasauka daga keken yashiga gidan, yana shiga falon babu kowa ciki cikeda wannan baccin ran yayi ihu sosai. "Bitch where are you"? Yayi maganan yana hawa staircase yana tafiya sama kaman daga sama Precious dake zaune adakinta da kumburarrun idanunta taji muryansa dagudu tamike tayo kofa daidai tana budewa Saleem na kokarin bude kofan, hada idanu sukayi, Saleem yayi ido da ido da ita tana kokarin magana yadaga kafa yawani kwadeta Precious tai ihu tazube akasa, Saleem yaduka yasa hannu yaja gashin attachenent na kanta tai ihu. "Baby you are hurting me" dasauri yace "that's what I want to do, I want to hurt you soo deep, dan gindin ubanki pastorn kauye ni zakima asiri, all this thing happen because of you, kika turama yayana sex video dinmu eh"?
Precious na kokarin magana kawai yarufe Precious da duka da kafafu da hannu tana ihu sosai Saleem yace "how dare you ruin my life? You spoil my marriage da yanzu nine mijin Amirah, do you how fine and beautiful that girl is, did you see her boobs kuwa ba irin naki da Dr yabaki ba, nata na Allah ne, kinsan asaran dakika jamin, I will kill you today Shegiya tsinannan mai tsarki da toilet paper" dukanta yake kaman zai halakata tana ihu batasan sanda tace "I'm pregnant Saleem!" Chak Saleem yasa tsaya da dukanta dayake, kansa na kasa amsa I'm pregnant din datace, saiyasa hannu yakamota ya mikar da ita ya tsayar da ita, Precious na haki sosai dan ta daku tana kallon fuskansa kaman yanda yake kallon nata, saiya fashe da dariya sosai yace "you're Pregnant kalleni da kyau Precious do I look those men da za'ayi using yara akama su hahahahha" yakara fashewa da dariya yace "ashe bakisan waye Saleem ba, wlh kokin haifi abinda zaki haifa banso bazan taba karba daidai Shegiya tsinanniya" yasake kwadeta yanaji kaman yakasheta saiya saketa yawuce wardrobe nadakin yabude yashiga fito da kayanta yana watsarwa yace "pack your things and leave my house right now I'm selling this house park and leave mu house" sosai Precious ke kuka tanajan guiwanta tazo gabansa tana rawan jiki tace "Saleem I'm sorry I'm so sorry, I agreed I made a mistake but please forgive me wlh wlh bazan karaba please for the sake of our Baby don't throw me out" jefar da hannunta yayi yace "wlh kuka kara tavanı zan kasheki agidan nan nasayo acid na narkan da naman jikinki a sick and flush you" zaro idanu Precious tayi, Saleem yace "ke banda Imani you made a mistake what you did with me dakin bari kawai naciki nabaki kudi na kula dake, I mean I even bought a car for you amman ni zakima asiri, ki hanani aure, ki tonamin aşırı kina turama yayana video ina sex I can never ever forgive you, I don't consider auren mu aure amman dudda haka kije na sakeki saki uku, ciki da ke da cikin durun uwarku, barmin gida Shegiya karuwa kafin na kasheki" yayi maganan yana karasa jefar da kayanta yadauki wasu papers harda papers na motan daya sayamata tadauki akwatinsa yabude drawer ya kwashe duka kudaden sa yace "leave this house or masu gidan zasuzo su fitar dake good bye, and don't try touching motan dana sayamiki na karbi kayana the papers are here duk inda kikaje da ita za'a nemoki"Yana maganan yawuce kofa Precious na kuka sosai tabiyosa Amman harya shige motarsa ya kunna yafita kansa kawai ya hargitse yana edge he's having wani feeling na wlh zai iya turining duniyan nan up side down idan har zai iya samin Amirah abun yanasa yawa ya gangara gefen titi yayi parking yadauki wayansa daya dauko daga gidan daya fito yanzun nan kaman yazare yashiga tattaba wayan baida lokacin neman contact na Marwan yashiga saka number sa sai yayi dialing amman har wayan yagama ringing ya katse ba'a dagaba ihu yayi a mota yace "pick up the call, pick up the call you monster" yana zaune a motan nan Marwan kawai yake kira yakira Marwan yakai sau 30 Marwan bai daga ba saiya shiga turamai message.
"Dan gindin ubanka nine kadaka? Ni kama jina jina? Wait for me, wait for my comeback, Marwan we will settle this score saina maka shegen duka da saika koma wajen uwarka Mami kana kuka ta lallasheka, and let me make this clear to you, Amirah is mine she belongs to me, wlh wlh wlh if you touch her, or sleep with her, I will kill you Marwan".
Turamai messege din yayi saiya jefar sa wayar jikinsa har rawa yake saiya kara kunna motan yaja kaman yazare saiya wuce gidan da aka bama Daddy a old GrA, parking yayi a kofar gidan dasauri ya tsaya gaban gate din yana dukan gate din kaga Saleem zaka dauka yazare, Maman Baby ne tafito anci gayu dan su yanzu duniya tamusu dadi tace "waye haka ke knocking kaman mahaukaci jama'a" tai wajen gate din tana lekawa daidai Daddy dabai dade na dawowa ba shima yana fitowa yace "dakata Sweetheart" tsayawa Maman Baby tayi Daddy yazo saiya leka Saleem yagani wanda kallo daya yakai ya ganesa saiyace "koma ciki" tabe baki Maman Vaby tayi takoma ciki abinta, bude gate din Daddy yayi dasauri Saleem yajuya yakoma motan yabude bayan motan yaciro akwatin daya hada dazu saiya dawo yace "Ina wuni" Daddy dakemai kallo ganin kaman ya sami matsala ga kansa duk bandage yace "lafiya Saleem? Shigo" shigowa Saleem yayi Daddy yajawo gate din yarufe yayi gaba Saleem na binsa yana jan trolly suka shiga falo Daddy yasami waje ya zauna yakallesa yace "meke tafe dakai" Dasauri Saleem da jikinsa ke rawa yaduka yashiga bude akwatin, bundle bundan na yan dollars yashiga cirowa yana ijiyewa agaban Daddy akasa guda ashirin, sai yaciro takardun filayensa da motoci duka yashiga ijiye gaban Daddy jikinsa duk rawa yake, yace "duka wannan nakane Daddy inhar zakamin abinda nakeso" da sauri Daddy ya gyara zama yace "ina jinka"numfashinsa har wani karkacewa yake idanunsa na motsi ganin dukiya da takardun assets, yace "me kakeso Saleem?" Dasauri Saleem zuciyansa nayin wani haske ganin yanda har yayi winning DDdy over yace "kasan rannan daurin auren nan banzo ba shine aka daura auren da kanina Marwan" dasauri Daddy cikeda fadanci yace "ko kadan ban kaunar wannan likitan ni dama tunda yamin rashin kunya a asibiti" Saleem yace "nima bana kaunarsa yanzu danya yaudareni ya auri wacce yasan inaso, abinda nakeso kamin yanzu shine inaso karaba auren!"Dasauri Daddy ya kallesa dan baitaba hararo abinda Saleem keso ba, ganin yanayin Daddy yasa Saleem yace "nikeson aurenta! Diyarka ce kana iko karaba auren idan bakaso dan haka nabaka kwana uku kasa yasaketa karaba auren, nikuma nakama alkawari gabaki dayan gadona da share dina na duka na Kamapaninmu na gold zan baka gakuma wannan danake baka yanzu, Yayana bazai taba iya baka abin nan danake baka ba, inhar kasa yasaki Amira zan baka share dina na companyn mu namaka alkawari, Amirah kadai nakeso aduniya rayuwana ma zan iya badawa danna sameta!"
Daddy kallon Saleem kawai yake dayake mai kallon kaman yasami tabin hankali hankali, kaman baida lafiya lafiya, koko tsabagen obsession ne? Tunda yake baitaba ganin kalan wannan offer da kalan dukiyan nan da mutum yake kokarin ya salwantar sabida kawai yasami Amirah mahaukaciya ba jikinsa har tsuma yake dukawa Daddy yayi yashiga daukan kudaden yana dubawa ko fake ne yaga original kudi ne saiya shiga kirga bundle bundul yana jefawa a akwati, "daya, biyu, uku, hudu, biyar….." kirgawa yagama yi tsaf yajera kudin saiya dauki papers yana dubawa filaye uku a manya manyan waje dakuma motoci guda uku, ya kallesa yace "yaushe za'a aikomin da motocin"? Wani murmushi Saleem yayi yaji yana son mutumin nan yace "ko anjima kakeso zansa akawo maka" gyadamai kai Daddy yayi yazage jakan tsaf ya mikar ya maida akwatin gefensa yace "ko duniya zata hade sama da kasa zata kama da wuta saina kashe auren Amirah da Marwan na aurama Amirah kai, kwana ukun sunmin yawa bani address na inda zanga Marwan" Saleem baisan takamaiman gidan da Marwan ke zama da Amirah ba yace "bansan gidan dasuke ba amman zan baka address na unguwan mu especially masallacin mu dole zaka gansa" Abba yace "angama turomin awaya tashi katafi Son" Dasauri Saleem yaturamai saiya tashi Daddy ma haka sai kawai Saleem yawani hugging Daddy yace "thank you Daddy, thank you Daddyyyy, dagayau kaine Daddyna" Daddy yawani kwashe da dariya yanajin son Saleem sosai yace "ka tsani Marwan ko"? Gyadamai kai Saleem yayi yace "bafa asalin kanina bane, kanin matar Yayana ne, dan riko ne" wani dadin news din Daddy yaji, Daddy ya gyadakai yace "aiko zan kartamai rashin mutuncin dayafi tozarcin dayamin a asibiti, sai yayi nadaman abinda yamin wallahi" Saleem yace "we are team" suka wani kashe shida Daddy, Maman Baby dataji komi itama tafito tace "nima ina cikin team din kuma zan taka maka rawan gani Saleem" kai kunga dadin da Saleem yaji tafiyan da baiyi va kenan suka zauna aka shiga kulle kulle abinda za'ayi.
TOHHH FAHHHH!!! EPISODE 7️⃣9️⃣
**
Suna fita daga asibitin Saleem na tsaye bakin titi trying yatare abin hawa, yaga motan Marwan nafitowa daga asibitin bin motan yayi da kallo yanajin abu na zuwanmai wuya, da ace kallo na kisa da kallon da Saleem yakebin motan dashi daya kashe Marwan, Marwan ya fizgi motan da mahaukacin gudu shima yawuce sa abinsa, hakan yakara kuntatama Saleem rai sosai, irin shi Marwan yakema abubuwan nan sabida yaga yau yaci lagonsa yadakesa zaiko gwadamasa shi dan iska ne bashi yaci wanda he will pay komu jima komu dade.
Sosai Marwan ke sharara uban gudu akan titi, wani kalan tsoro Amirah takeji, gabanta na faduwa sosai, gabaki daya atakure take cikin motan ko inda Marwan yake takasa kallo at all, kanta na kasa sai wasa take da yatsunta, ahaka har sukakai gida, Marwan yadanna remote gate din yabude yashiga da motan yayi parking, yakashe motan batare dayayi motsi ba bai kuma ce kala ba, dan kallonsa Amirah tayi for the first time sai kawai ta runtse idanu da gudu sabida yanda yamata wani kwarjini yakuma kara kyau, farin T-shirt ne ajikinsa dawata 3quater na common flag green kaman na sojoji, fuskansa yayi ja, idanunsa sanye dawani glass farare dasuka kara masa kyau sosai, gashin kansa yayi coils sosai kaman bai taje ba dayayi wanka hakama sajensa da dan karamin gemunsa, yakai kusan 1min a motan sai kawai ya yunkura yabude kofan motan yafito yawuce wajen kofa saiya tsaya tareda juyowa yama motan wani mugun kallo dayasa Amirah taji kaman zatai fitsari ajiki, hannunta na rawa takai ta bude kofa tafito ahankali kanta akasa tana wasa da yatsun hannunta batare data kallesa ba, tamaida kofan tafito tafara tafiya ahankali tana zuwa wajen, dudda yanda Marwan baiso yama daura idanunsa akanta amman kasa daurewa yayi, daura manyan jajayen idanunsa yayi akanta wani abu na fizgansa yana fada da abin dan he's trying his best ya danne any feelings na so dayake dashi akanta dan he's so damn angry with her, ya tsareta da idanu yana kallon kafafuwanta daga hijabin da ake gani abu yakara zuwa wuyansa sabida wani mugun fitinannen kishi, abun ya tsaya yamai katutu awuya, harta karaso wajen, sumsum tabi ta gefensa tashiga falon danya bude mata kofan daman ahankali, shima shigowa yayi kawai saiya maida kofan ya kulle kofan da key hakan yasa Amirah tajuyo ta kallesa, juyowa yayi yazare key yasa a aljihun wandonsa yawuceta kaman baisan tana wajenba yayi staircase yafara hawa Amirah tabisa da kallo yanda bai kulata ba, bai kalleta ba, yana abu kaman baisan wacece itaba ya tsayamata arai kaman ya tsaneta.
Abu taji ya tsaya mata a wuya ganin ko kallo bata ishesaba kawai saita fashe da kuka ahankali tazauna akan kujera awajen tana matsa hawaye, first of all batasan metayi ba exactly, Miemie ta taba cemata Ya Umar nada kishi to shima Ya Marwan nada kishin ne? Sabida tarike hannun yayansa? Ai mistake ne tadauka shine kayansa yasaka, mesa yake fushi haka? Kuma ita bazata iya mai magana ba tsoro takeji karya mata duka itama.
Tana zaune awajen gashi batai salla ba amman tsoron zuwa sama ma takeyi tashi tayi ahankali saita shiga bayin dake nan falon ta dauro alwala tafito tana kallon falonta dayayi kyau tana kokarin tuna gabas nan da nan tagane dan tayi salla agidan ai rannan saita fara salla cikinta namata ciwo na yunwa, sai kallon kitchen take ahaka tana zaune har la'asar tasake zuwa tai salla abinta, jin yunwa kaman zai halakata yasa tamike tsaye ahankali tawuce kitchen data gani a wajajen dinning a falon.
Gab da za'ayi bikinsu daga rannan da Ammi tace an mata aure suka fara koyamata girki da yanda ake amfani dasu gas, shiga kitchen din tayi saita tsaya jimmm, ganin gas din dake nan ba irin gas din dasu Ammi suka koya mata yanda ake amfani dashi bane, kusan burners 6 ne akan gas din ga buttons dayawa na kunnawa chunkushe waje daya wanda batasan wannene na wannan, wannene na wanchan ba, cire hijab na jikinta tayi ta ijiye kan daya daga cikin kujerun dayake zagaye a island na tsakiyan kitchen din, saita tsaya saikuma tajuya tawuce tashiga store na kitchen din, the first abu da idanunta suka gani is kwalin indomie dasauri tadauka tabude dan bama abude ba saita ciro indomie guda daya ta maida kwalin ta ijiye ta dauki egg guda biyu tafito tazo gaban gas din ta tsaya tana kalle kalle saitakai hannunta ta kunna guda daya tadaiji shuuu amman batamasan wani gas ta kunna ba, saita rufe garin rufewa ta kunna another one kadan amma gas din yahau fita amman babu kara sabida kadan ta kunna, all this while bata saniba ta tsaya sai lissafe lissafe take, saitasa hannu tadauki lighter na kunna gas din tarike a hannu takai hannunta ta murza another different gas yafara kara……
Cikin bacci mai nauyi daya kwashe Marwan yaji warin gas dasauri yabude idanunsa yamika hannu yadauki glass yasaka ya kunna wuta yana tashi zaune, warin gas yaji sosai, kawai Amirah ne tafado aransa yana tuna the first abu dayaji tafadi this morning she's hungry, bugawa kirjinsa yafara baisan sanda yawani yaye bargo ya dirko daga gadon dagudu ba dagashi sai dan short ba singlet ko dogon wando jikinsa, yashiga saukowa daga stairs dawani kalan sauri yayi wajen kitchen daidai Amirah na kokarin kunna lighter, daga wajen yayi wani ihuuuu. "Amirahhhhhhhh!" Awani kalan firgitce Amirah tajuyo daidai yataho dagudu kaman zaki ya fizgota zuwa jikinsa tawani fado cikin kirjinsa atsorace, ya karbe lighter hannunta ya jefar yakai hannu yana kukkulle gas guda biyu data bude yariketa gam ajikinsa yawuce yashiga bude window na kitchen din dan gas din yafita Amirah tadan saçı kallon fuskansa he looks so damn worried and scared she could feel yanda kirjinsa ke bugawa gashi yarike gam protecting her with his entire life kaman yar baby dinsa kawai taji zuciyanta yawani narke yayi melting yabude kofan kitchen din na baya shima sannan ya tsaya awajen sai alokacin ya lura da yanda ya kankameta ajikinsa dasauri yasaketa ahankali Amirah takoma baya kanta akasa, cikin tsananin fushi Marwan yace "what are you doing in the kitchen?" Kasa kallonsa tayi takuma kasa magana, tsawa yadaka mata. "Badake nake magana ba"? Dan dagokai tayi saita kasa kallonsa ahankali tace "yunwa nakeji" indomie da 2 egg dayagani kan island yabi da kallo kirjinsa na bugawa cikin tsananin fada yace "bazaki iya zuwa ki sameni kicemin kinajin yunwa ba? What if something happen to you? Dayaya kikeso nayi da kaina? What if you got hurt? Ina kikeso nasa raina? Are you trying to kill me Ameenatu??" Ahankali Amirah tadago kanta for the first time takalli fuskansa jin maganganun dayayi that were shouting I love you Amirah I can't leave without you, hada idanu sukayi wani kunya Marwan yaji da maganganun daya fada da baimasan tayaya yafadesu ba, juyawa yayi dasauri strictly yace "leave this kitchen kafin ranki yabaci" ahankali tajuya sumsum tawuce tafita, ya tsaya a kitchen din shi kadai har lokacin bugawan zuciyansa bai dawo daidai ba, kusan 5min sannan ya kunna gas din da Kansa ya ja tsaki yadauki pot yasa akan gas din cikin 5min yadafa mata indomie da boiler eggs, yasa mata a bowl yadauki fork yasaka yakashe komi yafito daga kitchen din dan dagokai Amirah dake falon tayi suka hada idanu dasauri tasauke kanta, ijiye bowl din yayi akan dinning kawai yawuce stairs yayi sama abinsa Amirah tasake binsa da kallo saita taso ahankali tazo dinning din ta kalli indomie daya dafa mata saita kara kallon sama wani sanyi taji aranta saitaja kujera tazauna ahankali tashiga ci maganganun dayayi dazu nadawo mata akai.
"bazaki iya zuwa ki sameni kicemin kinajin yunwa ba? What if something happen to you? Dayaya kikeso nayi da kaina? What if you got hurt? Ina kikeso nasa raina? Are you trying to kill me Ameenatu??" Wani shauki taji ya lullubeta, he's angry but he's still very sweet and caring even though he is angry. EPISODE 8️⃣0️⃣
Daki Marwan yawuce yashiga, har lokacin his heart was racing zuciyansa nata gayamai wat if something yasameta dayaya zaiyi? He was so scared, kodayakai sama saida ya tsaya yakara lekota ahankali ta saman bene yaga takai indomie baki tadanyi murmushi kadan ya tsareta da idanu, wani kalan sonta yakeji a zuciyanta kaman zai halakasa, kokarin dago kanta sama Amirah tahauyi hakan yasa yabar wajen da sauri baiso tagansa, soyake yayi wanka yayi salla, baimasan ya akayi bacci mai nauyi yadaukesa ba, wayansa ne yahau ringing hakan yasa yakai hannu yadauka yaga Farida ne, hannu yasa yadauki wayan batare dayayi magana ba dasauri tace "Yaya muna kofar gida Mami tabamu abubuwa mu kawoma Ya Amirah" dan jim yayi saiyace "okay" cire wayan yayi daga kunnensa alokacin yaga text message from Saleem he knows Saleem so well da yasan yana bude text message dinnan ransa bacı zaiyi kawai saiya ijiye wayan akan gado, yawuce closet dinsa yasa jallabiya saiya fito Amirah na dinning tanacin indomie ta yafito tadan saci kallonsa ko inda take bai kalla ba, yawuce kofa yasa key yabude saiya fita yabude gate, Farida da Faiza yagani da flask har biyu saikuma wayan Amirah, strictly yace "get in" wucewa ciki sukai da sauri, shiya tsaya yana maida kofan yarufe suka shiga falo Amirah na ganinsu ta mike tana murmushi suma haka suka taho wajenta da sauri da flask din suna ijiyewa kan dinning Faiza tace "indomie kikece ga abinci mun kawo, wannan kazanki ne Mami tace ke kadai zakici" dasauri Amirah tasa hannu takarvi karamin flask din tana budewa tace "Mami ta dafamin, girkin Mami dadi" duk suna tsaya suna kallonta yanda take magana saita dago manyan idanunta ta kallesu tace "ku zauna muci tare" tai maganan daidai Marwan na shigowa falon dan satan kallonta yayi sabida aya da maganan yafito straight daga harshenta was so unlike her, suna kokarin bata amsa Marwan yace "Kids" dasauri suka juyo suka kallesa yau kowa is minding his business sabida ansan ransa abace yake, wani mugun kallo yamusu yace "kuzo kutafi" wani iri Amirah taji wlh taso su zauna saiga hawaye yacika idanunta Farida tace "ga wayanki don't cry gobe ma zamu dawo" gyadamusu kai Amirah tayi hawayen na suakowa takai bayan hannunta ta share suka wuce suka fita Marwan yarufe kofa yajuyo yawuce staircase harya fara hawa saiyadan kalleta yanda take share hawaye kaman zaiyi magana kawai saiya wuce abinsa, dago kai tayi ta ballamai harara tana turo baki saita bude kulan kazanta tadebi Kazan da romo sosai tazauna tafara ci dadinsa baima bari tagane Kazan magani bane tass ta cinye ta shanye romon saita wuce takai pates kitchen ragowan kazanta tasaka a fridge, shikuma dayan tabarshi a dinning tawuce tadawao falon bayan tasaka hijabinta ta zauna akan kujera tana danna wayanta tanaso takira Ammi da Miemie but bataso takirasu yana gidan, daganan tafarajin kamshinsa saukowa yashiga yi ya chanza kaya zuwa kaftan ash color riga da wando yana baza uban kamshi dan Satan kallonsa tayi kirjinta taji yana bugawa wani abu na fizganta tsabagen yanda yayi kyau looking very classy and expensive dasauri tadauke kanta ta kwanta a kujera tai lamoooo ko kallon inda take baiyiba yawuce kifa yasa key yafice tanaji yana kara kulle kofan da key jin bai dauki mota ba yasa tadanji sauki danhar tafara tsoro ita kadai a gida an kulleta maybe masallaci zaije ko wajen Mami saida taji fitansa saita daga wayan dasauri takira Ammi.