Baccin so complete by m shakur - Chapter 34
Baccin so complete by m shakur Chapter 34: Baccin so complete by m shakur Chapter 34. Koda sukakai gida Lami ne ta taresu hankalinta yatashi tana kallon…
4,334 words
Koda sukakai gida Lami ne ta taresu hankalinta yatashi tana kallon Ammi da Amirah zatai magana Ammi tace "samin ruwan zafi a wuta lami, kiramin Yaya yazo gida, tayani kiran Miemie itama, bansan inda wayata takeba kwata kwata" Mama Lami kawai ta gyadamata kai ganin ba lafiya Ammi tawuce tashiga dakinta Amirah tabiyota ahankali she's still crying, zama Ammi tayi bakin gado saita dago kanta ta kalli Amirah data shiga tahowa wajen Ammi ahankali cikin fushi Ammi tace "wlh wlh kikazo wajena nan saina nakada miki mummunan duka Amirah, saina miki shegen duka yarinyar nan" shigowa dakin Lami tayi da gudu dan bata tabajin Ammi na fada da Amirah hakaba, Lami tace "lafiya Ammi"?Ammi tace "dauki yarnan tabarmin dakin nan banson ganinta, ki taimakamata idan zaki iya ki hadamata da paracetamol kawai I'm not ready to see her now" kunga yanda Amirah ke kuka ga fushin Marwan ga Ammi na fushi da ita kalan wanda bata taba ganin Ammi tayi da itaba kawai saitaji dubiyan yamata zafi Lami tashiga dagata tace "muje muje Amirah me kikama Mamanki haka?" Amirah bamata iya magana Lami ya fitar da ita taje tahada ruwan dan itama talura da condition na Amirah sukaje bayi ita ta taimaka mata ta gasu saida Amirah taji kamanma mutuwa zatayi suka fito Lami tawuce da uta dakinta tabata wasu kaya tasaka daidai lokacin Umar na sauke Miemie akan machine jin ayanda Lami tace mata Ammi tace yazo he was so supportive kawai yakawota yace "idan kun gama ki kirani nazo na daukeki" gyadamai kai tayi daidai Baffa na zuwa shima Umar yashiga gaisawa da Baffa.
Kafin da Baffa da Miemie sushi go gidan tare yana rikeda hannunta suna hira suka shigo gidan da Sallama Mama Lami tafito ganin fuskanta kadai sunsan bakafiya tace "ku shigo nan" shigowa dakin sukayi zata wuce takira Ammi taga Ammi tafito idanunta sunyi jajir, Miemie nashiga dakin taga Amirah ga tea agabanta bata tababa dagudu tai wajen Amirah tace "Ya Amirah? Menene meya sameki? Baki da lafiya ne? Mama Lami meya sameta haka fuskanta duk ya kumbura"? Daidai Ammi na shigowa dakin tace "sakinta tasa mijinta yayi" atare da Baffa da Lami da Miemie sukace "mene!" Zama Ammi tayi saitai shiruuuu saikuma tashiga basu labarin komi daya faru tassss har zuwa dawowansu saita kalli Amirah cikin zafin zuciya Ammi tace "open your mouth kifada mana dalla dalla abinda kikaje kikayi ma Marwan da iyayensa inba hakaba ranki zai baci" Sosai take kallon Ammi gabanta kawai faduwa yake ashe uwa wacce bata taba dukanka ba take riritaka duk randa zata rikida tai fushi dakai jikake kafi tsoronta kan komi aduniya, Amirah bata taba sannin haka take tsoron Ammi ba sai yau sabida yanda taga ran Ammi yabaci har rawa jikinta yake takasa magana, Ammi tadaka mata mummunan tsawa. "Bazaki bude baki kiyi magana ba Ameenatu" rushewa dawani kalan kukan tsoro tayi kawai tashiga fadin abinda tayi ba karya dan ta dimauce, Ammi tafarfasa kawai takeyi, sanda Amirah takai wajen datace ita ta rungume Saleem dama yaga jikinta kawai Ammi ta taso Lami tana. "Ammi, Ammi" Inaaa fizgo Amirah Ammi tayi tashiga dukanta, though bawai wani lafiyayyen duka take mataba but just soft beating haka na fushi dayake nunama yaro yayi abinda ba daidai ba Lami tarike Ammi tace "dan Allah kimata hakuri dan Allah" Miemie ma ta tsorata bata taba ganin Ammi ta fusata hakaba har tana dukan Amirah tafashe da kuka itama tana rokon Ammi, Amirah nawani kalan kuka wlh har fitsari saida ya kufce mata, Baffa yatashi yazo wajen yace "saketa nace" Ammi tasaketa Amirah ta kankame Baffa tana wani kalan ijiyan zuciya kaman zata mutu jikinta bari kawai yake tana kuka, Baffa yace "haba so kike yarnan ta mutu gabaki daya kihuta da wanne zataji? Akanki fa taje tai abinda tayi" ran Ammi abace tace "banki takaba Baffa amman tarbiyan dana bata kenan, yaushe Amirah takoyi fitsara eh? Kallon Babba tamusu rashin kunya, tama Mahaifinsa tama Mamarsa haba an kace karna maketa, tarbiyan dana bata kenan, mijinki zaki cema kanin mata? Mijinki zaki gayama dan uwansa kikeso yanaga jikinki eh? Sabida kinga yana sonki? Naji dadi ai yanuna miki shi dan halak ne daya sakeki, saikisha zaman gida shashasha kawai, shekara nawa yau kikasan halin ubanki, da baki daya zaki sanar da mijinki abinda ke faruwa zasu magance abin nan bagashi yanzu yana police station ba but you decided to use the foolish way, kinma manya fitsara kin kaso aurenki wacce batasan mutunci ba sanda uban naki yadaukeki yakai asibitin mahaukata ya watsar ko biyar bai ijiyewmb wannan bawan Allah data zaga daga kudinsa Yaya kudin aljihunsa yayi admitting nata all her drugs everything was from his pocket ama samin likita haka a duniya? Ko wannan abun kadai baici ki rangwantamai ki kasa kallon idanunsa ki gayamasa wasu maganganun ba, Marwan fa kudi yadauka yaba Miemie wanda ban mamcewa kudin nayi amfani dasu har na kwaso kaya nazo gidan nan dan banda ko sisi a lokacin the only person daya miki wannan adalcin kikama haka I'm so embarrassed ace diyata ce tai wannan abun wlh kuwa, Idan Matar dana tamin kalan abinda Amirah tayi saina cewa dana wannan ba Matar aure bace ita da kai har abada, yanzu ai kin huta ki sha zaman gida zawarci kikeso ko, kin dauka ana auren marasa kai ne Allah ya rufa miki asiri amman ke kin tonama kanki shikenan" Baffa ya fizgo Ammi yace "keeee" yakalli Miemie yace "dauki Amirah kuje chan dakin" Miemie takama Amirah dake kuka suka fita Baffa yakalli Ammi daya dade baiga matan nan tai fushi hakaba yace "yakuri yakuri nasan yanda kikeji yakuri kinji yakuri" sai alokacin kukan da Ammi keji tarushe tafashe dashi, Allah sarki ashe idan aka saki diyarka sakin yamafi yima uwa ciwo akan diyar, wlh Lami itama saitahau matsar hawaye taji bala'in tausayin Ammi, Baffa yace "ya isa, kiyakuri, kimata afuwa, duka duka yaushe tasami lafiyan? Yaushe tai hankalin? Meta sani? Dole ta tafka shirme, ayanda Amirah ke sonki kome akace tayi kanki zatayi eh" cikin kuka Ammi tace "nasani kawai tacima yaron mutunci dayawa ne maganganun data gayamai baisuyi kama da maganganun mara kan gado urinta ba yanda kasan an zaunar da İta an koyamata, kunyan Marwna nakeji, Baffa Amirah bata kyautaba, I can never excuse action nata koda kashenin akayi, she can simply go kobazata fada musu ga abinda ke faruwa ba tayi demanding sakin batare dataci musu mutunci da fuska ba"Baffa yace "rashin hankalin kenan, amman ya isa, tayi abinda tayi yanzu ne mu manya zamu gyara kuskuren Alhamdulillah saki dayane, inhar matarsa ce zasu dawo su koma su zauna tare, gobe in sha Allah zamu shirya muje gidansu da safe mu uku mu bada hakurin abinda diyarmu tayi hakan zai nuna munsan me mukeyi, kiyakuri go easy on her kar fushinki ya maidata gidan jiya, correct her kinuna mata ga yanda rayuwa yake, ba'a wulakanta masoyi, I'm sure by now ita kanta tai nadaman actions nata, dan Allah kibita ahankali kinji, saki ba komi bane face kaddara wacce Allah yarubuta maka zai sameka, wani zubin sai bayan an sami matsala anyi saki ake dawowa a kulla soyayya wacce tafi nada so calm down kinji" Sosai Baffa da Lami suka dunga bama Ammi baki har fushin datakeyi yaragu sosai.
WAYYYOOO AMMI SAKIN NAN YAMATA CIWO WLH😭 EPISODE 9️⃣9️⃣
Miemie da Lami ne suka kula da Amirah sosai tea kawai ta iya sha Baffa yaje pharmacy yasayo mata magungunan zazzabi tasha takara gashin yamma bayan sallan magrib bacci yakwasheta, taba su Miemie tausayi, tashi Miemie tayi ta tafi dakin Ammi, Ammi na zaune kan dadduma tana lazimi tabita da kallo saida tazo wajen ta zauna ahankali Ammi na kallonta tace "yaushe zaki tafi?" Ahankali tace "bayan magrib Ya Umar yace zaizo muwuce" Ammi ta gyadamata kai, suna zaune ahaka har aka kira isha sukai ishai.
Washegari still Lami tama Amirah komi tabata breakfast tadanci kadan taji sauki sosai wajen yarage mata ciwo kawai rayuwanta baya mata dadi ne, wuraren 10 suka tafi gidansu Baffa akabar Amirah kawai agidan dan bazasu dade ba.
Around karfe goma na safe yasauka a garin Netherlands, fitowa yayi anan airport yasai, using WiFi saiya shiga WhatsApp yaturama Mami message. "Mami I just arrived, I wanna remove my SIM card, go off social media for a while, when my mind is calm and settled I will call you Mami, take care" yana tura maganan yacire Nigerian sim nasa yasauke WhatsApp Wanda daman shine social media app dayake dashi, wani VIP car yashiga aka wuce dashi lafiyayyen 10star hotel dayayi booking ana tafiyan yana kallon hanya yana tunani, Amirah ce azuciyansa but he's trying yadake ya danna duk sanda zatai popping up azuciyansa saiya danne tunaninta he just want to close her chapter baimaso yadinga tunata balle yadinga tuna mai tace masa that's what is hurting him the most kawai saiyayi alkawarin hakan zaiyi.
** Har gidan sukakai da tsananin farin ciki Mami ta tarbesu while Abba yashiga turama Alhaji Hamza message kan yazo, zama aka yiyyi Mami tace "bari akawo breakfast" Mami Lami tace "ahh mun koshi" Mami tace "wlh ban yardaba" dasauri tawuce kitchen tana kiran Twins dasuka shiga saukowa sukazo suka gaida kowa na dakin sannan suka wuce kitchen saiga Alhaji Hamza yana sanye da manyan kaya milk color yana baza kamshi da sallama yashigo falon yar zuciyanta Ammi taji muryansa amman taki daga kai, Abba yamike yace "bismillah shigo shigo" yashigo saiya nunama Baffa Alhaji Hamza yace "ga babban aminina Alhaji Hamza, tsohon soja ne toh kukan kirasa da general" Baffa yabasa hannu suka gaisa anadan raha sai Alhaji Hamza yajuyo yakalli Ammi wani kallo dabaya boye soyayya yace "ina kwana Hajiya, dafatan kin tashi lafiya, ya jikin? Akwai abinda ke miki ciwo?" Kowa na dakin saida yajuyo yakalli Alhaji Hamza kunya yasa Ammi takasa ko motsi, tamaki magana saiya kalli Lami yace "ina kwana dan Allah tasha magani kuwa" lami tawani washe baki tana kallon Ammi dataki magana tace "eh tasha Alhamdulillah lafiya kalau duk muka kwana" anatse yace "diyata fa Amirah?" Wani sanyi Ammi taji yanda ya tambayi Amirah, Lami tace "itama haka tasha shayi munbarta takoma bacci ma" gyadamata kai yayi saiya juya yawuce wajen su Abba yazauna Baffa nadan binsa da kallo saiga abinci an shiga kawowa, Lami tadan matso kusada Ammi cikin muryan gulma tace "wannan general yakamu fa Maman Amirah yaushe kuka hadu?" Dan dago kanta Ammi tayi ta saci kallonsa tadauke idanu dasauri ita kanta batamasan mesa takejin mutumin aranta ba daga ganinsa jiya. EPISODE 1️⃣0️⃣0️⃣
The last time wani namiji yataba shiga ranta was 22yrs ago tun mahaifin Amirah, that same feelings takeji yanzu akan Hamza tarasa dalili sake dago idanunta tayi karaf suka hada idanu dasauri ta dauke kai Mami tafito tareda yan aikinta dakuma twins aka jera abinci, waina ce da farfesu sai kunu, da shayi dakuma dumamen tuwo da miyan kuka da man shanu da yaji sai ruwa tace "dan Allah ku sauko muyi kari" babu Wanda yayi musu, duk aka sauko Hamza kaman zai cinye Ammi da idanu babu wanda bai lura a dakinba imagine Ammi na gidan in-laws dinta amman idanun Hamza yahanata sukuni, dumame taci bada wani yawa ba da kunu mazan ko sunci abinci da kyau, Abba ya warware yasaki jikinsa bai daurama kansa damuwan Saleem ba yashiga coma ance shock ne zai dinga zuwa yana dubasa kullum yabisa da addu'a shiyasa kansa in this situation he pray Allah have mercy on him.
Gama cin abincin akayi tass akai clearing komi aka zazzauna Baffa yayi guaran murya yace "toh Alhamdulillah mungode da wannan karamci, zanso na tambaya ina Marwan saikuma shima Saleem din zanzo duk mugansa kafin afara magana"dan gyaran murya Abba yayi yace "toh with everything that happened jiya konima nan kafin nakoma gida Yayarsa ke sanar dani Marwan yabar kasan!" Abba yadanyi shiruuu sai ahankali yace "Ahhhh Marwan wani kalan mutum ne mai hakuri mara fushi, koni baimin sallama ba, I'm sure yayarsa ma sabida ita tagansa saisa tasan da tafiyan, yatura mana message ya sauka lafiya amman zai sauke komi na wayansa when he's ready zai kiramu, I know he's just hurting me for now, but nasan waye d'ana bazai taba rabuwa da Amirah ba aurensu zai dawo let's give him sometime to cool off" jikin kowa na dakin yayi sanyiii, Abba yace "akwai something daban fada muku ba, sabida bantaba daukan abin hakaba, Saleem kanina ne uwa daya uba daya, while Marwan kanin matana ne wanda tadaukesa tun yana shekara daya sakamakon hatsari da iyayensu sukayi toh a hannunta yataso, Saleem yataso a dayan matata shi yana shekara uku lokacin mahaifiyar mu tarasu, dukansu na daukesu a matsayin yarana dan a hannuna duk sukai girma, Abba yayi shiru yace "dukansu sun taso a hannuna as two opposite yara, while Marwan is a calm, nutsasstsen yaro, Saleem is opposite of that, mata, shayeshaye duddai irin abubuwan nan wanda akasan waje abokan banza duk anan ya koya, daidai gwargwado munyi iyakan kokarin mu amman ba riba, rana daya yaje wajen dan uwansa Marwan a asibiti yaga Amirah a office na Marwan, Allah ya doramasa kaunar ta, for the first time saiya fara kokarin ya chanza ya zama mutum na gari, Abba yadanyi shiru yace "mukaje muka nemi aurenta amman kash rannan daurin auren wata ta shagaltar dashi jama'a sun taru narasa yanda zaiyi sainasa a daura auren da Marwan tunda nasan shi yarone mai hakuri da kawaici nasan bazai taba kunyatani ba" Abba yasake yin shiru sai chan yace "bamu gansa ba sai bayan wata daya da auren Marwan ma yaganosa ashe yarinyar dayakebi tamai asiri yaje ya karya tom shine tunda Saleem ya lura Marwan ke auren Amirah rigima yatashi, yaki hakura, yaki imani yadage sai Marwan yasaketa shine yadinga abubuwa haryane yahade da babban su bansan tayaya suka zama team ba, yanzu dai haka Saleem na asibiti ita yarinyar datamai asiri ta yankemai gaba ta gudu!" Kowa ya kalli Abba, murmushi yayi na manya yace "hmm Alhamdulillah jiya akai surgery yafito amman he's on coma I pray Allah yasa sanadin shiryuwan sa kenan, kuma one thing dana sani is alhakin raba auren nan ke kamasu duka" Baffa yace "ba shakka, to Allah ya magance komi, daman munzo baku hakuri ne bisa ga abinda diyarmu tamuku mara kyau mara dadin ji kuma" Abba yayi murmushi yace "mukuma namu dan dayayi nasa shirmen fa Marwan? Koko shi kanina da shine ummul aba'isi na komi? Shine haddasana daya hada wannan gurmin" Abba yasauke ijiyan zuciya yace "Amirah yarinya ce wacce keda condition da hikiman Alkah yasa ta warke, sunsan this is the exact way zatai handling abinga sabida ba wayau, amman muna iyaye idan har kunkai maganganunta zuciya ai mun tapka shirme" Mami tace "kwarai, wlh banma dauki maganganunta wani abu ba, bata batamin raiba, konine zanyi haka dan haka munema mukai abin baku hakuri ba Amirah ba, kuma in sha Allah aurensu zai daidaitu Marwan na son Amirah fiye da misali, dan haka bakomi mun zama daya mun zama family" duk ijiyan zuciya aka sauke sai aka shiga hira Alhaji Hamza yadan dago kansa karaf suka hada idanu da Ammi sai kawai yakalli Baffa, anatse yace "Baffa" Dasauri Baffa yakallesa jin yanda yakirasa da Baffa yace "Naam Alhaji Hamza" Baffa yace "sunana Hamza, Baffa dan Allah kabani damar neman auren kanwarka, ina matukar kaunar ta" lullube fuska Ammi tayi kunya kaman zai kasheta batasan sanda tace "kasan ina gidan surukaina ko" Dasauri Alhaji Hamza yadafa kirji yace "Alhamdulillah finally tamin magana" haba zokaji dariya harshi Baffa saida ya kyakyata Ammi ta tashi dasauri tace "sai anjiman ku" tai kofa Mami tabita tana dariya tace "jirani" da Mami da Lami suka bita, Alhaji Hamza kaman zaiyi kuka, ahankali Baffa yace "nabaka daman nemanta Hamza, inhar ta yarda ko gobe ne zan daura muku aure, yau tafita daga idda indai lissafina daidaine" Dasauri Alhaji Hamza yace "bani number ta dan bazata bani ba" Baffa da kansa yabasa sai suka taso aka sake musabaha suka fito.
Wayan Amirah Mami taba Ammi tace "ga wayanta nan akaimata dan Allah agaishemin da ita sainazo Ammi tace zataji.
** Bayan sati biyu! A sati biyun man kusan kwana goma Amirah rashin lafiya tayi sosai dan har saida aka mata allura, tadamu wani kalan damuwa dabata tabajin tanayin kalansa arayuwanta ba, ko rufe idanu tayi Marwan take gani, tun Ammi najin haushinta hartazo tarage tafara kulata tashiga koya mata abubuwa yau 4days da warkewanta daga ciwo abinci aka koya mata yanzu kullum ita keyin abincin gida, gyaran gida da Shara kunna turaren wuta duk wani abu dabata yi da yanzu tanayi, Ammi da kanta tasata a islamiyya na matan aure yaune second day datake zuwa duk ta rame yafice hayyacinta, sai ta ciro number Ya Marwan dake wayanta taitai kallo saita ita kira bayama shiga tarasa ina zatasa kanta. Alhaji Hamza yayi pressing charges on Abba, kidnapping, torture da sauransu Ammi bataso taje police station sai shi yakawo mata yan sandan har gida akasa tarubuta statement aka maka Abba a kotu take yanke alkali yaturasa 30yrs prison Abba baitaba sanin baida kowa ba sai yau, dudda an basa waya yakira Maman Baby yakira yakira harya gaji wayanta baya shiga, baida number Baby akansa kona mijinta baida wani wanda zai kira baitaba sanin he's a nobody arayuwansa ha sai yau, yanada kudi ba amfani baida means na communicating ko reaching family nasa kawai rayuwa tamai duhu gidan yari ha dadi sai ciwo kanzuwa takamasa soshe oshe yake kaman mene ga mugaye a prison dake kwacemai abinci kawai ya wulakanta iya wulakancewa, zama Ammi tayi tana tunani Allah yasani tanaso tai aure kuma takamu da son Alhaji Hamza kawai Amirah take tunani dake gabanta, bazata iya tafiya gidansa tabar Amirah anan ba damuwa zai kara mata yawa, text tana Alhaji Hamza kan tana nemansa, takwas tamasa agidan shigowa yayi falon Abba Ammi tadan bata lokaci saita fito da hijabinta har kasa taje dakin tasami waje tazauna tana kallonsa tace "ina yini" sosai yake kallonta kaman zai cinyeta da idanu ahankali yace "dan Allah ki aureni my love" dan kallonsa Ammi tayi tace "ammm maganan danakeso nayi dakai kenan" Dasauri ya gyara zama yace "ina jinki" Ammi tace "zaka yarda na tare gidanka da Amirah?" Wani kallo yamata na bacin rai yace "what are you saying sweetheart? Amirah is my daughter gidana gidan mahaifinta ne, haba raina yabaci da tambayan nan? Kin dauka nida kaina zan barkı ki barta anan ne? Idan kowa na gidan nan ma kinaso kije dashi my house is big enough inason jama'a I have just two children maza duka suna US suna karatu ni kadai in that big house so duk inda kike Amirah has to be there" wani natsuwa Ammi taji aranta tadan sauke ijiyan zuciya ahankali tace "ka shirya kazo gobe na yarda zan aureka, zan tare gidan ka sati na sama" wani saukowa daga kujera Alhaji Hamza yayi sai yajawo guiwansa, yazo gaban Ammi yace "sweetheart can you please repeat abinda kikace?" Dan kallonsa Ammi tayi cikeda so tace "na yarda zan aureka" Alhamdulillah yafadi da sauri yana sunjada akasa Ammi tai shiru sabida itane har wani yake sujjada sabida tace zata aureshi Allahu Akbar, wato mahakurci mawadaci.
Tasowa yayi Ammi tace "wuce katafi before I change my mind" murmushi yayi yace "to ranki shi dade natafi natafi take care of yourself" Ammi tai murmushi tashiga dakin Lami kai tsaye tace "Yaya yashigo ki gayamasa gobe zasuzo adaura mana aure na yarda zan auresa" ihu Lami tayi ta rungume Ammi duk kunya yakama Ammi tawuce takoma daki taga Amirah kwance agado tai shiruuu ta lumshe idanu wanda yanzu haka rayuwanta yadawo wucewa tayi tazauna bakin gadon tace "Amirah" bude idanunta Amirah tayi, ahankali Ammi tace "meke damunki Ameenatu?" Shiru tayi kaman bazatai magana ba sai wani kuka yashiga taso mata takasa magana amman tawani kalan fashe da kuka agaban Ammi kuka mai taba zuciya Ammi ta tsaya tana kallonta bata cemata komiba, anatse Ammi tace "sai yanzu kikasan kina sonsa, I've been watching you, naga yanda kike kiran number sa sana da sau dari arana, bantaba cemiki komiba sabida i want keda kanki kiji ajikinki me kika rasa, yanda kikeson mijinki, and how important Marwan is to you, you did this to yourself"
Wani kalan kuka Amirah take harda shesheka da ijiyan zuciya da majina tarasa inda zatasa kanta dawata kalan wutan son Marwan datakeji da ke Wanda da begensa da kwadayin ganin fuskansa, tabama Ammi tausayi, tunda tai abin nan Ammi bata kara lallashinta ba, amman yau zuciyanta ya sosu, ahankali tabude hannayenta tace "come" kaman abinda Amirah take jira kenan she missed hug na Ammi da gudu ta shiga jikin Ammi ta kankameta tana kara rushewa da kuka tace "Ammi I'm sorry kiyafemin" Ammi tashafa bayanta tace "shiiiii" cikin mugun kuka tace "Ammi Ya Marwannnnn, Ammi ina sonshi, wayansa baya shiga yayi blocking dina tayaya dan basa hakuri, lumbarsa bata watsapp, Ammi idan bangansa ba zan mutuuuu"Dagota Ammi tayi tace "ya isa" takai hannuwanta tashiga share mata fuska tace "now listen to me zan koyamiki wani important abu dakowace matan aure yakamata kisani" ahankali Ammi tace "aduk lokacin dazaki sami wani gagarumin matsala da mijinki ya zamto ya tsaneki, he's distance baya kaunar ki ko kaunar ganinki, abinda yakamata kiyi is, ki koma ga Allah, kibisa da addu'a, ki daga hannuwanki sama ki roki Allah ya karka to miki da hankalin mijinki gareki, Allah ya saukar da kaunar ki zuciyansa wanda yafi da, Allah ya daidaita ku, Allah yadawo miki dashi rayuwanki, Amirah babu abinda yafi karfin Allah shine gatanmu, so me kike jira? Face Allah and beg him ya daidaita tsakaninki da mijinki, idan Marwan yadawo gareki start afresh ki kunamai kim girma kinyi hankali bazaki kara wannan kuskuren dakikai da ba kinajina, stop crying" gyadama Ammi kai tayi tace "dagayau kullum kidage da tashi sallan dare okay, zan dinga tashinki" gyadama Ammi kai tayi. Washe gari bayan sallan azahar aka daura auren Ammi, bata tambayesa komiba kawai saiya bata sadaki babban gida da miliyan biyar, kuma yayi hakane yakira Baffa privately yabasa gida da mota Baffa yaki karba, koda Ammi tamai maganan yanuna mata Baffa yakeso taba yabar gidan nan, Ammi saida tai kuka sabida yanda abin yamata, haka taba Baffa gidan kyauta yaji dadi, nan fa aka fara shirye shiruen tarewan Ammi next week, Amirah ne kawai bata walwala babu abinda kemata dadi aduniya, ko abinci bata iyaci, tadage da addu'a dakuma azumi. EPISODE 1️⃣0️⃣1️⃣ MINI
Bayan 3weeks Tashi yayi ahankali yazauna dan gabaki daya yakasa gane meke damunsa tunda yazo garin nan azumi kawai yake back to back one day on one day off, he's trying his best ya mance da Amirah yakasa
Wani Kara kansa yayi kiiiiiiiiiiii kirjinsa yawani buga da saida yakai hannunsa kan kirjinsa Mai tace "babu wanda yasan da cikin kawai rashin lafiya ya rufeta Ammi da Alhaji Hanza kasan sunyi aure sai suka kawota asibiti, ba'a fadan mana mene ke damunta ba but she's in extreme danger da Dr yace ko ita ko Babyy dole sai mijinta yazabi daya and they need you here Marwan, ana nemanka" wani kalan bugawa kirjinsa yake ba kakkautawa, Abba ya karbi wayan yace "already jirgina yasauka a Netherlands please Marwan drop this phone kataho matarka is on oxygen batasan ina kanta yakeba she really needs you, kai kadan ake jira, every second the danger keep increasing haka Dr yace" lumshe idanu yayi sai kawai ya jefar da wayan yariga yayi sallan azuba komawa bacci kawai yayi da kayan fake jikinsa kawai yadaki takalmi yasaka da jacket yadauki passport nasa da waya duk wani sauran abu yabari awajen kawai yajuya yafice daga dakin dagudu.
Guys I'm really sorry!
I lost all typing na novel dinnan! Telegram dina is not back! So many things went wrong, amman In sha Allah on Friday Mun gama!
Please duk wayanda sukamin magana ban amsasuba resend chats naku, yan telegram nabude muku WhatsApp group cha me up nabaku link. EPISODE 1️⃣0️⃣2️⃣
Ko zama Marwan yakasa yi bini bini Ammi ke kallonsa bata taba sanin haka Marwan keson Amirah ba, like the love is soo obvious kana ganinsa kuruuu a idanunsa kowannensu na zaune bandashi dake tsaye dab da kofan yayi folding hannu kana ganin alamun yana zikiri da yatsunsa, sai kuma chan kaga yadaga hannu yana kallon agogon sai zuciyan Ammi yayi sanyi yakuma natsu.
Awa biyu Amirah tayi a dakin sai gashi an shiga fito da ita dawani kalan sauri Marwan yashiga kokarin bude kofan aka bude suna fitowa yace "Amirah Amirah! Dr how is she"? Yayi maganan yana kama hannunta yarike yana shafa fuskanta, Dr yace "she's fine, anyi wankin ciki anjima kadan zata farka, you guys can leave the hospital in the morning" ahankali Marwan yace "Alhamdulilah" kowa na wajen ma haka sukagungurata zuwa daki Yanda Marwan ke tsaye kanta daga Ammi har Mami sai duk suka ja baya, Abba ne yayi gyaran murya yace "tunda ga mijinta kuwuce kuje gida kusami bacci" dudda Mami bataso su tafi amman Marwan da Amirah na bukatan alone moment sai tace "toh" hakama Ammi dudda bataso ta tafi amman sai itama takalli Alhaji Hamza tace "muje" Duk suka wuce suka fita dakin yarage Marwan kadai da Amirah, yakama hannunta yarike gam yana kallonta he feels all this was his fault, da ace yana tareda ita da tuni yasan da cikin nan, yabata kulawa na musamman su raini cikinsu tare, but sabida bakar zuciyansa da bakin kishinsa yasa sun rasa babynsu, yasan abinda Amirah tayi bata kyauta ba, but kuma yazauna yayi tunani mai zurfi wannan tafiyan dayayi, Amirah batada wayau, she was a sick girl da bata dade da samin lafiya ba, yaushe tasami hikiman handling situations like that? Batadashi, ayanda abin yazo mata ahaka zata bisa, he knows yanda takeson Amminta there's nothing's bazata iyayi akan Ammi ba, on the other hand shinema yakeda babban laifi, shi amatsayinsa na mai hankali bai dace ace yasaketa ba no matter what she said to him cus yasan ba gaskiya bane, kawai yasan komi daya faru kaddarane Allah yariga yarubuta cewa hakan zai faru saisa hakan yafaru.