Baccin so complete by m shakur - Chapter 4
Baccin so complete by m shakur Chapter 4: Baccin so complete by m shakur Chapter 4. Shigowa gidan Daddy yayi dawasu karafan maza guda uku tika tika dasu…
4,352 words
Shigowa gidan Daddy yayi dawasu karafan maza guda uku tika tika dasu dasu bouncers yana gyara belt na jikinsa ga katon bandage akansa yace "yauwa kubiyoni, mahaukaciyar na flat dinnan kumuje" yayi gaba, Ammi tana tsaye a kitchen taji an bugo kofa dan jim tayi duk fadan dazatama Miemie bata buge bugen kofa toh kodai Amirah ne ta tashi hakan yasa dasauri tasa hannu ta murza gas tana kashewa zata juyo taji muryan Daddy yace "kushigo nace"wani mummunan faduwa gaban Ammi yayi dasauri tai wajen kofan kitchen tabude Daddy tagani yana sanye da riga da wando na jean da shirt da belt dawasu kattai su uku yayi hanyar bedroom dinta yace "tana nan dakin zoku bude" yamatsa gefe dawani kalan sauri Ammi hartana neman tai tuntube ta taho wajen dasauri tace "Daddy lafiya su waye wayan nan? Lafiya" tai maganan tana karasa jawo kofan, wani kallon tsana yama Ammi batare daya kulata ba yace "kai Lasdon bude kofan nace ku shiga ku daukota muje" arude Ammi tawani sha gabansu tace "tsaya ban ganeba wa za'a dauko? Mesa kake aika mazan daban sani ba zuwa cikin turakata kasan munada yara mata idan basu da sutura ajiki fa"? Ammi tai maganan tana kama hannun kofan gabanta na faduwa sosai, ran Daddy yafara baci yanunata da tsaya yace "ki kiyayeni Haleema, Haleema ki kiyayeni, ko tsirara mahaukaciyar yarki take I don't care, sabida akwai dubu irinta dake yawo tsirara a titi, yau saita bar gidana ta koma asibitin mahaukata, tunda haukan nata haryakai matsayin tana neman daukan rai, tana neman kasheni, ijiye yara irinsu a gida mummunan hadari ne ga alumma, inada yara kanana bazata halakamin gidaba dan haka ki matsa ga maza nan nakawo su daukanmin ita muwuce asibitin mahaukata"tunda Ammi take bata tabajin tsoro ya shigeta ya ratsata irin na yau ba, amman tadaure tace "Daddy nasan abinda tamaka jiya bata kyauta ba kuma duk bisa kuskure ne amman dan Allah kayakuri ka sallamesu su tafi idan yaso saika hukuntata anan kaji, amman mazan nan su dauketa akaita asibitin mahaukata duk bashine daidai ba ayanzu, wlh batada lpy yanzu nan muka dawo daga asibiti bacci ma take, tun jiya sai yanzu tasami bacci, na rokeka da girman Allah ubangijin daya hallicemu kayakuri kaji" wani shegen kallon fitina Daddy yama Ammi sannan yadaki bango yace "kinga Haleematu ko kinaso ko bakiso yoh ke ko zaki mutu anan naga walakiri na zaran ranki Billahillazi saina aika yarnan asibitin mahaukata itada gidana har abada, tagama zama gidana, taje chan cikin yan uwanta mahaukata tayi rayuwa, mahaukata irinsu masu kisan kai ba'a barinsu rayuwa agida sai asibiti dan haka tun ina miki bayani dalla dalla kitashi daga jikin kofan nan inba hakaba zanyi mummunan saba miki"Ayanda Ammi tasanshi tasan yanda baison Amirah bazata taba yarda da abinda zaiyi ba, ahankali tace "idan na dauketa muka barmaka gidan ka fa?" Wani dariya yayi yace "nan ne kuma zan gwadamiki ubanki yayi kadan! Tunda bakene ubanta ba kowani hukunci na yanke akanta daidaine, Kai ku shiga ku daukomin ita" Ammi ta tsaya gaban kofan tai ihu cikin dakewa tace "babu wanda zai tabamin diya, Baban Baby wai menene haka"? Hayaniya da Miemie taji yasa takashe pampo da sauri tana goge fuskanta taji muryan Mami na ihu da Daddy dasauri tabude kofa tafito tafito daga dakin ganin maza saida gabanta yafadi dasauri takalli Ammi tace "Ammi" Ammi juyowa tayi ta kalleta ba hijabi kanta ba hula tace "koma daki ki dauko mayafi maza Maryama" kasa motsi tayi kukan datake rikewa tafashe da shi takalli Daddy cikin kuka tace "Daddy maisa ka tsani maman mu eh? Meta maka ne? Karabu da ita idan baka sonta kadena azabtar mana da Maman mu D……" Maryam! Ammi tadaka mata mugun tsawa dayasa Amirah ta firgita tare da bude idanunta ras dasukai ja cike da bacci alluran da aka mata harda na bacci cus masu mental issue haka na bukatan bacci, Ammi tace "Babanki kikema magana haka?" Daddy yace "ahap kungani ba, she poised my daughters mind against me, one tries to take my life yesterday and the other is insulting and abusing me yanzu, kinga tarbiyanki Haleema you see!"Jin muryan Daddy wani kararrawa kan Amirah yafara bugawa, tana ganin jiri tashiga tashi all abinda ke zuwa kanta is Mamanta is in danger tashiga kalle kalle adakin tana neman abinda zata dauka babu wani makami the only thing idanunta suka gani is slippers kawai tadauki slippers tashiga tafiya bakinta na furta Ammi Ammi Ammi ahankali da bazama ka iyaji ba, Ammi na tsaye jikin kofan kawai taji an bude kofan dawani irin sauri tajuyo kowa ma yajuyo Amirah ne daga ita sai gown na jikinta ga gashinta ya zubo tana rike da slippers tadaga hannunta sama Daddy na ganinta yakoma baya dasauri Adan tsorace, Ammi tai Maza takama hannunta tace "Ami…." Fizge hannunta tayi daga rikon da Ammi tamata tawani yunkuro zatai kan Daddy yakoma baya again dasauri yace "kungani ko, kun gani, kasheni takeso tayi ku kamata nace" dasauri Ammi ta fizgo Amirah tana kaita baya kawai maza ukun sukayo kan Ammi data wani tsorata ta tura Amirah cikin daki zata rufo kofan kawai gardi daya yawani fizgo Ammi ta watsar jikake jagab atare Amirah da Miemie sukai wani ihu sabida mugun faduwa da Ammi tayi zube a tiles goshinta ya tsage jini dudda haka ta yunkuro zata taso amman ina kawai takoma kasa a sume warwas, dawani irin gudu Miemie tayo wajenta itama Amirah tafito dagudu zatayi kan Ammi kawai chak namiji daya ya chapketa, tai wani ihu dayakusan tsaga gidan. "Ahhhhh!"Miemie dake kan Ammi tadago tama rasa mezatayi ga Ammi sume akasa ga Amirah maza sun dauka tana ihu da top of her voice tana wuntsila kafa tana tokare duk wanda karfinta yakai tana yakushi da Cizo tana kururuwa tana kallon Ammi dake kasa a sume, ganin tana neman gagaran bouncers din Daddy yace "ta haukace sosai jama'a bari nakawo igiya ku kulleta"Daddy yajuya yafita dasauri Amirah na kokawa dasu tana ihu da duka muryanta, saiga daddy yadawo da igiyan shanya, yabasu kwantar da ita sukai kaman rago suka hade hannayenta suka take saida tai wani irin kara na azaba, Miemie tasaki Ammi tazo wajen tana kallon yar uwarta takalli Daddy dayake basu instruction na yanda zasu kulleta asanyaye tana hawaye tace "Daddy is it because she's not your biological daughter?" Dasauri Daddy ya kalleta saiyawani taso azafafe yayo kanta yana huci yace "repeat what you said? Inaso akaita gidan mahaukata before she kill me or even you and look at what you're saying stupid girl"ahankali tace "Daddy is it because she's not your biological daughter?" Tassss! Daddy ya dauke Miemie da Mari yana ihu how dare you? Ni kike ma rashin kunya? Amirah takara ihu ganin Daddy na Marin Miemie, Cikin kuka Miemie tace "this girl is the daughter of your own late brother uwa daya uba daya, Daddy all this wealth including this house da motan dakake tukawa duka gadonta n…" Mari Daddy yakaima bakinta akaro nabiyu yace "shut up! Ni kikema rashin kunya, wlh zan kira family su Umar na gayamai na fasa auren naku fitsararriya kawai" ya hankadata daki yarufo kofan yana murza key, Miemie tana ihu tana bubbuga kofan, Daddy yawuce inda Amirah ke ihu har lokacin tana kallon Ammi sun daureta tana ihu yace "ku dauketa muje" daukanta sukayi suka fice da ita tana ihu with top of her voice tana kokawa da duka power ta idanunta sunyi jajir kaman wuta gashinta ya barbaje yama rufe fuskanta gabaki daya kanta nawani irin sarawa suka jefeta a bayan mota maza biyu abaya daya a gaba Daddy na tuki sai asibiti.
Tunda suke motan bouncer daya dake baya dake right side nata yake kallon Amirah yanabin duka jikinta da kallon in his entire life baitaba ganin kyakkyawar mahaukaciya like extremely extremely super beautiful mahaukaciya like this girl ba, she looks like an Arab with her hair, skin dinta is so soft, batada kiba she's skinny but tanada wani irin curved hips da full ass ga boobs cike tam a kirjinta dake jiggling sosai tsayayyu, skin dinta so fresh kasan bata wahala she's so damn sexy, kawai take gabansa ya mike dawani irin sauri ya kalli gaban motan da dayan bouncer na side din yake danna wayansa abunsa, yay maza ya harde kafafunsa hannunsa na kaikayi yana rawa yasauke idanunsa gaban kirjin riganta dan boobs dinta na bouncing sosai sabida kokawa datakeyi har lokacin tana kokarin kwance kanta, ga bakinta dasuka sakama handkerchief dan ta ishesu da ihu, ahanakali stylishly yashiga kai hannunsa yana kallon kowa na motan zai taba mata kirji daidai Daddy na juyowa yakallo baya yace "mahaukaciyan tai shiru" dasauri bouncer yamaida hannunsa back bawanda ya lura, ahaka sukakai hospital din.
Daddy yayi parking duk suka bude motan suka fito boucer yawani fizgota kaman yana fizgo akuya taji wani sharp pain ajikinta da hannayenta da kanta, taji cikinta na ciwo, itama ga karfin hali sai kokawa take dan duk ta daburce ta dimauce ganinta dasu duk bata sansu ba, sai mutsu mutsu take, Daddy na gaba suka shiga cikin asibitin anan reception babu mutane sosai dasauri Nurse dake wajen sanye da uniform kafinma suyi magana tataso tace "ammm please untie the patient and remove the clothes from her mouth Sir" cikin fushi Daddy yace "Malama don't tell me what to do, can't you see my head she bites and injure people she's a total lunatic" nurse din tace "dudda haka please untie h….." "ke don't tell me wat to do nakawo ta ance asibitin kyauta ne kuna neman mahaukata, gatanan kisan kai take tuburan tuburan, Allah ne ya kaddara inada kwanaki agabana da jiya anmini jam'i na janaiza, I can't watch her kill people in my family I have other kids, kananu yara , she's a threat to me and my family dan haka kuyi admitting dinta for as long as she gets better"respectfully nurse din tace "still Sir untie her first before all the formalities" ran Daddy abace kaman yarufe nurse din da duka yakalli boucer yace "kwanceta".
Tunda suka shigo reception din yake kallonsu ta window wani emergency room dayake dake first floor treating wani male patient nasa, yaga an shigo da wata yarinya da he can't see her face dan gashi yacika mata fuska but he saw yanda suka kukkulleta akasa tsumma abakinta, and he heard what the man was saying. yana tsaye daga jikin window yaga boucer ya duka yana kwance igiyan kafanta harzai dauke kai saiyaga boucer yadaga kasan gown dinta kaman zai leka saiya fasa yadan juyo yana kalle kalle kaman mara gaskiya, chak ya tsaya anytime yaga mutanen that loves taking advantage of masu matsalan kwakwalwa he knows, he had many cases da ake kawo mahaukata masu ciki, he wonders wat does people gain by taking advantage of someone that is mentally unstable duk masu halin nan deserve death as punishment wlh, ahankali yabude kofa yashiga fitowa yana tafiya one one without making a single sound, ganin babu hankalin wanda ke kanshi batare daya kwance hannunta ba yakai hannunsa dasauri zai daura saman boobs dinta dake moving sabida yanda Amirah ke motsi trying to free herself chak yaji an rike hannunsa dawani irin sauri yadago kansa ido da ido yayi dawani hadaden Dr dake sanye da glasses da labcoat yana wani irin kamshi mai bala'in dadi, mummunan faduwa gabansa yayi sai yayi murmushi awayance yace "cewa akayi na kwanceta Dr" babu ko alamun rahama atattare dashi yaki sakin hannunsa kuma baice masa kalaba boucer yashiga kokarin fizge hannunsa sabida azaba dayaji amman duk karfinsa na boucer yakasa yayi wani ihu jin zai balla masa hannu. "Ahhhhh!" Hankalin kowa yadawo kansu, saida Marwan ya karya yatsansa daya tass boucer yayi wani ihun azaba Daddy yazı wajen dagudu yace "kai lafiya Dr yahaka? Are you guys okay kuwa a asibitin nan? Ko kuma mahaukatan ne" Marwan yasaki hannunsa tareda dauramai wani lafiyayyen mari da saida yayi tangal tangal zai fadi cikin zafin murya yace "call the securities I need this man arrested and charge to court for attempting to take advantage of a patient" before kace a saiga Kamal dasauran security su biyar sun shigo an kama boucer, Daddy yace "Bangane ba ahh likita tareda ni yak….." hannu Marwan yadagama Daddy ransa amasifan bace alamun baison maganan wlh saida Daddy yaji tsoro, strictly yanuna Amirah yace "you said she's a patient and you are treating her like an animal" dasauri Daddy yace "of course i have to, she's violent she tries to kill m…." Rudely Dr Marwan yace "get her details from him and send him out of my hospital immediately! I don't care who you are to her" tunda Daddy yake in his life baitaba ganin mara mutunci likita like this one ba, abun yabasa mamaki.
Sai yama kasa magana, Marwan yajuyo saiya duka gaban Amirah ahankali, hannunsa yakai gently yazaro tsumman daga bakinta ya ijiye ya tsaya yana kallon fuskanta baya ganin fuskanta da kyau banda bakinta da pink lips dinta yanada kalan numfashin datake dayake fita akarkace, she's tense, she's in panic mode, her breath is very hot too she's running temperature, saiya ya tsare lips dinta dake motsi da kallo wanda direct yagane metake furtawa. "Ammi….Ammi….Ammi…." Sauke kansa kasa yayi yakai hannunsa gently yana warware daurin igiyan hannunta, hannayenta sunyi ja sosai sabida daurin, kaman jira Amirah take dudda kanta na sarawa yana bugawa amman Marwan na karasa kwance hannunta tamike tsaye da sauri sai baice mata kala ba tabi ta gefensa ta wuce riganta na shafan jikinsa tashiga tafara tafiya dasauri sauri tana numfashi sama sama tayo kan Daddy, abala'in tsorace Daddy yace "nurse nurse kuriketa mana" nurse tai banza da Daddy, Daddy yakalli boucer biyun yace "kuriketa" strictly Marwan yace "if any of you lay a hand on my patient you will go to prison as well duk suka tsaya" gabbage can Amirah tadauka tawani kalan bi Daddy da gudu ta kurma ihu Marwan yayi folding hannu yana kallonta, Daddy na ihu sosai yace "wlh zata kasheni, help me guys" yanda Daddy ke gudu tana binsa Daddy baisan sanda yace "likita, Dr Dr, Dr" amman ko ajikin Marwan, wani kallo yama nurse hakan yasa takawo mai wani tray da wani allura guda daya ke kai daidai sunzo ta side dayake kawai Marwan ya tsaya gaban Daddy hakan yasa Daddy ya tsaya Amirah ta risko Daddy batai wata wata ba tadaga gabbage can din zata bugamai hannu daya Marwan yasa yarike yace "no, cizo zakiyi" Daddy yawani kwalalo idanun tsoro ganin ikon Allah yau yaga likita mahaukaci aiko Amira ta gantsarama Daddy cizo a hannu Daddy ya tsala ihu yakai hannu zai daketa gently Marwan yakama hannun daddy yarike ya ijiye bin din yasa dayan hannunsa yamata allura a gefen wuya tanakan cizon Daddy, ko sakan biyu ba'ayiba tai bacci. Nurses suka gunguro gado aka kawo wajen suka jayeta daga jikin Daddy aka sata agado, Dr Marwan yace "room 424" sannan yakalli Daddy dake kallon inda Amirah ta cijesa kaman zaiyi kuka yace "thanks for the help" cikeda fada Daddy yace "help of wat? Kabata jikina ta ciza sabida kamata alluran chan? Is that what you do here? Wani kalan likita ne kai dabakasan me kakeba" wucewa Marwan yayi batare daya kulasa ba, ran Daddy yayi matukar baci baitaba ganin dan iskan Dr irin wannan ba, nan da nan yaji kawai ya tsanesa, nurse tace "Sir I need you to sign some forms pls". EPISODE 7️⃣
Rai abace Daddy da har lokacin dukan kirjinsa bai dawo daidai ba sabida tsoratan dayayi yace "rainin hankali kawai, sabida kana likitan mahaukata sai kaima kazama mahaukacin da gangan fa yatareni yabari takamani ta cija, saura kiris fatana ta fice, hakora uwa na vampire" dan dariya Nurse tayi sosai tace "Yallabai Dr Marwan study our patients, he thinks like them sometimes, he understands them, if there's one thing I can say is kama patient namu laifi, he understood that and let her take revenge" cikin fada Daddy yace "maganan banza maganan wofi waye ubansa eh, yasa an kama mini bouncer yasa a chijeni" Nurse ganin da gaske masifa mutumin yake yafara bata haushi, sufa ma'aikatan asibitin gwamnati mutuncin su ragagge ne, tace "koma kai waye his patients comes first, once kuna cikin building dinnan our patients comes first kafin kowa, and duk wanda yatabasu Dr Marwan stand for them, all the patients loves him, zancen ubansa kuma ka shiga ward kaje ka tambayesa, please fill in this form and sign, zaka biya 50k kuma shine kudin da ake biya on patient da aka kawo for admission"dawani irin sauri Daddy ya kalleta kaman miliyan hamsin tace, yace "50k naji kince, ba free bane gwamnati tafadi" nurse tace "yes it's free amman you need to pay 50k na bed fee na 10days each day 5k that's not free Sir" Daddy yayi shiru sai bai kara magana ba, yasa hannu ya karbi takardan yana rubuta komi da komi yayi signning yamikama nurse din ta karba tace "that office is account office kaje kabiya ka kawomin receipt" gyadamata kai yayi yace "bari na dauko kudin a mota" yajuya yayi waje voucher suka bisa nurse na kallonsa yabude mota yashige yatada motan abinsa yaja nurse kafin ta taho yafice daga gate din yace "nida ku kara ganina har abada wlh wlh" yaciro 100k yana tukin yaba bouncers yace "ga kudin ku shikuma wanchan kuje police station duk yanda ake ciki ku sanar dani".
Mamakine yakama nurse din ganin yatafi, but somehow she refuse to believe cewa Baba zai bar yar karaman yarinyar sa a asibiti batare daya biya kudin komiba, maybe yaje ciro kudinne, takoma tana duba all the details daya bada a form din, taga this exact patient with same information tazo dazu da safe ai, Nurse Rasho ke morning ta tafi gida hakan yasa saita dauko file nata na safiya tafito tawuce dakin emergency da Dr yake. General asibiti ne so obviously is a big hospital, amman psychiatrist building dinnan dayake UNICEF sunyi renovating wajen kaman akasan waje, akwai jeren dakuna da numbers haka daki daya na facing daya kaman hotel, dakunan yawanci ana saka dangerous patients ne, da masu yin tsirara da sauransu, saikuma akwai ward na mata dana maza wajen ana ijiye patients that are not harmful patients nada yawa in a ward zaka iya ganin 10, 8 dasauransu, saikuma akwai main hall da kujeru ana fito dasu su zauna suci abinci ga tv asamusu kallo, akwai classes kuma, music class, educational class saikuma bathroom nasu na maza daban bangaren daban na mata daban bangaren ma daban, akwai single single toilet saikuma dogon bayi da akayi kaman irin na yan hostel dinnan, sunada compound da play ground dakuma garden, ga ma'aikata ta ko'ina, akwai cleaners, care takers masu assisting patients da basa iya komi ma kansu, aikinsu is gyara patients din, musu wanka chanza musu kaya da sauransu, ga nurses, ga Doctors.
Ahankali tai knocking kofan tabude Dr Marwan naciki tareda wani elderly patient babba haka yana sanye da uniform na asibiti ga paper a hannunsa yana wasu yan rubuce rubuce Dr Marwan na tsaye yana paying attention to rubutun bayako dauke idanu, tace "Dr you need to see this" batare daya dago kansa ba yace "go ahead" ahankali tace "I think this patient was here this morning Aminatu Adamu, Mamanta takawota dasafe an mata allura ma aka bata magani, and Babanta ya gudu yanzu batare daya biya kudin bed ba, what should we do? Muyi admitting nata still cus yace bari ya dauko kudi a mota yatafi" Har lokacin Marwan kallon rubutun da mutumin yakeyi yake dasuke nan a jujjuye daidai yagama rubuta yawani kwashe da dariya yace "Dr M sunana kenan Isuhu Muhammad Kwari"dan murmushi Marwan yayi yana karban paper wanda abunda yarubuta baida alaka da sunansa at all ga rubutun a jujjuye yace "good job Malam Isuhu" mutumin yasake fashewa da dariya harda tafi yace "nafi kowa iya rubutu ko Dr? Kasan zamanin nan Wole Soyinka wannan novelist din classmate dina ne" Marwan yace "yess yess you told me yesterday, now I want you to do even better tommorow okay, gobe you will write about your family" yanuna masa book dake kan gadonsa yace "karubutamin anything daka tuna aciki nazo zan duba", patient din still yana dariya irin na marasa kan gado yace "okay Dr M" yamika masa hannu yana dariya, hannu Marwan yabasa without any fear yace "idan an kawo maka magana take it, don't trouble my nurses okay" yana dariya sosai yace "okay Dr M" karbe hannunsa Marwan yayi yajuya yafice daga dakin nurse ma tafito tai danna wani bottun dake locking door din sannan tabisa abaya, Marwan na tafiya yamika mata hannu alamun tabasa file na yarinyar, dasauri tabasa, karba yayi yana dubawa, sai kawai yacigaba da tafiya Nurse Nucy tace "still mu kwantar da ita batare da yabiya kudin gadon ba Doctor?" Shiru yayi kaman bazai magana ba sai chan yace "do you have anyway to send her?" Shiru Nurse din tayi saitace "a'a" calming Marwanyace "focus on her health do your duty that's the most important thing" ya kalli agogon hannunsa yace "she will wake up in the next one minute let's go"yawuce nurse Nucy na binsa abaya zuwa single room ward wanda nan aka kwantar da ita, agaban dakin ya tsaya ya danna botur dake unlocking door sannan yabude kofan yashiga dakin, bed ne acikin dakin sai bayi da shelf na just few book that are educational book da small couch na zama, Amirah na kwance akan gadon, gashinta yarufe fuskanta, she looks very innocent dudda ba'a ganin fuskanta, dan dakatawa Maryan yayi daga wajen kofan ya tsaya, ahankali yace "remove that attachment from her head" murmushi Nurse Nucy tayi tace "I think is her hair Dr" daga inda yake yakalli gashin sosai sai baimasan mezaiceba kawai yadauke kai, kaman nurse din ta lura tace "bari ayi parking gashin na tattare sa gu daya" akwai hair band a wrist nata sai kawai tazo wajen tadan dago Amirah dataji batada nauyi ta tana tattare gashin daga gaban fuskanta, file nata yake dubawa amman hakanan yaji kaman abu na fizgansa, kasa daurewa yayi saida yasan matsar da folder ya daura idanunsa akan fuskanta she literally looks like a baby a hannun Nurse Nucy dake kwashe gashin nata, bugawa kirjinsa yayi dum! Saiya dauke kansa ya maida kan folder. Maida ita Nurse Nucy tayi ta kwantar saita tsaya kallon fuskanta cus yanzu ne fuskan Amirah yafito da kyau, tunda take in her life bata taba ganin kyakkywan yarinya mahaukaciya irin wannan ba tunda tafara aiki as a psychiatric nurse, funny enough all patients dasuke dashi on admission this girl is youngest, yawancin mata mahaukata dasuke dashi yan age 30 upward ne, youngest patients nasu is 31yrs, this is the first karaman yarinya mahaukaciya dasuke samu in the hospital, "What are you doing?" Taji muryan Dr da babu wasa ko daya aciki, dasauri Nucy tajuyo takalli Dr Marwan daya jefomata tambayan takallesa rubutu ma yake da pen tarasa ma mezatace dasauri takoma baya tana barin jikin gadon tace "ahh sorry Dr, dama daman naji she's running serious temperature ne" shigowa dakin yayi da kyau zuwa wajen gadon ya ijiye folder nata yamakala sthethoscope a kune yakama bakin saiyadan kalleta gabansa yasake fadi amman saiya dake like the man he's yadaura sthehoscipe din a wuyanta batare da one single finger nasa yataba fatan jikinta ba, daidai idanunta sukai motsi yamaida kwayan idanunsa kan fuskanta, ahankali Amirah ke bude idanunta jin sanyi dataji a wuyanta, kadan kadan take bude idanunta, dan jikinta yamutu sosai, jikinta yamata nauyi kaman banata ba, batada karfi ahankali take bude idanunta kwayan idanunta na motsi kadan kadan, dogayen gashin idanunta suma suna motsi trying to open, lips dinta ma dasuke very pinkishi kanana na motsi, gashin goshinta a kwance sosai, hannunta tafara dagawa da kyar cus batajin karfi jikinta kaman ba nataba, sanyi dataji awuyanta yasa kai tsaye takai hannunta tadaura saman kan hannun Dr Marwan dake rike da bakin sthethoscope din daya saka a wuyanta while idanunta na motsin kokarin budewa, wlh yafara medical school at the age of 17 daidai a UK, tundaga rannan zuwa rana tayau baitaba having any form of body contact da any patient datasa kawai yaji kirjinsa nabugawa ba sai yau, and he doesn't know why, faduwa gabansa yayi rasss! Hannunta feels extremely warm, soft and tafin hannunta palm nata were so sweaty dayasa yaji sanyin dumi da lema saman hannunsa, instead of tasaki hannunsa saita kara rike hannunsa gam idanunta na motsi sosai tana bude idanunta duka but not wide open bakinta na furta. "Ammi!" Cikin wata yar kankanuwan karaman cool sexy baby bedroom naked voice daidai kuma tana karasa bude idanunta dasuka dan mata dishi dishi kaman bata gani, ita and a new born baby basu da wani much of a difference, ko kadan Marwan baiyi motsi ba cus he wants to gets her heart beat especially idan tai recognizing condition da situation datake ciki, daura manya manyan idanunta gajiyayyu that looks very lazy tayi akansa, da farko dishi dishi take gani but slowly idanun suka fara washewa taga wani kyakkywan mutum da farin glasses ke kan idanunsa yana kallonta, yana sanye da farin labcoat ajikinsa bugawa kirjinta yayi kanta na wani ringing bell tana tuna komi daya faru tundaga jiya zuwa yau, kaman taga dodo tawani irin kulle idanunta ta yunkuro zata tashi da kyar dan ba karfi alluran daya mata na slowing karfinsu down, tazare hannunta dake kan nasa da sauri tareda ture nasa dake jikinta ta kabar da hannunsa da bakın sthethoscope din zata taso saiya matsa ahankali taking 2step back ya tsaya batare dayace anything ba.
Cikeda karfin hali Amirah ta sauka daga gadon da saita jujjuya tanabin dakin da kallo kwata kwata batai recognizing environment datakeba, bataga Ammi ba, bataga Miemie ba, saitin Dr Marwan ta kalla amman bata dago kai takalli fuskansa ba wani tsoronsa taji tanaji saita duka ahankali sai kawai tashige karkashin gadon tai facing bango jikinta kawai yahau rawa, zuciyanta da kirjinta na bugawa, taji kawai batada kwanciyan hankali tahau yarfe hannu bakinta na motsi tafara murza hannayenta a cinya lips dinta na motsi tana kiran Ammi da bama'aji at all. "Ammi! Ammi! Ammi!". EPISODE 8️⃣