Baccin so complete by m shakur - Chapter 5
Baccin so complete by m shakur Chapter 5: Baccin so complete by m shakur Chapter 5. Ahankali yadan sauke ijiyan zuciya gently yace "bring her food and…
4,108 words
Ahankali yadan sauke ijiyan zuciya gently yace "bring her food and snacks" dasauri Nurse Nucy tace "toh" saita juya ta tafi, zare stethoscope din Marwan yayi daga kunnensa yatura a aljihun labcoat dinsa saiya duka ahankali daidai gaban gadon dasauri Amirah takara mannewa da bango jikinta na kakkarwa tana murza hannayenta sosai, calmly yake kallonta dudda ta sauke kanta kasa gabaki daya, her lips are moving tana wani irin strange wasa da fingers nata na nervousness, tana mummurza hannayen, ahankali very calmly da tattaushiyan murya trying to get her to calm down yanuna kansa yace "My name is Dr Marwan!"yayi dan shiru yana kallonta, yakara tausasa murya yace "I am here to make you feel better"yayi shiru yana nazarinta nothing changes in abinda takeyi, sake rage murya yayi yace "I will not hurt you and nobody will hurt you here, can you tell me your name?" Duk yayi maganan yana kallonta, reaction dinta ma doesn't look like tamasan akwai wani awajen banda ita, kaman batasan Allah yayisa awajen ba and yasan taji komi, ahankali yace "Kinsan sunanki"? Still shiru, dan ijiyan zuciya kadan Marwan ya sauke, da voice na nuna tsantsan kulawa yar karama yace "meke miki ciwo yanzu"? Still shiru Amirah taki kallonsa but tanajin komi yake cewa kirjinta kawai ke bugawa, gawani kamshi dayakeyi dake shiga hancinta wanda takeji kaman tabude baki taci kamshin sabida yanda kamshin keda dadi, daidai lokacin nurse tashigo da tray na abinci rice and stew da egg, sai bowl na fruits, da bowl na biscuits tazo wajen ta duka tace "ga abinci Dr" hannu yasa yakarba yakalli abincin sai yadauki spoon din yajuya rice din da stew din sannan ya kai abincin gabanta ya ijiye yana kallonta yace "eat"wlh kaganta zaka rantse batamasan akwai mutane awajen ba, Nurse tace "ohh my God, non verbal patient are the hardest to deal with Dr"If there's one thing he's sure of is bazata ci this food ba no matter what, gashi tasauke kanta kasa hannunta kawai ke rawa and he's hearing the sound of her breath which is not really clear she's tense, mikewa yayi ahankali saiya dauki iPad dinsa yayi rubuce rubuce yabama nurse din yace "get everything from the pharmacy" gyadamai kai tayi saita wuce tafita shikuma saiya tsaya ya dauki folder nata yabude yana karanta condition dinta again for the second time tunda aka kawota, she's sick, she's traumatized, she's non verbal all 3, but this morning Mamanta bata yarda ya kwantar da itaba why in the evening Babanta yakawota dawasu kattai a daddaure? Her Mother doesn't look like wacce zatabar maza su kakkama mata yarinya haka, kaganta kasan she protects yarinyar nan with everything she got, did something happen to her Mom? Is that what triggers her? Saiyadanyi shiru yakalli karkashin gadon, he doesn't wants to think much, all that matters is his patient not her family, he will do everything he can to help her, she needs food if she's refusing to eat he needs to go for option B abata abinci ta drip cus she needs treatment this temperature and everything ya sauko kafin yafara treating underlining condition nata which is her mental issue.
Yana tsaye awajen nurse din tashigo da everything daya aika wani bell dake kusa dashi ya danna within seconds saiga wata babbar kosasshiyar katuwan mace sanye da uniform tace "Dr M which patient do you need help with? Naga you paged me"? Karkashin gadon ya nunamata dasauri tace "Ohhkay let's see what do we get here"saita wuce taduka karkashin gadon tana kallon tray na abinci tace "laaaaaa bataci wannan abincin mai dadi ba"Nurse dake tsaye gefenta tace "bataci ba Iyawo" Iyawo tadauki plate din tamikama nurse din ta karba sannan takalli Amirah datake kara matsawa tana mannewa da bango Iyawo tamika hannunta tace "zo kinji we will take good care of you here don't be afraid uhnn Pretty girl"tai maganan daidai tana daura hannunta kan cinyan Amirah, Amirah ta kurma ihu kaman wuta ya tabata. "Ahhhhhhhhhhhh!" Marwan ya kallesu, ta wuntsila kafafunta takai hannunta zata cire hannun Iyawo, cikin asalin experience Iyawo takama hannu kawai tashi daya tajawo Amirah tana murmushi Amirah na kokawa da ita, Iyawo tadagata Amirah takara daburcewa tahau ihu sosai ihunta kaman zai fasa musu kunne tana kokawa gashi batada karfin ma, hakan yasa Marwan yajuyo yakallesu ahankali yanda Iyawo tadagata kaman yar baby tadaga, daurata tayi akan gado, tawani dirko daga gadon Iyawo zata kamata ga mamakinta kawai tai kan Marwan agigice zata fada jikinsa, baya yakoma dasauri Amirah tayo kansa zata shige jikinsa dawani irin sauri Marwan yakawo hannunsa gaba strictly yace "ke!" Chak Amirah ta tsaya gabanta na faduwa saita koma gefensa ta tsaya dab dashi takai hannunta takama kasan rigan labcoat nashi tarike gam tana numfashi da sauri da sauri kaman kirjinta zai fito, daga Nurse har Iyawo suka kalli yanda tarike labcoat din Dr da yanda ta tsaya a gefensa looking petite. Ahankali yashiga tafiya batare daya sa tasaki rigansa ba har zuwa wajen gadon tabiyosa gadon ya nuna mata yace "sit" ahankali Amirah ta zauna tana rikeda labcoat dinshi sosai, cikeda lallabawa yace "bani hannunki" ko kallonsa Amirah batayiba balle yasaran zata basa hannunsa, batare daya kalli su Iyawo ba yace "I need her hand" matsowa Iyawo tayi wajen ihu tayi sosai Marwan yabata hannunsa daya saka gloves yace "give me ur hand then idan bakiso ta tabaki" boye hannunta tayi abaya cus ta tsani anything allura hakan yasa Iyawo tazo wani tasowa Amirah tayi zata fado jikinsa dasauri yadan matsa baya Iyawo takamata wani irin ihu take tana kokawa zata fita daga jikinta, Iyawo tace "kina tsoron allura, hannun Dr ba zafi, tsaya amiki kihuta kema kiji sauki kinji yarinya" gyaramai hannunta Iyawo tayi tace "you can do it now Dr" takowa yayi yamatso this time bai kalli fuskanta ba dan baiso tabasa tausayi ahankali yasa alluran yadan kalli fuskanta tama rage shure kafa tagaji sosai kuma da alamu bataji zafi ba, sai ijiyan zuciya take gashin goshinta ya mammanne sabida zufa datayi daga dan kokawan datayi, dauke kansa Marwan yana setting drip din yayi yace "can you get her a cap for her hair, idan tai bacci change her to hospital uniform" Iyawo tace "toh Doctor M" within few minute ya gama fixing mata drip yasa allurai a ruwan duk Iyawo na rike da ita tadena ihu amman sai numfashi take sama sama tana wani irin ijiyan zuciya dake fitowa sosai irin na yanda yara suke, Marwan yace "kwantar da ita" kwantar da ita Iyawo tayi Amirah ta kwanta lamooo idanunta na lumlumshewa, Iyawo tadan leka fuskanta tace "she's asleep lemme get her uniform da cap" saita wuce tafita, ahankali yakai hannunsa saitin hancinta yana kallon agogon hannunsa yana noticing breath nata murya chan kasa yace "you need to calm down" yayi maganan still hannunshi na wajen yanason nunfashinta ya daidaita, lumshe idanunta ruff tayi numfashin yakoma yana fita ahankali hakan yasa ya maida hannunsa yadauki folder nata yayi rubutu sannan yajuya yafita daga dakin yashiga another room, daya daga cikin ma'aikatan dake aiki a wajen tace "don't tell me yanzu wannan ma da Babanta yakawota yagudu Dr M ne zai biya kudin?" Dayan tace "shine mana, da a komar da patient gwara yacire kudi daga aljihunsa yabiya wlh bantaba ganin selfless Dr irinsa ba, yau shekaru kusan 20 ina aiki a asibiti" duk sukai hmm suka wuce.
Wajajen magrib Marwan yafito daga office nasa yadauro alwala, idan yatafi sallan magrib baya dawowa, ward yashigo direct 441 yashiga yana bude kofa ahankali, night nurse yagani tanama drip da ke shiga jikinta next injection daya rubuta amata at that time, an chanza mata kaya zuwa blue uniform dinsu wanda yake riga da wando an dan rufa mata bargo sannan an saka mata wani dark blue hula daya zauna akanta yayi kyau, kallo daya yama fuskanta hakan nan kawai yasami kansa da cire idanunsa daga kanta da sauri, ya makala sthethoscope a kunnensa yana duba pulse nata sannan yakalli nurse din, yace "I will be going home now be checking on her after every 30min, if anything come up akirani" dasauri tace "yess Dr, saida safe" baicemata anything ba yajuya haryakai kofa ya tsaya saiya juyo yadan kalleta sannan ya kalli nurse yace "get blanket from my office cover her" dasauri nurse din tace "yes sir"yajuya yafita tabisa da kallo tama mamakin meya sami dan karamin zanin gadon da aka rufa mata dayace adauko bargo daga office nashi, are they related? Saikuma ta kauda tambayar tawuce tafito he never lock office nasa hakan yasa ta shiga wani bargo mai kyau da taushe na Hermes ne akan kujeran sa sai ta dauka tafito daga office din. EPISODE 9️⃣
Masallacin yashiga yabi jam'i akayi magrib sannan yafito yashiga mota, yadanyi jimmm kafin yakunna motan yaja, baya wani gudu sosai, tsayawa yayi wajen fruits yasaya dayawa kwallo kwallo aka lodamai a booth sannan yaja motan, koda yakai unguwansu it's already isha'i time, ya tsaya yayi sannan yadawo yaja motan yayi horn aka budemai gate ya shiga ciki, parking yayi gateman din yazo wajen motan da sauri kafin yabude yarigasa bude masa yace "sannu da zuwa Dakta" murmushi kadan yamasa, Musa yace "Dr kaga kaman dan kankare naso yakamani hannun sai zugi yakemin mezansha"? Anatse Marwan yakalli dan yatsun dayake nuna masa daya kumbura sai yace "kanada ciwo haka tun safe maisa baka sanar dani ba"? Cikeda fara'a yace "banso na dameka ne Dakta, dan karamin ciwo haka sainaita raki kaman mace"Marwan yasake kallon hannun again saiya koma mota yadauko wani karamin box yabude, wani katin magani yabasa yace "kasha biyu yanzu biyu da safe, idan baiyi sauki ba zan tafi dakai hospital gobe, and kaje ka kwanta don't work again" murmushi sosai Musa Allah yasani yana son bawan Allahn nan Marwan yace "nagode Dakta"juyawa yayi zaitafi Marwan yawuce a natse yabude booth din bayan motan yashiga ciro fruits din zai dauka kaman ance mai hadin yajuyo dasauri yataho yace "laaa bari na tayaka Dr" wani kallo Marwan yamasa yace "wuce kaje ka kwanta kahuta" baiyi musu ba yawuce yana murmushi sosai, babu wani ma'aikaci da bayason Dr agidan nan, da kansa yadauki all the fruits yawuce babban dankararen flat na gidan yabude kofa ahankali tareda sallama, Mami ne kadai a falon da waya a kunnenta tana magana ganinsa yashigo Niki Niki da kaya saita zare wayan daga kunnenta tace "why are you carrying all of this"? Baice komiba yawuce kitchen ya ijiye yafito Mami tace "ina Musa"? Ahankali yace "I told him to rest yanada Wicklow a hannun"zama yayi kusada Mami saiya dauki plate na abincin daya gani agabanta wanda salad ne yarage da chicken yashiga ci, Mami tace "ga abinci a dinning why are you eating wannan dayayi sanyi" cikin yar karaman murya yace "i am very hungry Mami"tsaresa da idanu Mami tayi yanda yakecin salad din ahankali, ijiye plate yayi bayan ya cinye zai tashi tace "badai bazakaci abinci ba"? Dan yatsine fuska yayi ahankali yace "lemme shower first zan sauko nabaki magani" yayi maganan yana kallon kafanta daya koma normal saiya wuce stairs Mami tabisa da kallo, sama yawuce ahankali yake tafiya kana gani kasan yadan gaji sai kawai ta maida wayan kunnenta tana sauke ijiyan zuciya daga ta dayan bangaren muryan wata tace "Menene Yaya Mami? Naji kina ijiyan zuciya"? Ahankali tace "Marwan ne, he bearly have time for kansa all he does is take care of others, hospital, hospital, hospital, he doesn't do any other thing, baya hutawa, bayama tunanin aure Nafisa" Nafisa tace "to ba idan mun faramai maganan aure kice kaza kaza kaza ba, yaki yayi aure sai kallonsa kike"……
One of daily routine nasa is inhar yadawo before yaje dakinsa saiya shiga dakin kannensa spend time with them cus he's always busy but yadawo dole saiya basu time, he's their uncle, dudda they're just 16 but he respect privacy nasu, knocking yayi kafin yagama knocking din har an bude kofa, daki ne mai kyau da gadaje biyu masu kyau hadaddu, Faiza ce tabude tana sanye da yar rigan bacci data saukan mata har knee kalaba ne akanta tai wani tsalle ganinsa tareda hugging nasa tace "Uncle M welcome, ya clinic yau" bayanta yashafa yace "it's okay where's Farida"? "She's in the restroom" sakinshi tayi tajawo kofan yawuce yana bin dresses daya gani akan gadonsu da kallo yace "who bought this dresses?" Murmushi tayi tace "Mami ne takawo mana tsaraba" daidai Farida na bude bayi tafito daga ita saidan towel pink ta taho da gudu tai hugging dinsa tace "Uncle M kadawo, kaga Faiza has been troubling me ko? Daman nace saina gayamaka" hannunsa Marwan yakai yana share mata kumfan dake kunnenta, Faiza tace "learn how to bath first kafin kidinga kai kar…" Wani kallo Marwan yamata hakan yasa ta hadiye tai shiru kawai Faiza fa fashe da kuka abinma dariya yaso bashi but yahadiye cus yana dariyan kukan zai karu, Faiza akwai saurin kuka tace "kaga wai ban iya wanka ba ko she always bully me Uncle Marwan" shafa bayanta yayi sounding very caring yace "don't mind her, kin iya wanka kumfa a kunne even me it happens to me sometimes so don't cry because of that" yakalli Farida dake murmushi yace "stop teasing your sister okay" Gyadamai kai tayi tace "to nima hug me" hannu yamika mata saitazo dukansu yayi hugging nasu yace "did anything happen today a school ko Islamiyya?" Farida tace "no, revision kawai muke next week Monday zamu fara WAEC, Islamiyya kuma yau anje hutu next week zamu koma" atare sukece "how is hospital today"? Dan shiru yayi kaman mai tunani, atare dukansu suka turasa kan gadonsu ya zauna, Faiza ta dauko chair ta zauna agabansa Farida kuma na nanike dashi suna kallonsa sukace what happen today? Lumshe idanu kadan yayi saiya bude ya kallesu yanda suke kallonsa yace "we got a new patient today" sai yayi shiru, ahankali yace "she's just like Farida" yasake shiru yace "she's gentle, super fragile morethan Farida and she's also so a small girl, she's my first small patient since when I came back to Nigeria, she's none verbal, I have no clue on how to go about her treatment, do you guys have an idea for me future Doctors?" Duk shiru sukayi sai Farida dake rungume dashi ta tashi tace "Uncle kaga in public I hardly speak I only talk at home, mutane na cewa wai bana magana, you see I have two uncle you and Uncle Sam but I hardly talk to Uncle Sam cus he doesn't play with us, my point is idan I see someone that genuinely care for me, he's thoughtful and he's intentional about me just like the way you are very caring I will talk to you" Dasauri Faiza tace "you're right Farida, Uncle M kaga naturally you're caring haka Allah ya yika, I think if you continue like that with her maybe she will open her mouth and talk to you, she will trust you, then you can help her get better, don't just study her study everything that she does read her like a book remember uncle this is statement naka kace mana shine first rule na idan kanaso kazama psychiatrist"Murmushi yayi kadan yana kallonsu he loves them morethan anything a duniyan nan, saiya mike strictly yana kallon Farida yace "wuce kije kisa kaya anjima kihana mutane bacci da tari" mikewa tayi tana murmushi, yaba Faiza hannu yace "goodnight" highfive tabashi tace "gud night BUM,best Uncle M" Farida ta dawo da sauri tace "nima" high-five yabata yace "rigimammiya" yawuce yafita daga dakin abinsa yawuce karshen wajen akwai wani corridor nan yashiga saiga dakuna biyu tsayawa yayi yakalli second room din saiyadan sauke ijiyan zuciya yabude kofan yashiga dakine that's very simple yet very fine, Baban bed ne adakin sai shelf wanda medical books da Islamic books ne cike tam awajen maida kofan yayi yarufe, yakarasa yashiga closet nasa ahankali yasa hannu yazare glasses na idanunsa ya ijiye kan slap sannan yarage kayan jikinsa yadauki glasses din yamaida idanunsa saiya bude bathroom ya shiga akwai wani specific chamber dayake bayin next to wajen shower zare glasses din yayi ya ijiye kan chamber saiya shiga shower yayi wanka yafito yadauki glasses din yamaida yawuce yayi brush tareda dauro alwala yafito yashiga closet nasa ga karamin towel a hannunsa yana goge kansa tsayawa yayi sabida Amirah ne tafado ransa, did that man ohh father nata forcefully brought her to the hospital? What about the Mom? The girl isn't violent but why is she hitting her father? Maisa taji masa ciwo akai haka cus he saw it, He also saw kalan cizon data masa wanda it wasn't funny, how can a father zaisa wasu unknown kattin maza suyi man handling sick daughter ka haka da batada lafiya? How can a Dad brought his child to the hospital and left without paying a dime? No explanation? Bai damu da wani hali zata shiga ba? Baidamu da idan hospital din rejected her ba, He saw mutumin he looked into his eyes unlike mahaifiyar yarinyar there's no single affection or soyayya na yarinyar a idanunsa ba kaman mahaifiyarta ba da kallo daya yama matan yasa tana matukar kaunar yarinyar, the next question dayazo ransa is does the mom even knows cewa an dauki yarta? An kawota asibiti? Idan Maman tasan da zuwa asibiti he knows kotana ciwon kafafu zatai rarrafe tabiyosu akawo yarsu tare to the hospital something is fishy? Just today daya ga yarinya he knows she's not having wani autism dasuka lakaba mata, and he's sure he can help her to get better but the way yarinyar keson mahaifiyarta he can't do it alone, he needs the mother, family factors na yakara wan gani a mental condition mai kyau ko mara kyau, Babanta is a bad agent a mental condition nata but Mamanta is a very positive agent in her mental condition idan zaisa yarinyar nan ta warke he needs the Mom she's the first step na therapy yarinyar Ijiyan zuciya ya sauke yana shafa mai wayansa ringing yahauyi screen din ya kalla Mami yagani hakan yasa ya dakatar da abinda yakeyi yadauki wayan kafin yayi magana tace "Marwan zo kasa maza Abban ku baida lafiya he just entered the house banso yaran su sani" dasauri ya ijiye wayan da pajamas zaisa amman saiya dauki wata 3quater black yasaka dayar farar T-shirt mai kyau bai feda turare ba amman kamshi yake sosai yadauki wayansa yafito.
EPISODE 🔟
Dasauri gaske Marwan yayi stairs tundaga staircase ya hango Mami tareda wani dattijo daya manyanta sosai atleast zaikai 66yrs yana kwance flat akasa yana wani irin haki Mami ta rude, dawani irin gudu Marwan yayi wajen yace "what happened to him Mami?" Yayi maganan yana tallabo Abba dasauri, Mami tace "wlh shigowansa kenan ransa abace nasan dai ya ambato Saleem saikawai yafadi saida na yayyafamai ruwa ma yafara numfashin nan" ahankali yace "Mami bring first aid box wanda na ijiye a dakin Abba" mikewa Mami tayi tace "toh, toh" ahankali Marwan yace "Abba, Abba, calm down please nothing is going to happen to you kaji" daidai nan Mami tadawo bude akwatin yayi da hannu daya yadauki wani allura yakama hannun Abba tashi daya yamai alluran a jijiyan hannunsa hakan yasa jikinsa yadena rawan Mami takama hannunsa tace "Alhaji Alhaji" ahankali yake bude idanunsa, Marwan daya rikesa yace "Abba follow hand movement dina nagani if you can hear me" Yayi moving hand nashi Abba yabi hannun da idanu hakan yasa alhankali Marwan yace "Alhamdulillah" Mami ma tace "Alhamdulillah Alhamdulilah you scare me to death Hassan meya sameka eh?" Ahankali Marwan yace "let him rest Mami, give me pillow" Dasauri Mami tabasa pillow kwantar da Abba yayi kan lallausan carpet na wajen yana daura kan Abba akan pillow dake maida ijiyan zuciya yana kallonsu zai tashi danya basu waje Abba yarike masa hannu dasauri yajuyo yakalli Abba, ijiyan zuciya Abba yasauke ya tsare Marwan da idanu saiyakai hannunsa ahankali yasa agefen fuskan Marwan yana kallonsa still, hannunsa Marwan yarike yace "Abba menene what happened to you?" Ahankali Abba yace "Marwan" dasauri yace "na'am Abba" murya chan kasa Abba yace "kai d'ana ne Marwan and you will always be one kaji" lumshe idanu Marwan yayi yabude, Mami data gama rudewa tace "wai Alhaji menene kake magana haka Innalillahi wa innailaihi raji'un" ahankali Abba yace "amatsayina na wanda yake tamkar mahaifi agareka" ahankali Marwan yace "Abba kai mahaifinane you are and will always be Abba to me" ijiyan zuciya Abba ya sauke yace "amatsayina na Abban ka inaso na rokeka wata alfarma zaka iyamini"? Ahankali yace "Abba me kakeso zan maka" dan ijiyan zuciya Abba yasauke, yace "nasan Saleem yayane agareka ya girmeka da shekaru biyu but in reality ni I see you as yayansa, shekaru is not age, shekaru shine hikima da basira da sanin yakamata dakuma kwazo na yaro wanda kafi Salim in that aspect nesa ba kusaba" ahankali yace "Saleem amanata ne kafin mahaifina yarasu last year dudda yanda ya tsufa yanada shekaru 97 amman saida ya barmin wasiyya guda daya tak wato ga amanan Salim autanmu nayi hakuri dashi, nakuma rikesa amana, I tried my best nothing is working today I saw some disturbing pictures daya girgizani duk suna wayata"Abba yayi shiru yace "mistake danayi shine tun bayan mahaifiyar mu tarasu lokacin yana 3yrs dana kawo Salim nan wajen naba Mami shi tabasa tarbiya ba uwargidana ba, look at you yanda kasamu kyakkyawan tarbiya a hannun yayarka look at the man you've become, all abinda Saleem yasani is shaye shaye, zuwa club, party, mata, Astagafurullah" Abba yayi shiru sai chan yakalli Marwan yakama hannunsa duka biyun yace "I believe in you Marwan sabida nasan waye kai, I trust you dako yau nafadi na mutu nasan zaka kula da iyalaina kap dinsu da dayan gidan da nan, Marwan inaso nabaka amanan Saleem, I want you to help Saleem, and change him to be a better person, bring him back here yadinga rayuwa anan damu, help me change him kaji, inama Salim kwadayin halinka da dabi'unka help me Marwan, ko na rasu yau inaso kowa ya shaida cewa na damka amanar Saleem a hannunka kaji Marwan he's just an orphan shima like you kome kayi akansa Allah zai baka lada sosai, na rokeka da gir….." Hannu Marwan yadaura akan bakin Abba yana girgizamai kai yace "Abba bankai matsayin dazaka bude baki ka rokeni ba don't do it, Saleem dan uwana ne, me and him are one, I will try my best on him Abba, he's a good person you will see, all abinda kake gani inada shi shi yama fini he's better than me Abba and one day you will see it" Abba yayi wani murmushi na manya ahankali yace "shikenan Allah yamaka albarka Marwan, thank you"ahankali Marwan yace "where is he now?" Ahankali Abba yace "last 2 weeks he told me zaije Dubai yafara masters I gave him card na kudi da komi amman yana Nigeria one of my workers send me this picture ina wayata Wife"? Dasauri Mami taciro wayansa a aljihun wandonsa yace "bude kiba Marwan" budewa Mami tayi tabasa pictures Marwan yashiga saiya ijiye wayan kawai Abba yace "yanzu haka yana this address club ne wai can you go get him kudawo gida Marwan? Already nakira manager na nasa duk anyi freezing account dinsa this evening" gyadama Abba kai yayi ahankali yace "okay" saiya mike saikuma yadawo yaduka ahankali yace "Abba kadena daga hankalinka akan abu, you have BP avoid tashi hankali kar zuciyanka tabuga karka kara damuwa akan Salim tunda kabani responsibility nashi, all I want is kamai addu'a kaji Abba" gyadamai kai Abba yayi yace "Naji Marwan" tashi yayi yadauki key motan Mami dake wajen kawai yafita Abba yabisa da kallo saikuma ya kalli Mami yace "how did you train this boy Wife? Remind me please tayaya kika iya tarbiyantan da Marwan yayi girma yazama this responsible Man?" Murmushi Mami tayi tace "Allah ne kawai" Abba ya tsareta da idanu kafin ahankali yace "I'm very proud of you and I am so lucky to have you as my wife" Mami ta girgiza kai tace "I am the lucky one, bakowani miji zai yarda ka dauko kaninka dan one year ka kawosa gidanka ba bayan iyayenku sun rasu baki riga kin haihu ba, you supported me, ba'a yaye Marwan ba lokacin kaine d first person daya sayomai abincin yara dayaci, we trained him together, and I know your reason dayasa ka kai Salim dayan gidan bayan Umma tarasu sabida kaga ina fama da dan 1yrs old akanme zaka kawomin kaninka that was 3yrs old then saisa ka kaishi dayan gidan, don't worry we will save Saleem all together and he will be a better person kaji" gyadama Mami kai yayi sai ya rungumeta sukai shiru.