Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 12
Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 12: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 12. Murya Anna ke maƙewa tana cewa "ku taimaka wa tsohuwa sadaka…
4,400 words
Murya Anna ke maƙewa tana cewa "ku taimaka wa tsohuwa sadaka fi sabilillahi! Tsohuwa na yi muku bara " in an bamu kuɗi sai ta ɗauke masu manyan farashi ta saka a jaka su kuma ƙwandalolin ta bar su cikin kwano haka muka dinga zagaye har sai da muka samu kuɗi masu yawa,sannan ta saya mana ƙosai muka zauna muna ci.Daga nan zaunen ma Anna ba ta yi shiru ba haka take roƙon masu bi suna wucewa.
Bayan mun gama cin ƙosan muka je kusan wata randar ruwa irin wacce ake ajiyewa kan titi,ni na soma sha sannan ita.Ina kallon yadda Anna ta saka harshe cikin moɗar tana lasar ruwa kamar yadda mage ke yi.Sai a lokacin abin da ya faru jiya ya dawo min a kai,wani tsoro ya kama ni amma na fara ƙoƙarin ɓoye shi.
Mun yi gaba kaɗan na kasa haƙuri na ce "Anna jiya na yi mafarkin kin koma mage" ni kaina ban san ta ya aka yi na yi mata wannan zancen ba. Cak ta tsaya cike da mamaki ta ce "ni ma fa kamar na yi wannan mafarkin,wai fa har da jinin wata mage na tsotse"
Shuru na yi ina nazartar ta,sai na ga haƙiƙanin gaskiyarta fa ce take faɗa.
'Kenan in haka ne wato Anna ba ta san cewa ta rikiɗa a gasken ba?' na tambayi kaina a zuci kafin kuma na ce "Anna ba mafarki ne ba gaske kin yi hakan,don bayan kin tsotse jininta ni ce kika bai wa gawarta na cillar a ramen shara"
Wata irin dariya Anna ta yi irin kar na raina mata hankali kafin ta buga min sandar hannunta ta ce,"ja'ira wato ni za ki saka na yi zawo a wando ban shirya ba,ke ɗin ce za ki ɗauki mage ina kika kai tsoron naki to?"
Bayan ta jefo min wannan tambayar ni ma sai na ƙara yi wa kaina ita a zuciya 'to ko dai gaske ni ma mafarkin ne na yi?' banda amsa sai dai ina da shaida wacce zan tantance gaske ne kuwa.
Bararmu muka ci gaba da yi,ba mu dawo ba sai yamma lis.Muna ƙoƙarin shiga gida na hangi motar nan ta jiya wacce ba zan manta ba ta wata Hajiya ce wacce ta bamu abinci da nama da kuma lemun kwalba.
"Kaka ina wuni?" muryar matar ta daki kunnena,a tare muka juya ni da Anna wacce ta washe baki tana cewa "ƴar nan ke ce? Lafiya lau ya gida ya aiki?"
"Lafiya lau,nan ne gidanki ashe?" ta yi tambayar tana kallon ƙyauren gidanmu da ke a laƙwanshe.
Anna ta ce "i nan ne" "Ah bari na shiga na gani" ta faɗa tana ɗan murmushi,Anna kuwa daɗi ne ya luluɓe ta don shegen kwaɗayi ne da ita.
Da sauri ta buɗe ƙyauren duk muka shiga,Hajiya na ga tana dube-dube kamar mai neman wani abu amma sam ban kawo komai a raina ba. Ina shirin zama don na yi muguwar gajiya saboda yawon da muka yi Anna ta ce "Habiba je ki samo mana itace mu ɗumama tuwo"
Ba don na so ba haka na ɗauki igiya na fita,haka na dinga ratsa dajin da muke yo itace ba tare da tsoro ba don mun saba zuwa har cikin dare sai dai ban ta zuwa goshin magrib ba kamar yanzu.
Ko da na isa tuni duhun ya yawaita haka na soma karya busashin itace ina ɗorawa saman igiyata da na ajiye a ƙasa har zan ƙulle itacen sai idona ya sauka a wani wuri da koren haske ke ta ɓulɓulowa ta can cikin ƙasa.
Haka na je na soma tona wurin har na kai ƙarshen ramen inda na ci karo da wata ƴar koriyar lula.Jiki na ɗan ɓari na kai hannu na ɗauko ta duk a tunanina diamond ce tun da na ji ana zancen tana da ƙyalli ,sai dai contact ɗin da na samu da lular ya haifar min wani irin sanyin jiki tare da wata irin nutsuwa.
A hankali nake kallon yadda lular ke nitsewa cikin tafin hannuna haskenta kuma na ragewa har ta kai ta shige na bar ganinta.Idona ne suka ɗauki wani irin caji ta yadda har na rasa ganina na wuccin gadi,da sauri na dafa ƙasa ina fitar da wani huci . Tsayuwar inuwa na ji a bayana,tare kuma da jin wannan yanayin in ana kallonka ko kuma ba kai kaɗai ne a wuri ba.
A hankali na juyo,nan na yi arba da wasu ruhika guda biyu masu matuƙar haske.A lokaci guda kuma suka ɓace wa ganina bayan sun yi wani furuci da ban fahimci na mene ne ba.
Dakyar na iya ɗaukar itacena na nufi gida,tuni kuma masu yin sallah sun yi waɗanda ta dama don ni da Anna muna dai amsa sunan musulmi ne amma ba yin sallar muke yi ba dama-dama ita tana yin ta asubah shi ma don neman sa'a ne wurin Allah ya kawo mana cinikin bara.
Ko da na isa gida ban tarar da Hajiya ba,itacen na ajiye ina mai cewa "Anna ga su nan"
"Kin ga ɗora mana ruwan ɗumi mu yi wanka gobe tun da safe za mu bar ƙauyen nan" Anna ta faɗa tana wani duba kaya masu kyau. Na ce "ina kika samu wannan?"
"Hajiya ce ta bamu kin ga ke naki nan yi wanka sai mu saka" ta faɗa cike da murna tana miƙo min tawa ledar.Da murna ni ma na karɓa na duba kafin na fita na hura wuta,da ruwa suka tafasa Anna ce ta fara zagawa can bayan ɗaki domin yin wanka sai a lokacin na nufi ramen shara don duba mushen magen.Dare ne babu haske,sannan ba mu da ƙwan lantarki ballantana na gani ina shirin juyawa sai hannuna ya kawo haske ina haskawa sai na ga babu komai a ciki sai shara.
"Me kike yi kuma a nan?"na ji muryar Anna wacce ta yi daidai da ɓacewar hasken tafin hannuna. "Babu komai Anna "na bata amsa.
"Je ki yi wanka " ta bani umarni,ba tare da na ce komai ba na je na yi wankan sannan na canza kaya sai a lokacin kuma ta fiddo mana lafiyayen abinci muka ci muka hauda da lemun kwalba.Ban ɗauki wani lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni,sai dai wannan karon ba irin baccin da na saba ba ne .Yana ɗauka ta na soma yin mafarkai iri-iri,wasu masu daɗi wasu kuma na ban tsoro haka na yi ta yinsu har Anna ta tashe ni muka yi wani wankan muka shirya sannan muka tsaya jiran Hajiya .Babu jimawa kuwa ta zo,ba mu ɗauki komai ba kamar yadda ta ce za ta saya mana sabbin kaya in mun je can.
Da na shiga motar har sai da na ji wata kasala,tamkar waɗanda suka shekare ita da Anna haka suka ta yin hira a hanya har muka fita daga ƙauyenmu.Ba zan iya ce ga adadin lokacin da muka yi ba,sai tashi na aka yi .
A hankali na ware idona na soma kallon ƙaton mansion ɗin kai ka ce ba za a mutu ba yadda aka ƙera shi yayi kyau. Hajiya na gaba muna take mata baya har muka isa cikin ƙayatacen falon,a ƙasa muka zauna duk da ta ce mu zauna kan kujeru kuwa. Saman bene ta hau ta bar mu nan muna ƙauyenci ni da Anna,can kuma sai ga su sun dawo su biyu ita da wata mata wacce kana kallonta za ka gane ƴar uwarta ce sai dai wannan ɗin ta fi samun hutu.
Tun da ta fito ta kafe Anna da ido tana wani murmushi,mu kuma bakinmu har rawa yake wurin gaishe ta.Abin mamaki sam ba ta da wannan ɗagawar irin ta masu kuɗi,ta amsa cikin sakin fuska kafin ta ce "Binta ki kira masu aiki su kawo musu abinci,Mama ya hanya? Kun dai sha tafiya"
Anna ta ce "alhamdullah! Ai kam da nisa"
Wacce muke ta cewa Hajiya ashe sunanta Binta ,daga nan zaune ta fara kiran sunayen masu aikin gidan.Ƴan mata biyu ne suka fito a tare suna cewa "na'am Hajiya ƙarama"
"An yi baƙi sai an ce ku kawo abinci za ku kawo?"ta yi musu maganar cikin faɗa,da sauri suka shiga bata haƙuri kafin su je su ciko mana faranti da abubuwa iri-iri.
Duk sai suka tashi suka bamu wuri,muna tsaka da ci sai ga wata budurwa kuma ta shigo sanye da kayan likitoci ."Momy? Momy?" shine abin da ta ce,can kuwa sai Hajiya babba ta fito tana mai cewa "Fateena har kin sauko?" ba ta bata amsa ba sai mu ta kalla a wulaƙance kafin ta ce "su kuma waɗannan tarkacen?"
"Sabbin ƴan aiki ne mana, wannan wacce za ta dinga yi miki hidima ne " Momynta ta bata amsa ,cike da gadara ta ce "to ta taso ta wanke hannunta ta yi min tausa"
Haka ina son cin abinci amma na fidda hannuna aka zuba min ruwa na wanke hannuwana sannan na je inda ta baje na soma yi mata tausa,sai dai ban yi nisa ba idona ya sauka a wuyan Fatee wani ɗan rame na gani wanda yake da alaƙa da wata cuta ta sprituality sai dai ban san taƙamaimai ta mece ce ba ko kuma yadda za a magance ta.Yadda na ƙure wurin da ido sam ban san Momy ta fito ba,ashe ta lura da irin yadda nake kallon wuyan ƴarta.
"Fatee tausar ya isa haka ke kuma zo" ta faɗa tare da yin gaba na take mata baya har muka shiga wani ɗaki. "Me kike kallo a jikin Fatee?" "Babu komai Hajiya " na bata amsa sai ta tsure ni da ido na wani ɗan lokaci kafin ta bani damar tafiya.Sai a lokacin kawai na je na ci abinci,bayan mun gama cin abinci aka nuna mana ɗakin da za mu zauna.
Da dare bayan duk mun kwanta sai na yi mafarkin an nuna min wasu abubuwa ciki kuwa har da Maheer, sannan kuma wata tsohuwa ta shaida min wannan abin da na tsinta matarsa ce zan bai wa ita.An kuma nuna min rayuwata na cikin haɗari, washegari kuma ko da muka tashi bayan duk mun yi abin da ya dace sai ita wannan ɗiyar Hajiya ta ce a tare za mu je asibitin da take aiki a nan ne na ga Maheer shi ne na biyo sawunsa da kuma na shigo sai na ga Hajiya wacce ta kasance ƙanwar Mamana ce,tun ina karama Anna ke faɗa min ai Hajiya ba ta da mutumci ba ta son dangi wannan dalilin yasa na ɗora aljanun ƙarya ko su sa ta bari na zauna nan gidanta sannan na ce sun rufe Anna don ta ji tausayinta ta je ta tawo da ita don ko tantama babu wancan gidan na ƴan MAFIYA(MRS SADAUKI) ne" tana kawowa nan da labarin sai ta yi shiru,kafin kuma in ce wani abu Maheer ya buɗo ƙofa ya shigo .
"Ku taso ku duka biyun ki biyo bayana" ya faɗa tare da ficewa,Habiba ta kalle ni cike da tsoro kafin ta ce "kar dai a ce ya ji abin da muka ce?"
"Ke dai taso mu je" na faɗa tare da tashi na yi gaba,ta biyo bayana .Da muka fito falon babu kowa sai Maheer da muka tsinkaya yana taka step haka muma muka je muka hau har muka isa ɗakinsa.
Sai duk muka ja muka tsaya ganin wani madubi mai kamar Teku sai ruwa ke gudana a ciki,"ku matso ku yanka yatsunku manuniya jinin ya ɗiga a nan" ya furta cikin bayar da umarni,ba tare da mun yi muso ba muka matsa ya miƙa mana reza muka aiwatar da abin da ya ce ɗin.Jininmu na ɗiga a ciki madubin ya soma sauya kala yana bori kamar hadari ya taso haka ya koma baƙi ƙirin kafin kuma gidansu nurse Fatee ya bayyana a ciki.....
My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822 My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
20
Gidansu nurse Fatee na gama bayyana Maheer ya matso ya soma yin wani Yare,a hankali aka soma nuno mana ainahin cikin falon mai ɗauke da hoton ahali.Da na ga hoton Oga har sai da gabana ya faɗi,murya na ɗan rawa na ce "wannan shi ne mahaifin nurse Fatee?"
Maheer ya dube ni kafin kuma ya ɗauki wani abu mai kamar magani ya ɗiga min cikin ido,ya matso bakinsa dab da kunnena ya soma yin wani furici kafin kuma ya ɗauki hannuna ya ɗora jikin madubin.
Tamkar wacce ake yi wa saukar wahayi haka tarihin gidan da duk mutanen cikinsa suka fara ziyartar kwanyata na kuma soma bada labari tiryan-tiryan.
"Alhaji Mansoor,shararren kuma fitaccen ɗan kasuwa ne wanda ya laƙanci makirci, damfara da kuma cin amana.Ainahin wannan gidan ba nasa ba ne,na shugabansa wanda shine yayi sanadiyar kashe shi don yayi babakere da duk wata dukiyarsa.Matarsa Hajiya Jamila ita ce ƙashin bayan duk wata harƙalla tasa ita ce mai taimaka masa wajen ganin baƙin nufinsa na zama babban mutum wanda ya fi kowa kuɗi a duniya ya ci gaba da yin tasiri.Daga cikin taimakon da ta yi masa akwai ɗaukar ƴan mata aikatau wanda a ƙarshe Alhaji Mansoor zai neme su da alfasha ta haka ne zai tsotse duk wani energy nasu,a cikin irin wannan halin ne ƙanwarta Hajiya Binta ta zo gidanta da niyyar karatu amma sai Alhajin ya nuna yana sonta ko kaɗan Hajiya Jamila ba ta wani damu ba duba da cewa ƙanwarta ce,sai ma fara kyautata ma Binta ɗin ta soma yi tana yi mata duk abin da take so shi ma alhajin haka .Cikin iya tattako suka sa saurayin Binta yayi mata wulaƙanci sai ta dawo gida cikin baƙin ciki,babu kowa gidan sai Alhaji shi ne ya tarbe ta cikin raha yana cewa "wa ya taɓa kyakkyawar ƙanwata haka?" ita kuma abin ka da wanda yake shirin kuka an jefi shi da kashin awaki kawai sai ta faɗa masa sun yi faɗa ne da saurayinta wanda suke shirin aure ,nan ya feso mata romon baka yana cewa "kai saboda wani can za ki ɓata ranki bari na kawo miki lemu mai sanyi in na dawo zan yi miki hira mai daɗi har sai kin manta" bayan haka ne ya shiga kitchen ya kawo mata lemun da ya zuba gubar tsafi,ta karɓa tana sha yana yi mata hira sai kuma ya soma shafar jikinta a ranar ya rabata da budurcinta wanda yayi silar shigar ciki a jikinta.Tun daga wannan ranar kuma ya mayar da ita tamkar matarsa,ƙarin baƙin ciki kuma shi ne yadda suka haɗa kai da Hajiya Jamila suna janye taurarin Binta .A haka har cikinta ya tsufa wanda tun daga rainonsa har izuwa haihuwarsa ba ta tayar da hankali ba,tun ranar da nurse Fatee ta zo duniya sai ita Hajiya Jamila ta karɓe ta ,ita ce ta raine ta a matsayin ƴar cikinta saboda ita ba taɓa haihuwa ba tun a ciki BAƘIN RUHI ke ɗaukar jariranta matsayin sacrifice.Har zuwa wannan lokacin kuma Binta ba ta dawo hayyacinta ba, sai ma ci gaba da yi musu hidima take irin haka ne ta je yawon farauta ta gamu da Anna da Habiba ta basu sadaka ,a matsayinta na mai ido uku ne ta fahimci cewa Anna na ɗauke da wani kambun sprituality mafarin ta kawo su nan gidan Alhaji Mansoor" ina kawowa nan na yi shiru,Maheer ya ce "shi kuma ɓoyayyen sirrin da ke jikin nurse Fatee? " shiru na yi saboda an kasa faɗa min komai shi kuwa Maheer sai sake jefo tambayar yake,can na ce "nurse Fatee?"
"Eh nurse Fatee ! Mene ne ga wuyanta?"
"Abin ga ne...am...wani sirri ne"
"Sirrin nake son sani ai"
"An saka masa matakan tsaro sosai ta yadda ban iya ganin komai,dole sai in ita nurse Fateen ce za ta faɗa da bakinta" ina gama faɗar haka sai ya cire hannuna daga saman madubin,sai kuma ya ɗauki wani tissu ya goge min idona.
"Ku fita!" ya furta. Cike da mamaki na dube shi,sam ban yi tsammanin haka daga gare shi ba."Na ce ku fita ko ba ku ji ba?" ya sake faɗa cike da masifa.
Muna shirin fita Hajiya ta shigo tana washe baki ta ce "Maheer ga Ikilima nan da Mamarta sauko ku gaisa .Mene ne nan kuma?"
Tun da ta shigo na tsaya cak ina sauraren abin da take cewa,Maheer ya ɗauke madubin yana cewa "ki je gani nan"
Hajiya ta zo ta gabana ta wuce tana kallona,ni ma cike da mamakinta kamar ba yanzu ta gama hawaye ba amma ga shi tana washe baki.
'Wace ce Ikilimar nan da zuwanta ya saka Hajiya murna?' na tambayi kaina a zuci amma da mamakina kai tsaye na ji Maheer ya bani amsa da "budurwata ce! Ita ce wacce zan aura"
Ido na tsura masa ina kallonsa,ya haɗe rai tare da shan mur kamar ba shi ne yanzu ya nemi taimakona ba don samun wasu bayanai.Da sauri na kawar da kai jin idona na shirin cikowa da ƙwalla ko ma na ce sun fara. "In kin gama hawayen sai ki rufe min ɗakina" yayi furicin tare da nufar ƙofa sai dai yana buɗewa suka yi kaure shi da Ikilima ,ta saki sautin azaba kafin ta ce "likitana ka buge ni,tun ɗazu nake jiranka amma ba ka fito ba.Wace ce wannan?" ta yi tambayar tana nuno ni da yatsa,don wulaƙanci irin na Maheer sai da ya juyo ya kalle ni kafin ya ce "ƴar aiki ce mai yi wa Hajiya wanke-wanke"
Ta ɗan taɓe baki kafin ta ce " shi ne kuma ta yi tsaye tana kallon mutane don iskanci ba za ta ko gaishe ni ba?"
Ina gani lokacin da ya kalle ni ta gefen ido kafin ya ce "mu je falo"
Ta ce "a'a Please mu zauna falonka wallahi wata Albino na gani nan kujera ni tsoronta nake" ta yi furicin tare da ida shigowa da ta zo ta gabana don iskanci sai ta take min ƙafa da takalminta mai tsini,ina gani kusan a tare muka rumtse ido ni da Maheer.Har cikin tsokar raina na ji zafin abin da ta yi min,raina yayi mugun ɓaci sai na kasa haƙuri tana shirin zama na juya idona na kwashe dukkan ƙafafunta tare da yin sama da ita ta faɗi timmm da ƙasa har goshinta na buguwa ga table nan take jini ya soma yi mata zuba.
Ta fasa ihu tana kiran sunan Maheer,shi kuma ya je da sauri ya tayar da ita kafin ya je ya ɗauko akwatin aiki ya wanke mata wurin da ya fasa ya rufe da bandeji.Rigarta duk ta ɓace da jini,murya a ɗan dake ya ce "je ki ɗauko min wata sabuwar riga cikin drowerta " duk da na san da ni yake amma haka na ƙi tafiya na nufi ƙofar fita idona na rufewa saboda baƙin cikin abin da ban san mene ne ba.
Ina zuwa kuma ƙofar ta ƙi buɗewa,na soma jijigata amma ta ƙi ta buɗu.Tuni kuma hawaye sun soma wanke min fuska,daga bayana na ji tsayuwarsa har ƙirjinsa na gugar kaina . Hannunsa ya ɗora kan nawa da ke faman juya handle,daidai kunnena ya ce "wai kishi ne kike ko me?" hankali tashe na juyo jin abin da ya ce,sai aka yi rashin sa'a laɓana suka gogu da nasa .Wani irin ja da baya na yi na shige jikin ƙofa ,duk sai jikina ya ɗau kyarma musamman da na ga ya ƙure lips ɗina da ido kamar mai son kissing nasu.
Mahaukaciyar buduwarsa ban san me ta gani ba ta sake sakin ihu tana mai tawowa za ta buga min rose/faux du fleurs nan ɗin ma ƙafafunta kawai na kalla ta faɗi timmm.
Maheer yayi wani murmushi mai haɗe da ƴar dariya wanda ya tafi da imanina na kafe shi da idona ina jin wani sanyi na ratsa ni yana sanyayya zuciyata.Na shagala sosai wajen kallon ƙwayar idonsa na ji ƙarar buɗe ƙofa,sai kuma na ji hannunsa kan nawa yana cewa "je ki sha ruwa masu sanyi" Dakyar na fito ina mamakin dama yana dariya? Sai na saki murmushi tuna yadda yayi mugun yi masa kyau,da kuma na tuna irin muguntar da na yi wa buduwarsa sai na sheƙe da dariya kafin na sauko ƙasa.
Ban ga uwar Ikilimar ba,ƙila suna can sashen Hajiya sai Habiba na taras ta saka Yasmine tana kallo.
Na ce "shi ne kika fito kika bar ni?"
Ta ce "ah to ba dole ba,ni fa tsoronsa nake ke kuma na ga da alamu taurin kai ne da ke"
Na saki murmushi kafin na wuce kitchen,Lubna na tarar tana aikin tuwon gobe."Yunwa nake ji"
Ta ɗan saki fuska kafin ta ce "ai kuwa sai in naman da na soya zan zuba miki "
Na waro ido na ce "rufa mini asiri so kike Hajiya ta kore ni da rana tsaka"
Ta yi dariya kafin ta ce "ina Aliya ta je?"
"Wallahi ni ma ban sani ba,ga shi kuma magarib ta gabato "
"Ki taya ni Please ina son na yi sauri na gama gida zan je,na kwana biyu ban ga Ummah ba kuma sai nake ji a jikina kamar ba ƙalau ba.Tun da Zuly ta yi arba da ni na san za ta iya yin komai don ta ga na koma cikin family,kina ji har da ja min sharri wai ba kai musu ziyara"
"Kin yanka yatsanki jininki ya zuba jikin logon ƙungiya ko kin manta?" na tambaye ta.
Cike da jin haushi ta ce "Aliya ce duk ta jefa ni cikin wannan matsalar,ni sam ban yarda da ita ba.Ta ya ma aka yi ta san logon family ne?"
"Ita fa yadda kika san aljana haka take,zancen kuma Zuly za ta je wurin Umma ki cire shi a ranki don ba za su yi wannan kuskuren ba saboda Ummarki mace ce mai addini,tana riƙo da Azkhar sam ba za su iya yi mata komai ba.In akwai abar tausayi to ke ce ,don haka ina baki shawara ki je wurin Maheer ki faɗa masa komai duk da dai na san ya san da duk abin da ya faru amma ki basa haƙuri sannan ki shaida masa"
Hawaye ne suka soma sauka a idon Lubna,kafin ta share su ta ce "haƙiƙa Haule ke mai kirki ce duk da musguna miki da na yi amma sam ba ki canza min ba,ina neman ki gafara don Allah ki yi haƙuri ki yafe min sharrin zuciya ne ..." na yi saurin katse ta da "bai komai Lubna,ni na san da zuciya guda kike sona kawai kishi ne ya rufe miki ido amma ai ban ga laifinki ba.Sai dai ki sani ni ban son Maheer haka kuma ranar da kika ga na fito daga ɗakinsa ni ma tsintar kaina na yi a can ban san me ya faru ba"
Lubna ta yi wani murmushi ta ce "kina faɗar ba ki sonsa amma idonki na ƙaryara abin da bakinki ke faɗa,Haule soyayyar Oga Maheer ce shimfiɗe a cikin idonki luntsum ta yi gida har ta zuba ƴaƴa" ta ƙarashe cikin raha,ban san lokacin da na kai mata duka ba na ce "Allah kiyaye min ni ban sonsa sai dai in ke ce ke sonsa,me zan yi da mutum siririri kamar zaren Lipton "
Dariya muka shiga yi kafin na taya ta aikin har muka gama,bayan duk mun yi sallar isha'i sai muka ɗauko abincin dare amma har yanzu Aliya ba ta dawo ba haka ita ma Yasmine ba ta farka daga baccin da take yi ba.
Cike da zullumi na fita waje don dubo ta,sai na ji Habiba a bayana tana cewa "ina ga zan je na dubo halin da Anna take"
Na juyo na dube ta sai na ga duk alamun damuwa a tattare da ita,sam kuma ban ga laifinta ba don uwa ba wasa ba.Sai na ce "mu je na yi miki rakiya " cike da farin ciki ta amince muka isa bakin titi,ta tsayar da taxi muka shiga ita ce ta biya lokacin da muka sauka ban san kuma inda ta samu kuɗin ba.
Muna shiga gidan sai na ji tamkar ana kiran sunana,har muka isa falon babu kowa.Habiba ta nufi ɗakinsu wanda aka sauke su yayin da ni kuma ƴar ganin ƙwam na soma bin wata hanya da na ga babu haske sai duhu,ina zuwa kuwa na ci karo da wata ƙofa na buɗe na shiga cak na tsaya ganin wata sabuwar duniyar ifiritu duk wani abu da ya shafi tsafi da mafiya akwai shi.Hakan yasa na fahimci cewa wannan shi ne ɗakin sirrin Oga Mansoor,a hankali kuma na taka zuwa gaban wani ƙwarangwal na kai hannu na ɗauko sai kawai na ga dukkan ɗakin ya ɗau wani irin haske irin na wutar murhu yayin da kuma capet ɗin da ke shimfiɗe a ƙasa ya zama tamkar magudanar jini.Ko kafin na yi wani motsi kuma Oga ya bayyana ɗakin tare da caka min wani tsinke a gefen wuya,nan take idona suka lumshe ban sake sanin abin da ya faru ba sai farkawa na yi na gan ni wata cikin wani falo.
Da Boss na soma haɗa ido kafin Oga da Zuly waɗanda suke yin wani irin murmushi irin sun yi nasara. Boss ɗin ya buɗa baki da niyyar yin magana wayarsa ta ɗau ringing,cikin harshen Hausa yake magana yana mai cewa "Jagaba yanzu nan nake da niyyar kiranka,yarinyar da ta ɓata mana aiki tuni yarana sun kawo min ita ni ma yanzu zan kawo ma ita " cike da ladabi yake maganar,da dukkan alamu shi ma da na gaba da shi yake magana.
Cike da shaƙiyanci ya ce "ke ce mai zarrar shiga gonata ko? To yau za ki haɗu da fushin Jagaba sai kin yi da na sanin zuwa duniya" na yi tunanin mota za mu shiga lokacin da za su kai ni wajen shi Jagaban,amma sai na ga ya ƙyarta wani abu mai kamar ashana nan take hayaƙi ya turniƙe wurin kafin ƙyaftawar ido kuma mun isa wani gidan ko kuma na ce wata ƙasa.
Falon sosai yake da abubuwan ban mamaki yadda komai yake a tsare sai dai tamkar suna numfashi,haka mutum yana jin wanzuwar halittun da ba a gani.
Muna nan jibge kamar kayan wanki kafin wata jiniya mai kama da kukan jinnu ta sanar da fitowar da Jagaban,ƙarar saukowar takalminsa yasa duk suka wani duƙe kamar sun yi ruku'u yayin da ni kuma ke zaune duk jikina an ɗaure shi da kacar tsafi.