Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 13
Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 13: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 13. Tun da ya fito na kafe shi da ido zuciyata na dukan…
4,414 words
Tun da ya fito na kafe shi da ido zuciyata na dukan tara-tara,kansa a sunne yake ga kuma wata hulla da ta rufe masa fuska iya tafiyarsa kawai nake kallo.Yana zuwa tsakiyar falon ya ɗago kansa sai dai ba ni yake kallo ba,ni kuma murya na ɗan rawa na ce "Yaya Aliyu?" taram ya juyo da dubansa gare ni tare da zuba min idonsa da suke cike da tsantsar dafin baƙin tsafi ya ce "Haule?" nan take duk kacocin suka tarwatse na wani tashi da mugun sauri na yi tsalle na ƙanƙame shi gam tare da fashewa da matsanancin kuka...... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
21
Sai da na ci kuka sosai kafin na janye jikina daga na Yaya Aliyu ,tsakiyar idonsa na kalla kafin na juya na kalli su Boss da suka yi cirko-cirko kamar kaji.
"Ku fita ku bamu wuri" ya basu umarn,sai duk suka fice.Ya ja ajiyar zuciya kafin yayi mana masauki kan doguwar kujera mai zaman mutum uku,hannuwana na cikin nasa muke fuskantar juna kowannen mu da abin da yake saƙawa a zuci.
"Haule me ya haɗa ki da su Mansoor?"
"Ni ma tambayar da nake son yi ma kenan Ya Aliyu,mene haɗinka da matsafa? " wani kallo yayi min kafin ya ce "duk ba wannan ba,duk tsawon shekarun da kika bar gida ina kika shiga? Innarmu ba ta taɓa faɗa mini kin bar gida ba sai da na je na tarar ba ki nan.Haule kin san irin halin da Innarmu ke ciki a yanzu? Duk ta rame ta dalilin tunaninki duk da yanzu ba mu rasa komai na rayuwa ba har masu aikatau duk na zuba musu na kuma canza fasalin gidanmu an mayar da shi ginin zamani"
"Yaya Aliyu don Allah ka kira mini Innarmu a waya" na faɗa wasu sabbin hawayen na zubo min.
"Faɗa min mene ne dalilin barin gida kika gudo inda ba uwa ba uba ?"
"Ya Aliyu ai na san Innarmu ta faɗa ma"
"Eh sai dai ba ta fayyace min komai ba"
So nake na soma basa labarin amma ina jin tsoro,tsoron abin da ban san taƙamaimai na mene ne ba.Ban sani ba ko ya lura da hakan ,sai ya ƙara jawo ni jikinsa cikin sanyayyar murya ya ce "ina jin ki mana Haule ki faɗa mini ,ki sani ni ɗin BANGO(MRS SADAUKI) ne a gare ki yanzu ba ki da kowa in banda ni.Ke ɗaya ce kika rage min wacce zan kalla na ji daɗi ko bayan mutuwar iyayenmu,don haka kar ki ji komai ki sanar da ni"
"Kana nufin Fahad ma ya mutu?" na jefa masa tambayar ina mai jin tsoron amsar da zai bani.Kai ya jinjina min alamar eh,na zabura zan miƙe amma yayi saurin mayar da ni.
Wani sabon kuka na tsira ina jin wani irin raɗaɗin mutuwar ɗan uwana,wato cikin mu biyar mu biyu kawai suka rage."Ya Aliyu na san shi ma Fahad su suka kashe shi ko? Yaya Aliyu karon farko da na ji tsoro kuma na yi takaicin fitowa daga tsatson iyayenmu maza.Da farko sun kashe Haidar,suka ɗauki anty Aliya suka miƙawa mugu yayi sanadiyar mutuwarta yanzu kuma Fahad.Gobe kuma wane ne? Ni ko kai..."
"A'a dama komai a tsare yake Haule,wasu su rayu wasu kuma su mutu domin haska goben rayayyun su samu ci gaba a rayuwa.Ni da ke mune zaɓaɓi kamar yadda su iyayen namu maza suka faɗa ,kina tunanin in ba don kina ta daban ba har za ki iya ganin abin da ido bai kamata ya gani ba kuma ki rayu ko kuma ki tsaya da idonki?"
Cikin tafasa zuciya na ce "Yaya Aliyu ka san irin azabar da suka gana min kuwa? To bari ka ji na baka labari.Bayan maciji ya cije ni an yi mini magani,haka duk dare na Allah iyayenmu maza ke ɗauka ta suna jefa ni cikin akwatin macizai duk da ba su taɓa cizona ba amma ina tsorata sosai.Haka kuma washegari ban iya buɗe baki na sanar da Innarmu,riƙe abin iya ni ɗaya a raina sai ya haifar min da ciwon damuwa .Ni kaɗai in ina zaune zan soma firgita ina jin tsoro,duk wannan bai ishe su ba sai suka ƙara min da mafarkan ban tsoro yau in an kai ni maƙabarta,to gobe MUTUWARE(MRS SADAUKI) zan tsinci kaina ni ma a kwance shanɗal kamar gawa.Bayan wannan sai aka soma kawo min ziyara,a duk lokacin da kowa ke bacci haka zan ga Kaka ya shigo ɗakinmu yayi tsaye a gabana yana kallo ba tare da yayi magana ba.Tsawon sati yana yi min haka,kawai wata rana na yanke shawara ƙara zuwa ɗakin sirri sai dai wannan karon ba iya leƙawa na yi ba a'a shiga na yi.Ban san ta yaya ba,kawai dai na kalli ƙofar da ido sai ta yi ƙiiii ta buɗe kanta.A hankali na soma taka ƙafata har na shiga cikin ɗakin mai matsananci duhu,tako biyu kawai na ƙara sai na ji na taka wani abu mai kamar ƙwallo kasancewar ɗakin da duhu yasa na duƙa na ɗauko abin.Daidai nan kuma wani haske ya soma fitowa irin kamar ana walƙiya ya haska min tashin hankalin da ke cikin hannuna,Yaya Aliyu ba komai ne ba sai ƙwarangwal ɗin kan mutum.A firgice na yi cilli da ita,sai dai me zan gani? Kusan ɗakin cike yake da ƙwarangwal ɗin kanun mutane.Na juya da baya da niyyar fita ƙofar ta ƙara rufe kanta,sai na yi tsaye cak ina rawar disco.Ban ida firgita daga tashin hankali ba sai da na ga ƙaton hoton Kaka ya soma motsi,Yaya Aliyu a gaban idona Kaka ya fito a zahiri ba a ɗauki kuma wani dogon lokaci ba ya soma rikiɗa yana komawa wata halitta wacce tsabar shock ta saka na suma a nan take.Ko da na farka kan shimfiɗata na tsinci kaina ,yayin da Innarmu ke zaune tana faman gasa min goshina da wani towel.
Muna haɗa ido da Innarmu ta feso min wasu kalamai,"lokaci yayi da za ki bar gidan nan Haule,don tseratar da rayuwarki da kuma tawa.Kar ki tambaye ni ina za ki je,ko don me iya ke ɗaya za ki tafi kawai ki amince ki bar gidan nan tun yanzu kafin gari ya waye" a lokacin ba ƙaramin tashin hankali na shiga ba Ya Aliyu .Amma duk da haka Inna ta haɗa min kaya kala uku ta bani wasu ƴan kuɗaɗe kafin ta yi min rakiyar har bakin iyakar fita daga gari.Cike da soyayya da begen juna muka rabu,rabuwar da har yanzu ba mu sake ganin juna ba.Na fahimci cewa so da ƙauna suka tunzira Innarmu har ta yi min iyaka da gida,sai da na yi tafiya kamar ta awa biyu sannan gari ya soma haske sai kuma na soma ganin ababen wucewa na roƙi alfarma a rage mini hanya.Da aka shigo cikin gari aka sauke ni,na nemi ruwa na soma yin sallah sai na ga mutane na kallona wasu ma dariya suka dinga yi min.A ranar ne na fahimci ba bisa kan ilimi ne duk muke yin sallah ba,amma ban damu ba saboda ban ma san ta ya zan koya ba.Cikin kuɗin da Innarmu ta bani na fitar na sayi abinci,na koma can gefe ina tsaka da ci kenan sai ga wani mutum ya parker ƙatuwar motarsa bayan ya gama sanye abin da zai saya sai ya dube ni ya ce "taso mu je" ban san shi ba,amma haka na tashi ya taimaka min na shiga motar wacce zamana ke da wuya bacci ya ɗauke ni ko da na farka kuma kan titi na tsinci kaina ga shi kuma dare yayi.Cike da tsoro na soma dube-dube,a daidai kuma wannan lokacin ne Husseina ta bayyana a gare ni ta shaida min maƙasudin zuwana a nan shi ne nemo wanda zai dakatar da duk macce-maccen da ake yi gidanmu.Sai dai fa na kwashe wajen shekara biyar ina yawo gari-gari amma ban gansa ba,na san za ka ce ta ya aka yi na rayu duk tsawon shekarun nan to gaskiyar zancen aikatau nake yi ana bani abinci maganar da nake yi ma a yanzu haka gidan wata Hajiya nake aikin sayar da abinci cikin haka ne na haɗu da Yasmine " ban san dalilin da yasa na dunƙule labarina ba,amma haka kawai na ji ina son ɓoyewa Ya Aliyu zancen Maheer da kuma duk taimakon da muka yi wa mutane .
Ya ja wata ajiyar zuciya ya ce "yanzu kin samu shi mutumin?"
Na girgiza kai na ce "a'a har yanzu ban gansa ba"
"Yanzu me kika yanke za ki koma gida?"
"A'a ina jin tsoro"
Yayi wata dariya kafin ya ce "tsoron me kuma Haule? Ko har yanzu ba ki gane ke wace ce ba?"
Shiru na yi ina kallonsa,ban ce komai haka shi ma ya miƙe tsaye kafin kuma ya ce "taso mu je gidana "
Haka na bisa muka fito,su Boss duk sai suka nufo mu. "Wannan ɗin ƙanwata ce,ita ce excelency da nake baka labari" Yaya Aliyu ya faɗa yana kallon Boss wanda jikinsa har rawa yake wurin rusuna min haka su ma Oga da Zuly,ni abin dariya ma ya so ya ban amma na cije ina mai kallon Yaya Aliyu ya sakar min murmushi kafin ya ja hannuna mu fita can harabar wurin .
Wani Bature ne ya buɗe mana wata latsetsiyar mota muka shiga,na saci kallon Ya Aliyu kafin na ce "wannan motarka ce?"
"Haule ko kina son ta ne?"
"A'a ni me zan yi da mota? Yaushe za ka kira min Innarmu?"
"In mun isa gida zan kira ta video call ku gaisa" ya bani amsa,mun yi tafiya mai ɗan nisa kafin mu iso gidan wanda yake zagaye da turawa masu tsaron lafiyarsa.
Ko da muka shiga ciki wata baturiya ce ta zo ta tarbe shi da gudu ta rungume shi tare da yi masa kiss,can kuma ta nuna ni tana tambayarsa cikin Yaren French "ita kuma wannan?"
Ya bata amsa da "ƙanwata ce Haule "
Ta washe baki ta ce " Hawule"
Na yi murmushi jin yadda ta kira sunana,hannu ta bani muka gaisa na kalli Aliyu na ce "matarka ce?"
Sai da ya ɗan yamutsa fuska sannan ya ce "kusan haka ne" da mamaki na sake dubansa,amma ya tari numfashina "za ki fara yin wanka sannan ki ci abinci sai na kira miki Innarmu "
Na turo baki gaba na ce "ni dai ..." ya katse ni "a'a fa so nake ta gan ki cikin shiga mai kyau yadda hankalinta zai kwanta"
Ba don na so ba haka na je na shiga toilet ɗin da ya nuna min wacce sai ka rantse ɗakin bacci ne saboda tsabar haɗuwa,bayan na fito baturiya ta kawo min kaya da mai da turare na kimtsa sannan na fito.
Abinci aka kawo min,kallo guda na yi masa na ji hankalina bai kwanta da shi ba na ce "ni dai a kawo min salade na fruits " bai takura ni ba yasa aka kawo min,bayan na sha ne ya kira min Innarmu ta ƙatuwar system ɗinsa.
Lokacin da fuskar Innarmu ta fito raɗau kan screen sai da na ji numfashina ya kusa fita ita ma na lura ta ɓangarenta haka abin yake.Kuka duk muka soma yi muna kallon juna,sama da shekara biyar ba ma tare da juna.Duk da Innarmu ta rame amma hakan bai hana fatarta sheƙi ba ta yi kyau,hakan kuma na san bai rasa nasaba da canjin rayuwar da suka samu.
"Innarmu!" na furta ina shafar screen ɗin,ta amsa da "na'am Haulena" sai kuma duk muka yi shiru, Aliyu ne ya ce "sai yau kawai muka haɗu ,am...zan fita na bar ku in kun gama hirar sai ta kashe" haka ya fice ya bar ni da Innarmu muka soma bai wa juna labari,da na faɗa wa Innarmu labarin Maheer sai na ga tana murmushi tare da bayyanar da farin cikinta.
"Kina ji Haule duk kin jima gidan Aliyu kar ki wuce gobe,ki koma can ki ci gaba da yin aikinki sannan ki rage taurin kai sannan ki dinga girmama Alhajin ban son ƙara jin kin yi masa gardama ko kin yi abin da bai so"
Na turo baki gaba na ce "wato kin fi sonsa da ni,mugu ne fa kuma son ƴan matan bala'i ne da shi ƴan matansa sun fi ɗari"
Nan ma Inna murmushi ta yi kafin ta ce "farin jini ne da shi dai,amma da dukkan alamu yana da kirki"
Ban san dalili ba haka nake jin daɗin yadda Innarmu ke yabon Maheer,ni kuma kawai sai na buɗe baki na yi ta zuba ina bata labarin duk wani abu da ya shafe shi ina nuna mata yadda yake haɗe rai da kuma zuba masifa ita kuma tana saurarena tana murmushi.
★
A ɓangaren Maheer kuwa Haule na fita ya dakawa Ikilima tsawa yana cewa "da kika kwanta kika wani wargaje nan nufinki na zo na tashe ki ko me? "
Cike da ta kaici ta ce "hearty amma ai dai ka ga a gabanka yarinyar can ta yi min mugunta shi ne ka buɗe mata ƙofa ta fita ko ka hukunta ta ka yi mata ko da mari biyu ne amma ba ka yi ba.Shine yanzu ma ba za ka iya taimaka min na miƙe ba "
Cike da masifa ya ƙanƙance ido ya ce "kin manta dukan da na yi miki? Ko kin manta a wane dalili ne? To bari na tuna miki akan raɓar jikina ne,na faɗa miki duk wani abu da zai sa na raɓi jikin mace ko mu samu contact na tsane shi in kika cire fannin aikina shi ma don yana dole ne"
Ikilima ta tashi zaune tana kallonsa,idonta na zubar da ruwan hawaye ta ce "amma yanzu ai na gani ka ɗora hannunka kan na ƴar aikinka.Maheer me yasa kake yi min haka? Ka gwammaci ka taɓa jikin waɗanda ke ƙarƙashin ikonka kan nawa? Na faɗa maka ni ban damu da duk wata shuɗaɗiyar rayuwarka ba,in ma tsoro kake ji don kar na zarge ka ne na ce ka saba yin ..." bai bar ta ta ida ba yayi kutufo da ƙafafunta kafin ya daka mata tsawa "fita! Fita na ce! Ni kike kira da sunana gatsal? Sa'anki ne ni? Wato ni ne matsoraci? Kar ki zarge ni akan na yi iskanci a baya ko? To za ki ga iskanci kuwa don wallahi ba zan aure ki ba na fasa" yayi furicin tare da yin gaba ya shige bedroom ɗinsa ya bar ta can a falo.
Jikin ƙofa ya jingina tare da lumshe ido yana tunanin Haule,wani irin mugun feeling ɗinta yake ji.Da ya ɗora hannunsa kan nata ji yayi kamar ya ƙurma ihu saboda abin da ya ji,yana cikin wannan tunanin ne ya ji Ikilima na bubuga ƙofa tana kuka tare da roƙonsa kan yayi haƙuri.Ya ja tsuki kafin ya wuce toilet,wanka yake amma tunanin Haule ya hana zuciyarsa shaƙat sai shafar lips ɗinsa yake waɗanda suka gogu da nata.
Fitowa yayi ya shirya a tsanake ,ko da ya fito bai ga Ikilima ba .Masjid ya wuce ya yo sallar magrib bai fito ba sai da yayi isha'i sannan ya koma gida da zumuɗin idonsa su ƙara yin tozali da ita. Ɗakin Hajiya ya wuce direct,kan dadduma ya tarar da ita tana jan casbi.Kamar wani ƙaramin yaro ya haye bed ɗinta yana kallon sama yayin da kuma yake ɗan lilo da ƙafafunsa.
"Me ka yi wa Ikilima? Ta shigo nan tana kuka mun tambaye ta amma ta ƙi faɗa, sannan da za su tafi ka ƙi fitowa ku yi sallah kuma ko gaishe da surukarka ba ka zo ka yi ba" Hajiya ta faɗa tana mai ajiye casbin hannunta.
Tun da ta soma magana ya lumshe ido har ta gama bai buɗe su ba kuma bai ce komai ba. "Meke damunka ne Maheer?" Hajiya ta tambaya a ɗan ruɗe,dama abin da yake jira kenan kawai sai ya soma yi mata magana cikin salon da in ƴan shagwaɓar nasa sun motsa.
"Kawai ni ban jin daɗin jikina ne, Please ki ce ta haɗa min tea ta kawo min" ya furta idonsa na rufe.
Hajiya ta yi saurin tashi don duk abin da ya shafi Maheer tamkar farilla haka take ɗaukarsa da girma.Gefen wuyansa ta shafa da bayan hannu ta ji shi da sanyi kamar ƙanƙara kafin kuma ta ce "bari to na je a haɗo maka,Haule?" ta fara kiran sunanta tun kafin ta fita,shi kuwa har da wani murmushi ya saki amma bai wani ɗauki lokaci ba ɓacin rai ya maye gurbinsa da shi ba.
Hajiya ta dawo tana cewa "ka ji wai sun fita ita da Habiba "
Wata irin zabura yayi kafin ya miƙe ya fito,da Lubna ya ci karo wacce ita ma take cike da zullumi. "Ina suka je?" ya watso tambayar.
"Ni ma ban sani ba,da farko dai ita Haulen ce ta fara fita sannan Habiba kuma shikenan ba su dawo ba" ta basa amsa. Rai ɓace ya ce "ina Aliya?"
"Ita ma ta fita tun ɗazu " ji yayi kamar ya shaƙe wuyan Lubna ko zai ji sauƙi.Ɗakinsa ya koma duk yadda ya so ya lalubo Haule a cikin tunaninsa amma abu ya cuttura bai kuma sha wahala wurin gane cewa tabbas ta ƙetara iyaka ba ta wannan ƙasar,zuciyarsa ce ya soma jin tana tafasa.Key ɗin motarsa ya ɗauka ya fito,yana son tafiya wurin Yabobo ne amma Hajiya ta tare shi tana cewa "ina kuma za ka je?"
Idonsa sun yi jawur ya ce "zan je nemo su" Hajiya na shirin yin magana wayarsa ta ɗau ringing,da ya fiddo ya ga sunan nurse Fatee sai ya ji kawai zancen su Haule na gidansu ne za ta yi masa sai kuma ya ji wata sabuwa.
Cikin kuka nurse Fatee ke cewa "ka zo asibiti yanzu Please ga Dr David nan yana kan gargadar mutuwa,kuma...kuma. wannan yarinyar nan mai kama da aljanu ita ma ga ta a nan tana ikirarin sai ta ida kashe shi"
Ji yayi kamar an buga masa guduma,rasa abin da ke yi masa daɗi yayi.Yana fita ya shiga motarsa ya wuce asibitin,tun daga nesa ya hango Aliya sai dai ba a siffar da ya santa ba cikin wata irin rikitaciyar siffa ce wacce ya kasa tantance shin aljana ce? Dabba ko ƴar Adam??????? My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
22
Daidai lokacin da Maheer ya isa wurin Aliya a wannan lokacin ne kuma ta ɗauki siffarta ta normal mutum amma ta ƙi yarda su haɗa ido da shi . Nurse Fatee ce ta fito tare da nuna masa ɗakin da Dr David yake a kwance .Da ya shiga sai da ya razana ganin irin mawuyacin halin da yake,duk wasu tsiran gashin jikinsa jini ne ke fita ga kuma sabon tashin hankali yadda al'aurasa ta yi ƙaba ta fi girman jinjirin jariri.
Maheer ya ƙanƙance ido yana kallonsa,ya rasa me zai ji takaici ko kuwa tausayinsa?
Murya na ɗan rawa Dr David ɗin ya soma yin magana,"ni na jawa kaina Maheer,ban taɓa sanin yaudarar ƴan mata abu ne mai illa ba sai yau da na yi gamo.Tun ranar da idona ya sauka kan Aliya na ji wata muguwar sha'awarta ta tsarga min wannan yasa na jawo ta a jikina,sai kuma na same ta mai sauƙin kai sam ba bani wuya ba sai dai fa ta kafe kan cewa tana son sanin a gaske na yi soyayya da Lubna? Shi ne na ce zan bata labarin komai amma ta same ni nan asibiti ƙarfe shidda na maraice ,da ta zo ne ni kuma na yi amfani da ilimina na jefa mata ƙwayar magani mai kashe jiki ba tare da na yi lura nan ɗin asibiti ne wurin ceton rayuka ne ba na tarwatsa rayuwa ba.Aliya na gama shan lemun na bijiro mata da buƙatata ina mai bata labarin soyayyata da Lubna. "A wani yammaci ne muka fara shan romon soyayyarmu kamar dai yadda nake yi miki yanzu" na yi wannan furucin ne lokacin da na soma raba ta da kayan jikinta na soma shafarta,dukkan jikinta yayi sanyi liƙis ba ta da wata zarrar hana ni amma a cikin idonta ina hango tsanar haka amma na ci gaba da bata labari "Lubna ta zo min da buƙatar tana son sperm ɗina,wadan ni kuma na ga faɗuwa ce ta zo daidai da zama don na jima ina sha'awarta amma sai take nuna min addininsu ya haramta haka.Ranar da ta nemi wannan alfarma mun yi da ita ta zo ta karɓa a can gidana,shi ne fa ta je ita ma magani na zuba mata a jus ta sha sai dai ita nata mai tayar da feeling ne .Mun yi soyayya a ranar nan,tsabar yadda na yi mata romance ita ce ta dinga roƙona na kusance ta.Bayan komai ya kammala ne na zuba mata sperm ɗin cikin ɗaya daga cikin kwalaben da Maheer ke ajiyar jininsa,don a lokacin ma da kumfar jininsa a jiki kuma ban wanke kwalbar ba .Ban san me ya faru ba a ƙarshe dai ta rabu da ni rana tsaka ta koma son Maheer ashhhh!" Dr David yayi shiru da bai wa Maheer labarin yadda suka yi da Aliya kafin can ya ci gaba da cewa "Maheer ban san cewa Lubna a ƙungiyar asiri ta kai sperm ɗina ba sai da Mamana ta faɗa min tare da yi min faɗa na bar ɗabi'ar nan ta banza ta yin fasiƙanci da ƴaƴan mutane amma na yi fatali da nasiharta har ta kai yau na nemi Aliya wacce da farko tun ina cikin yin sex da ita na ga ta rikiɗe ta zama tsohuwa tuguf kafin kuma ta koma wata halitta kamar Bushiya 🦔 dukkan jikinta gashi ne,to a lokacin ne na soma yin ihu amma ga banza don kuwa babu mai jin mu,daga ƙarshe dai maganin da na saka mata ya saki jikinta shi ne ta yi wata irin kururuwa ta soma yayaga min jiki, Allah ne yayi sa'a nurse Fatee ta zo kan lokaci ashe ita ma tana ɗauke da wani sirri nan ta fitar da Aliyar waje.Please Maheer ka taimaka min kar na mutu ina kafiri,dama can saboda na yi ta aikata abin da nake so ne yasa na ƙi musulunta amma na san da tabbas addinin Musulunci ne gaskiya"
Idon Maheer sun yi mugun ja kamar za su faɗo tsabar tashin hankali,sai a lokacin kuma Dr Muhamud ya shigo.Yayin da Dr David ya soma ihun fitar rai,duk yadda suka so su basa kalmar shahada kuma abu ya cuttura don ba a yi wa Allah wayo.Shi yasa yake yi mana hani akan kar mu jinkirta yin tuba,ga shi dai Dr David ya san Allah ɗaya ne amma ya biyewa son zuciyarsa don ya sha giya yayi zina son ransa ya ƙi musulunta.
"Ya fa mutu!" cewar Dr Muhamud cikin wata irin murya,Dr Maheer ya lumshe idonsa da suka yi masa mugun nauyi kafin ya ce "na gani,ka rufe shi da zane ka kira gidansu ka sanar "
Dr Muhamud ya ce "ya kake magana haka Maheer? Ko addu'a ai sai yi masa amma kana yin abu kamar ba abokinka ba"
"Me kake so na ce? Na saɓawa umarnin Ubangijina akan soyayyar da nake yi wa abokina? Ina ka taɓa ganin an nema wa kafiri gafarar Allah? Ina ce kusan kullum a gabanka nake faman yi masa shelar shiga musulunci amma ya ƙi duk da kuwa ya san gaskiya ce, wannan ma izina ce ga masu hali irin nasa ni babu abin da zan ce in banda Allah ya bamu haƙurin rashinsa " yana gama faɗa ya fita ya bar ɗakin,a can wurin flowers ya tsinkayi Aliya ta game kai da gwiwa tana kuka.
Dakyar ya iya isa inda take,maƙishinsa na yi masa wani irin ciwo ya ce "kukan me kike yi bayan burinki ya cika ya mutu ?"
Ta ɗago cike da takaici ta ce "ka san tsawon ƙarni nawa nake cikin duniyar nan amma ban taɓa sanin ɗa namiji ba? Ka taɓa rasa wani abu naka mai muhimmanci ne? Na sani Ni tsohuwa ce banda wani budurci amma mutumcina fa? Gangar jikin da nake ciki shin na yi mata adalci ne?"
Ƙure ta da ido Maheer yayi jin tana zancen ƙarni,wanda duk ƙarni ɗaya ya fi shekara ɗari biyu.
Aliya ta saki wani murmushi mai ciwo kafin ta ce "mutane na min laƙabi da matsafiyar aljana saboda an haife ni da ido guda uku ,biyu normal da ƙato a tsakiyar goshi wanda sai da na sha wuya sosai kafin na ɓatar da shi a bar ganinsa.Sanadin ido ukuna aka tsane ni,kullum cikin tsangwama ta ake duk da kasancewar ina da kirki,ina kuma son bil'adama duk da cewa dai wani sa'in na kan sha jininsu .Mahaifiyata ta haife ni tun ƙarni biyu da suka gabata,ta kuma mutu a ranar da ta haife ni.Na samu labarin cewa mahaifiyata ta samu cikina ne silar tozarta wani tsohon almajiri da yake yawon yin bara cikin gari da kayansa masu datti.Wannan tsoho shi ne mahaifina,wanda ƙiyasin mutane sun tabbatar cikin ɗayan biyu ne,ko dai jinsin aljanu ko kuma tsohon matsafi da ya laƙanci baƙin tsafi wanda yake dawo da ruhi izuwa duniyar bil'adama.
Na yi rayuwa ni ɗaya na tsawon ƙarni biyu,duk mutanen da na sani tun ina ƴar ƙarama duk sun mutu an haifi wasu su ma haka suke tafiya suna barina.Dayawan mutanen ƙauyen da aka haife ni suna mamaki in sun ji ina labarin abubuwan da suka shuɗe tsawon shekaru,amma kuma ga ni nan dai cikin ganiyar ƙurciyata saboda ban tsufa,alƙalamin daɗuwar shekaruna ya tsaya cak tun sa'ilin da na shiga shekara ashirin da huɗu tun ƙarni biyu na baya.
Ina rayuwa ni ɗaya ,cikin wani ɗakin kara da na gina shi da hannuna a can cikin daji.Yanayin shigata ya banbanta da na mutane ,don tamkar wata mahaukaciya haka nake suturta jikina.
Ba zan manta ba wata rana,ina tsaka da cin tururuwa da ƙwari don sune abincina sai na ji an bubu min ƙofa tare da cewa " ɗari shidda da sittin da shida?"
Kawai sai na samu kaina da amsawa "na'am" ina yin wannan furicin sai na ji tamkar an yi min wankin ƙwaƙwalwa,sai a lokacin ne kuma na tuna cewa sunana shi ne Evaliya.