Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 14
Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 14: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 14. "Evaliya? Evaliya? Evaliya?" na ji wata murya ta kira ni har…
4,450 words
"Evaliya? Evaliya? Evaliya?" na ji wata murya ta kira ni har sau uku,sai dai wannan karon ban amsa ba sakamakon ƙaton buzuzu da na saka a bakina. Shiru duk muka yi ni da baƙuwar muryar da ban san ta wace ce ba,amma duk da haka ina jin tamkar tsayuwar wasu sabbin abubuwa waɗanda ba a gani.To daga wannan lokaci ne kuma na fahimci wace ce ni, sannan na gane zan iya sauya siffa hakazali zan iya yi wa wani aiki irin yadda bokaye suke yi dalilin da yasa na soma cutar da duk wani da ya biyo hanyata nake kuma kyautatawa waɗanda suke zaman lafiya da ni.
Baƙin aikina na farko ba zan manta ba,wata rana ne ina zaune bakin ƙofar ɗakina ina wasa da maciji sai kawai na ji muryar wani namiji.
"Evaliya mai ƙarfin iko,budurwa jeji,shugabar matsafa na zo nan ne domin ki taimake ni" iya muryarsa kawai na ji tukuna ban gansa ba,sai da na nutsu na duba sai na ga ashe shi ne a cikin siffar wani ƙayon ɓera.Muna haɗa ido na gane shi,domin kuwa na san iyayensa waɗanda duk suka yi mulki a ƙalla zamani kusan biyar.
"Me na zo nema?" ita ce tambayar da na yi masa wancan lokacin.
"Ina son kawar da ɗan uwana ne kafin shi ya kashe ni,saboda mun yi tarayya akan buri guda wato hawa karagar mulki a yadda kuma na fahimta yana iya yin komai akan hakan" wannan ita ce buƙatar da ya zo min da ita wacce kuma ya san ina iya yi masa maganinta.
Sai da na yi dariya mai isata,su ma maƙarabaina suka shiga taya ni wato aljanai da ruhikan da nake rayuwa da su, can kuma duk muka yi shiru.
Na ce masa "Mene ne farashin da za ka bayar?" a wancan lokacin in za a iya mutum mugun aiki ba wai kuɗi ake buƙata ba kamar yadda bokayen wannan zamani ke yi,a'a mu jini muke so jinin kuma na ƴan adam.
"Ƴata zan baki mai wata ɗaya da haihu" ya faɗa saboda ya yarda ya rasa ƴarsa akan kujerar mulki wacce duk rintsi wata rana zai sauka ko kuma mutuwa ta sauke shi.
"Ka tabbata za ka iya kawo min ita a yanzu?"
"Eh wannan ba damuwa ba ce,zan sa masu tsaron lafiyata su kawo miki ita a nan.Ai babu abin da ya fi muhimmanci kamar sadaukar da rai domin samun muƙami da ƙarfin iko"
"Je ka kawo min ƴar taka" na basa umarni,ina gama faɗa sai ya nufi hanyar da za ta mayar da shi can cikin gari.Ni kuma haka na ci gaba da zama tare da ƙaguwa na ga babyn wacce nake ji a raina za ta iya yi min wani amfani domin kyautata gobena.
Daga ƙarshe dai ɗaya daga cikin masu yi masa hidima ya kawo min babyn,saura ƙiris na mutu don daɗi saboda yadda na ga taurarinta na da mugun haske . Cikin ƙwarewa da iya aikin siddabaru sai na soma bincike akan rayuwarta ta gobe,sai na gano cewa ita ce sarauniyar zamaninsu muddin ta rayu har zuwa lokacin.Sannan za ta yi farin jinin samari,daga cikinsu akwai sarakuna da kuma masu muƙamin mulkin gwamnati,ba kamar ni ba da babu wanda ya taɓa cewa yana sona saboda ni ɗin banda kyawun gani sannan kuma na banbanta da mutane. Wani tambari na yi na matsafa na yi zanen ido,da ƙwarangwal da niyyar canja gangar jikina daga nawa zuwa na ƴar ƙaramar babyn haka na soma yin baƙin tsafin duk da na san aiki ne mai matuƙar haɗari amma na gaji da gangar jikina.Cike da ƙwarewa na kammala aikina,ruhina ya shiga cikin gangar jikin babyn,yayin da na mayar da na babyn cikin nawa.A wannan lokacin abin da ya rage min shi ne samun ahali,wannan yasa na bazama yawo a cikin doron duniya a haka na haɗu da wasu mata da miji waɗanda sun shekara wajen goma sha biyar amma ba su taɓa haihuwa ba. Ni ce nan na ɗauke jinin period ɗinta wanda yayi silar zuwanta asibiti aka tabbatar mata tana ɗauke da juna biyu,a ranar ita da mijinta kamar su yi hauka tsabar murna ba tare da sanin ni ce nan zan zama ƴarsu ba.Kamar da wasa haka na saka cikin matar yana ta girma cikin ƙanƙanan lokaci har ta shiga watan haihuwa,kamar yadda na tsara haka komai ya tafi a gida ta haifo ni wanda a ƙiyasi watana goma sha ɗaya a duniya amma a wurinta yau ne ta haife ni.Sosai na shiga canyara kukan jarirai wanda hakan ne ya jawo hankalin maƙwabta suka san ta haihu.Bayan ta yi min wanka ta kimtsa ni cikin wani tatausan tawel sai ta soma yi min hoto ,yadda fitila ke dalle min ido sai na ji duk na tsani haka a ranar na tarwatsa wayarta ta ci screen kafin ma ta kai ga turawa mutane hotunana.
Bayan mijinta ya zo shi ma sai hau murna,tuni kuma maƙwabta suka soma shigowa duk wacce tsakani har da Allah ta yi murnar haihuwata haka zan yi mata abin alkhairi ta hanya buɗe mata business ɗinta,ƴan baƙin ciki masu hassadar uwar riƙona kuma haka na bi duk na cutar da su don ba zan manta ba wata mata uwar ƴan surutu sai cewa ta yi "Fannah wannan baby taki ƙatuwa da ita dube ta kamar ba jaririya ba" sosai na ji haushin furucinta,amma kuma don iya ƙwanƙwanto haka ta tsure ni da shegun idonta tana kallo.Ni kuma don in nuna mata ba duka komai ne in an gani ake tankawa ba kawai sai na ɗaga mata gira tare da murguɗa mata baki a tsorace ta ajiye ni tare da fita tana waiwayena nan ɗin ma gwalo na yi mata wanda yayi sanadin faɗuwarta to tun daga lokacin ta zama mai shanyewar ɓaren jiki kuma ta kasa yin magana.
Sai mace ta biyu wacce bakinta yake kamar na aku ga kuma shegen tambaya kama ma'ila'ika.Ba zan manta ba bayan ta sha kunun barka kawai ta soma yi wa Mamana tambayoyi har ta so kan haihu,"Fannah kika ce je ɗaya kika haihu babu ungozoma to wa ya yanke miki cibiyar jaririya? Ko kin iya? Har mahaifar ke kika rufe ta? Na ce duk uban jinin nan na haihuwa ke ce kika wanke shi alhalin kin haihu?" ji na yi kamar na kama da wuta,saboda a cikin abin da ta zano babu ko ɗaya da ya samu Fannah wacce take sabuwar uwa a gare ni sam ban bata wahala ba haka ta haifo ni kamar wacce ta zo yin kashi,sannan babu wani jinin haihuwa,ita kuwa mahaifa da cibiya duk babu su saboda tun ranar haihuwar wacce nake cikin gangar jikinta aka yanke su.A lokacin Mamana wato Fannah shiru ta yi ta kasa cewa komai,ita kuwa ƴar jarida ta je za ta sake jego wata tambayar na yi amfani da ƙarfin ikona na dantse mata harshe tun lokacin ba ta sake yin magana ba.Ba kuma shikenan iya abin da na yi mata ba,a'a haka duk dare nake zuwa can gidanta na shiga cikinta ina juyi tare da bata azaba irin ta naƙuda haka za ta haifo ni na faɗo jini na yi mata zuba sannan in ta zo yanke cibiya sai na mayar da ita maciji a ƙarshe dai tun hankalinta na iya ɗaukar dramar har ta kai ta rasa hankalinta.
Bayan sati guda da haihuwa ta sai aka zo zaɓen suna,ni ce nan na juya kwanyar wanda yake sabon mahaifi a gare ni ya zaɓar min sunan Evaliya.Sosai na yi murna ganin yadda suke nuna min so,na ji daɗi ni ma na samu asali sai dai fa babu wani abu da ya canza dangane da ruhina iya gangar jikin ce ke sabuwa.Ban farga cewa har izuwa yanzu aikin banza ba ne nake ,domin ba a canzawa tuwo suna sai da na soma yin wayo aka saka ni makaranta haka yara za su dinga yin wasa suna ware ni ba su so na shiga cikinsu,wasu ma da zarar sun ganni guduwa suke sai daga baya ne na gane cewa idon yaro na ganin sharrin abin da mayafi ya luluɓe.Wato idona uku haka ya bayyana a sabuwar gangar jikina,babu mai iya ganinta duk duniyar nan sai yara ƙanana ko kuma aljanai.
Wannan yanayi da na samu kaina na rashin karɓuwa a wurin ƴan uwana ƙawayena sai ya soma jefa ni cikin damuwa.Kullum in Mama ta bani abinci sai na ƙi ci haka komai ta yi min wanka sai na sake mayar da dattin jikina,in kuma Baba ya dawo sai yayi ta yi wa Mama faɗa sai kuma hakan yake yi min ciwo.Don ba zan manta ba akwai ranar da ya mari Mama,ni kuma na saukar masa da ciwon hannu wanda kuma shi ne farkon binciko matsalar gidan.Don kuwa ana ta neman magani amma hannu ya ƙi warkewa,da aka soma yin na gida ne wani boka ya ce "ai wannan sihiri aka yi masa,ba zai warke ba dole sai ya nemi gafarar wanda ya cutar" Baba na jin haka sai ya nemi Mama gafara ni kuma na cire ciwon da na saka masa.Na yi tunanin duk komai ya ida, kwatsam Baba ya fito da zancen aure wanda hakan ya tayar da hankalin Mamana amma duk ƙoƙarina na ganin an fasa auren abu ya cuttura,sai ranar da aka kawo amarya na fahimci cewa wata shararriyar matsafiya ce ya auro na saki murmushin mugunta don na san ai duk iya ƙwarewarta da tsafi ba za kai ni ba ƙila rabon a yi ne yasa ta auri Babana.Tun daren farko na caza mata kai yadda na jefa wa Baba wani laƙanin tsafi ya shatata mata fitsarin kwance,sai takaicin nata ya zama biyu ga shi bai kusance ba ga kuma yayi mata fitsari kan sabuwar katifa.Tun asubah ta fito tana masifa,ni kuma ina gefe kusa da Mamana macen da ke mugun sona duk da yadda ta soma lura ba normal mutum ba ce ni.
Da rana ƙawayen amarya suka zo,ana ta yi wa Mamana habaici daga cikinsu ma akwai wacce tsatsauyi yasa ta dungure min kai tare da shammata ta wai mai idon kifi,a zuci na ce ' za kuwa ki ga idon kifi'
Gefe na koma daga can bakin ƙofa ina kallon yadda suka ɗoran manyan tukane kan wuta wai al'adarsu ce washegari garin aure amarya za ta yi girki a rarrabawa mutane. Ina zaune hankali kwance har lokacin motsa miya yayi,ita wannan wacce ta dungure min kai ita ce ta je don motsa miyar tana buɗe tukunya muka haɗa ido huɗu da ita .Don a maimakon naman kaji a'a kaina ne kwance cikin tukunyar ina yi mata wani makirin murmushi,ta haɗiye yawun tsoro kafin ta waigo inda nake zaune nan ɗin ma ƙure ta na yi da ido.Ƴan magana na cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne,to haka take ita ma ƙawar amarya matsafiya ce amma ko a cikin matsafan ita jaririya ce.Murmushi na sakar mata mai nuni da ba ta ma ga komai ba ,tun da ta yi karanbanin taɓo ni har na bayyana ɓoyayyar fuskata a gare ta to ta shiga uku.Cike da mugunta na sa ta tsoma hannunta cikin tukunyar da ke kan wuta tana tafasa,ta ƙurma uban ihun da ya jawo hankalin dukkan sauran duk suka yi kanta sai a lokacin kuma na shige ɗaki...... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
23
Har suka gama tsiyar guminsu suka gama Mama ba ta fita ba haka ta jawo ni ta shimfiɗe kusa da ita tana dadaɓa ni irin in ana so yaro yayi bacci.A lokacin shekaruna biyar ne a cikin sabuwar gangar jikina,ido na lumshe amma hakan bai hana ni ganin Mamana tana hawaye ba. Ban san cewa na yi mata ƙuri da ɗayan idona na tsakiyar goshi ba sai da na ji hannunta na shafar idon kafin ta ce "ban so kina buɗe idon nan Aliya" saboda ita haka take kirana a cewarta wancan sunan kiristoci ne,na saki murmushi na ce "Mama kenan kina ganinta?"
"Ina gani mana Aliya ,tun ranar da na haifo ki na ganta"
"Amma me yasa ba ki nuna alamun tsoro ba?"
Sai da wasu hawayen suka zubo mata kafin ta ce "saboda ita uwa tana son ɗanta a duk yadda yake,sannan duk abubuwan da suka gudana wurin haihuwarki na fahimci ke ƴar baiwa ce ƙila shi yasa na haife ki haka nan"
Shiru na yi tare da buɗe idona biyu sai na ƙure ta da dukkan ukun,wato abin da na fahimta matar nan tana mugun sona duk da ta ga alamomin da zai sa ta ji tsorona ko kuma ta yi wa kanta tambayoyi amma ta yi shiru ta ƙyale saboda ta jima tana roƙon Allah ya bata haihuwa gani take in ta nuna ba ta sona kamar ta yi wa Allah butulci ne.Na rungume ta ƙam,a wannan ranar ce na ji a raina ina iya canza BAƘIN RUHIna izuwa fari,komai niyya ce hatta shaɗan da yake hatsabibi farko ba haka yake ba shine ya mayar da kansa sheɗaniya.Sai na yi ta tunanin ta ya kenan zan canza? Amma ban samo amsar ba muryar Baba ta ratso ɗakin da muke kwance.
"Ki warware baƙin sihirin da kika yi wa ƙawar matata ko kuma na lakaɗa miki shegen duka" shi ne abin da ya faɗa cikin kumfar baki. Da idona na tsakiya na kafe shi,amma da dukkan alamu shi bai iya ganin haka.
Cike da ladabi Mama ta ce "to babu matsala" tana gama faɗar haka sai ta dube ni tare da sakar min murmushi wanda tuni na fahimci abin da take nufi,na saki ruhin abokiyar amarya sai dai fa hannunta na nan a ƙone.
Da suka yi girki sai suka hana mana ni da Mamana ,ni kuma na lalata dukkan abincin amma idonsu bai iya ganin haka ba wannan yasa duk suka ci cikinsu ya kumbure suka yi ta yin amai da guduwa.Ni kuwa da Mamana ɗan abin da ba a rasa ba ta nemo muka ci, da dare muna jin yadda Baba da amaryasa suke saffa da marwar shiga banɗaki a taƙaice dai wannan daren ma babu wani zancen raya sunnah.
Tsawon kwanakin da Baba yayi a ɗakinta haka na yi ta ƙirƙiro musu matsala iri-iri wacce ta hana su kasancewa abu ɗaya.A cikin ranakun akwai wanda na haifar mata da zubar jini,wani daren kuma na mayar da Babana shi da mace babu banbanci,yayin da wani dare kuma na fesa musu dafin cuta duk ƙuraje suka fito musu suka kwana dare soshe-soshe.
A ranar da Babana ya dawo ɗakin Mama na warkar da shi garas,sai kuma na yi balaguron ruhi don ba zan so na ji ko na ga yadda suke mu'amala ba tun da ni dai ba yarinya ba ce.A cikin balaguron ruhin da na yi ne na haɗu da wata mata mai ɗauke da farin ruhi ana ce mata Yabobo.Ban san me ta gani a tattare da ni ba wanda yasa ta rage min ƙarfin mugunta sai kuma ta bani wata power mai tsabta.A cikin wannan daren kuma ta zaga da ni duniyoyi biyu mabanbanta da ke can ɓoyayyar duniya.Ta koya min karatu da kuma bani labarinku kai da Haule,sannan ta sanar da ni mission ɗina wato kula da duk wani lamarin Haule da nuna mata hanyar da ya dace.Yadda muka shagala sosai ni da ita yasa ba mu farga gari ya waye ba a duniyar bil'adama,sai da na ji ana kukan makoki wai na mutu a lokacin ne kuma na dawo da esprit da RUHIna a gangar jikina.Sosai Mamana ta yi murnar haka,ta zubar da hawayen farin ciki tare da rungume ni ƙam a ƙirjinta.
Kasa ɓoye mata abin da na je na yi,amma da mamakina sam ba ta ji tsoro ba kuma ta ci gaba da zama da ni a haka ƙila don ba ta taɓa haihuwa ne ba.
Kwana biyu Baba yayi a ɗakin Mama kafin ya koma na amarya,a wannan gaɓar so nake na kawo ƙarshen komai wannan yasa na shiga tunanin Baba na soma controling ƙwaƙwalwarsa.Sosai na saka ya ɗirkawa amarya shegen duka ya yi mata rauni sosai don sai da ta samu kariya a ƙafa ,hannunta guda kuma ya goce.Ban tsaya a nan ba haka na sa Baba ya dinga yin Yare ya fi kala goma na mutanen ƙarnin da suka wuce,sannan sauyawa idonsa fasali sannan na sa yayi ta aman ɓoyayyen sirrin amarya da take tunanin babu wanda ya sani.
Washegari tun da safe danginta,dangin matsafa suka zo suka tafi da ƴarsu da Baba ya je biko kuma suka hana masa duk a tunaninsu manyan aljanai ne a kansa ba su san ni ce sheɗaniyar ba.
Tun daga wannan lokaci zaman lafiya ya wanzu a gidanmu,sosai iyayena suke nuna min so da ƙauna.A lokacin da na shiga shekara ta goma ce Mamana ta kwanta ciwo,jinyar da ba ta tashi ba ta yi sanadin mutuwarta.Rashin Mama a gare ni shine ya koyar da ni yadda ake jin ƙunci da damuwa,sai duk na bi na ɗaga hankalina da na Babana don kusan kullum sai na tashi tsakar dare ina nemanta.
Tsawon watanni uku muna cikin jimamin rashi kawai sai guɗa muka ji wai Kaka mahaifiyar Baba ta yi masa sabon aure.Tun da idona ya sauka kan amaryar na ji wata irin muguwar tsanarta a raina,sai dai kuma babu yadda zan yi da ita saboda mace ce mai son addini da kuma yawan yin sallar dare.Ina ji ina gani Baba ya tare shi da amarya,wacce ba ta rage ni da komai ba tun daga wankin kayana,abinci breakfast da duk wani abu da ya shafe ni baiwar Allah haka take yi min komai sai dai fa ba su sa na so ta ba.Saboda ina taya Mamana kishi,akwai ranar da na yi niyyar cutar da ɗan cikinta amma ban samu nasara ba saboda yadda duk bayan sallah asubah take yin Azkhar ta shafe dukkan jikinta sannan hatta cikin ma tana yi masa addu'o'in tsari.
Da na rasa hanyar da zan bi na kore ta kawai sai na tsiro da sabon iskanci na bar cin abinci kwata-kwata.Juyin duniya ta yi-ta yi na ci abinci amma na ƙiya,in Babana ya zo sai yayi ta yi mata faɗa ni kuma ina jin daɗi.Da na fahimci in an taɓa ni Baba na yin fushi,sai na dinga ƙirƙiro ƙananun matsaloli a tsakaninsu.In ta wanke kayana sai na furza musu datti su koma kamar ba a wanke ba,sai na ta yin kuka ina cewa Baba an bar kayana da dauɗa don an ga mahaifiyata ba ta da rai.Haka shi kuma zai tsare ta yayi ta balbalin bala'i,wani sa'in har marinta yake yi sannan sai su fi sati guda ba su yi magana ba wanda hakan ya fi komai yi min citta don in suna gaba nan ɗakin Mamana Baba ke zuwa ni kuma na ta yi masa hirarta.
Ban taɓa sanin addu'a makamin mummuni ba ce,kuma duk wanda ya riƙe ta ya riƙi hanyar tsira sai da matar Baba tsiro da wani sabon salo.Haka za ta yi ruwan addu'a ta feshe duk katangun gidanmu da na dakuna,turare Habbatu sauda da kuma zuba ta a cikin abinci sai ya zama ɗabi'arta.Babban abin da ta toje akai shine sallar dare,haka take kwana kan dadduma tana yin addu'a Allah ya tunkuɗe fitinar da ke sa suna samun saɓani ita da mijinta.Sosai addu'arta ke ƙona min ruhi tana raunata ni,so nake na bar gidan sai dai ban san ta yaya ba.
Wata rana ina kwance kan shimfiɗa dukkan jikina yayi ja sai raɗaɗi yake yi min saboda yadda take neman tsari daga sharrina ba tare da ita kanta ta san cewa ni ce matsalarta ba.Kawai sai ga Yabobo ta bayyana a ɗakina,"lokacin barin gidan nan yayi Evaliya zan nuna musu kamar kin mutu in sun rufe ki zan je na tono ku amma ki yi haƙuri ki bar Babanki na aro ya huta yayi rayuwar farin ciki,na san in kin yi haka mahaifiyarki ta aro ita ma za ta ji daɗin haka" shine abin da Yabobo ta ce min,banda wani zaɓi kuma da ya wuce na yarda da haka ɗin.
Washegari suna tashi suka ga gangar jikina ta sandare,aka kai ni asibiti likitoci suka tabbatar musu da na mutu.Baba ya kuka sosai na rashina ba tare da ya san cewa ni ba ƴarsa ba ce,haka aka yi min wanka aka je aka haƙa kabari aka binne ni.
Ina nan kwance ina jiran Yabobo ta zo ta tono ni,sai ga kuma wata gawa da aka kawo ba tare da ita ma ta mutu ba.Haka nake kallon komai har suka ida binne ta,a daidai lokacin ne kuma Yabobo ta zo ta ciro ni daga cikin kabarin sai kuma muka zuba ma na wannan baiwar Allah ido yadda take motsi take shirin yin mutuwar gasken.
Mu muka taimaka mata muka fitar da ita,sai kuma ta bamu labarin cewa ita Yayar Haule ce sunanta Aliya ga kuma silar zuwanta maƙabarta ba tare da ta mutu ba.Tun daga ranar ne kuma na ɗauki sunan Aliya matsayin nawa dama can haka Mamana ke kirana,sai kuma na shigo wannan ƙasar don nemo Haule ban kuma sha wahala ba aka kawo ni gidan da take aiki" Aliya na gama feso tarihinta Maheer ya ce "ita kuma Aliyar tana ina kin ce tana da rai?"
"Eh tana can dajin ceto,tun lokacin ta rasa hankalinta za ka ga ta yi maganar masu hankali bayan minti biyu kuma ta koma ruwa biyu.Na ɓoyewa Haule tarihina ne gudun kar ta shiga damuwa ta kasa ajiye hankali ta fuskanci babban ƙalubalen da ke tunkaro ta"
"Me yasa kika karɓa gayyatar Dr David ?"
"Ƙaddara ce da kuma neman ƙwaƙwaf na bin didigin abin da bai shafe ni ba,haka ba zai amfana min komai ba.Ina son sanin cikakken labarin Lubna ne shi yasa nake kula Dr David ashe shi da tasa manufar"
"Yanzu ai kin samu sai ki tashi ki koma gida,gobe ma ki je ki nemo gulmar" Maheer ya faɗa cike da takaici yana tunanin ina Haule ta shiga? Suna nan tsaye mahaifiyar Dr David ta shigo tana kuka,da aka nuna mata gawarsa kuwa sai da aka bata gado tsabar yadda ta shiga shock amma hakan bai hana aka soma shagalin bikin rufe shi ba. Tuni kafafen watsa labarai sun samu labarin mutuwarsa.Duk yadda Dr Maheer ya so kwantar da hankalinsa da ture lamarin Haule amma zuciyarsa ta kasa ɗauka,haka ya je ya buɗe ofis yayi zaune abin tausayi.Mutane dubi suke mutuwar Dr David ce ta jefa shi wannan halin ba su san cewa tunanin abincin ruhinsa yake yi ba.
Lokacin da Aliya ta koma gida ta tarar da Yasmine ta farka da dogon baccin da take ta ɗora wata sabuwar drama a gidan Hajiya . A falo ta tarar da Lubna da kuma ita kanta mai gidan,yayin da Yasmine ta jera kiras ɗin ƙwai ya fi ashirin tana ta ɗaukar ɗaya bayan ɗaya tana haɗiyewa ido a rufe. Aliya ta yi tsaye tana kallonta,tuni ta fahimci MACIJIN CIKI(MRS SADAUKI) ne cinye ɗanyen ƙwan ba wai ita Yasmine ɗin ba.
"Ki taimaki ki hana ta cinye min ƙwayaƙwayi,kaf abincin da aka yi na gobe ta cinye shi yanzu kuma ta koma da ƙwai.A ƙalla ta cinye kiras ya fi biyar" Hajiya ta faɗa tana hawaye,Aliya ta ce "hajiya ki koma ciki zan sa ta amayo duk wanda ta haɗiye" ai kuwa Hajiya sai ta ɗauki shawarar Aliya ta shige ɗakinta sai a lokacin kuma ita Aliyar ta yi amfani da powerta don dakatar da Yasmine sai ta fahimci cewa macijin jikinta ana ciyar da shi da jinin mutane yau kuma da aka killace ta babu yadda ya iya shi ne yake cin abinci don gusar da yunwarsa sai dai abu ya cuttura don abinci ba zai yi masa maganin yunwa ba.
Aliya ta dubi Lubna kafin ta ce "matso ki gani" ba ta musa ba ta matsa,sai Aliya ta kama yatsan Lubnar ta tsaga shi nan take jini ya soma zuba.Yasmine wacce idonta ke rufe tana jin ƙarnin jini kawai ta buɗe idonta waɗanda suke sak na maciji,tana ganin jini sai ta kama yatsan Lubna ta soma tsotsa na tsawon lokaci kafin ta saki ta ɓingire bacci.
Cike da tsoro Lubna ta ce "me hakan ke nufi?"
Kai tsaye Aliya ta bata amsa da "saboda a kullum ɗaya daga cikin member ɗin family yana shayar da ita ɗigon jininsa,shi yasa na bata naki "
Murya na rawa Lubna ta ce "amma ai ni na fita daga cikinsu"
Aliya ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo kafin ta ce "har yanzu sunanki yana rubuce cikin fayil ɗinsu,ba zai taɓa gogewa ba sai ranar da kika yarda kika bada ainahin labarinki sai a yi miki magani" tana gama faɗar haka ta yi gaba.
★JAPAN
Bayan mun gama waya da Innarmu sai na soma jiyo wani irin kuka kamar na doki kamar na jaki.Ban tsaurara bincike akan sai na san na mene ne ba kuma daga ina ya fito,kawai na samu wuri na kwanta.Bacci nake son yi amma tunanin halin da Maheer yake a wannan lokaci sai ya tsaya min a rai,a hankali na lumshe idona tare da lalubo tunaninsa cikin ikon Allah kuwa na same shi a zaune a ofis duk ya hargitsa kashin kansa,idonsa sun yi ja jawur kamar wanda yayi kuka. Muna haɗa ido,ya jefo min tambayar"ina ne nan kuma kika je? Da izinin wa kika fita?" ban kuma kai ga basa amsa ba sai ya juye dubansa kan system ɗin da na gama hira ni da Innarmu.Wani furici yayi nan take ta tarwatse ta zama gari liƙis,yadda ƙarar fashewarta ya fita sosai har sai da na zabura amma ban buɗe idona ba.
Hannnsa ya tsaga tare da yin amfani da jininsa yayi min wani rubutu a ƙasan marata,ban san mene ne ya rubuta ba saboda ba da Yaren Hausa ko turanci ba ne harufan ma ban san su ba.
"Haule?" na ji muryar Yaya Aliyu,da sauri na buɗe ido ina mai amsawa "na'am!"
"Karar mece ce na ji?" ina jin tambayar da yayi sai na dubi system ɗinsa sai kuma na ganta ras babu abin da ya same ta.Ban sani ba ko don ya ga na kalli saitinta ne yasa shi zuwa ya soma dubata,can kuma ya ɗago ya dube ni ya ce "Haule me kuke ɓoye min ke da Innarmu? Mene ne ba ku so na sani? Ko kina tunanin zan iya cutar da ke ne?"
Cike da mamaki na ce "don me yasa kake faɗar haka Ya Aliyu? Ni ban ɓoye ma komai,kawai dai Innarmu ta ce na koma can inda nake aiki lokacin karɓar muƙamina bai yi ba" na faɗi haka ba tare da na san dalilin yi masa ƙaryar ba.