Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 15
Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 15: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 15. Ya ce "amma me yasa kika goge duk hirar da kuka yi ke da…
4,467 words
Ya ce "amma me yasa kika goge duk hirar da kuka yi ke da Innarmu? Sannan ba ma iya ita kaɗai ba har da wasu bayanaina masu muhimmanci.Tun yaushe kika fara sarrafa ƙarfin ikonki? Kuma ma da kike cewa ba yanzu za ki karɓi kujerarki ba kenan sai yaushe alhalin hatta sarƙar juya ruhaniya ga ta nan a wuyanki?"
Na kai hannu na taɓa sarƙar da na ɗauko a dajin sirri,shiru na yi na kasa ce masa komai .Ya furzar da huci ya ci gaba da cewa "me yasa ba ku so iyayenmu maza su san da bayyanarki?"
"Saboda lokacin bai yi ba Ya Aliyu,ka sani shi fa komai yana da tsari ba haka ba ne ake yinsa kara zube .Ko ita sarƙar wuyana ban soma yin aiki da ita ba"
"A'a kin soma mana Haule,tun da har kika iya gane duk members Family wannan yasa kika raba ni da Yasmine.Faɗa min son ta kike yi ko me?"
Sai da zuciyata ta buga jin wani zance da Yaya Aliyu ke yi min,amma sai na kawar da kai ban ce komai ba.Ya ce "na ji na bar miki amma ki mayar da ita gidansu lokacin amfani da ita bai cika ba sai ta kai 18 years"
Zuciyata na luguden tashin hankali na ce masa "okay!" kawai sai ya fice ya bar ni nan,sam kasa bacci na yi haka na tashi na yi alwala sai dai babu hijabin da zan yi sallah kawai sai na hau yin zikiri.
Washega haka na haddace lambar Innarmu kafin Yaya Aliyu ya kai ni ɗakin sirrinsa wanda ta hanyarsa ne yake yin balaguro ya kuma zaga duniya.Sam ban yi mamaki ba ganin ta madubin tsafi ne zan bi na koma can Kamaru,da jininsa yayi amfani ƙofa ta buɗe muna kallon juna cike da soyayyar ƴan uwantaka muka rabu na ratsa madubin ina ayyana wa a raina inda zan sauka.Gidan Hajiya na ce ,sai dai ban faɗi a wane wuri ba hakan yasa na faɗo a cikin ɗakin Maheer a kuma bisa gadonsa.....
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
24
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 ________________________
Agogon da ke manne da bangon ɗakinsa na duba,ƙarfe bakwai da wasu ƴan mintina.Na tashi na fita falo sai dai ƙofar fita a rufe take dole na dawo na ƙara haye bed ɗinsa ina mai tunanin ƙila a can asibiti ya kwana.Na lumshe ido tare da ƙanƙame pilow ina shaƙar ƙamshin turarensa da ya mamaye ko ina,kamar an mitsike ni kuma na tashi na soma yin binciken duk wurin da na samu har ya kai da na buɗe drowersa.Cak na tsaya ina kallon wani dunƙulalen dutse mai shegen haske,a samansa an yi zanen shatin yatsu biyu manuniya babba da ƙarami.Dutsen na shafa nan take hoton fuskata ya bayyana tare da soma rawa tamkar a cikin ruwa,ban san lokacin da na furta "waooo!" haka na ci gaba da tsayuwa ina kallon dutsen da ban san mene ne amfaninsa ba.
Na rufe drower sai kuma na shiga toilet ɗinsa,na taɓe baki ina mai cewa "yau ni ma dai sai na yi wankan cikin bahon wankanka,ah to kullum sai dai in yi ta gyara shi amma ban taɓa amfani da shi ba" na yi furucin kafin na soma haɗa ruwan wanka masu ɗumi na zuba kalolin sabulu kamar wata baƙauya haka na cire kayana na shige ciki ido rufe nake tunanin abubuwa dayawa har tsautsayi yasa na soma yin nasa tare da yin furicin haɗa tunaninmu wuri guda.
Cak ya tsaya da tafiyar da yake yi yana mai kallona,ganin ya ƙure wuri guda da ido yasa na dubi saitin sai na sarƙar wuyana ce yake kallo wacce ta tsaya tsakiyar ƙirjina.Da wani mugun sauri na nitse cikin ruwan kafin kuma na buɗe ido tare da zaro su.Cikin sauri na yi wankan na fito na je gaban shower na ɗauraye jikina sannan na saka kayana,bayan na fita na ɗauko hiraminsa da yake ɗaura a kai na luluɓa na yi sallah.
Yunwa nake ji,ga kuma ɗaki a rufe.Dubarar buɗa frigine nasa na yi babu komai a ciki sai ruwa na ja tsuki na ce "baƙauye kawai" ban ida rufe baki ba aka turo ƙofa aka shigo.
Shi ne sanye cikin kayan likitoci,fuskar nan tasa kamar kullum babu fara'a.Jikina ne ya soma ɗan rawa amma na daure tare da kawar da kai daga dubansa,ina fara jin ƙarar takun sawunsa na yi saurin rugawa na yi cikin bedroom tare da tura ƙofa zan rufe amma ya tare ta ya wani hankoɗo ni na dawo baya kan ƙirjinsa.
Cikin masifa na ce "ni ka bar taɓa ni ka yi tunanin irin ƴan matanka ce waɗanda ba su san ƙimar jikinsu ba har suke yarda suna haɗa jiki da kai kuna...kuna..." sai kuma na yi shiru saboda girman kalmar.
"Muna me uhum? Me muke yi? " ya tambaye ni yana mai tsure ni da shegun idonsa irin na maciji ,tare kuma da haɗa dukkan hannuwana wuri guda ya matse.
"Ni ka sakar min hannu tun da ba matarka ba ce" na faɗa ina shirin hawaye.
"Allah ya kiyaye ma da ki zama matata,haka da ke ƙazama ko tsarki ba ki iya ba har kike ikirarin nan?"
Hawayen da nake ƙoƙarin mayarwa ne suka soma zuba kan kumatuna kamar an buɗe pampo,tun da nake ba a taɓa yi min wulaƙanci ba irin na yau.Murya a ɗan disashe na ce "kai ma ba ka iya ba"
Yayi wani murmushin gefen baki ya ce "me a ban iya ba?"
"Ban sani ba! Ba zan faɗa ba tun da ba ƴar iska ba ce"
"Ni ai shi ne ko na nuna miki?" yayi tambayar yana matso da fuskarsa kusan tawa da sauri na duƙe kaina tare da kafa haƙorana kan hannunsa na basa giritsiii na cije shi amma don masifa bai sake ni ba duk da kuwa na san ya ji zafi.
Ida tura ni yayi cikin ɗaki tare da yin furici ƙofar ta rufe kanta,sai kuma a lokacin ya sake ni.Idonsa na kalla cike da firgici yadda ya sauyawa kansa kammani ya ɗauko rigar rashin mutumci ya yafawa kansa.Yana fara cire kayan jikinsa na ruga a guje zan shiga toilet amma ƙofar ta matsa kanta ta koma can gefe,ko da nake juyowa daga shi sai gajeren wando hatta rigar ya cire hakan ya ƙara ninka farashin tsorona.
Tamkar mai cutar sandarewa haka na kafe jikin katanga ina jin duk jijiyoyin jikina na tsinkewa,kafin kuma numfashina ya tsaya cak a daidai lokacin da Maheer ya soma ƙoƙarin yin ƙasa da abin da ya rage masa na sutura.
★MAHEER
Tun jiya bayan sun samu kusancin tunani shi da Haule ya fahimci a ina ne take .Sannan system ɗin Aliyu da ke ɗauke da zantukansa ita da kanta ne ta sanar da shi wannan yasa ya goge komai da ke cikinta.Tun bayan kuma da suka rabu ya ji hankalinsa ya kwanta,saboda ko BAƘIN RUHIN ne da kansa ya zo ba zai iya kusantar Haule ba ballantana wani banza shi Aliyu duk da kuwa ba ya jin Aliyun zai yi yunƙurin taɓa Haule,amma sanin gurɓatacen jini ke yawo a jikinsa to kwanyarsa za ta iya faɗa masa banza-banza sannan yin rubutun a ƙasan mararta haka shine nutsuwar ruhinsa yayi shine domin tsaro ba don tsoro ba.
Yanzu kuma da ta lalubo tunaninsa sai ya ga tambarin baƙin ruhi a tattare da sarƙar wuyanta wacce bai taɓa sanin da zamanta ba sai lokacin.Dalilin da yasa ya zaburo ya dawo gida,sai kuma ya taras da tana zaginsa da kalmar baƙauye.
Wani makirin murmushi ya saki ganin numfashin Haule ya tsaya cak,da sauri ya ƙarasa ya ɗauke ta ya ɗora kan bed. Maɓallan rigarta ya cire yana mai kawar da kai don bai son kallon ƙirjinta duk da cewa kuwa ita ɗin matarsa tun tuni .
Ido ya lumshe ya soma bincike akan sarƙar ,har sai da ya gano amfaninta kafin ya gyara mata zaman rigarta.Fita yayi ya leƙa ya ga tuni su Hajiya sun bar gidan,sai a lokacin kuma ya dawo ya ɗauko Haule kamar wata baby haka ya manna ta a ƙirjinsa ya sauka ƙasa da ita.Can ɗakinsu ya kwantar da ita kafin ya saka harshensa a kunnenta yana yi mata wani abu wanda zai dawo da numfashinta ya kuma saka ta bacci.Can ta ja ajiyar zuciya tare da wawuro hannunta ta riƙe gam tana mai ci gaba da yin baccinta cikin nutsuwa.
Maheer ya ƙura mata ido yana kallo,dogon hancinta ya duba yana ƙiyasta ina ma ace ta yi ɓullen hanci ta saka ƴar sarƙar nan da indoyawa ke sakawa da tabbas sai tafi haka kyau.
Ya kai bayan hannunsa ya shafi gefen fuskarta yana jin wani masifafen sonta mai haɗe feeling ɗinta na tsarga masa.Cikin dabara ya janye hannunsa da ta rungume yana shirin tashi ya ji tana magana cikin shagwaɓa.
"Ban so Please! Ban so kar ɗora mini shi tsoronsa nake! Innarmu kin gani zai ciza min maciji,wayyo zai ƙara cije min ƙafa" tana furicin ne tana yamutsa fuska haɗi da juye-juye garin yin haka saura ƙiris ta faɗo daga kan katifa amma yayi sauri ya tallabe ta sai ta faɗo kan ƙafafunsa yana ƙoƙarin sake mayar da ita Lubna ta banko ƙofa ya juya da sauri,suna haɗa ido ta tsaya cak tana mai kallon Haule take ƙara lafewa a kafaɗar Maheer.
"Ki yi sauri ki tawo Hajiya ta ce..." Aliya ta shigo tana faɗa amma ba ta ƙarasa ba ita ma ta yi turus tana kallon ikon Allah.Shi kuwa Maheer wani irin abu ne ya ji marar daɗi,duk da ba laifi ya aikata ba amma ya san za su zarge su musamman shi da suke ganin ƙimarsa suke kuma jin tsoronsa.
Cikin takaici ya haɗe rai tare da maida Haule ya shimfiɗe,kafin ya miƙe tsaye ya ce "me?"
Sai suka kalli juna,Aliya ce ta yi saurin cewa "Lubna na zo kira"
"Sai kuma kika tsaya yin gulmar da kika saba yi ko? Ke kuma kallon me kike yi mata haka ko ƙyaftawa ba ki?" ya dakawa Lubna tsawa wacce ta kafe Haule da ido tana jin kamar ta je ta shaƙe mata wuya ta mutu kowa ya huta. Tana jin yadda Maheer ke ɗaga mata murya saboda Haule kawai sai ta soma yin hawaye kafin ta fice,ita ma Aliya sai ta take mata ba sai a lokacin shi ma ya fita ya koma part ɗinsa domin yin wanka ya shirya ya tafi gidansu Dr David wanda ake bikin jana'izarsa.
Da su Lubna suka koma can cikin mota wacce za ta kai su restaurant Hajiya ta ce "lafiya wannan take kuka?"
Aliya ta ce "saurayinta ya rasu"
"Allah jiƙansa dama tana da saurayi ne?"
"Eh abokin Alhaji ne ai,ƙila ma kin san shi Dr David " Aliya ta faɗa. Lubna ta ɗago da sauri don ita ba ta da ma labarin mutuwar Dr David ,wani irin shock ta ji amma ta kasa cewa komai.
Hajiya ta ce "au! Kirista ma ne nake ɓarnar bakina wurin yi masa addu'a"
Haka dai suka isa restaurant ɗin,babu kuma ɓata lokaci suka fara abin da ya kawo su amma sam Lubna ba ta da nutsuwa sai ta rasa da wanne za ta ji. Can ta daure ta tambayi Aliya," da gaske Dr David ya mutu?"
"Eh!" "Amma ya aka yi kika sani?" "Saboda ni ce silar mutuwar tasa" "Kamar ya?" "Kamar yadda kika ji" "Laifin me yayi miki?" "Irin wanda yayi miki lokacin baya" ta bata amsa tare da yin gaba ta bar Lubna cike da mamaki da kuma tsoro.Amma don fitina ta ƙara zuwa kusa da ita ta ce "Aliya me Dr David ɗin yayi miki?"
Cike da takaici Aliyar ta ɗago ta dube ta tsakiyar ido ta ce "irin abin da yayi miki, ai na san har abada ba za ki manta da wannan ranar ba ko?"
Lubna ta haɗiye wasu yawu saboda tsantsar gaskiya da take hangowa a cikin idon Aliya ,amma sam ba ta ji za ta iya bada kai tun yanzu ba a san ɓoyayyen sirrinta.
Aliya kuwa baki ta taɓe kafin ta ci gaba da cewa "ina jiye miki tsoron komawa inda kika fito,duk ki bar ganin ki samu ɗaurin gindi wurin Maheer akwai lokacin da wacce kike jin tsanarta a ranki ita ɗaya ce za ta iya raba ki da lukutar masifar da kike ƙoƙarin komawa" Aliya na gama faɗar haka sai ta fita can inda ake cin abinci tana mai kwashe plate ɗin da aka ɓata sannan ta ƙara gyara table ɗin.
Wanke-wanke ta soma tana yin waƙoƙin habaici,wanda sarai Lubna ta gane da ita ne take.Ficewa ta yi ba tare da ta yi wa Hajiya sallama ba,direct gidansu ta wuce a cikin soro ta tarar da Ummah tana tsefewa auta kitso.Dakyar ta iya gaishe ta kafin ta wuce ciki,bokiti ta cika da ruwa ta shiga toilet ta yo wanka ko za ta ji ɗan dama amma kamar an kunna wa zuciyarta wuta haka take jin tana yi mata ƙuna. Hoton Maheer tallabe da Haule ya kasa fitar mata daga madubin idonta,sosai take jin kishin Haule.Ita ba ta damu ba don ba ta samu Maheer ba,don dama kaso biyar ne cikin ɗari gare ta na nasarar samunsa amma ya kasance da Haule ne sam ba za ta juri haka ba.
Ido ta rumtse tana tuno mummunar ranar da Dr David da kuma Zuly suka ha'ince ta suka yi sanadiyar raba ta da budurcinta.Babban takaicinta kuma yadda Boss yayi mu'amala da ita a gaban kowa na family tare kuma da wasu idanu waɗanda ba ta iya ganin gangar jikin mamallakinsu sai dai tabbas tana jin suna kallonta. Baƙar ranar da ta fi tsana kuma ranar da Jagaba ya bata zaɓi uku,na farko ta yarda yayi luwaɗi da ita,ko kuma ta je su yi mu'amala ita da mahaifinta ko kuma ta bayar da jinin Abbanta matsayin fansa,sai kuma ɗauki zaɓin ƙarshe.Wani kuka ne ya ƙwace mata tana jin zuciyarta na wani irin kumbura tare da yi mata saƙa iri-iri,' Lubna tun da har kika iya bayar da ran Abbanki mene ne kuma ba za ki iya yi ba a duniyar nan? Lubna me yayi miki saura na jin daɗi a duniyar nan alhalin ba za ki ƙara jin daɗin mu'amalar aure ba? Kawai ki yarda ki sadaukar ki tunkuɗe tsoronki ki nemi Zuly ta haɗa ki da Jagaba ki amince da buƙatarsa shi kuma ya baki ƙarfin ikon da za ki hallaka Haule ' wannan sune soki burutsun da zuciyarta ke kimtsa mata,sai kuma ta girgiza kai cike da tsoron irin yadda ta ga Jagaba na mu'amalantar wasu daga cikin members tamkar doki haka ƙarfinsa da zubin halittarsa yake.
Tsoro sosai take ji,ba wai na haramcin baƙar ɗabi'ar ba,a'a yadda take jin labarin cewa masu yin luɗu ba su iya riƙe kashi don wasu ma har zuba yake yi musu.Ta goge hawayenta tare da ƙara fita ta cika bokiti ta je yi wanka,bayan ta gama sai ta shige ɗaki tare da yin kwance ta yi lamo tana tunani.
"Meke damunki Lubna ?" ta ji muryar Ummah kamar daga sama. "Babu komai" shine kawai abin da ta iya cewa.
"Me ya maido ki gida alhalin Hajiya ta ce min sai weekend kawai za ki dinga zuwa kina ganinmu saboda aiki yayi miki yawa?" Ummah ta sake tambayar.
Lubna ta mayar da hawayen da suka taru a idonta sannan ta ce "babu komai Ummah.Ni ma kawai ji nake ban jin daɗin jikina "
Ummah na jin haka ta ce "tashi zaune ki fuskance ni" ba don ta so ba ta tashi ɗin sai dai ta kasa kallon cikin idon Ummah.
"Ni mahaifiyarki ce,ba ki da wadda ta fi ni.In ba ki sanar da ni damuwarki ba wa za ki faɗa wa kenan?"
Lubna ta rungume Ummah tare da fashewa da kuka,can ta soma magana muryarta ba ta fita "Ummah Dr David ya rasu bai karɓi shahada ba,ya mutu yana kafiri shi ne abin ke ci min rai"
Abin ka ga uwa wacce ta san ciki da baya na ƴaƴanta,sai Ummah ta ce "bayan kuma wannan sai me ke damunki?"
Shiru Lubna ta yi kamar ba za ta yi magana ba sai kuma ta ce,"ina son wani ne,amma shi ƙawata wannan wacce muka zo da ita yake so shine ita kuma ta amince masa alhalin ta san babu wanda nake so sai shi"
Ummah ta yi mumushi mai ciwo kafin ta ce "sau tari abin da muka fiya so ba alkhairi ba ne a gare mu,kawai ki ci gaba da yin addu'a Allah zai cire miki sonsa ya kawo miki wanda ya fi shi .Sannan ina mai miki nuni da ki ji tsoron Allah kar ki yi abin da za ki kauce hanya domin biyan wata buƙata"
Aliya ta ja wata ajiyar zuciya tana ɗan jin sauƙin ƙuncin da take ji ya rage,ta ce "in sha Allah Ummana"
★HAULE
Ban san iya adadin lokacin da na ɗauka ba ina baccin da ban san yaushe ya ɗauke ni ba.Kukan Yasmine ne ya kawowa kunnuwana farmaki,a hankali na buɗe idona ina ƙarewa ɗakin kallo sannu a hankali kuma abubuwan da suka faru suka dawo min a kai.Ban san lokacin da na buɗe baki na furta "mugu!" sai kuma na miƙe na fita can falo,tana ganina ta zo ta rungume ni.Tamkar uwa da ƴa haka na soma rarrashinta kafin na kawo ta ɗakinmu na sa ta je ta yi wanka sai na zaɓo mata kayan Aliya ta saka,bayan nan sai na haɗo abinci muka ci tare amma na ga alamun kamar bai ishe ta ba.
"Yasmine me kike ci yake ƙosar da ke?" na tambaye ta.
Idonta ya ciko da hawaye ta ce,"jini! "
Da furta haka sai na dubi cikinta,tuni kuma na fahimci ba ita ce ke shan jinin ba macijin da ke cikinta ne. "Kina da lambar ƙawayenki?" sai ta girgiza kai,ni kuma na tambaye ta ne saboda su ma suna da buƙatar a yi musu magani.
Shiru na yi ina tunanin abin da zan yi mata wanda zai hana ta fita,kalaman Yaya Aliyu ne suka faɗo min ni excellency wato shugabarsu baki ɗaya.In dai haka ne kenan ina iya controling macijin da ke cikin Yasmine,sai dai ban san kuma ta yaya ba.
So nake na fita na je can gidansu domin ina son jin labarin Anty Bahijja ta yadda aka yi har ta auri Boss ,sai dai kuma barin Yasmine ita ɗaya babban haɗari ne don na tabbata masu aikin Hajiya babu wani abu da za su iya yi akai.Wata dubara ta faɗo min sai na fita falo na duba lambar wurin aikinmu na restaurant,sai na dawo na ɗauki waya na kira cikin sa'a kuwa Aliya ce ta ɗauka.Na yi tunanin za ta tambaye ni ina na je amma shiru sai ma cewa ta yi "ya dai Hajiya ko kina buƙatar wani abu ne?"
"Ni ce kuma Hajiyar ?"
"I mana! Big Hajiya ma kuwa,tun da kin zauna gida kina bacci abinki kin turo mai restaurant ɗin da kanta tana aikin da ke ce ya kamata ki yi"
Na ja numfashi na ce "duk ba wannan ba, Please ki dawo gida ki zauna tare da Yasmine ina son zuwa can gidansu akwai binciken da zan yi"
Aliya ta tuntsire da dariya kafin ta ce "yo in ba ki koma gidan Boss ba ai ba Haule kike ba,wato duk ƙara'in nan da aka yi so kike ki koma?"
Na ce "don Allah ki zo kin ji, lokaci na ƙure mana"
"To a gaskiya ba zan iya tafiya ba sai dai ki kira Lubna,don ni aiki nake yi"
"Ba ku tare da ita ne?" "Eh ta fice kuma ban san inda ta tafi ba"tana gama faɗa ta kashe.
Ni kuma sai na rasa yadda zan yi na kama hannun Yasmine muka fito,direban Hajiya na roƙa ya kai mu can gidan Boss ban kuma sha wahala ba mai gadi ya bar mu muka shiga.
Kamar wancan lokacin yau ma tana zaune tsakiyar falo,tana ganinmu ta miƙe hankali tashe ta ce "me yasa kuka dawo?" kafin na bata amsa Yasmine ta yi wani ihu tare da buɗe bakinta wanda ya zama gudan ƙatoto tana shirin haɗiye mahaifiyarta.
Sarƙar wuyana ce na ji ta soma ɗaukar wani caji kamar an jona ta da lantarki,kawai sai na samu kaina da soma yin magana cikin wani Yare ina yi wa dodon da ke jikin Yasmine tsawa amma ya ƙi dakatawa kamar daga sama sai na ga wannan Goril wato gogwan Birin nan ya bayyana a ɗakin ya cira Yasmine sama da hannu guda tare da matse mata wuya,nan ta soma aman wani abu mai yauƙi kafin kuma ta dawo normal sai ya jefar da ita kan sofa kafin ya ɓace ɓat yayin da ita kuma ta shiga baccin wahala.Sai a lokacin kuma na fuskanci anty Bahijja na ce "na zo ne nan domin jin labarinki,kar ki ɓoye min komai kuma domin ta wannan hanyar ce zan samu damar taimakonki"
Ta buɗe baki kenan da niyyar yin magana kenan Yaya Aliyu ya bayyana cikin ɗakin yana mai kafe ni da idonsa da suka soma yi min fassarar zuwan nasa........ My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
25