Kenza eBookz

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 16

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 16

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 16: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 16. Gefen da Yasmine ke kwance na kalla kafin na soma magana mai…

4,361 words

Gefen da Yasmine ke kwance na kalla kafin na soma magana mai kamar gargaɗi,"kar ma ka gwada ɗaukarta,don in ka yi wannan kuskuren zan manta cewa kai Yayana ne.Mun riga da mun gama maganar nan,na faɗa ma Yasmine tawa ce"

Yaya Aliyu ya dubi anty Bahijja wacce tuni ta soma hawaye jikinta na kyarma,da dukkan alamu kuma ta yi masa farin sani ba yanzu ne ta soma ganinsa ba.

"Haule wannan alƙawari ne,tun kafin ki dafe matakin iko aka mallaka mini ita kuma ga mahaifiyarta nan a gabanki za ki iya tambayarta.Haule ban so rikici ya shiga tsakaninmu ,don haka kawai ki kiyaye abin da manyanmu suka tsara"

Raina ne na ji yana ɓace,haka kuma na ji jinina yana tafasa ina kuma daɗa jin wani canji na bayyana a gare ni.Anty Bahijja na duba na ce "soma bani labarinki kar ki damu,yi kamar bai wurin nan sannan ki bar jin tsoron..."

Yaya Aliyu yayi saurin katse ni "Haule ya kike magana haka kamar kin manta wane ni ?"

Cikin ɗaga murya na ce "a nan ni ce babba ba kai ba,don haka ka yi min shuru " A cikin ƙwayar idonsa ina hango tsantsar mamaki amma sai yayi shiru bai ƙara cewa komai ba,anty Bahijja kuwa kusa da ni ta zo ta tsaya tare da kamo hannuna ta jimƙe cikin muryar kuka ta ce "don Allah ki fitar da ni daga wannan gidan shi ne kawai fatana"

"Kar ki damu ba zan tafi na bar ki a nan ba"

Tana jin haka sai ta kai hannu ta goge hawayenta kafin ta soma bani labarinta yayin da shi kuma Yaya Aliyu ya koma inda ya fito.

"Kamar yadda kika ji sunana Bahijja,ban cikin mata masu dogon buri hasali ma na fi ɗaukar so da muhimmanci fiye da kuɗi.Sai dai duk da haka mijin aure yayi min wuyar samu,ko saurayi na yi da zarar maganar aure ta shigo sai ya ɓace ban sake ganinsa cikin irin haka ne na gamu da Sahil wato mahaifin Yasmine.Ranar da muka fara ganin juna a makaranta ne,ya zo ne a matsayin malaminmu na scientific ina da ƙwarewa ta wannan fannin wannan yasa ban yi wuyar sabo da shi ba a kaf ɗalibansa.Kusan zan iya ce miki a tare muke darasin don ni ce mai ƙwazo da juriyar amsa tambayoyinsa.Mr Sahil Albino ne,kamar yadda ya bamu labari ya ce wannan dalilin ne yasa bai iya jurar zafin Afirka ya koma can Faransa da zama yanzu ma don ya zo wani aiki mai muhimmanci ne yasa ya fara koyawa don zama malami yana ɗaya daga cikin abin da yake buri.Ya bamu labarinsa sosai tun yana yaro yadda mahaifiyarsa ta yi fama da shi da kuma ƙalubalen da suka fuskanta shi da ita,zan iya ce miki tun a lokacin son Mr Sahil ya ɗarsu a raina don na kasance mutum mai tsananin tausayi.Bayan ya gama yi mana darasi kamar kullum sai na ɗauki jakarsa don kai masa ajin da zai ƙara shiga,kamar daga sama na ji muryarsa yana cewa "Hijja!" da mamakin yadda ya kira ni na juya muka haɗa ido sai na ga ya sakar min murmushi tare da cewa "kina da masifar kyau" cak na tsaya ina kallonsa,sai ya kai hannu ya karɓe jakarsa tare da yin gaba ni kuma kamar wata doluwa haka na tsaya ina kallosa har ya shige ajin da zai yi karatu.Sai a lokacin na juya na koma ajinmu,sai dai fa sam ban da nutsuwa.Bayan mun tashi daga makaranta ina ta ƙoƙarin ganin na isa gida sai kawai na ji tsayuwar mota kusa da ni.Na san motarsa ce duk da kuwa madubinta ba a ganin na ciki irin baƙaƙen nan ne,gidan gaba ya buɗe min tare da bani umarni "shigo na sauke ki gida" ban iya musawa ba saboda idonsa masu dafi da ya kafe ni da su,haka na shiga na zauna.A lokacin da na shiga motar sam sai na ji tamkar ba normal mota ba ce,ban ida daidaita nutsuwata ba kuma na ji hannunsa ya kamo typing hannuna.Da sauri na kalle shi sai na ga hankalinsa na kan titi yana driving da hannu ɗaya,ni kuma kai na sadda ƙasa ina kallon hannuwanmu da suke cikin na juna.Kamar daga sama na ji ya soma yin magana,"a yau kin ji labarina,sai dai akwai abubuwan da na ɓoye wanda bai kamata mutane su sani ba.Kin ga Albino na ɗauke da wata irin baiwa ta musamman,wacce har da ita ke sa mutane suna tsangwamar mu.Saboda kawai muna iya hango goben mutum" da ya kawo nan sai yayi shiru,hakan yasa na ɗaga kai na dube shi daidai nan shi ma ya juyo facing inda nake sai muka haɗa ido ya sakar min murmushi kafin ya ci gaba da cewa "tun ina ɗan shekara goma nake ganin mutuwa da idona,in mutum zai mutu ina ganewa haka zan dinga faɗa wa mutane kuwa.Ko kuma in mutum yana tare da matsala shi ma ina sani,kamar ke dai ɗin nan kin ga baƙin jinnu ne ke hana ki aure..oh yi haƙuri na faɗi abin da ba a tambaye ni ba"

Ni kuma jin an taɓo damuwata sai na gyara zama na ce "Mr kenan da gaske jinnu gare ni? Ka san akwai wata Goggona ta sha faɗawa Mamana cewa ta tashi tsaye wai jinnu sun aure ni "

Mr Sahil ya ce "eh Goggonki ta yi gaskiya Bahij,amma komai ya zo ƙarshe tun da gani na zo gare ki" ya ƙarashe faɗa yana kallon tsakiyar idona yana yi min murmushi mai kashe jiki wanda tsabar abin da na ji ya halbi ƙahon zuciyata har sai da na ja numfashi.

Sai kuma na ji yayi parking,da na duba sai na ga ƙofar gidanmu ne ya kawo ni.Da mamaki na ce "dama ka san gidanmu?"

Bai bani amsa ba sai hannuna da ya soma ɗan matsewa kafin ya ce "Hijja me yasa kike zama babu ɗakwali? Kuma har tsakar dare shiga banɗaki kike ki daina hakan bai da kyawu"

Abin da ya faɗa gaskiya ne, wannan yasa na ƙara jin na yarda da Mr Sahil ɗan baiwa ne,cike da girmamawa na ce masa "to in sha Allah "

"Ok ki shiga gida ki gaida kuma Mama,in na isa gida zan kira ki"

Nan muka yi sallama na fita na shige gida,sai dai fa na kasa sukuni dakyar ma na iya cin abinci saboda tunanin Mr Sahil .Ina ta jiran kiran nasa kamar yadda ya ce amma shiru sai da aka kusa yin awa ɗaya currr sannan ya kira ni,sai a lokacin kuma tunanin ko a ina ya samu lambata ya zo min amma kuma ban tambaye shi ba saboda gani na yi wanda ya san gidanku ai lamba ba za ta yi masa wuyar samu ba.

"Kin ga sai yanzu na shigo gida, na tsaya Masjid Imam Khumaini ne na yi sallah" shine abin da ya furta,wanda kuma ba ƙaramin tasiri maganar tasa ta yi min ba saboda a lokacin na fahimci mutum ne kuma mai addini mai kiyaye sallah saboda masjid Imam Khumaini masallaci da in suna sallah kai ka ce ƙiyamul laili ce suke saboda yadda suke yin ta bisa ƙa'ida.

"Sannu to! Fatan ka isa lafiya?"

"Alhamdullah! Fatan ke ma kin isar da saƙona wurin Mama?"

Gaskiyar maganar ita ce ban faɗawa Mama ba,amma da yake ina son yin gwaji na gani shin da gaske ɗan baiwar ne ko yaya sai ce masa na yi "eh na sanar da ita" a lokacin wani murmushi kawai yayi sai kuma ya ɗauko mini wata hira "yunwa nake ji fa,kin san abu da tuzuru sai na fita na nemo kuma"

Da mamakin yadda mutum mai kuɗi irinsa bai da ƴar aiki ko kuma masu yi masa hidima na ce "amma me yasa ba ka ɗauki ƴar aiki ba?"

"Subahanallah! Ina namijin zan ɗaukar ƴar aiki? Gaskiya ba zan iya ba kin san fa sheɗan na yawo a cikin jinin mutum ne, musamman yanzu da mata sam ba su da kamun kai sai ki ga ma ta tsaya babu hijabi a cikin gidan fa,ni kuma lafiyayyen namiji ne ko da zan kawar da kai ai kin ga hakan babu kyau"

Ko da ya faɗi haka sai na ji jikina yayi sanyi,saboda ni mace ce marar lafiya .Duk da ban yi aure ba amma ina gani a littafai ana cewa mace mai lafiya da zarar an ɗauko hirar da shafi abubuwan cikin aure to hankalinta na tashi ko kuma ta ji wani abu,saɓanin ni da har BF na kalla amma ban ji komai ba ƙamas haka na ji ni.

"Bahij zan shiga kitchen na ɗora wani ɗan abu in na gama zan kira ki" ya sake faɗa sannan ya kashe,haka na wuni cikin zullumin yanzu ko da ace Mr Sahil ya ce yana sona da aure ba zan iya aurensa ba saboda ba zan iya ɗaukar nauyin buƙatarsa ba.

Da dare ina tsaka da ɗaukar lesson saƙonsa ya shigo,ya shaida min yana ƙofar gida kuma yana son na yi masa izini ya shigo ya gaishe da iyayena.Jikina ya ɗauki wata irin kyarma,dakyar na iya shaidawa Mama a lokacin kuma an yi katari kuwa tuni Abba ya dawo gida .

Hijabi na saka sannan na fita,a tsaye na tarar da shi jikin mota yana sanye cikin dogayen kaya da suka yi masa mugun kyawu ƙila kuma don yadin yana baƙi.Bayan na gaishe shi sai na yi tsaye,ya ce "ya na ga duk kin yi wani iri ko kina tsoron su ƙi amincewa da ni saboda ina zabaya(Albino)?"

Da sauri na ce "a'a ko ɗaya,ai iyayena ba haka suke ba.Kar ka manta Allahn da ya yi ka ni ma shi ne ya yi ni.In ya ga dama sai ya canza halittata ma a yanzu da nake tsaye"

"Yawwa malamata,mu je ki yi min iso"

Haka muka wuce ina gaba yana baya,,cike da girmamawa ya duƙa har ƙasa ya gaishe da iyayena,yayin da ni kuma na je na kawo masa ruwa ya sha sai na basu wuri na koma can uwar ɗaka amma ina jin duk hirar da suke yi.

"Dama na shigo ne don na nemi izininku kamar yadda shari'a ta gindiya, Allah ya gani ina son Bahijja kuma da niyyar aurenta na zo.Ko gobe aka bani dama zan iya turo magabatana domin a yi magana" wannan shi ne bayanin da Mr Sahil yayi wanda ya jefa kwanyata ta tafi duniyar tunani hakan yasa ban ƙara jin abin da suka tattauna a kai ba sai zuwan Mama da na ji ta zo ta ce na je tuni ya fita yana jirana.

Jiki a mace na fita,mota ya buɗe min na shiga na zauna yayin da shi kuma yayi tsaye ya riƙe murfin yana kallona.Ya saki ɗan murmushi ya ce "ai hakan yayi ko? Kar mu shiga ciki a yi dubin wata tsiyar muke shukawa,kin san mutane dama ƙiris suke jira"

Ni ma murmushin na yi ina jin ƙimarsa na daɗa wanzuwa a birnin zuciyata.Haka muka ta yin hira wacce rabinta duk kusan labarin kansa ne yake bani,irin yadda yayi gwagwarmaya da kuma yadda yayi aikin hajji da duk wani nau'in bautar Ubangiji sai da ya faɗa min.Sunayen littafai kuwa wasu ma ban taɓa jin sunansu ba,amma cikin nuna kamar ya isa da ni ya ce na koma makarantar Islama sannan ya ƙara da cewa "kin san shi ilimi kogi ne bai yin yawa,kamar yadda ba ki tsayar da na boko ba to shi ma ki ci gaba don ina so ki zama uwa tagari gun ƴaƴana"

Na ɗan rufe fuskata da tafin hannu ina murmushi mai ɗan sauti,sai ya zagaya ya je ya buɗe ɗaya seat ɗin ya zauna kafin ya miƙo min kyautar da kawo min.Na karɓa a kunyace tare da yin godiya ina jin cewa shi wannan na musamman ne kamar yadda komai nasa yake haka.Sai da muka yi hira sannan na koma ciki shi kuma yayi tafiyarsa ,bayan na shiga gida na tarar su Mama na ta yabon Mr Sahil saboda yadda ya shigo tun ranar farko ya gabatar da kansa ba tare da sun san cewa shine mabuɗin duk wata matsala tamu ba.

Cikin abin da bai fi sati biyu ba wata irin soyayya mai haɗe da shaƙuwa ta shiga tsakaninmu hatta a makaranta sai da mutane suka gane saboda yadda Mr Sahil yake kasa controling tunaninsa da hankalinsa,duk da cewa dama tun farko yana bani kulawa amma ba kamar lokacin ba.Tuni kuma zancen aure ya kankama,ƴan uwansa sun zo har gidanmu suka kawo dukiyar aure kuma ba a ɓata lokaci ba aka sha shagalin biki,bayan an gama duk wata hidima aka miƙa ni gidana wannan da nake ciki yanzu.

Tsabtatacciyar soyayya muka yi da Mr Sahil bai taɓa nuna sha'awar yin wani abu da ni ba,hakan yasa na shiga zumuɗin zuwansa saboda yadda Mamar Yusuf mai sayar da maganin mata ta kwantar min da hankali ta haɗa min magunguna iri-iri na motsa sha'awa da kuma ni'ima.Babu jimawa kuwa Mr Sahil ya shigo shi ɗaya,bai kuma wani ja lokaci ba ya kamo ni tare da rungume ni ƙam a ƙirjinsa yana mai cewa "na gode Allah da ya mallaka min zuƙeƙiyar amaryata Bahij"

Ni ma murmushin na saki ina jin wani irin yanayi wanda ban taɓa ji ba,can ya sake ni ya ce "zan je ɗakina na yi wanka,kin ga ki ci abinci ki yi wanka ki ɗan huta kafin na zo sabodaaaa...." saurar maganar ya ƙarasa min ita cikin kunne sai na ji ta tamkar busar sarewa,tsabar yadda na ji wani abu ya tsirga min tun daga kan yatsan ƙafata har kwanyata yasa na ƙanƙame shi ina jan numfashi.Ban taɓa sanin haka ake jin feeling ba sai a yau a daren farkona kuma duk silar gyaran da na sha ne wurin likitar mata,ban sani ba ko Mr Sahil ya fahimci halin da na shiga kawai sai na ji bakinsa yana kissing ɗina.Ji na yi tamkar na ƙurma ihu tsabar yadda nake jin abubuwa marar misaltawa ,cikin ƙanƙanan lokaci muka fita hayyacinmu abin ka da wacce ba ta saba jin wannan yanayin ba sam na manta da wani abu wai shi tsoron daren farko,burina bai wuce mu yi sunnar aure ba.

Zafin da na ji shi ya fargar da ni duniyar sama da na shiga,sai na soma yi masa kuka amma bai kula ni ba har sai da muka gama komai nan ne na ga ikon Allah yadda Mr Sahil ya sa baki ya lashe duk ƙazantarmu ni da shi hatta jinin budurcin kuwa.

Ina a galabaice wannan yasa ban samu damar yi masa ƙorafi ba,wanka yayi mana amma ba na tsarki ba kawai dai normal wanka.Nan ma ban yi ƙorafi ba don na yi tunanin ƙila don mun gaji ne,sai dai washegari iya ni ce kawai na ƙoƙarta na tashi na hada jikina na yi wankan tsarki,har na gama sallah Mr Sahil na kwance kan bed yana bacci hankali kwance.

Na tashi dakyar na je na soma tashe shi,amma kamar wata gawa haka yake ko motsi bai yi.Sosai hankalina ya tashi don na yi tunanin mutuwa ce yayi,har ina shirin kiran gida na sanar sai kuma ya buɗe idonsa waɗanda suka firgitar da ni.Wallahi Haule ina faɗa miki yadda kika san garwashin wuta haka ƙwayar idonsa take,ta cikinsu kuma nake hango hoton fuskata yadda kika san dai a gaban madubi nake.Bai iya cewa komai ba ya miƙe ya fita,shiru ina ta zaman jiransa amma bai dawo ba har na gaji na kwanta na sake shan bacci sai wuraren ƙarfe goma yunwa ta tashe ni.A lokacin ne kuma na jawo ledar da ya shigo da ita na ci abinci,sai na fito falo wanda yake tsit babu kowa.Haka na dinga zaga ko ina gidan kafin na koma na yi wanka na yi ƴar simple kwalliya,wayata na ɗauko wacce na fara kira ita ce Mamar Yusuf saboda ta cancanci na yi mata godiya irin yadda ta gwangwaje ni da kayanta na Sokoto masu kyawu(ga waɗanda suke son samu nasu ingantattun magunguna masu kyau ku tuntuɓe ta kai tsaye ta akwatin lambarta kamar haka:+234 706 971 1327) .

Bayan mun gama waya sai ta yi min bayanin yadda zan yi amfani da sabulun da ta bani mai taimakawa wurin kashe duk wata ƙwayar bakteriya.Har na miƙe zan ɗauko ƴar trollyn da na zuba tarkacena sai kuma na ji motsi,da sauri na fita ina tunanin ko Mr Sahil ne sai dai babu kowa iya motsin kawai nake ji wanda bai tsaya ba .A hankali na bi inda sautin ke fitowa har na isa kitchen sai na tarar da tukunya biyu kan gas,sai na buɗe su.Ɗaya farar shinkafa ce irin ta larabawa,ɗayar tukunyar kuma miyar kaji ce sai ƙamshi ke tashi. Sosai na yi mamakin ta ya aka yi har aka yi girki ƙasa da mintin ashirin alhalin da na yawuce gidan ban ga alamun wuta ba? Ina cikin wannan tunanin ne kuma na ga wutar gas wacce ke ci a hankali ta kashe kanta,sannan murfin tukunyoyin da na buɗe ma haka ruf suka rufe kansu.Da wani irin gudun bala'i na fito daga kitchen ɗin ina ihu,sai na ci karo da Mr Sahil wanda ya fito daga shi sai towel ɗaure a ƙugu na je bayansa da sauri na ɓuya ina mai basa labarin abin da ya faru da ni a kitchen,na yi tunanin zai nuna damuwa ko kuma ya ce bai yarda ba amma sai ya shayar da ni giyar mamaki ta hanyar ce min.

"Fatalwar matata ce ta zo ta yi girki,oh! Na manta ban faɗa miki ba ashe.Na taɓa yin aure amma matar ta mutu a wata gobara da muka yi .To tun bayan rasuwarta tana zuwa lokaci zuwa lokaci tana yi min girki da kuma gyaran gida shi yasa ban taɓa ɗaukar ƴar aiki ba"

Tamkar an dasa shuka haka na daskare wuri guda,can kuma na ƙyalƙyace da dariya na ce "haba don Allah Dear ai daga jin wannan wasa kake yi min"

Ya dube ni ya ce "kin manta yanzu kika ce min kin ga tukunya kan gas?" Nan fa tsorona ya dawo,sai dai kafin na iya furta wata kalma tuni kuma wani abin tashin hankalin ya ƙara zuwa.Haule yadda kika san dai wata hikaya ko irin gatanar nan da tsofin ƙauye ke bayarwa,haka na ga wani abu mai kamar inuwa riƙe da faranti ya zo ta gabanmu ya wuce tare da jera kwanukan abinci kan dining.

Ita wannan inuwa ina iya hango siffarta duk da kuwa ba gangar jiki ba ce,amma tabbas inuwar mace ce saboda ga dogon gashinta nan yana tashi cikin iska.A lokacin ikon Allah ne kawai ya hana igiyar numfashina tsinkewa,amma tabbas na shiga wani hali mai kama da mutuwar tsaye irin wacce ko da za a cake ka ga da wuƙa ba za ka ji ba.

Sanyin ruwa masu mugun sanyi ne suka maido ni cikin nutsuwata,sai kuma Mr Sahil yayi min wani mai kamar rainin hankali kamar kuma gaske.Dariya ya shiga yi har da hawaye kafin ya ce "ke wasa fa nake yi miki kar ki tsorota,ni ne na yi girkin kuma fa ai kin san na faɗa miki na iya girki"

Da yake ni ma ina fatan ace abin da na gani ɗin ba gaske ba ne kawai sai na sa a raina eh hakan ne shi yayi girkin.Da ya ga na yarda ɗin sai ya ja ni muka zauna muka ci abinci,bayan nan sai kuma ya bijiro min da buƙatarsa ta hanyar aika min saƙonni masu taɓa ruhi,tuni kuma na ɗau caji sai dai a wannan karon ɗakinsa ya ja ni wanda ya sha banban da yadda aka tsara nawa komai na cikinsa ja ne Haule.Kan gadonsa yayi min masauki wanda yake facing madubi,tun da muka hau bed ɗin sai na ji salon yadda yake yi min komai ya canza tamkar dai hannu bibbiyu ne ke shafata,tsoron zafin da zan ji yasa na buɗe idona na kasa rufe su a daidai lokacin da Mr Sahil ya soma nemana ta haramtacciyar hanya a daidai lokacin ne kuma idona yayi mugun gani Haule.Wata irin siffa ce a cikin madubi tana tsaye tana kallonmu,wannan tashin hankalin shi ya mantar da ni bala'in da ya soma faruwa da ni har sai bayan komai ya kammala na ji tamkar an tsaka ni gida biyu.

Na ci kuka sosai a waccan ranar,sai dai kuma na kasa yi wa Mr Sahil ƙorafin yin amfani da yayi ta haramtacciyar hanya.

Cikin ƙirjinsa ya rungume ni tare da yi min furicin da har in koma da Allah ba zan manta da shi ba,"na gode sosai Hijja na matakin ikon da kika sa aka bani,na ji daɗi sosai da na same ki a daidai ba ki taɓa baiwa wani bayanki ba..." yadda yayi murnar alfasha shi ya fi min ciwo,a jiya sam bai yi min godiyar kyautar budurci ba amma ga shi yana godiya akan luɗu da yayi da ni.A ranar nan ne na fahimci mugu bai da kama,sannan gaggawa aikin sheɗan ne yana kuma daga cikin babban kuskuren da na tabka a rayuwata da ban tsananta yin bincike a kansa ba kawai na aure shi na jefa rayuwata a garari..." anty Bahijja na kawowa nan da bani labarinta sai ta dakata tana mai ci gaba da yin kukanta.

Sosai na ji ta bani tausayi sai na soma bata haƙuri,na tayar da Yasmine sannan ta haɗo kayansu muka fito.A wannan karon kuma ban samu matsalar komai ba,sai bayan mun shiga taxi ne nake ta tunanin abin da kuma zan cewa Hajiya a wannan karon in na je. A daidai lokacin da taxi ɗinmu ta tsaya a ƙofar gidan Hajiya a wannan lokacin ne kuma Dr Maheer da Mahmud suka shigo layin gidan .Sai na yi tsaye har suka iso,a motar Dr Muhamud ɗin ce suke.Wani irin kallo na ga Maheer na yi min tare da jefo min maganar ido,"a ina za ki sauke su? Ko an faɗa miki nan ɗin asibitin jinnu ce da za ki dinga kwaso shara da tarkace kina kawo min a gida?"

"Ka yi haƙuri don Allah Alhaji , za ta dinga yin aiki ne ita ma kuma tana buƙatar taimakonmu " na basa amsa ni ma ta ido.

"Taimakonku ke da wa? "

Duk da na ga tambayar kamar cikin salon wulaƙanci amma haka na daure na ce "taimakonka nake nufi"

Sai yayi wani murmushin gefen baki kafin ya kawar da kai,ya ce "Dr Mahmud mu je daga ciki"

Sai a lokacin ne kuma na gaishe shi,sai na taimakawa anty Bahijja ta shigo da kayanta.A ɗakina na yi mata masauki kafin na ce "nan ɗin gidan da nake aiki ne,in Hajiyar ta zo ki ce mata Alhaji ne ya kawo ki za ki dinga yi mata aikin tuwo-tuwo.Na san hakan zai yi miki wuya duba daga gidan da kika fito amma..." da sauri ta katse ni "a'a wallahi zan yi kar ki damu na gode sosai "

Sai na saki murmushi na ce "jira na dawo" sai na fita zuwa kitchen,ruwa na zuba a tukunya ina shirin kunna gas ɗin na ji tsayuwar mutum a bayana,hannunsa ya ɗora kan nawa da ke kan makunni.Tuni ƙamshinsa ya yi wa ruhina dabaibayi,kasa motsi na yi na soma takurewa wuri guda don babu ta hanyar da zan bi na gudu sosai ya manna ƙirjinsa da bayana.

Cikin bazata na ji hannunsa ya zagaye cikina kafin ya ɗora haɓarsa kan kafaɗata ya soma magana a hankali cikin wani salo kamar tsohon kwarto. Duk illahirin jikina ne ya soma yin rawa,ya busa min iska a kunne yana mai sake tambaya ta "kawai don kina son Maheer sai ki ta yin ƙarya da shi ? Me yasa ba za ki ce su dinga cewa ke ce kika kawo su ba uhum? Kina tsoron Hajiya ta kore ku ke da su ne ? Me yaya Aliyu ya miki? Ya shaida miki wani abu ne da ya shafi gidanku?"

"Ka sakar min ciki tun da ni ba ƴar iska ba ce!" na faɗa da sauri ina jin zuciyata na tafasa,sai yayi baya kaɗan hakan ya bani damar juyowa.Yatsunsa biyu yasa ya matse laɓana yana mai cewa "duk ranar da kuka sake furta kalmar iskanci a gare ni sai na nuna muku yadda ake iskanci" yana gama faɗa ya sake su.

Na banka masa harara ina mai cewa "don ina gidanku sai aka ce maka ba zan iya faɗar gaskiya ba,in ba ɗan iska ba wane ne zai taɓa jikin wacce ba matars..." ban kai ƙarshe ba saboda wata irin fizgowa da yayi min da ƙarfi har sai da kaina ya bugu da ƙirjinsa.Da wani irin mamaki na waro ido jin a inda ya sauke min hannunsa,ban kai ga cewa komai ba na ji saukar laɓansa kan nawa.Irin abin nan da anty Bahijja ta gama bani labari ta ce ana ji shi ne ya soma dirar min ba tare da na shirya ba,na yi tunanin mugunta ce zai yi min amma sai na ji yana shan leɓana na ƙasa a hankali yana kuma sauke min numfashinsa kafin kuma ya soma yi min ainahin sumbar wacce ban san dalili ba na ji idona na fitar da ruwan hawaye..... My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

26

Wata irin kasala ce ta saukar mini,duk wata lakkar jikina ta mutu murus.Banda wani ƙarfi ko izzar ture shi,hasali ma jikina rawa ya ci gaba da yi yayin da shi kuma Maheer yake kissing ɗina kamar wanda ya samu alawa haka yake yi wa lips ɗina da kuma harshena. Sai da ya gaji don kansa kafin na ji ya zare bakinsa daga cikin nawa yana mai sakar min numfashinsa a fuska,a hankali kuma na buɗe idona da ke ta tsiyayar da hawaye na zuba su cikin nasa da suka yi ja suke kuma fallasa min muradinsa.Duk da uwar masifar da na gani cikinsu bai sa na sunne kaina ba ko kuma na kawar da dubana ,haka muka ci gaba da kallon juna cikin ido kafin a hankali na ji hannunsa da ke bayana tun ɗazu ya soma ɗan janye shi a hankali har ya cire gaba ɗaya ya maido shi kan fuskata da take shaɓe-shaɓe da hawaye.

Readers Also Read