Kenza eBookz

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 22

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 22

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 22: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 22. "Ki zo ki amsa " ya faɗa tare da ficewa,banda wani zaɓi banda…

4,499 words

"Ki zo ki amsa " ya faɗa tare da ficewa,banda wani zaɓi banda na take masa baya har can cikin ofis ɗinsa.Wani akwati ya buɗe ya fiddo abubuwan da zan buƙata ya miƙo mini kafin ya ce "makullin da zai rufe babin BAƘIN RUHI da duk wasu maƙarabansa ke ce,amma kina yin kamar ba ki sani ba"

Na karɓi kayan ina mai mayar masa da martani "ta ya zan bayar da abu mafi muhimmanci a rayuwata ga mutumin da bai cancanta ba,bai kuma san darajata ba?"

Ya ƙanƙance ido cikin masifarsa da ya saba ya ce "kuma duk tsiyarki dai shi ɗin ne zai karɓi abin mai muhimmanci, sannan ina so ki sani duk wani abu da ke faruwa laifinki ne don da a ce kin aiwatar da abin da zai dakatar da duniyarsa da tabbas komai ya tsaya kamar ɗaukewar ruwa"

Kanzil ban ce masa ba na fito na barsa can,ina jin zuciyata na azalzala.Abin da na fahimta shi Maheer so yake a ce ni ce na neme shi har muka gudanar da sunnar aure,saboda girman kansa ba zai bari shi ya neme ni ba.

Ina komawa can ɗakin na yi amfani da farar hodar na zagaye gadon da yake kwance sannan na kunna kyandir na soma yin furicin jawo esprit ɗin mutum ko da yana cikin bacci ko kuma in ya mutu.Ba a ɗauki wani lokaci mai tsayi ba ya soma yin magana.

"Sunana Davido,Kirista ne ni,ina aiki gidan nepa ne.Shekaru uku da suka wuce na auri matata wacce da farko take mai ladabi,mai addini mai tausayi,mai magana cikin taushin murya.Sana'arta shi ne kitso da gyaran gashi ,tana da gidan saloon ɗinta wanda babu laifi tana samun ciniki duba da yadda ta iya aikinta.Komai yana tafiya daidai a rayuwar gidan aurenmu,kafin kuma ta samu canjin wurin aiki .Wata hamshaƙiyar mace ta bata wani saloon irin babba sosai ɗin nan ta ci gaba da gudanar da aikin gyaran gashi.To tun daga wannan lokaci komai ya canza,matata wacce ba ta iya cin abincin dare in ba tare da ni ba sai ta daina yin girkin ma kwata-kwata.Sannan ba ta shigowa sai dare yayi sosai,ban da ikon kuma tambayarta dalilin ciko dare in na yi magana haka za ta saka ni a gaba tana yi mini tsawa tamkar ɗan da ta haifa.Sannu-sannu abu ya ƙara ƙamari yadda take zuba sutura mai daraja,ƴan kunnan zinare da gwal waɗanda ni dai ban saya mata su ba.Wasa da kuɗi kuwa tamkar wata ƴar siyasa,kuma su ma banda ikon tambayar a ina ta same su in ma na tambaya ba ta faɗa mini.

Wata rana kawai sai na yanke shawarar bin didiginta ba tare da ta sani ba.Tana fita na bi bayanta,sai na ga ta tsaya a wani katafaren gida wanda faɗar kyawunsa ɓata lokaci ne,cikin dare ne amma abin da idona ya gane mini har sai da ya saukar min da zazzaɓin tashin hankali da kuma tsoro.

Mata ne sun fi su ashirin kowacce ta saka baƙaƙen kaya sun yi da'ira a gaban jar wutar kyandirori,yayin da matata ke tsakiya tana wasu abubuwa haɗi da yin magana cikin Yaren da ko rantsuwa na yi ba na wannan duniyar ba ne.Saura ƙiris na fasa ihu amma na ja da baya na koma can gida kafin ita,kasa bacci na yi har sai da na jira ta shigo ta same ni a kwance kan bed.Duk a tunaninta na yi bacci,sai ta fiddo wani baƙin akwati da take ɓoyewa ƙarƙashin gado,ban san me ta yi da shi ba amma sai tana gamawa ta mayar da shi kafin ta maida shi sai ta shiga toilet.Da sauri na sauko daga bed na jawo akwatin na buɗe,a ciki na samu gashin mutane duk jini ya ɓata shi,ga kuma gashin doki an ɗaure da wani jan zare,babbaƙun allurai sai kuma madubi an yi masa zane da tambarin ƙungiya wacce ban san wace ce ba.

A wannan lokacin kasa jura na yi kawai sai na jira ta fito daga wanka na ce mata "duk mene ne wannan?" Murmushi kawai ta yi ta ce mini "Davido duk matsayin nan da na taka ta dalilin Hajiyar nan ne,na san ba za ka fahimce ni ba yanzu amma gaba za ka fahimta kuma za ka gani" tana gama faɗar haka ta je ta haye bed ta yi kwanciyarta.

Ni kuma tun daga wannan daren ban ƙara samun lafiya ba,kullum cikin mugayen mafarkai nake yi shanu na bina,wani sa'in kuma karnuka ne suke biye da ni suna cire mini gashi.Wani sa'in kuma sai ana zaune ƙalau sai na ji ƙwan lantarki ya tarwatse,ko kuma wuta ta kama duk yadda kuma nake son bar mata gidan na kasa saboda ina jin wani abu mai mugun ƙarfi ya riƙe ni yayi mini ɗaurin huhun goro,abin da na fahimta shi ne matata ba iya saboda kuɗi take aikin nan ba akwai wani ɓoyayyen ruhi da take shayar da jini take kuma yi masa bauta.Ki taimaka ki cece ni ki raba ni da ita,ban taɓa sanin cewa ba duka aure ne ke kawo farin ciki ba,haka kuma ba lallai abin da ya saukar wa da ɗan uwanka zaman lafiya da nutsuwar ruhi kai ma a ce za ka samu haka" yana kawowa nan igiyar da ke saita esprit ɗinsa ta yanke,na dubi Aliya na ce "me kika fahimta a duk case ɗin da muke samu dangane da BAƘIN RUHI?"

Aliya ta bani amsa da "duk mafi akasarinsu hassada ce da kuma rashin godiyar Allah ke sa su faɗa komarsa.Dubi dai matar Davido,tana fa da aikinta amma son ta ɗaukaka fiye da yadda take samun halal yasa ta shiga hannun Momyn nurse Fatee"

Da sauri na kalle ta na ce "ta ya aka yi kika san mahaifiyar nurse Fatee ce?"

Ta ce "saboda a yayin da yake bayar da labarin ina kallon ruhinsa ne,na ga gidan da suka je shi da matar tasa a cikin wutar kyandirorin nan kuma Hajiyar Fatee ce,sannan ita ce abin harinmu na gaba duk da dai akwai ƙura don tana da power sosai ko da yake mun karya ɗaya ɓoyayyen sirrin nasu na jikin nurse Fatee "

Na ja ajiyar zuciya kafin na ce,"ki taimaka min mu warware zaren da ya dabaibaye masa ruhi"

Aliya ta ce "bari dai na kira Oga Maheer kamar yadda ya ce ɗin" tana gama faɗa ta fice,babu jimawa kuwa ya shigo yana shan ƙamshi.Na kawar da kai gefe,da ya zo ɗibar jinina ma sai da ya yada mini magana "duk an ɗebe mini jini ƙila so ake ya ƙare don na faɗi na mutu don shi mutum ya gansa lukuti "

"Ai babu wanda ya ce sai mutum ya bayar da gurɓatacen jininsa mai kalar zuciyars..." yadda ya take mini ƙafa ya hana ni ƙarasa abin da na so faɗa,na dube shi da idona da suka ciko da hawaye ya saki murmushin farin ciki kafin ya cire allurar daga jikina ya saka ta a nasa hannun ya soma jawo jininsa.

Murya ƙasa-ƙasa ya ce "sai saɓa dokar aikina ma nake alhalin an haramta a soki mutum biyu da tsinken allura guda"

"HIV gare ni " na faɗa tare da rama takar ƙafar da yayi min,ya ce "wa ya sani abu cikin duhu"

"Ai kai ne duhun" "A'a jikar Nalado ya za ki ce haka kuma?"

Ban kula shi ba na fice Aliya ta biyo ni tana dariya ta ce "wallahi kun fi kyau a haka in kuna shirme,amma wai ni kam HAULE dama kin taɓa koyon tsafi ne?"

"Kin manta na faɗa miki na yi zama MAKARANTAR MATSAFA?"

"Oh! Haka ne na tuna amma ya kuka yi a waccan ranar ke da mai shan jinin ɓera?" Na ce "amsa gayyatarta na yi na amince zan bi ta don kai wa kakanta ziyara a duniyar matattu,wani tsumma ta shimfiɗa wanda aka tsuma shi cikin jini bisansa muka hau kafin ƙyaftawar ido Aliya sai ga mu a cikin tsohuwar maƙabarta.....

🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟

*_GYARA SHINE MACE_*

*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻

*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*

Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje

Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir

Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi

Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare

Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,

Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi

*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰

Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

33

Yanayin duhun wurin da kuma yadda babu motsi ko ɗaya ko ina tsit ne,sai ka rantse da Allah haka su ma matattun suke sai dai fa ba haka abin yake ba Aliya.Da farko haka na soma rarraba ido ina kallon kabruruka da suka tsufa ba a iya ganin ma tudunsu sosai,kafin kuma na koma sauraren sautin ƙusƙus da ake yi a tsakanin matattu.Hira ce suke yi irin wacce kana ji ka san ba mutuwa ce suka yi aka kawo su wurin ba sai dai dama sun tsara tafiyar ne don cimma wata manufa.

"Saura ƙiris na koma duniya" "Ina fatan a ce ko a can mun haɗu duk da cewa dai har yanzu ban samu gangar jikin wanda zan tsoma ruhina ciki ba" "Ni ma haka! Amma na san ba zan rasa ba ko da kuwa irin na jariran da iyayensu suke sakacin yi musu addu'a tun suna ciki ko kuma in sun zo duniya" "Ni kam na fi son na budurwa mai dukiyar Fulani a tsatsaye" "Hahaha! Kamar na waccan kenan?" "Wa? Wai jikar Nomau?" "A'a ƙawarta dai ga ta nan a tsaye ta buɗe kunnuwa fankam-fankam tana saurarenmu "

Daidai nan hirar tsofin biyu ta yanke sai kuma na ji wani yanayi tamkar ana kallona,da na nutsu sosai na baza idona nan na yi arba da wasu kabari guda biyu na wasu tsofin mata.Ba a iya ganin gangar jikinsu sai dai ƙazamin ruhinsu da kuma manya idanunsu na mayu.

Muna haɗa ido sai ɗaya ta ja baki ta ce "hum! Wannan ai ta fi ƙarfina,ga jinin BAƘIN RUHI nan na yawo a jijiyoyin jikinta "

"Oh ! Wai dama wannan ɗin ce magajiyar Nalado wacce za ta gaje shi ?" "I ita ce,nan da wasu shekaru ai ita ce BAƘIN RUHIN da kanta,ko kin san cewa a cikin gangar jikin Nalado BAƘIN RUHI ke rayuwa?"

"I na sani,ai an ce a ranar da ya je domin kiransa daga ɓoyayyar duniya izuwa ta bil'adama cewa yayi ya mallaka masa kansa da kuma dukkan ahalinsa a matsayin hadiya don shi ya mallaki ƙarfin ikon da babu matsafin da ya taɓa mallakarsa "

"Ai kuwa ya samu don yanzu tuni ya cika ya bunƙasa ya saki rassa da dama a bangon duniya"

"Wai ni kam mene ne abin tsayawa ana sauraren hirarmu alhalin ba gaishe mu za a yi ba?"

"Kin san abu ga sarauniya akwai izza sosai,amma kuma ya na ga kamar tana gudun muƙamin?"

Ban ƙara jin amsar da ɗayar ta bayar ba sakamakon dafa kafaɗata da na ji an yi.Ina juyowa sai muka haɗa ido da Kaka Nalado a sanye cikin kayan matattu,"ziyara kika kawo mini?" ban iya basa amsa ba tsabar firgici saboda a sanina dai na baro shi a can gida sannan ta ya aka yi ya iya zuwa har inda nake? Ban gama tunanin ba na ji wani hazo ya rufe mini ido ko da nake dawowa hayyacina sai na ga duk an ɗaure ni da wata kacar tsafi ko ƙwaƙwaran motsi ban iya yi.Gawarwaki ne a zagaye da ni kowanne sanye da farin likafani kafin Kakana Nalado ya matso ya taɓe bakina ya saka min wani abu mai kamar tiyo har sai da na ji shi yana taɓo zuciyata.Wasu ɗalasimai ya soma yi yana son canza min nufin zuciyata daga fari zuwa baƙi,yana tsaka da yi na dinga jin muryar Innarmu na yin nata ɗalasiman kamar a mafarki kuma sai na tsinci kaina a can makarantar nan kwance kan shimfiɗa.

Matashiyar budurwar nan dai mai shan jinin ɓera ta matso kusa da ni tana mai cewa "ashe ke ce duniyar Ruhaniya gaba ɗaya ta ɓangaren duhu"

Cikin ɓacin rai na ce mata "ai ban taɓa tunanin munafuka ce ke ba,shi ne kika ja ni izuwa can saboda a cutar da ni? Me yasa ban gan ki ba ma haka shi ma kankan naki?" a hassale nake furicin ina jin wani tuƙuƙin baƙin ciki na taso mini ,tana shirin yin magana kuma ta faɗi ƙasa tana shure-shure kamar kazar da ƙyanda ta kama sai kuma na ji tsoro na rasa me zan yi mata ta dawo normal.

Ina ƙoƙarin fita sai ga headmaster ya shigo,da niyyar ya kira mu zuwa ɗakin darasi ne ya shigo sai kuma ya tarar da wannan aika-aikar da na yi wacce ni ban ma san ni ce sila ba sai da ya faɗa mini. Idonta ya haska da wata ƴar fitila kafin ya ce "zo da sauri ki zuba yawunki a bakinta kafin ta mace"

"Yawuna kuma headmaster?" na tambaya cikin mamaki. "Kar ki tsaya tambaya ki yi abin da na ce"ya faɗa cikin tsawa hakan kuma da yayi sai ya ɓata mini rai na je na taɓe bakinta na zuba yawuna,ina shirin miƙewa kuma na ga shi ma headmaster ya faɗi idonsa na kakafewa,ganin ita ta miƙe ras yasa shi ma na basa yawun nawa sai ya miƙe yana jan numfashi kafin ya ce "gimbiya HAULE ina buƙatar ganinki a keɓe,ke kuma Laurat ki wuce aji" a nan ne na san sunanta.

Na dube ta kafin na take masa baya har zuwa ofis ɗin nasa,bayan ya zauna ni kuma ina daga tsaye sai ya soma yi min bayani cikin taushin murya ta yadda ba zai hassala ni ko ɓata mini rai ba.

"Haule duk wani ƙarfin iko da kike gani ana so mamallakinsa ne zai dinga controling nasa ba wai ya bari power ta dinga juya shi ba.Kin ga ki guji duk abin da zai ɓata miki rai ko kuma hirar da za ta sa abokin hirar taki ya fusata ki,in kuma hakan ta faru da buƙatar ki basa yawunki don dole muddin ana so a fitar da kambun maitar da kika jefa masa"

"Ni ba mayya ce ba" na faɗa . Ya ce "na sani! Amma kina da power kashe mutum ta hanyar fushinki a kansa in hakan ya ɗauki lokaci ba ki gusar da ƙwayar cutar ba za ta iya yin sanadinsa "

"Na ji zan kiyaye" na faɗa ina tunanin to tun yaushe kuma hakan ta fara faruwa da ni? Tabbas hakan nada nasaba da ziyarar da na kai sannan Kakana Nalado yayi amfani da wannan damar don saka min wannan bala'in.

Cike da jin daɗi headmaster ya ce " yawwa ungo wannan littafin zai taimaka miki wurin gane wace ce ke" na karɓi littafin wanda har zuwa yanzu ban taɓa karanta ko sunansa ba ne ballantana kuma abin da ya ƙumsa.Bayan nan sai na wuce can ɗakin darasi kamar yadda ya ce,Aliya a nan ne na ga ikon Allah wai mutum da ƙafafun kaza,wasu kuma mutanen da gangar jiki normal amma kawunansu na karnuka ne in takaice miki dai magana iya ni ɗaya ce kaf ajin wacce take da cikakkiyar halittar ɗan Adam.A cikin darasin da aka gabatar mana ne na samu dalilinsu na sauya kawuna,na farko akwai ɓada kama wanda ko da a ce ka haɗu da wani mai ido ukun ne ba zai gane ka ba,na biyu kuma yana daga cikin ɗaukakar ƙarfin iko.

Darasi aka fara yi mana ana zuzuta ƙarfin ikon kowa sai abin ya bani dariya kuwa ƙyarƙyata bayan an tashi ina ƙoƙarin komawa makwancina kawai sai ji na an zagaye ni amma babu kowa a gabana iya ruhika ne" ina kawowa nan na yi shiru,saboda tsayuwar motar Oga Maheer.Na ɗan haɗe fuska na ƙi buɗewa na shiga ,Aliya ma sai ta yi tsaye tana kallona ƙila jira take har ni na fara shiga.Shi kuwa a zuciye ya fito ya zo ya tsaya a gabana,wani irin kallo ne yake yi mini mai ma'anoni dayawa na ɗan kawar da kai ina jin zuciyata na dokawa da ƙarfi,idon Maheer su ne raunina in ina kallonsu wani irin shauƙin sonsa nake ji yana fizga ta.Sam ban lura da lokacin da Aliya ta shiga ba sai ƙarar rufewar motar kawai na ji .Na lumshe ido da sauri jin hannunsa ya kamo nawa,"ke?" ya kira ni cikin wani yanayi,na buɗe idona tare da ɗago kai na dube shi."Me kike so da ni uhum? "

Ban ce komai ba sai baki da na turo gaba,"mu je" ya faɗa ,na maƙe kafaɗa na ce "ni akwai inda zan je" "Gidan Oga Mansur ko? Ke me yasa ba ki jin magana ba ki kuma auna yadda abubuwa za su tafiyar miki? Kina tunanin ita matar Oga Mansur kamar sauran mutanen da kike zuwar musu ne kai tsaye? Tana da ƙarfin iko sosai,don ita nata kalar tsafin tsantsar shirka ce ga Allah in kika ce ki tunkare ta kina iya faɗawa cikin tarkonta ko an faɗa miki ita sokuwa ce ba ta san za a iya kawo mata farmaki ba musamman da gasar nan ta gwamna ta tunkaro za ta yi tsafe-tsafe da bugun ƙasa da komai"

Jin ya gane inda zan je sai na saduda na ce "to amma ya za a yi mu tunkare ta kuma mu yi nasara ba tare da wata matsala ta auku ba?"

Murya ya rage can ƙasa ya ce "kin fa ji abin da Papy ya faɗa Queen dole ki yarda da King ki basa kanki " a yadda yake maganar kawai za ka iya jin yadda yake cike da tsantsar buƙatar hakan amma yadda ya jingini ko kuma na ce ya nuna shi bai so sai kawai na mazge na ce masa "a'a mu sake wata dubarar dai" kanzil bai ce ba ya buɗe mini murfin mota tare da wani cilla ni ciki irin ya ji haushina kafin ya zagaya ya shigo,a tsiyace ya ja muka bar asibitin.

Muna isa gida muka yi wanka tare da shirin zuwa restaurant,Hajiya ba ta gane komai ba.Da muka je can haka muka zauna muna ta hirar gasa da kuma yadda za a kawo ƙarshen BAƘIN RUHI.

Aliya uwar surutu ta ce "Haule kawai ki yarda ku angonce ke da Oga Maheer wannan ita ce babbar mafita akan dukkan matsalolin da suka addabi duniyar nan dangane da gubarsa da ya saki"

Na ɗan dube ta kafin na ce "Aliya ko dai ke kike zuwa wurin Oga Maheer ɗin?"

"Wa ni in ji ɗan daudu? Wannan lamari sai ke kaɗai ce za ki iya"

"Saboda ita kaɗai ce mace ko?" cewar Lubna.

Aliya ta bata amsa da "eh to kusan haka ne,saboda ko matan duniya sun haɗu sun yi sintiri ba za su yi wani tasiri a gun Oga Maheer ba sai ita iya Haulen kawai ce za ta iya ji da shi"

Lubna ta taɓe baki kafin ta ce "a faɗawa kaji zabi hira suke "

"Ke ma ai kazar ce" Aliya ba ta rufe bakinta ba Lubna ta kai hannu ta buge shi,nan suka hau dambe ina ta ƙoƙarin raba su amma sun ƙi.

"Waranceee!" muryar wata matashiya ta furta duk sai suka tsaya suka yi cirko-cirko amma da alamu kamar ita Aliya ta san ta .

"Kun tsaya yin faɗa kun bar costumers a can waje suna jira" ta faɗa tana mai kallonsu,a tare duk suka fita yayin da ita kuma ta matso kusa da ni tana mai ciro wata ƴar ganɗama ta miƙo mini.Kamar wacce ta asirce haka na karɓa tare da buɗewa na shanye abin da ke ciki tas kafin na jawo kujera na zauna ina kallonta,ta juya mini baya kafin ta soma yin magana "Papy ya baki layar da za ta baki damar yin abubuwa da dama ciki kuwa har da jin ƙarashin labarinsa da abokinsa Maitama amma tamkar ba ki san aikinki ba kin wani tsaya shirme.Ruwan da kika gama sha saƙo ne daga Innarki,magani ne da ya ƙumshi sirrika dayawa,tun daga gyaran jikin amarya zuwa tsimin amare sai dai wannan ya sha banban saboda tun ranar da kika zo duniya aka soma aiki a kansa.Na san ba ki san ni ba,to bari na gabatar miki da kaina sunana Ayush Yayar Innarki ce ni wacce Nalado ya bayar da jinina matsayin hadiya ga dodonsa.Ya nemi ya aure ni amma shi mahaifina Maitama ya ƙi yarda shi ne shi kuma ya kashe ni tun ina ƴar budurwata,amma ko dayake daga yau zuwa kwana uku za ki san komai" tana gama faɗa sai ta juyo muna facing juna .

Murya na ɗan rawa na ce "mene ne kika bani na sha?"

Ta yi wani murmushi kafin ta ce "maganin da zai yi miki jagora ne har zuwa turakar mijinki"

Idona suka ciko da ƙwalla kafin na ce "me yasa za ki bani abin da zai zubar min da ƙimata ? Saboda me ba ki shawarce ni ba?"

Ta tako ta iso inda nake ta dafa kafaɗata ta ce "saboda lokaci yayi da za ki cika burin FARIN RUHI"

Hawayen sai a lokacin suka samu damar zubo mini,na girgiza kai na ce "ni ban so kuma ni ban shirya ganin Maheer matsayin mijina ba wallahi ba zan je turakarsa ba"

"Aikin gama ya riga da ya gama,kin ga maganin da na baki iya kwana uku kawai za ki iya jurarsa in kuma kika zarta to tabbas ina mai shaida miki cikin biyu sai ɗaya ya faru ko dai ki rasa rayuwarki ko kuma dai BAƘIN RUHI yayi galaba a kanki ya mallaki gangar jikinki don kuwa saura ƙiris ya sabunta gangar jiki daga ta Nalado zuwa taki tun da ke ce magajiyarsa "

Ban iya ce mata komai ba sakamakon irin abin da nake ji yana game mini jiki tun yanzu,na miƙe dakyar na ɗauki kuɗin da zan shiga adaidaita na fice.

A cikin napep ma ji nake kamar na ƙurma ihu,muna isa na yi saurin shiga gida amma tamkar wani mayen ƙarfe haka benen Oga Maheer ke zuƙo ruhina,idona har wani rufewa suke lokacin da na nufi can na soma taka matakalar.

Ina tsayuwa a gaban ɗakin sai ƙofar ta buɗe kanta,wani zafi ne nake jin yana dukar mini fata.Kamar wata mahaukaciya haka na shiga toilet,sam ban yi lura da shi ba.Kayan jikina na tuɓe duka kafin na tsoma ƙafata cikin bahon wanka da na gani a cike da ruwa.

Ji na yi kamar na taka mutum,na ɗago idona masu kamar na mai jin bacci kowacce ta yi maye.Ido huɗu muka da shi ya kafe ni ko ƙyaftawa bai yi hakan sai tsunduma ni cikin wani mugun hali har ban san lokacin da na ida shiga ba.

Maheer yayi mini masauki kan ƙirjinsa,yadda jikinmu ya mannu da na juna yasa muka sauke numfashi a tare kafin Maheer ya soma yi mini sumba gefen wuya yana sauke mini numfashi mai ɗumi.Ƙanƙame shi na yi ina jin tamkar na fasa ihu,jikinsa na rawa ya ɗago fuskata yana mai kamo leɓena na ƙasa haɗi da soma yawo da hannunsa a sassan jikina.

Tuni casbin hankali da nutsuwarmu sun tsinke,dakyar ya iya fiddo mu daga toilet ɗin ya zube mu kan gado .Muryarsa can ƙasa a shaƙe ya ce "don Allah ki ci gaba da romance ɗina"

Ban iya ce masa komai ba,saboda abu biyu da suka saukar mini tsoronsa da kuma buƙatar zama abu ɗaya da shi.Oga Maheer namijin duniya ne cike da salon jan hankalin mace ya fara tafiyar da ni yana mai karanto addu'a,na rumtse ido da ƙarfi saboda azabar da na soma ji tana ratsa ni yayin da kuma kwanyata ke hasko mini ƙauyen Papy lokacin da ya shiga uƙubar Nalado.

Maitama na gani shi ma riƙe da wani littafi yana kirari wa fararen ruhika,har izuwa lokacin da suka wanzu a doron duniya suka shiga jikinsa.Nan take kuma garin ya dawo normal,yayin da kuma abotarsu da Nalado ta ci gaba da wakana ba tare da kowa ya bai wa ɗan uwansa labarin kiran dodon da yayi.A cikin sharuɗan da baƙin ruhi ya zartarwa da Nalado shine babu haihuwar mata a ahalinsa,duk macen da aka haifa shi ke shanye jininta,yayi da kuma ƴaƴansa maza suka taso cikin mugun sonsa da yin biyayya a gare shi.Tun yarinta suka fahimci wane ne mahaifinsu har izuwa ranar da Nalado aka wayi gari ya mutu,shi ne ya sanar da ƴanƴansa ko da an kai shi maƙabarta an rufe in dare yayi su je su tono shi su maido su ajiye a wannan ɗakin don ci gaba da rayuwa a cikinsu.Suna sonsa shi yasa bayan an gama komai suka je suka haƙo shi suka dawo da shi a cikin keɓaɓen ɗaki,tun a ranar ya tashi zaune kamar ba shi ya mutu ba.

Readers Also Read