Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 24
Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 24: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 24. Toilet na shiga na sakarwa kaina shower,ruwan pampo da na…
4,482 words
Toilet na shiga na sakarwa kaina shower,ruwan pampo da na idona suna ta zuba lokaci guda.Ina nan tsaye na ji an shigo ana guɗa wanda hakan ke nufi an ɗaura auren dai ,sautin kukana ne ya ƙaru ina ta tunanin yadda Maheer ya shayar da ni zumar soyayya. Sama da minti talatin ina ciki ban fito ba har sai da na ji Aliya na bubuga ƙofa,kasa kallonta na yi na je na canza kaya kafin na hau dadduma na fara sallah.
"An ɗaura! An ɗaura! Yau dai Oga Maheer Allah ya yi nufi zai angonce waiii irin wannan shekaru da ya ɗauka bai yi aure ba yau akwaita " Lubna ce ta shigo tana faɗar haka,duk da ina cikin yin sallah sai da na ji hantar cikina ta kaɗa a haka dai na daure na ci gaba da yi.
"Haba Lubna ya kike murna abun ko kara babu?" anty Bahijja ta faɗa .
"Kara ta me? Ai na haƙura da shi kin san an ce in son gaske kake yi wa mutum to dole ka so duk abin da ke saka shi farin ciki"
"To an gode kina iya tafiya" Aliya ta faɗa .
"In tafi in je ina? Hahaha! Ina ce dai kafin duk ku zo nan gidan ni ce farkon zuwa kuma k..." sauran maganarta ce ta maƙale mata a maƙoshi saboda kamun sandar makauniya da na yi wa maƙogoronta ba tare da kuma na motsa daga inda nake zaune ba.
Lubna ta fara kakari tare da ƙoƙarin yin magana amma ta kasa,sai ta saka idonta cikin nawa.Cike da izza na ce "ko akwai abin da za ki iya yi yanzu? Ki ci gaba da zagina,sai dai ki sani wutsiyar raƙumi ta yi nisa da ƙasa.Ke ko a matsayin ƴar aiki ba za ki samu wannan darajar ta shiga gidan Maaaheer! " ina gama faɗar haka sai na jawo kalolin da aka zubo abinci na buɗe na zuba na ci na ƙoshi na hauda ruwan sanyi.
Bayan na gama na ce "anty Bahijja ina zan samu maganin mata mai kyau mai aiki kamar yankan wuƙa?"
Ta saki ɗan murmushi kafin ta ce "in dai maganin mata ne ki kwantar da hankalinki don Mamar Yusuf likitar mata babu abin da ba ta tanada ba domin ma'aurata su more rayuwar aurensu"
Cike da farin ciki na ce "yawwa a yi mini odersu ,Aliya ina buƙatar kayan bacci masu kyau please "
Aliya ta yi wani makirin murmushi kafin ta ce "tun tuni ai na saya miki su fa,amma ina tsoron in kika saka su a sake yi miki wani ɗinkin hahaha" suka shiga yin dariya yayin da ni kuma na rufe ido saboda kunya.
Aliya ta miƙe tana mai cewa "bari na je falo na yo gulma,kin san tun da na ga autar Daddynsu Maheer na mugun kama da ke sai Allah ya ɗora mini ƙaunarta.Ashe wannan ƙauna taki da Oga Maheer ta cikin jini ce,da a ce tun farko kin faɗa mini cewa Daddyn Maheer shine yayan Innarki kina tunanin zan bari a yi wannan gantalalen auren da ba zai amfani kowa ba sai zallar asarar kuɗi"
Na saki ɗan murmushi ina shirin yin magana aka turo ƙofa,da sauri na turo baki gaba don cikin idona nasa suka sauka. Anty Bahijja ta ce "barka da shigowa Allah sa alkhairi " Aliya ta yi karaf ta ce "ki zo mu tafi ya fi wannan maganar muhimmanci " kana jin sautin muryarta ka san ranta a ɓace yake,ina ganin lokacin da Maheer yayi wani murmushi ƙila ya fahimci cewa Aliya na taya ni kishi ne.
Suna fita Lubna ƴar kurma ta yi yunƙurin take musu baya amma na harɗe ƙafafunta ta kasa motsi. Sai kuma na yunƙura na tashi,Ba ki gaishe ni?" Maheer ya faɗa yana wani ɗan tura ni baya na faɗa kan katifa.Kamar wani ƙaramin yaro haka ya zauna kan ƙafafuna,a shagwaɓe na ce "ni kar ka karya ni "
"Ni mene ne a ba ki yi mini ba uhum? Duk wannan uƙubar da kike yi mini ta fushi ba ta ishe ki ba har da hana ni duba lafiyarki" da sauri na lumshe idona jin bakinsa kan nawa,yayin da hannunsa ke yawo cikin hijabina ko kaɗan kuma ban yin yunƙurin hana shi ba don ina son na nunawa Lubna cewa iya su ɗaya ne Oga Maheer zai yi wa izza da ɗagawa amma ni tuni mun zama ɗaya.
Tsawon lokaci muna a haka kafin na kauce fuskata,"ki taso mu tafi please " ya faɗa kamar zai yi kuka. Ina jan numfashi na ce "a'a na ƙiya don ka sake yi mini mugunta ko? " sai a lokacin kuma na saki ƙafafun Lubna ba tare da na kalle ta ba amma ita ma ƙila don ta nuna mini ta kai ƴar iska sai ta ƙi gusawa ballantana ta tafi.
"Ba zan yi miki mugunta ba babyna ki yarda da ni" Maheer ya faɗa .Hijabin jikina na cire nan kuma hankalin Maheer ya ida tashi don rigata irin mai ɗame jiki ce ga shi ko bra ban saka ba ko kafin na yi wani yunƙuri ya soma kiciniyar ɗaga ta sama.Fararen cinyoyina na bayyana Lubna ta nufi ƙofa a guje,na saki murmushin mugunta don na ɗauki alƙawari muddin za ta tsaya to ba zan ji nauyin barin Maheer ya sarrafa jikina duk yadda yake so a gabanta ba duk da kuwa tsoro ne fal zuciyata.
Tana fita na ƙanƙame jikina wuri guda tare da soma yi masa kuka dole ya rabu da ni ya koma gefe yana kallona.A cikin idonsa wata muguwar ƙaunata nake hangowa mai cike da buƙatata,a yadda na lura muddin yau ban yarda na basa haɗin kai ba ƙila feeling nasa ne zai yi masa jagora zuwa ɗakin Ikilima wacce don munafurci suka ce za ta tare a yau alhalin can da farko iya auren kawai aka ce a ɗaura.
"Ke ba ki tausayina?" na ji muryarsa,in yana magana irin haka har mamakinsa nake ji kamar ba shi ne mai shegen girman kan nan ba.
"Ka tafi can sashenka zan same ka,nan kar wani ya shigo ya ganka" na faɗa ina jin zuciyata na bugawa. "To amma don Allah kar ki jima" ya faɗa tare da ficewa,na bi bayansa da kallo kawai.Bayan ya fita anty Bahijja ta shigo ta miƙo mini kofi na karɓa na shanye abin da ke ciki kafin ta ɓare wani sabulu ta miƙo min ta ce "ki je ki yi tsarki da shi"
Cike da ɗan tsoro na ce "na mene ne shi?" kafin ta bani amsa Aliya ta shigo tana mai cewa "ke dai ki yi abin da aka ce,muna son kankaro miki daraja kin tsaya tambaya.Ki tashi ki yi wanka ki soma shirya wa,ƙarfe biyar na bugawa ki wuce ɗakin mijinki"
Ina jin haka na ce "Aliya mene ne kike shirya wa haka?"
Ta tuntsire da dariya kafin ta ce "oh ni jikar jinsi biyu wai HAULE sai yaushe za ki yarda da ni ɗari bisa ɗari?"
Ban ce mata komai ba na shiga karanta saƙon Maheer da ya shigo yanzu,na saki murmushi jin wani zance wai saura ƙiris ya mutu .Ba tare da na maida masa ba na soma gyaran jikina,su anty Bahijja na taya ni wurin shafa mini dilka.
MAHEER
In akwai abin da ya fi tsana a duniya to bayan Ikilima yake, kwata-kwata bai sonta saboda mugun rawar kanta sam ba ta da jin aji sannan kwaɗayinta a kansa a bayyane yake kusan kullum sai ta yi yunƙurin taɓa shi ko kuma ta roƙa yayi mata kiss. Ya aure ta ne a bisa bin umarnin Hajiya ,don duniyar nan ita ce ya fi so fiye da kowa sannan yana kiyaye abin da zai ɓata mata rai.Tun da aka ɗaura auren nan yake cikin ƙunci,bai ji sassauci ba sai da ya shiga part ɗin su Haule sannan ya ji sassauci haɗi kuma da jefa kansa cikin wani hali.A matuƙar buƙace yake amma ya lura kamar ma Haulen tsoronsa take ji,kuma bai ga laifinta ba saboda karonsu na farko ya wahalar da ita sosai.
Tun da ya aika mata saƙo yake dakon jiran amsa amma shiru ba ta maido ba har aka kira sallar la'asar.Kasa tashi yayi sai da yayi da gaske kafin ya je yayi wanka ya fita,bayan ya dawo daga masjid ya nufi ɗakin Hajiya ya kuwa ci sa'a ita ɗaya ce a ɗakin ta gama sallah.
Kamar wani yaro ya zube kan capet yana mai dafe kansa,"lafiya meke damunka kuma?"
"Babu komai kawai ciwon kai ne saboda cacaniyar mutane, Please ki sa waccan yarinyar ta haɗa mini Lipton ɗina irin wanda take yi ɗin nan.Kina da paracetamol?"
Hajiya da hankalinta ya ɗan tashi ta ce "tun ɗazu kana jin abu ba za ka faɗa mini ba MAHEER? Jira na je na haɗa maka Lipton ɗin da kaina"
Da sauri ya katse da cewa "no Mama don Allah kar ki wahalar da kanki ki saka ta kawai ta yi tun da dama shi ne aikinta,bari na haura sama na nemo maganin da zan sha" tun kafin ya fita kuwa Hajiya ta soma ƙwala kiran sunan HAULE .
Kamar daga sama nake jin amon muryar Hajiya a daidai lokacin da anty Bahijja ke ɗaura mini kallabi a kai ne kuma Hajiya ta turo ƙofa ta yi turus baki buɗe ta ce "yau na ga ikon Allah! Dama duk uban ihun da nake yi kina ji na? Haule ni kam me kika zama? Kwana biyu kin ƙume cikin ɗaki kin ce ba ki lafiya duk kin bar mu da aiki ,haka yau kowa ya fito yayi hidimar biki banda ke.Wannan uwar kwalliyar fa? Ina za ki je?"
Kasa furta komai na yi ina kallon Hajiya ,ta taɓe baki kafin ta ci gaba da cewa "ko ma dai ina za ki je ki fara haɗawa Alhaji Lipton kuma ki ajiye hankali ki yi don in kika kuskure wallahi ba zan bari ki fita ba" tana gama faɗa ta fice,na ja ajiyar zuciya kafin mu ci gaba da kwalliyarmu.
Sai bayan an gama ne na fita,mutanen da ke falo na gaishe da su kafin na wuce kitchen ina jin suna cewa "ita waccan kyakkyawar fa?"
"Ƴar aiki ce kin ga ta yi kyau kamar ita ce amaryar"
Jin wannan yasa na fahimci da matsala in sun ga na nufi sashen MAHEER wannan yasa na koma ɗaki na shaidawa Aliya za su kawo mini cikas.Ban san me ta yi ba amma ko da na sake fitowa ba su nan,a gaggauce na haɗa Lipton ɗin na nufi sashensa.
A kwance na tarar da shi a falo kan doguwar kujera,a hankali ya ɗago muka haɗa ido.Sai na yi saurin sunne kaina saboda ba zan jurar kallonsa a haka ba,tsabar kuma tsoro hannuna ya soma yin rawa.Shi ne ya taso ya karɓi tray ɗin yana mai damƙe hannuna,murya na ɗan rawa na ce masa "jira na zuba ma"
"Ni ke nake so Queen "
"Maaa..heer ka ga banda lafiya" na faɗa cikin i'ina,ya ce "zan duba ki ne" yana faɗar haka ya soma ɓalle maɓalan doguwar rigata wacce ta ɓoye fitsararun kayan baccin da Aliya ta sayo mini.
Saura ƙiris numfashinsa ya tsaya lokacin da yayi ƙasa da rigar,da sauri na shige ƙirjinsa ina ɓoye jikina.Maheer ya ɗauke ni ya kai ni can bedroom ɗinsa,jikinsa har rawa yake wurin duba ni.Har addu'a na soma yi kar ya je ya ji mini ciwo wurin fidda mini zaren,cikin ikon Allah dai komai ya tafi daidai sai kuma ya canza salon aikin.
Yadda na sha azaba sai da na yi anty Bahijja Allah ita da ta haɗo mini kayan da suka haukata mini MAHEER ɗina,ita ma Aliya wacce na ja mata ta fi cikon casbi.Dukkan illahirin jikina rawa yake ga wani irin zazzaɓi da ya saukar mini fiye ma da na daren farko.Hankalin MAHEER a matuƙar tashe ya tsabtace mana jikinmu,yanzu ma kayansa ya saka mini kafin ya ɗora mini doguwar rigata daga sama.Yana shirin ɗaukata na girgiza masa kai ina kuka,saboda yadda gidan nan yake da mutane ba lallai mu fita ba a ce babu wanda ya gan mu.Sam bai saurare ni ba haka ya ɗauke ni ya saɓa a kafaɗa,muna saukowa ƙasa kuwa muka yi kiciɓis da Hajiya ...... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
36
"Innalillahi me nake gani haka? MAHEER wace ce wannan?" Hajiya ta furta ,da sauri na rumtse ido ina jin lokacin da yake ba ta amsa da "Queen Haulat ce babu lafiya,ki matsa na wuce asibiti zan kai ta"
Hajiya ta waro ido tana mai cewa "yaushe HAULE ta zama sarauniya ban sani ba?"
"Mama don Allah ki matsa kar na makara "
"Kutumar ubanka sauke ta ƙasa,ba ka ji abin da mahaifiyarka ta ce ba ne?" ɗaya daga cikin dangin Daddynsa ta faɗa ,amma MAHEER duk ya ƙetare su ya wuce ,bai dire ni ko ina ba sai cikin mota.Yana zagayowa ya shiga a mugun haukace ya ja ta ya soma gudu,idona sun fara lumshewa tsabar galabaita amma hakan bai hana ni satar kallonsa ba ganin irin yadda ya tayar da hankalinsa.
Muna isa ya kira wasu nurse suka fara bani taimakon gaggawa,babu jimawa kuma sai ka muryoyin Hajiya da maƙarabanta.
Yadda aka banko ƙofar ɗakin da nake ciki ya kusa tsinka igiyar da ke saita numfashina amma na daure na ci gaba da kallon ikon Allah yadda uwar Ikilima ta fara zagina tana ce mini karuwa,tana dab da kai hannu jikina MAHEER ya ture ta faɗi can gefe aka yi rashin sa'a kuma kan ƙashin hannunta ne ji ƙasss,ta fasa uban ihu tana ta mutu ta lalace.
Sauran waɗanda suka zo tare da ita ne suka nufe ta yayin da kuma wata kuma ta yi ƙoƙarin dukana ita ma, MAHEER ya tari numfashinta yana mai cewa "na rantse da Allah duk wanda ya taɓa ko da gashin matata ne zan shayar da shi mamaki,ku fita daga nan kafin na sa a yi muku matsuguni a gidan yari.
Hajiya ta daki ƙirji ta ce "matarka?"
"Eh matata ce " ya bata amsa yana mai zaunawa bakin gado tare da wani jawo ni ya rungume gam kamar zai mayar da ni ciki.Na ja ajiyar zuciya ina mai yin hawayen farin ciki,Hajiya ce dai ta saka kowa a gaba suka fice suka bar asibitin.Maheer kuwa bayan kowa ya fita ya ɗan janye ni daga cikin ƙirjinsa kafin ya kafe ni da ido yana kallo,murya na ɗan rawa ya furta "I love You HAULEna"
Tamkar busar sarewa haka na ji amon muryar nasa,sam ban yi tunani ko tsammanin jin wannan kalma daga bakinsa ba.Kasa cewa komai na yi na rungume shi kawai ina goga fuskata ga sajensa,cikin kunnena yayi mini raɗa wacce ta sa na saki ɗan guntun murmushi mai sauti.
A hankali ya mayar da ni ya kwantar ,bayan yayi mini allurar bacci kuma ya fice.Idona ne suka far yin wani lummm,ban san lokacin da bacci ya ɗauke ni ba.
MAHEER
Bai bar asibitin ba sai da ya tabbatar ya saka tsaro a ɗakin da HAULE take sannan ya wuce gida inda Hajiya da kuma sauran ƴan uwa ke jiran zuwansa. Ransa a matuƙar dagule yake,bai taɓa jin takaicin auren Ikilima ba irin na yanzu da uwarta ta nuna hauka da dukkan alamu kuma ta waya ne aka shaida mata abin da ya faru shi ne ita kuma ta je asibiti ta yi masa hauka.
Yana shigowa falon ya dire idonsa cikin na Hajiya wacce ta zama wata iri duk ta fita hayyacinta,ba komai ke cin ranta ba kuwa illa yadda MAHEER ɗin ya auri ƴar aiki ba tare da saninta ba,sannan kuma duk wasu tsoffin abubuwa da suka wuce sai yanzu suka dawo kwanyarta daram. Cike da ladabi ya je ya tsuguna a gabanta ya kamo dukkan tafukan hannuwanta ,"Mama?" ya furta can ƙasan maƙoshi.Hawaye suka zubo kan kumataun Hajiya kafin cikin sarƙewar numfashi ta fara magana "Maheer ka rasa wacce za ka aura sai ƙasƙantaciyar,marar galihu wacce ba a san daga inda ta fito ba ballantana an sa su wane ne iyayenta? Ni za ka tozarta Maheer? A cikin gidan nawa ake ninke ni ana mayar da ni shashasha,kuna can kuna ta aurenku na sirri ba tare da ni na san wainar da kuke toya wa ba"
"Ya kike yi masa magana cikin sanyi Hajiya ? Wannan ai sangarta shi kike,ki fito ki yi masa gwari-gwari ba mu yarda da auren tsintaciyar mage ba don haka yanzu ba sai gobe ba ya warware wannan auren cikin sirri kamar yadda yayi sa in kuma ba haka ba ..." MAHEER bai bari ta ƙarasa ba ya katse ta yana mai cewa "ita ɗin jininki ce! Kuma aurena da ita mutuwa ce za ta raba,in kuma kun yi gardama ku gwada yi mata wani abu sai ku fahimci ita ɗin tsatson Maitama ce"
Tsit falon yayi suka fara ƴar kallon-kallon,kafin ɗaya daga cikinsu ta ce "haba ni fa na ce biri yayi kama da mutum,wallahi yadda na ga ƴar aikin nan sai na ga kamar tana kama da auta" faɗar haka yasa duk sai aka juya kallon ƴar autar tasu,idon Hajiya tsabar yadda ta fiddo su kamar za su faɗo ƙasa.Ta haɗiye wasu yawu kafin ta ce " MAHEER wankin ido ka yi min ko kuwa dai gaske fuskar Haule nake gani a jikin ta auta?"
Ya ɗan saki murmushi kafin ya ce "Mama gaskiya nake faɗa miki,Haulat jininmu ce ba bare ba.Na jima da sanin haka amma na ɓoye ko ita ba a wani daɗe ba da na sanar mata"
Nan fa hira ta kancame,ɗaiɗaikun dangin Ikilima da ke gidan sai suka cika rigunansu da iska suka koma can gidan biki inda amarya ta ci shiri ta yaɓa kwalliya sam ita ba ta san abin da ke faruwa na sai da ƴan gyaran ɗaki suka dawo suka gulmata mata.Sai kuma a lokacin ta samu labarin abin da ya samu da ummarta,kiran wayar MAHEER ta yi hankalinta duk a tashe amma ya ƙi ɗagawa a ƙarshe ma aka ce wayar a kashe take.
So take ta je ko da can asibiti ne ta duba Umma amma an hana ta,haka ta yi ta kuka ana bata haƙuri . Allah ya yi mata sa'a ma Ummar ta dawo gida da gotacen hannu an yi mata aiki da shi,Ikilima ta nufo ta tana mai cewa "saboda wata can banzar ƴar aiki ce yayi miki haka?"
"Ba fa ƴar aiki ba ce wallahi matarsa ce,kuma ƴar uwarsa ta jini" cewar ɗaya daga cikin waɗanda suka yi jere.
Umma jin furucin ta yi kamar saukar aradu amma ta san in ba a yi haka ba to tabbas ba za su yi mata ƙarya ba.Wani zare-zare ne take ji yana yi mata yawo a maƙoshi,ta fi jin zafi da ciwon yadda MAHEER ya fifita Haule a kan ƴarta Ikilima fiye da ciwon da ya ji mata .MAHEER ɗin da ta daɗe tana kashe kuɗaɗenta wurin bin malamai da bokaye saboda kawai ƴarta ta aure shi su ci dukiyar da babu wanda ya san da ita daga Hajiya sai ita ko shi MAHEER ɗin bai san da cewa Hajiya tana yi masa tanadi mai kyau ba domin rayuwarsa ta gobe ba.
Mayafin jarumta ta aro ta yaɓawa kanta kafin ta ce "shi namiji mijin mace huɗu ne dukkanmu mun yarda da haka,kuma ba matsala ba ce.Amma abin da yayi mini zafi shi ne yadda aka ɓoye yana da wata mata amma ba komai Allah sa haka shi ya fi zama alkairi Ikilima je ki ci gaba da harakokinki kar ki wani ɗaga hankalinki" kowa ya shaye da mamaki yake kallonta amma yadda ta ƙware wajen salon iya munafurci babu wanda ya zarge ta sai kuwa duk aka ci gaba da shagali.
Umma na shiga ɗaki ta ɗauki waya ta kira bokanta ta shaida masa abin da ke faruwa,cike da izzarsa wacce ya saba musu su ɓatattun ya ce "wannan ai ƙaramin aiki ne ,ina mai tabbatar miki da ƙafarta za ta bar gidan kuma ba za ta sake waiwayarsa ba.Sannan zan aiko da wani magani wanda ita yarinyar ta wajenki za ta yi amfani da shi " godiya ta yi masa bayan yayi mata bayanin yadda za a yi amfani da sh,ba a ɗauki lokaci ba kuwa tsudum ta ga baƙin ɗaurin magani ya bayyana ta saki murmushi don tuni zuciyarta ta ruɓe wajen gaskata maganar bokaye.
Bayan sallar isha'i suna ta jiran motocin ɗaukar amarya amma shiru babu ko ɗaya wacce ango ya turo,duk da balbalin wutar da ke cin zuciyar Umma haka ta daure ta ɗauko hayar motoci aka zo aka kwashi mutane tare da amarya aka kaita ɗakinta.Sai ma da su Hajiya suka ji guɗa ne suka farga cewa ashe yau za su tarbi amarya,duk rawar kan nan da Hajiya ke yi a farko akan auren duk sai ta rage ta.Dangin mahaifin MAHEER ma haka,amma sun daure babu laifi sun tarbi amarya haka suka yi abubuwansu babu abokin ango ko ɗaya suka watse.
Hajiya kasa sukuni ta yi ta kira MAHEER ya shaida mata kuwa har zuwa yanzu yana asibiti yana jiran HAULE ta farka .Ta ce "ko na zo kai ka dawo gida?"
"A'a Mama na dawo gida na yi me ?"
"Dama an kawo Ikilima ne"
"Wa ya kawo ta? Ni na ce a kawo ta ne? To waɗanda suka kawo ta su mayar da ita"
"A kawo amaryar yau kuma a mayar da..." shiru Hajiya ta yi sakamakon haɗa ido da suka yi ita da Ikilima wacce duk ta ji hirar tasu,hawaye suka ƙara zubo mata kafin ta juya da sauri.
Hajiya ko da take duba waya sai ta ga tuni ma MAHEER ya kashe kiransa.
★ASIBITI
Tun da na soma yin bacci aka ja ruhina zuwa wani wuri mai bala'in duhu ,haka na yi ta tafiya amma ban ganin komai a gabana can kuma na ji an riƙe ƙafafuwana,wani lantarki ne na ji ya ja ni da sauri na rumtse ido na sake buɗe su tare da sauke kaina ƙasa amma ban ganin kowa saboda matsanancin duhu.
Amon wata murya na soma ji mai cike da rauni da kuma neman agaji tana cewa"ina yi miki wannan furicin ne idona suna masu shatatar da hawaye,ni ɗin na kasance mace mafi shekaru a danginmu kaf don na kai shekara talatin har da bakwai amma ban taɓa samun tsayayyen saurayi ba ,ina son aure amma babu mijin.Gorin ahali,cin fuskar ƙawaye ba su taɓa tunzura ni zuwa wajen malami ba ballantana boka.Abin da na riƙe shi ne kawai addu'a,ana cikin haka ne mahaifina ya kawo mini wani a matsayin wanda zai aure ni.Sosai ji daɗi,duk da yanayin shi mutumin bai yi mini ba amma haka na yarda na amince ko ba komai dai ni ma zan yi aure kamar kowa.Cikin ƙanƙanen lokaci aka fara shirye-shiryen aurenmu,bayan biki bayan an kai ni ɗakina amma sai shi mijin nawa ya ce za mu je can gidan iyayensa mu yi sati ɗaya haka al'adarsu take.Bayan mun je can gidansu ina ta baza ido domin ganin a inda za mu kwanta sai dai babu,gidan iya ɗaki ɗaya ne da falo.Surukata ce ta matsa mini na je na yi wanka sai na canza kaya,bayan na yi wanka ina tsaka saka kaya sai ga mijina ya shigo yana mai shaida mini wai daren farkonmu mu huɗu za mu yi shi ,da na ce masa ban gane ba sai yake shaida mini za mu yi tarayya mu huɗu ni da shi da kuma iyayensa.Dukan furucinsa bai gama hucewa ba sai ga iyayensa sun shigo babu sutura a jikinsu,ban taɓa ganin bala'i ba irin wannnan kawai sai na fasa ihu na fito a guje sai ban kai bakin ƙofa ba na ji na zurma cikin wannan ramen da nake ciki,sama da kwana uku nake a nan ko ƙwaro ban taɓa gani ba in ba ke ba ki taimaka mini ki cece ni" ƙarshen labarin nata yayi daidai da farkawata daga bacci sai dai tamkar recoding haka amon muryarta ke yi mini suwa a cikin dodon kunne,na lumshe ido ina jin zuciyata na bugawa don kuwa na gane muryar wace ce,ita ɗin ƴar uwata ce Ƴa kuma ga Kawu Hamza babban Yayan kaf iyayenmu maza.Da na buɗe idona a karo na biyu sai na lura a inda nake,sai kuma na dinga jin motsi a cikin toilet duk da ban ga wane ne ba amma na fi kyautata zaton MAHEER ne.
Cike da tausayinsa saboda hukunci da zuciyata ta yanke mini a yanzu na yi saurin tashi ina mai furta wasu harufan da suka haifar da wani iska ya soma kaɗawa har gashin kaina na tashi sama,ƙofar ce ta buɗe da kanta na bi na wuce har na fito bakin ƙofar asibitin nan na yi arba da ainahin protector ɗina,wata jibgegiyar mage ce mai zanen tambarin tauraro da wata a goshinta,idonta sharrr suke sai haske suke fitarwa.A kan magen nan na hau ta soma yin wani juyi kamar ana kaɗa majaujawa kafin kuma ta cillo mu tushena,garinmu a kuma cikin gidanmu....... My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
37
Kallon tsanake na yi wa gidan namu,duk an sauyawa komai an zuba uwar dukiya.Tsarin gidan tamkar aljanu ne suka ƙera shi tsabar yadda yayi kyau ya tsayu cikin tsari.Na ɗan saki murmushi jin kakari tamkar na fitar rai,ko da yake shi ɗin ma ne saboda mutuwar ce ke tunkaro mai kakarin saboda ina ɗauke da makami ƙwaya ɗaya tal da zai iya kashe shi ya koma inda ya fito.
A hankali na ci gaba da takawa ina dosar ƙofar da za ta sada ni da babban falon gidan.Tsit ko ina yake lokacin da ƙofar ta buɗe mini da kanta na shiga,yadda aka jera ɗakunan da kuma yadda aka tsara su bai hana ni na gane ɓangaren kowace direct sai na doshi ɓangaren Innarmu har na je bakin ƙofa na ji an dafa kafaɗata ta baya.
Da sauri na juyo,nan na yi tozali da Hassana a tsaye kan ƙafafunta gurbin idonta na kawo jini.Na rungume ta cikin farin cikin ganinta kafin na kira sunanta cikin sanyin murya,ta amsa mini da "na'am HAULE kin dawo?"
"Eh na dawo "
"Ina buƙatar mu keɓe a wani wurin da ba gidan nan ba domin sanar da ke komai da ya faru bayan ba ki nan"
Ba ta ida rufe bakinta ba na soma jujuya iskan bakina ,nan take wasu katangu huɗu suka yi mana iyaka da gidanmu ta yadda ko da wani ya shigo ba zai ji abin da za mu ce ba haka kuma bai ganinmu .