Kenza eBookz

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 9

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki - Chapter 9

Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 9: Baƙin ruhi complete by mrs sadauki Chapter 9. Cikin kwantar da hankali Dr David ya ce "kawai ka furta mata…

4,428 words

Cikin kwantar da hankali Dr David ya ce "kawai ka furta mata kalmar so shi ne mafita" a zafafe ya katse shi da cewa "wa ya faɗa maka sonta nake? "

Dr David yayi murmushi ya ce "shi kuma laƙabin da ka yi mata na Queen fa? "

"Wannan kuma daban yake amma ni ban son ta"

"To tun da haka ne ina ruwanka da ita ? Kawai ka fita harakarta,in shi Dr Muhamud ɗin a gaske yake son ta ai abin alfahari ne a gare mu"

"Ka ga Please fita ka bani ofis " cewar Maheer yana mai nuna masa ƙofar fita,Dr David ya girgiza kai ya ce "dole fa sai ka fidda wannan aƙidar taka daga cikin ranka na cewa Maheer ba zai so kowacce irin mace ba,saboda da dai wallahi son yarinyar nan kak..."bai barsa ya ƙarasa ya yi saurin shigewa toilet ya bar Dr David ɗin nan a tsaye.

Jingina yayi a jikin ƙofa tare da yin shiru yana sauraren bugun zuciyarsa wacce ya lura ba ta yin irin wannan dokawar sai in Haule na magana da wani namiji.... My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

15

Wani irin feshin wuta zuciyar Maheer take,ko tantama babu ya san a halin yanzu ita da Dr Muhamud ne suke a tare.Ya cije leɓensa na ƙasa kafin ya ɗaga ƙafarsa dakyar ya je gaban shower ya kunna pampon ruwa suka soma dukansa.Kamar wani mahaukaci ya soma magana shi ɗaya,"daga yanzu ba zan sake yi miki magana ba kuma wallahi ni ban son ki nake ba kawai ina kula ki saboda mahaɗin sirrin da ƴar aike ta baki,babu wata mace da Maheer ke so wannan ƙarya ne ban son ƴar kowa" sai kuma ya ɗaga kansa sama tare da buɗe idonsa ruwan na ta bugunsa,ya kwashe tsawon lokaci kafin ya cire kayansa ya ɗaura towel ya bi ta ɗayar ƙofar da za ta kai shi da keɓaɓen ɗakinsa da ke cikin ofis ɗin.

Dakyar ya iya ture tunanin Haule ya shirya cikin suit baƙaƙe ya fesa turare,baƙin tabarau ya manna saboda yadda ya ga idonsa sun yi ja . Ko da ya fito Dr Umar ya tarar a zaune kan kujera fuskarsa da alamun damuwa,yi yayi kamar bai gansa ba ya nufi ƙofar fita amma shi Dr Umar ɗin ya tsayar da shi ta hanyar kiran sunansa,ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce "ban cikin yanayin magana Please ka bari za mu tattauna daga baya"

"Don Allah ka yi haƙuri ka saurare ni ka fi kowa sanin Fateema ita ce komai nawa,in wani abu ya same ta ba zan yafewa kaina ba.Please ka sanar da ni mene ne taƙamaimai ciwon nata? Ka ga fa tana can tana kuka ta rufe kanta a toilet "

Ran Maheer ne ya sake ɓaci,wato kowa so yake ya masa maganin matsalarsa amma shi babu wanda ya damu kan ya samu farin ciki."Fateema lafiyarta lau babu wata matsalar kwanya da take da,wasa take da hankalinka akwai wani ƁOYAYYEN SIRRI da ta ɓoyewa kanta,muddin kuma ba ta fitar da shi ba to duk maganin da nake yi mata zai tashi a banza ne don ko na zuƙe mata ruwan da an ɗauki lokaci dole wasu su taru" yana gama faɗa ya fice daidai kuma wannan lokacin ne Dr Muhamud ya fito daga ɗakin Haule yana wani sanyayyen murmushi mai fallasa sirrin zuciya.

Da wani mugun sauri ya ɗauke idonsa gare shi tare da ficewa ya bar asibitin kwata-kwata.Hanyar fita gari ya ɗauka yana ta sharara gudu kafin ya soma gangarawa zuwa cikin ciyayi,wuri ya samu yayi parking kafin ya soma tafiyar ƙasa.Sai da ya ɗauki kamar minti goma kafin ya iso wata tsohuwar rijiyar marar murfi,yasa tafukan hannuwansa ya dafa bakin rijiyar tare da ƙanƙance idonsa yana kallon baƙaƙen ruwan da ke kwance can cikin dogon ramen.

Zanen hoton fuskarsa ne ya soma haɗuwa kafin kuma ta fito daidai kamar yadda take a zahiri.Sannu a hankali ruwan suka fara tunkuɗowa suna yo sama har suka zo dab da fuskarsa,ido ya lumshe kafin ya soma yin wani Yare yana ambaton sunan wata mata kamar walƙiya haka matar ta bayyana a zaune a bakin rijiyar yayin da kuma ruwan suka ci gaba da yin motsi ta yadda suka rufe ƙafafuwanta ba a iya ganinsu.

"King sai yau aka kawo min ziyara?" dattijuwar matar ta faɗa wacce ta kasance shararriya kuma fitacciyar matsafiyar tsafi sai dai nata kan turbar arziki take gudanar da shi.

Ba tare da ya ɗago kai ya dube ta ba ya ce "Yabobo na zo nan ne domin neman wata alfarmar a gare ki fatan za ki yarda da muradina"

Wani murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce "ka yi haƙuri King Maheer,dole Queen Haulat na buƙatar dogon lokaci domin yin nazari akan abin da kake guje mata sai dai kai ma da naka laifin me yasa ba ka fallasa mata sirrin zuciyarka ba"

A hankali ya ɗaga kansa yana kallon Yabobo ta baƙin tabarau ɗinsa,muryarsa har sai da ta shaƙe tsabar yadda baƙin ciki ke naƙarƙasar zuciyarsa ya ce "ni fa ba na sonta,kuma babu yadda za a yi na aure ta don ba zan iya bayyanar da sirrina ga ƙanƙanuwar yarinyar da ko tsarki ba ta iya ba.Sannan please Yabobo ki taimaka ki sa ƴar aike ta je ta karɓe mahaɗin sirrin da ke ga waccan yarinyar in ya so ko Ikilima ce ta bai wa"

Nan ɗin ma murmushin ta yi kafin ta ce "Ikilimar da ka ɗirkawa shegen duka ita ce kuma yau kake son a baiwa ƙarfin iko mai tsarki? Ka sani power da ke jikin Haulat tsarkaken matakin iko ne wanda ba a ko wane irin gangar jiki zai zauna ba sai mai tsarkaken ruhi wanda ba a yi baɗala da shi ba"

A zuciye ya ce "baɗala kuma ta nawa Yabobo? Tana can asibiti ta saki gangar jikinta wani ƙaton banza na kama kafaɗunta yana fakewa da sunan taimaka mata ne yake don ta tashi,sannan har hannunta yake riƙewa fa"

Yabobo nutsuwa ta yi tana kallon yadda Maheer ke zuba masifa mai bayyanar da tsantsar kishinsa,amma idonsa sun rufe kan ƙudirinsa na bai iya soyayya da kowacce irin mace sai ya bincika ya tona ya samo mai tsabta.

"Riƙon da Dr Muhamud ya yi wa Haulat ba za mu iya kira shi da baɗala ba,in ma akwai wanda za a kira a haka bai fi kai wanda ka yi mata ba ka raba ta da suturar jikinta ka kalle mata jiki saboda kana tantama da shaƙu a kanta.King ina so ka sani kowacce ragaya da tata ƙwarya,haka kaina ƙyaure ita kuma ƙofar rufin asirin ɓoyayyar duniyar.Kar ka bari ego ɗinka ya rinjaye ka ya rufe ma ido ka kasa ganin gaskiya,yanzu dai ka koma ka bata maganinta ko ta samu ta koma a bakin aikinta kuma ban son jin ka yi min gardama"

Duk da ya ji kunya na abin da ya aikata,amma sai ya fuske tare da cewa "ba zan warkar da ita yanzu ba,zan bari na ga iya gudun ruwansu ita da shi Dr Muhamud ɗin da yake yi min ɗagawa shi ma ai likita ne.Please Yabobo ki bani wannan damar,yarinyar nan ba ta jin magana ɗazu fa har masifafe ta ce min"

Yabobo ba ta ce komai ba sai fara nitsewa da ta soma yi cikin rijiyar har ta ɓacewa ganinsa.Haka ya koma can inda ya ajiye motarsa,direct kuma gida ya wuce a falo ya tarar da Hajiya sai masifa take an bar gida da ɗauda wuni guda kacal da Haule ba ta nan amma har gidan ya canza.

Bai iya cewa komai ba ya haura sama ba tare da ya amsa gaisuwar da Lubna ke yi masa ba.Yana shiga can ɗakinsa ya rage kayansa tare da haye bed,tunani ya soma ranar da ya ɗauko Haule ya kawo ta kan shimfiɗarsa duk don son tabbatar wa shin da gaske ita ce murfin jallonsa ko kuwa? Ya samu cikakkiyar amsa sai dai kuma ya ƙi yin aiki da ita.Daga nan inda yake a kwance kan bed ya soma juya idonsa yana zuƙo awarwaron Haule da yayi mata ƙwacensa ta ƙarfi,tuni ya haɗe awarwaron wuri guda .Wani furicin yayi sai kuma ga macijinsa ya bayyana,ya saki murmushi kafin ya rataya wa snak ɗin nasa shi a wuya yana wani irin murmushi.

★ASIBITI

Bayan na gama shan tea ɗin Dr Muhamud ya zo min da wani zance mai daɗi,shi ne batun yana son bani waya in na yarda.Duk da babu wanda zan kira amma ina son yin game a rayuwata sai na ce masa " duk abin da ya fito daga gare ka ina maraba da shi"

"Na gode ki kwanta ki huta" shi ne abin da ya faɗa kafin ya fice sai kuma ga Aliya ta shigo.

"Daga ina kike? Ina Lubna?" na tambaye ta. "Tun ɗazu suka koma gida fa,dama Alhajinki ne ya matsawa Hajiya kan cewa ta zo ta duba ki don da wuya in za ki rayu shine ita kuma ta yi ta kuka hhh." ta ƙarashe tana dariya kafin ta zauna gefen gado tana kallona.

"Me aka yi?"

"Babu komai ! Amma dai gaskiya ban ji daɗin yadda kika ɓatawa Alhajinki rai ba na ga ya fito yana fushi a lokacin da muke tare da Dr David "

Jin ta ambaci sunan David yasa na yi saurin cewa "yawwa wai don Allah ko shi ne saurayin Lubna?"

Aliya ta yi wani murmushi kafin ta ce "eh shi ne,kuma fa sun ga juna ɗazu amma ba wanda ya yi wa ɗan uwansa magana hum! Da dukkan alamu Lubna ta raina mana hankali ƙarya ce kawai ta shararo mamu,amma da sannu zan gano gaskiyar labarinta tun da shi Dr David ɗin ma ya ce yana sona "

Na wato ido na ce "saurayin Lubnar ? Kuma ya na ji kina kiran sunanta kai tsaye babu ko ƴar Anty ?"

Dariya ta yi kafin ta ce"ke ban ƙara ce mata Anty tun da har ta munafurce mu,kuma sam ban yarda da zuwanta na yanzu ba ƙila a tunaninta a gaske mutuwar za ki yi"

"Ni ban riƙe ta a zuciya ba na yafe mata,sai dai zan faɗa mata ta dinga controling kishinta don ni ko a ƙafa aka ɗaura min Maheer sai na kwance shi yo me zan yi da ƙarmasashen mutum jiki duk ƙasusuwa ta je can su ƙarata .Ai sosai ma haɗin nasu zai yi kyau kowanne da tasa masifar"

"Kina nufin ba ki son Maheer?" Aliya ta jefo min tambayar,wani irin rasss na ji a zuciyata da sauri kuma na ɗan lumshe idona nan take kuma na yi arba da shi yana kwance daga shi sai gajeren wando cinyoyinsa a fili duk gargasa ce ko ina,sannan ko riga bai da.

Numfashina ne ya soma gudu da sauri-sauri ina jin Aliya na tambayata lafiya haɗi da kiran sunana amma na ƙi buɗe ido sai kallon kyakkyawar surar Maheer nake yadda yake fari fesss babu wani tabo a jikinsa. Ban sani ba ko ya ankara da na ziyarce shi ne ko me kawai sai na ga ya ɗago shegen macijinsa mai ƙwala-ƙwalan ido da mugun sauri na buɗe nawa idon ban shirya ba.

Aliya ta ja wani dogon numfashi mai bayyanar da tsoronta ta ce "ina shirin fita nemo Dr " Na ɗan murmusa na ce "ba fa abin da ya same ni kawai dai wani abin na gani?"

"Me kika gani?"

"Komai" na faɗi haka tare da lulawa duniyar tunani amma sam ban yarda na rufe ido ba. Sai wuraren sallar isha'i yaron nan Amar ya farka,kuma sai aka fitar da shi.Ni kuma Aliya ta dinga taimaka min wurin tashi,da dare Dr Muhamud ne ya kawo mana abin da za mu ci sannan ya damƙa min sabuwar waya har da layi a ciki.Bayan ya fita Aliya ta taɓe baki ta ce "wai son ki yake ko me?"

Ban kai ga bata amsa ba Lubna ta shigo ɗauke da kwanon abinci,a kunyace ta tambaye jikina na amsa mata a taƙaice kafin ta nemi wuri ta rakuɓe.Aliya ce ta katse shurun namu ta hanyar cewa "please Haule ki bani ci gaban labarinki mana"

Na ɗan yamutsa fuska har zan ƙiya sai kuma na ga babu abin da ya fi dacewar ma kamar na ci gaba da bata labarin don zuwan Lubna ba zai bari mu yi hira yadda ya kamata ba.Sai da na ɗan kishiginɗa kafin na soma "sau ɗaya tak saurayin nan ya zo suka zanta shi da Anty Aliya sai kawai aka fara zancen biki,Innarmu ba ta wani tayar da hankali ba duba da ba tsoho ne aka zaɓa mata ba ashe ba ta san tsiyar da ya shirya wa ƴartata ba.Muna ta shirye-shiryen shagalin biki,tuni na manta da wani zancen abin da na ji iyayenmu maza na tattaunawa game da ni.Ana gobe biki ne kuma na sake yin mafarkin Husseina,ta zo ne don isar min da saƙon kar na bari anty Aliya ta auri Abbas wanda ya kasance ƙanen ɗan Sarkin garinmu sai dai ba ta faɗa min ta wace hanya ce zan bi ba.Washegari da na farka tuni ma an ƴan ɗaurin aure sun fara zuwa,na rasa wanda zan tunkara da maganar dama ko can Hassana ce abokiyar shawarar to ta zama kurma.Ganin ban samu mafita ba kawai sai na ja bakina na yi shiru,ba a kuma ɗauki lokaci ba aka ɗaura aure a kuma ranar aka miƙa ta gidan mijinta .Tun kuma a ranar ya soma yi mata izaya,daren farkonsu ya mayar da shi daren mutuwarta don kuwa yarjejeniya suka yi da wata ƙungiyar asiri kan cewa zai bayar da ruhin matarsa fansa saboda yana son hawa karagar mulki.Sai bayan watanni uku da aurenta ne na ziyarce ta,yadda na anty Aliya sai duk hankali ya tashi ita kuma rungume ni kawai ta yi ta soma kuka.Ban sani ba ko ta ga wani abu a tattare da ni da yasa ta fallasa min sirrin gidan aurenta,bayan ta ci kuka ta ƙoshi ni ma ina taya ta sai ta kama hannuna ta ce "Haule ina cikin matsala,Abbas matsafi ne tare yake da ƴan ƙungiyar shan jini kuma Ni ce wacce ya bayar matsayin sacrifice ɗinsa na farko,tun bayan da mutane suka watse ranar da aka kawo ni gidan nan ya shayar da ni jinin baƙar dabba sannan...sannan a cikin wani ƙaton akwati ne yayi sunnar aure da ni,jinin budurcina kuma shi ne ya tanɗe shi.Ta so ki ga " sai ta ja ni muka nufi ɗakinsa mai ɗauke da wasu irin zanen tambarin ƙungiya kina gani kin san abubuwan tsafi ne,a kusa da bed ɗinsa kuma wani zundumemen akwati ne irin wanda Nasaru ke saka gawa,anty Aliya tana kuka ta ce "in dare yayi a nan ciki nake bacci ,haka zai tirsasa ni na shiga ba zai buɗe ni ba sai gari yayi haske rana ta ɓullo.Duk yadda nake son guduwa daga gidan na kasa,in kuma na yi niyyar faɗawa wani sai na ji na koma tamkar kurma ba na iya yin magana.A jiya na gwada tserewa amma ina fitowa daga cikin akwatin nan yadda kika san kifi ya bar ruwa haka na ji ina shirin mutuwa dole na koma,ya zan yi Haule?"

A lokacin shekaruna sun yi ƙarantar da zan iya zurfafa tunani har in samo mata mafita,abu guda ne na gani maslaha shi ne na sanar da Innarmu sai dai ina zuwa gida da na fara sanar mata sai ta toshe min baki tana girgiza kai haɗi da yin kuka a cikin idon Innarmu nake hango rashin madafa sannan da wani irin rauni.Dakyar kuma ta iya cewa "Haule babu abin da za mu iya yi wa Aliya a yanzu in banda addu'ar Allah ya kuɓutar da ruhinta kar ya isa ɓoyayyar duniya,don izuwa yanzu sun gama yi mata raunin da ba za ta rayu a wannan duniyar ba"

Cikin kuka na ce "Innarmu kenan kin san duk abin da ke faruwa?"

"Ban sani ba Haule,amma kar ki manta ni uwa ce sannan ita uwa tana fahimtar ƴaƴanta ba tare da sun yi magana ba.A yadda na ga Aliya kawai na fahimci ba ta jin daɗin gidan aurenta,ba wai rashin daɗi irin na saɓani ko ƙunci ba a'a baƙin ciki ne mai sukar ruhi.Kin ga daga yau in kin yi sallah ki roƙa mata Allah ya bata mafita da cinye jarabawar nan sannan kar ki saki ki nunawa wani kin san labarin nan.Hum! A ranar ne na ida fahimta mu da dabbobi banbancinmu ƙalilan ne,don in ba dabba ba babu wanda zai yarda a kashe ɗansa a gaban idonsa ba tare da yayi komai ba.A cikin wannan daren aka zo aka shaida mana Aliya ta rasu,wanda kuma ba wai mutuwar ce ta yi ba a'a mijinta ya ji tsoro ne ta yadda kar a je ta kawo masa matsala don tuni ya ji a jikinsa ta fitar da labarin.Lokacin da muka je babu wani alamun rauni a tattare da ita,Innarmu ta matsa kan lallai dole gawar Aliya ba za ta kwana ba a cikin daren za a rufe ta shi kuma mijin ya ce sai gobe ya faɗi haka ne saboda tsarin gunƙiyarsu akwai tsafe-tsafen da za a yi wa gawar kafin a binne ta.Iyayenmu maza irin masu tsaurin nan ne hakan yasa suka tsawatar wa Innarmu tare da cewa a yi yadda mijinta ya ce ɗin sai dai washegari da aka buɗe gawar anty Aliya abin ya girmi mai tunani.... My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

16

Washegari gawar anty Aliya ta koma baƙa ƙirin babu kyawun gani,haka kuma idonta suna fitar da kukan jini.Amma bari ku ji wani abin mamaki iya ni da Innarmu ne kawai muka ga haka sai iyayenmu maza waɗanda jikinsu yayi sanyi don su kansu ashe ba su san cewa MUGUN MIJI (Mamar ƴan biyu) ne suka aura wa Aliyar ba,ko ma dai sun san cewa yana da ido uku ba su zata zai iya bayar da ita ba.Duk a tunanin kuma iyayenmu maza iya su ɗaya ne kawai suka ga abin tsoratarwar nan ba su san cewa ni da Innarmu mun ga komai ba.

Bayan an yi wa anty Aliya wanka haka na faɗa jikin gawarta ina kuka,a lokacin sai na ji hannuwanta kan gadon bayana a take kuma na ji wani irin yanayi ya ratsa ni amma ban san cewa hakan na nuni da ba ta mutu ba kawai gidan kaso aka rufe ruhinta ba sai har bayan an rufe ta ne Husseina ta ziyarce ni tana tuhumata akan laifin da ban san hawa ba ban san hauka ba.A cewarta ni ɗaya ce ke da ikon tsayar da wannan mummunan al'amari da ke faruwa a gidanmu da kuma kewayen garinmu da ya soma yaɗuwa amma ban san ta yaya ne zan yi na dakatar ɗin ba.

Bayan sadakar uku muna zaune a cikin ɗaki,ni da Innarmu wacce ke waya da Yaya Aliyu yana jajanta mutuwar ƴar uwarsa don tuni ya je can ƙasar waje karatu.

A cikin kalaman Innarmu ne na tsinci wasu kalmomi waɗanda ba na wannan duniyar ba ne na Ruhaniya ne amma sai ban tambaye ta ma'anarsu ba.Bayan ta kashe wayar sai ta dube ni da kyau ta ce "Haule me iyayenki maza suka ce miki? Ko har yanzu ba su yi miki bayanin komai ba?"

Shiru na yi ,sai kuma hirarsu ta wancan lokacin ta tun kafin auren anty Aliya ta dawo min.Kai na girgiza mata na ce "a'a babu abin da suka ce"

"Ko dai kina ɓoye min ne?"

"A'a Inna wallahi ba su ce min komai ba" na faɗa sai kuma na ɓoye mata zancen na dai ji suna magana a kaina,saboda ina da zurfin ciki ba komai ne za ki ji ina faɗa ba. Innarmu ba ta ce komai ba sai ta je ta buɗe wani ƙaton sanduki ta ajiye wayarta sai ta fice.Tana fita kuwa na buɗe shi da niyyar ɗauko wayar na yi game,sai dai wani abu ya ja hankalina wani ƙaton book na gani mai hoton aljanu suna rawa sannan a can gefe wani babban aljani yana dariya ya buɗe manyan haƙoransa.

Jikina har rawa yake wurin ɗauko shi,a hankali na karanta sunan littafin wanda aka rubuta da manyan baƙi."WANZUWAR *BAƘIN RUHI* A DUNIYAR BIL'ADAMA " da farko haka na yi ta mamakin jin sunan sai dai ina buɗe shafin farko na ji tamkar an yi min wankin ƙwaƙwalwa sai na soma gane bayanin abin da ya ƙunsa.

A cikin wannan littafin akwai sunayen dodanni iri-iri kuma kowanne da aikinsa, sai dai na kasa gane wane ne ainahin BAƘIN RUHIn wanda na ga kamar saboda shi aka wallafa littafin.

Daki-daki na soma karanta littafin har na zo ga sunan wani dodo ,bayanansa kawai na karanta sai na tuno da anty Aliya wannan yasa na rufe littafin da sauri tare da mayar da shi inda yake.

Can tsakar gida na fita, lokacin ƙarfe uku ne na rana da wasu ƴan mintina.Aiki nake son aiwatarwa wanda kuma a yadda na karanta dole sai cikin duhun dare kawai zan iya yin haka, wannan yasa na je na yi duk wani aiki da na san ni ce zan yi shi.

Ko kafin sallar magarib na gama komai,sai na faki idon Innarmu na koma ɗaki na ƙara buɗe sandukin na ɗauko littafin tare da buɗe shi daidai shafin dodon da nake so.Yage takardar na yi tare da cusa ta cikin riga,mutane na hada-hadar yin sallah na yi wuf na bar gidan ba tare da kowa ya sani ba.

A lokacin duk wani tsoro ji na yi ya fice min,haka na tafi cikin daji na soma karanto harufan da ke jikin takardar amma shiru dodon bai bayyana a gare ni ba har sai da na gaji zan koma sai na ji wata irin tsagewar ƙasa da sauri na soma ja baya ganin wani hayaƙi na fitowa a cikin siffar dodo.

Tsoro ne ya aure a nan take,ban ida ruɗewa ba sai da na ji muryarsa yana cewa "mene ne dalilin kirana a wannan duniyar?"

Murya na ɗan rawa na ce "ina son ɗaukar fansa ne ga mijin antyna,ya kashe min antyna alhalin shi yana can yana rayuwarsa"

"Me kike so a yi masa?"

"A haukata shi ta yadda ba zai cimma nasarar abin da yake so ba" na bada amsa.

"Komai yana da farashi,amma za a yi yadda kike so kafin nan daga yau kin zama shugabata" yana gama faɗar haka sai ya soma dunƙulewa wuri guda yana ɗaukar wata siffa kamar ta mutum sai dai kafin ya ida bayyana na ji sarar maciji a ƙafata,kuma daga nan ban sake sanin abin da ya faru ba na dai tsinci kaina a gida ƙafa a ɗaure da Abbana na soma cin karo yana yi min wani irin kallon ƙwarilla yayin da muryar Kawu Hamza ta daki kunnena "Haule me kika je yi daji?"

Na ɗan zabura na kalli gefen da yake,sai yanzu na lura ma a ɗakinsa ne nake sannan kuma kaf iyayenmu mazan suna ɗakin kowanne yana jiran amsar da zan bayar.Kasa cewa komai na yi don kuwa muddin na buɗe baki na yi magana kashina ya bushe,"ke ba magana ake yi miki ba?" Abbana ya katsa min tsawar da tasa na fashe da kuka ban shirya ba.

"Ibrahim ka bi ta a hankali mana,in ka ce ta ƙarfi za ka yi mata kana tunanin za mu samu amsar abin da muke son ji?" Kawu Hamza ya cewa Abbana kafin ya maido dubansa gare ni,"ina jin ki ƴata Haule me ya faru da ke har kika je cikin jeji?"ya tambaye ni cikin taushin murya.

Na ɗan rage shashekar da nake na ce "wallahi Kawu ni ma ban sani ba,yaushe na tafi daji?" Ransa ne na ga ya ɓace amma yayi saurin shanyewa ya ce "ki faɗa mana wa ya kira ki izuwa can?"

"Kawu na faɗa maka..."sauran maganar ce tawa ta maƙale ganin guntuwar takardar da ya nuno min,"me kike yi da ita a hannunki? A ina kika same ta shi ne abin da ya fi komai yi mana muhimmanci "

Tabbas a lokacin na tsorata ainun ,don kuwa na san muddin na faɗi cewa a ɗakin Innarmu ne na samu takardar to na jefa rayuwartar a cikin gagarumar matsala.

Dodon da ke manne a takardar na kalla tare da ƙura masa ido,nan take ya bani satar amsa na ce "shi wannan wane ne a jikin hoton ? Sam bai da kyawun gani" da na yi furicin sai suka kalli juna,wato raina masu da hankali ne na yi .

Kawu Hamza ya ja dogon tsuki ya dubi Kawu Laminu ya ce "ka ce min a hannunta ka same shi"

"Eh to kusa da ita na gansa shi yasa"

"Mtsw! Aikin banza shine kasa duk muka taru akan abin da ba ka da tabbas,kai Ibrahim ɗauki ƴarka ka fitar min da ita"

Haka Abbana ya sungume ni ya fito da ni ya kai ni ɗakin Innarmu wacce ke zubar da hawaye.Tana ganina ta zo ta fara shafar kaina,"Haule me ya kai ki yin wannan karanbanin?" ta tambaye ni bayan Abbana ya fita daga ɗakin.Ban iya cewa komai ba na lumshe ido ina tunanin zuci 'dama ana iya kiran dodo daga duniyarsu izuwa duniyarmu? To amma me yasa ya kira ni da shugabarsa?' ire-iren tunanin nan na yi ta yi har bacci ya ɗauke ni.

Washegari sai aka kira mai bayar da maganin maciji,abin mamaki matar nan dai ce wacce ta baiwa Hassana magani har ta tafi da idonta,abin da na fahimta kuma iya ni ɗaya kawai na gane dama wancan lokacin iyayenmu maza ba su nan ta zo.

Ɗaurin da aka yi min ta shiga buɗewa tana mai kallona tsakiyar ido,ba tare da ta buɗe bakinta ba kuma take min magana wacce sarai nake ji sai daga baya na fahimci cewa ashe ana iya yin magana ta ido.

"Me yasa kike ɓoye damar da aka baki? Me yasa kike rufe ido akan gaskiyar da ke ta bayyana a gare ki? Shin ba ki san cewa ke ɗin ƴar baiwa ce ba wacce aka haifa da ido uku tun zuwanki duniya ba? Ko ba ki san cewa ke ce za ki yi silar dakatar da gidauniyar gidan nan ba?"

Readers Also Read