Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 30

Bakar inuwa book 1 - Chapter 30

Bakar inuwa book 1 Chapter 30: Bakar inuwa book 1 Chapter 30. A can kuwa ɗakin Ramadhan shigar Bappi tayi dai-dai da fitowarsa wanka, ya sauke towel ɗin da…

4,177 words

A can kuwa ɗakin Ramadhan shigar Bappi tayi dai-dai da fitowarsa wanka, ya sauke towel ɗin da yake goge fusakarsa zuwa suma kawai yaji saukar mari haggu da dama. Gaba ɗaya wutar kansa ta ɗauke ganin wanda ya maresan. Bappi, abinda bai taɓa faruwa ba ko a tarihin ƙuruciya. Dan ko laifi yayi yana yaro sai dai Anne ko Pa su dakesa amma ba Bappi ba. A karshe ma Bappin ke komawa lallashinsa da masa nasiha. Amma sai gashi yau da girmansa. Shekara dai-ɗai har 36 a duniya kakan nasa ya rufe ido ya yarfata masa maruka har biyu bayan wanda Pa ya masa ɗazun.... “Ramadhan ka kiyayi haduwata da kai wlhy!!”. Bappi ya faɗa cikin gargaɗi da ke nuna tabbatarwa. Kafin yay wani yunkuri kuma ya juya yay ficewarsa.........✍

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*

*_Episode. 60_*

.........*_TAURA HOUSE_*

Tunda suka baro government house a sirrance da Raudha kai tsaye Taura house suka nufo. sai dai anan ɗin ma dai babu wanda yasan da dawowar tasu kamar yanda kowa bai san da fitarsu ba. Sake dukufa Dr Hauwa tai akan Raudha har sai da ta tabbatar komai ya daidaita. Abin tausayi har ɗinki akai mata saboda bidirin da Ramadhan yay a jikinta. Hakan ya sake kona zuciyar Bappi da Anne sai dai babu wanda ya iya cewa komai har Dr Hauwa ta kammala aikinta ta wuce. Barci Raudha take saboda allurar barcin da Dr Hauwa tai mata. Dan haka Bilkisu ta zauna ta zayyanema Anne komai data sani har wanda Raudha ma bata san ta sani ɗin ba. Anne harda hawaye tausayin Raudha mai tsanani na cin zuciyarta. Koba komai sune suka jefata a wannan masifar. Maybe dasun barta ta aura dai-dai da ita da duk hakan bai faruba. Sai dai kuma ƙaddara ta riga fata inji masu iya magana. Sannan kuma babu mai sawa ko hanawa daga abinda yazo a littafin ƙaddarar wani bawa koda yana kalon kansa matsayin SILA.

*_WASHE GARI_*

Raudha ta jima bata farka ba har kusan tara, koda ta farka ɗin kuma Anne fidda kunya tai ta taimaka mata sosai kodan ɗinkin da akai mata. Ga Dr Hauwa ta tabbatar musu kar ai wasa da wani motsin Raudha mai karfi saboda cikinta a ɗofane yake. Hasalima bed rest shi tafi bukata fiye da komai a yanzun. Tabbas abu biyu da Raudha tayi ya matukar birge Anne da Bappi. Na farko tambayar duniya sun mata akan abinda ke tsakaninta da Ramadhan ta keƙashe ƙasa ta dage akan babu komai. Tushen abinda ya faru tsakaninta da shi a jiya harya doke ta (dan duka suka danganta abun saboda alkunya da kawaici irin nasu) amma sai Raudha tace wai faɗuwa tai a toilet. Batasan su da idonsu sukaje sukaga halin da take a ciki ba. (Saboda sun ɓoye mata cewar Bilkisu ce ta kaita asibiti suma acan suka amso ta). Na uku tunda ta tashi babu wanda yaga ko ɗigon hawayenta alamar ta dake, wannan ya sakama Anne ƙwarin gwiwar cewar lokaci yayi da zatai training ɗin Raudha a bigiren da sai Gimbiya Su'adah da shaiɗanunta sunyi dana sani. Ramadhan kuwa zai matuƙar gane kuskurensa, ba ita zata hukuntashi ba Raudha ce da kanta zata hukunta shi.

Hhhhh ashe akwai sabon show😋😉🤣.

*____★____★_____★_____★_____*

Tsahon kwanaki uku Raudha na a Taura house babu wanda ya sani sai Bilkisu da Pa da su Anne. Koda Gimbiya Su'adah taga Bilkisu bataji komai ba tunda tasan dama tana shirin dawowa gida ai. Zuwa yau baƙi sun fara isowa daga masarautar su gimbiya Su'adah. Hakama a bangaren sauran matan gidan tunda kowa zai aurar da ɗa. Daga Taura ma dai wasu sun iso sai dai maza ne. Babu wanda ya sake jin labarin Ramadhan babu kuma wanda ya bibiyesa, a kwanaki ukun nan ma ko a labarai sai dai kaji ance Shugaban kasa Ramadhan ya kaddamar da kaza da yawun wane. Amma shi ko sau ɗaya ba'a nunasa ba sai a yau da kowa yasan za'a tafi hutu na ƙarshen shekara da Christmas. Kuma kakakin shugaban ƙasa ya sanar a Taura house shugaban ƙasa zaiyi hutun nasa baki daya. Hankalin Adda Asmah ya tashi matuka, musamman data kira bokanta yace sam karta yarda. Ita da suka gama cin burin kai Aynah government house kai tsaya ya Ramadhan ɗin zai musu haka, ya tabbatar mata ajiye Aynah a Taura house bazai taɓa haifar musu ɗa mai ido ba. Garama tayi duk yanda za'ai ta gyara barnar. Zuwa dare kuma tazo tare da Aynah zai mata wankan magani na ƙarshe da shine sirrin mallakar Ramadhan da duk ma wanda zai raɓesa, zai koma baijin magana ko umarnin kowa sai nata ita kaɗai Aina'u. A rikice tai kiran Number Gimbuya Su'adah. Ita kanta gimbiya Su'adah ranta ya baci dan yau bata maida hankali akan television ba balle tasan da labarin. Tana can suna tafka rigima da Pa akan kofa dinner sai sunyi har guda uku idan ance sauran an hanasu. Shi kuma yace isar da bataiba kenan. Ramadhan ta shiga nema, dan rabonta da shi yau kwana uku kenan tun randa ta kunna zuciyarsa akan kiran daya sanar mata su Bappi sun masa. Maimakon hankalinta ya tashi matsayinta na uwa ta nemesa sai ta share da cewar yana lafiya shiyyasa ko kuma aikin office ne ya rikesa. A lokacin kwance yake yana barci, dan tunda aka baro Raudha daga gidan ya tsinta kansa a wani irin yanayi mai matukar wahalar fassara a garesa. Ya rasa mike masa daɗi mi kuma zai kama. Ransane a ɓace? Ko damuwa da halin daya jefa ƴar mutane? Kokuwa halin da ke shirin riskarsa na auren wadda shi kansa har yanzu baisan dalilin da yasa yake mata wannan mahaikacin son ba. Bisa lallabawar cos yake fita office. Sai dai baya wani jimawa yake dawowa gida. Kuma kullum ya shigo sai yaje ɗakin Raudha da mama ladi bata gajiya da gyarawa. Hatta jinin da Raudha ta zubar a wancan ranar idan bama faɗa maka akaiba bazaka sani ba. Yakanje ya kwanta a saman gadonta. Sai dai baya haɗa mintuna biyu kansa zai shiga sarawa da karfi har sai ya fito ya koma nasa. Kunnawar da Ginbiya Su'adah tai masa yau ma ya sakashi tashi cike da fusata. Yay azamar dafe kansa dake juya masa da karfi. Sai kuma ya mike yana kallon agogo. Ƙarfe kusan sha ɗaya na dare. Amma tsabar yanda yake jin zuciyarsa tuni ya fice cikin ɓadda kama dan bazai iya jira sai gobe da zai huce Taura house ɗin ba ma, yanda yake komai saika ɗauka ana controling nashi da remote ne, dukya birkice, baya gane komai sai abinda su gimbiya Su'adah sukace yayi. Maimakon ma ko a motane yay fitar sirrin kamar yanda yakeyi, sai kawai ya fice da ƙafa ta karamin gate da taimakon odilan ɗinsa da baida ikon hanashi yin hakan saboda akwana biyun nan sam baya gane kan shugaban ƙasa, baya son yace wani abu kuma ga wani game da hakan saboda gargaɗi da Ramadhan yaja masa mai ƙarfi akan yanda yake fitar sirri inhar ya bari wani ya sani bayan shi duk hukuncin daya zartar a kansa yay kuka da kansa kawai. Cab ya tare sai taura house.

A dai-dai lokacin da Ramadhan ke nufar Taura house Adda Asmah ce da Aynah sun dawo daga gidan bokanta anyo mata wankan maganin mallaka. Sam batai tunanin haɗuwa da Ramadhan ba, shiyyasa ta yanke shawarar biyawa ta Taura House takai maganin da bokan ya bata akan gimbiya Su'ada tai turare da shi matsayin na rufa idon su Bappi akan events ɗin da suke sonyi. Sai dai a zahirin gaskiya ba hakan bane. Na rabata da Ramadhan ne baki ɗaya yanda zai koma karƙashin ikon ita Addah Asmah ɗin. Kusan a tare Ramadhan da su Addah Asmah suka iso Taura house. Sai dai shi ya rigasu shigowa saboda an tsaya buɗe musu gate shiko yay wuff ya shige yanda ko mai-gadi ma bai lura da shi ba. Kai tsaye falon hutawa na gimbiya Su'adah ya nufa ta baya kamar yanda ta sanar masa ya sameta a can. Ko zama baiyiba Addah Asmah da Aynah suma suka shigo kamar yanda Gimbiya Su'adah ta sanarma Adda Asmah itama ta sameta anan. Adda Asmah bata san Ramadhan zaizo taura house ba. Haka zalika gimbiya Su'adah batasan Adda Asmah na tare da Aynah ba tunda tasan dokar dake tsakanin kar Ramadhan da Aynah su haɗu sai bayan an ɗaura aure.......

*_Tofa dole na dara kafin na cigaba🤣😂🤣😂, wannan fa shine ana dara ga dare yayi🤣. Ga boka yace kar.....🤭😂bara dai kawai na tsuke bakina muga yaya wasan zai kaya to._*

★Wani irin ihu Adda Asmah da Ayna'u suka fasa a tare cikin tsantsar tashin hankali. Dan kuwa sallamar Aynah dake gaban Addah Asmah tayi dai-dai da ɗagowar Ramadhan saboda ƙofar falon da aka buɗe batare da yayi tunanin wani zai shigo musu ba. Ita kanta Gimbiya Su'adah dake ƙoƙarin kunna buner ta saka turaren hayakin magani da boka yace ta dinga sakawa a duk sanda Ramadhan yazo gareta ta saki tare da yin wani uban tsalle tana dafe ƙirji. “Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Allahumma ajirni fi musibati.....” Ramadhan ya ambato a jere saboda suna haɗa ido da Aynah gabansa yay wani irin mummunar faɗuwar da har sai da kansa ya sara. Hannu ya kai ya dafe kan saboda yanda ihunsu ke shiga masa har tsakkiyar kwakwkwararsa. Duk da kunne sa daya toshe ihun bai fasa shiga ba. Kai bama shi ba, hatta duk wanda yake kusa da sashen gimbiya Su'adah dole ne yaji tagwayen ihun nan. Pa ne ya fara shigowa a kiɗime. dan kamar yanda ya saba duk dare kafin ya kwanta sai ya zagaye gidan ya tabbatar da komai normal jininsa kuma ya motsa yauma hakance ta kasance. Yana ta wajen babban gate ɗin gidan baki ɗaya yaga shigowar Ramadhan. Duk da ya rufe fuskarsa da hular jacket ɗin jikinsa da facemask hakan bai hanashi shaidashi ba. Dan babu wata ɓadda kama da Ramadhan zaiyi bai gane abinsa ba. Shiru yay ransa fal al'ajab, bai gama dawowa hayyacinsa ba kuma sai ga motar su Adda Asmah ta danno kai. hakan ya sashi kiran Anne da Bappi da Yafendo a waya yace suzo dan ALLAH. Shi kuma ya biyo bayan su Addah Asmah ɗin. Takan kowa Pa bebiba tsakanin Aynah da Adda Asmah data zube ƙasa kamar wadda ma ta suma. Yakai ga ɗansa dake jujjuya kansa cikin tafukan hannunsa alamar akwai abunda ke faruwa da shi. A dai-dai nan su Anne ma suka iso, suma duk kan Ramadhan ɗin sukayi hankalinsu tashe. Sai kawai sukaji ya fasa wata gigitacciyar ƙara da duk wanda ke a gidan nan ƙarya yake yace bai jita ba. Innalillahi kawai suke ta ambato, Pa ya riko Ramadhan dake shirin kaiwa ƙasa ya ringumesa a jikinsa. Rawa sosai jikinsa keyi kamar mazari. Hakan yasa Bappi ma tallafawa suka riƙosa. “Basheer kafin attention ɗin kowa ya dawo nan ɗin mu fita da shi”. Shawarar Bappi Pa yabi, suka kama Ramadhan da har yanzu yake faman jujjuya kai sukai waje da shi, fitarsu kamar ƙyaftawar ido jama'ar gidan suka fara tururuwar shigowa falon a gurguje. Su kum ganin Adda Asmah kwance duk sai sukai kanta. Da wannan damar Anne da su Yafendo suka zame jikinsu suka bar falon.

★★ “Ya ALLAHU miya faru? Suma yay?”. Cewar Anne dake shigowa falon Bappi idonta akan Ramadhan da suka shimfiɗar a ƙasan carpet Pa na kokarin shafa masa ruwa. Kai kawai Bappi dake zaune kan Ramadhan ɗin a cinyarsa ya ɗaga mata. Wani nannauyan numfashi Ramadhan ya ja a fisge sai kuma ya sake riƙe kansa zai fasa ƙara Bappi ya rufe masa bakki. “Tabbas akwai matsala, inaga akwai lamarin azzaluman aljanun sihiri tare da shi”. Cewar Yafendo tana kuka. Da sauri Anne ta fita a ɗakin tana faɗin bara ta ɗakko alkur'ani. Bappi na kiranta tazo ta ɗakko na ɗakinsa bama taji ba harta fice. Zaune ta iske Raudha na karatun alkur'ani da alama sallar shafa'i da wutiri ta idar. Ai tama manta da batun bedrest da Raudha keyi ta kamo hanuntan. “Ameenatu taso ga inda ake buƙatar karatun nan naki can.” Hankali tashe Raudha ta dakata, ganin Anne a firgice yasa batabi ba'asi ba ta mike kawi ta bita. Sanye take cikin dogon hijjab fari har ƙasa. Dan haka baka iya ganin komai nata sai fuska da tafukan hannu.........✍

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*

*_Episode. 61-62_*

...........Wani irin tsargawa kanta yay ganin Ramadhan shimfiɗe a ƙasa Bappi ya toshe masa baki, ga Pa a kansa yana karatun suratul baqara. Tuni jikinta ya fara rawa. Ta matsa da sasaarfa takai duke gabansa cikin rufewar idon manta waɗanda suke a falon. “Ya ALLAHU na shiga uku ni Raudha Ya Ramadhan mike faruwa da kai haka?”. “Kinga Ameenatu yi hakuri baya cikin hayyacinsa yi masa karatun kawai”. Ai Bappi baima kai karshe ba ta fara karatun itama cikin suratul baqaran. Wata muguwar zabura ya kara yunkurowa zaiyi saboda masu karatun sun zama biyu, ga zazzaƙar murya da ALLAH ya azurta Raudha da ita inhar tana karatu komai taurin zuciyarka saika nutsu a saurare. Tun sunayi yana fisge-fisge har ya fara lafawa a hankali. “Idan ma mu an koremu ai akwai wanda suke tare da shi tun yana yaro”. Bakin Ramadhan ɗin ya faɗa a kausashe, amma a tabbaci bashi bane sai kuma ya fara sakin tari mai ƙarfi. Raudha da Pa basu dakataba suka cigaba da karatunsu sudai. Yayinda Anne ke duke gabansa tana rike da kansa ita da Bappi. Tsahon mintuna talatin suka sake kwashewa suna karatun kafin jikinsa yayi laƙwas. Duk da hakan Raudha bata dakata ba har sai da takai karshen suratul baqara lokacin agogo ke nuna karfe ɗaya da wasu mintuna na dare.

Ta matuƙar birgesu, sun sake jin kaunarta mai tsanani da taya gudanjininsu murnar samunta matsayin mata uwar ƴaƴansa. Bayan ta rufe da addu'a suka shiga sanya mata albarka. Ita dai kanta a ƙasa tana sharar hawaye. babban burinta tasan miya kawo mijinta gidan a wannan halin? Yama akai yazo? Miya faru da shi?. Waɗan nan sune jerarrun tambayoyin dake mata yawo bisa kai. Sai dai ta kasa furtasu ga kowa. Anne da tasan lokacin barcin Raudhan ya gota cikin sanyin murya tace, “Ameenatu kije ki kwanta kinga kema fama kike da jikinki. Tunda Alhmdllhi da alama komai ya dai-daita barci ne ya ɗaukesa. Kamar Raudha zatace a'a sai kuma tay yunkurin mikewa domin bin umarnin Anne. Caraf taji an ruƙo mata hannu, bama ita kaɗai ba kowa a ɗakin sai da ya kalli hanun Ramadhan ɗin, kafin ya firta. “Ameenatu ruwa! Bani ruwa na sha inajin ƙishi”. A hankali yake maganar amma hakan bai hanasu jinsa ba. Raudha duk kunya ta isheta. Amma saita daure ta dauka goran ruwan dake kusa da Anne, a sanyaye tace, “Ga ruwan to buɗe idonka”. Bakinsa kawai ya buɗe mata yana ɗan girgiza kansa, kamar zata sake magana sai kuma Bappi ya dakatar da ita ta hanyar ɗago kan Ramadhan ɗin yanda zata iya zuba masa ruwan batare da ya cutar da shi ba. Duk da kunyar da takeji haka ta daure ta ɗora masa gorar a baki. Sai ko gashi yana zuƙarsa da yawa harya shanye. A hankali ta janye goran shi kuma ya ɗan buɗe idanunsa yana kallonta. “ALLAH yayi miki albarka”. Ya faɗa a hankali tare da maida idanunsa ya lumshe. Kusan atare duk suka amsa da amin tare da sauke ajiyar zuciya. banda Raudha datai kasa da kanta ta amsa a kan laɓɓa. Bappi ne ya basu umarnin zuwa su kwanta, shi kuma zai kwana da Ramadhan ɗin sugani ko zuwa asuba zai dawo hayyacinsa su samu ya koma can government house kafin a farga. Dan sun tabbatar fitar ɓadda kamar daya sabayice yayo yau ɗin ma.

Badan Raudha taso ba ta mike. Koda suka isa ɗaki Anne wanka ta sakatayi, ta bata tea tasha kamar yanda ta saba turketa a duk dare kafin ta sakata kwanciyar dole. Sai dai ta lumshe idanune kawai badan barcin ba. Amma ita kanta tasan idan tace zatai barci a irin wannan halin yaudarar kanta zatai kawai...

A ɓangaren su gimbiya Su'adah kam kowa tunda baiga Ramadhan ba sai hankalinsa ya karkata akan Addah Asma'a da suka samu a kasa wanwar. Ruwa aka bata tasha, aka kuma dagata zuwa kujera sannan suka shiga mata sannu. Bayan numfashinta yaɗan daidaita Gambiya Su'adah ta sallemsu su duka falon ya rage daga ita sai Adda Asmah da Aynah. “Adda inaga kuje gida zanzo da safe na sameku, dan zamanku yanzu anan akwai matsala zai iya fargar da jama'ar gidan wani abu. Su kuma ku barni dasu game da Ramadhan zanma tufƙar hanci”. Addah Asmah da ba fahimtar komai takeba a yanzu gudun kar gimbiya Su'adah ta ɗagota ta jinjina mata kai ko maganin da suka kawo ɗin bata samu bata ba suka fice cikin taraddadin da ƙaulani. Numfashi gimbiya Su'adah saukewa, kafin ta nufi sashen su Anne. Sai dai tana tu karowa taji sautin karatun Raudha da Pa. Wani irin kunci da duhu zuciyarta ta sake shiga najin tsantsar tsanar Raudha da batasan yaya akai tazo gidanba ya riketa. Tunanin ko dama tare da Ramadhan sukazo ya sata juyawa ta fasa shiga baki ɗaya ta koma sashenta tana haɗiyar zuciyarta data cika kirjinta fam kamar zata fashe.

★_★★____________★★_★

Da asubar fari Bappi ya fita raka Ramadhan government house, kamar yanda ya fita ta barauniyar hanya yanzun ma tanan yabi da taimakon odilan nashi da shi kaɗai dama yasan da fitar. Tunda yaga bai dawo akan lokaci ba hankalinsa yake a tashe. Shi kansa yasan irin waɗannan fitar da shugaban ƙasar keyi akwai haɗari a cikinta. Sai dai shi ko'a jikinsa. Ko'an nuna masa illar fitar ɓadda kamar baya nuna damuwa ko hango wata matsala. Amma har cikin rai odilan ɗin nasa na tsoron randa wani zai farga a cikin gidan ko waje.

A taura house kam koda aka wayi gari babu wanda ya tada zancen. Musamman daga sashen Anne. Ita kanta gimbiya Su'adah tana son ma Pa magana tanajin tsoron a yanda ya tashi yau fuska kamar hadarin gabas. Amma har cikin rai tana buƙatar jin halin da yaronta ke ciki. Ta kira wayarsa amma ba'a ɗaga ba, ta rasa inda zata tsoma ranta ta huta har baƙi dai suka fara isowa irin su Safina da tawagar ƴaƴanta. Sai daga masarautar Bina kuma. Zuwa Azhar gidan ya fara ɗaukar baƙi sosai. Hakan ne ya tilasta Gimbiya Su'adah fasa fita gidan Addah Asmah dan tun jiya da suka bar gidan bataji daga garesu ba. Ta kira duk wayoyinsu a kashe. Ta aika Muneera ta dawo ta sanar mata Aynah da Addah basa gida wai tun safe suka fita baƙi ma daketa isowa babu wanda ya samesu a gidan sai ma'aitan gidan keta saukesu. Wannan zance ya sake tada hankalin gimbiya Su'adah matuƙa dan haka ta kira fulani da suke shirin tahowa da yamma ta sanar mata. Duk da fulani tasan komai sai ta ɓoye mata akan ta kwantar da hankalinta zata bincika. Amma tasan Addah Asmahn bazataje wani waje ba daban. A sanyaye tace to. Fulani ta sauke wayar tana taɓe baki. Dan yanzu sun ƙudiri aniyar daina faɗa gimbiya Su'adah komai akan shirinsu. A ganinsu sakacintane ya lalata komai a daren jiya kokuma akwai abinda take son gujemawa. Itako fulani burinta da alwashinta sai ta nunama Anne ba itace kaɗai keda iko da Ramadhan ba, yayinda Addah Asmah ke nuna itama shine burin nata. Sai dai acan kasan rai ba haka bane. Baƙar hassadar ƴar uwartace kawai ke cinta akan ta fita komai na rayuwa. A ganinta mallakar Ramadhan matsayin mijin ƴarta, zaisa abinda Gimbiya Su'adah ke takama da tinƙaho da shi ya dawo tafin hanunta ƙarƙashin ikonta. Faruwar komai a jiya yasa Aynah kwana kuka akan bazata iya haƙuri da Ramadhan ba a yanzu. Ita duk ma yanda za'ai ayi ƙoƙarin gyara matsalar nan da suka tabbatar komai ya watse. Wannan shine dalilinsu na tafiya gidan boka bayan tun dare sun kirashi yanata faɗa akan abinda tunkan su sanar masa yace musu ya sani tunda aljanin daya turama Ramadhan yaci ubansa hanun Raudha da Pa da ayar ALLAH. Tun tafiyar da sukai da asubahin nan suna can har yanzu anata sake tsumo Aynah da shaiɗanci kala-kala akan Ramadhan kawai....

To bara muga wazaiyi winning anan kuma🚶🏻🤕.

*_____________________________*

Ƙarfe biyar na yamma dai-dai tawagar shugaban ƙasa Ramadhan ta iso Taura house bisa rakkiyar jami'an tsaro da wasu na jikinsa. Kamar wancan hutun tako ina anguwar ta zama ƙarƙashin mulkin mallakar jami'an tsaro ne. Sauƙin ma dama can anguwar manyace bawai hayaniya ko yawan shigi da fici ake samu ba. Sai dai abin ya shafi masu tururuwar zuwa biki. Dan duk waɗanda suka iso yau dasunci karo da jami'an tsaron nan sai tsoro ya kamasu duk da sunsan yanzu Taura house yana da wani sabon girma bayan wanda kowa yasan gidan da shi. Babu wanda yaga Ramadhan, domin motar da yake ciki har jikin ƙofar falon Bappi ta baya aka kaita, yana fita kuma ya shige ciki abinsa.

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull