Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 31

Bakar inuwa book 1 - Chapter 31

Bakar inuwa book 1 Chapter 31: Bakar inuwa book 1 Chapter 31. Raudha na bedroom ɗin Anne kwance ta gama ƙwallar shan kunu da Annen ta tsareta tayi Bilkisu…

4,475 words

Raudha na bedroom ɗin Anne kwance ta gama ƙwallar shan kunu da Annen ta tsareta tayi Bilkisu ta shigo ɗakin da sallama. Wayar ta dake hanunta tana game ta ajiye, dan dama game ɗin kawai takeyi amma hankalinta naga mijinta da tunanin miyake ciki yanzun? Yana ina? Jikinsa da sauƙi ko babu?. “Sai a daina mana shagwaɓa ga boss nan ya iso”. Bilkisu daba sanin abinda ya faru da Ramadhan ɗin tai jiya ba ta faɗa tana dariya bayan takai zaune kusa da Raudha. Murmushi kawai Raudha tayi da faɗin, “Kai aunty ni shagwaɓar mi nayi?”. “Ai ba abun jayayya bane bara na lissafa miki yanzu kuwa ɗaya bayan ɗaya ta Brothe......” Ta kasa karasawa saboda wanda ya shigo ɗakin. Da farko tsoro taji sosai ita kanta Bilkisun, sai dai yanda taga yanayinsa kamar a sanyaye ya sata ɗan sassautawa ta gaisheshi zata mike. Sai dai Raudha tai saurin riƙo hanunta idanunta na cika da ƙwalla. Sosai yanzu tsoronsa takeji, tsoro mai tsanani dan ita kaɗai tasan azabar da taci a hanunsa har sau biyu da bazata taɓa iya mantawa ba. Raunanannun idanunsa ya sauke akan hannayen da Raudhan ta sarƙe. Sai yaji wani irin tausayinta mai tsanani yana dirar masa daga tsakkiyar kai har tafin kafa. Da ido yayma Bilkisu alamar ta fita. Dan haka tai saurin son zame hanunta cikin dabara tana faɗin, “Aunty Raudha bara na dawo tanan sai Yaya ya zauna nan”. Sam Raudha bata yarda ba, saita ƙara ƙwaɓe fuska zatai kuka. Bilkisu da ita kanta tausayinta takeji tunda batasan ko yayan nasu bai dawo cikin hankalinsaba har yanzu ta zame hanunta ta gudu. Sosai jikin Raudha ya fara rawa ganin ya maida ƙofar ya kulle harda key. Babu shiri ta miƙe a kan gadon tana ƙoƙarin sakkowa. Sosai tayi ƙiba, tako'ina komai yayi zam, damma doguwar rigar jallabiyace a jikin nata baƙa. A hankali ya lumshe idanunsa tare da harɗe hannayensa duka a ƙirjinsa, sai kuma ya sake buɗesu ya zuba mata. Yanda take rawar jiki yasa ko'ina nata ke motsawa, ga rigar mai santsi ce, sai hakan ya ƙara taimakawa wajen motsawar jikin nata. Murmushin takaici da tausayin kansu ya saki. Baiga laifinta ba, dan yasan dolene taji irin wannan tsoron nasa. Ya ɗan furzar na numfashi tare da warware hannayensa daga ƙirji ya fara takowa gareta cike da nutsuwarsa da kasalar yanayin rashin jin daɗi da yake a ciki........✍

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_YADDA ZAKA SIYA LITTAFI A AREWABOOKS_*👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾

*Recharge* - inda ake shiga domin saka kudi cikin account.

*Balance* - Zai nuna kudin account dinku da zaku iya sayayyan littafai cikin kasuwar ArewaBooks.

*Credit/Debit Card* - Hanyar farko kuma mai dadi wajan Recharge din account dinku.

A inda (Enter your amount) za'a saka kudin da akeson Recharge din sai a taba "Proceed". Zaibude muku inda zaku saka bayanan katin banki, kuna gamawa kudinku zaishiga account dinku kaitsaye (instant).

--------

Akwai wasu hanyoyin saka kudi a ArewaBooks account kamar:

*Bank Transfer* *Airtime Transfer*

Saidai su ba kaitsaye bane (instantly) sai ArewaBooks ta tabbatar da Transfer din, amman bayakai 1hour za'a gansa a Balance.

*Bank Transfer* - kamar yadda akwai bayani a sama da kuma account number ArewaBooks.

_Account No_ - *1220077999* _Account Name_ - *Arewa Books Publishers* _Bank_ - *Zenith Bank*

Bayan anyi Transfer dinne sai a cike wannan Form din:

Amount Paid: - Nawa aka tura?

Name used for transfer: - sunan da aka saka wajan turowa

Transferred time: - lokacin da aka turo

Name of bank: - sunan bankin da aka turo dashi

Deposit date: - ranar da aka turo

Sai ayi SUBMIT.

*Airtime Transfer* - muna bada shawaran ayi amfani da *Debit Card* kokuma *Bank Transfer* akan *Airtime Transfer* , amma idan yakama babu mafita saishi tau muna amsar:

MTN, 9Mobile Glo Airtel

Amma kamar yadda akayi rubutu a sama afara tuntubar ArewaBooks a WhatsApp domin akwai percent da ake cirewa na canji(convert) kafin kudinka yashiga Balance.

*WANNAN SHINE BAYANAN*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*

*_Episode 63-64_*

...........Ƙasa takai durƙushe cikin rawar jiki. Ta haɗe hannayenta waje guda alamar roƙo. “Ya Ramadhan dan girman ALLAH kayi haƙuri, na tuba kar kayi zan iya mutuwa yau. Wlhy wajen har yanzu yana ciwo”. Kasa jurewa yay, sai da ƙwalla suka taru masa a ido. Matarsa ta sunna ke tsoronsa saboda yaje gareta tamkar karen farauta. Ya kusanceta tamar babu zuciya a ƙirjinsa. Maimakon abinda Raudha tai tunanin sai taga saɓanin hakan. Dan shima gabanta yakai durƙushe. Ya ɗora duka hannayensa kan nata ya riƙe. “I'm vary sorry Ameenatu ki gafarceni dan ALLAH”. Ya faɗa cikin wata iriyar murya mai tsananin rauni da rawa. Da sauri Raudha ta buɗe idanunta dake rufe, danjin furucinsa da sautin muryarsa. Sosai ƙirjinta ya buga ganin hawaye a fuskar mijinta. Sai ta sake fashewa da kuka tana girgiza masa kanta. “Dan ALLAH Ya Ramadhan kabar kuka”. Hanunsa dake cikin nata ya riko, ya jawota ta faɗa jikinsa, sai kawai suka saki kukan a tare abin tausayi. Tsahon mintuna uku suna a haka. Kafin Raudha ta ɗago tana share hawayenta tana magana. “Kaga dan ALLAH kabar kukan Abokina. Kaga nima na daina. Kuma ni ban taɓa rikekaba dama na yafe maka. Kai harma wanda zakamin a gaba na yafe maka Ya Ramadhan. Dan ALLAH ka daina kuka kar wani ya shigo, idan wani ya ganka a haka bazan yafema kaina ba”. Ta ƙare maganar tana kai hannayenta saman fuskarsa ta shiga share masa nasa hawayen. Murmushi yay mata, wani irin kaunarta na ratsashi. Ya riƙo hannayen nata da take share hawayensa ya sumbata. Idanunta ta lumshe a hankali, saƙonsa na ratsa mata jini da ɓargo. Ciki disashiyar muryarsa yace, “Ustazah!”. Idanun ta buɗe a hankali tana kallonsa. Ya kafeta da nashi dake cikin yanayin shauƙi da bege. *_“I love you!. Am serious I love you more than you can ever comprehend. Kinada muhimmanci a duniyata. Ina miki irin son da bayan mahaifiyata da Anne ban taɓa yima wata mace a duniya ba sai ke. Bazance miki ban taɓa so ba, sai dai inajin naki daban. Ga Ramadhan nan Ameenatu, Ramadhan B. Hameed Taura ya mallaka miki kansa da duk abinda yake nasa sai yanda kikai da shi, dan ALLAH karkici amana, karkiyi butulci, karkiyi amfani da wannan soyayya da dama ki cutar da shi......”_* Gaba ɗaya jikin Raudha rawa yakeyi, gaba daya ya kashe mata jiki, ya sakata cikin taradadadi da kaulani. Ta fashe masa da wani irin sassanyan kuka mai tsuma zuciya. “Nima ina sonka Ya Ramadhan, ina ƙaunarka da iya gaskiyata. Insha ALLAH bazan taɓa cutar da ko dabban Taura family ba balle kai. Har abada ko wanda zai ci amanarka bazan barsaba ma balle ni kaina. Ina fatan ko mutuwa ta ɗaukemu rana ɗaya, lokaci ɗaya, mu zama maƙwaftan juna a kabari sannan mu kasance ma'aurata a aljanna.....” Fuskarta ya kamo cikin tafukan hanunsa ya haɗe goshinsu, sai kuma ya manna lips nashi akan nata tare da rungumeta a jikinsa.

Da sauri Anne da Bappi dake tsaye jikin window suna kallonsu suka ɗauke kansu. Anne tasa hannu ta share hawayen da suke saukar mata a fuska na ɗunbin tausayin waɗan nan ma'aurata. Tun fitowar Ramadhan daga falon Bappi Anne ta biyosa da shirin dakatar da shi, dan ta ɗauki aniyar saita wanashi akan Raudha. Biyota Bappi yay da hanzari shima da zummar dakatar da ita, sai dai tana ƙoƙarin gitta window ɗin ɗakin nata dake tabayan sashen Bappin ta tsinkayi roƙon da Raudha kema Ramadhan. Cak ta tsaya, a kuma dai-dai nan Bappi ma ya iso, ganin taja birki shima yaja ya kai dubansa ga abinda take kallo. Wannan yasa komai dake wakana a kan idonsu ne akuma kan kunnuwansu. Hannunta Bappi ya kama suka bar wajen.

“I need you Please”. Ya faɗa murya a sarƙe lokacin da yake janye lips nasa daga kan nata. kai ta shiga jujjuya masa cikin tashin hankali, har hawaye sun sake cika mata idanu. “Please Ya Ramadhan forgive me wlhy akwai ciwo”. Da ƙyar ya iya rumtse idanunsa da suka kaɗa sukai jajur, dan tabbas bukatarta yake mai tsanani, bakuma zaiso cutar da ita ba. Amma dole ya samawa kansa mafita ba kuma a ɗakin Annensa ba, dan akwai kunya a raka baƙo ya ruga... “Shike nan naji, amma muje zan duba naga ɓarnar da nayi dan ALLAH”. Yay maganar a wani irin marairaicewa kamar bashi ba. Zatai magana itama ya girgiza mata kai tare da ɗora hanunsa kan lips nata alamar kartace komai. Dole tai shiru, ga tsoro ga fargaba. Haka ya kamata ya miƙar, batare daya bata damar cewa komai ba ya kama hanunta suka fito. Addu'a take a ranta ALLAH yasa babu kowa a falon, duk da tasan dai ta inda zasu ratsa ɗin ba falon da kowa ke iya shigowa bane sai iya ahalin gidan kawai. Ta ɗanji sanyi da basu haɗu da kowa ba, sai dai mai aikin Anne dake ƙoƙarin shirya abincin dare a dining. Koda suka fito kam kasa tai da kanta tana gaida Ramadhan ɗin. Hannu kawai ya iya ɗaga mata suka wuce, dan yasan inhar yay magana kai tsaye za'a gane yanayin da yake ciki. Ko'ina ƙal yake a sashen nasa. Sai ma kamshi na musamman dake tashi dan Bilkisu da Basma ne sukai bautar gyaransa. Suna shigowa cikin ɗar-ɗar Raudha tace zanyi fitsari dan ALLAH. Sakar mata hannu yay kawai batare da yace komaiba. Sai ma ƙoƙarin rage babbar rigar shaddar jikinsa yake. Babu wani fitsari da zatayi, tayi hakane danta kuɓutar da kanta daga garesa. Sai dai tasan hakan bamai yuwuwa bane. Amma tanada tabbacin yace zaiyi wani abu yanzu ɗinkin jikinta zai farke ne. Bayan kuma Dr Hauwa ta mata gargaɗi matuƙa akan ta kiyaye ta kuma kula sosai, shiyyasa Anne ke tsaye kanta kullum sau uku take shiga ruwan zafi. Jin sautin kiran salla ya sata lumshe ido daɗi na matuƙar ratsata. ALLAH ya kawo mafita kenan. Jin kamar ana taɓa ƙofar tai saurin fara alwala. Kallonta kawai ya tsayayi sai kuma yay murmushi. “Duk dai wayon Amarya Ustazah...” Baki ta tura gaba lokacin da take ɗagowa bayan kammala alwalar, “Toni wane wayo nayi”. Tai maganar da kauda idonta a kansa dan ya cire har ƴar cikin da ga shi sai wandon shaddar da singlet baka. “A'a ni minace kuma. Kefa daɗina dake fassara bawa a mizanin da bai kai ba. Ke dai jirani nai alwala kawai”. Gwalo ta masa batare da tunanin ya ganta ta mirror ba. Sai dai yay shiru kawai dariya na cinsa a ciki. Bayan ya kammala suka fito, shine yay musu jam'i, dan duk nasihar datai masa akan zuwa massallaci nunawa yay ai lalura ce zata hanashi. Tasan ya bijirene kawai dan son ransa. Amma badan baisan hakan ba. Bayan sun idar ta ɗauka alkur'ani zata fara karatu ya riƙe. “K ALLAH inaga zare miki ido zan komayi maybe zaki fara tsorona. Mai kan kwakwa kawai”. Ya kare maganar da mangare mata kai. Fuska ta kwaɓe tana shafa wajen. “Ni gasky ban yarda ba”. Cikin ɗage gira yace, “Ko? To zoki rama mana”. Tashin kuwa tai ta bisa, yana ajiye Alkur'anin zai ɗago ta bashi mintsini mai shegen zafi a damtsen hanunsa. “Kamm lalai yarinyar nan kinci abinci, ni kikama wannan muguntar?”. Dariya ta ƙyalƙyale da shi tana ƙoƙarin kwasa da gudu yay tsalle ɗaya ya cafkota. Jikinta ta fara fisga tana haɗiye dariyar dake cinta amma ina tazo hannu, gaba ɗayanta ya dauka cak yay kan sofa da ita. Duk yanda take watsal-watsal da ƙafafu bai saurareta ba. Sai ma dariya da yake mata harya direta. “Rama cuta ga macuci ai ibada ne yarinya”. Yay maganar da kwashe hijjabinta gaba daya ya ajiye. Hannayenta dake kai masa ƙananun duka a ƙirji ya riƙe tare da kwantowa kanta, sai dai bai sakar mata nauyinsa ba. Cikin ƙanƙanin lokaci ya ladabtar da zille-zillenta ta nutsu tana amsar saƙonsa. Sai dai acan kasan ranta a matukar tsorace take. Sai da ya tabbatar tayi laushi ya nema bin hanayar da take tsoro ta fara masa kuka da magiya. Dama ba zuwan zai ba. Amma ya tabbatar mata zai ƙyaleta idan tai masa abinda yace. Ko musu babu kuwa ta amince. Dan gwara hakan ita dai da abinda takewa tsoron.......

Luf take shiru a jikinsa tana sauraren yanda yake sauke numfashi a hankali da sanya mata albarka. Yayinda hanunsa ke cikin sumar kanta yana faman wasa da ita duk ya birkita mata ita. Murya can kasa a ɗashe tace, “Ya Ramadhan sallar isha'i fa akeyi”. “Uhhm naji ai”. Ya faɗa a shaƙe idanunsa rufe. Shiru tai bata sake cewa komai ba har kusan mintuna biyar sannan ya miƙe. Kai tsaye toilet ya shiga, hakan yasa Raudha lumshe idanu da sauke ajiyar zuciya takai hanunta saman cikinta tana shafawa. Bata san yaya zaijiba idan yasan tanada ciki, ita kanta a duk sanda ta tuna akwai ɗa mai alaka da shi tanajin tsantsar farin ciki. Badan shi shugaban kasa bane, badan shi jinin Taura family bane. Sai dai ɗunbin soyayyarta da take hangowa a cikin idanunsa. Motsin fitowarsa a bayin ya sata dawowa hayyacinta daga dogon tunanin data lula. Yanda ya fito yana goge sumarsa da jiki ya tabbatar mata wanka yayo, saurin ɗauke kanta tai ta maida gefe. Yay ɗan murmushi da ƙarasawa jikin Wadrobe ɗinsa domin duba kaya. “Madam tashi kiyi wanka muyi salla”. “Ni alwala kawai zanyi”. Ta faɗa a shagwaɓe tana mikewa a gadon itama. Murmushi kawai yayi amma komai baiceba harta shige toilet. Sai dai kuma ashe cika bakinne kawai, dan itama dai hummm kawai............✍

*_Alhmdllhi barka da salla, ALLAH ya maimaita mana ya amshi ibadunmu baki ɗaya. ALLAH ya dawo mana da mahajjatanmu gida lfy, ya jiƙan iyayenmu, ya ƙara mana lafiya da zama lafiya. Inama kowa barka da salla ina kuma jiran naman salla dan nagafa sai nayi tuni za'a kawon kenan🤕👩🏻‍🦯_*.

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*

*_Episode 65-66_*

...........Fitowarta dai-dai da ƙoƙarinsa na kammala busar da sumarsa. Ya kalleta kawai ya ɗauke kansa baice komaiba. Dan rigartace dai a jikinta data shiga da ita ala dole babu abinda tayo. Sai da ya shimfiɗa abin salla ya miƙa mata wandonsa mai taushi na adidas da farar t-shirt. “Saka muyi salla lokaci na shigewa”. Kanta a kasa batare data kallesa ba tace, “Bafa abinda ya sameta”. “Humm Ameenatu kenan, karki manta na rigaki zuwa duniya. Bayan rigaki shekaru kusan goma sha takwas na baki, kinga a lissafi kuwa lokacin da nake a mizanin shiga shekarun girma na ɗa namiji aka haifeki”. Kunya kamar ta nutse. Dan sam batai tunanin ya ganeba. Dama sotai ta masa dabara sai sun tada sallar ta gudu ɗakin Anne ta canja kayan tai salla. “Hallo! Ko sai na nuna miki shaida ne dan rigar kanta ta tona miki asiri tare da wannan”. Ya tura hanunsa cikin hular kanta ya jawo silin jiƙaƙƙen gashinta a ciki. Da sauri ta kwashi kayan zata koma toilet”. “Hii aini ba surukinki bane canjasu anan konazo na canja miki kina ƙara makarar damu”. Babu yanda ta iya dole tabi umarninsa, bayan ta saka kayan suka gabatar da sallar. Suna idarwa wayarsa ta hau ruri, yasan Anne ce dan haka ya miƙe zuwa bedside drawer ya zauna a bakin gadon yana daukar wayar.... “Kai ka fita idona kawomin yarinya taci abinci tana fama da kanta”. (Mutum da matarsa ƙarfin hali kenan) ya faɗa a zuciya yana sakin murmushi. A fili kam yace, “Okay Gimbiyar Bappi yanzu kuwa maida wukar”.

★Gaba ɗaya Raudha jitake kamar ta nutse dan kunya. Kanta a kasa ta risina ta gaida Anne da Bappi. Zata zauna kusa da Bilkisu dake tare da su yaja mata kujerar kusa da shi tare da kamo hanunta yanda su Bappi bazasu gani ba. Sai dai ya makaro sun gani ɗin. A kuma kallo ɗaya Anne ta fahimci wayo yaje yayma Raudha, sai dai addu'arta ALLAH yasa bai aikata abinda zai cutar da itaba tunda ɗinkin jikinta bai gama warkewaba. Tunda tazo ɗaki taga babu su tai niyyar kiransa a waya Bappi ya hanata. Acewarsa yasan Ramadhan na cikin hankalinsa bazai sake yarda ya aikata abinda zai cutar da Raudha ba. Gara su barsu su sasanta kansu da wuri kodan su Gimbiya Su'adah ma. Bilkisu ce ta zuba musu abincin, dan Raudha dai ta kasa motsin kirki. Gani take kamar su Anne sun fahimci abinda duk ya faru tunda har abu yakai ga canja kaya. Kowa nacin abincinsa hankali kwance amma banda ita. Tsakura kawai take kaɗan-kaɗan. “ALLAH in bakici abincin nan ba zan tonaki yanzu su Anne susan mikika aikato a ciki da hujja”. Wani irin ƙululu cikinta ya bada. Harta kasa daurewa saida ta ɗan dubesa. Gira ɗaya ya ɗage mata da sakin wani munafukin murmushi daya tilastata maida kanta ƙasa da hanzari. Duk abinda suke su Anne na lure da su, sai dai kowa ya ɗauke kansa kamar bai san anaiba. Farfesun kan rago Ramadhan yace Bilkisu ta zuba masa. Kamar jira tana buɗe bowl ɗin Raudha tai saurin toshe hanci da rike numfashinta. Babu wanda ya lura da hakan Bilkisu ta fara zubawa, kasancewar kusa da shi take tuni ƙamshin ya ƙara karfi a kusa da ita. Har takai amai na yunƙuro mata. Ta mike zaram zata bar wajen ya rikota. “Lafiya kuwa?”. Kanta ta shiga girgiza masa da nuna masa ya saketa amma yaƙi. Anne ce ta fahimci abinda ya ɗaga hankalin Raudhan da sauri tace, “Ramadhan saketa”. Tai maganar tana mikewa. Sam ya kasa fahimta, a zatonsa wani abune daban, ina kafin ya samu damar cewa wani abu ta kasa daurewa ta fisgi hanunta da ƙarfi. Sai dai kafin takai toilet na bayin ta saki aman a waje. Gaba ɗayansu sukayi kanta har Bappi, dama Ramadhan tunda ta fisge ya bita. Amai sosai takeyi a wahale. Shiko gaba ɗaya ya cimimiyota jikinsa duk a ruɗe. Sai tambayarta yake mike damunta?. “Ramadhan ka barta taji da abinda ya dameta mana Please”. Anne ta faɗa cike da tausayin Raudha. Sai da ya tabbatar ta gama ya ɗagata cak ya nufi sashensa da ita. Anne zata bisu Bappi ya riƙo hanunta yana girgiza mata kai da murmushi a fuskarsa. “Barshi shi daya jawo yay aikin”. Murmushi kawai tai da girgiza kai tana mintsininsa da nuna masa Bilkiau da ido. Yay karamar dariya da ita kawai tajisa. Mai aikin Anne ce tazo ta gyara wajen. Su kuma suka koma kan table suna karasa cin abincinsu kowa da tausayin Raudha a ransa

Bayan kamar mintuna goma sha biyar Ramadhan ya fito, a lokacin sun bar dining sun koma falo. “Yaya jikin nata?”. Bappi ya tambaya cike da kulawa. Cikin damuwa Ramadhan daya koma duk wani kalar tausayi yace, “Bappi na barota kwance zan sama mata wani abincin a kuma kira Momyn Jabeer”. “No kiran Mommyn Jabeer ba shine mafitaba ai. Da alama kamshin naman kan canne bataso. Taci abinci saita kwanta ta huta ALLAH ya raba lafiya”. Wani irin yarrr yaji har saman kansa. Cikin rawar harshe yace, “Anne ban gane ba?”. Hannu Bappi ya mika masa da faɗin, “Ajiye goro na ganar da kai”. Ganin Bappi a serious sosai Ramadhan yay ƴar dariya yana shafa aljihu. Sai dai babu komai a ciki, hatta wayoyinsa na ɗaki. “Bappi na maka alƙawarin baka koma mi kakeso faɗi dan ALLAH”. “Tabb ai an daina aikin banza a NAYA kai dai ajiye kasha labaru”. Rasa mima zaiyi yay, sai kawai ya kwanto agogon hanunsa ya ɗora a hanun Bappin. Bappi ya ɗan juya agogon, sai kuma ya taɓe baki. “Ba laifi mai nauyine ai. Bilkisu bashi yasha”. Bilkisu dake dariya cike da ɗoki ta nufi Yayan nata tayi ɗan hugging nashi, sai kuma ta sakeshi. “Yaya na kusa zama Mummyne fa, Aunty nada cikin wata biyu da kwanaki....” “What?!!!”. Ai kafinma ta ƙarasa bayani ya juya da sauri ya bar wajen zuwa sashensa. “Na yafe miki sauran labarin”. Ya faɗa yana ɗago hannu sanda yake gab da shiga. Mi su Anne zasuyi inba dariya ba. Pa dake tsaye tun ɗazu batare da sun sani ba yay murmushi kawai yana girgiza kansa. Ɗansa kenan abin alfaharinsa. Murɗaɗɗen mai wahalar fahimta ga wanda ke nesa da shi. Da yawan mutane akace musu Ramadhan mai sauƙin kaine a cikin gida zasu karyata. Domin shi mutumne mai yanyin mutanen da ake kira da girman kai kai tsaye. Dan kuwa tabbas magana ma sai yaso da wanda yay niyya yakeyinta. Dariya ko mutane da yawa kance basu taɓa gani daga garesa ba. Dan akan jima baiyi hakan ba sai a inda yaso. Sai dai ga wanda yaso kuma ya aminta shi mai sauƙin kaine da iya mu'amula matuƙa.

Cikin ɗan barcin daya fara figarta kawai taji an rungumeta. Tare da fara bata zafafan kiss's tako ina da ina a jikinta. “Ya Ramadhan lafiya?”. Raudha ta faɗa a kasalance dan da gaske barci ya fara ɗaukarta. Bai bata amsa ba. Sai rungumeta da yay tsam a jikinsa yana jero addu'ar nan ga wanda abin farin ciki ya sama. *الْحَمْدُ للهِ الَّذِي بِنِعْمَتِهِ تَتِمُّ الصَّالِحَاتِ .* *_Alhamdu lillahil-lazee bini’imatihi tatimmus-salihat._* _Godiya ta tabbata ga ALLAH wanda saboda ni'imarsa ce kyawawan ayyuka suke cika._ *اَلْحَمْدُ ِللهِ عَلَى كُلِّ حَالٍ.* *_Alhamdulillahi ala kulli halin_* _Godiya ta tabbata ga ALLAH a cikin kowane hali._ Rigar dake jikinta ya ɗaga nanma yana sumbatar cikinta. Kafin ya kwantar da kansa akai wasu hawaye na tuna Haseenah na sakko masa. Ashe bayan Haseenah yana da rabon sake haihuwar ƙanen a duniya. Ɗagowa yay ya sake sumbatar cikin, sai kuma ya fara karanto addu'ar nemawa ƴaƴa tsari (iyaye dan ALLAH a dingayi, kai ko yaron cikine dake karanta ki shafe cikinki kafin ya fito ki ɗora dayi masa a zahiri😘😢. Domin kuwa MANZON ALLAH tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, ya kasance yana nema wa Hassan da Husain tsari da wannan addu'ar: ). *أُعِيذُكُمَا بِكَلِمَاتِ اللهِ التَّامَّة، مِنْ كُلِّ شَيْطَانٍ وَهَامَّةٍ، وَمِنْ كُلِّ عَيْنٍ لاَمَّةٍ.* *_O'eezukuma bikalimatil-lahit-tammah, min kulli shaytanin wahammah, wamin kulli 'aynin lammah._* _Ina neman muku tsari da kalmomin ALLAH cikakku daga dukkan shaiɗan da wata dabba mai dafi, da kuma dukkan wani mai kambun baka, mai cutarwa_. Raudha dake murmushi takai hannu ta shafa kansa. “Irin wannan security ba ɗaga ƙafa haka?”. Tasowa yay gareta shima fuskar tasa da murmushi, ya kwanta kusa da ita tare da tokare kansa da hanunsa ya lakace mata hanci. “Uhmm barni gara na tofe abina tun yanzu kodan masu ƙarancin tsoron ALLAH. Yanzu nan Baby Luv kinsan da wannan abin farin cikin tun ɗazu kikaƙi sanarmin? Anya kuwa kina sona?”. Dariya tayi tana mai saka tafukan hanunta ta rufe fuska. “Kai Ya Ramadhan kawai kuma saina kama faɗama inada cikin ɗan fari dan banda kunya”. “Lallaima yarinyar nan”. Ya faɗa shima yana dariya da son zame hanunta. Ƙin yarda tayi, sai ma juyowa datai da sauri ta sinne kanta a ƙirjinsa. Idanu ya lumshe a hankali tare da rungumota ya kanƙame ta shima. ji yake kamar ya haɗiyeta kawai ya huta. “I love you sweetheart”. “I love you too Noorullah”. “Nice name dear I love more. Na huta an daina kaƙabamin Yaya babu dangin gabas babu na yamma. Dolene yau nayi celebrations biyu kenan”. Siririyar dariya ta saki tana mai ɗagowa ta sumbaci lips nasa ta sake maida kanta ta kudindine a jikinsa. “Hummm wlhy yarinya ki bani kwana uku kacal saina maidaki mara kunya ta bugawa a jaridar duniya”. Yay maganar yana mai rungumeta sosai a jikinsa murmushi yaki barin fuskarsa. Babu wanda ya karajin ɗuriyar Ramadhan da Raudha a gidan, kuma babu wanda ya nemesu. Garama ya kira Bilkisu daga baya ta kawoma Raudha sabon abinci taci ya busar mata da gashinta daga nan sukai kwanciyarsu............✍

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull