Bakar inuwa book 1 - Chapter 34
Bakar inuwa book 1 Chapter 34: Bakar inuwa book 1 Chapter 34. ★Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai babu ɓata lokaci Pa ya tunkari Anne…
4,478 words
★Kamar da wasa ƙaramar magana ta zama babba. Dan kuwa dai babu ɓata lokaci Pa ya tunkari Anne da Bappi da maganar. Sunji daɗi sun kumayi farin ciki, dan haka Bappi yace yabar komai a hanunsa. A ɓangaren Bappi ma bai tsaya jan al'amarin ba ya tunkari su Hajiyar Birni da shi, sai dai kamar yanda yay hasashe Asabe ta nuna bijirewa su Hajiyar Birni sukai mata can. Murmushi kawai Bappi yayi, tare da basu shawarar su barta tayi tunani, amma ta bama Alhaji Sageer Dogarai ɗin damar zuwa gareta tukunna sai ta yanke hukunci. Ta aminta da hakan, babu kuma ɓata lokaci Alhaji Sageer yazo gareta washe gari. Mutum ne kamilalle kuma mai tarin nutsuwa. Ba wani tsufa yayba dan shekarun nasa bazasu gaza dai-dai da Pa ba, ga iya magana dan a ƙankanin lokaci ya siye zuciyar Asabe har taji ta gamsu da shi. Sai dai bata amsa masa ba sai da ta garashi sosai. Shiko bai gajiya da binta ba har sai da ya samu amincewarta. Hajiyar birni kam ai likafa taci gaba burikanta nata tabbata bayan wahalar da taci a rayuwa da garari akansu. Wani lokacin bawa nayin gaggawa ne akan abinda baida masinaiyar UBANGIJI ya tanadesa cikin ƙaddararsa. Sai son zuciya ta sakashi tsayawa wajen nemansa koda ta hanyar data saɓama shari'a ne. Sai kaga yazo ya samu abin kuma daga baya. Alhaji Sageer ya matsa shifa ayi aurenau kafin nasu Fatisa. Itako ta dage akan a'a sai anyi nasu Fatisa. Bai haƙura ba ya cigaba da jajircewa har hajiyar birni ta tabbatar masa yanda yakeso haka za'ai. Sam Asabe bataso hakanba. Sai dai bata ƙaunar yima mahaifiyarta jayya ko kaɗan, sannan Aunty Halima na ɗorata akan shawarar ƙwarai na gara tai auren ko bikin ƴaƴan nata ya ƙara mutunci a idon mazajensu da al'ummar da zasu halarci bikin. Tasan gaskiya Aunty Halima ta faɗa mata, dan haka ta tara yaranta ta sanar musu Raudha kuma aka faɗa mata ta waya. Kamar yanda su Fatisa suka nuna kishin Abbansu a fili haka ma Raudha. Dan kuka ta dinga rusawa akan ita bata yarda Mummyn nasu ta sake aure ba. Shi dai Ramadhan ma da yaji tushen kuka. tagumi ma kawai yay yana kallonta. Sai da tayi mai isarta sannan yay magana. “Oh ni Ramadhana naga takaina. Ni karma a haifamin yara masu kukannan fa? Yanzu ke Partner dan ALLAH ba abin farin ciki bane Mummy tai aure? Kinada ilimin addini fa, kin kuma san babu sauran aure tsakaninta da Abba taya zata cigaba da zama kuma a haka bayan har yanzu shekarunta basuyi nisan da hakan zai kasance ba”. Baki ta tura gaba da juya masa baya zata kwanta ribda ciki ya riƙota. “K rufamin asiri, da wannan cikin zakiyi wannan kwanciyar?, ga Abba ya samu mai tayasa kishi ni ki halakamin nawa.” Dama ba kwanciyar zatai ba. Dan yay magana tai hakan, ta sake tura baki da buge hanunsa dake riƙe da cikinta daya sake fitowa sosai yanzu kowama zai iya shaida akwaishi. “Ni dai yi haƙuri karki cinyeni da baki, yarana suzo suga an gama gwaguyeni”. Filo ta ɗauka ta shiga kai masa duka yana karewa da dariya, sai kuma ta mike daga gadon ta sauka tana daddaga kafa. Saurin riƙota yay ya zaunar a cinyarsa. Zata ɓare masa da kuka ya ɗaura lips nashi kan nata daga haka labarin ya canja. Bai bartaba sai da ya tabbatar dukkan damuwarta ta gudu sannan suka shiga toilet suka tsarkake kansu tare. Bayan sun fitoma nasiha ya dunga mata har sai da ta fahimcesa ta sakama auren albarka. Suka kuma kira Asabe tare suka gaisheta da nuna mata goyen bayansu dan yanzu dama Ramadhan kanyi waya da Asabe da M. Dauda lokaci-lokaci. Hakanne ya ɗan ƙara sakama Asaben nutsuwar zaman Raudhan tare da shi.............✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥 _Mamuhgee_
Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇??_*
Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261 __________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*
*_Episode 73_*
..........A wata juma'a datai dai-dai da saura kwanki huɗu cikar shekarr Ramadhan guda a mulki aka ɗaura auren Alhaji Sageer Dogarai da amaryarsa Asabe. Aure ne daya tara ɗunbin al'umma musamman daya kasance juma'a ne mutane duk sun halarci masallaci. Aure ne daya saka wasu farin ciki wasu saɓaninsa musamman aunty Hannah da tun farkota nuna adawawta akai, sai dai kuma babu abinda ta isa ta hana daga hukuncin ALLAH. Ƴar walima kawai akai amarya ta tare ɗakinta cikin aminci da mutuntawa. A kuma daren Ranar M. Dauda da abokinsa suka iso Bingo a haukace a dalilin M. Gambon ya samo labarin a shanun ƴan talla. Inda ALLAH ya taƙaita al'amarin ya kira Bappi ta waya kafin su tunkari ko'ina. Hakan yasa Bappi saurin taka masa birki yasa Malam Adamu zuwa ya ɗakkosu. Babu wanda yasan da zuwansu Taura House sai Anne da Bappi. Aka basu masauki mai ƙyau da abinci kafin safiya. Da farko M. Dauda ya nuna shifa ba wannan ya kawosa ba Bappi dai ya sake lallashinsa.
Washe gari da suka zauna akan batun fir ya nuna shifa sai Alhaji Sageer Dogarai ya sakar masa matarsa inhar ana buƙatar zaman lafiya a NAYA. Iya nasiha yaƙi har sai da Bappi ya bama Ramadhan Umarnin sakawa a kawo masa Raudha gidan. Tana makaranta M. Adamu yaje ya ɗakkota. Gaba ɗaya hankalinta a tashe yake dan batasan mike faruwa ba. Gashi babu damar kiran Ramadhan ta damesa tasan yana office. Sai da suka iso taci karo da Abbansu ta sauke ajiyar zuciya. Yay sakalo yana kallonta da cikinta daya fito ɗas duk da ma hijjab ne a jikinta har ƙasa. Sai dai a yanda tai zaman sai da cikin ya fito. “Oh ALLAH sarki Raudha ashe wannan irin arziki ALLAH yaymin naketa shirme ma? Dama ciki ne da ke?”. Ina ƙasa Raudha ta shige dan kunya, Bappi yay murmushi mai faɗi da gyaran murya. “To kaga kariga ka fara zama babban mutum tunda ga jika kana shirin amsa duk da nasan bashi bane na farko. Ya kamata wasu abubuwan a ajiyesu hakanan kodan wasu dalilai Malam Dawood. Shi aure raine da shi, sannan ƙaddarace ta ALLAH. Ya riga ya ƙaddaro zaka zauna da mahaifiyar yaran nan na wani lokaci ku rabu, idan kuma da rabon sake zama sai kaga ta sake baro can ta dawo gareka ai”. Hawaye malam Dauda ya share dan harga ALLAH yana son Asabe, so irin wanda bai tabama wata mace ba. Dan ko auren nan daya kara na budurwa dal a leda bai maye masa gurbin rashin Asabe ba a ransa. Nasiha sosai Raudha da Bappi sukai masa, sai dai M. Gambo nata zungurinsa akan karya yarda wai. Tsaf Bappi ya fahimci M. Gambo, ya kuma gane shine matsalar M. Dauda. Dan haka a ranar ya saka aka maidashi Hutawa bayan ya haɗashi da shatara ta arziki. Sosai M. Gambo yaji zafin hakan, dan acewarsa ƙiri-ƙiri an nuna banbanci tsakaninsa da M. Dauda. hakan ya sashi ƙudirin abubuwan mugun abu da yawa cikin rai game da M. Dauda. Acewarsa in bai samu Asabe ba ai akwai hanyoyin ramuwa da yawa.
Kwanan malam Dauda biyar a Bingo, dan har gidan gwamnati aka kaisa ya kaso kwarkwatar ido wannan karon. Bappi kuma ya riƙesa akan ya zauna har sai anyi bikin cika shekara guda na Ramadhan a mulki. Hakan ya masa daɗi sosai, ya kuma sakashi farin ciki. Su Fatisa ma har nan Taura house sukazo gaida shi, har kuma zuwa yanzu bayan su Anne babu wanda yasan da zamansa a gidan.
*_GOVERNMENT HOUSE_*
Sosai aka shirya bikin cika shekara ɗayan nan har abun ya ɗan so bama mutane mamaki, dan lamarin tamkar wani arashi. An shirya ɗakin da taron zai gudana cikin tsarin ado na tutar ƙasar NAYA. Duk da gwamnoni suma zasuyi nasu a jihohinsu hakan bai hanasu halarta ba. Hakama sarakunan gargajiya da abokan kasuwancin Ramadhan. Su Alhaji yaro glass da muƙarrabansa harma da god fathers nasu kam sun halarci taron. Sai tarin manyan ƴan jam'iyya na kowace jiha. Kamar ko yaushe First Lady da mijinta shugaban ƙasar NAYA *_Ramadhan B. Hameed Taura_* suka iso wajen taron cikin shiga ta kamala ana take musu baya. Sanye take da hijjab har ƙasa fari ƙal mai hannu, sai kaɗan daga ƙasa ake iya ganin ƙasan doguwar rigarta mai kalar tutar ƙasar NAYA. Daɗin daɗawa akwai facemask a fuskarta tare da siririn farin glass iya hannayenta kawai ake iya gani da tsadajjen agogonta. Hakama shugaban ƙasa Ramadhan sanye yake cikin ɗanyar shadda fara ƙal daketa maiƙo da haska idanun mai kallo. Ta gaurayu da ɗinki na musamman daya ƙawatata ya kuma tabbatar fitar tutar ƙasar NAYA. Hakama hularsa zannah tayi matuƙar murzuwa. A kallo guda zaka tabbatar da tarin kwanciyar hankali da farin ciki tattare da shi. Yana riƙe da hanun matarsa har akai masa rakkiya wajen zamansa sannan mutane da suka miƙe dominsa na girmamawa suka koma suka zauna. Kamar yarda shari'a ta tanadar malamai sun gudanar da addu'oi kafin a fara gudanar da abinda ya tara mutane a wajen. Inda bayanin shugaban ƙasa yay matuƙar birge mutane da ƙara darajarsa a idanusu. Lokacin da aka buƙaci cewar first lady. Wata hamshaƙiyar mace ta miƙewa da takarda a hanunta ta tabbatar musu ga saƙon first lady ita wakiliyarta zata isar bisa umarnin shugaban ƙasa amma matsayin miji ba shugaba ba basai tace wani abuba. Hakan ya bama wasu mamaki, ya birge wasu. Wasu kuwa sun gumtsi gulma da sauya zancen a muhali na daban. Oho hakan bai damu Ramadhan ba, shidai burinsa tsare mutuncin iyalinsa da kuma kishinta da yakeyi. Bayanan da aka gudanar matsayin na first lady ma sun kayatar kuma sun birge mutane daban-daban. Daga haka taro ya cigaba da guna. Anci ansha anyi hani'an first lady da shugaban kasa babu wanda yasha ko ruwa a wajen. Sai da ana gab da tashi a taron ne Raudha ta hango Abbanta tare da Alhaji Hameed Taura cikin shiga ta kamala tamkar bashi ba, dan kayan daya saka sun masa ƙyau matuƙa duk da jikin ya nuna ba'a saba sakawa ba. Taji daɗin yanda ya kame kansa a wajen har aka tashi lafiya.
Duk yanda Raudha ke ɓoyen cikinta a hijjab hakan bai hana wasu ganewaba, tuni kuma yan jarida suka hau yaɗa cewar shugaban ƙasa gab yake da zama angon karni kuma Baba dan firt lady na ɗauke da ciki. A fanin ƴan adawa kuma sun gama baza zance first Lady dai turancine bata iyaba shiyyasa Ramadhan ya hanata magana a wajen aka samo kwararriya aka fake da kishi. Maganar tayi nisa sosai, sai dai cikin Raudha yaso danneta tare da manyan ayyukan da aka zano shugaban ƙasa Ramadhan ya shinfiɗa a shekara guda kacal. A ɓangare. su Alhaji Yaro glass sunyi zaman meeting akan cikin nan, inda kai tsaye suka ƙalubalanci Aunty Hannah data ɓoye musu hakan. Ta nuna batasan Raudha nada ciki ba itama, amma hakan bashike nuna batai murnaba. Dan ita tanada manufa akan cikin koba komai zasu kasance da wani kaso na dukiyar Taura family musamman idan aka dace Raudha ta haifo namiji. Wannan magana tata ta banƙanta ran su Alhaji Yaro glass, harya faraji a ransa Aunty Hannah bazatai dogon zangoba zai kawar da ita. Dan ya tabbatar shi ɗinma zata iya yin kalar tunanin da take furtawa akan dukiyar Taura family akansa kenan. Duk da kuwa Samha ce kawai a tsakaninsu har yanzun. To komadai miye, mudai ƴan kallone ai.🤣
Kwanaki biyu da yin wannan biki na cikar masu mulki shekara ɗaya akan madafun iko Malam Dauda ya koma hutawa da shatara ta arziƙi. Dan kuwa kujerar makka har uku, tare da kuɗi masu yawa da galleliyar mota da alƙawarin buɗe masa manyan shaguna a hutawa da kuɗi zasu dinga shigo masa akoda yaushe. Wannan farin ciki ya sashi danne son Asabe daya san har Abada bazai iya dainawaba. A randa M. Dauda yabar Bingo a ranar hoton wani video ya karaɗe yanar gizo da duk mai wayar da take iya buɗe data zai gani. Video ne daya kasance na Aynah a cikin club ana aikata masha'a da ita. Sai kuma wani shima a cikin ɗaki kusan su biyar duk mata. Abinda zai baka mamaki na club ɗin babu face mask kamar yanda Ramadhan ya sani. Aminu ya saki wannan video ne bayan ya saka dukan abokansa sunyi amfani da Aynah a wannan dare wasuma harta baya (Wa'iyazubillah😭) yayi hakane a dalilin kawo mata ƴammatansa da yay gidan ta nuna itafa ta gaji ya sallameta hakanan kokuma ta tona masa asiri ga iyayensa da yake yaudarar nuna musu shi ɗin mutumin kirkine. Shiko ya tabbatar mata kafin tayi hakan shi zai fara tona nata a sirin wa duniya sai yaga nata da nashi wannene zaifi gawurta da kayatarwa. Tayi kuka ta roƙesa iyakar roƙo amma yay kunnen uwar shegu da ita sai da ya saki. A lokacin da wannan video ya riski su Addah Asmah data haukata kanta a neman asirin hallaka Ramadhan da wulƙanta rayuwarsa data Gimbiya Su'adah har ƙasar China ta yanke jiki ta faɗi. Kwannta biyu kenan da dawowarta NAYA, wata kawarta ta rakata China wajen wani gagarumin masanin tsafi. Sun dawo zuciyarta cike da jin ɗunbin nasara saboda abinda matsafin ya haɗo musu, ta tabbatar idan har tai amfani da su Gimbiya Su'adah da zuri'arta sun zama labari kenan. Sai gashi a yau da take shirin zuwa Taura house da fuskar yaudarar roƙon gafarar gimbiya Su'adah danta aiwatar da aikinta wannan mummunan labari ya baje ƙasar NAYA dama duniya tunda abune na media ako ina zaka iya ganinsa. A firgice ma'aikatan gidan nasu da kanwar Aynah suka rufu a kanta sai dai babu alamar numfashi tattare da ita. Dole Zulfah tai kiran asibitin da suke ganin likita dan ta nema no na daddyn su ma bata samuba kasancewar shi bayama kasar.
Hatta da gimbiya Su'adah da ayanzu babu wanda ta tsana a duniya sama da ƴar uwar tata abin ya firgitata, balle kuma Fulani da itama ta yanke jiki ta faɗi ƙasa a sume dalilin tanada hawan jini. Raudha ma ta gani kafin Ramadhan, amma ta kasa nuna masa sai zama datai taita kuka dan abun ya ɗaga hankalinta. Musulma ɗiyar muslmai gaba da baya itace a wannan halin duniya ke gani babu ko kunyar mahaliccinmu. Kaicon wata wayewar, kaicon wata dukiyar, kaicon wata damar dan da wata BAƘAR INUWA ce da ita gara rana ma. Koda Ramadhan ɗin shima ya gani baiji abin saboba tunda a gabansa aka aikata, sai dai abinda ya bashi mamaki fitar videon bayan shekaru. Hakan na nufin dan kinyi barna ko kayi ka binneta da tunanin ta wuce mutane bazasu ganiba watarana UBANGIJI idan yaso sai ya tonota ta hanyar da kai bakai tunani ko tsammani ba. Sannan ya jiraka a madakata kazo ya hukuntaka dai-dai da laifinka dan shi bai kasance azzalumin sarki ba...........✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥 _Mamuhgee_
Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261 __________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*
*_Episode 74_*
..........Faɗuwar Addah Asmah ta jawo mata shanyewar ɓarin jiki, yayinda lokacin da Aminu ya kawo Aynah har gida da takardar saki uku bayan dukan daya lakaɗa mata ya sake ruɗar da jikin na Adda Asmah har sai da takai Zulfah ta kira gimbiya Su'adah tana kuka akan tazo ta taimakesu Mom ɗinsu zata mutu. Jini ba wasa bane, dan duk yanda gimbiya Su'adah taso ignoring al'amari ya gagara gareta, har hawaye tayi itama ganin video na Aynah hawan jininta ya nema tashi. Tanda halayen banza ta wani fanin, amma tanada zuciya mai ƙyau kuma. Dama can zugar Addah Asmah ɗin ce da fulani ke sake kangarar da ita wani lokacin. Haka ta shirya Safina na roƙonta kartaje dan ALLAH Mardiyya tace danmi? Ita rayuwa ai ba'a maida sharri da sharri. Koba komai ai ALLAH ya nunama Adda Asmah ita ba komai bace ba, sannan duk makircinta a karƙashin hukuncin ƙaddara da jarabawa yake. Idan Maah taje gareta a yanzu Ai sake tabbatar mata zakaran da ALLAH ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi ne. Sannan babu hanun daya isa canja ƙaddarar ALLAH sai dai kai wahalarka ka ƙare a wahale wanda kakeyi dominsa yana ƙara zama sama da kai. Da wannan zantuka na Mardiyya suka ɗunguma gidan Addah Asmah, inda suka isketa ita kwance Aynah kwance cikin jini na dukan da taci hanun Aminu. Da taimakonsu aka wuce da su asibiti, a kuma daren mai-martaba da fulani suka iso suma. Sunji daɗin ganin Su'adah da yaranta a wajen, suka shiga sanya musu albarka. A daren shima Daddyn Aynah ya iso, bai kumayi zaman ɓata lokaci ba akai shirin fita da su waje dan jikunan nasu su duka yayi tsamari sosai. Da Fulani suka tafi, gimbiya Su'adah tai kememe tace babu inda zataje hakama ƴaƴanta. Babu wanda yaga laifinta anan, dan ansan an cutar da ita...
___________________________
Wannan hatsaniya na cigaba da yaɗuwa cikin Raudha na ƙara girma. Komai nata ya canja, idan kaganta sai kace ba ita bace. Auren su Fatisa hanata zuwa hutawa Ramadhan yayi, iyakarta nan Bingo sabon gidan Mummynsu da yake anan akai yinin biki kamar yanda Alhaji Sageer Dogarai ya roƙa. Anyi yinin biki laraba Raudah ma a kwance ta yini da zazzaɓi, amma dan jaraba tana a gidan ɓoye. Da dare Alhaji Sageer Dogarai da kansa ya maidata government house duk da kuwa anzo daukarta, kuma dama tana tare da guards nata. Ba kowa yasan Raudha na gidan ba ƴan biki, sai da zata wuce gida. Aiko abin ya bama kowa mamaki kodan yanda Aunty Hannah tazo ita tana baza mulki kaikace itace matar shugaban ƙasar ma. Washe gari Alhamis ƴan biki suka ɗunguma Hutawa, inda akai musu tarba ta mutunci dan yanzu M. Dauda Alhmdllhi, duk da dai ginin shagunansa ko muce super market bai gama kammaluwa ba har yanzun. Amm kuɗaɗen daya samu ba ƙaramin barje guminsa yake ba. Kujerar makka kuwa ya rike sirrin a ransa shi da Inna da Baba Nafi zasu. Ranar Juma'a aka daura auren su Fatisa da mazajensu. Auren daya bada mamaki kasancewar shugaban ƙasa Ramadhan ya halarta tare da wasu gwamnoni da ministers. Hakama Alhaji Hameed Taura da Alhaji Basheer Hameed Taura. Ga Alhaji Sageer Dogarai da tasa tawagar dan a cewarsa su Fatisa shima ƴaƴansa ne. Saboda Asabe ta riƙe masa nasa da amana, duk da kalubalen data ɗan fuskanta ga yaran a farkon auren, sai dai halin kirki data dinga nuna musu da nuna rashin damuwa da abinda suke matan ita da Yasmin sai suma suka risina suka bata haƙuri ta haɗa ta rungume ta zame musu uwa.
Sam Raudha bata san Ramadhan zaije ɗaurin auren ba sai gani tai alabarai da aka nuna dalilin zuwansa wajen. Jitai fushin da take da shi ya kwaranye. Dan tunda yace bazatajeba take haushi da shi, ta kama matsar kwalla Basma na lallaahinta. Koda ya dawo gidan bayan la'asar kasancewar a helicopter yaje ya dawo saita rungumesa tana kuka da jera masa tagwayen godiya. Murmushi yay kawai ya kama hanunta suka shige ɗakinsa. Ya zauna akan sofa tare da ɗoraya bisa cinyarsa duk da ƙaton cikinta bai damu ba. Sai da ya ɗan sumbaci lips nata yake faɗin, “Partner yanzu kin lalace wlhy, komai kuka komai fushi kamar ba Ustazah ɗina mai haƙuri da juriya ba. Anya kuwa ranar shiga labour room ba akwai aiki gagarumi a gabana ba?”. Kwanciya tai jikinsa tana murmushi da hawaye. “ALLAH Noorullah dan baka san wahalar bane. Cikin nan ya isheni ji nake kamar na cire na huta”. Murmushi yayi mai kayatarwa, ya ɗaura hanunsa a saman cikin nata yana shafawa. “Kiyi haƙuri jarumata saura ƙiris insha ALLAHU. Kedai kawai mu cigaba da addu'a ALLAH ya saukeki lafiya ok”. Kanta ta ɗaga masa da sumbatar kumatunsa. Kafin tace, “Shine ka tafi Hutawa ɗaurin aure koma ka sanar min”. “Hhh haba ƙawata, ina sanar miki rigima zaki sakamin da shagwaɓa, ni banjeba ke bakije ba”. “To amma tunda kasan zaka basai kaje dani ba da an ɗaura auren sai mu dawo tare”. “Ke ɗin ce zaki yarda muje mu dawo a ƙanƙanin lokacin nan. Yi haƙuri ai dakin haihu insha ALLAH zakije ki kai musu baby su gani. Kimma san ya mukai da Anne?”. “A'a”. Ta faɗa tana girgiza masa kai. “Wai Taura house zaki koma da zama har ki haihu yaro yay ƙwari. Cikin farin ciki ta miƙe zaune sosai a jikinsa. “Kai amma naji daɗi ALLAH, koba ko....” Baima bari ta ƙarasa ba ya mangare mata kai yana hararta. “Oh kinmaji daɗi kenan. To ai a take nace mata ban yardaba sai dai ita ta dawo nan”. Baki ta tura masa gaba. “ALLAH wannan buƙulune kawai zakamin”. Dariya ya ƙyalƙyale da shi mai kayatarwa. “Naji gara hakan, nida aka shirya yima buƙulun barina gaurofa. Muna nan tare ki haihu muyi rainon babynmu kamar yanda mukai na cikin”. “Uhmm kaji wai mukayi, nadaiyi abina”. Gira ya ɗage sama, yana mai kai bakinsa saitin kunenta. “To amma wake ƙarama babyn ƙarfi bani ba”. Kansa ta ture da sauri tana ƙoƙarin tashi ya hanata. Haka ya cigaba da tsokanarta yana kunnata tana masa shagwaɓa. Daga ƙarshe suka koma gado sannan sukai wanka tare kamar yanda suka sabarma kansu a yanzu musamman irin wannan wankan na lada. Kamar koda yaushe langyare masa tai, dan ba karamin jigata take ba a duk sanda hakan ta faru, sai takai ya mata tausa da lallaɓata tayi barci ake rabuwa lafiya. Yanzun ma bayan tayi barcin fita yay zuwa dinig yayi lunch dan yunwa yakeji sosai.
*____________________________*
A kwana a tashi babu wuya wajen UBANGIJI. Raudha ta cigaba da rainon cikinta cikin kulawar ALLAH da Ramadhan, duk da nauyin Al'umma dake a kansa yana iyakar ƙoƙarinsa gareta itama. Ga gimbiya Su'adah kadaran kadahan tsakaninsu, ba gallazawa babu nuna damuwa. Dan ko Taura House taje zata gaisheta ta amsa ba kamar da ba sai dai iyakar gaisuwarce. Bazata kulataba bazata kuma hantareta ba. Hakama tsakaninta da Aunty Hannah, takan leƙo gidan lokaci-lokaci su gaisa, wani lokacin da mutanenta ƴan siyasa, wani lokacin ita kaɗai sai guards nata. Sau uku tana zuwa gidan Mummynta Asabe. Hakama gidan su Bilkisu dake nan Bingo duk taje. Su Fatisa ne dai har yanzu bata leƙaba saboda ba'anan Bingo suke ba. A haka cikinta ya shiga watan haihuwa raki da shagwaɓa ya ƙaru, dole kuma Aunty Zuhrah ɗiyar Yafendo ta dawo nan government House da zama dan Anne dai taƙi hakan duk da kuwa Ramadhan jikane. Tunda watan ya shiga kwanakin haihuwa ta daina zuwa makaranta, sai ta dai su Basma suzo su mata bayanin abinda akayi. Randa takejinta da lafiya ta fahimta, saɓanin hakan tace su barta karatunma baza'ayiba. Sukan mata dariya da tausayinta. Dan hatta uban gayyar idan ta birkice masa da rikici dariyarsa yake kwasa kafin ya koma lallashinta a shirya da ƙyar. Tun dai ana saka ran haihuwar har kwanakin da aka bata a sibiti suka gota, koda Ramadhan ya nuna damuwarsa Dr Hauwa tace karya damu ana samun irin hakan ai ba komai bane. Adai cigaba da mata addu'ar sauka lafiya ..........✍