Bakar inuwa book 1 - Chapter 35
Bakar inuwa book 1 Chapter 35: Bakar inuwa book 1 Chapter 35. *_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke…
4,220 words
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥 _Mamuhgee_
Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261 __________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*
*_Episode 75_*
...........Alhmdllhi a wani dare na juma'a da yay dai-dai da cikarta watanni goma cif ta farka da gigitacciyar naƙuda. Rikicewa Ramadhan yayi, da ƙyar ya iya control ɗin kansa ya saka jallabiya sannan ya fito kiran Aunty Zuhrah. Da taimakonta suka ɗauki Raudha zuwa clinic ɗin gidan, yayinda tuni su Basma sun sanar ma Anne. Babu bata lokaci a daren Anne da Dr Hauwa suka nufo gidan, inda suka samu har wata Dr ta shiga da ita ɗakin haihuwar. Babu ɓata lokaci Momyn Jafar ta rufa musu baya itama, aiko ta tarar Dr Ingoze na niyyar halaka yaro dama uwar. wata irin muguwar bangaza takai mata tare da sauke mata tagwayen maruka, daga haka ta hankaɗota waje ta koma kan Raudha. Kowa yayi mamakin yanda aka hankaɗo Dr Ingoze waje. Gashi Dr Hauwa tace security su rike mata ita har saita fito. Hakan kuwa akai zuciyar su Anne fal wasuwasi. Dama shi Ramadhan suna kawota ya koma ciki kamar yanda Aunty Zuhrah ta bashi umarni. Maimakon zama sai yay alwala ya fara nafilfili da nemawa matarsa sauƙin naƙuda da fatan sauka lafiya. Tabbas Dr ingoze tama Raudha lahani, sai dai cikin amincin ALLAH an samu damar ciro jaririn ta hanyar theatre kamar yanda Dr Hauwa ta yanke shawara. Dan ƙarfin Raudha ya nema karewa saboda yanda Dr ingoze ta dinga danna kan yaron yana ƙoƙarin fitowa kafin zuwa Momyn Jafar. Sai gabanin asuba suka fito, anci nasarar ciro santalelen yaro gashi ƙato alamar uwarsa taci ta ƙoshi. Sai dai babu damar ganin Raudha har sai ta samu isashen hutu kamar yanda Dr Hauwa tace. Atake murna ta gauraye gidan na gwamnati, kowa kuma nama Raudha fatan samun lafiya. Lokacin da jariri yaje hanun uban gayya Ramadhan hawaye yaji sun cika masa ido. Ya sumbacesa tare da rungume abinsa yana maijin kaunarsa na ratsashi. Wannan shine karo na biyu da ALLAH yay masa ƙyautar da kuɗi basa badata, hakama mulki da ɗaukaka. Ya bukaci ganin Raudha duk da Dr Hauwa taso dakatar dashi ya bata haƙuri, dole aka ƙyalesa ya shiga shi kaɗai ya dubata. Tausayinta ya kamashi, ya dinga jera mata tagwayen kiss's da addu'oi.
Zuwa wayewar gari labari ya karaɗe lungu da sako na ƙasar NAYA akan shugaban ƙasa ya samu ƙaruwa. Ga hoton Baby nata yawo saboda su Basma da sukaita turawa ƴan uwa da abokan arziki. Sai yazam kowa ƙoƙarin ɗorawa yake a shafinsa, wasu idan sun gani suma sai su ɗauka daga haka ya karaɗe wayoyin mutane. Yaro yasha addu'oi yayinda ƴammata da yawa suka koka dajin kishin inama daga jikinsu ya fita. Sultana dake ƙasar America kam harda kwanciya ciwo dan har yanzu ciwon son Ramadhan na zagaye da ita. Kawai dai babu yanda zatai ne tunda ya faɗa mata iya gaskiyarsa shi baya ra'ayinta tayi haƙuri ta samu mai sonta.. Karo na farko, lokaci kuma na farko da Gimbiya Su'adah ta kira waya tasa aka haɗata da Raudha data farka a washe gari da rana. Yajiki tai mata da fatan samun lafiya. Ita dai Raudha abun ma har hawaye ya sakata. Ramadhan dake gefenta yasa hannu yana share mata fuskarsa ɗauke da murmushi. Ɗansa dake hanunsa yanata barci ya kalla. Ya shafi lips yaron jajaye yana faɗin, “Ba kuka zakiyi ba Partner. ALLAH zaki godemawa a wannan gabar, ni shaida ne Maah ta jima dayin nadamar abinda tai miki, ta shanye a cikintane kawai saboda nauyin tunkararki. A yanzu kam koda abinda ke faruwa da Lubnah a gidan miji ya isa sake tsoratata”. Da mamaki Raudha ta dubesa. “Aunty Lubnah kuma?”. Kai ya jinjina mata batare da ya kalletaba ya cigaba da wasa da sumar yaron. “Eh Lubnah. Tun satin da aka kai Lubnah gidan aure bata sake farin ciki ba. Kuskure kaɗan miji zai lakaɗa mata duka tare da ƙanensa. Ke hatta da uwar mijinma ba ƙyaleta taiba itama dukan nata take. Duk da dukiya irin ta gidan su Mansur ƙiri-ƙiri suka sallami kaso ɗaya bisa biyun ƴan aikinsu aikin ya koma kan Lubnah. Cikin ƙanƙanin lokaci ta fita hayyacinta saboda azaba. Ameenatu, tun sanda Lubnah ta kawo Mansur garemu matsayin miji na nuna ƙin amincewata, saboda na jima dajin labarin mahaifiyarsa bata zama da sutukai. Hakama kanensa basu da isashen tarbiya. Amma sai Maah taƙi saurarena saboda Lubnah tace tana son sa akace ai nima wadda nake aure bata dace dani amma suka amsa. Dan haka Lubnah zata auresa ko ina so ko banaso. To ga sakamakonan sun gani, dan yanzu a dalilin dukan da surukar mijinne tai mata tai ɓarin cikin jikinta, maimakon Mansur ɗin yaji tausayinta sai ya maidota gida da takardar saki har uku wai yana zarginta da tarayya da drivernsu kiji sharri. Koda nai bincike uwarsace duk ta tsara hakan kamar yanda take koran matan ƴaƴan itama tai sanadin da za'a korota”. Sosai abun ya taɓa zuciyar Raudha duk da zaluncin da su Lubnah suka dinga mata a baya. Ta jingina kanta da kafaɗar Ramadhan tana kallon babynsu hawaye na zubo mata. Shima rungumita yay da hanunsa cikin son kore mata damuwarta yace, “Ustazah dawa yaron nan ke kama?”. “Dani mana” Ta bashi amsa tana share hawaye. Ƙeyarta ya ɗan tallara kaɗan. “Son kanki yayi yawa madam. Kowa yaga Abdull-Hameed Ramadhan Taura yasan gida ya ɗakko, mufa jininmu ƙarfine da shi yarinya”. Murmushi tayi mai ƙayatarwa da cewa, “Uhm nidai basan cika baki. Dama da Pa kace yana kama ko Bappi sai na yarda”. Dariya yay yana mai sumbatar kumatunta. Hakama babyn ya sumbaci goshinsa. “Bakice komai akan sunan dana kirashi da shi ba”. Murmushi tayi mai kyatarwa da shafa kumatunsa. “Saboda shine ra'ayina shiyyasa nima”. “Woow sweetheart inajin daɗi idan muka kasance bisa tarayyar abu guda”. “Noorullah! Idan duk yarana zasu kasance da sunan Bappi ko Pa ko Anne ko Maah ko kai bazan taɓa baƙinciki ba. Fatana dai ALLAH ya bani ikon sauke nauyinka dake kaina ka kuma zamemin miji har a gidan aljanna. ALLAH ya raya Abdull-Hameed Ramadhan Taura ya albarkaci rayuwarsa. Yasa yay gadon ƙyawawan halayen Bappin da Pa da kai kanka”. “AMin ya rabbi sweetheart. ALLAH yay miki albarka ya ƙara miki lafiya. Yasa nan da wata shekarar mu sake dawowa labour room.....” Da sauri ta rufe masa baki ƙwalla na ciko mata ido. “Wannan ai fatan tsiyane”. Dariya ya kyaƙyale da ita yana ture hanunta. Miye na wani fatan tsiya anan ai nasan zaki iya Mrs Taura. Haka suka kasance cikin nishaɗi har saida Aunty Zuhrah tazo ta korashi ɗakinsa sannan.
★Sai da Raudha ta warke sosai aka fara shirye-shiryen taron suna, amma kowa dai yasan sunan yaron Abdul-Hameed anma Bappi takwara. Ramadhan yaso ayi suna a Taura house Bappi ya hana yace ayi a government house kawai. Badan yaso ba dole hakan aka shirya. Taron sunane daya haɗa manyan mutanen ƙasar NAYA lungu da saƙo, inda amaryar jego da baby sukaci ƙyau har suka gaji. Shi kansa angon jegon yayi tsaf dashi kamar yana shirin yin sabon aure. Anci ansha an kumayi bishasha, inda yaro ya samu ƙyaututtuka masu ban mamaki wasuma dan riya sukai badan ALLAH ba. Dan kawai wane yayi kar ace su basuyiba.. Hatta M. Dauda ba'a barsa a bayaba ya haɗo kayansa na jego harda saitin robobin wanka da saƙe saƙin wanka na icce da ƙatuwar garwarsa ya kawo. Wannan abu yasa su Aunty Hannah takaici duk da ba'a wajen taron ya bayarba. Sai dai ita Raudha farin ciki tai ita da Ramadhan. A zahiri taro ya tashi lafiya, sai dai a baɗini wasu sun iso wajen taron ransu da ƙulli. Ba su kowa bane sai su Alhaji Yaro glass da ko Aunty Hannah yanzu batajin sirrinsu. Bayan taro ya tashi lafiya wajen ƙarfe biyar na yamma a tsakanin government house zuwa Taura house aka buɗema motar Alhaji Hameed Taura wuta. Harbi ne irin na kwararrun maharba da ko a nesa suka harbo harsashi sai ya isa ga wanda suka hara ɗin. Sai dai in ALLAH ya kaddara da kwananka a gaba ka tsalle domin ikonsa.
Tabbas masu harin sunyi nasarar kaima motar hari sai dai basu taki sa'a ba, amma duk da haka ɓarnarsu ta shafi Taura house. Bayan kammala walima Alhaji Hameed ya shiga mota shi da Anne da su Yafendo domin komawa gida. Sai dai kiran Daddyn Aynah ya riskesu akan rikicewar jikin Adda Asmah gashi ya kira Gimbiya Su'adah bata amsa ba. Hakanne yasa suna ɗan gota government house Bappi da Anne suka fita amotar suka shiga wata harda Yafendo, Inna kuma dake fama da ƙafa tunkan su tafi wajen walimar dama danta dagene Bappi yace a wuce da ita gida. Kasancewar motar da su Muneera ke ciki suka amsa ɗin yasa Muneera dawowa wajen Inna ita kuma. Su Alhaji yaro glass basu san da wannan canji da aka samuba suka sanarma yaransu tahowar Bappi da sanar dasu motar da yake ciki su shirya. Idan UBANGIJI bai ƙaddara mutuwarka ga makiyiba, komai wahalar mai wahala sai dai ya dawwama cikin wahalar farautar zafin rana data ɗacin zuciya babu nasara.
*_ALLAH ka shiga tsakaninmu da maƙiyanmu😭🙏🏻._*
Take a wajen ma ALLAH yay ma Inna Rasuwa, dan sai gawarta aka nufi asibiti da ita. Driver da Muneera ne kawai ke numfashi. Shima driver ko mintuna biyar basu cikaba ya rasu. Karaɗewar labarin wannan hari da aka kaima Alhaji Hameed Taura cikin kanƙanin lokaci yasa ko zama basuyi a gidan Adda Asmah dake a mawuyacin hali itama suka taho. Hakama Raudha da Ramadhan da su Aunty Zuhrah duk sun rikice a government house. Dan kuwa babu abinda kake gani a yanzu akowane gidan tv sai harin da aka kaiwa Alhaji Hameed Taura. Amma abinda yaba mutane mamaki kamar yanda yan jarida ke faman shelantawa babu shi a motar duk da kuma daga government house kowa yaga motar ya shiga har shugaban ƙasa yay masa rakiya. Zamu iya cewa a wannan dare gaba ɗaya NAYA a hargitse ta kasance. Dan ba'a samu damar bizne gawar Inna ba saboda jami'an tsaro sun rike. Kuka Raudha take tana sambatu da ambaton “Su din azzalumai ne. Dama sun ce sai sun kashemu, miyay musu, mi kai musu kaima mijina?. Na tsanesu, da ace sun samu nasara kan Bappi yau da kaina zan kashesu, amma ko yanzu karka ƙyalesu Ya Ramadhan. Na rokeka karka barsu suma su dukansu”. Kalaman Raudha sun girgiza Ramadhan, dan haka ya tsareta ta sanar masa suwaye? Mita sani? Mi take boye musu. Shi tun sanda ta karema Bappi hari ya tabbatar tasan wani abu. Cikin kuka ta shiga girgiza masa kanta. “Wlhy bansan komai a sannanba Ya Ramadhan, sannan bansan su wanene ba. Nayi hakane saboda shima ya taimaki wani tsohon daya fisa shekaru a filin idi. Amma badan na sanshi ba. Badan nasan komai daga garesaba. Sai dai zan faɗa maka abinda na sani nima, amma wlhy ka yarda dani, ban yarda da aurenka saboda su ba. Nayine kawai dan yima mahaifina biyayya da gujema mahaifiyata tsinuwa da Gwaggo tace zatai mata inhar ban yarda da aurenka ba...........”✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥 _Mamuhgee_
Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261 __________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar??🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*
*_Episode 76_*
..........Tsaf ta zayyane masa komai data sani na firar su Aunty Hannah da taji, har zuwa aikama bappi takarda, da batun canja driks nashi da ake kawowa cikin gidan. Ya daɗe da bincike akanta game da drinks saboda yanda kuɗi ke yawan fita a accaunt ɗinta, wanda duk watan duniya ake saka mata kason kudi na Taura family da ake bama kowa. Bai mata magana ba ya shiga bincike akan son sanin mi take da kuɗi, cikin ikon ALLAH kuwa yay azamar ganowa saboda companyn da take aikama kuɗin. Ta hanyarsu ya gane ana kawo drinks gidan, baiyi ƙasa a gwiwa ba yasa akai masa bincike akan wanda take canjawa da wanda take sakawar. An gano wanda take cirewar wasunsu akwai guba a jiki mai shiga jiki a hankali, wanda take canjawar kuma lafiya lau yake. Tun a sannan yasan Raudha tasan wani abu, shiyyasa koda suka samu rubutunta yazama irin na wanda aka aika musu wasiƙa bai tada hankalinsaba. Burinsa kawai yasan asalin tushe da mafari, yau kuma ta zayyane masa komai. Kyawawar runguma ya bata yana mai sanya mata tarin albarka. Sai dai hakan bazai hanashi kafa kwamitin bincike ba domin tabbatarwa. Badan bai yarda da itaba, sai dan haka dokar shari'a take shaidarta bazata wadatar ita kadaiba dole sai da wasu shaidun musamman da su forma president suka zama manyan kusoshin ƙasar. Dama Dr Ingoze dake hanun security na gidan ta tabbatar musu ita ba laifinta bane sanyata akai ta hakala Raudha da jaririnta inba hakaba itama za'a halaka kaf family nata.
*_WASHE GARI_* akai jana'izar Inna da driver aka mikasu gidansu na gaskiya. Ciki kuma harda Shugaban ƙasa Ramadhan da yaje har makabarta. Bayan sun baro makabarta kuma ya wuce ya duba jikin Muneera da batasan ma ina hankalinta yake ba. Sosai ta canja kamanni saboda yanda motar ta kife ta dinga katantanwa da su a kan titi ga harbin data samu har biyu a ƙafa ɗaya da ƙugunta. Cike da damuwa da tausayin ƴar uwar tasa ya koma gida.
Sosai a wannan karon ma su Alhaji Yaro glass sukai baƙin ciki na rashin nasara. Har zukatansu suna sanar musu lallai Alhaji Hameed Taura na tsafi shiyyasa dukkan harin da suke kai masa sai ya kauce masa. Acewarsu to ai idan yasan wata baisan wata ba. Suna kusan sahun farko na zuwa yin jaje da ta'azziya Taura House. Sun kumaje har government house sunma Ramadhan shima dan ana gama jana'iza ya koma gida.
Randa akai addu'ar uku ranar Raudha ta koma government house tare da sabuwar mai kula da ita. Dama Anne nata faɗan zuwanta tun randa akai rasuwar acewarta tana riƙe da laɓuɓun yaro yawo ba nasu baneba ai. Duk da ba wankan jego take irin na mutanem da ba tana samun kulawa sosai dan babu ɗaga ƙafa Hajiya Mama ta dinga mata wankan towel. Yanzun ma koda suka dawo haka ta dinga kula da ita da ƙyau ita da Abdull. Dan Ramadhan ya hana a ɓoye masa suna. wasu kan kirasa Abdull wasu suce Abdull-Hameed ɗin. Shi dai Bappinsa yake kiransa, itama kuma takance bappi wani lokacin ko tace babban mutum. A haka kwanakin jegonsu suka shuɗa duk da dai wajen da akai mata cs ya warke sarai Alhmdllhi. Ga gyara tana samu na musamman daga shahararriyar mai gyaran nan ƴar Nigeria dake jihar sokoto *_Maman Zara sokoto 07034251528_* (hummm kunga maman zarah ɗin nan karku bari kayanta su wuceku, ku garzaya domin kwasar rabonku, dan koda kuɗinka sai da rabonka kuwa) Gefe kuma Miss xoxo na kasheta da kayan gyaran jiki na musamman dana kamshi. Duk wanda yaga Raudha dole ya sake kallo, dan haihuwar ta sata buɗewa ta zama wata babbar mace da zaka iya bata shekaru ashirin da tara bawai sha tara ba. Shi kansa gogan nata haƙuri kawai yake da juriyar ɗauke kai. Amma inhar ya samu damar ritsata a ɗaki su kaɗai yana ɗan rage zafi ko rokonmi zata masa baya saurarenta. Dama aunty Zuhrah ce ke saka musu ido, ita hajiya Mama akwai kunyar surukuta shi kansa baya yi idan yasan tana kusa. Ana saura kwanaki uku suyi arba'in Anne ta sanar masa ya kamata yabar Raudha taje hutawa, ta kuma je Bina masarauta duka tayo kwana bibbiyu. Fuska sosai ya tsuke kamar yana gabanta, sai da yaji ta sake maimaita masa sannan yay magana cikin marairaicewa. “Amma Anne dan ALLAH...” Kaga Ramadhan ni bance tilas ba. Ina dai tunatar da kaine abinda ya dace. Kai yanzu kana ganin ya kamata ace har yanzu matarka bata taɓa takawa gaishe da mai-martaba ba? Sannan tunda akai bikinta bata taɓa zuwa gaida mahaifinta ba?. Nasan dole ne ai muku uziri saboda a yanayin da kuke yanzu, amma bashi ke nuna bazakuje ayi zuminci ba. Kodan kaga tanada haƙurin shanye komai batare data matsanta maka ba”. Ajiyar zuciya yaɗan sauke, dan yasan tabbas maganar Anne gaskiya ce Raudha nada matuƙar haƙuri, kamar kuma hanata zuwa gaida mahaifinta tauyeta yayi tunda tasha nuna son hakan duk da bata taɓa tunkararsa ba.
Da wannan shawara ta Anne ya shiryama su Raudha tafiya cikin kwanaki biyu. Zatai tafiyar bisa rakkiyar su Hajiya Mama da tawagar securitys. Koba komai hakanma ai ya taimaketa tunda tana son zuwan. Hutawa suka fara zuwa, inda Mal. Dauda ya rikice ya rasa inda zai tsoma ransa dan daɗi. Hakama Baba Nafi da Inna da sauran yaran gidan. Amarya ma dai ba'a barta abayaba, tace dolene ta tarbi first lady kodan baƙanta ran Larai abokiyar hamayyarta. Aiko kamar yanda ta shirya kunna larai tako kunnuta harta kasa riƙe baƙin cikinta ta dinga sakin magana da aibanta Raudha harma da Asabe. Uban gayya Mal. Dauda dake ƙwaƙume da Abdull babu wani jan lokaci ya sauke mata maruka, tare da tabbatar mata yau tata ta ƙare a gidan taje ya saketa. Dan ya rantse duk wanda ya nuna baya son mai sunan Innarsa Raudha to shima bazai taɓa yasosa ba, domin Raudha dai farar haihuwa ce. Da farko Larai ta ɗauka abun wasa, sai da Inna tace “Idan bazata tafi ba ƙara mata guda Dauda”. Haƙuri Raudha da Aunty Zulfah suka shiga badawa. Yayinda Hajiya mama ko'a jikinta. Take anan ma ta kira Asabe ta guntsa mata. Bawani daɗi Asaben taji ba. Dan acewarta saki koda kaine ka nema bashi da daɗi. Sosai maƙwafta sun shigo gaishe da first lady, dan ma wasu tsoron securitys dake zagaye da gidan na mal. Dauda ya hanasu. Washe gari da safe taje har gidan hakimi takai gaisuwa da masa godiya. Shiko ya amshi Abdul yana mai sanya masa albarka shi da ƴan fadarsa da matansa. Sunbiyo ta super market ɗin M. Dauda da Raudha taji har ƙwalla ya cika mata ido dan babu abinda zatace da Bappi sai dai addu'a. Da zasu taho jitai kamar karta baro garinta, M. Dauda ya shirya tsaraba mai yawa wai duk na Abdull, ita Raudah abinma dariya ya bata. Yaushe Abdull ɗin yazo duniyarma dazai fara shan kayan zaƙin nan dana ciye-ciye. Da tace a rage cayay bai yarda ba. Itama Inna ba'a barta a baya ba tama Raudha tsaraba da kayan sirrinsu na tsoffi masu kyau da dama ta tanada tunda Raudha ta haihu. Dan ko lokacin suna da sukaje dama takai mata wasu.
Daga Hutawa Bina suka nufa cikin masarauta. To anan dai kam daga mai-martaba ta samu tarba ta ƙwarai. Fulani ce dai kadaran kadahan. Dan ko Abdull ƙin cewa a bata tai sai da Aunty Zuhrah ta ɗauka da kanta ta bata tace a sanya masa albarka. Sai kuma duk taji kunya. Mai-martaba kam acan suka baro masa Abdull, ba'a dawo musu dashi ba sai da ya fara ƙananun kukan yunwa. Anan ɗin ma dai shatara ta arziƙi mai-martaba da sauran matan sarki suka bama Raudha dan Ramadhan yana girmamasu shidai. Babu ruwansa da wata aƙidar dake tsakanin iyayensa da su.. Ganin sunzo har Bina ta kira Ramadhan ta roƙesa zuwa gaida Aunty Halima itama. Bai hana ba, dan tun farko ma daya san Aunty Haliman a Bina take itama da kwanan akai mata. Sai dai gsky a matse yake da matarsa, burinsa kawai ta dawo. Aunty Halima taji matuƙar daɗi dayin farin cikin zuwan na Raudha. Hakama yaranta. Kasancewar Ramadhan yace sukai har dare sai su biyo jirgi yasata baje kolinsu sosai a gidan Aunty Halima. Dan sai kusan tara suka nufi airport jirgin 9:30 zasu bi.
Ƙarfe goma bataiba ma suka iso Bingo. Motocin da suka tafi tarbarsu da securitys suka kwasosu sai government house. A ranar ma dai Ramadhan yayi kawaicin kauda idonsa saboda yasan da gajiya tattare da su. Dan ko keɓewa bai yarda yayi da Raudha ba. A ɗakin da take jego ya shigo suka gaisa da su Aunty Zuhrah itama Raudha ta gaisheshi ya ɗauka Abdull ya fita. Kusan mintuna talatin yay kiran Basma a waya tazo ta ɗakko Abdull ɗin ta dawo da shi. Washe gari su Hajiya Mama suka tarkata yan kayansu kafin Ramadhan haƙurinsa yakai karshe ya fara rashin ta ido. Shatara ta arziƙi suma ya haɗa musu suka tafi Raudha na matsar kwalla. Tsabar ya shiryama wannan weekend suma su Basma cayay zuje Taura house suyi weekend. Raudha zatai magana ya dinga zuba mata harara da mintsini. Doleneta tai shiru..........✍
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida 💯 Natural/organic
maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai Akwai soap 3k Student package 7k Beauty kit 11k Bridal kit 18k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Chapter notes and social links
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*