Bakar inuwa book 1 - Chapter 36
Bakar inuwa book 1 Chapter 36: Bakar inuwa book 1 Chapter 36. Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 *_Typing📲_* *_Episode 77_* .........Bayan…
4,425 words
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 *_Typing📲_* *_Episode 77_* .........Bayan wucewar su Basma sai da ta tabbatar an gama shirya abinci a dining tabar sauran komai hanun mama ladi sannan ta shigo ɗakinta da yanzu ta dawo. Abdull dake a bayanta goye ta sauke saman gado, dan Anne ta gargaɗeta matuƙa akan ta dinga goyasa yanajin ɗumin jikinta batason wannan halayyar da matan yanzu keyi naƙi goya yaro ko ace za'a bama masu aiki suyita faman raino ke uwa kina hutawa. Wanka ta shiga, fitowarta babu jimawa tana ƙoƙarin neman kaya marasa nauyi ta saka Abdull ya farka ya fara ƙananun kuka. “Oh oh babban mutum yi haƙuri ina zuwa. Nasan matsalarka yunwace acici”. “Ai duk ke ya gado cin nan ba wani ba”. Ta tsinkayi amsa daga bakin Ramadhan da bataji shigowarsa ɗakin ba. Ɗan juyiwa tai tana kallonsa, dai-dai yana karasawa saman gadon ya dauka Abdull yana sawa a kafaɗa. Murmushi tayi da ɗauke kanta tana cigana da ɗakko kayanta. “ALLAH ya Ramadhan kaima kasan banda ci, sai dai in kai”. Ta ƙare maganar tana nufosu kaya a hannu. Kayan ya ɗanbi da kallo, cikin neman magana yace, “K har kina tunanin saka kaya a yau?”. Cikin rashin fahimta tace, “Kamarya? Kana son na zauna da towel ne na kwashi mura?”. Murmushi yayi mai ƙayatarwa, ya sauke Abdull daya koma barci saman ɗan gadonsa ya gyara masa kwanciya. Tana ƙoƙarin saka riga ya riƙeta. “Idan ma kinsa zan ciresu ne, minene na wahal da kai?”. Kunya ce ta kamata, cikin marairaicewa tace, “ALLAH ya Ramadhan ba kyau, kaifa yanzu ka girma sunanka Daddy”. Kai ya dungure mata yana murmushi, sai kuma ya zare ribbon ɗin kanta tare da tallafo kannata ya manne goshinsu waje guda suna shaƙar numfashin juna. “K miyasa kin iya fassara mutum. Ni karki lalatani bankai can ba”. Mintsini takai masa a gefen ciki, ya janye jikinsa da sauri yana faɗin “Ouch yarinyar nan muguntar da kika koyo kenan a yawon arba'in ɗin”. Dariya Raudha ta ƙyalƙyale da shi da masa gwalo. “Ai kaɗan ma kenan”. Ƙwafa yay fuska a cuskule kamar gaske. “Haba yarinya zan rama ne idan kikazo hannu zaki gane kuranki”. Juyowa tai da sauri garesa fuska a narke, dan tasan wanene mijin nata. “Please Noorullah sorry”. “Ba wani sorry ai saina rama”. Da sauri ta nufosa ta ɗane masa baya duk da ta zama lukuta yanzun, “Ya ilahi, yarinyar nan kin koma biri ne?”. Ya faɗa yana juyota ta sakko suka faɗa saman gadon. “Gaba ɗaya kin zama ƴar lukuta amma ƙibar ta miki ƙyau”. Yay maganar a hankali yana busa mata numfashinsa a kan fuska. Kafin ta samu damar magana ya manne lips nashi kan nata. Itama a zalamen take, dan haka babu musu ta miƙa wuya ita shaidace mijin nata yayi haƙuri, kusan kwana hamsin ai ba wasa ba. Sai da taga zasu wuce hanyar da suka ɗakko ta fara ƙoƙarin janye jikinta. Amma ya nuna shifa sam bai yarda ba. Roƙon duniya da magiya ya nuna mata baiji bai gani. Dole ko ta miƙa wuya. Daga baya kuma ta shiga tsoro, dan tasan taji gyara babu ƙarya balle algus. Tafiya tai nisa Abdull ya sake farkawa yana kuka. Amma Ramadhan sam yaƙi nuna yama jisa, itako Raudha hankalinta duk sai ya koma kansa (uwa kenan. Uwa mafi uba koda uban sarki ne👍🏻). Lokacin daya kai inda yake buƙatar zuwa Abdull yaci kuka harya godema ALLAH, da ƙyar ta iya dauriyar tashi ta nufi bayi, Bata ɓata lokaci wajen gasa jikinta ba ta fito dan har yanzu Abdull bai bar kuka ba duk da tabar Ramadhan na ɗan shillashi cikin ɗan gadonsa. A yanzu ɗinma haka ta samesu, batace da shi komai ba ta yafa towel ɗin da take goge jiki a kafaɗarta ta ɗauka Abdull ɗin. Tashi yay shima batare da yace mata koman ba ya nufi bayin. Lokacin daya fito tana shayar da Abdull ɗin idonta kan yaron nata da ɗan wasa da sumarsa. Ramadhan ya zauna kusa da ita da riƙe kafar Abdull dake motsawa. “ALLAH sarki kakan Dadynsa kaji yunwa da yawa. Mamanka ce ta cika zalama da wuri take son a farauto maka ƙanne”. “Innalillahi... Kai Ya Ramadhan”. “Ba wani Ya Ramadhan anan. Inba azalame kike ba miye daga zuwana duba Bappina zaki wani kadandaneni sai da nayi”. Ina kasa Raudha ta shige dan kunya. Ta ture kansa daga kafaɗarta, shiko ya ƙyalƙyale da dariya. “Uhhm tundafa kin samu kinmin kat aiƙyafa tureni, dama Ustazan nan shiru-shurunku aiba na lafiya bane. Yanzu haka nasa kina nan kina addu'ar a koma second r.......” Hannu tasa ta rufe masa baki, idanunta har suna tara ƙwalla. Ta dangwarar masa da Abdull a cinya zata miƙe tabar wajen ya riƙota yana dariya. “Yi haƙuri wasa nake my Partner, duk fa nine zalamammen”. Ita dai bata sauraresa ba, da ƙyar ya samu ya lallasheta cike da salonsa da yake kasheta da shi. Daga karshe suka ɗunguma falo sukai dinner aka sake dawowa filin daga.... Rayuwa ta cigaba da tafiya cike da farin ciki da jin daɗi ga waɗan nan ma'aurata, hakama mulkin Ramadhan kowa nata san barka. Bayan sun gama amarcin jegonsu ta tattara ta koma makaranta. Ramadhan ya sake maida hankalinsa ga harkokin mulkinsa. Yayinda a gefe ya naɗa kwamitin bincike akan harin da aka kaima Bappinsa. Sai dai kuma mi a hankali rikice-rikice suka fara tashi a wasu yankuna na ƙasar NAYA. Ga yawaitar ƴan fashi a tituna da gidajen manya. Al'amarin kamar wasa sai ya dinga faɗi da gawurta harya fara fin ƙarfin jami'an tsaron dake a tsaye kan matasalolin. Sosai hankakin Ramadhan ke tashe. Tsabar ruɗani har wata rama yay yay duhu sosai. Ita kanta Raudha dake ƙoƙarin kwantar masa da hankali dauriya kawai take, dan zubda jinin ya fara yawan wuce hankali. Dan takai anabin manyan malamai ana musu yankan rago a cikin gidajensu. Komai daya shafi mulki sai ya fara tangal-tangal musamman manyan ayyukan da ake shimfiɗama talakawa. to ana ta rai waketa wani aiki. Mutane ma idonsu ya daina ganin ayyukan tashe-tashen hankulan kawai suke gani, akoda yaushe cikin zaman meeting ake tsakanin jami'an tsaro da masu faɗa aji, sai dai babu alamun samun wani sauyi. Ba Ramadhan kawai ba, hatta su Anne hankulansu a tashe yake matuƙa, dan duk mai hankali ya kalla abubuwan da idon basira yasan ƙirƙirarsu akai da gayya.. Ramadhan na gab da cika shekara biyu a mulki Bappi ya bashi shawarar sauke duka manyan shugabanin tsaro, hakan kuwa akai, aka sauke su aka ɗakko wasu aka ɗora... Hakan ya tada hankalin su Alhaji Haladu Gwandu matuƙa, dan shirine da babu wanda yasan dashi wayar gari kawai akai shugaban ƙasa ya zartar da hukunci. A gefe kum aka tara matasa takowane yanki aka basu aikin sakai sai dai gwamnati zata dinga biyansu albashi mai tsoka. Sannan aka saka maƙudan kuɗaɗe ga duk wani farar hula daya kawo sunan ɗan ta'adda uku ya tabbata kuma ɗan ta'addanne. Wannan shirifa ya zaburar da natasa da talakawa, burin kowa ya samu wani maraji ya kwafe sunansa a takarda da mafakarsa yakai hukumomin sirri da aka baza a kowace jiha ta ƙasar NAYA. Sai gwamitin bincike na musamman da aka ajiye su kuma a gefe akan son sanin ta inda makamai ke shigowa ƙasar ta NAYA. Lallai wannan shiri ya zaburar matuƙa, dan ya maida kowa jami'in sirri mai himma. Takai har ƙananun barayi ma basu da wata sakewa yanzun, dan kan barci ne makwafcinka na maka minshari. Burinsa kayi kuskure kaɗan yakai sunanka a sauke masa kuɗaɗensa. Tofa inji masu jimamin fitar magana, bincike fa ya fara daukar hanya, dan wasu sunaye da ba'ai zato ko tsammani ba sun fara bayyana kansu ta hanyar yaransu da aka fara cafkewa. Bincike yanayin nisa firgici da ruɗani na sake bayyana ga su forma president. Har wani zama na sirri suka ƙirkira da Ramadhan, bai musaba ya amshi baƙuncinsu, ya kuma saurari dukkan soki burutsinsu daya sake tabbatar masa lallai sune ke ƙulla komai kamar yanda yake hasashe shi da Raudha. Ƙin cemusu komai yayi hakan kuma sai ya ƙona ransu. Sunma rasa inda zasu saka hankalinsu suji daɗi dan sai tsinci ɗai-ɗai akema yaransu, abinda zai baka mamaki harda wanda suke cikin mulkin dumu-dumu. Ta ɓangare ɗaya suke ɗan jin sassauci idan suka tuna ta Ramadhan ta kusa ƙarewa tunda sunada tabbacin ya shaƙi gubar da suka shirya ya shaƙa ɗin ta shekaru biyu. Ya kuma sha a drinks sai dai ganin bai taɓa kwanciya ciwo ko canjawar jikinsaba na ɗan saka musu wasuwasi. Sai dai a randa suka bama zukatansu salama da wannan madogarar a ranar jami'an tsaro suka cafke Aunty Hannah a dalilin maganar drinks da kuku ya tabbatar itace ke bashi. Ranar Raudha taci kuka sosai, Ramadhan yayta aikin lallashi. Ya tabbatar mata dama sun gama da kammala wannan bincike shiyyasa aka cigaba da riƙe kuku. A ɓangaren Hajiyar Birni ma hankalinsu a tashe yake, dan Raudha ta kira tana kuka saboda zuwa yanzu kowane kafar yaɗa labarai babu wani sabon labari sai na kama matar vice president da ake zargi da haɗa kai da kuku domin halaka shugaban ƙasa. Asabe ma ta kira Raudha, hakan sai ya sake rikitata har Ramadhan yama rasa ta ina zai lallasheta. Kukan da taci ya jaza mata zazzaɓi sai da Dr Hauwa tazo dubata, a gwajin farko kuma ta tabbatar musu Raudha nada cikin wata biyu. Sake rikicema Ramadhan tayi, tayama za'ace tanada ciki bayan shekarar Abdull ɗaya da watanni huɗu. To shi dai abun yafi karfinsa. Ga rikicin mulki ga nata sai kawai ya haɗata da Anne............✍
Sister's duk wacce batayi anfani da sabulun mg's ba inamai shaidamuku anbarku acan baya domin duk wnd yajaraba mg's sai sanbarka duk wani Mai tantama Akan kayan gyaranjiki toh tabbas yacire sabulun mg's domin yahadu bakarya zegyarajiki yafidda dattin fata Dama duk wani matsalan fata duk Wanda kefama da matsalan fata walau pimples ko spot, sunburn acne,stretch mark dama dukkan wani prblm yajaraba mg's bi'iznillah komai zaizama labari bayan jikinku yy fresh zaisa jikinku yy smooth yadinga glowing,gawanda basa San anfani da Mai zaku iya using sabulu mg's batare da kunbukaci wani Mai b🤗nd guess what😍munyi upgrading kayanmu gbdy domin jindadinku🥰bama cika Baki kujaraba kugane ma idanku domin ance gani yakoriji Kuma siyan nagari maida kudi gida 💯 Natural/organic
maiso yy mgn 08062991549 07046881166 07067210195 Call 08064532391 Instagram:glow_with_mgs Facebook:mg's skincare
Masu bukatar cream Shima munadashi harda ma complete set nagyaranjiki komai da komai Akwai soap 3k Student package 7k Beauty kit 11k Bridal kit 18k
Munatura Kaya kowani gari dayardar Allah Amma delivery is not free
Be part of the glow team😍karkubari abaku lbr👏 *_Typing📲_*
*_Episode 78_*
..........“Tabbas dole Hannah ta mutu kafin a miƙata kotu”. Forma first lady ta faɗa tana duban su Alhaji Yaro glass dake tare da ita harma da god fathers nasu a yau. Mr MM da duk yake a firgice yay saurin faɗin, “Ina bayanki your excellency maa”. Gaba ɗaya falon dubansu suka maida ga Alhaji Yaro glass da tunda ya shigo baice komai ba, sai ma uban tagumi daya rafka. Numfashi yaja mai ƙarfi ganin sun dawo da kallonsu garesa alamar amsa suke nema. Yaɗan ɗage kafaɗa da yarfa hannuwa. “Ni a gareni babu matsala, da nasan ma wannan ranar zata zo da dakaina zan kashe Hannah tun kafin zuwanta. Dan tun randa case ɗin kuku ya shigo ya kamata a ɗauka wannan matakin, amma sai muka ɗauka hakan ba komai ba. Sai dai ku sani ba Hannah ce kawai zata mutu ba harda Kuku, dan kuwa Hannah da Bushira kuku ya sani ba Hannah kawai ba”. “Amma kasan shi ɗin ɗanane jinina ko?”. Cewar Forma first lady Bushira hamada a harzuƙe. “Nima ai Hannah matata ce, cewa a kasheta bashike nufin bana sonta ba. Sannan idan baku manta ba matar Ramadhan jinin Hannah ce, amma da akace zata iya mutuwa a cikin shirinmu batai jayyya ba, ashe kuwa indai nasara muke bukata dolene mu ɗanɗani ɗacin rashin jinanannmu koda kuwa ƴaƴan da muka haifane”. A take kowa ya goya bayan maganar Alhaji Yaro glass. Hakan yasa Hajiya Bushira hamada yin shiru. Oga kwata-kwata da baice komai ba sai da duk suka gama hayaniyarsu sannan yay gyaran murya. Dukansu hankali suka maida garesa. “Idan har ta kisan wane da wane ne zamubi ta hanyar rufe sirrikanmu mutane da yawa zasu mutu a wannan gaɓar. Dan haka ba shine mafita ba, babbar mafita a garemu yanzu harin maƙiyinmu kai tsaye. Ramadhan shine kawai zamu hara kai tsaye mu sami nasarar daƙile duk wata damuwarmu. Amma dan mun kashe su Hannah kamar mun kashe macijine bamu datse kansa ba, domin kuwa kisan nasu tamƙar buɗe hanyar da masu bincike suke nemace kai tsaye muka bayar. A take ɗakin taron ya ɗauka kananun hayaniya. Dan kuwa zantukan shugaba sun fargar dasu abinda basu hango a farko ba. Dan haka a daren yau basai gobe ba Ramadhan zai baƙunci lahira.....
“Idan shi bai baƙunceta ba, ku zaku baƙunceta ai”. Cewar Alhaji Balarabe Andu daya daɗe tare da su da fuska biyu. Alhaji Balarabe Andu tsohon jami'i ne da tun komawar tsohon shugaban kasa Usama D. Hamada mulki na biyu ya shigo jikinsu. Koda yake zamu iya cewa tun a mulkin farko ma yana tare da su, sai dai basu sakin jiki da shi har sai lokacin mulki na biyu da suka tabbatat yana tare da tafiyarsu. Tun usul ya shigo tawagarne akan binciken wani gagarumin ƙulli da akai a wancan mulkin, sun buga sun buga suka kasa gane kansa. Shine yay shigar burtu ya zama ɗaya daga cikinsu. Yaso barinsu bayan kammala mulkin Usama D. Hamada, sai dai ƙullin da suka fara akan daura Alhaji Hameed Taura a mulki ya sashi dakatawa. Duk abinda suke yana biye da su, hatta da ac da suka saka poison a ciki na gidan gwamnati yaso zama silar da zai sa a cire sai Raudha ta rigasa, amma da taimakonsa su bappi suka cire batare da suma sun sani ba. Ya cigaba da tattara bayanan sirri akansu batare da sun sani ba, kuma ko ayanzu da aketa faman kama musu yara duk da saka hanunsa a ciki.... A firgice duk suke kallon Alhaji Balarabe Andu, dan wasunsu sun ɗauki abin wasa ne ko almara ko subutar baki, “Alhaji balarabe kasan mi kake faɗa kuwa?”. Cewar Alhaji Haladu Gwandu. Alhaji Balarabe yay wani murmushi tare da rausayar da kai gefe ya tafa hannayensa yana kallon Alhaji Haladu Gwandu batare da yace komai ba. A take jami'an tsaro suka shigo falon suka zagayesu su da makaman da suka tile a tsakkiyar falon wanda a yau ɗin nan aka iso da su ƙasar NAYA.....
★Cikin ƙanƙanin lokaci ƙasar NAYA da kewaye ta ɗauki sabon labari na kama waɗan nan manyan mutane da wasun su ko'a hasashen zuciya bata taɓa kawo zasu aikata abinda ake zarginsu da shi ba. Bakin ƴan siyasa ya buɗe ta ko'ina bakajin komai sai kace nace. Abinda ma ya takaice kace nacen tsayawa akan jam'iyya mai mulki kawai waɗan nan mutane gaba ɗayansu suna tarayya ne a cikin mabanbanta jam'iyyu. Hakan na nufin kenan dama ƴan siyasa da yawansu a bayan fage kanwunansu a haɗe yake a zahiri kuma suyita gwara kan talakawan ƙasa da sasu luguden laɓɓa batare da sun hankalta ba. (Ƴan uwa idan zamuyi soyayya muyita dan ALLAH kuma saisa-saisa. Hakama kiyayya muyita saisa-saisa kuma domin ALLAH musamman irin ta siyasa. ALLAH yasa mu cika da imani).
A yinin wannan rana kawai hankalin al'ummar ƙasar NAYA ya dawo kan shugaban ƙasa Ramadhan. Aka dinga sanbarka a garesa da wanke laifukan da ake kallonsa da su. Yayinda wasu keta faman bankaɗe-bankaɗen abubuwanma da ba'asan da su ba sai yanzu. A wani fanin Raudha na farin ciki, wani fanin kuwa tana baƙin cikin kasancewar yayar mahaifiyarta cikin tawagar waɗannan azzalumai. Ga laulayin ciki mai wahala da take fama da shi a wannan karon. Ga karatunsu ya ɗau zafi dan suna lavel 3 ne. har zuwa yanzu kuma bata taɓa kuskuren nunama wani ita wacece ba. Abdull bada shi take zuwa makaranta ba. Gida ake barinsa wajen Mama Ladi. Dama Alhmdllhi yana ɗan takawa zuwa yanzun, damma haƙora na maidashi baya idan yay zazzaɓi. Bayyanar cikin nan na Raudha kuma yasa Anne zuwa ta ɗaukesa a gidan ma baki ɗaya ya koma Taura House yaye. Sudai basu da ikon cewa komai, amma gimbiya Su'adah taji haushi dan ta ƙullama ranta itama abinda akai mata na ƙwace Ramadhan saita kwace Abdull, sai gashi Anne ta sake mata kwaf ɗaya kafin ta farga ta ɗauke ita (🤣😂Bashin gaba lol).
★★________★★★________★★
Rayuwa ta cigaba da shurawa su Alhaji Haladu Gwandu na cigaba da zama a tsare a gidan yari, a gefe kuma ana sauraren ƙararsu a kotuna mabanbanta saboda laifukan nasu sunzo daban-daban. Kowanne akwai babban laifin da yake shugabanta da ake tuhumarsa a kansa kai tsaye. Wanda sukai tarayya akai shine cin hanci da rashawa da shigo da makamai.
Ɓangaren shugaban ƙasa kam zamuce abubuwa sun fara dai-daita, domin ɓarnakun da tashe-tashen hankali ya kawo su akebi ana gyarawa kafin a ɗora sauran ayyukan da aka fara. A gefe kuma ya sake samun kwanciyar hankalin kasancewa da matarsa abar sonsa da alfaharinsa ƴar darunsa kuma dake fama da ciki. A haka ALLAH ya sake saukar Raudha lafiya, a wannan karon kam da kanta ta haihu yaronta namiji again, shima yaci sunan Pa wato Basheer. Suna kiransa Alhaji ƙarami. Duk da Ramadhan yaso kar ai taron suna dan bai manta abinda ya faru ana Abdull ba su Bappi sukace sai anyi. Haka dai akayi taro mai kayatarwa anan ɗin ma Raudha ta cigaba da shayar da yaronta. Yankema su Alhaji Usama D. Hamada tsohon president hukunci dai-dai da abinda suka aikata yayi dai-dai da sake kaɗa tamburan siyasa. Dan hatta yunƙurin kisan Ramadhan da sukai tsautsayi ya koma kan Amnah ɗiyar Alhaji Haladu Gwandu sai da jami'in tsaro Balarabe ya fallasa. Wannan hukunci da aka yankema waɗannan azzalumai ya zama makamin campaign na Ramadhan a wannan lokaci, dan kuwa yanda abubuwa ke tafiya bama sai ance maka shine zaiyi nasara ba kowace alama ta nuna hakan. Sai kuma wani babban abin farin ciki da Ramadhan ɗin ya aywatar a wannan lokaci shine hana bangar siyasa yin tasiri a ciki dabai na ƙasar NAYA. Duk ɗan siyasar da aka samu ya bama yara makamai ko kayan maye domin masa campaign ko makamancin hakan to takararsa ta ruguje bazaiyiba. Wannan al'amari shine ya saka ƴan siyasar shiga hankalinsu, matasan kuma dama mafiya yawansu sunda aikinyi wasu sabo dayine da kuma shegen kwaɗayi ke ingiza zukatansu. Alhmdllhi campaign ya wanzu cikin nutsuwa da burgewa, inda har akai aka gama babu wanda yaga matar shugaban ƙasa ko da a poster. Sai dai Ramadhan yasha fita da Abdull da Alhaji ƙarami da shima yake neman cika shekara guda da haihuwa. Zuwa yanzu mutane da yawa sun fahimci shugaban ƙasa Ramadhan baya ra'ayin matarsa a harkokin siyasa ne kawai, yana kishinta yana killace abarsa matsayin tashi shi kaɗai. Hakan ya matuƙar birege mutane, harma a wannan campaign ɗin wasu ƴan siyasar sukai koyi da hakan musamman ƴan takarkaru. Dan hatta abubuwan alkairi da Raudha ke shimfidawa a bayan fage bazaka taɓajinsa a bayyane wa duniya ba, acewarta tayine domin ALLAH badan wani ya sani koya yaba mata ba. Mijinta kuma ya bata goyon baya ɗari bisa ɗari.
Alhmdllhi an gama campaign lafiya ankumayi zaɓe shima. Yayinda sakamakon zaɓe ya tabbatar da sake zaman *_Ramadhan B. Hameed Taura_* matsayin shugaban ƙasa a karo na biyu a ƙasar NAYA. Duk wani masoyinsa ya tayasu murna da fatan sauke nauyin al'umma a kansu. Inda a wannan karon ya shigo sabon tsarin da sabon tsare-tsare da ƙudirirrika na musamman. Yayi sauye-sauyen wasu a cikin ministers da suka kasance zabin su Alhaji Yaro glass a wancan karon. Hakama vice president an sake sabo tunda su Alhaji Yaro ana can ana cin gabza a prison😝. Rantsar da shugaban ƙasa baifi da sati uku ba su Raudha sukai GRADUATION a makaranta. A kuma lokacin ta bayyanama school mate nata ko ita ɗin wacece. Ansha mamaki, ansha al'ajab da kace nace ga ƙasar NAYA ma ba makarantar kawai ba. Gaba ɗaya hidimar bikin fitar tasu ita ta ɗauki nauyin komai. Ansha hotuna na tarihi kowa burinsa firt lady karta manta da shi duk da bata yarda ta buɗe fuskarta ba ko a wajen bikin kamar yanda Ramadhan ya bada doka. Yadai yarje mata ta sanar dasu ko ita wacece kawai.. A randa suka kamma bikin gama karatu a ranar ta sake fahimtar tana da ciki, taci kukanta tai gum da bakinta, sai dai batasan mai gayya mai aiki shi ya san da abunsaba tunkan ta sani. Sai ranar kawai yake bayyana mata ta gama boye-boyenta shi ya jima da sanin ya samo ribar farautarsa ai. Galala tai tana kallonsa, shiko yay mata gwalo ya fice. Jitai kamar ta zauna taita kuka kawai. Ita wannan wane irin abune bata yaye yara sai sabon ciki. To babu yanda aka iya da hukuncin ALLAH, wasuma nema suke basu samu ba da kuɗi. Tun tana zumbure-zumɓurenta harta ware suka cigaba da rainon ciki Mama Ladi ta yaye Alhaji Ƙarami. A randa Raudha ta haihu a ranar ALLAH yayma Addah Asmah dake fama da jiyya har yanzu rasuwa. Ba kowa yaji mutuwarba. Dan dama masu jiyyar tata sun matuƙar gajiya. Yanda bata nema yafiyar kowaba babu wanda yace ya yafe matan har gimbiya Su'adah da yanzu akai sanyi. Bata sakema Raudha dai bakuma ta takura mata. Babbar damuwarta ma yanzu zaman Lubnah a gida da Muneera da a yanzu ta koma sai wheelchair saboda ƙafarta ta samu matsala a wancan haɗarin. Har kuɗi da gida da mota aka saka ga wanda zai auri Muneera amma duk wanda yazo ya ganta saboda raunikan da tayi a fuska sun canja mata kamani sai ya gudu. Bilkisu kuwa tuni harta haihu abinta ita da su Fatisa. Yanzu hakama shirye-shiryen bikin su Basma akeyi.
A wannan karon dai Ramadhan ya dage baza'ai bikin suna ba, ya dai ɗauke matarsa bayan arba'in sukai tafitarsu America domin hutawa na sati biyu tare da yaransu uku vice president ya cigaba da riƙe ƙasar NAYA kafin ya dawo. Dan jinjirin shima yaci sunan Mal. Dauda. amma suna kiransa Dawood. Raudha da Ramadhan na cemasa Abbati. Satinsu biyu suka dawo NAYA harkokin mulki suka cigaba da tafiya yanda akai fata...........✍
*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻♀️⛹🏻♀️😘_*
*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*
*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_
*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_
*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_
*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_
*1*~ *_NOOR ALBI_*❤🔥 _Mamuhgee_
Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k
*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*
Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank
Number shaidar biya👇🏼
*_09032345899_*
*KATIN MTN*👇👇
09166221261 __________________
*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*
Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F
*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼
+227 95 16 61 77
*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*
_____________________
*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*
Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.
_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*
https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com
*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*
*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*
+234 903 177 4742
_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_* *_Typing📲_*
*_Episode 79_*
...........*_BAYAN SHEKARU BIYAR_*
Alhmdllhi abubuwa da yawa sun faru na cigaba a cikin waɗannan shekaru daga mulkin shugaban ƙasa Ramadhan. Ciki harda haihuwa da Raudha ta ƙara har sau uku. Bayan Dawood tayi ƴammata biyu tagwaye da sukaci sunan Saleeha da Zainab. Ta kuma sake Hauwa'u, sai auta da yaci sunan mai-martaba suna kiransa Saraki. Babu abinda ƴan ƙasa zasuce sai sambarka. Dan kafin shekarun mulkin Ramadhan su kammala ya shimfiɗa manyan ayyukan da har abada baza'a manta da shugabanci irin nasa ba. Daɗin daɗawa bai saukaba sai da ya gyara wasu da yawa a dokokin kundin tsarin mulkin kasar NAYA. Ciki harda dokar shugabanci. Duk shugaban da ya haura shekara sittin bazaiyi mulkin ƙasar NAYA ba koda kansila ne. A kowace ma'aikata ana son kaso biyu bisa uku matasa su sami rinjayen samun aiki bawai lallai sai a manya ofisoshi ba. Kokai wanene kar'a baka aiki a gurbin da baka cancanta ba. Babu wani ɗan siyasa da zai tilasta ƴan ƙasa amsar zaɓinsa a kowace jam'iyya sai wanda takalawan kasa suka zaɓa. Duk ɗan siyasar daya tara matasa da kayan maye da makamai domin bangar siyasa bashi ba mulki har abada. Duk shugaban daya hau mulki dolene ya tsaya akan lafiya, tsaro, ilimin ƴan ƙasa da samar da aikin yi koda ta kananun hanyoyi ne ba lallai sai manya ba. Babu wani shugaba da zai gama mulkin gwamna ya koma mulkin majalisa. Daga mulkin gwamna kanada zaɓi na neman takarar shugaban kasa ne kawai koka koma gefe ka saka ido tunda mulkin ba dole bane. Waɗan nan dokoki sun gamasar sun kuma saka jama'ar ƙasar NAYA farin ciki matuƙa. Aka dinga masa addu'a da fatan alkairi da sambarka. Wasu harda kukansu a randa ya miƙa mulki ga sabon shugaban ƙasa da yaci zabe wanda shima shekarunsa basu wuce arba'in ba kacal. Ramadhan da Raudha sunyi bankwana da jama'ar kasar NAYA suna kuka da neman gafarar kowa suma harda Abdull mai shekaru tara a duniya daya fara zama ɗan saurayi abinsa. Hakama kanensa ganin iyayensu na kuka da yayansu sai suka dingayi suna dagama al'ummar ƙasar naya hannu alamar bankwana garesu.
(Kai ALLAH sai naji kamar gaske nima sai da nai kuka😭😂🙏🏻)