Kenza eBookz

Bakar inuwa book 1 - Chapter 37

Bakar inuwa book 1 - Chapter 37

Bakar inuwa book 1 Chapter 37: Bakar inuwa book 1 Chapter 37. Koda forma president Ramadhan B. Hameed Taura ya iso Taura house da tawagar masu rakiya…

3,127 words

Koda forma president Ramadhan B. Hameed Taura ya iso Taura house da tawagar masu rakiya talakawa da abokan mulki da iyalansa tarba suka samu mai girma daga su Anne da tsufa ya ƙara kamawa. Hakama kanensa dake gidan aure kaf suna gidan. Ya rungume su Bappi yana mai zubda hawayen farin cikin sauke nauyi da fatan ALLAH yasa bai taho da hakkin kowa a kansa ba. Sosai mutanen wajen suma suka sake shiga matsar kwalla duk da Ramadhan ɗin ya sakasu wani acan gidan gwamnati kafin su iso nan dama. Anyi addu'oi godiya ga UBANGIJI, Ramadhan ya sake mika godiyarsa ga su cos da wasu manyan muƙarabbansa da alkairinsu bazai iya musltuwa da baki a garesa ba. Akaci akasha aka sake addu'ar bankwana kowa ya kama gabansa. Daga Raudha har Ramadhan zazzaɓi suka kwanta har kusan sati, dan har Ramadhan na tsokanar Raudha kodai ciki ne tace ALLAH ya kiyaye tayi kenan. Ganin alhini yaƙi sakinsu Bappi ya bashi shawarar daukar iyalan nasa suje su huta.

Haka kuwa akai, Ramadhan ya tattara ƴaƴansa da matarsa suka wuce ƙasashen duniya shakatawa. Bayan sun ɗan zazzaga suka yada zango a ƙasar America inda yafi wayo. Sun sami tarba ta musamman ga abokansa da abokan kasuwanci ciki harda Sultana datai haƙuri yanzu haka itama yaranta biyu da A.J. Rayuwar America rayuwace da Raudha da Ramadhan bazasu taɓa mantawa da itaba. Dan kuwa ta riskesune batare da hayaniyar komai ba kasancewar a baya harkokin mulki na yawan cinye lokutansu. Yanzu ko idan yaran suka nema shiga musu hancima tuni suke tattarasu su aika gidan A.J ko Mufeed ko Sultana. Babu abinda suke sai more ƙara'in amarcinsu da basu sami damar yi a baya ba duk da yanzu kam akwai nauyi na ƴaƴa da canjawar abubuwa da yawa na rayuwa. Dan kuwa dai da gaske Raudha ta koma yar lukuta (kamar bilyn Abdull😂😝👍🏻lol). Shi kansa mai gayya da aikin ƙibar yayi harda tumbi dake tabbatar da shekarun kuruciya sun fara nisa a garesa, dan kuwa arba'in da biyar yake tunkara yanzu. Yayinda Raudhansa ke tunkarar ashirin da takwas. Amma yanda ta buɗe ta zama babbar mace sai kace takai talatin da biyar. (Mace kenan ai, da zarar ka haihu kuma ai sai addu'a. Kai kobaka haihunba inhar akace an wuce shekarun nan na ƙuruciya sai sambarka, duk da dai akwai masu karamin jiki da zakagansu duf-duf abinsu masha ALLAH. Koma dai miye kowa da irin halittar da ALLAH ya tsara masa).

_________________________

Watansu biyu kenan da baro gidan gwamnati, suna dawowa daga America suka sake dawowa Taura house dan Ramadhan baida sha'awar zama wani gida daban sai cikin family nashi, musamman da yanzu gidan ya koma iyayen sune kawai kasancewar kowa yayi aure kanensa dan Muneera ma dai ALLAH ya iyakance mata tayi auren zuwa yanzun, hakama Lubnah tayi itama. Sai jikoki idan sunzo musu hutun weekend. Shine namiji dole ƴaƴansane zasu kasance a gidan famanet, dan haka ko a yanzu bada wani ra'ayin gina gida ko saye balle tunanin komawa. Ita kanta Raudha nan ɗin yafi mata daɗi tunda tun usil ta rayune a cikin family house. Wasu abubuwan sun canju, wasu ko ALLAH daya halicci bayinsa akansu kawai ne ka iya canjawarsu. Dan kuwa har zuwa yanzu babu wata shaƙuwa tsakanin Raudha da Gimbiya Su'adah. Sai dai tana nuna son su Abdull kam. Hakan yasa Raudha batajin komai a ranta tunda dai su Abdull jinintane ya wadatar sonsu ya zama ƙauna tsakaninta da surukar tata mai murɗaɗɗen hali. Sosai Bappi da Anne tsufa ya sake baibayesu, dan Yafendo ma tana fama da jiyya a yanzu. Hakama Inna ta Hutawa ALLAH yay mata rasuwa, yayinda shima M. Dauda ke fama da ciwon hanta sakamakon shaye-shaye sigarinsa. Raudha tsaye take akan maganinsa amma al'amarin nasa dai sai addu'a kawai.

A ɓangaren su Hajiyar Birni itama dai tana fama da ƙafa sosai, dan takai yanzu ko'inama bata iya zuwa. Har ƙasar indiya Raudha tasa aka fita da ita taga likita. Sai dai an samu sauki amma ba'a warke ba abinka da harda tsufa. Hajiya Mama ma ta koma gidan mijinta na farko, hakam Asabe na zaune lafiya da mijinta da ƴaƴansa. Dan a yanzu hakama shirye-shiryen auren babban ɗan Alhaji Sageer Dogarai da Yasmin akeyi saboda sun dai-daita kansu. Babu abinda Asabe zatace da ALLAH itakam sai godiya. Ga su Fatisa na zamansu lafiya a gidan aurensu suma da yaransu abin sha'awa. Taga ribar yin tuba na gaskiya da dogaro ga ALLAH da maida dukkan lamura garesa.

Ga yan prison kam sai muce ALLAH ya cigaba da rabamu da halayya irin tasu ta masu san zuciya, wasunsu baƙin ciki yasa zukatansu bugawa tuni sun bakunci lahira, dan kuwa da ransu ga Ramadhan na mulkin kasar NAYA amma basu da ikon ko ganinsa sai dai su karanta a jarida, wanda suka kai labari kuwa yanda ya sauka cikin salama ƴan ƙasa na kuka da begensa yay mugun haddasa musu ciwon zukata a dalilin hawan jini suma sukace ga garinku nan. Irin su Bushira Hamada da suka rage da rai rayuwar kawai ake cikin baƙin ciki dajin garama a mutu a huta da kallon wani takaicin da baƙin cikin rayuwar. dan a yanzu haka Aunty Hannah fama take da jiyya sakamakon zaftare kafa datai da fatanya wajen yin aiki cancer ta shigeta. Har prison ɗin Raudha takai mata likita na zuwa dubata lokaci-lokaci dan su Asabe kan kanje busting nata, itama Raudha ta taɓa zuwa sau ɗaya lokacin suna kan mulki. Bushira Hamada wai zata kashe Raudha aiko taci duka ranar hanun jami'an gidan prison ɗin. Daga lokacin Ramadhan ya hanata zuwa takuma bi maganar mijinta bata sake zuwa ba sai bayan saukarsu taje harda yara suka duba Aunty Hannah ɗin saboda jikin yayi tsanani sosai.

A hutawa ma dai komai Alhmdllhi, idan ka cire ciwon M. Dauda dake fama da shi, duk da dai yana samun kulawa Alhamdulillahi. Sai dai Rasuwar Inna data gitta ce ta girgiza kowa Har Raudha da Ramadhan dama jama'ar Taura Family duka sun mata halacci sunje harda Gimbiya Su'adah a karo na farko. Hakan yama Raudha daɗi, dan bayan sadakar bakwai data dawo har ɗaki taje taima gimbiya Su'adah godiya.

Rasuwar Inna baifi da watanni biyu ba Fulani ma ta rasu, nanma dai sun girgiza suka dunguma masautar Bina. Inda su Aynah dake zaune yanzu a masarauta itama dai tana fama da ciwo saboda abinda abokan Aminu sukai mata tun wancan lokacin yafi tabata, dan tasan dai Fulanin ce kawai ta rage gatanta kanwarta Zulfah tunda ta samu tai aure bawani zuwa takeba sosai sai hadimai ke dawainiya da ita saboda tsoron Fulani. Yanzuko babu fulani sai abinda ALLAH yayi kuma kenan tunda Hadiman ba tsoronta sukeba kamar da da idan tazo take takasu kamar itace ta haliccesu. Babanta ko tuni yayi aurensa yana zaune lafiya da matarsa dan harta haifa masa yara biyu maza kyawawa da yaketa alfahari da abinsa. Zulfah dai na tare da shi da matarsa dan ta ɗauketa uwa ita babu ruwanta.......✍ *_Typing📲_*

*_Episode 80 END_*

...........Cikin sauri-sauri take ƙarasa shirin nata. Tayi matuƙar ƙyau cikin ɗanyan shadda da taji wadataccen aiki. Sosai ta zama babbar mace da duk inda ta gitta dole ne a bata girma kodan yanda take cika idon mai kallo. Kwalbar turaren hanunta ta ajiye tana mai juyiwa jin an buɗe ƙofar ɗakin. Batai magana ba, sai dai ta tsurama ƙyaƙyƙyawar yarinyar da bazata wuce 4years ido ganin yanda taketa faman tura baki gaba cike da shagwaɓa. Sanin halin ɗiyar tata ya sakata takowa a hankali gareta, ta amshi bowl ɗin hanunta tana kallon abinda ke ciki. “Zee miya faru?”. Sake ɓata fuska yarinyar tai hawaye na ciko mata ido. A shagwaɓe tace, “Mamie ba Daddy bane da Saleeha suka cinye min”. Kai Raudha ta dafe, a zuciyarta tana tunanin yaya zatai da Ramadhan a gidan nan itako akan cin nama, ƙoƙari take duk yanda zata hanashi ci kamar yanda likita ya saka masa doka. Shiko yasan duk hanyar da zaibi yacisa. Komai batace ba ta kama hanun Zainab suka fita. Kai tsaye falonsa ta nufa inda take jiyo ƙiriniyar Jiddah da Saraki. Dan su Abdull sun wuce Islamiyya. Zee ɗin ma dan bata da lafiyane bataje ba, itako Saleeha ganin Zee bazataba itama ta maƙale.

Kwance yake a tsakkiyar lallausan carpet ɗin falon, Jiddah da Saraki nata tsalle a kansa. Tun kan ta ƙaraso ƙamshinta ya sanar masa. Saraki ya sauka daga kansa da gudu ya nufeta. Ɗaukarsa tai tare da subatar kumatun autan nata. Shima ya sumbaceta da faɗin “I love you Mamie”. “I love you too Darling”. Ta faɗa cikin shafa kansa tana murmushi Fuska Jiddah ta ɓata tana hararan saraki, hakan yasa Ramadhan faɗaɗa murmushinsa tare da sumbatar goshinta itama yace “I love you sweetheart ”. Dariya Jiddah ta sanya. Ta rungume Daddyn nasu tana faɗin “I love you too Daddyn mu”. Raudha dake kaiwa zaune tai murmushi da girgiza kanta. Sai kuma ta ɗan taɓe baki da faɗin, “Duk mai kishi da autana dai zai rame a gidan nan”. Tashi zaune Ramadhan yayi sosai yana murmushi shima idonsa akan matar tasa, dan kwalliyar tata ta tafi dashi sosai. Kai kace wata anguwa zata. Ido ya kashe mata cike da salo yanda yaran bazasu gane ba. Itako ta hararesa tana nuna bowl ɗin hanun Zee daketa ɓata fuska. Idanu ya waro sosai tare da miƙewa ya koma saman kujera idonsa akan Zee. “Zee yaushe kika fara gulma a gidan nan? Mi kikaje ki ka ce?”. Cikin shagwaɓa Zee tace, “Daddy bakaine ka cimun dambun nama ba da Saleeha, kuma Mamie tace indai kaci na faɗa mata”. Sake waro idanun yay akan Raudha, “Ustazah wannan haɗin faɗan fa?”. Fuska ta marairaice masa sosai, a hankali tace, “Dan ALLAH ka daure kabi dokan Doctor, yaushe ka gama shan wahala, sugar ɗinka a shekaran nan kullum sama yake ba ƙasaba Please Noorullah”. Murmushi yayi yana kauda kansa. “Ko naci ko banci ba zan mutune Partner. Mizaisa naita azabtar da kaina wajen ƙin cin abinda nake so. Komai inabin dokarsa ai amma bazan iya ƙin cin nama ba gaskiya”. Ido kawai ta tsura masa kamar zatai kuka. Dan ita kam batasan taya zata masa bayani ya dinga fahimtarta ba. Su Pa nada sugar amma da yake suna bin doka nasu bai tsanani ba. Shiko sam yaƙi daina cin nama, gashi baya masa cin sauƙi, inhar ya samu zai masa cin tuwo ne. Kuma in zaici safe rana dare bazai gaji ba. Ganin yaƙi yarda su haɗa ido ta ɗauke kanta tana duban Zee da tuni ta ajiye bowl ɗin naman ta koma tsalle-tsalle tare da su Saraki. “Zee ina Saleeha?”. Kafin Zee ta bada amsa Jiddah ta amshe da faɗin, “Taje wajen Granny Mamie”. Kowa a gidan yasan a gidan Saleeha ƴar ɗakin Maah ce, dan ita da Dawood (Abbati) ma basa kwana ko'ina sai can, hatta kayan sakawarsu kashi biyu bisa uku nacan. Itako ji take da su kamar mi. Abdull kuwa na gaban goshin Anne ne kowa ya sani. Cikin ɗan sauke numfashi Raudha tace, “Okay Zee ki ɗauka bowl ɗin can na saman dining kuje har auta a kaima Granny, ai an kaima Anne nata ko?”. “Eh Ya Abdull ya kai mata da zasuje islamiyya”. Cewar Jiddah.

Suna fita Raudha ta mike ta koma kusa da Ramadhan daya maida hankalinsa akan labarai da ake nunawa a tv. “Wai fushi kake dan nace ka daina cin nama?”. Hararta yayi ya ɗauke kansa. Da sauri ta taro fuskarsa cikin hanunta ta hura masa iska ganin zai lumshe ido. “Noorullah Please ka fahimceni, rayuwarka nada muhimmanci a gareni da yaranmu dama duk jama'ar gidan nan. Ina fatan yanda su Bappi sukaga yaranmu muma muga yaran su Abdul haka a duniya. Please sweetheart i love you more”. Murmushi ya sakar mata mai sanyi, shima ya tallafo muskar tata. Shanyayyun idanunsa ya zuba mata, “My Heartbeat kinyi ƙyau”. Ƙaramar harara ta sakar masa ganin zai kautar da wancen zancen. Ta buɗe baki zatai magana ya manne lips nashi. Idanu ta lumshe a hankali kamar yanda shima ya lumshe nashi, ta san kuma ƙarshen maganar kenan dan haka yake mata a duk lokacin data ɗakko masa irinta. Sunyi matuƙar nisa a faranta ran juna sallamar su Abdull ya ziyarci kunnuwansu. A hankali Raudha ta janye jikinta, shima janyewar yay ya kwanta jikin kujera yana mai lumshe idanunsa da shafa kansa. Sai da ta saisaita kanta ta basu izinin shigowa kamar yanda suka horesu. A nutse matasan samarin uku suka shigo cikin fararen kayan Uniform. A nutse suka gaishe da iyayen nasu, Abdull ɗan shekaru goma sha ɗaya da hankalinsa ke kan Daddynsu ya kai zaune gefensa cikin damuwa. “Daddy baka da lafiya ne?”. Murmushi Ramadhan ya saki, a hankali ya shafa kan Abdull yana ƙoƙarin saisaita kansa. Muryarsa a dasashe kamar wanda mura take son kamawa ya girgiza masa kai. “Lafiya lau nake My son. Kawai dai inajin barci ne?”. Abdull yay ɗan murmushi, cikin nutsuwarsa kamar wani babba ya ce, “Oh Daddy babu ƙyau barcin la'asar fa”. “Ai bazanyi ba My dear. Kuje ku canja kaya kuyi alwala ku jirani muje Mosque. A kira Auta ma yana sashen Granny”. Yay maganar yana shafa kan Abbati da Alhaji ƙarami da suka lafe masa a jiki suma. “Okay Daddynmu”. Abbati ya faɗa cikin ƙiriniyarsa dan kam shi dai babu sauƙine. Yanzun ma shirun nasa nada nasaba da dukansa da Raudha tayi kafin su wuce islamiyya saboda yayi faɗa da Alhaji ƙarami.

Suna fita Ramadhan ya dubi Raudha yana murmushi. “Kinsa Abbana duk yayi laushi kamar bashi ba”. Murmushi tai itama tana ƙoƙarin miƙewa. “Daban masa hakaba da yanzu da gudu zai shigo mana kuma faɗan har islamiyya za'aje anayi dan nacinsa. Nikam dai idan ya biyo darun Abba (Mal. Dauda) wahala zaici”. Dariya sosai Ramadhan yayi, tare da kamo hanunta ya maidata ya zaunar. Rungumeta yay cikin raɗa da sakar mata kisses a gefen wuya. “Muje daga ciki kiji wani labari”. Cikin ɗan waro ido da ture kansa “Kai Ya Ramadhan sallafa kacema yara zaku”. “Wayo na musu ai, dan bazan iya sallar nan a hakaba kuma da sauran lokaci ai”. “Wai miyasa kakemin hakane? Duk sanda nai kwalliyata saika bata”. Tai maganar murya a narke cikin shagwaɓa. “Tukuyci nake badawa ai, tunda dama ni akaimawa ko”. Zatai magana ya sake rufe mata baki ya hanata. Babu yanda ta'iya dole ta amshesa hannu biyu. Daga ƙarshe suka shige bedroom.✍

Hummmm bari dai na tsaya daga nan kar bin ƙwaƙwƙwafin yay yawa kuma😜.

*_ALHAMDULILLAHI! ALHAMDULILLAHI!! ALHAMDULILLAHI!!!_*

_Godiya ta tabbata ga UBANGIJI daya bani dama da rai da lafiyar rubuta wannan ɗan littafi. Abinda na rubuta dai-dai ALLAH ya bamu ladan baki ɗaya. Wanda nai kuskure ALLAH ka yafemin ni da ku da kuka karanta._

*Kamar ko yaushe ina neman afuwan duk wanda na ɓatamawa a yayin rubuta wannan littafin. A yafemin, a yafemin, a yafemin. Nima duk wanda ya ɓatamin na yafe masa, sai dai banda wanda ya zalinceni akan ganganci ko son zuciyarsa. Shima inhar yazo ya roƙa gafarata ya sanarmin zan iya yafe masa da fatan zai kiyaye gaba. Zata iya yuwuwa wannan shine littafi na karshe da bilyn Abdull zata rubuta a duniyar rubutu😭🙏🏻 babu ruwan mutuwa dauka take a duk sanda taso.

*_Bazamu gaji da godiya a garekuba masoyanmu, kun nuna mana halacci kamar yanda kuka saba. ALLAH ya saka muku da alkairi ya bar zuminci, alkairin ALLAH yakai gareku a duk duniyar da kuke. Zafafa biyar na muku son so irin trillions ɗin nan wlhy. ALLAH ya saka da alkairi musamman wanda ke tare da mu tun farkon zafafa har zuwa yau. Kai harma wanda suka fara binmu yanzu duka mun gode sosai🙏🏻_*

_Kamar yanda na faɗa BAƘAR INUWA ƙirƙirarran labarine. Idan kaci karo da abinda yay kamanceceniya da rayuwarka kayi haƙuri bakai din ake nufi ba. Sannan bazan gaji da sanar da mai karatu cewar littafi nishadi ne, faɗakarwa ce, harma da ban haushi. Idan kaci karo da nishaɗi kayi badan dole saika samesa ba ko ka nema. Idan kaci karo da ilimi ka amfana gwargwadon fahimtarka. Idan abin haushine ka ɗauka adon labari ne. Rayuwar novel bawai babu ita a zahiri bane, sai dai ba lallai kowa ya sameta 100% kamar littafin ba, idan ma ka samu kasa a ranka akwai ƙaddara da jabawar da zata iya banbanta da hikayoyin marubuta_.

*Abinda kaso gani baka gani na rubuta ba amin afuwa ajizancine irin na ɗan adam da mantuwa. Wanda yazo ba'a yanda kaso ba shima kayi haƙuri ba komai ake samu a yanda ake son gani ba. ALLAH ya sadamu da alkairinsa a zafafa karo na 7 da zasu zo muku nan kusa insha ALLAH😘😘😘😘🙏🏻👍🏻*

*Mallakin Bilkisu Ibrahim musa (Bilyn Abdull)*

*_Yi ƙoƙari ka biya na kuɗi ne, kar kuci hakkin daba naku ba_*

*_Ku garzaya AREWABOOKS ta app ɗin dake a play store, domin samun pages fiye da wanda kuke gani a WhatsApp da zaran kinyi Searching littafin BAƘAR INUWA ⛹🏻‍♀️⛹🏻‍♀️😘_*

*_ZAFAFA BIYAR (5) ZAZZAFAR TAFIYA🔥🔥👇👇👇_*

*1*~ *_KUFAN WUTA_*🔥 _Safiyya Huguma_

*1*~ *_BAQAR INUWA_*💥 _Billyn Abdul_

*1*~ *_RAYUWAR MACE_*💅 _Hafsat Rano_

*1*~ *_MASARAUTA_*💪 _Miss Xoxo_

*1*~ *_NOOR ALBI_*❤‍🔥 _Mamuhgee_

Guda 1👉300 Guda 2👉400 Guda 3👉500 Guda 4👉700 Guda 5👉1k

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANAN👇👇_*

Bilkisu Ibrahim Musa 1487616276 Access bank

Number shaidar biya👇🏼

*_09032345899_*

*KATIN MTN*👇👇

09166221261 __________________

*_JAMA'AR JIGER zaku iya biyan kuɗin littatafan ZAFAFA BIYAR kuma ta nan👇🏼_*

Guda daya=300F Guda biyu=400F Uku=500F Hudu=700F Biyar=1000F

*ZAKU TURA KATIN WAYA NA (MOOV ko AIRTEL) ZUWA WANNAN NUMBER,TARE DA SHAIDAR BIYA*👇🏼

+227 95 16 61 77

*_TEAM ZAFAFABIYAR🔥🔥🔥🔥_*

_____________________

*_BAƘAR INUWA...👇🏻_*

Da ɗumi-ɗuminsa💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

Please *_Follow me_* *_Share_* *_Comments_* akan abinda ya shige maka duhu.

_AREWABOOKS, dan zaku dinga samun sabbin pages galla-galla akan lokaci insha ALLAH. Maza garzaya ka karanta naka hankali kwance. Ka kuma yi following ɗina ko dan kar ayi babu kai, da a baka labari gwara ka bayar🥰🥰🤝🏻👇🏻_

*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks💃🏻😂.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

*_AREWABOOKS LINK kai tsaye_*

https://arewabooks.com/book?id=620032232dff83519bbad5a3

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu https://arewabooks.com

*_Kuzo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin gyara tafiyarmu. Koba komai ɗan uwanmu ne bahaushe ya zauna ya tsara ya kuma buɗe App... Ɗin domin cigabanmu da jin daɗinmu. Wannan abin alfaharine_.*

*_MARUBUTA DAKE NEMAN ƘARIN BAYANI KO MASU KARATUN MA, ZAKU IYA NEMANMU TA WANNAN NUMBER_*

+234 903 177 4742

_Alkairin ALLAH yakai gareku masoya a duk inda kuke, tare da fatan alkairi muna sonku irin trillions ɗin nan😍😘😍🥰😍😊_.

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull