Bakin rijiya part 1 complete novel - Chapter 5
Bakin rijiya part 1 complete novel Chapter 5: Bakin rijiya part 1 complete novel Chapter 5. "ke!!!! Karki kawowa mutane raini kinji ko,kune da kanku kuka…
4,324 words
"ke!!!! Karki kawowa mutane raini kinji ko,kune da kanku kuka fada masa kuma yaji,aljani meramo yaso taimakonki ne idan bakyaso kije can,amma kin san na sanar miki asirin ze karye kuma ke zaki haukace,idan kin fisan haukar kije da mahaifar keda hankali sedai ki gani ga wari" zaro ido tayi tace "Kayi hakuri boka ba haka nake nufi,abunda ya kadar dani zancen qwace masa sha'awa" zbura yayi " K'wace masa sha'awa tare yake tafiya da sanya ya manta daduk wani abun da ya faru kuma yana ji yana gani yankasa magana koda be samu mantawar duka ba,shida sha'awar wata mace bama keba har gaban abada,kuma kece da kanki kikace dukiyarsa kadai zaki kwashe kiyi gaba to meye naki da sha'awarsa" haka dai dole suka yarda atake awurin aka hanawa zuciyar shammaz daukar wani mataki yaji a rayuwa baze iya mata koda tsawa ba,mahaifiyar haleemah ta kalli bokan tace "Aiki yayi kyau ya saki kishiyarta sedai yan gidansu nasan zasuce ya dawo da ita bama san hakan shifa ya za'ayi?"
"Dama kin dena wahalar da kanki,sabida wannan yaron basan yarinyar yakeba,bana tunanin ze maidata kudinku da jikinku su huta hakanan" Godiya sukayi sannan suka wuce masaukinsu inda zasu qarashe tambad'ewa Allah ya shiryar damu ya kare muna imaninmu.....
Hafsat Ajikin umma tayi baccinta jirgi,gaba d'aya Dr. Sayyeed duk wani motsi da zatayi idonshi na kanta masifar tausayinta yake ji, gashi yarasa dalilin daya sanya a wuni idan dai har ko kiranta beyiba seyaji wani uban zazzab'i na shirin rufeshi gaba daya,yakuma kasa fahimtar meyake damunshi arayuwa......
*INDIA*
Kwanan su biyu a can agidan su maman Dr.sayyed suka sauka dukansu kasancewar gidan babban gidane ga kuma family d'in sananne ne a mumbai, Abba haris shikad'aine ya sauka a masauki sabida ganin rashin dacewar tarewarsa gidansu alhalin shi namijine....Ranar da aka shiga tiyata da hafsat har Dr.sayyeed dashi aka shiga tunkan amata allurar da za'a shemar dabita take kuka,sosai Dr.sayyeed yaji tausayinta ya kama ta ajikinsa shi dinma sanda yayi kuka da adu'a d'auke a bakinshi aka soma aikin..........
*Bayan kwanaki biyu*
Cikeda fad'uwar gaba ake jiran sakamakon idon hafsat,wanda tsabar fad'uwan gaba ya sany Dr.sayyeed gaba daya ya kasa cin komai ranar,Kasa shiga yayi wurinta sedai a waje ya zauna wurin su Abba haris, sunfi 3 hours zaune zugum zugum kafin fitowar Dr . Din yana zuwa ya miqawa Dr. Say hannu da murmushi d'auke a fuskarsa sannan yace "Congratulations brother, we've succeeded" Miqewa yayi lokaci d'aya " Are you sure my Dr.?" murmushi ya kuma sakar masa
"Sure bros" Rungumeshi yayi sannan yaja hannunshi zuwa d'akin da hafsat take a kwance,takasa banbance tsakanin farin ciki da bak'in ciki wanne takeji,Matsawa yayi kusa da ita yace
"Sannu Hafsat,Alhamdulillah komai yayi normal yanzu" kallonshi tayi ta gane muryanshi amma bata taba zata haka kyawunsa yake ba sekace wani haihuwar larabawa,lokacin datake ganinsa bata cikin hankalinta batama iya tuno waye a kanta bare ta tantance fuskoki,ganin batayi magana ba ta qura masa ido ya sanya yayi gyaran tsayuwa yace "Beauty sannu kinji?" murmushi ta sakar masa sannan hawayenta ya silalo da gudunshi tace " Thank you,thank you so very much uncle say,may Allah bless and reward u abundantly" hannunta ya riqe sannan yace yana fad'ad'a fara'arsa " Beauty nafiso inji kina fad'an Alhamdulillah shine ya baki lapiya Allah,soni nawa taimako yazone ta hanyarshi" murmushi tayi amma ta kasa tsaida hawayenta,hannu ya sanya ya share mata hawayen sannan yace "Beauty kiji sauqi gaba d'aya da sauri so nakeyi na kaiki yawo,watannin da kikayi bakya gani duk sekin rama wannan kallon" murmushinta ta fad'ad'a har fararen haqoranta suka bayyana,sannan tace "Uncle say i so much like you,apart from my parents ur d only person nasan yana kulawa dani tamkar blood d'aya yake yawo ajikinmu,bana fatan abunda ze raba zumuncin mu har abada" murmushi kurun yayi haka kawai ya tsinci kanshi da matukar jin dad'in kalamanta "Ameen ya rab" ita kad'ace kalmar daya tsinci harshensa da furtawa,kan wani ya kuma yin magana har su Abba sun afko d'akin.. Da sauri Abba ya rungume hafsat jin ta kira sunan sa,suka yita kukan murna sam barka abinsu.
*Bayan sati biyu*
Hafsat gaba d'aya jikinta yayi saiqi har yawo sun zaga garin ba laifi,sabida har shirin komawa sukeyi,gaba daya qannen say mata suna matukar qaunar hafsat sun shaqu da ita itada khairii ba kadan ba,har roqa sukeyi wai su zauna dasu india suma suyi karatu dayake dukkansu sunajin hausa sabida babansu dabhausar yake musu magana mamansu kadai ke musu yaren india kan tarasu kuma itama tanajin hausar,koda Hafsat ta roqi Abba haris akan abarta anan tanasan tayi karatun low mmbe hana suba har khairii yace su zauna atake aka nema musu gurbin karatu inda dukkansu suke karatu a jami'a d'aya se dai hafsat low take karatu yayinda kharii ke karantar business admn.....
*NIGERIA*
Zaune ake a babban parlor ana hirar dawowar yan india daddy ba qaramun dad'i yakejiba ganin cewar hafsatunsa harta fara sabon karatu,sabida anan niger tamayi missing semester d'aya kowa se murna yake shi sam yaa shaam hankalinsa baya wurinsu sabida damuwarsa ma ta isheshi sam baya iya tab'uka komai a shinfid'ar matarsa sannnan kumanya kasa gane dalilin daya sanya komai zatayi baze iya yi mata magana ba,tazo tayita karb'ar kudade hannunsa amma baya iya cewa da ita kanzil,daddy ne yace
" Shaammaz kaji qanwarka ta samu gurbin karatu a india,tana can mumbai tana sha'ani abinta banji ka sanya albarka ba" Dan tab'e baki yayi sannan yace "ni anawa tsarin banason banso yarinya taje wani qasar karatu,kawai dai ina mata fatan alkhairi,banza kowa ya masa aka ci gaba da hira,shi dama abba baya amsa koda gaisuwarsa ne......
Kwance hafsat take tana karatu Dr.say ya kirata, "Uncle say ina wuni" kwaikwayar maganarta yayi sannan yace "Duk wannan ladabun baze hanani zazzanekiba,an gayamun bakyashan magani mesa haka?" shagwab'ewa tayi
"Allah ni uncle say ka yarda dani ina shan magani,sameera fa qarya takemun"
"Naji amma mesa bakya shansa akan tsari,Allah idan kukayi hutu punishment dinki shine bazakizo Nigeria ba" kukan shagwaba ta saka masa dakyar ya hakura sannan sukayi sallama....
Mom Nu'aiym [1/25, 8:54 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
*wannan shafin nakine kyauta Ta ma'aiki,inajin dadin comment naki Allah yabar zumunci*
15 Tun bayanda su hafsat sukaji labarin auren uncle say sataji gaba d'aya duniyar ta mata qunci tayaya ma uncle say ze hanata zuwa hutu,ace bikinshi sukutum wai bada ita za'ayi yishiba,gaskia abu beyi ba kam wannan ya sanya taketa fushi dashi,shi kuwa ya kafe akan bazata zoba wanda wannan umarni ne na abba haris,bayaso ya hanata da kanshi amma sam bayaso tazo ta sake tada hankalinta akan shammaz gashi ance su kula sabida matsalar ta na heart,haka akayi bikin tanata qunci batazo ba,gashi su sumayya da suhaila duk sun tafi itada da khairii ne kawai shekara d'aya kenan rabonsu da gidan.......
*Bayan shekara Biyu*
*Takun saqa*
Ba kad'an ba hafsat kejin dad'i zatazo hutu Nigeria bayan shekaru biyu cur datayi harma da yan watanni bata Nigeria,tsakanin itada khairii bazakace wa yafi wani zumud'i ba,koda jirginsu ya sauka hafsat ji takeyi tamkar ta bangaje dukkanin mutanen dake tafiyar yangarnan ta sauko,sabida ba qaramun missing gida tayiba, A yangace yangar dabata san sanda ta koyeshiba take tafiya,ba shakka wanda yasan waccen siririyar hafsat kamar ka busata ta fadi baze yarda cewar wannan data tara mula mulan abun zama da iyayen heeps tare da doka dokan breast cewa itace hafsat d'in daba,sanye take da straight skirt na roba light blue da top red wacce ta d'ameta takuma bayya no ainahin surar da Allah ya mata,ga wani tsukakken flat tommy da bazaka tab'a yadda cewar mamallakiyar wannan booties ne dashiba,tamkar arayuwa ba'a saka masa komai aciki,sanye a idonta dan qareren qaton shade ne me kyau,a saman kanta sirirn fayafine ta yane kanta dashi,tun daga kan goshinta har girar idonta gargasa ne baqae wuluk se sheqi sukeyi,lallai hafsat tayi kyau, takuma qara girma side bag ce me kyau kalar ja rataye a kafad'arta yayinda a k'afarta take sanye da wages blue masu kayu matuqa, khairii ma irin shiga d'aya sukayi kalace kawai ta banbata domin kuwa ita pink and white tayi,sunyi kyau matuka,Abba haris suka fara hangowa inda basuyi qasa a gwiba suka zarce wurinsu suka rungume shi suna murna,
"Abba kai kad'ai kazo ina su momy?" hafsat ta tambaya cikeda k'osawa,murmushi yayi yace "Nine nace kowa ya zauna ba wanda zw biyoni duk suna gidana ku kadai ake jira yau daddy ma na gayyata can sabida yara nema zasu dawo" murmushi tayi sukayi gaba abunsu zuwa mota.......murna sosai akayi domin zuwansu anyi girke girke na masifa masu matukar qayatarwa da dai hafsat nak tayi kasancewar ta jima rabon dataci abuncin gida,su momy suka wuce ita kuwa tace bazata ba se gobe,da dare bayan sun huta wayanta ya soma ya ringing tana dubawa taga sunan uncle say,qin d'agawa tayi gaba d'aya ta turo baki tamkar zatayi kuka kuma kamar yana ganinta,kallonta khaiirii tayi "Uncle say nefa ki d'aga mana" harara ta wurgo mata sannannta tsiyayar da hawayen datake ta faman tarewa "Bazan d'agaba ai cewa yayi dani shine ze dakkomu daga airport shine be zoba kuma na kirasa yama kashe wayan" murmushi kawai khairi tayi indai fad'ane dama tasaba ganin sunayi batanan sanda suke shiryawa abunsu....
Washe gari yamma liqis hafsat tace da driver ya ajiyeta gunsu momynta,haka ta shirya ta wuce yauma kalar dressing na jiya tayi sedai wannan karon lemon green and orange tayi ga alama wannan dressing shine d'abi'ar ta yanzu,a baking katafaren gate d'in gidan tace driver ya ajiyeta yayi tafiyarsa,ba komai a hannunta se wayarta kirar iphone 7 da side bag lemon green dake rataye a kafad'arta,koda ta shigo gate d'in gidan wayarta take dannawa,acikin qatoton madubin idon dake idonta,murmushi takeyi har fararen haqoranta suka bayyana ganin khairii na mata iya shege kan whatssapp akan tafiyanta gida, jitayi ance
"Hafsat ce" D'agowa tayi fuska a had'e jin muryar me mata magana tana taunar cingam dake bakinta,batace dashi kanzil ba ta wuce taci gaba da tafiya abunta,mamakinta ne ya kama shaam ganin abunda ta masa,se wani yanga takeyi yayinda duk taku d'aya se yalwataccen qugunta yayi magana,ko kallon inda yake bata qara yiba tayi gaba,sosai tabashi mamaki ya had'iye wani yawu me d'aci a rayuwarshi yace "Lallai idan kika zomun da raini sekin gane kuskurenki" ...
A parlor ta tsaya suna gaggai sawa dasu momy da daddy,daddy kallonta yayi "Lallai kulelen daddy girma yazo miki kinga yanda kika dawo kuwa,kuma yanzu naga ba rigima" murmushi kawai tayi batace komai ba, shine ya kuma cewa "Banga jakar kayankiba na zata zakizo gidane ai" sosai kanta tayi tace "Daddy nan gidan ba kowa ni gobe zan koma Allah kuwan"
"Ni bazan takurakiba kulele so karki damu kinji" Miqewa da zummar zuwa kitchen ta hadaw onion samosa da ta zame mata jiki,kullum setaci ko a can dama abuncin suce,kan taje ko ina sega yaa shaam ya shigo ko kallonshi batayi kuma kowa ya kula da hakan shi kuwa ya qurawa yalwataccen gashinta ido harta b'acewa ganinsa,zama yayi kusa da daddy cikeda fusata yace "Daddy kagan kuwa hafsat wulakancin datamun ko gaisawa mafa batayi daniba ko kallona ma batayiba" murmushi daddy yayi yace "kayi hakuri zan mata magana,wataqil fushi takeyi dakai har yanzu" bece kanzil ba harta dawo d'auke da plate dinta na onions samasas ta zauna kusa da momy
"Mommy zakiji samosar albasa zallah,da dad'i wlhy" kallonta momy tayi ta d'an b'ata fuska "Hafsat mesa baki gaida yayan kiba,ko baki ganshi bane?" cikeda rashin kulawa tace "A a momy waye kuma yayan nawa naban gaidaba,nina gaisa da duk wani jinina dama wanda ba jinina ba a gidannan kumafa kina kallo"
"yayanki shammaz nake magana,hafsat" d'an tab'e baki tayi ta yamutsa fuska "Hmmm lallai ma mommy,bakin rijiya fa ba wurin wasan makaho bane,ina nayi matsayin dazan gayarda d'anku,kuma ni wlhy Allah ya kiyaye ya zama yayana" mamakin kalamanta kowa keyi daddy yace cikin fushi "Hafsat kinad hankali kuwa,a gabanmu kike fad'ar wai shammaz ba yayanki bane" turo baki tayi ta soma hawaye sannan ta miqe ta tattare mayafinta ta yane kanta ta wurga wayarta ajaka ta shuri takalminta,wlhy indai kukace zakuna takurani akan gaida wannan wlhy bazan qara zuwa muku ba,ku tambayeshi mana yaya mukayi dashi,ai mun raba duk wata alaqa tsakanina dashi to meye kuwa ruwansa dani" tana kaiwa nan tafito daga main parlor d'n tana kuka, Ganin Uncle say a tsaye jikin motarshi ya sanya ta qara turo baki takuma qara sautin kukan datake har tana doka kafarta a qasa,da sauri yazo kusa da ita
"subhanallah Beaty,.eya sameki kike kuka?" sauke hannunta tayi tace "Bayan su daddy da mommy ne wai sena gayar da shammaz,ni kuwa alqawarin nayi har abada bazan kuma masa magana ba,ni Allah bazanma kwana musu ba" hannunta ya janyo
"Hafsat ur 19 fa,why are u still behaving so childish? Gaskia banaso kuma zamuyi fad'a,meye idan kin gayar da yayanki?" turo baki tayi tace "Uncle say bazaka ganeba banaso ina tunaninshi kuma banso ina ganinshi,tsanar kaina nakeyi kuma wlhy zuciyana yanamun zafi ko tunasa nayi,uncle say plss karkace na gaidashi kaji" tausayinta yaji ya sani sarai har gobe hafsat tanasan shammaz,kuma yasani zuciyarta a cunkushe yake da tsanar abubuwan da ya mata,kan yace wani abin daddy da shammaz sun fito,gaisawa yayi dasu yayinda hafsat tayi kici kicin,bayani daddy ya masa akan fushi zata gida,lokaci daya ya hade fuska yace "Hafsat kinsan shiyasanya na hanaki zuwa hutunnan Allah idan baki nutsuba nida kene,kina girma amma bakya wayau maza ki koma ciki" turo baki tayi tana hawaye "Uncle say bamu mafa gaisa kuma its been long,dama ba wurina kazo ba?"
"Gunki nazo amma yanzu ammun waya yayarki tana labor so zanje gunta" matsowa tayi kusa dashi ta soma doddoka k'afa "Allah ni Uncle say sena bika dama tunda nazo banga Aunty ba" girgiza kanshi yayi a gefe d'aya kuma yana jinjina girman da hafsat tayi da kyau,se d'an karen wawta data qaro,kuka kuwa ya saba kullum ne ko a waya se an masashi akan zuwa gida.....
Mom Nu'aiym
*Babu tabbacin cewar gobe zaku samu,se yanda Allah yayi ina busy ne sosai kwanakinnan* [1/28, 8:22 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
Wattpadd@ 68billygaladanchi
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
* A shafin daya gabata,munyi kuskuren number,amaimakon 14 se muka saka 15,idan muka ce zamu dawo baya da matsala wasu zasu rikice sabida haka zamu ci gaba da 16 inshaa Allah,nagode.*
16 A asibiti kuwa uncle say gaba daya hankalinsa ya tashi jin za'a shiga da suhail cs sabida ta kasa haihuwa,sosai hankalinsa yaqi kwanciya,yakasa zaune ya kasa tsaye shi kuma ba b'angarnsa bane gefen haihuwa,Ganin Dr. Hafiz ya fito daga thereter room ranshi a b'ace ya sanya qirjin say ya doka da k'arfin gaske,yana fatar ba abunda ya faru kenan ba, Gwiwa a sace Dr. Hafiz yazo kusa dashi kallanshi yayi sannan ya d'ora hannunshi a kafad'arshi ya kura masa ido,hannun nashi Dr. Say yabi da kallo sannan a hankali ya mayarda dubansa zuwaga Dr. Hafiz amma beyi magana,cikin dakiya hafiZ yace dashi
"Im so sorry to say we lost both the mother and the child,tunka mufara thereter d'in Allah yayi ikonsa akansu kayi hakuri abokinaHaka Allah ya tsara"Kasa koda motsi yayi idonshi sun qeqeshe sunyi jajir amma ba alamun ruwa acikinsu,ihun da hafsat ta kwallah ne ya dawo dashi duniyar tunanin dayaje,da sauri sukayi kanta se gunjin kuka take wayyo ita Allah Aunty suhaila, bata taba ganinta ba se a hoto kasancewar wancen lokacin dasukayi shiri sosai ita bata gani kuma tunda ta warke bata zoba amma sunyi wata irin shaquwa mara misaltuwa kullum se sunyi waya yafi a irga,ko jiya sanda sukayi waya,yauma da safe haka, sosai hafsat ta gigice dajin zancen Dr.Hafi,say shi yama rasa me zeyi Dr.bafiz ne ya lallashinta azatansa qanwar marigayiyar ce, A haka ya lallaba yayiwa mahaifinshi waya da kuma nata mahaifin kasancewar dama basusan ankawota asibiti ba,mutuwar suhaila ta rikitar da Dr. Say sabida yana matukar qaunar matar tasa,sannan be tab'a kawo mata mutuwa ba ko kan yafita da safe lapiya lau ya barta kuka yake tayi tamkar wani qaramun yaro har akayi sadakar uku,hafsat ma gaba d'aya ji take duniyar ta mata duhu,batajin dad'in komai,haka dai dole kowa ya haqura wanda ya fisu san baiwarsa ya dauke abarsa gaba daya.......
*Bayan sati uku*
Yaa shaam zaune a parlor din gidansa kusa dashi haleema ce take ta faman taunar cingam sekace abun dole, shi kuwa gaba daki daya hankalinsa baya kan kallon dasukeyi yana gun wannan hafsat da gaba d'aya tun zuwanta ta sauya masa tunani,be tab'a zata akwai ranar da tunanin hafsat ze hanashi sakat ba,anya kuwa bazece da abba yayi nadama ze maida itaba,kai idan yaje gun abba baze saurareshiba wataqil gwara ma yaje gun daddy,da wannan tunanin yaje ya kwanta.... Niko nace hmm ubanka zakaci d'anye wlhy..
"Mero ni kuwa wai in tambayeki?" kallon hafsat meron tayi "Ina jinki mana Allah yasa na sani" gyaran zamanta tayi ta tattare nutsuwarta gun mero tace
"meyake damun yaa shaam? Naga duk yabi yayi baqi ya rame,kuma ya rage kiza kiza" kura mata ido mero tayi na yan dak'k'u kan daga nisani bayan ta gama nazarinta ta nisa tace
" kaidin mace ke d'awainiya da shaam hafsat,wlhy haleema tagama da yaa shaam ta shanyeshi tas,danma su momy sun tashi tsaye da adu'a,danma bazaki fahimta bane amma da kunnena naji tana magana da qanwarta harira akan naqasashin dasukayi,ko kad'an fa baya sha'awar mace wai sabida karya tuna abunda suka aikata,in taqaice miki dai kud'ad'e take karba a hannunshi da kadarorinsa baji ba gani nan da kika ganshi yanzu bashi da komai se asibitinsa shi d'inma sabida daddy yana tsaye ne akan asibitinsa da takardun wurin gaba d'aya,sedai tayita yawon banza nabin maza,ni a ranar danaji suna zancen aunmai asiri a ranar na sanarwa momy nanne fa aka d'an samu sauqi domin adu'o i da magungunan tsari sukayita nemar masa,gashi baya kula da ibadunsa da addininsa seda daddy ya tashi tsaye yanzu dai yaji sauqin rashin jin sha'awa duk nice yar rahoto akwai lokuta da dama da idan naje gidan nikan tadfasu suna wasaninsu wasu time ma har kwanciyar aure nake fahimtar sunayi dukda ni ban yarda da matar ba,yanzu abu daya ya gagaremu shine rabashi da matar sabida tsananin santa yakeyi fa,gashi ita kuwa komai ya samo seta qwace shi tatas ni na rasa wane irin kaine sa yaa shaam,gashi kumansu daddy sun saka yana adu'o i kema dai ki tayashi gaskia,yana cikin wahalar mace" nisawa tayi sannan tace "Allah ya kyauta musu,Allah ya shiga tsakaninsa da ita" kallon tausayi mero ta mata ganin tana kwallah tace
" Nasani hafsat har yanzu kina san shaammaz ina rokon Allah ya daidaita tsakaninku" kallonta takumayi tana me sharar kwallan daya zubo mata tace " Mero bana fatan sake zaman aure da shaam,ko a mafatki naganni matsayin matarshi lallai senayi adu'ar tsari daga mugun mafarki had'eda yin sadaka, har kwanan gobe ina san yaa shaam sedai a yanda na fahimta sam wannan bashi bane mafita agareni,so tari zakiga abubuwan damu y'an adam muke so basu suke zamtowa mafakar alkhairi agaremu,yaa shaam ko banda asiri ba sona yakeyiba kuma tsana ta zahiri,nidai wlhy kinji na rantse miki nidashi har gaban abada,ina dai masa fatan alkhairi" jinjina kai mero tayi "To Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki" "Ameen" ta fad'a ataqaice sannan ta kwanta ta runtse idonta......
*Bayan sati biyu*
Shaam durqushe agaban daddy da abba haris dasu momy harma hafsat wacce dominta aka tara zaman,kasancewar wai shaam yace ze aureta kuma ze barta harseta qarasa karatunta a india,kowa yayi shiru yana kallon ta tsuniyar daddy domin kuwa ilahirin jama'ar wurin kallon me bada tatsuniya suke masa harya idar,hafsat dai batace qala ba kazalika bata koda girgiza da zancen ba tunda taga yana mata bata dagawa be dena kiranba ta tabbatar cewar lallai da wata aqasa..... Kallon su Abba yayi yayi wani malalacin murmushi sannan ya kalli hafsat yace "y'ata nasan bazaki tab'a watsan qasa a idoba,ina sauraronki menene naki ra'ayin ni duk abunda kikeso shi zan miki" kallon shi ta dago tayi ido cikin ido suna had'a ido abba ya gano ta shaqa,ta nisa sannan tace idonta a qanqance
" Bazan sake fad'ar abunda zan fad'a a yanzu ba,abu d'aya nake san kusani shine,dukkanin abinda kukaji zan ambata yanzu babu wasa kokuma wani abu makamancin raini aciki,kuskurewa qa'idata d'aya ka iya janyo lalacewar komai musamman idan na aikata abinda zan aikata idan aka kuskuremun qa idar" shiru ta danyi kowama yayi tsit taci gab
"Ni bazawarace ba budurwaba kuma a tsari na addinin musulunci nice dakaina nake da haqqin zab'awa kaina mijin aure a yanzu,bazan lamuncewa zab'in kowa ba tsarin addinina zanbi, kuma wlhy summa tallahi bazan tab'a komawa auren shammaz ba,ko gawata akayi kuskuren daurawa aure da shaam ban yafewa wanda yayi ba koda mahaifinane kuwa, idan aka qarabtayarmun da zancennan wlhy na sanya qafa nashiga duniya nida gida har abada,idan dame tantama kuma ya gwada tada zancen kuga ikon Allah, ku tambayeshi kuji dalilansa naqin zama dani idan dai basankai kuke sanyi ba ai bazaku qara cutar saba kamar yanda kukayi abaya,da bakinsabyace dani ya tsaneni!! An cuceshi da aka had'ashi aure dani,da bakinsa gashinan zaune ya kalli tsabar idona yace dani Babu tabinda ze zauna da mace bushashiya ni menakedashi,mena ajiye ajikina ina fama da qasusuwa,da bakinsa ya kalli tsabar idona yace dani na dena mafarki ze tab'a had'a shimfud'a da banza irina bushashiya,ashe nidin nan icce ce a idonku,ashe bajini a jikina,ashe qarfeceni bansan dadin mijiba,idan har baku sani ba toku sani yau nasha baqar wahala rayuwa da miji fanko,ina da aure an kawar dani sabida gudun wannan yaso ya cillani gayinta banda a litttafan hausa da fina finai ina kuka tab'ajin anyi aure shekara daya amma namiji be taba koda riqe hannun matarsa ba duk sanda kuka ga jikina da nashi ya hadu tofa duka ne,kuma da bakin sa ya sanar mun cewar bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine ina makauniya zan dauki kaina inkai daidai bakin rijiya,sabida bana tsoron afkawa aciki,toku sani ina tsoro!! Na rantse da Allah kona rasa mujin aure bazan auri yaa shaam,ninan ni kadaice na san baqar wahalar danash a hannunsa,a ranar dana samu matsala dakaina na roqeshi akan waze aureni idan yasaken ya taimaka ya maidani gidansa,bud'ar bakinsa se cewa yayi dani be soni sanda nake da lapiya ba se yanzu dana dawo nakashashiya,bayan shine silar lalacewar rayuwata da quruciyana kowa namun kallon bazawara!! Kullum zancensa d'aya ya tsananeni yana tunasar dani bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane,shine yanzu ze bazamo kome ya gani ajikina oho!!! Ko kuwa dai yanzu zan iya wasa a bakin rijiyar tunda naqasa ta tafi oho!!! D'aukacin mutanen parlor dinnan ku shaideni ranar dazaku qara zuwamun da zancen komawa gidan shaam kun rasani kenan har abada!!!!""
Jikin kowa yayi sanyi yayinda abba haris ya zabgeta da albarka,shaam kuwa ya saka kuka wiwi wai ta taimaka masa....to phaaaa..
Zaune suke idata Uncle say a babban parlor na gidan daddy se shagwab'a takeyi wai bazata koma india ba,shi biyeta yakeyi ya saba haka sukeyi da qannenshi sesu sakashi gaba abu beje yazo ba su saka masa kuka
"Haba dan Allah uncle say,idan kuma na tafi bazan qara ganin kaba fa" murmushi yayi yace "Dan Allah hafsat ki dena rigimarnan,bakya ganin khairi batayi haka ba? Ke komai se kace jin jira,komai rigima komai kuka,na sanar miki akwai wani coirse dazanyi a india na shekara daya kuma nxt montj zanzo,tunda kunfara school seki koma kafin nazo" turo bakinta tayi waje " Ni dai jiranka zanyi bazan iya juran rashin ganin kaba na tsawon wata ni yanzu im used to you over,i just cnt imagine my self with out you around" Murmushi ya sakar mata "Nima haka beauty amma ya zamuyi yanzu idan namiki aure ya zakiyi? Sekice dani zaki tafi" B'ata fuska tayi
"Ni nace dakai zanyi wani aurene,ni bazan taba aureba aje ana dukana,maza basuda kirki wlhy" janyo hannunta yayi shi yarigada ya saba da al'adar indiyawa yace
"Beauty banasan wannan mummunan tunanin dakika sakawa kanki,sam be dace kina cewa bazaki qara aure ba,adu'a zakinayi Allah ya kawo miki muji na gari me qaunarki tsakani da Allah" kallonshi tayi ido cikin ido tace
"Ni koba wannan ba bazanyi aureba,idan nayi aure mijin baze bari ina ganinka kullum ba,nikuwa that will be d worst thing that will happen to me ever,i just cnt imagine my self living a day with out u" murmushi ya sakar mata yana nazarin kalamanta sannan yace
"yanzu dai naji,amma ki daure ki koma school Allah zan siya miki sabon waya da sabon laptop da sabon ipad kuma zan siya miki sabon kaya ma,na zuwa school madam gayu" tana murmushi tace "Thank you for that,buh bana buqatar komai daka lissafa i just need u beside me,idan wannan baze samu ba,zan haqura nace haka Allah ya tsara" sakin hannun mata yayi yace yana miqewa "Thats very good of u gold,zancen waya kuma i already bought one for you, samsung s8 your favorite product,yana mota muje nabaki " miqewa tayi tana ihu tamkar ta rungumeshi,say akwai principles seyaga dama suke riqe babbar waya fa!! A hanyar fita suka had'u da yaa shaam,uncle say ya miqa masa hannu su gaisa,dakyar ya bashi hannu sannan yace " ke hafsat wai an sanar miki kowane mutum kika dakko secikin gida ake kaishi haka akeyi?? Ga guest parlor can kuje amma se ciki,ba wani privacy kuma bare ma" kallon mamaki say ya masa ita kuwa taja hannun say batare data koda kalle shiba domin kuwa ita alqawari tayi idan yayi sallama zata amsa,ita kuma tashigo koda shi kadaine a wuri zata masa sallama amma bazata taba yi masa magana ba,koda ze mata bazata kulashi ba, gabansu yasha sekace wani dolo yace "ke badake nake magana ba?" say ne yace "kayi hakuri Dr. Shammaz inshaa Allah bazan qara zuwa muku gidan bama gaba daya bare kayi fadan bare ya shiga ciki" kawai se hafsa ta saka masa kuka