Kenza eBookz

Bakin rijiya part 1 complete novel - Chapter 4

Bakin rijiya part 1 complete novel - Chapter 4

Bakin rijiya part 1 complete novel Chapter 4: Bakin rijiya part 1 complete novel Chapter 4. "waye acikinku ya nemi sanin inda Hafsat take da baku ganta ba"…

4,426 words

"waye acikinku ya nemi sanin inda Hafsat take da baku ganta ba" mero ce tayi saurin cewa "Abba mun tambayeta amma yaa shaam ya sanar mana wai tana makaranta" wani kukan kura Abba haris yayi ya shaqi wuyan shaam ya miqar dashi tsaye ya surfafa masa lapiyayyen mari har guda uku a jere a jere,cikin mamaki d'aukacin mutanen dake parlor din suka miqe daddyy ne ya riqeshi "Harisu lapiyan ka kuwa meya faru?,yaro yana cikin zillar rashin yaronshi zakazo kana surfafa masa marika haka,meya maka" cikin huci yace "Sabida yaronshi ya mutu seya nemi kashe yar mutane,wai har shammaz dan bashida imani ba Allah a ranshi ze riqa baiwa hafsat renon yaro cikin dare yashige da tsohuwar matar daya ajiye suna holewa,kuma sabida Allah ya karbi ranshi rana daya ya ce wai hafsat ce ta kasheshi kuma ya mata dan banzan duka harta suma,bayan sakinta dayayi duk wannan be isaba se sanin ya dasa mata ciwon zuciya ba wanda ya sani harma da hawan jini,yanda ga wayannan kuma gashi likita ya tabbatar mun cewar wai hafsat kanta ya tabu sabida dukan daya mata aka,wlhy Yaya Abu bazan tab'a yafewa Shammaz ba,na yafewa duniya shi kuma bazance masa komai ba yaje duniya ce,daga rana me kama da ta yau kar naji kona qara ganin yace nine nan na haifeshi ko mutuwa nayi wlhy banda shammaz a gadona kuma ko'a lahira se an mana hisabi dashi,yaci mutuncina yaci mutuncin dan uwana,yaci mutuncin matarshi yaci mutuncin aure,kuma be ragawa Allah ba,na kuma tabbatar Alkah bazenraga masa ba" Da sauri Daddy ya rufewa Haris baki tare da zaunar dashi dukkuwa danyake yaji maganganun tamkar saukar aradu,wai kan kulelen sa ya tab'u kuma a dalilin dukan da shaam ya mata,sa'annan kuma wai tanada ciwon zuciya adalilin mene wannan? Dakyar ya saisaita kansa ya kalli shaam "shammaz kaji abubuwan da harisu ya fada hakane??" sadda kanshi yayi qasa sannan yace

"Daddy niba abunda nake mata,kuma wlhy bansan da zancen ciwon zuciyaba,da ina mata wani abin aidanta fada tuni,zancen khaleefa kuma itace da kanta taroqi Haleemah akan yana kwana gunta kuma jiyan ma wlhy banso ya kwana candin ba,dukan dana mata kuma ba'a san raina bane harma sakin dana mata duk acikin b'acin raine da gigicewar rasuwa khaleefan" Shiru daddy ya kasa magana kowama yayi shiru se momy dake kuka lokaci lokaci tana jan hanci kasancewar kukan nata bame sauti bane,yafi mintuna biyar kafin yace

" Harisu dan Allah markayiwa d'anka baki,ka janye wayannan kalaman daka masa kuma ka nutsu wannan maganarbta gida ce ba abun tashin hankali bane" miqewa Abba yayi

"wato yaya ba kadan ba ka ke sakarwa shammaz dama yana durun uwarsa san ransa,ni za'a gayawa wai harkar gida wlhy tallahi sena maka wannan yaron kotu senaji dalilin wannan ha'incin kuma koban masa bakiba haqqin yata seya kamashi rasa kunya kawai b'eran tanka,dana sani shine babban amininka koba yanzu sekun kulla babbar abota dashi wlhy" yana kaiwa nan yayi waje,yayinda momy tayi kiran mero suka nufi asibitin uduth daddy ma da shaam din suka bi bayansu kasancewar haleemah tana gidansu.....

Acikin d'akin kowa yayi zugum zugum an qurawa hafsat dake wance ido, A hankali ta bud'e manya manyan dara daran idonta,sunanan dai a lumshe tamkar mejin bacci a kowane lokaci,d'aya bayan d'aya take bin kowa da kallo,har shaam wanda taqurawa ido bata ko k'iftawa,a hankali kuma ta rufe idon tamkar me bacci can kuma bayan yan mintuna tamkar wacce aka tsira kuma seta fara fizge fizge kan kace me wannan ta soma zabga sambatu

"Dan Allah karka dakeni wlhy ba abunda nawa khaleefa,yaa shaam ka dena dukana zaka kasheni,wayyo Allah daddy kazo ze kasheni,Abba yaa shaam ze kasheni" dak'yar suka rirriqeta shaam yaje yayi kiran nurse dake kusa akan ya akira doctor sannan ya koma kanta, koda dortor yazo seta fara kuka sekuma ta saka dariya kowa a d'akin kuka yakeyi yayinda lokaci d'aya kunya,danasani,nadama da bak'in ciki suka qara taruwa suka lullub'e shaam yama rasa me yake ciki a yanzu,Dr.sayyeed ne yazo dubatan ya kalli shaam ya miqa masa hannu suka gaisa sannan yane kai tsaye wurin hafsat,cewa yayi kowa ya saketa sannan ya sauke mata lallausan murmushi bayan ya riqe hannunta na dama,qura masa ido tayi dukda acikin rashin lapiya take amma setake masa kallon rashin sani yace yana ci gaba da fad'ad'a murmushinsa "Hafsat sannu kinji meye ne yake damunki? Cikeda wowta tamkar wata yar shekaru biyar tace "Bayan yaa shaam kullum yake dukana na ganeshi so yakeyi ya kasheni,ni ku fita dashi a d'akinnan inba haka duka na zeyi kuma banasan ganinshi" K'ara riqe hannunta yayi yace "Ai indai ni Uncle sayyeed ina nan wancan shaam din baze dakeki ba idan ma yazo dukanki nine zan mar d'an banzan duka yanzu sanar dani ina ne yake miki ciwo?" amaimakon ta bashi amsa se kawai ta matso ta qamqameshi tana kuka da sambatu alamun ba hankali atattare da ita "Uncle sayyeed karka bari yazo kusa dani dan Allah,daddy idan bazakuce ya wuce ba ni bana sanku"k'wallah Abba ya share cikin hikima yayi waje a haka a haka kowa ya watse ya kama gabanshi cikin k'unan rai,Dr.sayyeed be ajiyetaba seda tayi bacci shida kanshi yarinyar ta bashi tausayi over,be tab'a ganin case maka mancin wannan ba awurin yara dai......

Shaam na fitowa yakira Haleemah suka gaisa se kukan munafurci takeyi dak'yar ya rarrasheta ya sanar mata halin da ake ciki,cikeda kirsa tace "Amma ai yaa shaam na sanar maka karka daketa ba laifin ta bane ba inaga kaddara ne kawai" sallama dai ya mata ta ajiye wayar ashe sam shi be ajiyeba yana jiran yaji tace I love you boo me,yanda suka saba se kawai yaji an tafa hannu ana sowa

"Wlhy umma gabad'aya jin wannan labarin senaji gwarama da khaleefa din ya mace,dama kinsan ance seka haifi wanda zeyi silar arziqinka to zuwan khaleefa kenan a duniya,nifa da farko dakikace boka yace rayuwar khaleefa fansa har naji bakya sona,ashe kinfini kaifin hankali tunda ko yanzu nakeso zan iya qara haihuwa,amma fa wannan aikin da tsauri yake umma ji nayi kince bokan yace sena kwana biyar a gidanshi yana saduwa dani kuma kince wai idan har mijina yasan zanje konan dacan aikin bazeyiba sannan kuma idan har yayi koda tunanin muna masa asiri bare ma ya gane to aikin ya karye,ni kuwa ai bazanso hakan ba yanzu ya kenan??"

"Kinga hali dubu yar mama,barni da shegen yaronnan maganinsa zamuyi ai,yanzu ki hau bori zaki tsaya anan,kinga gobe seki je,duk ya kira akan zezo ki hanashi harse mungama aikinmu,kuma kinji boka yace daga zaran kin sadu dashi na karshe karki bari awuce awa ashirin da hudu ba tare da kin sadu da mijinki ba,kina yin hakan gaba daya ze kwashe mana dukiyar sa ya bamu,daga nan idan munso mu kasheshi ko kuma mubar masa gidansa inyaso mu koma lalubo wani me kudin,karfa ki manta khaleefa kika bayar akan kinasan yin arziki gudan jininki sabida ki nutsu kar a samu kuskure kuma ki tabbatar yaji wannan ganyen a abinci sabida shine ze gusar mas d hankali yakwashe mana dukiya a arha" dariya tayi suka tafa wanda shaam yaji komai zufa se keto masa takeyi ya kasa sauke wayar a kunnenshi yana saurarensu sunata shirya makirci,shi gaba daya ma ya rikice musamman jinda yayi suna zancen sun dasa masa qiyayyar hafsat,lokaci daya ma yaji ya tsani kansa kuma soyayyar dayake mata ta yaya da kanwa kai tsaye ta dawo da gudun fanfalaqi,amma fa har yau bawai yaji yana santa na soyayyaba.........

Dr. Sayyeed ne ya kalli shaam bayan sun zauna,yace raunin na kanta ya taba mata kwalwa harma yana neman zautar da ita,sannan kuma ga zuciyarta ta tsananta abinda na fuskanta duk sanda kazo wurinta se hawan jininta ya tashi ga bugun zuciyarta dake qaruwa,sabida haka kadan daga mata qafa,zancen gaskiya kuma aikin manta bame wahala bane sedai zeci kudi,abu mafi muhimmanci danakeso ka sani matsayinka na likita shine,lallai wannan jijiyar tata me aika jini me makon saqonnin fahimta akanta aikinta ze janyo wani matsalar,kodai lalacewar ido,kokuma ta kunne sabida haka sekun saka haquri a lamuranku" kuka shaam ya saka tamkar wani qaramun yaro sabida shi gabadaya tunaninsa ya tsaya cak,tayaya ze kalli su abbba da daddy da wannan zancen? Ina courage din? Menene ma mafita agareshi?" A yanda ran Abba haris ya baci idan wani abun ya samu hafsa agarin aikinnan ai tsaf ze tsine masa wlhy kowa ya huta,dak'yar Dr.sayyed ya rarrasheshi yabar asibitin....

*Ur vote is important also ur comment fan's,inasanjin ra'ayoyinku,i hope ur enjoying this story*

Mom Nu'aiym[1/21, 9:43 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

12 Dr.sayyed tunda yaje gida yake tunanin yanda zasu b'ullowa lamarin hafsat,haka kawai ya tsinci kansa da tsananin tausayin yarinyar,indai har acikin halin hauka bata manta muguntar da yake mata tokuwa lallai abun ba qaramun abu bane yana cutar da ita over,sam bayaso wani abu ya tab'u a jikinta kuma yasani sarai chancess na rashin samun hakan ba qaramun abu bane, yanaso ayi aikin as soon as possible amma fa sam bayaso ayi garaje a samu matsala.......

Shaam kuwa koda yaje gida masa bacci yayi,bangaren zuciyar sa na masa zafi akan abinda yaji da kunnensa haleemah na fad'a itada uwarta,yayinda dayan bangaren na zuciyarsa ke masa rad'ad'i akan abunda abbansa yace dashi akan hafsat,wani dogon tsaki yaja yace a asarari "Gaba d'aya wannan hafsat d'in ta jamun masifa wlhy,dabadan ta maqale akan seta aureniba wlhy daban shiga wannan mugun yanayinba,ita kuma haleema yaya zatamun haka?? Ina sanki sosai haleema ko baki sani bane" a haka ya dinga sambatu shi kadai harna shirme.......

Dr. Sayyeed da kanshi yayiwa su Abba bayanin rashin lapiyan hafsat da kuma da kuma abinda yake hange idan har aka mata wannan aiki,fatanshi d'aya ayi aikin lapiya kuma adu'arsu itace abun nema" Babu yanda suka iya dole su yarda da akan ayi aikin dukkuwa dayake Abba haris yaso a fita da ita waje daddy ne yace duk inda akayi aikin nasara a wurin Allah take,da wannan aka tsaida ranar aikin nan da sati d'aya......

Hafsat dai tana nan jiya iyau,ba abinda ya ragu har yau ba hankali akanta,yaa shaam tunda suka yaji wannan zancen nasu haleema seya kirata yace ta zauna gidansu se bayan sati biyu zuwa lokacin hankalinta ya kwanta dama kuma hakan takeso ya sanya ta kwantar da hankalinta tayi gidan bokan ta....

Sati ya zago Aka shirya shiga da hafsat tiyata yaa shaam har kuka yayi abubuwa sun taru sun masa yawa yanzu ya tabbatar wa kansa cewar abinda yaji gaskiyane,coz kwana kusan uku baya samun number wayan haleema kuma koyaje gidansu se a ce masa wai batanan sunfita da momy........Aiki dai anyishi cikeda nutsuwa da kuma na sara an samu damar kwashe duk wani jini daya taruwa hafsat a kai, yanzu jira kawai akeyi ta farfad'o, a ga yanda zata tashi......

Umma da momy sunyi jigum jigum suna adu'ar farfado war hafsat lapiya,se suka jiyo maganarta sama sama "Saro kunna mun fitilar d'akin nan kuma ki bani ruwa" kallon juna su umma sukayi sabida su sam basusan da wani zancen wai za'a iya samun matsala ba,da sauri suka miqe atare sukayi kanta,umma ta riqe hannunta tace

"Sannu hafsat ai ranane aikin da'aka mikine akai,inaga lallai alluran nan ne be sakeki ba shiyasanya kike ganin duhu,sannu kinji" Shiru tayi tafara tunano abubuwan da suka faru da ita ita dai bata jin wani jiri gashi ta tabbatar wa kanta cewar idonta abude yake yama za'ayi ace wai allurace,amma seta kama bakinta tayi shiru kawai tana me mamakin har meyake damunta daza'ace wai ammata aiki akai,wasa wasa hafsat haka ta wuni ta kwana bata gani zuwa wannan lokacin har su momy sunsan halinda ake ciki kowa ya sakata agaba har Shaam tana bacci tana farkawa tace

"momy zansha ruwa?" ruwan momy ta bata tasha sannan ta kwantar da ita gyaran kwanciya tayi tace "Momy dan Allah wai se yaushe gari ze waye ne,ni nagaji da ganin duhu idan ma garin be waye ba ku kunna mun fitila" D'aukacin mutanen d'akin suka saka kuka sabida tsabar tausayi daddy ne ya qarasa gunta yace

"Hafsat nasani maganar dazan fad'a miki zaki jita wani iri kuma tabbas zata tayar miki da hankali,amma inaso kiyi hakuri ki yarda da khaddarar Allah ya d'aura miki,khaddarace ta sameki sakamakon dukan da yayanki yayi miki wannan ne ya sanya kanki ya samu matsala na tab'in hankali, to agarin yi miki aikine kuma wata khaddarar ta sake samuwa gashi dai munyi nasara hankalinki ya dawo jikinki amma an tab'a miki wata jijiya aka wacce tayi sana diyar lalacewar idonki yasanya kika dawo makauniya bakya gani" shiru tayi kamar yanda kowa yayi shiru tamkar bataji meyace ba secan hawaye ya fara gangara daga cikin idonta da suke abude bazaka taba cewa basuda lapiyaba ,batayi magana ba wannan ya sanya kowa ya sanya bakinshi ana bata baki seda taji kowa yayi shiru sannan ta sanya daya hannunta dabashida ruwa ta dafe qirjinta tace cikin d'aga murya

"meya sanya a rayuwa nayi rashin sa'an zuwana aduniya? Meya sanya wannan baqar zuciyar tawa takesan mutumin da yafi qaunar mutuwarsa akan ya d'aura idonshi koda akan me ita,meya sanya a rayuwa sam na zab'i bak'in cikina akan farin cikina,meya sanya zuciyata keson wanda bashida buri illah yaga qarshenta,lallai ina cikin tashin hankali ba adadi,lallai yaa shaam da inada ikon raba wannan wahalalliyar zuciyar tawa da k'aunarka wlhy da nayi a yanzu,inama ace inada ikon raba raba rayuwata da ruhina ko zan huta da wannan baqar soyayyar da batada ci gaba ko kad'an seci baya,ina ma ace zan iya sanya hannu in lalubo inda rad'ad'in sanka yake inyi wurgi dashi,kaico na dana zab'i abu mafi muni arayuwata,kaicona dana zab'i mummunan k'haddara da hannuna khaicona dana siyo makancewar idona da hannuna kaicona ni hafsatu,kaicona ni lelen daddy da Abba" wani razanannen kuka ta saka me tsuma zuciya wanda baya misaltuwa duk kuwa cikin d'akin aka rasa me rrrashinta.......Dr.sayyeed ya tabbatar musu da cewar matsalar bame yawa bace idonta ze iya bud'ewa yanzu,ko gobe ko anjima ko wata ran ko wata shekara kokuma har abada,Allah shine yabarwa kansa sani,haka hafsat tayi wata daya a asibiti gashi sam ya kasa yiwa halima komai sabida san dayake mata kurin dai ya qaurace mata kuma sannan be nuna mata komai ba,har aka sallami hafsat ta koma gidan Abba haris.

A gida Abba haris yayi kiran shammaz agabdan daddy da momy ya kalleshi cikeda nutsuwa yace

"shammaz abinda yasanya nayi kiranka ba komai bane illah zancen komawan hafsat d'akinka wato gidan auren ta" Da sauri ya d'ago ya kalli abba yace dashi "Abba nifa na rigada na saki hafsat kuma bance zan maida ita ba wane komawa kuma zatayi,kurin dai Allah ya bata wani mijin ta aura" cikeda mamaki kowa ya kalleshi wannan karon har daddy abba yayi karfin halin cewa

" Ai wlhy tunda ka nakasa ta seka zauna da ita,so kakeyi ka gama lahanta mata rayuwa" cikin bacin rai yace

" Haba abba nifa ba qaramun yaro bane,sa annan kuma zakuce zakumun dole,yarinyar ban sota tanada lafiyaba se yanzu,dan Allah na rokeku karkuce zakumun dole kalar na farko kundai ga ba aci nasara ba,ba alkhairi a tare da wannan auren,inshaa Allah zataji sauqi ku aura mata wani,kuma ni ba qinta nakeyiba kurun dai ina gudun gurbacewar zumuncine sabida kunga bawai san aure nake mata ba,kuma ma koba itaba banasan auren zumunci" Sosai da sosai maganganun shi suka girgiza rayukan ilahirin mutanen wurin,lallai shaam baze rasa yin shaye shaye ba,Abba haris miqewa yayi yace

" Bazan maka baki ba Shammaz amma kaje duniyace,inshaa Allah kana darai hafsat zataci gaba kaikuwa kana bayan yan baya" yana kaiwa nan yayi waje,daddy ma waje yayi batare da yayi magana ranshi a b'ace momy ce tace

"kaima danane shaam amma dan Allah inaso ka dubi girman zumunci ka taimaki qanwarka,waye ze aureta tana makauniya yarinya ga qarancin shekaru ko haihuwa batayiba" budar nakinshi se cewa yayi

"momy dan Allah kiyi hakuri wlhy bazan iyaba" aikam momy kuka ta saka cikeda takaici shikuwa ko a jikinshi yayi waje abunshi....

Mom Nu'aiym [1/22, 7:56 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

13 Yaukam rayuwar daddy tayi matuqar b'aci da wulakncin shaam akan hafsat,lallai wannan yaron yazo da salo na raini iri iri,banda haka tayaya ma agaban su kaikoma ba agabansuba zece wai baze auri hafsat ba haryana iqirarin be sota tana da lapiyaba se yanzu data zama nakashashiya,ba abunda zece dashi koya nuna masa zega iya gudun ruwanshi tare da jiran matakin da Haris ze dauka.......

Hafsat zaune tanaso taci abuncin dake gabanta amma bata saka cokalin wurin daya kamata,har ranta takejin wani tuquqi,wannan ya sanya ta ajiye cokalin ta laluba ta gincira,duk wannan abun datakeyi khairri na kallonta tana hawayen tsananin tausayinta,zuwa tayi ta zauna kusa da ita ta kamo hannunta tace "Sister ya bakici abuncin da yawa ba kaddai harkin koshi?" Murmushin yake tayi tace " Na qoshi ne wlhy"

"Nasani baki koshiba hafsat,kawai sabida bakya saka spoon din inda ya dace ne,kiyi hakuri na baki kanki saba kuma inshaa Allah zaki warke ai haka doctor yace zakiji sauqi kinji" hawayen da dukkaninsu ke qoqarin tarewa ya silalo musu hafsat tace "Khairiyya haryaufa yaa shaam bezo ya duba niba,da gaske manufarshi kenan ya rabu dani har abada?" kukane ya kwace mata ta toshe bakinta,khairiyya tama rasa me zatace mata "kiyi hakuri hafsat,amma barin kira miki shi awaya" batace komai ba wannan ya sanya khairiyya taje waje tayi kiran shammaz akan dan Allah yazo hafsat ta damu da rashin zuwansa,beyi musu ba yace yana nan zuwa da dare.....

A parlor zaune hafsat take a kujera me mazaunin mutum biyu,se shaam dake zaune a me mazaunin mutum d'aya,dak'yar ya iya bud'e bakinshi yace

"Hafsat ya jikinki"

"Naji sauqi Alhamdulillah"

"Akace kina nemana?" sadda kanta tayi qasa "Yaya dama zancen komawa nane gidanka,dan Allah kayi hakuri abubuwan dasuka faru wlhy ko mutuwan khaleefa ba laifina bane lokacin sa ne yayi" murmushi yayi yace

"Haba hafsat,kewai bakya fahimtar abubuwane? Ban soki nakuma zauna dakeba sanda kike mutum me lapiya,se yanzu dakika zama nakashashiya,na dade da fad'a miki sam bakin rijiya ba wurin wasan makaho bane saura miki yaushe ki gama iddah,idan ma banyi kuskure ba aiba idda a kanki,saboda haka kiyi hakuri ki kalli dahir ni bazan taba dawo dake gidana ba,ina miki ao irinna yan uwantaka matsayinki na kanwata amma bawai zancen aure ba" dukda bata gani amma hakan be hanata duban inda take jiyo sautin muryanshiba tace tana kuka

"Yanzu yaa shaam idan kai dakake dan uwana ka gujeni akan inada matsala waye aduniya ze aureni? Kaine sanadin lalacewar rayuwata,ka b'atamun duk wani abu danake taqama dashi,bani ga karatuna babu labarin future na,banida d'a ko d'aya a duniya da wanne kakeso inji?" murmushi ya kuma yi

"Hafsat wlhy kinji na rantse bazan tab'a iya zaman aure dakeba,ke ni idan ma kinamun wannan maganar haushi kike bani wlhy,kimun magana kanki tsaye indai zaki bani matsayin yayanki to zakiga gata na haduwa,amma zancen aurennan yarabu kenan har abada,idn bakida wani abun fada zan wuce"......sanda ta d'anyi shiru sannan tace

" Nayi dana sanin saninka arayuwa,nayi danasanin kasancewarka d'an uwa na jini agareni,nayi danasanin aurenka,nakuma yi danasanin aurenka,nayi danasanin kasantuwar zuciyata tawa ina ma ace canje aka mun bisa kuskure dana roqa a sauyamun da tawan sabida na kaucewa wannan wahalalliyar soyayyar,daga rana me kama da yau inaso ka nemo biro da takarda kakuma rubuta ka ajiye cewar ni hafsat nakashashiya nafita arayuwarka na har abada,na yanke duk wata alaqa dake tsakanina dakai, harta zamanka d'an uwana,ko a hanya ka ganni karka nuna sanayya tsakanina dake,bana buqatarka arayuwata ka sani ayau d'innan wlhy na tsaneka tsana mafi munin tunani,bazan hana zuciyana haukanta na sanka ba amma zan iya haramtawa rayuwata koda gaisawa dakai koda hakan yana nufin zan rasa ilahirin rayuwata kuwa tunda ai ka gama nak'asani meya ragemun,nice nan yaa shaam zan tabbatar maka da cewar bakin rijiya sam ba wurin wasan makaho bane" Yad'anyi mintuna biyu bece komai ba secan ya nisa yace "Hafsat me kuma ya kawo maganar tsana anan nifa d'an uwankine" miqewa tayi ta soma doddogara sandarta tana neman hanyar waje,kasancrwar tasan tsarin gida. Yasanya tayi amfani da basirar ta ta nufi cikin gidan zuwa dakinsu.....duk wannan zantutuukan nasu akan kunnen abba haris tausayinta me tsananin gaske ya rufe shi,daganan ya qudiri niyyar nemawa hafsat lapiya kota halin qaqa koda kuwa dukkanin abinda ya mallaka ze qare.....

Hafsat tama kasa kuka,gaba d'aya wani mummunan yanayi takeji a zuciyarta game da shaam,tabbas yau tafara jin yana fice mata arai cikin qanqanin lokaci,wayantane ya soma ringing tashiga lalubarta tana kamowa dama wurin sazata amsa kira baze mata wuyaba ya sanya ta d'aga ta kara a kunne

"Assalamu Alaikum" shine tajiyo am fad'a a d'ayan b'angaren tun kafin tayi magana,cikin sanyin murya tace

"Amun wa Alaikassalam,barka da wuni"

"Hafsat ya gida ya kuma jikinki?" "Da sauqi Alhamdulillah" ta bashi amsa "Sunana Dr.sayyeed Hameed Ali uncle d'inki" Murmushitayi tamkar yana gabanta sannan tace "Ayya Uncle say ya aiki yakuma kwana biyu?"

"Alhamdulillah hafsat,dama Number din abban ki damuke da afile nayi tankira baya zuwa gashi kuma emagency case ne ya taso,shiya sanya nace barin nemeki ko zaki had'ani dashi"

"Babu damuwa uncle say barin je ingaya mishi seya duba last call nawa ya kiraka,amma sekayi hakuri ni kadaice adakin khairii batanan,idan tashigo seta rakani gun abban" sosai ta bashi tausayi yace "Babu damuwa hafsat,nagode sosai" "nima nagode sosau uncle say Allah ya saka ma da alkhairi" har ranshi yaji dadin adu'arta lokaci d'aya ya tuna da matarsa margayiya data tafi ta barshi da tsananin kewa,itace take yawan masa adu'a irin wannan tun bayan mutuwar mahaifiyarsa......

Office Abba yaje ya sameshi,bayan sunyi magana awaya,da suka gaisa Dr.sayyeed ya tattara nutsuwarsa gun Abba sannan ya gyara zaman gilashin idonsa yace da Abba

"yallab'ai Allah shine ya dasamun tsananin tausayin hafsat wanda tunda nake ban taba jin tausayin patient kwatankwacin yanda naji akan hafsat ba,musamman yanda na kula da karacin shekarunta, da farko dai ni haifaffen qasar India ne amma kuma d'an asalin Nigeria,mahaifina likitane kwararre wanda gaba d'aya acn yake aiki acanne ya had'u da mahaifiyata datake Ba'indiya kasancewarta musulma gaba da baya ya sanya basusha wahala iyayensu suka aminta dasuyi aurensu, acan aka haifeni kuma acan nayi karatu na gaba daya,bayan mahaifiyata ta rasune mahaifina ya dawo ainahin qasarsa wato nan Nigeria a kuma birnin sokoto,inada qanne na mata guda biyu suna gidansu mahaifiyata dake Babban birnin indiya wato Goa acan suke karatunsu,ni kadaine nabiyo mahaifina nayi aurena anan har Allah ya karb'i ran matata a wurin haihuwa......Dalilin daya sanya na baka tarihin rayuwata shine sabida inaso kaje kayi bincike kaji koda zaka da abinda zan fad'a maka yanzu,dukda yake dakai nakesan muyi tafiyar idan ma hakan ta kama" Dukda yake Dr.say yayi magana me harshe damo amma abba be katse shiba yace "Ina jinka sayyeed"

"Mahaifina ya mallaki qatotuwar asibiti tashi ta kanshi a k'asar india inda kusan garuruwa hudu a fadin qasar zaka tarar akwai branches nata,zan baka komai sekayi browsing ka gani,akwai wani qwararren likita dake aiki a asibitin na mahaifina wanda shararre ne a b'angaren k'walwa shine nayi waya dashi sabida al'amarin hafsat yana damuna a bakin shi naji cewa inshaa Allah indai tanada rabon gani a duniya Allah ze bashi ikon mata aiki kuma fitowar farko ta warke sabida badashi aka haifeta ba, dama nikuma zanje india gun yan uwana dakuma kula da asibitin ta mahaifina shine nake sha'awar zuwa tare dakai da hafsat idan bakuda damuwa,nidai ayanda nake tausayin hafsat bana san ko sisin ku har jirgi ma nine nan zan dauki nauyi amincewarku kawai nake buqata dakuma uwa uba adu'arku" sosai Abba haris yaji dad'in wannan zancen yace "wannan ai babban ci gaba ne sayyeed,kuma zancen yadda tun yaushe aina yarda zancen kuma wai kyauta duk bata taso ba nine nan zan biya komai har zancen tafiyar ma,kuma wlhy na gode nagode maka sayyeed Allah ubangiji ya albarkaci rayuwarka ya sanya haske acikinta yakuma d'aukaka,Allah ya jib'anci lamuranka ya baka wata matar ta gari ya ilmantar da bayanka yakuma tallafi bayanka sayyewd" godiya sayyeed din tun kafin abba yabar asibitin yafara processing visa batare da sanin kowaba.......

Ranar wata juma'a hafsat na kwance ta rufe idonta acewarta ba amfanin bud'asu wayanta ya soma ringing janyowa tayi ta kara a kunenta bayan ta d'aga,jin muryanshi kad'ai ya sanar mata waye me kiran cikin shagwaban dabata masan tana dashiba tace "Uncle say se yanzu,ni baran ma kula kaba Allah kuwan" murmushi yayi tamkar tana gabanshi

" Beauty kefa rigimanki baya qarewa,wlhy Aikine yasha kaina matuqa kiyi hak'uri yanzu ya jikinki ina fatar kinji sauqi?" turo baki tayi "Ni bazan kulakaba" dariya sosai tabashi amma sabida bayasan ya b'ata ranta yace "Kiyi hakuri mana Beauty,aina sanar miki uzurina kuma fa yau zan siya miki pop corn da ice cream plus frozen coffee amor" murmushi tayi

"Ni bazaka siye ni da wannan ba bazan ma shaba,nidai kawai ka kawomun qawata dan Allah itane take d'ebemunnkewa"

"Naji zan kawo tan indai suhaila ce amma dai gaskiya se gobe,yau ina riqe sosai" murmushi tayi tace "Babu damuwa uncle say Allah ya kaimu goben" sallama sukayi sannan suka ajiye wayoyin su, hafsat se murmushi takeyi tun zuwan suhaila arayuwarta take jin sanyi abubuwa da dama suna canja mata ko yanzu tanata faman tunanin yanda zatayi idan tabar qasar,shiya sanya taso ayi auren uncle say da suhaila kafin tafiyarsu india dase su tafi tare da qawar tata me yawan d'ebe mata kewa......

Yauce ranar tafiyar su hafsat india,kowa se adu'a fatar samun nasara suke musu, tafiyar har da umma aciki, da abba......nima ina musu fatan alkhairi..

Don't forget to vote and comments...... [1/23, 9:57 PM] Billy Galadanchi: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

13 *FLASH BACK*

A ranar da yaa shaam yaji komai a ranar Haleemah taje wurin bokanta,kallonsu yayi itada uwarta yace

"Kunyi sakaci dukkannin aikinku ya lalace,kuma mijin yarinyarnan yaji komai ciki kuwa hadda kashe masa gudan jininsa,kunsan cewar wannan abun ba qaramun b'ata ran shi yayi ba,sabida haka wannan aikin dazakuyi bashida wani amfani,idan kuwa kunaso amasa sabon aiki daze rufe masa baki tokuwa ke Haleemah sekin baiwa Aljani kyautar mahaifarki sukutum,tareda sha'awar mijinki ma'ana zamu cire dukkanin wata sha'awa dayake da ita a 'ya mace" zabura haleemah tayi tace "Nashiga uku boka,shikenan ni bazan qara haihuwaba? Kuma shi mijin nawa baze qara samun wata sha'awa akaina ba to meye amfanin auren??" Tsawa ya daka mata

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull