Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 11

Bakin ruhi complete - Chapter 11

Bakin ruhi complete Chapter 11: Bakin ruhi complete Chapter 11. "Na rantse da Allah ni ban yi masa komai ba" ta faɗa tana mai ci gaba da kuka.

3,327 words

"Na rantse da Allah ni ban yi masa komai ba" ta faɗa tana mai ci gaba da kuka.

Na dubi mahaifiyarsu na ce ,"ki ce ta yi bayani da kanta ko kuma na kira ƙanwata ta tirsasa mata"

Cikin rarrashi ta ce "Nadiya ki yi bayani mana kin ga halin da ƙanenki yake ciki dai ko?"

A tsorace ta soma yin magana,"dama uku ga watan Mayu ne wata rana ina suyar awara sai ..sai wata ƙawata da muka taɓa aji ɗaya da ita ta zo ita da saurayinta a mota suka saya a nan ta karɓi lambata ta saka ni wani group na ƴan mata ƴan gayu kullum sai sun aiko hotunan kansu kowacce tana gasar sutura,yayin da kuma gefe guda suke ta wayar iphone.A duk lokacin da na suna turo hotunan iphone hankalina tashi yake,don ni wata tsohuwar itel ce gare .Wata rana sai na kasa haƙuri na tambaya wayar za ta kai dubu nawa sai suka shiga yi min dariya,nan ne na ji labarin wai sama da miliyan ɗaya.Sosai na yi mamaki,amma sai wata ta biyo ni ta pc ta ce min in dai ina buƙatar iphone zan iya samu da na tambayeta ta yaya kenan ? Sai ta ce "kawai ɗigon jini uku ne za ki ɗiga a wani zobe shikenan " a lokacin sam ban yarda ba don dariya ma abin ya bani,sai kuma na share ta amma da yake ƴar fitina ce haka kullum take aiko min hotunan sabbin wayoyi da kuma kuɗi bugun Amurka tun ban damuwa har zuciyata ta kwaɗaita min kan cewa ya kamata ni ma in samu tawa.Kawai sai na tura mata saƙon "ina son samun iphone ɗin ya zan yi?" sai ta ce "ki same ni a ƙofar babbar kasuwar turaren wuta in kika tambaya da shagon J ƙamshi za a kawo ki" haka kuwa aka yi bayan na kai markaɗen awarar da zan yi sai na shiga taxi na je can shagon nata.Duk a tunanina wata babbar mace ce zan gani amma sai na tarar da wata matashiya wacce ba za ta wuce shekara ashirin da biyar ba,da murna ta tarbe ni bayan ta bani wurin zama sai ta miƙe ta ɗauko wani baƙin zobe mai kamar gawayi ta miƙo min na karɓa ina juya shi.Sai ta yi min bayani "ɗigon jini uku kawai za ki ɗiga a samansa shikenan in kin yi sai ki zo ki karɓa amma jinin cikin wani family ɗinku in kuma kina ɗa ƙane ko ƙanwa nasu ma yana yi"

Sam ban yi tunanin cewa hakan zai kawo wata matsala ba, wannan yasa da dare bayan Amar yayi bacci na tsikare shi da allura tare da ɗiga jinin nasa kuwa ga zoben,a lokacin da na yi haka sai na ga zoben ya bado wani irin haske kafin kuma ya ɗauke sai na je na ɓoye shi cikin jakata.Washegari haka na je don kai wa J ƙamshi zoben sai na karɓo wayata,amma sai ta nuna min cewa ai ba ita za ta bani ba sai dai mu je ta yi min rakiya na karɓo.

Shi ne fa ta ɗauke ni a motarta muka je can wani ƙauye ,gidan wata tsohuwa ne ba mu ma shiga ba ita ta fito ta tara min hannu na ciro zoben na bata ita kuma ta miƙa min iPhone ɗin.To tun daga wannan rana sai Amar ya soma firgita cikin dare yana mugayen mafarkai,da Mama ta tambaye irin mafarkin da yake sai na ji yana zayyano irin siffar tsohuwar nan wai tana zuwar masa a mafarki.Da farko an fara yi masa hayaƙi,to duk in an yi masa shi sai ya soma yin haɓo jini na yi masa zuba ta hanci wannan yasa aka watsar .A jiya ni kuma na soma ganin abin ban tsoro,a duk lokacin da zan ɗauki hoto sai na ga Amar a bayana yana kuka jini yau da na gwada yi ma har da muryarsa na ji yana cewa "anty Nadiya don me? Don me za ki bayar da ni ? " ina cikin wannan shock ɗin ne kuma muka ji kukansa a banɗaki da muka je sai muka ga yana kukan jini." tana kawowa nan ta yi shiru,yayin da kuma mahaifiyarta ta yi cikinta za ta dukanta amma su Dr suka hana tare da fitar da su waje.

Raina na ƙuna,zuciyata na zafi na ce a kira Aliya.Sam ban san meke damun ƴan matan yanzu ba da suka ɓace don kayan ƙyalƙyali,wasu ma ko tsarki ba su ida iyawa ba amma suna son yin ɗagawa da tunƙahon nuna wa duniya su ma wasu ne.

Bayan Aliya ta zo na faɗa mata komai,ɗan murmushi ta saki kafin ta zo dab da kunnena kafin ta ce "jininki da na Maheer ne magani,ban san haka ba sai ɗazu da na ga ya yi wa Meelat allura da shi.Hanya mai sauƙi ita ce ku yi aure ku zama abu ɗaya,amma ina ganin kamar shi Maheer ba zai iya aurenki ba shi yasa yake haɗa jininki da nasa don magance matsalar da ta shafi BAƘIN RUHI "

Shiru na yi ina nazari,kusan abin da ta faɗa sai na ga gaskiya ce.Sosai kuma na ji ciwon abin da Maheer ɗin yayi in dai tunanin Aliya ya zama daidai na bai iya aurena ne duk da cewa shi tun tuni ya san da dama wannan ce solution to tabbas zan nuna masa ni ma ƴar daba ce ta ƙarshen lamba.

Ban gama tunanin yadda zan ɓullo masa ba ya shigo ɗakin yana wani hura hanci,idona bai sauka ko ina ba sai akan farar rigarsa wacce shatin laɓa ya fito ɓaro-ɓaro duk jan baki ya ɓata ta.Na kawar da kai ina jin zuciyata na tafasa yayin da kuma amon muryar nurse Fatee yake dawo min na abin da ta ce.

'Ko mene ne yayi mata? ' na tambayi kaina a zuci,na kuma ba kaina amsa da ' me fa zai yi mata in ba iskancin da suka saba ba?'

Sai kuma na juya ina kallonsa,ƙarin ruwa ne yake haɗawa tare da sakawa yaron Dr David shi kuma uban surutu yana basa labarin abin da ya faru yayin da Dr Muhamud ya koma gefe yana hararen Masheer sai kuma na ji haushin haka har ban san lokacin da na ce "Dr Hamuuud!" ba wai Dr Muhamud ba hatta Masheer sai da ya juyo ya kalle ni ,shi kuwa David wani iri na ga yayi kamar bai tsammaci haka ba kuma bai ji daɗi ba.

Shi kuma Dr Muhamud murmushi ya sakar min yana mai cewa "Haulatu ya dai? Allurar kashe jikin ta sake ki? Kina jin yunwa ne?" na ɗan yamutsa fuska ina kallon Maheer na ce "tea kawai nake so mai zafi" da sauri ya kawar da kansa,ina jin lokacin da Dr David ke cewa "Maheer na zata ita ce Queen ɗin da kake bani labari"

Bai basa amsa ba,ya miƙa masa allura ya ce "please ɗebo jininta ka kawo min" ya karɓa ya zo ya kama hannuna ya soma jan jinina Dr Muhamud da ke shirin fita ya ce "me za a yi da jininta? Patient ɗina fa ce wannan"

Dr David yayi ƴar dariya kafin ya ce "kar fa ka manta ni na yi mata ɗinki yanzu,to ka ga ni ma patient ɗina ce" sai kuma duk suka yi dariya shi ya fita shi kuma ya kaiwa Dr Maheer jinin ya karɓa ya jawo nasa sannan ya zuba shi a cikin ledar ƙarin ruwan Amar.

Dr David ya zo ya ja hannun Aliya suka fice har da rufo ƙofa,wani irin tsoro ne na ji ya dirar min musamman da na ga shi gogan ya juyo yana yi min wani mugun kallo mai cike da tsana.Da ya soma takowa inda nake wani irin yunƙurawa na yi zan tashi amma na kasa,cikin zafin rai ya ce "mene ne haɗinki da Dr Muhamud? Ɗan uwanku ne? Kun haɗa iri da shi ne? Shishigin mene ne kike yi masa? "

Cikin tsiwa na ce "ina ruwanka to? Kai ɗan uwanmu ne da kake yi min masifa? "

Ya waro ido da alamu bai yi tunanin haka ba,a zafafe ya ranƙwafo yana mai dafa gadon da nake "ni ne masifafe?"

"Eh ɗin in banda masifa ni ƴar uwarku ce da za ka bi duk ka takura mu ni da saurayina"

"Saurayinki? Okay soyayya kuke kenan?" ya watso min tambayar yana canza launin idonsa,sai a yanzu na farga cewa fa na yi katoɓara don kuwa zargi ne kawai nake Dr Muhamud na sona amma bai furta ba.

Sam ban ga fitarsa ba sai ƙarar ƙofa na ji gammmm,na kalli ƙofar ina jin duk babu daɗi a raina.Babu jima kuma Dr Muhamud ya shigo hannunsa riƙe da kofin shayin,shi ya taimaka min na jingina kafin na sha shayin duk da kuwa ba da son raina ba nake haɗiye shi.

★MAHEER

Dogon saurayi mai cikar zati da kyawu,matashi ɗan kimanin shekara talatin da shidda.Maheer dai fari ne sol mai doguwar fuska,yana da cikar ƙasumba da sumar gashi mai santsi irin ta Hausa Fulani.Bai da ƙiba,siriri ne sai can saman ƙirjinsa da ya ɗan buɗe,manyan idonsa sune suka fi fito da kyawunsa da kuma jan hankalin ƴan mata don tamkar na mai jin bacci haka suke.Izzarsa da jiji da kai da kuma tsantsani su suka hana shi har izuwa yanzu zaɓar abokiyar rayuwa,don duk gani yake in ba macen da ta san ciwon kanta ba to ɗaiɗaiku ne suka iya wanka mai kyau.Yana ɗaya daga cikin rainin hankalin da yake yi wa ƴan mata masu bibiyarsa da sunan so ya ce su je har su iya tsarki.Duk fitinar budurwa da nacinta ba ya ɓata lokacinsa wurin tunaninta,sannan kuma yana alfahari da hakan sai dai zuwan Haule gidansu duk ta zubar da wannan ajin nasa.Tun ranar farko da yayi mata kallo ɗaya ya ji wani lantarki ya ratsa kaf illahirin jikinsa,a lokacin ma tana cikin dattinta irin na buzayen daji amma a haka ya ji ta yi masa musamman yanayin saurin bayyanar da tsoronta.Don lokacin da suka fara ganin juna ya dawo daga aiki ne a gajiye ya shigo sanye da kayan likitoci ita kuma daidai tana yi wa Hajiya bayanin duk abubuwan da ta iya amma tana ganinsa ta tsorata tare da yin shiru.A ranar da ya shiga wanka yana rufe ido ɗan ƙaramin bakinta kawai yake gani yana motsi,bai taɓa kissing ɗin kowacce mace ba a kanta ya ji sha'awar yinsa amma ya basar tare da yin tsuki yana ganin kuma me ma zai yi da ƴar ƙauye.

Sai dai duk yadda ya so hakice ta abu ya cuttura don ta samu wuri a zuciyarsa ta yi tsiron da kullum sai sabon toho yake tare da fure da ƴaƴa.Kafin ya gane ya kamu da sonta ya sha wahala,don haka kawai yake komawa gida don ya ganta tana aiki ko kuma ya tsiri kallon tv a babban falo don kawai ya ji ta kusa da shi,a cikin irin kallon ƙurillar da yake yi mata ya gano tana ƙumshe da wata baiwa wacce bai fahimci ta mece ce ba sai a ranar da ya tarar Hajiya ta sha yawunta.Tun a lokacin kuma ta ƙara samun wuri a zuciyarsa ta zauna daram,abu na farko da yayi don yi wa muguwar ƙaunar da yake yi mata adalci shine haɗa tunaninsu wuri guda ta hakan ne yake samun duk wani motsinta.

Yana jin mugun kishi a duk lokacin da Dr Muhamud ya tambaye shi ina likitar gargajiya,amma bai kai ga samo hanyar da zai toshe wannan matsalar ba shi ne ita ma Haulen ta tsiro da nata salon.Don iya shege har da guntule sunan Dr Muhamud ta mayar da Hamud,sosai abin yayi masa ciwo shi yasa ya kasa ɓoyewa yayi mata jan kunne shi ne ta yaɓo masa baƙar magana.

Yana fitowa daga wurinta dakyar ya iya kawo kansa cikin ofis ɗinsa saboda yadda idonsa ke rufewa tsabar ɓacin rai. Nurse Fatee wacce ke kwance tana baccin gajiya kan kujera yasa ƙafa ya tura ta da mugun ƙarfi har sai da ta wuntsile ta faɗi ƙasa,babu shiri kuma ta farka za ta soma yi masa kukan sangartar da ta saba ya daka mata wata mahaukaciyar tsawa ya ce "fitaaa! "

Sumi-sumi ta miƙe ta fice tana ɗingishi,Dr Maheer ya shiga watsi da duk abin da ya samu kafin ya cusa yatsunsa cikin gashinsa yana jin tamkar ya ciro zuciyarsa ya jefar ko zai huta da azalzalar da take yi.

Yana cikin wannan halin ne Dr David ya shigo ya tsaya yana kallonsa kafin ya ce "mene ne kuma duk wannan?"

Cikin masifar da ta zame masa jinin jiki ya ce "kenan ma ba ka sani ba? Ba ka ji da salon da ta kira Dr Muhamud ba? Mene ne haɗinta da shi? Ɗan uwanta ne? Babu fa dangin iya ballantana na Abba ,a gidanmu ya ganta shi ne ita kuma har ta iya kallon tsabar idona ta kira ni da masifafe "

Cikin kwantar da hankali Dr David ya ce "kawai ka furta mata kalmar so shi ne mafita" a zafafe ya katse shi da cewa "wa ya faɗa maka sonta nake? "

Dr David yayi murmushi ya ce "shi kuma laƙabin da ka yi mata na Queen fa? "

"Wannan kuma daban yake amma ni ban son ta"

"To tun da haka ne ina ruwanka da ita ? Kawai ka fita harakarta,in shi Dr Muhamud ɗin a gaske yake son ta ai abin alfahari ne a gare mu"

"Ka ga Please fita ka bani ofis " cewar Maheer yana mai nuna masa ƙofar fita,Dr David ya girgiza kai ya ce "dole fa sai ka fidda wannan aƙidar taka daga cikin ranka na cewa Maheer ba zai so kowacce irin mace ba,saboda da dai wallahi son yarinyar nan kak..."bai barsa ya ƙarasa ya yi saurin shigewa toilet ya bar Dr David ɗin nan a tsaye.

Jingina yayi a jikin ƙofa tare da yin shiru yana sauraren bugun zuciyarsa wacce ya lura ba ta yin irin wannan dokawar sai in Haule na magana da wani namiji.... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

15

Wani irin feshin wuta zuciyar Maheer take,ko tantama babu ya san a halin yanzu ita da Dr Muhamud ne suke a tare.Ya cije leɓensa na ƙasa kafin ya ɗaga ƙafarsa dakyar ya je gaban shower ya kunna pampon ruwa suka soma dukansa.Kamar wani mahaukaci ya soma magana shi ɗaya,"daga yanzu ba zan sake yi miki magana ba kuma wallahi ni ban son ki nake ba kawai ina kula ki saboda mahaɗin sirrin da ƴar aike ta baki,babu wata mace da Maheer ke so wannan ƙarya ne ban son ƴar kowa" sai kuma ya ɗaga kansa sama tare da buɗe idonsa ruwan na ta bugunsa,ya kwashe tsawon lokaci kafin ya cire kayansa ya ɗaura towel ya bi ta ɗayar ƙofar da za ta kai shi da keɓaɓen ɗakinsa da ke cikin ofis ɗin.

Dakyar ya iya ture tunanin Haule ya shirya cikin suit baƙaƙe ya fesa turare,baƙin tabarau ya manna saboda yadda ya ga idonsa sun yi ja . Ko da ya fito Dr Umar ya tarar a zaune kan kujera fuskarsa da alamun damuwa,yi yayi kamar bai gansa ba ya nufi ƙofar fita amma shi Dr Umar ɗin ya tsayar da shi ta hanyar kiran sunansa,ya tsaya ba tare da ya juyo ba ya ce "ban cikin yanayin magana Please ka bari za mu tattauna daga baya"

"Don Allah ka yi haƙuri ka saurare ni ka fi kowa sanin Fateema ita ce komai nawa,in wani abu ya same ta ba zan yafewa kaina ba.Please ka sanar da ni mene ne taƙamaimai ciwon nata? Ka ga fa tana can tana kuka ta rufe kanta a toilet "

Ran Maheer ne ya sake ɓaci,wato kowa so yake ya masa maganin matsalarsa amma shi babu wanda ya damu kan ya samu farin ciki."Fateema lafiyarta lau babu wata matsalar kwanya da take da,wasa take da hankalinka akwai wani ƁOYAYYEN SIRRI da ta ɓoyewa kanta,muddin kuma ba ta fitar da shi ba to duk maganin da nake yi mata zai tashi a banza ne don ko na zuƙe mata ruwan da an ɗauki lokaci dole wasu su taru" yana gama faɗa ya fice daidai kuma wannan lokacin ne Dr Muhamud ya fito daga ɗakin Haule yana wani sanyayyen murmushi mai fallasa sirrin zuciya.

Da wani mugun sauri ya ɗauke idonsa gare shi tare da ficewa ya bar asibitin kwata-kwata.Hanyar fita gari ya ɗauka yana ta sharara gudu kafin ya soma gangarawa zuwa cikin ciyayi,wuri ya samu yayi parking kafin ya soma tafiyar ƙasa.Sai da ya ɗauki kamar minti goma kafin ya iso wata tsohuwar rijiyar marar murfi,yasa tafukan hannuwansa ya dafa bakin rijiyar tare da ƙanƙance idonsa yana kallon baƙaƙen ruwan da ke kwance can cikin dogon ramen.

Zanen hoton fuskarsa ne ya soma haɗuwa kafin kuma ta fito daidai kamar yadda take a zahiri.Sannu a hankali ruwan suka fara tunkuɗowa suna yo sama har suka zo dab da fuskarsa,ido ya lumshe kafin ya soma yin wani Yare yana ambaton sunan wata mata kamar walƙiya haka matar ta bayyana a zaune a bakin rijiyar yayin da kuma ruwan suka ci gaba da yin motsi ta yadda suka rufe ƙafafuwanta ba a iya ganinsu.

"King sai yau aka kawo min ziyara?" dattijuwar matar ta faɗa wacce ta kasance shararriya kuma fitacciyar matsafiyar tsafi sai dai nata kan turbar arziki take gudanar da shi.

Ba tare da ya ɗago kai ya dube ta ba ya ce "Yabobo na zo nan ne domin neman wata alfarmar a gare ki fatan za ki yarda da muradina"

Wani murmushi ta yi mai sauti kafin ta ce "ka yi haƙuri King Maheer,dole Queen Haulat na buƙatar dogon lokaci domin yin nazari akan abin da kake guje mata sai dai kai ma da naka laifin me yasa ba ka fallasa mata sirrin zuciyarka ba"

A hankali ya ɗaga kansa yana kallon Yabobo ta baƙin tabarau ɗinsa,muryarsa har sai da ta shaƙe tsabar yadda baƙin ciki ke naƙarƙasar zuciyarsa ya ce "ni fa ba na sonta,kuma babu yadda za a yi na aure ta don ba zan iya bayyanar da sirrina ga ƙanƙanuwar yarinyar da ko tsarki ba ta iya ba.Sannan please Yabobo ki taimaka ki sa ƴar aike ta je ta karɓe mahaɗin sirrin da ke ga waccan yarinyar in ya so ko Ikilima ce ta bai wa"

Nan ɗin ma murmushin ta yi kafin ta ce "Ikilimar da ka ɗirkawa shegen duka ita ce kuma yau kake son a baiwa ƙarfin iko mai tsarki? Ka sani power da ke jikin Haulat tsarkaken matakin iko ne wanda ba a ko wane irin gangar jiki zai zauna ba sai mai tsarkaken ruhi wanda ba a yi baɗala da shi ba"

A zuciye ya ce "baɗala kuma ta nawa Yabobo? Tana can asibiti ta saki gangar jikinta wani ƙaton banza na kama kafaɗunta yana fakewa da sunan taimaka mata ne yake don ta tashi,sannan har hannunta yake riƙewa fa"

Yabobo nutsuwa ta yi tana kallon yadda Maheer ke zuba masifa mai bayyanar da tsantsar kishinsa,amma idonsa sun rufe kan ƙudirinsa na bai iya soyayya da kowacce irin mace sai ya bincika ya tona ya samo mai tsabta.

"Riƙon da Dr Muhamud ya yi wa Haulat ba za mu iya kira shi da baɗala ba,in ma akwai wanda za a kira a haka bai fi kai wanda ka yi mata ba ka raba ta da suturar jikinta ka kalle mata jiki saboda kana tantama da shaƙu a kanta.King ina so ka sani kowacce ragaya da tata ƙwarya,haka kaina ƙyaure ita kuma ƙofar rufin asirin ɓoyayyar duniyar.Kar ka bari ego ɗinka ya rinjaye ka ya rufe ma ido ka kasa ganin gaskiya,yanzu dai ka koma ka bata maganinta ko ta samu ta koma a bakin aikinta kuma ban son jin ka yi min gardama"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull