Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 10

Bakin ruhi complete - Chapter 10

Bakin ruhi complete Chapter 10: Bakin ruhi complete Chapter 10. "Ni ce na jawa kaina,silar hassadar ƙawata aminiyata wacce duk iyayenmu da duniya suka…

3,365 words

"Ni ce na jawa kaina,silar hassadar ƙawata aminiyata wacce duk iyayenmu da duniya suka shaida ƙawancenmu.Ni da ita kullum muna a tare,suturarmu kusan iri ɗaya ce don tsabar ƙaunar juna da Twins ake kiranmu.Ba zan iya ɗinka ko da hijabi ba ne ba tare da na yi mata ba,ita ma haka.Ajinmu guda da ita,haka wurin zamanmu ma komai yana tafiya daidai har zuwa lokacin da ƙawata ta haɗu da wani saurayi mai kuɗi.Ban taɓa ganinsa ba sai dai alkhairansa na tardo ni har gadon baccina,na san za ki yi mamakin jin na ce ban taɓa ganinsa ba to abin yadda yake business man mafi akasari zuwan dare yake yi a can gidansu ƙawata sai kuma aka yi rashin sa'a sam iyayena ba su barina fita da dare.Haka suka yi ta soyayya wacce ba ta ɗauki wani lokaci ba zancen aure ya shiga,sai bayan kuma har an kawo komai ne muka haɗu da wanda ƙawata za ta aura ba kowa ba ne sai tsohon saurayina wanda na rabu da shi shekarun baya kafin na haɗu da ƙawata.Yanayin fatarsa kawai zai tabbatar ma da kuɗi sun kwanta saɓanin lokacin baya da ko suturar kirki bai saka wa,a ranar da na gansa kasa bacci na yi sai na ji tsohuwar soyayyarsa ta dawo min sabuwa amma na ɓoye hakan a raina muka dai gaisa a matsayin mijin da ƙawata za ta aura.Duk shirye-shiryen bikin da ake yi da ni duk aka yi su,ina dai yin murmushin dole amma ƙasan zuciyata hassada ce da ƙyashi suka min ƙawanya.Ana saura kwana biyu aurensu ne kwatsam sai na ga wata lamba a wani group ta wani malami ya turo abubuwan tsafi,an manna ƴar tsanar roba biyu mai hoton mace da namiji da kuma sauran tarkacen tsafi a ƙasan hotunan yayi dogon bayani kan cewa duk wani aiki yana yi,na ƙulla alaƙa tsakanin saurayi da budurwa da kuma raba masoya da sauransu.Baƙin kishina yasa na bi shi pc na shaida masa ina son yayi min aiki don raba ƙawata da kuma tsohon saurayina,har na tura saƙon sai kuma na goge amma abin mamaki bayan na kashe data sai ga baƙuwar lamba ta kira ni,ina ɗagawa sai na ji murya wani bagwari yana cewa "ƴalinyana aikinki tuni an fara shi yanzu haka abu guda kawai ya rage a fasa auren ƙawarki da shi saurayin a yi da ke,muddin za ki yi to fa shikenan buƙatarki ta biya" wani irin tsoro ne ya kama ni a lokacin amma in na tuna irin mahaukatan kuɗin da na ga saurayin nawa yayi,murya na ɗan rawa na ce "mene ne zan yi?"

Ya ce "ki nemo jaririyar baƙar kaza ki jefa ta cikin salanga " yana gama faɗa ya kashe,jiki na yi min ɓari na fita na siyo kazar kamar yadda ya ce kuwa na jefa ta cikin salanga da ranta ina gamawa kiransa ya ƙara shigowa bayan na ɗaga ya ce "akwai garin magani na nan na sa an ajiye miki a bakin ƙofar ɗaki ki ɗauke shi ki yi wanka da shi kina kiran sunan ƙawarki da kuma shi saurayin.Haka na aiwatar da duk wani abu da ya umarce ni ba tare da tunanin komai,a washegari kiran ƙawata Fa'iza ne ya tashe ni yadda na ji muryartar cikin kuka sai na ji wani irin sanyi ya ratsa ni don ko tantama babu aikina ya ci.Sai dai bayan na ɗauka saɓanin haka na ji,wai ba ta lafiya duk ƙuraje sun fito mata a duk illahirin jikinta duk da ba haka na so ba amma haka na je na yi wanka na je gidansu.Tun a bakin ƙofa nake jiyo hucinta tana kukan azaba,a zaune na tarar da ita an kunna mata fanka daga ita sai ɗaurin ƙirji.Sosai na tausaya mata kuma ko da wasa ban ɗauka wai tsafin da na yi ba ne ya kamata.Duba da yadda yanayin jikinta yayi ƙamari yasa aka ɗaga bikinta zuwa wasu watanni uku,sai dai kafin wa'adin ya cika Fahad ya janye maganar aurensa da ita saboda duk an yawuce asibitoci Fa'iza ba ta samu lafiya ba ga kamannin fuskarta duk sun canza.Lokacin da na fara jin tsoro a wata rana ce mun je asibiti duba ta sai wata mata take bada shawarar a mayar da ita gida don ciwonta ba na asibiti ba ne da alamu baƙin sihiri aka yi mata.Har muka dawo gida ina juya wannan maganar a ƙwaƙwalwata,a daren ranar ne kuma na fahimci cikin bala'in da na tsoma kaina don kuwa shi malamin nan ba iya bokanci ne kawai aikinsa ba a'a shararren matsafi ne wanda suke da ƙungiyar asiri ta kansu.Da farko mafarkai na fara yi barkatai irin ga mu nan a maƙabarta muna hira da matu,wasu kuma gani nan na canza siffa rabi mutum rabi dabba,wasu mafarkan kuma muna cikin ɗakin taro muna cin nama ɗanye da kuma lemun jini.A duk lokacin da na yi mafarki makamancinsa ina tashi da ciwon kai da kuma kasala,sai abin ya soma damuna har nake tsoron yin bacci kamar a daren da na yi gamdakatar da wata mummunar halitta ta bayyana a gare ni tana kiran sunana tana cewa " Aiyush ki zo zuwa gare mu,ki tawo cikin family lokacin ƙaddamar da ke yayi" sai na fasa ihu tare da yin ƙara wacce ta tashi ƴan gidanmu.Da na koro ba'asi babu wanda ya yarda da ni,tun daga wannan lokaci kuma farashin abubuwan ban al'ajabi ya ƙara hauhawa .Ina zaune sai in ga abubuwan da ba su da rai suna numfashi,kamar cokali ta miƙe tsaye ko kuma tsintsiya ta dinga shara ita ɗaya.An yi wani lokaci kuma da zan ga inuwar mutum jikin bangon ɗaki ko kuma bayan labule da na yi ihu sai ta ɓace.

Tsawon sati biyu kuma aka hana idona bacci,na koma kamar Kare bana yin bacci sai in an yi kiran sallar asubah.Tsawon dare kuma ina a farke ana nuna min abubuwan tsoratarwa,a wani dare ne kuma saƙon waya shigo min kallo ɗaya na yi wa lambar na gane bagwarin malamin nan ne wanda babu neman da ban yi wa lambar ba amma aka ƙi nuna min ita haka har cikin groups na WhatsApp na duba ban same shi ba.

Ina ɗaga kiran ya ce "ki je ƙaddamar da aikinki na gaba,ki kawo mana jinin jariri sabuwar haihuwa za mu yi amfani da shi don sabunta soyayyarki da Fahad " cikin kuka na ce "ni na fasa ! Ban so ka daina aikin haka nan ya isa haka,ka faɗa min kuɗin aikinki sai na turo ma son aikin da ka yi ya wadatar tun da ka raba su ni dai ko bai aure ni ba to babu komai tun da duk mu biyun mun rasa"

Wata irin dariya yayi kafin ya ce "kin kuwa yi kuskure ,don mu Family ba ma taɓa yafiyar member duk wanda ya shigo to ya shigo kenan ba zai fita ba,in kuma kika yi kuskuren ƙin yin abin da muka ce to ki kuka da kanki " yana gama faɗa ya kashe,ni kuma na buɗe murfin wayar na cire batirin tare da ɗaukar niyyar ba zan taɓa kunna ta ba sai ko kafin in ajiye ta ƙarar shigowar ssƙo ya shigo wayar.Saƙo ne mai ɗauke da bayanin dokokin abin da zan yi, ninkin tsorona ya lunku sau ba adadi saboda na fahimci suna da power sosai tun da har suka iya aiko min saƙo a wayar da babu batiri ciki.

Abin da suka sharuɗa min abu ne mai tsanani,ba komai suke buƙata ba sai jini.Jinin na ɗan mutum, wannan ya haifar min da zazzaɓi mai tsananin da yasa sai da aka kai asibiti kwana biyu na yi a can mafi haɗari don kuwa a can na gano cewa asibiti na ɗauke da wani ƁOYAYYEN SIRRI(MRS SADAUKI) wanda ta ɓoye iya masu ido uku kawai suke da izzar ganinsa.Bayan mun koma gida na samu shimfiɗa na yi bacccin da rabon da na yi shi har na manta,a cikinsa ne na yi ga ƙawata Fa'iza a zaune kusa da wata ƙorama tana kuka yayin da ni kuma ke ta yin dariya ban bar dariya ba har sai da na farka kuma tun a lokacin na soma jin canji a jikina.Da farko ƙaiƙayi na soma ji,da zarar na sosa sai ƙurji ya fito tun ina ɗaukar abin wasa har na soma yin jinya don kuwa haka gashin kaina duk ya siɗe kamar yadda kike gani ,duk wani kyawuna kuma ya ɓata na dawo mummuna.Amma dai hakan bai sa na yi abin da suka ce ba saboda tsoro ba zan iya kashe jinjirin yaro ba" tana kawowa nan da labarin ta ƙara ƙaimi wurin kuka,na ce "ita kuma ƙawarki Fa'iza ta samu lafiya ne?"

"A'a har yanzu tana kwance ita ma tana jinya" ta bani amsa ,sai a lokacin na maido hankalina ga Aliya,ban ɓata lokaci ba kuma na yi mata bayani bayan ta gama saurare ta ce "kamar yadda ta faɗa ɗin baƙin tsafi ne aka yi wa ƙawarta,ba za ta taɓa warkewa ba sai ranar da aka cire baƙar kazar nan da ta jefa salanga.Ita kuma maganinta banda labarin yadda za a yi ta warke,ke ce za ki faɗa"

A bayanin Aliya na fahimci cewa a dole dai ni ce zan samo mafita,sai dai kuma a zahiri ban san ta yaya ne zan yi ba don warkar da ita.Aliya ta miƙe tsaye ta ce "zan je na buɗe dakalin salangar da ta jefa kazar na fito da ita,ke kuma ki aje hankalinki da kyau ki yi tunani na tabbata za ki samo amsarki tun da ina ji a jikina tamkar ɗazu da muka je AOKIGAHARA wato dajin sirri an isar miki da saƙo sai dai cikin biyu ne ko dai ba ki fahimci me yake nufi ba ko kuma kin yi shiru ne"

Kalaman Aliya sam ba su sa na ji a raina cewa ai fuskata da ta Maheer ita ce ainahin saƙon da aka isar min ba,abu guda kawai na ce mata shine zan yi tunanin.Bayan fitarta sai hankalina ya kawo kan sarƙar wuyan da na ɗauko,na saki murmushi kafin na kai hannuna cikin riga na shafo ta tare kuma da riƙe ɗan dutsen tsakiyar da aka yi wa ado.Tamkar yadda in aka saka gogagen kaset yake rawa bai kawo hoto mai kyau to haka aka soma kawo min kilishen hotuna da bidiyoyin wasu lamurra da suka shuɗe na tsofin ƙarni da kuma na yanzu.Wani irin ɗaukewar numfashi ne ya riske ni yayin da nake kallon komai ido rufe,ban fahimci komai in aka cire hoton farar yarinyar da na gani tana leƙena a saman bene a ɗazu da muka je can gidan Alhajin da ya cuci Meeel.

Ganin matashiyar yarinyar nake tana gudu tana waiwaye haɗi da kuka tana kiran sunan Daddy,tana dab da faɗowa daga saman bene wani farin maciji wanda yake sak kamar irin launin fatarta ya zo ya tare ta daidai nan kuma na ji shiga tsinin allura a muscul ɗina da sauri na buɗe ido sai na ga Maheer ne yake jawo jinina cikin kwararon allura bayan ya gama ja ba tare da ya nemi izinina ba sai shi ma ya zuƙi nasa,kafin ya je daidai gadon Ayush mai siɗaɗen gashi ya zuba rabin jinin cikin ledar ƙarin ruwanta sauran kuma ya saka shi a aljihu ban san uwar me zai yi da shi ba. Nan take ita kuma ta soma yin wani fizge-fizge tana huci can kuma sai ta soma yin bacci mai nauyi.

Maheer ya ɗan juyo ya kalle ni,a cikin kallon nake hango takaicina a cikin ƙwayar idonsa sannan kuma da wani abu mai kama da gargaɗi.Daidai nan Dr Muhamud ya shigo,direct wurin gadona ya zo ya ce " Haulatu ya jikin naki?" ban amsa ba sai ma uban masifafu da nake kallo,shi kuwa Dr Muhamud ci gaba yayi da cewa "mu je ki yi wanka ki canza kayan jikinki,zuwa ƙarfe tara na dare za a shiga da ke ɗakin tiyata don ciwonki na buƙatar ɗinki"

Wani miskilin murmushi na ga Maheer yayi wanda na ji sam ban yarda da shi ba,sai na cewa Dr Muhamud "a'a ban so ni dai a bari ba sai an yi" ina gama faɗae haka sai ya juya ya kalli Maheer kafin ya ce "kar ki wani damu kin ji,zan tsaya har sai komai ya kammala sauko kin ji"

Dauriya na aro na gyaɗa kai kafin na ziro ƙafafuwana ƙasa,dakyar nake takawa Dr Muhamud na riƙe da hannuna muka bi ta gaban Maheer muka fice .Nurse Jamila ya kira ita ta kai ni toilet ɗin da zan yi wanka,bayan na cire sutura ta haka na daure na yi wankan har na gama ina tambayar kaina mene ne ma'anar murmushin da Maheer yayi.Rigarsa na wanke masa tasss,yayin da kuma nurse Jamila ta miƙo min wasu riga da buje ƴan kanti na saka.

A dadafe na fito ina bin bango,duk yadda nake jin rauni da idona ya sauka kan Maheer riƙe da hannun nurse Fatee sai da na ji kamar in arta a guje na je na raba su,dakyar na samu dai na kawar da kaina ina kuma sake maido dubana sai na ga ya shigar da ita wani ofis. Maganar Lubna ce ta dawo min a tunani ' ai shegen son matan tsiya ne da shi' tsabar tsiyar gumi yasa na fara takawa har na isa bakin ƙofar ofishin kunnena na kai jikin ƙofa don jin wainar da ake toyawa,muryarta na ji ƙasa-ƙasa tana yi masa magana cikin magiya "don Allah kar ka yi min ban so ,wancan karon ma da ka yi min kasa bacci na yi don zafi haka na kwana na wuni wurin na ta yi min zafi "

Saura ƙiris zuciyata ta buga jin wata lukutar masifa,na dafe ƙirji ina jin maduban idona na yi min gargada haskensu na ragewa. "Kina da zama ne tare da Dr Maheer?" na ji wata murya,dakyar na iya ganin mamallakinta wata haɗaɗiyar budurwa ce ta ci uwar kwalliya,kai na girgiza mata.

Ta ce "to me kike yi bakin ofis ɗinsa?"

Murya na ɗan rawa na ce "na zata na Dr Muhamud ne"

"Shi ga ofis ɗinsa can,mu je na kai ki" ta faɗa tare da kama hannuna,dakyar nake ɗaga ƙafata sam ban san idona na zubar da hawaye ba sai da na ji muryarsa yana cewa "Kuka kuma Haulatu? Kwanta mu ga ciwon" sai yanzu ma na farga da mun iso ofishin nasa.

Kallon tsanake na yi wa fuskar Dr Muhamud,fari ne irin mai haɗi da ja.Fuskarsa tana da ɗan faɗi,ta samu kuma albarka dogon hanci mai ɗan kauri,bai da saje sai dai bakinsa kewaye yake da gashi wanda shi ma salon gayu ne.A takaice dai shi ɗin mai kyawu ne,zuciyata na ji tana raya min ' me zai hana ki mayar da dukkan hankalinki a wurin da ake yinki? ' can kuma wani sashen ya ce min 'to mene ne ma abin damun kanki a lamarin Maheer? Ko dai sonsa kike?' ban samo amsa ba na ji muryarsa yana rarrashina.

"Ki yi haƙuri ba wani jimawa za a yi ba in an shiga ɗakin tiyatar,kuma fa na faɗa miki zan tsaya har a yi komai gabana "

Kai na jinjina masa,sai ya ja kujera ya umarce ni na zauna sai da ya taimaka min.Waya ya shiga yi ,na dai ji yana Dr David kafin kuma ya ce yana jiransa bayan ya gama kuma sai ya ƙara kiran nurse Jamila ta zo ta kai ni wani ɗaki ta saka min ƙarin ruwan da suka saka ni bacci.

Ban farka ba sai a ɗakin tiyata,dukkan likitocin mata ne sai namiji guda wanda nake kyautata zaton shi ne Dr David.Babu jimawa kuma aka fito da ni ,da fuskar Dr Muhamud na fara cin karo cikin waɗanda ke zaman jirana sai kuma Lubna da Meelat har da Hajiya .Aliya ce kawai a ban gani ba,Hajiya tana hawaye ta zo ta shafa kaina kafin ta ce "ya jikinki Haule?" ban iya cewa komai ba sai murmushi,na dubi Meelat wacce na gan ta cikin ƙoshin lafiya da dukkan alamu ita ma an yi maganin matsalarta wani sanyi na ji a raina haɗi da wata nutsuwa,ina shirin lumshe ido aka shigo da wani yaro yana fitsarin jini daidai nan ita ma Aliya ta shigo tana yi min ƙyaf-ƙyaf da ido alamun isar da wani saƙo..... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

14

"Duk ku fita waje don Allah "cewar Dr Muhamud nan duk suka fice,sai a lokacin ya matsa kusa da gadon yaron ya samu auduga ya shiga goge masa jinin haɗi da ƙoƙarin tsayar da shi amma tamkar ma ƙara jawo shi yake yi haka ya zubowa,wasu nurse ɗin tuni sun shigo.

"Ko a kira Dr Maheer?" wata ta tambaya.

"In Dr David bai riga ya tafi ba kirawo shi" cewar Dr Muhamud.

Da sauri ta fita sai ga shi sun dawo da Dr David ɗin wanda nake kyautata zaton shi ne wanda Lubna ta bamu labari,kana kallonsa kuwa ka ga kirista saboda sarƙar Cross da ke manne a wuyansa.Nan kuma na ga wani ikon Allah yadda yaron ya soma yin kuka da ya gansa yana wasu suratai,Dr David ya ɗan murmusa kafin ya cire sarƙar wuyansa ya mannata a goshin yaron a hankali ya fara rage sautin kukansa.

"Ina mahaifiyar yaron? Ku ce mata ta shigo don ciwon nasa ya haɗa da harakar sprituality "cewar Dr David ɗin,gyaran murya na yi sai Dr Muhamud ya juyo da ido na yi masa alama sai ya zo inda nake.

Murya ƙasa-ƙasa na ce "ina son ganin idon yaron,ka san na ƙware a harakar bayar da maganin gargajiya" yayi ƴar dariya kafin ya tura gadona kusan na yaron.

"Me sunanka?" na tambaye shi,a hankali ya juyo muka haɗa ido kuwa.Cikin shashekar kuka ya ce "Amar"

"Ko za ka faɗa min me ka gani kafin ka fara yin fitsarin jini?" ina yi masa wannan tambayar sai duk tsoro ya bayyana a fuskarsa,hannuna na kai na taɓa jikinsa nan take jinin ya tsaya daidai nan kuma mahaifiyarsa ta shigo tana hawaye.

"Amar faɗa min me ka gani?" na sake tambayar shi,cike da tsoro ya soma yin bayani "wata...wata mace mai fararen kaya,fuskarta baƙa ƙirin tana da dogayen faratai da kuma manyan ido ita ce ...ita ce... Ta kama ni tana sha min fitsari,shi ne na yi ihu da na ji zafi na ce wayyo Allahna Ya Wadudu sai....sai ta yi saurin saki na ta ɓace kuma sai na ga jini"yana kawowa nan yayi shiru tare da ƙoƙarin zuwa wurin mahaifiyarsa amma Dr David ya tare shi yana kallona kafin ya ce "ke kuma wace ce?" ban basa amsa ba na dubi Mamar Amar na ce "a cikin ƴaƴanki wa kika fahimci canzawar halayensa ko kuma kika ga wani abu na daban a tattare da shi?"

Shiru ta yi tana nazari kafin ta ce "babu .. am Akwai ,kwana biyu na ga Nadiya duk ta canza min kullum a tsorace take sannan kuma tana yawan yin tashin dare"

"A kirawo min ita"

"Ai tare muke da ita,bari na kirawo ta" ta faɗa tare da ficewa,babu jimawa sai ga shi sun dawo ita da matashiyar budurwar da duk ta yi gudu ba za ta haura shekara goma sha shidda ba,fara ce tasss mai kyau sai dai kukan da take yi ya hana a ga kyawun idonta don sun yi ja sosai.

"Ina buƙatar don Allah a bar mu ni da ita da kuma mahaifiyarta "na faɗa ,Dr David ne ya cewa nurse ɗin su fita amma shi da Dr Muhamud ƙin fita suka yi.

Na dubi Nadiyar na ce "ga ki dai ƙaramar yarinya amma kin tsoma kanki cikin haɗari me girma,mene dalilin da yasa kika sayar da ruhin ƙanenki ga aljanai?"

Ida firgicewa ta yi,dama can a tsorace take da farko ta so nuna ma kamar ba ta gane abin da nake nufi ba don har da rantse-rantse babu abin da ta yi . Ji na yi kamar na shaƙe mata wuya,na ce "za ki yi bayani ko kuma ni kike so na saka ki don dole ki yi?"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull