Bakin ruhi complete - Chapter 9
Bakin ruhi complete Chapter 9: Bakin ruhi complete Chapter 9. Ta ce "eh wanda aka ce ya kai ta ɗaki na musamman ne ya yi kuskuren lamba ya kawo ta nan,dubi…
3,339 words
Ta ce "eh wanda aka ce ya kai ta ɗaki na musamman ne ya yi kuskuren lamba ya kawo ta nan,dubi yake cikin ahalin Dr Maheer ne"
"Amma tana ina?" na sake tambayarta,sai na ga tana yi min kallon mamaki kafin ta ce "kin san ta ne?"
"Don Allah ki kai ni wurinta,muryarta ta yi min kama da ta wacce na sani" na faɗi haka ne don son gaskata al'amarin da ya faru yanzu .
Nurse Fatee ta ce "amma kuma ai ba ta yi magana ba"
Dr Muhamud ya shigo ya tambayi ba'asi,sai ta sanar da shi abin da nake cewa.Ya saki murmushi tare da zuwa ya kama kafaɗuna ya tayar da ni zaune ya ce "dama lokaci yayi da za ki ɗan motsa jiki kin jima kwance mu je" ɗan murmushi kawai na ƙaƙalo kafin na gyara zaman rigar Maheer a jikina na soma takawa a hankali har muka fita daga ɗakin.
Hira ya soma jana da ita yana tambaya ta matakin karatuna,ni kuma ina basa amsa jefi-jefi har muka iso wani ɗaki.Sai na yi tsaye cak ina kallon matar,tana zaune mahaifiyarta na bata koko a baki kamar wata ƙaramar yarinya.Wannan kaɗai yasa na ƙara yarda da cewa a kullum mu yara ne a gaban iyayenmu,yadda take kula da ita sai ya tuna min Innarmu.
Dr Muhamud ya ce "madam Rukayya ya ƙarfin jikin naki?"
Tana kallona ta ce "da sauƙi alhamdullah! Thank you!" ta ƙarashe tare da sakar min murmushi,hakan yasa na fahimci cewa wato ita ma ta gane ni kenan. Na juya kenan da niyyar fita ƙirjinmu ya mannu da na juna,na yi baya da sauri don gujewa masifarsa amma ya taro ni tare kuma da jawo ni ɗin irin sosai har muna jin hucin juna da bugawar zuciyoyinmu.
Ni dai na tsoronsa ne,shi kuma na fi kyautata zaton na masifarsa ce da ya saba.Bai ɗauki lokaci ba kuma ya soma zuba min bala'i har da dungure min kai,"da izinin wa kika tashi kika soma yawo?" yayi tambayar yana mai ɗan ja da baya bayan ya tabbatar na tsayu kan ƙafafuna.
Yawu na haɗiye muƙut ina jin farashin tsoronsa na ƙara hauhawa a zuciyata.Dr Mahmud ne ya basa amsa da "da izinin likitan da ka bar ta a hannunsa"
"Okay !" ya faɗa tare da fita fuuu bayan yayi min wani mugun kallo,mancewa na yi da ina da ciwo a ciki na fita a guje ina mai cewa "Alhajiii washhh" sai kuma na zube ƙasa ina mai dafe saitin cikin,ya juyo ya dube ni sai kuma ya ci gaba da yin tafiyarsa..... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
12
Idona ne suka ciko da hawaye,ba wai na raɗaɗin ciwona da nake jin yana wani irin motsi kamar cikin zai tsage a'a ta yadda Maheer ya tafi ya bar ni cikin wannan hali. Dr Muhamud ne ya zo ya ɗaga ni,hankalinsa kuma sai ya tashi ganin yadda ciwon ya buɗe jini na ta zuba.Kasa iya tafiya na yi sai da ya je ya ɗauko kujera ya taimaka min na zauna ya tura ni ya mayar da ni can ɗakina.
Cike da kulawa ya ɓalle maɓalin rigar daidai inda ke da ciwon,wani sabon bandeji yayi min bayan ya saka magani sai aukin sannu yake jero min kafin ya ce "wai kin ma ci abinci?" kai kawai na iya girgiza masa,sai ya fita.
Sai a lokacin kuma Aliya ta shigo,ita ce ta bani labarin tun ɗazu bayan an karɓe ni sun koma ita da Maheer can restaurant sun fiddo Meelat kuma tana can gidan Hajiya a bisa umarnin Maheer.Bayan na gama jin bayanin sai na ce "Lubna fa tana ina?"
Ta ɗan taɓe baki kafin ta ce "yanzu duk uwar kururuwar nan da ta yi ba ki ji ba? Ai in faɗa miki shegen duka Alhaji yayi mata duk ya kumbura mata fuska,tana can gidan Hajiya tana jinyar kanta don ta ce ba za ta je gidansu ba Ummarta za ta yi faɗa "
"To laifin me ta yi masa da ya dake ta?" na tambaya.Da wani irin mamaki Aliya ta dube kafin ta ce "saboda ta tura ki cikin akwatin gawa mana,ina ga fa Alhaji son ki yake shi yasa ma ake baki kulawa ta musamman a asibitin...." ba ta ƙarashe ba muka ji faɗuwar abu duk sai muka mayar da hankalinmu a bakin ƙofa.Nurse Fatee ce jikinta sai kyarma yake tana kallonmu musamman ma ni da take yi wa kallon ƙurilla.
"Ku yi haƙuri" shine abin da ta faɗa kafin ta duƙa tana kwashe abunuwanta da suka zube wasu kwalaban ma tuni sun fashe.Tana gamawa ta fice,Aliya ta taɓe baki kafin ta ce " ƴar wahala wai ita can Alhaji take so"
Haka kawai na ji raina ya ɓace amma na basar na ma canza hirar ta hanyar cewa "ya jikin Meelat ɗin ta warke?"
"A'a ba duka ba,sai dai gubar baƙin ruhi ta bar jikinta saura gurbin ne kawai za a cire daga jikinta na ji oga Maheeru na cewa sai kin dawo "
A zuci na ce ' in na koma to me zan yi mata ?' a fili kuma na ce "hajiya kuma fa? Ba ta yi faɗa ba?"
"Ta yi har cewa ta yi har a sallamo ki ba za ta tako nan ba" Aliya ta faɗa tana dariya,ni ma ɗan murmusawa na yi. Dr Muhamud ya shigo hannunsa riƙe da ledoji,Aliya ta gaishe shi kafin kuma ya miƙa mata ledojin ya ce " ki tabbatar ta ci ta ƙoshi don ta haka ne jikinta zai yi saurin warkewa"
"To in sha Allah " ta amsa,sai da yayi min wani kallo mai kashe jiki kafin ya fita. Sai a lokacin kuma Aliya ta buɗe ledojin,fruit ne da madara da jus ɗayar ledar kuma sabbin kaya ne kala biyu.Haka muka soma cin komai muna taɓa hira har ta kai da Aliya ta soma yin satin ta ce "ni kam ina son jin labarinki Haule"
Sai da na juyo da ƙafafuna ƙasa suna lilio kafin na ce "don me fa?"
Ta ce "akwai abin da nake son ƙiyastawa na ɗora a ma'aunin basira"
Murmushi na yi kafin na bata tun daga farko kamar yadda na ba Lubna,bayan ta gama ji sai ta ce "kenan fatalwa Husseina ta yi domin isar miki da saƙo?"
Na jinjina kai kafin na ce "a daren ranar sam kasa komawa bacci na yi,haka na yi ta tunani har garin Allah ya waye.Bayan duk an yi sallah muka fito domin sharar tsakar gida,muna tsaka da yi na ja Hassana gefe na shaida mata abin da ya faru.Sai ce min ta yi "dama Haule na faɗa miki dole akwai wani abu,yanzu ya kike gani?"
Na ce "ko ma mene ne zan gano shi a sannu Hassana ,amma ban faɗa miki ba na ga iyayenmu maza a daren ranar da Haidar zai rasu suna meeting kuma sun shiga ɗakin kulle wanda ba a taɓa buɗewa ba"
Ta ɗan waro ido kafin ta ce "mene ne wai a cikin ɗakin?"
"Wallahi ban sani ba don ban leƙa ba "
Ta taɓe baki ba tare da ta ce komai ba sai kuma muka ci gaba da yin shara,duk a tunanina Hassana ta bar maganar nan a inda muka yi sai dai sosai ta shammace ni don kuwa a daren wannan safiya bayan mun kammala zaman da muke yi na hira duk kowanne dare ina kwance cikin ɗakinmu sai na soma jin kakarin mutuwa yayin da kuma ɗakinmu ya shiga juyawa tamkar ana juya majaujawa.Dakyar na iya tsayuwa kan ƙafafuna,ina dafe bango na samu na fita babban falo nan na yi arba da tashin hankali.
Hassana na gani zaune dirshen ta sunne kai jini na ta ɗiga ga ƙasa ,yayin da hannuwanta ke riƙe da ƙwayoyin idonta.Ikon Allah ne kawai ya hana ni suma a wancan lokacin,cikin tsoro na ce "Hassana?" sai a lokacin ta ɗago kanta wanda ya koma kurma don kuwa babu ido a tattare da shi sai gurbinsu wanda ta ramensu ne jini ke yi mata zuba.
Na ƙwala wani ihu ina shirin zuwa gare ta amma wani irin abu mai ƙarfi wanda ba na iya ganin mene ne ya ja ni baya tare da cilla ni can ɗakinmu kan shimfiɗata.Duk yadda na yi yunƙurin kuma na tashi kasawa na yi,Aliya a daren nan da idona na ga wata baƙar inuwar ta tsaya a gabana tana umartar tunanina da ya kwanta yayi bacci sannan da ya manta abin da ya gani.Bayan haka kuma sai bacci ya kwashe ni,ban farka ba sai washegari da na ji cacaniyar mutane.Jikina duk a mace na fita can babban falo,kusan duk kowa na gidan ma ya fito an saka Hassana a tsakiya wacce idonta suka yi sutum suka kumburu suna zubar da wasu ruwa.
In faɗa miki a wannan lokacin shaf na manta da abin da ya faru a daren jiya wannan yasa na soma tambayar abin da ya faru sai dai kaf mutanen gidan babu wanda ya san taƙamaimai mafarin ciwon nata.A garinmu muna da wata al'ada,ba kowanne ciwo ne ake zuwa asibiti ba a'a sun fi ganewa magani na gargajiya wannan yasa lokacin da iyayenmu maza suka yi niyya suka fito sai suka fara kiran masu magani duk wanda ya zo da kalar abin da zai ce shine mafarin ciwon.Har Allah ya kawo wata tsohuwa mai ƙusumbi ta zo duba Hassana wacce ba iya ido ta rasa ba hatta maganarta ta ɗauke ba ta iya furta komai.
Kan wani farin yadi tsohuwar ta ce a shimfiɗe Hassana ,kafin kuma ta soma wanke mata ido da ruwan magani bayan haka sai ta ɗauki wani madubi mai kamar tabaron hannu ta soma duba idanun Hassana.Yanayin fuskar tsohuwar ne ya soma sauyawa tana ɓata rai can kuma ta ɗago ta dube ni,kallo ne take yi min irin na tantance wani abu kafin kuma ta maida dubanta ga Hassana ta ce "ta ga abin da idonta ba su dace su gani ba,a takaice dai zan iya ce muku ta yi gamo ne" Goggo Lami ta goge hawaye kafin ta ce "yanzu mene ne mafita Innaro?"
"Dole a yanke idon don tseratar da sauran gangar jikinta in ba haka ba dukkan jijiyoyin jikinta za su daina aiki kamar yadda ciwon ya taɓa kunnenta"
Yadda Goggo Lami ke kuka gwanin tausayi yasa mu waɗanda ke gida ba su fita ba muka taya ta yin kukan.Innaro babbar likitar gargajiya ce wanda ya haɗa da tsafi,a gaban idona ta saka wani abu kamar cokali ta ciro idanun Hassana duk kowa kasa jurar kallo yayi amma banda ni don tsaf na kalli komai tun daga cire wa har izuwa lokacin da ta saka ƙwayoyin idon cikin wani farin ƙyalle ta ɗaure sai ta jefa shi a jakarta wacce aka yi da fatar namun daji.
Wani ganye ta cika gurbin idanun Hassan da shi kafin ta tattare komai nata domin tafiya,ba ta karɓi ko sisi ba sai kallona da dai ta ribantu da shi don har sai da ta sakar min murmushi ta ce "kyakkyawar ragaya " sai kuma ta yi tafiyarta.Bayan fitarta na je na zauna tare da kamo dukkan hannuwan Hassana ina yi mata magana duk da na san ba za ta iya maido min ba,amma haka nake kyautata zaton tana iya ji bakin nata ne ba za ta iya buɗewa ba.Tsawon yinin a kusa da ita na yi shi,ni ce nake bata abinci da hannuna in kuma za ta yi wata buƙata na yi mata jagora zuwa banɗaki.
Da maraice iyayenmu maza suka dawo daga gona,abin mamaki sam babu wanda ya bi ta kan Hassana ballantana su tambayi ba'asin lafiyarta duk da kuwa sun gani sarai an yi mata aiki.
Ina zaune ina yi wa Hassana hira Innarmu ta kira ni,abinci ta umarce ni na ɗauka na kaiwa iyayenmu maza a inda suka saba ci.
Cike da ladabi na ɗauki ƙaton farantin na nufi wata bishiya inda suke zaune,ina dab na kai gare su na ji muryar Kawu Laminu wato mahaifin Hassana yana mai cewa "ban san dalilinta na zuwa ɗakin sirri ba,ga shi ta dalilin haka ta rasa idonta.Na ji zafin haka ,amma na ga ku tamkar ba ku damu ba"
Cak na tsaya don gulma,sai na ji Abbana na ce wa "haba Laminu ya ido suke da rayuwa? Ka san kuwa yadda nake mugun son Haidar? Ina ce kullum a gabanka da zarar na dawo daga aiki yana kan cinyata yanzu ina Haidar ɗin?"
"Ka ji wani zancen banza ya ƙaramin yaro yake da budurwa? Ka manta Bara warhaka kukan mutuwar Husseina ce ake? Kai ne farkon bayarwa ballantana ka faɗa min banza-banza" nan fa suka fara sa'insa suna ta feso abubuwan da suka ɗaure min kai,Kawu Hamza wanda shi ne babba cikinsu ya katse su ta hanyar cewa "ya isa haka dalla! Kun tsaya surutun banza maimakon ku yi nazarin yaranmu ku ga daga ciki wane ne yake da maɗaukin iko amma kun tsaya shirme.Ku yi tunani na manya mana,ku faɗa min a cikinku wa ya ga wasu alamun prophecy a ɗaya daga cikin yaransa don dab ake da ƙaddamar wa,Ibrahim kwanaki na ji ka ce ko ka ga me a tattare da Haule?" Kawu Hamza yayi tambayar ga mahaifina wanda ya buɗe baki kenan zai yi magana muka haɗa ido da shi.
Dukkan illahirin jikina rawa yake tun lokacin da na ji an ambaci sunana,dakyar na iya takawa na isa ina mai gaishe su kafin kuma na ajiye farantin.Har tuntuɓe nake wajen barin wurin,ko da na koma madafa don ɗaukar abincinmu ni da Hassana nan kuma na ƙara jin iyayenmu mata na yin nasu su suma.
"Wallahi Rabi na gaji da wannan al'amari yau wannan gobe wancan, wata rana ma ina ga mu za a fara ɗauka" Goggo Lami ce ta faɗi haka kafin sauran matan su ma su bada ra'ayi irin nata,can kuma sai Innarmu ta ce " Lami ki ɓoyi muryarki don wallahi muddin suka san da cewa kin san abin da ke wakana to kashinki ya bushe,ni yanzu damuwata bai wuce mijin da za su zaɓarwa Aliya ba don Abbansu na ji yana cewa lokaci yayi da za ta bar gidan nan"
Jin sun koma zancen aure yasa na yi gaba na koma can wurin Hassana,sam yau kasa yi mata hirar da na saba yi mata na yi iya abincin kawai na bata.Bayan na gama kuma na kai ta banɗaki ta yi fitsari tare kuma da ajiye ta kan shimfiɗarta,daga nan na wuce ɗakinmu nan na tarar da Anty Aliya a zaune cikin damuwa yayin da kuma Yaya Aliyu ke yi mata bayani.
"Dole ki yi biyayya kar ki saki ki nuna musu wai ba ki son zaɓinsu,yin haka Babbar illa ce a rayuwarki ta gobe.Kin ga ni zuwa jibi zan wuce wata ƙasa don ci gaba da karatuna"
"Ta ya zan yi rayuwar farin ciki da mijin da ba zaɓina ba?" bai ma kai ga bata amsa ba aka aiko kiranta a babban falo.Haka ni ma na bi bayanta sai kuma na tsaya ganin wani kyakkyawan saurayi a zaune ,ban san ta yaya aka yi ba amma na ji a raina kyawun ɗan maciji ne da shi kuma kuwa hakan ce ta kasance hummm" ina kawowa nan na yi shiru ina mai komawa na kwanta.Ina lumshe ido nan kuma na haɗu da oga Maheer a zaune cikin ofis ɗinsa yana duba wasu takardu fuskar nan kicin-cikin,sosai na yi mamakin ganin ashe har yanzu bai bar asibitin ba.
Dara-daran idonsa ya ɗago yana kallon esprit ɗina da yayi masa kutse ya kai masa ziyara,cikin zafin rai ya ce "ki cire tunanina a ranki,in kin yi haka ba za ki sake cin karo da nawa esprit ɗin ba ko da kuwa kin rufe ido"
"Wai don Allah me na tsare maka ne Alhaji ? Duk ka bi ka tsane ni" na faɗa sai dai kafin ya bani amsa wata irin kururuwa ta cika asibitin wacce ta yi sanadiyar buɗe idon nawa.
Ba a ɗauki lokaci ba kuma wasu nurse biyu suka shigo da nurse Fatee cikin wani irin matsanancin hali kamar ranta zai fita.Bayan sun shimfiɗe ta a gado mai facing nawa sai suka soma bata haƙuri,yayin da kuma ɗaya ke tambayar ɗayar dalilin kukan nurse Fateen.Shiru ta yi ba ta ce komai ba,babu jimawa kuma Dr Maheer ya shigo ransa a mugun ɓace .Duk ja suka yi baya yayin da shi kuma ya soma duba ta ,babban abin da ya fi yi min ciwo bai fi yadda na ga Maheer ya saka hannunsa a ƙasan rigar nurse Fatee yana ɗaukar bugun zuciyarta.
Ji na yi kamar na je na fito da hannun nasa,takaici bai gama rufe ni ba sai da na ji yana rarrashinta cikin wani irin salo.
"Mene ne duk wannan uhum? Me yasa za ki tayar da hankalinki haka? Saboda duk ki ɗaga mana hankali? Me kike ji yanzu?" shi ne abin da yake faɗa ,hannunsa dafe a saitin zuciyarta ya manna abin sauraren bugun numfashi haka kuma ya mayar da dukkan hankalinsa gare ta suna kallon juna.A yadda nurse Fatee take hawaye tana masa wani irin kallo mutum in dai ba makaho ba ne zai fahimci tana mugun sonsa fiye da yadda shi ya bata muhimmanci.
Ba ta iya cewa komai ba,can sai ga Dr Umar ya shigo shi ma hankalinsa a tashe. "Meke damunta?" ita ce tambayar da yayi ,sai a lokacin Maheer ya matsa kafin ya ce "ciwonta ne ya motsa ban san me ya tayar mata da hankali ba"
Nan fa na ga ikon Allah yadda aka dinga rarrashinta akan ta faɗi dalilin tashin ciwon amma ta ƙi faɗa .
"Ina ga kamar zuwan wannan ce a asibitin nan" ɗaya daga cikin nurse ɗin ta faɗa tana mai nuno gadona ,a tare suka juyo gare ni kafin shi Dr Umar ɗin ya ce "Maheer wannan kamar likitar gargajiya ko?"
Bai basa amsa ba sai cewa da yayi "nurse Jamila ku canza mata ɗaki" wacce ya kira da Jamila ita ce ta zo ta taimaka na sauko,ina ji ina gani aka fito da ni daga ɗaki na musamman aka kai ni na ordinaire mai cike da gadaje a ƙalla sun kai goma.Ji na yi kamar zan haɗiye raina don takaicin wulaƙancin da yayi min,sai kuma na ji tsanar nurse Fatee na game dukkan illahirin jinin jikina amma kuma da na tuna matsayina fa ƴar aikin gidansu ce sai na ji to mene ne na damuwa? Ina ƙoƙarin kwantawa don saka kaina baccin dole ko na ji sauƙin ƙunci sai idona ya sauka kan wata matashiyar budurwa tana kwance kan gado,gashin kanta duk ya siɗe,manyan ƙuraje sun cika mata fuska ga kuma ƙafafunta duk sun kumbura sun yi suntum kamar a caka allura su fashe muna haɗa ido da ita na hango wata baƙar inuwa a cikin ruhinta..... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
13
"Aliya duba min wata budurwa can tana ɗauke da gubar baƙin ruhi" na yi furicin ƙasa-ƙasa a daidai lokacin da Aliya ke ƙoƙarin zama gefen gadona.Ta waiga inda nake yi mata nuni kafin ta ce "sai dai kuma da alamu ƙaiƙayi koma kan masheƙiya ne,duba da yadda take iya sarrafa idonta ta yi magana"
Ina jin abin da Aliya ta ce sai na sake mayar da dubana kan budurwar wacce har zuwa yanzu ba ta bar kallona ba.Ta ido na yi mata tambaya "wace ce ke?" ba ta bani amsa ba sai hawaye ne da suka zubo mata shaaaa ,ni kuma na ƙara jefo mata wata tambayar "me ya samu gashinki duk ya cire?" sai a lokacin ta soma yin magana .