Bakin ruhi complete - Chapter 8
Bakin ruhi complete Chapter 8: Bakin ruhi complete Chapter 8. Tun a bakin ƙofa wani irin iska mai zafi ya dake min,kuma tamkar an zuƙo mu ne ba tafiya muka…
3,370 words
Tun a bakin ƙofa wani irin iska mai zafi ya dake min,kuma tamkar an zuƙo mu ne ba tafiya muka yi da ƙafafuwanmu ba haka na ga mun yi saurin shiga tsakiyar wurin.Wuri ne mai cike da furanni masu tsantsar kyawu wanda ya ɓoye sharrinsu da kuma gubar da ke ɗauke da shi.Muna tsaka da tafiya muka dinga jin kukan jarirai,Aliya ce ta yi mana bayanin dalilin kukan.
"Dayawan matan da suka rasa rayukansu suna ɗauke da ciki su ne in sun shigo nan suke haife cikin,wani sa'in jariran na rasa madarar da za su sha ne to in sun ji ƙamshin bil'adama ne sai su fara kuka.In da mace mai shayarwa to haka za ki ga madara na ta ɗiga daga mamanta tana shigewa ƙarƙashin ƙasa" ina gama jin bayanin nan sai wani tsoro ya kama ni,duk gani nake ni ma hakan na iya faruwa da ni duk da kuwa ni budurwa ce.
Wajen wani koren fure muka ratsa sai ya soma yin rangaji yana motsi tamkar wani mai rai,Lubna ta kai hannu za ta tsinko amma Aliya ta buge hannun tare da cewa " ba ki ji na ce ba a taɓa komai ba?"
"Na manta" ta faɗa tana dariya.
Sai da muka yi yawo sosai kafin mu kamo hanyar fita,nan ne na ji tamkar na taka wani abu mai motsin rai.Ina ɗaga ƙafata sai na ga wata sarƙar diamond mai shegen kyawu sai ƙyalli take,kallo ɗaya na yi mata ina shirin kawar da idona amma wani abu ya ja hankalina a tsakiyar sarƙar harafin H ne aka zana sannan ga wasu duwatsu masu kaloli da aka ƙawata harafin.
Na duƙa na kai hannu na ɗauki sarƙar,ko da na ɗago sai na ga tuni su Lubna sun kai bakin ƙofa.Kamar wacce aka yi wa dole haka na saka sarƙar a wuyana tare da gyara ɗan ƙaramin hijabina sannan na ɗan ruga na cimmar musu.
Ko da muka fito waje sai Aliya ta ƙara mayar da mu can wurin nan mai datti. "Yanzu ya za a yi kenan?" Lubna ta tambaya.
Aliya ta ce "mafita guda gare mu a yanzu shi ne mu je can gidansa"
Kamar wacce aka tsikara na ce "na san gidan" duk suka kalle ni da mamaki,amma tun da abin da suke so ne kawai ba su tambaye ni ta yaya ba sai muka ɗau taxi ni ce na dinga nuna masa hanya har muka isa gidan.
Bayan mun sallami mai taxi muka fito muka yi cirko-cirko,unguwar tsit take sosai ma na yi mamakin ta yadda aka yi Meelat har ta iya ganin maƙwabtan Alhajin.
Aliya ce ta soma juya hannunta mai power ta ɓalle kwaɗon da aka rufe gidan da shi,su biyun duk suka shige ciki yayin da ni kuma na tsaya ina kallon wata matashiyar budurwa wacce ke zabaya tana leƙena ta wata can saman benen ɗaki.
'Wace ce ita kuma waccan mai farar fata kamar fulawa?' na tambayi kaina a zuci,ban kai ga samo amsa ba na ji kururuwar su Lubna daga can cikin gidan.A guje na nufi ciki sai na tarar suna gurmuzu su da wani gogon Biri duk yadda Aliya ke da power ta kasa tsayar da shi domin shi ma an tsafe shi.Abun mamaki ina shigowa sai ya tsaya cak tare da zubewa ƙasa yana wani irin abu kamar yana gaishe ni,ƴar kallon-kallon muka fara yi mu ukun .
"Haule ke ma irin wannan protector ɗin gare ki? Na ga duk jikinsa yayi sanyi" Aliya ta yi min tambayar da sam ban ma gane mene take nufi ba hakan yasa na share ta na ce "ga ɗakin akwatin gawar nan" na nuna musu shi da yatsa sai suka nufi ƙofar yanzu ma Aliya ce ta buɗe ta. Sai bayan sun shiga na take musu baya ina mai waiwayen Birin da har zuwa yanzu yana a yadda yake.
Kiciniyar buɗe akwatin suke amma sun kasa,don power Aliya ma ta ƙi yin aiki.Sai na zo na kama musu amma ta ƙi buɗuwa,Lubna ta ce "ina ga akwatin nan jini ne makullin buɗe shi"
Duk sai muka kalle ta,kai ta jinjina ta ce "wannan tambarin Family ne" ta nuna wani logo da ke jikin akwatin.
"To jinin wa za a tsaga?" na yi tambayar.
Aliya ta ce "in dai haka ne da na Lubna za a yi amfani duba da ta taɓa zama cikin ƙungiyar,na san har zuwa yanzu zanen hannunta bai goge a rubutun da suka yi ba" sam ba mu yi tunanin wannan babban kuskure ne za mu tabka ba,haka Lubna ta tsaga yatsanta ɗigon jininta ya ɗiga sau uku a jikin tambarin nan take akwatin ya soma buɗe kansa a hankali wari da ɗoyi yasa suka ja baya,yayin da ni kuma na toshe hancina tare da matsawa ina leƙen akwatin.Yana gama buɗewa na ji an tunkuɗa ni ciki na faɗa yayin da kuma akwatin ya rufe ruf da ni a ciki.Cike da tashin hankali na soma kiciniyar buɗe shi amma ya ƙi yi,ina jin muryar Aliya kuma na cewa Lubna "don me kika yi haka? Yanz..." ban ji ƙarashin maganar ba sakamakon ƙanƙame ni da gawar ta yi tana yi min maganar da ta birkita lissafina.Daidai nan free page ya ida in kina son ci gaba sai ki tura 500 via2670215530 ZULFAU YAHAYA ECOBABK sai ki turo min da shaidar biya ta WhatsApp +22795045822
🔞Yanzu nake rubuta shi Ni ma banda complete in kin biya group ne zan saka ki 06.Apr.25
[5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
11
Wasu irin ɗalasiman tsafi ne take furzowa tana mai ambaton sunana ,ban san ta ya aka yi ba har na iya jin Yaren da take yi ba.Amma dai na ji fassarar cikin kwanyata kamar haka,"ya uwar gijiya ki sahalce min na mallaki gangar jikin Haule ta zama tawa kamar yadda kika bai wa Manjo ikon kawo duk ƴan matan da kika buƙaci adadinsu "
Wata irin fitinaniyar azaba ce na ji ta ratsa min mara wacce ko tantama babu akaifunta ne ta caka min,cikin nishin azaba na rumtse idona da ƙarfi ina jin cewa shi kenan mutuwata ce ta zo sai dai me zan gani? Maheer ne a tsaye gaban ƙofar restaurant shi da Hajiya da kuma dandazon mutane ƙila costumer.
Ido muka haɗa da shi,nan take na fahimci tunanina da nasa ba za su taɓa haɗuwa ba dole sai in na lumshe ido ne.Bakinsa ya motsa yana yin wani yare harshensa sak irin na maciji na motsawa nan take na ji akwatin ya buɗe tare da cillo ni waje daidai nan ya fara ci da wuta.
Aliya ta nufo ni da sauri tare da kamo ni,ita ma Lubnar zuwa ta yi a rikice tana kiran sunana a ɗan firgice ni kuwa gefen cikina kawai da ke min azababen ciwo na dafe.
"Ɗakin ya fara ɗaukar wuta,Aliya mu sungumeta mu fita" cewar Lubna,nan suka ciciɓe ni suka fito da ni.Sai da muka zo bakin titi sannan muka samu taxi ,Lubna ce ta kawo shawarar a kai ni asibitin Maheer.
Yadda nake jin azaba shi ya kusan fitar da ni daga hayyacina,sai sannu Aliya ke jero min yayin da Lubna ke zubar da hawaye har muka isa can asibitin. Muna zuwa kuwa aka tarbe mu,bisa wani gado aka ɗora ni aka tura ni ciki.Likitoci uku ne a wurin namiji ɗaya sai mace biyu.
"Tana zubar da jini sosai nurse Fatee je ki kira Dr Muhamud " cewar namijin yana mai ɗaukar almakashi da niyyar tsage rigar jikina.
Cikin masifar da ta zame masa jiki ya ce "duk ku fita waje,kai kuma mene ne nan za ka yi? Bani nan? " duk fita suka yi,namijin har ya kai bakin ƙofa amma ya tsayar da shi yana mai ci gaba da cewa "Dr Mahmud ne ya shaida ma za a kawo patient da kake wani cewa a kira shi? In ya zo mene zai yi? Fita!" ya ƙarashe cikin tsawa kafin ya iso gadon da nake kwance na zuba masa ido ina kallo ko ƙyaftawa ban yi,don neman ciwon ma na yi na rasa.
"Ke kuma kin zuba min manyan idonki kina kallo kamar mayya,ina ce dai shegen rawar kanki ne duk ya kai ki da haka.In ba ki yi sannu ba shegen iya yinki da nuna ke wata jaruma ce su za su yi ajalinki" ya ƙarashe faɗa haka ne tare da yin wani furici nan take rigunan jikina duk suka fitar da kansu,da wacce na saka ta atamfa da kuma ta aiki.
"Washhh!" na furta tare da cabko hannunsa da ya matse cikina daidai ciwon ,ya ɗago manyan idonsa masu haske yana watso min wani mugun kallo da ya haifar min mugun tsoronsa.
Sai a lokacin kawai na ji hawaye sun zubo min tun farkon jin ciwon ,haka kuma ban ɗauke idona daga cikin nasa ba.Alama yayi min da na sakar masa hannu,amma na girgiza masa kai .Ɗaya hannun nasa yayi amfani ya cire nawa sannan ya ƙara matsa cikin wannan karon sai da na saki wata gigitaciyar ƙara.
"Gobe ma ki sake kwasar jiki ki je gudanar da abin da ba ki da ilimi a kai" ya faɗa tare da ɗan gusawa ya ɗauko wani magani,ya shiga wanke ciwon kafin kuma yasa bandeji ya rufe wurin sai kuma ya ciro audiga mai ɗan yawa yana goge min jikina inda jini ya ɓata.Nan ɗin ma ido na zuba masa ina kallo ina jin ƙasan zuciyata na raya min ' babu laifi yana da ɗan kirki kawai dai don yana masifafe'
Ƙofa aka turo,da sauri ya ƙara yin wani furucin nan farar rigarsa ta likitoci ta fita daga jikinsa ta shiga nawa sai kuma a lokacin na farga cewa daga ni sai bra ne banda riga ashe duk da cewa kuwa a gabana ya watsar da su .
Dr Muhamud ne ya shigo fuskarsa cike da damuwa ya ce ,"me ya same ta?"
"Ka tambaye ta ai ga ta nan gabanka " yana gama faɗa ya fice ya bar ɗakin.
Shi kuma Dr Muhamud matsowa yayi ya soma yi min sannu,sam ban amsa ba don na lura kamar Maheer bai ji daɗin zuwansa ba kuma kamar yana cikin fushi. Dr Muhamud kuwa ci gaba yayi da duba ni sannan yayi min wata allura wacce nake kyautata zaton ta bacci ce saboda yadda na soma jin idona na lumshewa sai dai ina fara yin baccin na soma yin wani mafarki.
Mafarkin tamkar gaske haka nake jin shi saboda a yadda nake kwance ɗin nan a gadon asibiti to kamar haka nake ganina.Wani gado aka turo mai ɗauke da wata marar lafiya aka ajiye ta kusan gadona,a hankali nake kallon yadda take azabtuwa cikin ciwon da ba ta da laifi ko ɗaya .Nurse Fatee ita ce dai na ga tana yi mata allura kafin ta fice,sai a lokacin kuma bacci ya ɗauke matar a daidai wannan lokaci ne kuma esprit ɗina ya samu damar tambayarta "baiwar Allah wace ce ke? Wane laifi kika yi wa mutane suke son nakasa miki rayuwa har haka?"
Cikin kuka ta soma bani labarinta,"sunana Zulfa,uwa ga marayu uku.Bayan rasuwar mijina bango uban ƴaƴana sai duk abubuwa suka canza min,duk dukiyar da ya bari danginsa suka kwashe ba tare da sun yi duba da ƙananan yaran da ya bari ba.Ƙunci da zafin rai su suka yi min jagoranci wurin ci gaba da karatuna don dama da ilimina ganin na yi aure na jingine shi saboda yadda mijina ke da mugun kishi sannan babu abin da bai yi min na rayuwa.Bayan kammala karatuna ban sha wahalar neman aiki ba kasancewar ni na fito zakaran gwaji a kaf cikin ɗalibai, wannan yasa kamfanoni da dama suka yi min tayin aiki sai na tsaya na zaɓi kamfani guda na soma yin aikin da ya taimaka min wurin gina goben yarana.Yadda nake da ƙwarewa da ƙwazon aiki shi yasa na ciri tuta har aka yi min ƙarin matsayi,wanda ba wai mutanen da muke aiki wuri guda ba ni kaina na yi mamakin kujerar da aka bani.
Kamfaninmu yana da girma sosai,haka kuma ɓangare-ɓangare ne wanda bene ya fi hawa shidda a ciki.A inda kake shine hawa na biyu,a wurin mu uku ne namiji biyu sai mace ɗaya .Muna mutumta junanmu sannan kowa na aikinsa yadda ya kamata, sai dai nawa duk ya sha banban da nasu a kullum kuma shugabanmu na faɗar haka a gaban kowa haka ko wasu manyan baƙi za a yi ni ce ke jagorantar kamfaninmu.
A wata ranar Laraba ,na tashi da tsananin ciwon mara saboda zuwan baƙon watana.Duk da na so ƙin zuwa wurin aiki haka na lalaɓa na tafi sanin shugaba ya ce akwai yiyuwar meeting ɗin bazata a yau.Tun da na tsoma ƙafata kamfanin nake jina wani iri,ina ƙarasawa can ɓangarenmu kuwa sai na tarar da ita abokiyar aikin nawa tana tsara zance irin na tarben baƙi da kuma yadda ake gudanar da meeting,amma muna haɗa ido sai ta ce "ke? Na zata ba za ki zo ba ai" da ɗan mamaki na ce "saboda me fa?" nan ta ɗan daburce kafin can kuma ta ce "na ga har lokacin da kika zuwa ya gota amma ba ki zo ba" eh gaskiya ta faɗa don na yi late,sai na ɗan murmusa kawai na gaishe ta tare da zama kan kujerata na buɗe system ita ma can ɓangarenta ta zauna babu jimawa su ma sauran mazan suka shigo duk kowa ya fara aikinsa.Amma wani abin da ban saba gani ba shine yau ya faru yadda lokaci zuwa lokaci Zulahait take kallona kamar kuma tana hararena amma sai na share.
Lokutan baya mun saba yin meeting da safe,amma yau sai shugaba ya ce sai da rana za mu yi.Hakan ya bani damar fita na aika a siyo min magani sannan a haɗa min tea,bayan na dawo sai ban tarar da Zulaihat ba amma ban damu ba abin da ke gabana shine kawai aikina.Ba a ɗauki lokaci ba aka kawo min magani da kuma tea,ina gama sha nan na soma yin bacci kamar matatta.Ba ni na farka ba sai kusan ƙarfe huɗu saura shi ma shugaba ne ya tashe ni,"Rukayya ki tashi baccin ya isa haka " ko da na duba agogo sai na fahimci cewa lokacin yin meeting ya wuce tun tuni ƙila ma har sun yi wani daga cikin abokan aikina ya jagoranci taron amma sai na ji shugaba na cewa "ki yi sauri ki shirya ƙarfe huɗu da rabi za a fara meeting ɗin " cike da kasala na ɗauki jakata na shiga toilet,pad ɗin da ta ɓace na fidda sai na saka ta a baƙar leda na yi wanka na canza wata sannan na fito .Ko mai ban kai ga shafawa ba shugaba ya shigo cikin sauri yana cewa "yi sauri ki zo ga baƙinmu can har sun zo" a yadda na gansa duk ruɗe ƙila kuma bai son ɓata ran costumersa ne yasa na ɗauki biro da takarda kawai na fita ,can hawa na shidda ne muka gudanar da meeting ɗin mai matuƙar muhimmanci don muna tsammanin ba ƙaramin ɗaga martaba kamfaninmu zai yi ba.Ko da muka gama meeting ƙarfe bakwai ta yi na yamma,tuni kuma duk kusan kowa ya tashi daga aiki .Da na isa ɓangarenmu ma ƙofar a rufe take wannan yasa sai da na kira mai gadi ya buɗe min don shi ma yana da key ɗin,ganin irin dogon lokacin da na ɗauka a ɗakin taro yasa na ji da buƙatar na ƙara canza pad kafin na wuce gida .Jakata na ɗauka wacce na bari kan teburina sannan na shiga toilet,sai dai fa ledar da zan jefa pad ɗin ce ta yi ƙasa ko sama ban ganta ba alhalin da na canza ta farko a nan na jefa ta.Komai na jakar na zazzage amma babu ita,sai kuma na soma bincike toilet ɗin ko ƙila mantawa na yi ban saka ta a jaka ba amma ban gan ta ba.Da na fito ma sai da na duba ofishin nan ma babu,jiki a mace na fita na isa gidana sai dai fa sam hankalina ya ƙi kwanciya.
Washegari da na dawo wurin aiki haka na kasa sukuni,ga shi kuma da kunya na tambaye abokan aikina ko sun tsinci pad ɗina haka na yi shiru na fara yin aiki.Wuraren ƙarfe sha ɗaya na rana aka kira ni a waya aka shaida min babban yarona ya mutu cikin swimming pool ɗin makaranta,hankali tashe na tafi can .Yanayin gawarsa da na gani yayi matuƙar girgiza ni,da kuma yi wa kaina tambaya ta ya yaron da ya mutu cikin ruwa amma yake hawayen jini kuma jinin bai goge ba? Na yi kuka kamar zan rasa raina amma ina ji ina gani aka binne min yaro,mutuwarsa ita ce ta hana ni zuwa aiki sai na zauna gida ina karɓar gaisuwa na tsawon sati biyu.A daren ranar da zan koma aiki kuma na soma yin wani zazzaɓi mai ƙarfi,dakyar ma na iya zuwa asibiti sai ga shi ciwo ƙarami ya zama babba don mafarin yin jinyata kenan.Kullum ciwo yin gaba yake,zafin jikina bai taɓa sauka ba,inda babban tashin hankalin yake sai da na soma ganin koren ruwa na fita ta jikina,in na yi fitsari sau goma to su ma sai sun zuba.Wannan kuma bai isa ba sai na soma ganin wasu gudaje-gudajen jini,ni ba miji ne da ni ba ballantana na ce ko ɓari ne na yi.Tsoro da fargabar abin da zan kuma gani gobe su suka haifar min da ciwon kwanya,duk da dai ba irin na haukace ba ne a'a zan dinga magana ni ɗaya kafin wani lokaci kuma sai na soma jin tamkar ana taya ni yin hira.A cikin ƙwaƙwalwata haka nake jin muryoyin mutane dayawa suna hira suna yin dariya,wani sa'in kuma har sunana nake jin suna ambata.Wannan ya ƙara hauhawar farashin tsorona na bar yarda na zauna ni ɗaya don na lura in ina cikin kaɗaici ne suke zuwar min.To a duk lokacin da na ji abin na min yawo a kwanya ina yin suratai wannan yasa asibitoci da dama suke korarmu don sun ce asibitin mahaukata ce ta dace da ni,yayin da Mamana wacce ta tsaya tsayin daka tun farko fara ciwon nawa take kula da ni ta ƙarya ta su ta ce ƴarta ba mahaukaciya ce ba,zancen da nake yi miki a yau ma daga wata asibitin aka koro mu shi ne wani mai taxi ya ce mu zo wannan asibitin mai ita yana da kirki ana kula da majiyantansa kamar sarakai " tana kawo ƙarshen bani labarin nata na ce " faɗa min ɗaukar fansa kike so ko samun sauƙi kawai?"
Kai tsaye ta ce "na samu lafiya shi ne kawai fatana "
Na ce "in sha Allah kin zo wurin da za ki samu maganinki ,za ki warke kamar ba ki taɓa yin ciwo ba" ina gama faɗar haka sai Dr Maheer ya shigo,nan ne kuma na ga wani abin mamakin sai na ga tamkar mafarkin nawa ne ya tsaya kamar kuma ci gabansa ne,kusa da gadona ya zo kama hannuna tare da sa allura ya jawo jinina,bayan haka kuma shi ma sai ya jawo nasa jinin wanda yake baƙi ƙirin kamar na kunama nan take jininsa da nawa suka fara haɗewa wuri guda sai suka bayar da wata kala kuma ta musamman.Kusa da gadon matar ya je ya ɗura mata wannan jinin a cikin jijiyarta yana gamawa ya fice daidai nan ni kuma na farka.
Da na duba gefena kuma sai ban ga matar ba,na dafe gefen kaina da ke mugun sara min kafin kuma na duba hannuna da ke yi min zugi sai na ga wata ƴar huda ta yi wani ɗan ƙurji irin dai kamar dai an caki mutum da allura.
"Kenan gaske ne abin da na gani? To in kuma haka ne ina ita matar take?" na tambayi kaina cikin son sanin gaskiya kuma na ƙure hannun nawa daidai inda na ga Maheer ya caka min allura ne kuma,nurse Fatee ta shigo tana yi min ya jiki bayan na amsa na ce "don Allah cikin bacci na ji kamar an turo wani gadon maras lafiya a nan ɗakin"