Bakin ruhi complete - Chapter 13
Bakin ruhi complete Chapter 13: Bakin ruhi complete Chapter 13. Da sauri na rumtse ido saboda wata uwar azaba da na ji ta ratsa ni,a take kuma na ji bakina…
3,367 words
Da sauri na rumtse ido saboda wata uwar azaba da na ji ta ratsa ni,a take kuma na ji bakina ya cika da yawu babu shiri na tofar da su nan take suka soma tafasa suna bori tamkar an zuba acid a ƙasa.Wani tsoro ne ya kama ni,sai tsohuwa mai ƙusumbi ta ce "kaicon wanda zai ɓata miki rai,ina tausayin wanda zai yi kuskuren yi miki ƙage ko sharri,Hahaha in kuwa haka ta faru shayar da su yawunki shi ne mafita" sai kuma ta ɗauko wani abu mai kamar mai ta shiga ɗiga min cikin ciwon wanda shi ya bani damar jin abubuwan da kunnuwan normal mutum ba su isa su ji shi ba.
A kusa da ni nake jin wani irin huci haɗi da numfashi sai dai idona ba sa iya ganin komai.Sai bayan ta gama yi min magani ta fita sai na fahimci cewa ita ɗin ce dai ke yin numfashin nan mai kamar na dabbar daji.
Ƴan gidanmu duk a tunaninsu jinyar ƙafa nake nan kuwa ba su san ban jin ciwon komai ba in banda motsin da nake ji babu dare babu rana. Bayan sati biyu da faruwar haka na soma zuwa makaranta tare kuma da yin duk wasu ayyukan da na saba yi,sai dai fa wani irin kwaɗayin na ga abin da ke cikin ɗakin sirrin gidanmu a kowacce daƙiƙa ƙaruwa yake.
Wata ranar laraba ce ana ruwan sama masu ƙarfi,dukkanmu kowa na ɗakin uwarsa duk da kasancewar dare bai wani yi ba amma haka dokar gidan take babu mai fita sai an gama ruwa.Muna zaune ni da ƙanena Fahad muna cin gyaɗa yayin da kuma Innarmu ta kishiginɗa tana bacci,kamar da sama kunnena wanda a yanzu ya zama kamar ba na mutane ba ya soma jiyo min maganganu iri-iri.Muryoyi ne na iyayenmu maza sai ƙwaya ɗaya tal wacce tun da nake ban taɓa jin ta ba,so nake na tashi amma na san Fahad zai iya bin bayana ko kuma ya tayar da Innarmu ya min gami kan na fita.
A karon farko ne na gwada powerta akan ƙanena,ina kallon idonsa na ga yayi baya ya lumshe ido tare da ɓingirewa bacci.Jiki na ɗan yi min rawa na tashi kamar wacce aka yi wa dole na fita babban falo,tsit yake babu kowa sai dai sawun takon takalma da ya ɓata wurin da kuma na bi ƙididiga sai na ga can ɗakin sirri sawun takun suka tsaya.
Tsit! Kunnuwa sun bar jiyo min komai har zan koma sai kuma na ci gaba da jin wani irin gurnani yana fitowa daga cikin ɗakin nan,a hankali na matsa ta ƴar hudar da ke jikin handle na leƙa duk da kuwa ɗakin na ɗauke da wani mahaukacin duhu bai hana ni ganin iyayenmu maza ba a durƙushe duk sun sunne kawunansu.
A cikin zuciyata nake tambayar kaina 'shin mene ne ke yin wannan gurnani?' ba a jima ba kuwa idona yayi tozali da wata halittar marar fasali.
Babu tsoka ko ɗaya a jikin halittar sai wasu irin sayu tamkar itaciya,haƙoransa manya zaƙo-zaƙo ga idanuwa tulu-tulu .Yanayin ƙirarsa kamar basamude yake,ga tsayi ga kauri sannan ga wani ƙaton doro a bayansa.Suman tsaye na yi daga inda nake ,ina shirin gusawa kuma na ga abin al'ajabi yadda dodon nan ya rikiɗe ya koma cikin siffar wani dattijo da na ƙanƙance ido sai na fahimci cewa wannan dattijo ba kowa ne ba illa Kakanmu,mahaifi kuma uba ga iyayenmu maza .Ban taɓa ganinsa ba amma sau ɗaya tak na taɓa ganin hotonsa kafin kuma a kwashe su a toye su duka,daga bayana na ji an dafa ni na zabura na juyo a tsorace sai na ga ashe Innarmu ce .
Ba tare da ta ce komai ba kuma ta yi saurin jan hannuna muka koma ɗaki.Bakin gadonta na ƙarfe ta dungurar da ni zaune yayin da ita kuma ta yi tsaye a gabana ta zuba min ido .
Dukkan jikina rawa yake yi,tsoro da fargabar abin da zai faru da ni duk sun ɗaure min jijiyoyin jiki.
"Me yasa? Me yasa ba ki jin magana? Kina tunanin za su bar ki ne? Tun da kika bankaɗowa kanki masifar da bai kamata idonki su gani ba to tabbas sai kin ji a jikinki"
Murya na ɗan rawa na ce "Innarmu ni ban ga komai ba"
"Je ki kwanta" ta faɗa cikin muryar bayar da umarni,haka na je na samu wuri na kwanta kwancin da ya zamo mafarin ƙalubalen rayuwata " ina kawowa nan na yi shiru saboda baccin da nake ji,Aliya da Lubna kuwa tsuru-tsuru suka yi suna kallona.
Ban ƙara ce musu komai ba kuwa na lumshe ido ina jin son ganin Maheer ai kuwa kiciɓis na yi da shi ya fito daga wanka daga shi sai towel a ƙugu.Ina shirin buɗe idona amma ya riƙe igiyar masarrafar ganina a dole na tsaya ɗin,wani miskilin murmushi ya saki kafin ya soma goge jikinsa da ƙaramin towel a inda nake a kwance ina jin yadda gangar jikina ke ɓari amma na kasa buɗe ido.Tsorona guda kar ya saki towel ɗinsa don ban shirya mugun gani ba duk da kuwa iya tunani ne ba a zahiri ba,kamar da gayya kuwa sai ya soma warware towel ɗin a hankali har ya fitar da shi hakan yayi daidai tsayawar numfashina a zahiri.Ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na gan ni maƙale da bututun shaƙar numfashi kuma da alamu tuni gari ya waye.
Sai da na ɗauki tsawon lokaci kafin Aliya ta zo ta taimaka min na yi wanka na canza kaya sannan na kawo sallolin da suka hau kaina.Bayan na gama ne na sha fruit salade wanda Dr Muhamud ya kawo min bayan ya duba jikina.
"Ya dai ?" na tambayi Aliya ganin ta ƙure ni da ido.Ta ɗan taɓe baki kafin ta ce "Haule ina ji a raina akwai abin da kike ɓoye min,don Allah ki sanar da ni kika sani ko akwai taimakon da zan yi miki "
"Don me yasa kika ce haka? Wai ina ma Lubna?"
"Tun jiya ta tafi ai bayan mun kira likitoci sun daidaita numfashinki,amma wai mene ne ya haifar miki da hakan?"
Shiru na yi ina tuna yadda na ga tsaraicin Maheer,ba zan iya faɗawa Aliya haka ba sai kawai na jawo wayar da Dr Muhamud ya bani na kunna amma da yake Aliya game da naci ita shugaba ce sai da ta sake ce min "please ki sanar da ni"
Na ɗan yamutsa fuska kafin na ce "ke kawai da zarar na rufe ido ne sai kawai tunanin Maheer da nawa su haɗe cikin na juna sai na dinga ganinsa kai tsaye fa"
Ta tuntsire da dariya kafin tace "saboda shi ne yayi connecting ɗin haka ne yasa da zarar kin rufe ido kike ganinsa,amma shi ai ba ki ganin yana kawowa tunaninki farmaki ko?"
Da mamaki na ce "eh ! Amma ta ya aka yi kika san haka?"
Wani kallo ta yi min kafin ta ce "Haule ina so ki sani daga ke har shi Maheer ɗin na girme muku a zuwan duniya shekaruna sun ninka naku ɗari kawai girman jiki kuka yi ni sannan duk wani abu da ya shafi duniyar Ruhaniya na rige ku saninsa"
Cikina na yi saurin dafewa saboda azaba lokacin da na ji wani abin dariya ga Aliya ƴar mitsitsiya da ita amma tana cewa ta girme min. "Kar ki damu ranar da na sanar da ke labarina za ki yarda,yanzu dai bari na nuna miki yadda za ki yi ki dakatar da shiga tunanin Alhajinki..." da sauri na katse da cewa "a'a ban so ki bar ni a haka"
Ta ce "dalla malama ba kwata-kwata nake nufi ba,irin ki kutsa kanki ba tare da kin shirya ba.Yadda kika san network ai haka ake saita komai,in kin ji kina buƙatar ziyarar tunanin nasa ke ce za ki shirya haka ta hanyar nutsuwa tare da furta wani furici " sake da baki nake kallonta,sai kuma na yarda ta nuna min yadda zan yi ɗin muna tsaka da aikin ne kuma kururuwar wata yarinya ta cika asibitin ni da Aliya muka kalli juna kafin kuma ta taimaka min mu leƙa wajen a tare,ido huɗu na yi da yarinyar wacce ganin fuskarta yasa na tuna a inda na santa wato farar yarinyar nan ce Albino ta can unguwar alhajin da ya cuci Meelat.
Muna haɗa ido da ita ta soma juya nata idon tana yin wani furici,nan take kuma ta soma zazzalo harshenta yana ƙara yin tsayi kafin kuma ya rikiɗe ya koma farin maciji .Wani irin cinno harshen ta yi zuwa inda nake tsaye da niyyar kai min sara kwatsam sai ga Maheer ya damƙe macijin yana mai furta "Sahut!" nan take yarinyar ta faɗi ƙasa a some...... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
17
Dr Maheer na gama furta haka a gaban idona macijinsa ya bayyana ya haɗiye farin macijin yarinyar wacce ita kuma nan take ta fasa wani uban ihu tare da buɗe idonta tarau a kaina.Ko kafin kuma ta yi magana wani mutum ya zo yana kiran sunanta da ƙarfi,sai kuma ya zo ya miƙar da ita kafin ya ja ta su nufi ƙofa.
Har suka fice tana waiwayena tare da yi min wani irin kallo wanda na kasa tantance na mene ne.Tana ɓacewa ganina sai na maido dubana ga Maheer wanda yake a tsaye a gabana ya tsure ni da ido,da sauri na ɗan haɗe rai kafin na ce "ina kwana ka tashi lafiya?"
Bai ce komai ba ya ci gaba da kallona,na turo baki gaba ina gunguni.Ya ja wani ƙyaci kafin ya ce "an ceci mutum amma shegen taurin kai ya hana shi yin godiya "
Cike da iya shege na ce "ai ba a ce ya taimaka ba shi ne da iya yinsa ya zo yayi taimakon saboda kalar dangi"
Wani murmushi yayi mai ɗan sauti wanda ya bayyana haƙoransa,sai na ga ashe in yayi fara'a ya fi kyawu hakan yasa na ɗan shagala da kallonsa har ban ga lokacin da ya tako inda nake ba sai hucinsa na ji.
Na ɗan ja da baya kaɗan ganin mun yi kusa sosai,ina shirin yin magana Dr Muhamud ya zo yana mai cewa "Haulatu zo mu wanke ciwo mu yi sabon bandeji"
"To Hamud" na furta cikin yanga ina kallon Maheer wanda ya haɗe rai lokaci guda kamar ba shi ne yayi tsadaden murmushin nan ba. Na motsa ƙafata da niyyar bin Dr Muhamud sai ji na yi wani abu ya harɗe min ƙafa nan take kuma na faɗi ƙasa rub da ciki,ban yi jinkirin fasa ƙara ba nan take kuma hawaye suka zubo min saboda azabar da ta ratsa cikina.
Dr Muhamud ya kai hannu zai taɓa ni amma Maheer yayi masa wata uwar banza wacce ta yi silar faɗuwarsa ƙasa,kana gani ka san ba iya ƙarfinsa ba ne yayi amfani da shi.
"Me kake taƙama da shi da za ka mayar da ita kamar matarka kana taɓa jikinta a duk lokacin da ka yi niyya?" Dr Maheer ya watso tambayar cikin zafin rai kafin kuma ya maido dubansa gare ni ya daka min wata uwar tsawa wacce ba ni da aka yi wa ita ba hatta Aliya da ke rakuɓe tun ɗazu sai da ta firgita.
"Ki tashi ke kuma kika wani yi kwance kamar gawa saboda salon munafurci,kin fi son yana damƙar kafaɗunki kamar wata mage kina lafe masa a jiki to ba a nan za a yi wannan iskancin ba ,sai dai ku canza asibiti ki" yana gama faɗar haka ya wani fizgo ni da ƙarfi na tashi tsaye kan ƙafafuna ban shirya ba,jini na yi min zuba a ciki.
Dr Muhamud shi ma ya miƙe tare da cakumo wuyan Dr Maheer ta baya yana mai cewa "me ka ɗauki kanka ne da za ka dinga dizga ni kullum a kan yarinyar da ba ka da iko akai?"
"Ka sakar min riga kar na yi maka abin da ba ka taɓa tsammani ba" Dr Maheer ya faɗa yana wani irin ƙoto kamar zai fashe.
"Na ƙi na sake ka ɗin,yi abin da za ka yi" ko baki bai ida rufewa ba ya fasa ihu yana mai yarfa hannu jini sai zuba yake yi masa .
Tamkar wata ƴarsa haka ya ja ni babu tausayi ko mutumci ya mayar da ni wancan ɗakin na farko.Muna shiga ya hankaɗa ni kan gado,na ɗago kai ina kallonsa hawaye na yi min zuba .Wani irin haushinsa nake ji,da ina da iko da babu shakka sai na yi masa dukan tsiya ko kuma na yi masa launin azabar da bai taɓa gani ba.
"H.lee wai me kike nufi da ni ne uhum? Raina ni ne kika yi ko me? Me yasa kike son yin abin da duk zai ɓata min rai? Sau nawa na sha faɗa miki cewa ki dakatar da wannan rawar kan naki akan abin da ba ki da ilimi a kai? Ita wannan yarinyar da kika jajiɓo kin san ƙarfin ikon da ke jikinta ko kuwa kin san ƴar wace ce ita? Me yasa duk wani abu da zai jefa rayuwarki cikin haɗari shi kike yi? Da kika mayar da kanki a arha kamar ruwan pure water kina ganin hakan daidai ne kin yi wa rayuwarki adalci? "
Zuciyata wani irin ɗaci take yi mini,sam babu tausayi ko rarrashi a tattare da Maheer.Yin komai yake yi cike da gadara da kuma zafin kai,ganin kowa yake a ƙasansa. "Rayuwarka ce ko tawa? Ba pure water ba ko baƙar leda na zama mene ruwanka a ciki? Ina ce dai ba kai ne ka ɗauke ni aiki ba kuma ba a ƙarƙashin ikonka nake ba don haka kar ka takura mu ni da...ni da..ni saur...." na soma i'ina saboda wani mugun kallon da na ga yana watso min mai cike da tafasasshen ɓacin rai,da na ga dai sam tsaurin idona ba zai yi wani tasiri sosai ba sai na turo baki tare da tashi da niyyar fita.
Bai ce mini komai ba,ni na tsaya na kasa motsi da niyyar kaina sakamakon ganin shegen macijinsa a tsaye a bakin ƙofa .
A hankali na ɗan waiga na saci kallonsa sai na ashe idonsa na kaina,ƙuri muka yi wa juna muna kallo kafin ya tako ya matso kusa da ni.
Na ja wani irin numfashi a daidai lokacin da ya hura min iskan bakinsa a fuska,ido na lumshe ina jin bugun zuciyata na tafiya sauri-sauri.Ban san ta yaya aka yi na tsinci kaina a kwance kan bed ba,amma sai a haka na ganni yana wanke ciwona da tuni ya cire min rigar gaba ɗaya.
Na kai hannu na ɓoye ƙirjirna da suka ɗan fito ta saman bra,shi kuwa bai ma ɗago ba aikinsa kawai yake bayan ya gama wanke ciwon sai yasa reza ya yanki yatsansa manuniya nan take jini ya soma zuba sai ya kai shi daidai saitin ciwona yana ɗiga a ciki.
Da sauri na ƙara lumshe ido ina jin wani sanyi na ratsa ni haɗi da wani ƙarfi.
"Mene ne kake yi mata?" muryar Dr Muhamud ta daki kunnena,da sauri na ware idona a kansa sai na ga tuni an naɗe masa hannu da bandeji. Kai tsaye kuma Maheer ya basa amsa da "abin da ka kasa yi mata kai da sauran likitocin da kuke gani komai kun sani a harakar likitanci"
"Wannan ai tsafi ne kaka yi"
"In fitsari banza ne kaza ta yi" Maheer ɗin ya faɗa yana mai wani nitsa yatsansa a ciwona duk da ban wani ji zafi sosai ba amma hakan da yayi yasa na maido hankalina a gare shi muna haɗa ido na ji ya ɗaure ni da wani abu kamar igiya.
"Alhajina don Allah ka bar fushi da Dr Muhamud ka san ba tsararka ba ne in dai ta ɓangaren ilimi ne.Ka yi haƙuri ka ci gaba da koya masa abubuwan da bai sani ba ka ji oga Maheet?" shi ne furicin da ya fito bakina ba tare da ni kaina na san ta yaya ba,sai uban murmushi nake zubawa.Ban san lokacin da Dr Muhamud ya bar wurin ba,na dai duba ban gansa ba kuma ban san dalilin da yasa ya tafi ba hasali ma hatta furicin da na yi bai cikin ƙwaƙwalwata saboda ba yin kaina ba ne an juya tunanina ne ba tare da sanina ba.
A karo na biyu Maheer ya cire rigarsa ya saka min,sai dai a wannan karon shi ne ya ɓalla maɓallan rigar da ya zo na ƙarshe na can sama haka ya ture hannuna tare kafe wurin da kallo kafin kuma ya saka min maɓallin yana wani jan numfashi kamar ransa zai fita.
Da mamaki nake kallonsa,sai na ga kamar ya tsargu ko kuma yana cikin damuwa.Ficewa yayi ya bar ni nan kwance shaye da mamaki,ƙamshinsa duk ya dabaibaye ni ya kuma sakar min wata muguwar kasala.
Aliya ta shigo tana murmushi kafin ta matso kusa da gadona ta ce "congratulation!" sai kuma ta yi ƴar dariya kafin ta shafi gashin kaina ta ce "kin ga abin da nake faɗa miki ko? Wallahi oga sonki yake yi"
"Sai yanzu kika ga damar zuwa inda nake?"
"Wallahi tun ɗazu na zo bayan nurse Fatee ta yi wa Dr Muhamud bandeji a hannu,kusan a tare muka zo ni da shi amma ni a bakin ƙofa na laɓe ina kallon oga Maheer na soyayya Hahaha wuuuu! Wai me kika ji da ya kalli ƙirjinki?"
Na haɗe rai na ce "wai Aliya ni sa'arki ce?"
Ta ɗan harare ni ta ce "Haule bari fa ganin kin fi ni girman jiki,na faɗa miki ni ba yarinya ba ce tsohuwa ce nan da kike gani na girme muku ke da ogan ƴan tsamin rai"
Na ɗan saki murmushi kafin na ce "Allah yasa ya ji ki"
"Amen! Faɗa min mana wace ce wannan yarinyar Albino ?"
"Ni ma ban sani ba wallahi,amma da buƙatar mu binciko.Ko kin san wani abu game da ita?"
"In na sani ta ya za a yi na tambaye ki? Amma da alamu shi oga fa ya sani"
Na ɗan taɓe baki kafin na ce "eh haka ne,don Allah je ki ɗauko min wayata ina son yi wa Dr Muhamud text"
Aliya ta ɓata rai kafin ta je ta ɗauko,kiransa na yi don akwai lambarsa amma ya ƙi ɗagawa haka ma da na tura masa saƙo ya ƙi maidowa.
Muna nan zaune sai ga Lubna ta shigo,fuskarta babu walwala dakyar ma ta iya tambayata ya jiki kafin ta nemi wuri ta zauna. Duk shiru muka yi,kafin kuma can ta ce "Aliya ina son yin magana da ke"
"To anty ina jin ki"
"Mu je daga waje"
"Don me ba a nan ba? Ko hirar sirri ce?" na tsoma bakina . Lubna ta yi murmushin yaƙe kafin ta ce "ina son yi mata wata magana ce Haule,kin ga ita yarinya ce ba komai ne za ta sani ba game da rayuwa"
Aliya ta yi wata dariyar shaƙiyanci kafin ta ce "su anty Lubna manya,in dai akan Dr David ne kar ki yi ɓarnar yawunki "
"Amma ai dai kin san saurayina ne ko?" Lubna ta faɗa cikin ɗaga murya.
Aliya ta ce "a'a gyara kalamanki tsohon saurayinki dai,kuma ina ce a jiya ba ki nuna kin san shi ba"
"Ok na ga da dukkan alamu kin kamu da sonsa ma tun tuni"
"Wannan kuma ba damuwarki ba ce" Aliya ta faɗa tana wani kaɗa ƙafa ni har mamaki ma ta bani,da na ga abin nasu zai yi nisa na dakatar da su ta hanyar cewa "ina ga dai sai na kira Alhaji sai ya raba muku gardama " duk shiru suka yi suna harar juna kafin kuma Lubna ta miƙe ta fice.
Bayan fitarta ne na dubi Aliya kafin na ce "Lubna ta yi gaskiya bai kamata ki kula Dr David ba,ko ba komai ana barin halak ko don kunya"
Aliya ta tsuke baki alamun ta ji haushi kafin kuma ta sauya maganar da cewa "za mu je can gidansu yarinyar ko kuwa sai oga ya baki izini?"