Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 14

Bakin ruhi complete - Chapter 14

Bakin ruhi complete Chapter 14: Bakin ruhi complete Chapter 14. Na ɗan harare ta kafin na ce "ya aka yi kika san wannan ne nufina? Tashi mu tafi yanzu ai…

3,332 words

Na ɗan harare ta kafin na ce "ya aka yi kika san wannan ne nufina? Tashi mu tafi yanzu ai na ji kamar ciwon ya gama haɗewa" Duk sai muka miƙe muka fita,mun yi sa'a kuwa har muka fita daga asibitin babu wanda ya gane mu.A bakin ƙofa muka ga Lubna tana jiran taxi ,sai da na ɗan rarrashe ta akan abin da Aliya ta yi kafin ta saki jikinta.

Bayan haka kuma a tare muka shiga taxi,a ƙarshe ita ce ma ta biya kuɗin har muka isa unguwar da na ga Albino ɗin yarinyar nan.

"Ga gidansu nan ,amma ta ya za a yi mu shiga?" na yi tambayar.

Aliya ta ce "ku zo mu je zan san yadda zan yi na shagaltar da mai gadin" sai dai muna zuwa abin ya zo da sauƙi sam bai hana mu shiga ba,ban san me ya gani a tattare da mu ba har ya bar mu.

Babban gida ne sosai mai bala'in kyawu,iya tsakar gidan ma abin kallo ne.Muna shiga babban falo duk muka ja muka tsaya,wata mata muka gani a zaune kan kujera ta ɗago ta dube mu da idonta da suke cike da rauni.Na haɗiye wasu yawu kafin na ce wa Aliya "kin ga abin da na gani?"

"Eh da alamu ita ma tana cikin matsala kawai mu ƙarasa sai ki san yadda za ki yi ta bamu labari"Aliya na gama faɗar haka kuwa muka ƙarasa muka zauna mu duka ukun.

Idonta suka soma zubar da hawaye kafin kuma ta ce "su wane ne ku?"

"Masu maganin matsalarki da kika yi shekara da shekaru a cikinta.Kar ki damu labari kawai za ki bamu mu kuma za mu san yadda za mu yi mu fitar da ke"

"Ni ban damu kan sai kun fitar da ni ba,burina kawai ku tseratar da ƴata Yasmine wacce ta kasance komai nawa duk da ana son ɓoye min haka amma tuni na fahimci ƴata ba ta da lafiya.Ƴata Yasmine ba kurma ba ce,amma dare ɗaya muka wayi gari ba ta yin magana.Haka na dinga yawon kai ta asibitoci amma duk wani scanning da aka yi ya nuna lafiyarta lau,amma ni na san ba gaskiya ba ce ƴata ba ta lafiya akwai wani abun sharri da ya same ta.Satin da ya wuce muna kwance kan bed tana gefena na soma jin muryarta tana cewa "Mama ki cece ni ki taimake ni sun ɗaure ni su sace min taurarina " lokacin da na farka ina kallon Yasmine sam bakinta bai motsawa amma tabbas muryarta ce ke fita,yayin da kuma ta buɗe dukkan idonta tana kallon sama cike da tsoro alamun wani sababin ta gani.Sai na yi ihu ina jijigata haɗi da ambaton sunanta,tamkar gawa haka take a sandare sai da aka ɗauki lokaci kafin ta dawo daidai. Washegari,sai na kira Goggona na shaida mata saboda ina yawan jin tana magana taurari,don kusan ma zan iya ce muku ita ɗin malamar duba ce.Ina gama faɗa mata sai cewa ta yi "akwai waɗanda suka damƙe ruhin muryar ƴarki,ƙila don su sayar ko kuma suna tunanin za ta kawo musu matsala gobe da safe ki kawo min ita in duba ta"

Haka kuwa aka yi, washegari muka je ni da Yasmine da zuwanmu Goggonmu ta ɗora hannunta bisa kan Yasmine sai ta soma yin magana cikin wani Yare can kuma sai ta ce "muryarta na nan sannan tana yin magana da ita a wata duniya wacce ba wannan ba,an dantse mata harshe ne ta yadda ba za ta iya furta wani abu ba a wannan duniyar da muke ciki"

Tamkar zan faɗi haka na ji,sai da na samu wuri na kwanta na maida numfashina.A gabana ta haɗa ruwan wanka ta wasu ganyayyaki ta yi wa Yasmine wanka tana yi tana yin wasu suratai daga ƙarshe kuma sai ta fasa wani baƙin ƙwai ta bata ta sha babu jimawa kuma jini ya soma ɓulɓulowa Yasmine ta hanci da ido sosai na ga tsoro a idon Goggo,jikinta kuma ya ɗau rawa cikin wata irin murya ta ce "wannan wane irin bala'i ne wannan? Ƴarki na cikin matsalar da ba zan iya yin aiki akai ba gaskiya.Ku tashi ku tafi kar ku shafain kashin kaji" tana gama faɗar haka sai ta bar mu nan,ina kuka ina ƙari na ja Yasmine muka dawo gida.Ko hutawa ba mu yi ba na samu labarin cewa Goggo ta haukace tana can ta bi duniya, wannan lamari yasa na ji tsoron kai ta wani wajen muka ci gaba da zama a haka.Kullum kowanne dare da misalin ƙarfe biyu sai Yasmine ta soma yin wani ihu yadda kika san na doguwar ruwa, in kuma ta sauko ƙasa haka za ta yi ta ihu tana dire-dire wannan dalili yasa kullum take can sama a kulle hatta ni mahaifiyarta banda ikon ganin ta sai dai na ji motsinta in kuma tsautsayi ya ja ni na je can to zan fito da rauni don ta zama kamar wata mahaukaciya ba ta son mutane.Yau fa tun daga can sama ta buɗe window ta diro ta fita ta bar gidan nan,ban ma sani ba sai da abokin mahaifinta ya kawo ta gida " tana kawowa nan ta yi shiru.Ko kafin kuma wani daga cikinmu yayi yunƙurin cewa wani abu muka ji wata murya na cewa "Leena?" kusan duk a tare muka juya yayin da ita kuma Lubna ta wani miƙe hankali tashe.....

[5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

18

"Leena manya! Dama kina ƙasar?" wata ƴar duniya ta faɗa tana mai shigowa cikin tsakiyar falon,ban wani caza ƙwaƙwalwata sosai ba na fahimci wace ce don a labarin da Lubna ta bamu ta faɗa mana sun canza mata suna.

Kallon masheƙan aya ta yi mamu ni da Aliya kafin ta ce "da waɗannan kika koma yawo? Hahaha! An ci baya gaskiya,am... Duk ba wannan ba me kika zo gidan Boss? Sanina dai ba ki dawo bakin aikinki ba duk da dai na ji oga na shelar cewa kin yi wa family bazata kin ziyarce su"

Lubna ta haɗiye wasu yawu kafin ta ce ,"ni ban je ba ƙarya ya yi miki "

"Hahaha! Ogan ne zai yi miki ƙarya? To ka ji.Oh na manta anty Bahijja ina wuni? Oga ne ya ce na zo na duba lafiyar Yasmine " Sai a sannan ne muka san sunan matar gidan Bahijja,adadin farashin tsoronta ne ya hau kafin ta ce "tana can sama"

Zuly ta kama hannun Lubna tana mai cewa "mu mana ƙawata ki yi min rakiya" ba ta ida rufe bakinta ba na kai hannu na zare hannun Lubna daga cikin nata kafin na ce "ba ki ta nuna miki ba ta son hulɗa da ke ba? Ko ana ƙawance dole ne? Mu tarkacen dai mu take ra'ayi,ke kuma da kike ƴar gayun ba ta yinki"

Wani irin juya ido Zuly ta yi da niyyar cutar da ni,sai dai tuni ta makaro don ni ma ina da tawa power ta hana abu motsi ko kuma saka shi abin da bai yi niyya ba tuni na gusar da ganinta ta koma tamkar makauniya sai kuma na saka ƙafa na shure ta nan ta faɗi jikin kujera kanta ya bugu har ya soma zubar da jini.

"Ku zo mu je mu fitar da Yasmine kafin su rige mu ɗaukarta,ke Bahijja ki tsaya nan yanzu mun fito" na faɗa cikin sauri.

Aliya ta ce "Lubna ta zauna tare da ita mu kuma sai mu haura can sama"

"Hakan ma yayi" na faɗa tare da kama hannun Aliya muka je da sauri muka haura can sama,tun kafin mu isa muke jin wani irin yanayi marar daɗin ji mai kuma tattare da tashin hankali. Aliya ce ta yi amfani da ƙarfin ikonta muka ɓalla ƙofar muka shiga,cak muka ja muka tsaya muna kallon Yasmine a kwance kan bed babu sutura a jikinta.Dukkan wasu alamu a bayyane suke,ana tarayya da ita ne kamar yadda ake mu'amalar aure banbancin kawai ita ba da mutum ba ne take yi ba ko dai ruhi ko kuma aljani.

Wani irin kuka ne ta fashe da shi kafin kuma ta tashi zaune tana ƙanƙame jikinta,zuciyata ce na ji ta yi rauni sai Aliya ce ta ƙarasa ta je ta ɗauki doguwar rigarta ta mayar mata sai kuma ta jawo ta suka zo gabana.

Yasmine ta faɗa jikina tare da ƙanƙame ni gam tana kuka,ba tare da na tambaye ta ba ta soma bani labarinta "ƙalubalen nan ya riske ni tun ina ƴar ƙaramata, lokacin da na cika shekara uku na san za ki yi mamakin jin ta yadda aka yi har na yi wayon riƙe abu a ƙanananun shekaru irin haka,to hakan nada nasaba da rainon da jinnu suka yi min tun ina cikin mahaifiyata.Tun daga wannan shekarar na soma fuskantar wani abu da ban san mene ne ba,sai ina tsaka wasa da yara sai na ji wani abu ya zo ya kwantar da ni yana wasa da sassan jikina haka za a yi ta ganin ina juye-juye kwance a ƙasa babu wanda ya san taƙamaimai abin da ke faruwa da ni hatta kuwa mahaifiyata.A lokacin da kuma na kai gaɓar shekaruna biyar sai na ɗauki tabi'ar auren hannu na yaɓa,haka zan dinga taɓa jikina ba tare ni kaina na san dalili ba ,ba zan manta ba Mama ta taɓa ganina ina wasa da jikina ta yi mini duka tare da yi min hani da hakan sai dai abin da ba ta sani ba haka nake shiga ɗaki ina yi ko kuma in ta yi bacci.Kar ki tuhume ni domin ba yin kaina ne ba,wata murya ce nake jin tana yi min suwa a dodon kunne tare kuma da bani umarnin yin haka.Lokacin da na kai shekara takwas tuni an saka ni makaranta,a daidai wannan gaɓar za ki ga yara suna sha'awar yin karatu amma ni ta baibaye lamarin ya zo min sam na tsani makaranta in ma na je to kallon yara mata ƴan ajinmu nake tsayawa yi ina jin wani abu na fizgta ,da farko ban gane me hakan ke nufi ba sai daga baya na fahimci sha'awarsu ce nake ji.Haka in mun fita shan iska zan dinga yin wasa da ƴan ajinmu ina taɓa jikinsu,su suna ɗaukar haka matsayin normal wasa ba tare sun san ni daɗin haka nake ji ba ko kuma na ce BAƘIN RUHIn da ke jikina ke jin daɗin haka ba.Sosai nake son mata ƴan uwana amma na tsani mazan ajinmu da duk mazan duniya in kika cire Daddyna.Har zuwa lokacin da na shekara sha biyu a duniya ina yin auren hannu ni da ƙawayena na makaranta wanda tuni muka jone muka zama tantiran kanmu,mu uku ne muke wannan mummunar ɗabi'ar,ni,Firdo sai Malika.Mafi yawan lokutan da muke biya juna buƙata shi ne lokacin shan iska,haka za mu je cikin banɗaki makaranta mu yi duk abin da muke so mu fito.Ko kuma a gidansu Firdo kasancewar iyayenta masu aikin gwamnati ne ba zama suke yi a gida ba,mun sha guduwa daga makaranta mu je can kawai don mu yi baɗala.Ina shiga shekara ta sha uku sai na fara period daga nan ne ƙalubalen ya ƙara ta'azzara kullum cikin baccina haka zan dinga ganin muna yin sex ni da wata halitta,da na shaidawa ƙawayena sai suka ce ai su ma suna yin irinsa kuma sosai suke jin daɗin haka.Wannan mafarkin da muke yi shi ya yi sanadin kuma barin lesbian ɗin da muke yi sai dai inda matsalar ta ƙara yawa shi ne ko a ina nake haka zan ji wani irin yanayi kafin kuma bacci ya ɗauke ni shikenan sai dodon nan ya zo min yana mu'amala da ni.Watannin da suka gabata na taɓa yin bacci cikin aji ,da na farka sai malamarmu ta kira Mamana ta shaida mata shikenan sai aka hana ni zuwa makaranta .Ashe wannan duk shirin ruhin da ke cikin jikina ne,saboda yana son yin mu'amala da ni duk bayan kowacce awa tun yana zuwar min a mafarki har na fara ganinsa a zahiri shi ne da na buɗe baki da niyyar yin ihu ya damƙe min murya Please ki taimaka min ki fitar da ni daga cikin gidan nan,a ranar nan da na gan ki sai na ji kamar ke ce fitilar da za ta haska rayuwata wannan yasa na faki idonsa a lokacin da ba ya nan na fita na je nemanki sai kuma aka yi rashin sa'a macijin da ya bani don kula da ni ya so cutar da ke" tana gama faɗa min labarin sai ta fita daga jikina tana wani waige-waige cike da tsoro, wannan karon da ido ta yi min magana don alamu sun nuna muryartata ta ƙara maƙalewa,"ga alamun zuwansa nan Please ku yi sauri ku fitar da ni"

"Aliya mu je" na faɗa tare da kama hannun Yasmine ɗin muka fito a guje sai dai muna fitowa falo muka yi tsaye cak sakamakon ganin mutumin nan na ɗazu wanda ya ja hannun Yasmine a asibiti sannan Zuly na tsaye kan ƙafafunta ga Lubna da anty Bahijja suna kuka.

Yasmine ta ɓuya a bayana tana riƙe ni gam,sai yanzu na fahimci wannan mutumin shi ne Oga. Kana kallonsa ka ga mugu,takowa ya soma yi yana tunkaro mu yayin da ni kuma na riƙe hannun Yasmine gam na soma ja da baya haka ma Aliya,har sai da muka dangane da bango.

"Su wane ne ku? Da izinin wa kuka shigo nan?" su ne tambayoyin da ya jero mana,ban iya cewa komai ba sai aukin kallonsa.

" Yasmine ɗin Daddy zo nan ,zo na kai ki wurin Daddynki " yayi furicin cikin taushin murya,ƙin tafiya ta yi ya zo da ƙarfi zai fizgo ta amma na yi saurin dakatar da shi ta hanyar amfani da ƙarfin ikona sai ya daskare wuri guda.

Da gudu muka barsa nan muka je can wajensu Lubna,Zuly ta kamo hannun Yasmine amma na buge ta a dole ta sake shi tare da daskarewa ita ma .Aliya da Lubna suka kama Yasmine ɗin tare da nufar ƙofa da ita,yayin da ni kuma na kamo hannun anty Bahijja sai dai fa fita da ita daga cikin gidan ya cuttura don da dukkan alamu an yi mata mugun kafi wanda ba zai bar ta iya fita ba.

Cikin kuka ta ce "ku tafi ku bar ni,ba zan iya ƙetare iyakar ƙofar nan ba"

"Ba zan bar ki ba wallahi,Aliya kawai ku tafi zan same ku a gida " na faɗa tare da soma duba ko ina na gidan ko Allah yasa na hango wani abu da ya shafi guru ko laya,su kuwa tuni sun bar wurin.

Sama da minti talatin ina bincikar gidan amma ban ga komai ba,can dubara ta faɗo min sai na riƙe hannun anty Bahijja sai na lumshe ido da niyyar karanto wasu formula masu taimakawa mutum ya tashi sama kamar leda.Azababen zafin da na ji ya caki hannuna shi yasa ni saurin buɗe ido nan na yi arba da Oga wato ya kwance ƙullin da na yi masa,ko kafin kuma na yi wani yunƙuri ya soma karanto ɗalasiman tsafi nan take gidan ya soma juyawa yana rangaji,guguwar da ƙura tuni sun turniƙe ko ina.A yadda na ji yana ambatar ƙasar Japan na fahimci so yake ya kai mu can ta hanyar tsafi,da sauri na lumshe ido na soma karanto abubuwan da Aliya ta faɗa min in ina son haɗa tunanina da na kuma Maheer.Cikin ikon Allah kuwa na samu nasarar damƙo tunanin nasa,yana tsaye cikin wani ɗako yana aikin tiyata idonsa sanye da wani gilashi ga fitilar tsakiyar goshinsa,yayin da fuskarsa ke rufe da facemask.

Hasken fitilarsa ne ya ƙara yawaita,wanda nake jinsa har cikin ɓargon raina ina dab da shiga komar Oga Maheer ya samu nasarar jefo ni wajen gidan.

Tari na soma yi ina kallon yadda hayaƙi yake tashi sama,iya ni ɗaya kawai na fito banda anty Bahijja.Ba don na so ba haka na tafi na bar ta saboda yadda jini ke yi min zuba a hannu,ko kafin na kai bakin titi jiri ya soma ɗibata saboda babbar jijiyar magudanar jini ce Oga ya tsinka min ba.

Da na tsayar da taxi na faɗa masa sunan asibitinsu Maheer,ko kafin a isa na fita hayyacina wai ma don mai taxi ya taimaka ya ɗaure min hannu.

Dr Muhamud ne kuwa kan aiki,shi ya bani taimako yana tsaka da rufe ciwon Maheer ya shigo da alamu sai yanzu ya gama aikin.Saurin sunne kai na yi don na san ko makawa babu sai ya aiko min mugun kallon nan nasa, Dr Muhamud na gama naɗe min hannun ya fita ya bar mu nan mu biyu.Duk da ina jin idonsa a kaina amma na ƙi ɗagowa,na yi shiru ina sauraren bugun zuciyata da ya ƙi daidaituwa ta ƙasan ido na ga lokacin da ya ja ƙafafunsa ya fice sai a sannan na ɗaga kaina ina mai jan wani numfashi.

★A can ɓangaren su Oga kuwa cike da baƙin ciki ya tsayar da manufarsa .Komai ya tsaya cak tare da dawowa normal,ya dubi Bahijja wacce ta kasance matar Boss ɗinsu cike da takaici sai dai babu damar yi mata masifa ko zaginta.Zuly ta fito ita ma a tsakiyar gidan fuskartar na bayyanar da tsantsar tashin hankali,"oga ina Yasmine?" ita ce tambayar da ta yi.

"Sun tafi da ita! Amma yaushe har Luby ta samu ƙarfin iko haka? Sannan wace ce wannan ta tare da ita mai ɗauke da wani abu na musamman mai bata kariya?"

"In akwai wacce za ta baka amsa ai anty Bahijja ce,don a tare na tarar da su" Zuly ta faɗi haka duk kuma sai suka tsurawa Bahijja ido wacce ke kukan farin cikin. Suna cikin halin ƙaƙanikayi kiran Boss ya shigo wayar Oga,babu damar ƙin ɗauka wannan dalilin yasa Oga yin shahada ya ɗaga kiran.

"Mene ne ke faruwa a can? " ita ce tambayar da Boss yayi.

Murya na ɗan rawa Oga ya ce "babu komai Boss".

"Ina Yasmine?"

"Tana bacci sai mahaifiyarta kawai ke farke"

"In ta tashi ka tabbatar ka bata maganinta,sannan ina buƙatar Leena nan da wani ɗan lokaci tun da ta dawo aiki tare da family wannan karon ya zama dole ta bani haɗin kai"

Oga ya ce "wannan ai dolenta ne,kuma kamar ta zo a shimfiɗarka ne ta gama don ba za mu ɗaga mata ƙafa ba" nan dai suka gama waya suka yi sallama,goshin Oga sai tsatsafo da zufar tsoro yake.

Ko inda Bahijja take bai kalla ba ya ja hannun Zuly suka bar gidan.Can kamfani suka wuce,bayan sun shiga ofishinsa ne ya dube ta da kyau kafin ya ce "ki san duk yadda za ki yi ki nemo Leena domin ta hanyarta ne kawai za mu samu Yasmine ,na baki nan da 24h ki nemo ta"

Zuly ta ce "Oga me zai hana mu yi amfani da ƙarfin tsafi wurin binciko su?"

"Matsalata da ke Zuly kwanyar kifi ce da ke,kina tunanin madubin tsafi na iya binciko mana inda suke? Kafin su je can dama sun yi dogon shiri ta yadda babu wani madubin sharri da zai iya nuno su.Ke dai ki zage dantse ki yi aiki tuƙuru kafin Boss ya farga ƴarsa ba ta gida,sannan in son samu ne har da waɗannan ƴan matan biyu duk ina buƙatar su "

"Na fi tunanin cewa ƙarfin ikonsu ya samo asali ne daga Uwa Yabobo,don kamar ira take aiki da power canza tunani da ta kuma daskarar da mutum"

"Kina tunanin in mun je ita Uwa Yabobo za ta faɗa mana wani abu dangane da su ne?"

"Eh ! Duk da na san sai ta nemi abu mai matuƙar muhimmanci a gare mu"

Suna tsaka da tattaunawar nan ne Boss ya bayyana a ofis ɗin,sanye yake cikin wasu baƙaƙen kaya ya ɗora hullarsa ta gado mai kamar ta sheɗan.Fuskar nan kicin-cikin,bai wani ɓata lokaci ba ya ce "ku faɗa min duk abin da ke faruwa kawai"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull