Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 15

Bakin ruhi complete - Chapter 15

Bakin ruhi complete Chapter 15: Bakin ruhi complete Chapter 15. Zuly ta haɗiye wasu yawun tsoro kafin ta soma koro masa bayani daki-daki,bayan ya gama…

3,319 words

Zuly ta haɗiye wasu yawun tsoro kafin ta soma koro masa bayani daki-daki,bayan ya gama saurare sai cewa yayi "a halin yanzu yarinyar da ta fitar da Yasmine ta fi yi min muhimmanci,don haka ita nake so.Duk ku ture tunanin ceton ƴata don ina da tabbacin ba cutar da ita ne za su yi ba "

Oga da Zuly wani irin sanyi suka ji zuciyarsu ta yi,jin Haule kawai yake so ba Yasmine ba.

★Asibiti Sai da na ci zama sosai kafin na fito,Dr Muhamud na gani a tsaye sam ban san cewa waya ce yake yi ba na matsa cikin sigar rarrashi na ce "Please Hamud ka yi haƙuri" wata irin zabura yayi yana mai ciro wayarsa daga aljihu ya kashe kiran sannan ya cire ɗan ƙaramin bluetooth ɗin da ke maƙale a kunnensa.

"Haulatu?" ya kira ni cikin wani sauti,ban kai ga amsawa ba wayarsa ta ɗau ringing sai ya ce "ina zuwa" sai kuma yayi gaba kaɗan kafin ya ɗauki kiran,yana magana yana kallona hakan yasa na ƙure bakinsa da ido har ta kai ina iya jin abin da yake cewa.

"Hearty wallahi gaskiya nake faɗa miki babu wata mace da ta zo kusa da ni,to wai me zan yi da wata ni da nake da kyakkyawa irinki? Ai a wurina duk sauran mata kwadon shara ne ..." ban tsaya ida jin abin da yake cewa ba na yi gaba na fita,tafiyar ƙasa na soma yi na ɗan yi nisa sosai kafin na ga mota ta parker a gabana.

Na yi tsaye ina kallonsa ina tuna ƙaryar da ya gama shararawa yanzu. "Zo ki shiga na sauke ki a gida" ya furta lokacin da ya fito yana mai buɗe min gidan gaba,saboda na ga da mutane a wurin sai na shiga na zauna ina shirin rufe murfin muka yi ido huɗu ni da Maheer yana tsaye gaban wani tsoho suna magana .Dr Muhamud ya ce "ya dai me kike kallo?"

Na ɗan yi murmushin yaƙe na ce "kamar Dr Maheer nake gani a can" na faɗi haka ne don sake gaskata shin wai da gaske shi ɗin ne ko yaya.Amma da mamakina sai ji na yi Dr Muhamud ya ce "ko dai idonki sun fara samun matsala ai babu kowa a can"

Na ce "a'a naka idon suka samu matsala ga Dr Maheer can shi da wani tsoho"

Dr Muhamud ya tuntsire da dariya kafin kuma ya soma tuƙa motar,har sai da ya kawo inda nake nuna Maheer na tsaye sannan ya ɗan tsaya ya ce "suna ina?" ban basa amsa ba saboda numfashina da ke barazanar tsinkewa,na farko irin kallon da Maheer ɗin ke yi min,na biyun da ya fi dukan zuciyata shi ne ganin mutumin nan da suke a tare sam fuskarsa babu wani alamun siffar mutum,babu ido ,babu hanci,haka ma baki babu fuskar a shafe take lis.Ko da Dr Muhamud ya ji ban ce komai ba sai ya ci gaba da driving har muka isa,ban ma tsaya mun yi wata sallama ba na wuce ciki sai na taras da Yasmine tana hauka yayin da Aliya ke ta ƙoƙarin ganin ta lalaɓe ta,Hajiya da Lubna suna a ɓoye bayan kujeru sai ido suke zarowa..... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

*Ina masu sha'awar karanta horror Books ɗina? To ga dama ta samu na yi muku bonanza ku zo ku zaɓi waɗanda kuke so a farashi mai sauki wacce ta shirya ta tuntuɓe Ni a waccan lambar tawa ta sama* __________________________________________________ *PAID PAGE* BONUS

19

"Yasmine???" na kira sunanta da ƙarfi sai ta tsaya cak tana juya manyan idonta da suka canza kala,tare kuma da maida harshenta da ya zazzalo har yana shirin jan ƙasa.A hankali na soma takawa har na tsaya kusa da ita sai na jawo ta na rungume ,wata irin ajiyar zuciya ta soma saukewa akai-akai daga nan bacci ya ɗauke ta,dakyar na iya janta na kwantar da ita kan kujera sai a lokacin Hajiya da Lubna suka fito daga maɓuyarsu.

Cikin balabalin bala'i Hajiya ta ce "wallahi wannan aljanar ba za ta zauna min a nan ba,ina dalili ni da gidana a hana ni shaƙat ana tsoratar da ni bari Maheer ɗin ya dawo wallahi sai dai ya kai ta can ɗakinsa tun da shi ya jajiɓo ta"

Ina jin abin da Hajiya ta ce sai na fahimci wato ƙarya su Aliya suka yi mata suka ce Maheer ne ya ce a kawo ta nan gidan.Da ido kawai na kalle su kafin na nufi hanyar bangarenmu, toilet na shiga na yi wanka na fito na zauna ina tsaka da shafa mai daga ni sai ɗaurin ƙirji aka banko ƙofa.Maheer ne,cikin halin nasa wanda in bai yi ba to ba zai ji daɗi ba ya ce "yaushe na yi da ke na ce ki dinga kawo min patient ɗinki a gida ? Sannan ban hana ki shishigewa Dr Muhamud na ba? Shine yau kika shiga gaban motarsa ke ga isasshiya wacce ta cika ta tumbatsa kin fi ƙarfin ki ɗauki maganar da aka yi miki"

Ban ce masa komai ba in banda ƙoƙarin nemo hijabin da zan saka da nake yi,ya ja uban tsuki ya ce "me ne za ki rufe wanda ban sani ba? Ƴan tsiri-tsirin abin kamar ƙwan budurwar kaza ko kuwa baƙin tambon da ke cinyarki?"

Cak na tsaya tare da tsure shi da ido,hankalina kuma sai na ji ya tashi.Murya na rawa na ce "ya aka yi ka san ina da tabo ga cinya?"

Wani banzan kallon yayi min kafin ya fice yana mai cewa "ki tabbatar kin samowa baturiyarki wurin da za ta zauna"

Sam kasa nutsuwa na yi haka na yi ta tunanin ta yadda aka yi har ya san ina da tabo a cinya,sannan shaf na manta da cewa ya taɓa kai ni ɗakinsa.Kamar kazar da ta fashewa a ciki haka na samu na kimtsa,da zan saka bra sai da maganarsa ta dawo min .Wato ƙirjina ne ke kamar ƙwan budurwar kaza tsabar ya raina ni,ina tsaka da fesa turare Aliya ta shigo tana mai cewa "ina son zan fita"

"Ina za ki je?" na tambaye ta,ba ta kai ga bani amsa ba kuma muka jiyo kururuwa can falo da sauri muka fita sai muka taras da wata baƙar ybudurwa ce ke wannan aiki,a cikin abin da bai fi minti biyu ba na hango tsantsar kamanninta da Hajiya .

Maheer na kalla wanda ke tsaye fuskar nan tasa ta yi kicin-cikin kamar zai fasa kuka,da na dubi ɓangaren da Hajiya take ita kuma sai na ga tana sharar ƙwalla kafin ta ce "ina Ummarki take ? Tun yaushe kuka shigo garin nan? "

Cikin kuka budurwar ke cewa "Umma tana can sun ɓoye ta ni ma guduwa na yi"

"Ya isa haka! Ta je ta yi wanka ta ci abinci ina zuwa" Maheer ya faɗa tare da tafiya ya soma taka matakalar benen da zai kai shi sashensa,na bi bayansa da kallo har ya ɓacewa ganina.

"Haule kai ta can ɗakinku,ki nuna mata yadda za ta yi wanka sai ki bata kaya ta canza" Hajiya ta faɗa .

Cike da ladabi na ce "to hajiya" sai kuma na je na kamo hannun yarinyar,wani irin shock ne ya ziyarce ni tamkar na riƙe wayar lantarki haka na ji har sai da na rumtse idona nan kuma na hango wasu abubuwa masu kamar mala'iku duk sun tsaya kan ƙafafunsu suna gaishe ni,da sauri na buɗe idona na zube su kan budurwar sai na ga ta yi min ƙuri tana kallo.

Na ɗan saki murmushin yaƙe kafin na ja ta zuwa sashenmu,kamar yadda Hajiya ta ce ɗin haka na yi mata wannan gatan ko kafin ta fito daga wanka kuma na fitar mata da kayan da za ta saka yayin da Aliya kuma ta kawo abinci ta fice.

Bayan ta fito daga wankan ta saka kayan,ta zauna za ta ci abinci kenan na ce "wace ce ke?"

Ta ɗago da mamaki kafin ta ce "kamar ya?"

Na ɗan gyara zama kafin na ce "ina nufin ya kuke da Hajiya ?"

"Da Ummana da Hajiya uwarsu ɗaya,muna zaune ne a can ƙauyen Kagota can ne tushenmu " ta bani amsa . Na ce "ya aka yi kika zo nan? Ko dama kin taɓa zuwa ne?"

"A'a yau ne farko kuma ni ma ban san ya aka yi na zo ba,kawai na tsinci kaina a ƙofar gidan ne sai kuma na ga Hajiya "

"Bani saƙon da kika zo kawo mini " na faɗa ba tare da ni kaina na san takamaiman abin da yasa na ce haka ba.

"Wane saƙo?" ta tambaye ni kamar ba ta san abin da nake nufi ba,cikin ƙwaƙwalwata na ji an faɗa min abin da zan ce sai kuma ni ma na furta "wanda aka baki"

Ta saki ɗan murmushi kafin ta ce "amma ai matar Maheer aka ce na bai wa ba ke ba,kuma alamu sun nuna ke ƴar aiki ce sam babu alamun siffar wacce aka ce na bai wa saƙon"tana gama faɗar haka sai na saka idona cikin nata tare da juya su na soma yi mata maganar ido,"ki bani labarinki to"

"Sunana Habiba,kamar yadda na faɗa miki daga ƙauyen Kagota nake.Ni marainiya ce,banda kowa in banda Ummana wacce dangin mahaifina da kuma danginta suka juya mata baya ba tare da na san dalilin haka ba.Haka mutanen ƙauyenmu suna tsangwamar mu sam ba su yin duba da irin halin talaucin da muke ciki wanda shi ne yayi sanadiyar soma yin bararmu ni da Ummana.Ta hanyar mara muke samun abin da za mu ci muka tufatar da jikinmu,muna samun kuɗi sosai don zan iya faɗa miki duk wanda Umma ta neme ya bata sadaka to sai fa ya bayar.Ina mamakin haka don na sha yi mata tambayar ko dai asirin yin bara take da amma ba ta bani amsa,a ranar da Allah ya so ya nuna min ɓoyayyar fuskar Ummana ta aike ni bakin hanya sai na manta abubuwan da ta lissafa min hakan yasa na dawo sai dai cak na tsaya a bakin ƙofa.

Dukkan illahirin jikina rawa yake ,amma hakan bai sa na motsa daga inda nake ba sai ma ci gaba da kallon yadda Ummana ke wani rufe ido tana tsotse jinin wata ƴar jaririyar mage wacce tun tana shure-shure har ta kai ta bar motsi. Ummana na wurgi da gangar jikin magen na yi saurin dafe saitin zuciyata da take ta ƙoƙarin faso allon ƙirjina ta faɗo ƙasa.Ji nake kamar a ce mafarki ne nake ba gaskiya ba ce,sai dai ruhina yayi amanna cewa abin da idona ya gani zahiriya ne.

"Habiba?" na ji shaƙaƙar muryar Ummana na kiran sunana,sai a lokacin na fita jikin ƙofar ina mai shigowa cikin tsakiyar gidan namu wanda yake kamar juji tsabar datti.

"Anna ga ni " na faɗa kasancewar shine sunan da nake kiranta da shi,ina ta ƙoƙarin danne fargaba da kuma tsorona,sai dai haƙata ba ta cimma ruwa ba saboda tambayar da Anna ta watso min.

"Me kika ga na yi yanzu?" ta yi tambayar tana mai kafe ni da jajayen idonta waɗanda na lura da canjinsu daga jiya zuwa yau ne suka fara yi mata haka.

Na ɗan ƙaƙalo murmushi na ce "kina hutawa abinki" "Ɗauki mushen magen nan ki jefa cikin shara" ta faɗa tana mai ci gaba da tsare ni da ido.

Ko motsawa ban yi ba daga inda nake saboda ina da mugun tsoron mage sai da ta daka min tsawa na yi saurin ɗaukar wani busashen icce na ja magen har can cikin wani rame da muka haƙa don zuba shara.Na ja ajiyar zuciya ina mai juyo wa sai wani luguden tashin hankalin ne na kuma cin karo da shi yadda Anna ta soma rikiɗa kamar wata hawainiya.Ƙafafunta sun koma na mage har ma sun gota don guda takwas ne suka fito ras, sannu a hankali kuma ta ida rikiɗewa ta koma komai nata na mage in aka cire kanta da ke na mutum a daidai wannan gaɓar ne igiyar da ke saita hankalina da kuma ganina ta katse.

"Habiba?" na ji muryar Anna kamar a mafarki tana dadaɓa ni, a hankali na ware idona sai na ga tuni gari yayi haske alamun safiya ta yi. Anna na duba wacce ke gyara zaman wata cakuɗaɗiyar jaka ta fata akan kafaɗarta,"ki tashi kar mu makkara kin san an fi samun kuɗi lokacin wucewar ƴan kasuwa"

Ba tare da na maida hankali da tunanin abin da ya faru jiya ba na miƙe,ko ido ban wanke ba ƙafata dai ta yi sa'ar samun koɗaɗin takalmi wanda tsabar yadda suka siɗe ko kalarsu ba za a iya ganewa ba.

Fita na yi daga cikin ƴar bukar tamu na samu Anna a tsakar gida tana daidaita ƙusumbin ƙarya da take yi a kullum in za mu fita yawon bara.Bayan ta gama sai ta ɗauki sanda ta ɗan duƙe ta soma tafiya kamar wacce ke da ƙusumbin gasken.Ni kuwa tsohon kwanonmu da muke fita da shi na ɗauka kafin mu fice,manyan titunan da muka san motoci na bi muka fara bi muna amsar sadaka har muka isa cikin tasha.

Murya Anna ke maƙewa tana cewa "ku taimaka wa tsohuwa sadaka fi sabilillahi! Tsohuwa na yi muku bara " in an bamu kuɗi sai ta ɗauke masu manyan farashi ta saka a jaka su kuma ƙwandalolin ta bar su cikin kwano haka muka dinga zagaye har sai da muka samu kuɗi masu yawa,sannan ta saya mana ƙosai muka zauna muna ci.Daga nan zaunen ma Anna ba ta yi shiru ba haka take roƙon masu bi suna wucewa.

Bayan mun gama cin ƙosan muka je kusan wata randar ruwa irin wacce ake ajiyewa kan titi,ni na soma sha sannan ita.Ina kallon yadda Anna ta saka harshe cikin moɗar tana lasar ruwa kamar yadda mage ke yi.Sai a lokacin abin da ya faru jiya ya dawo min a kai,wani tsoro ya kama ni amma na fara ƙoƙarin ɓoye shi.

Mun yi gaba kaɗan na kasa haƙuri na ce "Anna jiya na yi mafarkin kin koma mage" ni kaina ban san ta ya aka yi na yi mata wannan zancen ba. Cak ta tsaya cike da mamaki ta ce "ni ma fa kamar na yi wannan mafarkin,wai fa har da jinin wata mage na tsotse"

Shuru na yi ina nazartar ta,sai na ga haƙiƙanin gaskiyarta fa ce take faɗa.

'Kenan in haka ne wato Anna ba ta san cewa ta rikiɗa a gasken ba?' na tambayi kaina a zuci kafin kuma na ce "Anna ba mafarki ne ba gaske kin yi hakan,don bayan kin tsotse jininta ni ce kika bai wa gawarta na cillar a ramen shara"

Wata irin dariya Anna ta yi irin kar na raina mata hankali kafin ta buga min sandar hannunta ta ce,"ja'ira wato ni za ki saka na yi zawo a wando ban shirya ba,ke ɗin ce za ki ɗauki mage ina kika kai tsoron naki to?"

Bayan ta jefo min wannan tambayar ni ma sai na ƙara yi wa kaina ita a zuciya 'to ko dai gaske ni ma mafarkin ne na yi?' banda amsa sai dai ina da shaida wacce zan tantance gaske ne kuwa.

Bararmu muka ci gaba da yi,ba mu dawo ba sai yamma lis.Muna ƙoƙarin shiga gida na hangi motar nan ta jiya wacce ba zan manta ba ta wata Hajiya ce wacce ta bamu abinci da nama da kuma lemun kwalba.

"Kaka ina wuni?" muryar matar ta daki kunnena,a tare muka juya ni da Anna wacce ta washe baki tana cewa "ƴar nan ke ce? Lafiya lau ya gida ya aiki?"

"Lafiya lau,nan ne gidanki ashe?" ta yi tambayar tana kallon ƙyauren gidanmu da ke a laƙwanshe.

Anna ta ce "i nan ne" "Ah bari na shiga na gani" ta faɗa tana ɗan murmushi,Anna kuwa daɗi ne ya luluɓe ta don shegen kwaɗayi ne da ita.

Da sauri ta buɗe ƙyauren duk muka shiga,Hajiya na ga tana dube-dube kamar mai neman wani abu amma sam ban kawo komai a raina ba. Ina shirin zama don na yi muguwar gajiya saboda yawon da muka yi Anna ta ce "Habiba je ki samo mana itace mu ɗumama tuwo"

Ba don na so ba haka na ɗauki igiya na fita,haka na dinga ratsa dajin da muke yo itace ba tare da tsoro ba don mun saba zuwa har cikin dare sai dai ban ta zuwa goshin magrib ba kamar yanzu.

Ko da na isa tuni duhun ya yawaita haka na soma karya busashin itace ina ɗorawa saman igiyata da na ajiye a ƙasa har zan ƙulle itacen sai idona ya sauka a wani wuri da koren haske ke ta ɓulɓulowa ta can cikin ƙasa.

Haka na je na soma tona wurin har na kai ƙarshen ramen inda na ci karo da wata ƴar koriyar lula.Jiki na ɗan ɓari na kai hannu na ɗauko ta duk a tunanina diamond ce tun da na ji ana zancen tana da ƙyalli ,sai dai contact ɗin da na samu da lular ya haifar min wani irin sanyin jiki tare da wata irin nutsuwa.

A hankali nake kallon yadda lular ke nitsewa cikin tafin hannuna haskenta kuma na ragewa har ta kai ta shige na bar ganinta.Idona ne suka ɗauki wani irin caji ta yadda har na rasa ganina na wuccin gadi,da sauri na dafa ƙasa ina fitar da wani huci . Tsayuwar inuwa na ji a bayana,tare kuma da jin wannan yanayin in ana kallonka ko kuma ba kai kaɗai ne a wuri ba.

A hankali na juyo,nan na yi arba da wasu ruhika guda biyu masu matuƙar haske.A lokaci guda kuma suka ɓace wa ganina bayan sun yi wani furuci da ban fahimci na mene ne ba.

Dakyar na iya ɗaukar itacena na nufi gida,tuni kuma masu yin sallah sun yi waɗanda ta dama don ni da Anna muna dai amsa sunan musulmi ne amma ba yin sallar muke yi ba dama-dama ita tana yin ta asubah shi ma don neman sa'a ne wurin Allah ya kawo mana cinikin bara.

Ko da na isa gida ban tarar da Hajiya ba,itacen na ajiye ina mai cewa "Anna ga su nan"

"Kin ga ɗora mana ruwan ɗumi mu yi wanka gobe tun da safe za mu bar ƙauyen nan" Anna ta faɗa tana wani duba kaya masu kyau. Na ce "ina kika samu wannan?"

"Hajiya ce ta bamu kin ga ke naki nan yi wanka sai mu saka" ta faɗa cike da murna tana miƙo min tawa ledar.Da murna ni ma na karɓa na duba kafin na fita na hura wuta,da ruwa suka tafasa Anna ce ta fara zagawa can bayan ɗaki domin yin wanka sai a lokacin na nufi ramen shara don duba mushen magen.Dare ne babu haske,sannan ba mu da ƙwan lantarki ballantana na gani ina shirin juyawa sai hannuna ya kawo haske ina haskawa sai na ga babu komai a ciki sai shara.

"Me kike yi kuma a nan?"na ji muryar Anna wacce ta yi daidai da ɓacewar hasken tafin hannuna. "Babu komai Anna "na bata amsa.

"Je ki yi wanka " ta bani umarni,ba tare da na ce komai ba na je na yi wankan sannan na canza kaya sai a lokacin kuma ta fiddo mana lafiyayen abinci muka ci muka hauda da lemun kwalba.Ban ɗauki wani lokaci ba bacci yayi awon gaba da ni,sai dai wannan karon ba irin baccin da na saba ba ne .Yana ɗauka ta na soma yin mafarkai iri-iri,wasu masu daɗi wasu kuma na ban tsoro haka na yi ta yinsu har Anna ta tashe ni muka yi wani wankan muka shirya sannan muka tsaya jiran Hajiya .Babu jimawa kuwa ta zo,ba mu ɗauki komai ba kamar yadda ta ce za ta saya mana sabbin kaya in mun je can.

Da na shiga motar har sai da na ji wata kasala,tamkar waɗanda suka shekare ita da Anna haka suka ta yin hira a hanya har muka fita daga ƙauyenmu.Ba zan iya ce ga adadin lokacin da muka yi ba,sai tashi na aka yi .

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull