Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 18

Bakin ruhi complete - Chapter 18

Bakin ruhi complete Chapter 18: Bakin ruhi complete Chapter 18. Murya na ɗan rawa Dr David ɗin ya soma yin magana,"ni na jawa kaina Maheer,ban taɓa sanin…

3,295 words

Murya na ɗan rawa Dr David ɗin ya soma yin magana,"ni na jawa kaina Maheer,ban taɓa sanin yaudarar ƴan mata abu ne mai illa ba sai yau da na yi gamo.Tun ranar da idona ya sauka kan Aliya na ji wata muguwar sha'awarta ta tsarga min wannan yasa na jawo ta a jikina,sai kuma na same ta mai sauƙin kai sam ba bani wuya ba sai dai fa ta kafe kan cewa tana son sanin a gaske na yi soyayya da Lubna? Shi ne na ce zan bata labarin komai amma ta same ni nan asibiti ƙarfe shidda na maraice ,da ta zo ne ni kuma na yi amfani da ilimina na jefa mata ƙwayar magani mai kashe jiki ba tare da na yi lura nan ɗin asibiti ne wurin ceton rayuka ne ba na tarwatsa rayuwa ba.Aliya na gama shan lemun na bijiro mata da buƙatata ina mai bata labarin soyayyata da Lubna. "A wani yammaci ne muka fara shan romon soyayyarmu kamar dai yadda nake yi miki yanzu" na yi wannan furucin ne lokacin da na soma raba ta da kayan jikinta na soma shafarta,dukkan jikinta yayi sanyi liƙis ba ta da wata zarrar hana ni amma a cikin idonta ina hango tsanar haka amma na ci gaba da bata labari "Lubna ta zo min da buƙatar tana son sperm ɗina,wadan ni kuma na ga faɗuwa ce ta zo daidai da zama don na jima ina sha'awarta amma sai take nuna min addininsu ya haramta haka.Ranar da ta nemi wannan alfarma mun yi da ita ta zo ta karɓa a can gidana,shi ne fa ta je ita ma magani na zuba mata a jus ta sha sai dai ita nata mai tayar da feeling ne .Mun yi soyayya a ranar nan,tsabar yadda na yi mata romance ita ce ta dinga roƙona na kusance ta.Bayan komai ya kammala ne na zuba mata sperm ɗin cikin ɗaya daga cikin kwalaben da Maheer ke ajiyar jininsa,don a lokacin ma da kumfar jininsa a jiki kuma ban wanke kwalbar ba .Ban san me ya faru ba a ƙarshe dai ta rabu da ni rana tsaka ta koma son Maheer ashhhh!" Dr David yayi shiru da bai wa Maheer labarin yadda suka yi da Aliya kafin can ya ci gaba da cewa "Maheer ban san cewa Lubna a ƙungiyar asiri ta kai sperm ɗina ba sai da Mamana ta faɗa min tare da yi min faɗa na bar ɗabi'ar nan ta banza ta yin fasiƙanci da ƴaƴan mutane amma na yi fatali da nasiharta har ta kai yau na nemi Aliya wacce da farko tun ina cikin yin sex da ita na ga ta rikiɗe ta zama tsohuwa tuguf kafin kuma ta koma wata halitta kamar Bushiya 🦔 dukkan jikinta gashi ne,to a lokacin ne na soma yin ihu amma ga banza don kuwa babu mai jin mu,daga ƙarshe dai maganin da na saka mata ya saki jikinta shi ne ta yi wata irin kururuwa ta soma yayaga min jiki, Allah ne yayi sa'a nurse Fatee ta zo kan lokaci ashe ita ma tana ɗauke da wani sirri nan ta fitar da Aliyar waje.Please Maheer ka taimaka min kar na mutu ina kafiri,dama can saboda na yi ta aikata abin da nake so ne yasa na ƙi musulunta amma na san da tabbas addinin Musulunci ne gaskiya"

Idon Maheer sun yi mugun ja kamar za su faɗo tsabar tashin hankali,sai a lokacin kuma Dr Muhamud ya shigo.Yayin da Dr David ya soma ihun fitar rai,duk yadda suka so su basa kalmar shahada kuma abu ya cuttura don ba a yi wa Allah wayo.Shi yasa yake yi mana hani akan kar mu jinkirta yin tuba,ga shi dai Dr David ya san Allah ɗaya ne amma ya biyewa son zuciyarsa don ya sha giya yayi zina son ransa ya ƙi musulunta.

"Ya fa mutu!" cewar Dr Muhamud cikin wata irin murya,Dr Maheer ya lumshe idonsa da suka yi masa mugun nauyi kafin ya ce "na gani,ka rufe shi da zane ka kira gidansu ka sanar "

Dr Muhamud ya ce "ya kake magana haka Maheer? Ko addu'a ai sai yi masa amma kana yin abu kamar ba abokinka ba"

"Me kake so na ce? Na saɓawa umarnin Ubangijina akan soyayyar da nake yi wa abokina? Ina ka taɓa ganin an nema wa kafiri gafarar Allah? Ina ce kusan kullum a gabanka nake faman yi masa shelar shiga musulunci amma ya ƙi duk da kuwa ya san gaskiya ce, wannan ma izina ce ga masu hali irin nasa ni babu abin da zan ce in banda Allah ya bamu haƙurin rashinsa " yana gama faɗa ya fita ya bar ɗakin,a can wurin flowers ya tsinkayi Aliya ta game kai da gwiwa tana kuka.

Dakyar ya iya isa inda take,maƙishinsa na yi masa wani irin ciwo ya ce "kukan me kike yi bayan burinki ya cika ya mutu ?"

Ta ɗago cike da takaici ta ce "ka san tsawon ƙarni nawa nake cikin duniyar nan amma ban taɓa sanin ɗa namiji ba? Ka taɓa rasa wani abu naka mai muhimmanci ne? Na sani Ni tsohuwa ce banda wani budurci amma mutumcina fa? Gangar jikin da nake ciki shin na yi mata adalci ne?"

Ƙure ta da ido Maheer yayi jin tana zancen ƙarni,wanda duk ƙarni ɗaya ya fi shekara ɗari biyu.

Aliya ta saki wani murmushi mai ciwo kafin ta ce "mutane na min laƙabi da matsafiyar aljana saboda an haife ni da ido guda uku ,biyu normal da ƙato a tsakiyar goshi wanda sai da na sha wuya sosai kafin na ɓatar da shi a bar ganinsa.Sanadin ido ukuna aka tsane ni,kullum cikin tsangwama ta ake duk da kasancewar ina da kirki,ina kuma son bil'adama duk da cewa dai wani sa'in na kan sha jininsu .Mahaifiyata ta haife ni tun ƙarni biyu da suka gabata,ta kuma mutu a ranar da ta haife ni.Na samu labarin cewa mahaifiyata ta samu cikina ne silar tozarta wani tsohon almajiri da yake yawon yin bara cikin gari da kayansa masu datti.Wannan tsoho shi ne mahaifina,wanda ƙiyasin mutane sun tabbatar cikin ɗayan biyu ne,ko dai jinsin aljanu ko kuma tsohon matsafi da ya laƙanci baƙin tsafi wanda yake dawo da ruhi izuwa duniyar bil'adama.

Na yi rayuwa ni ɗaya na tsawon ƙarni biyu,duk mutanen da na sani tun ina ƴar ƙarama duk sun mutu an haifi wasu su ma haka suke tafiya suna barina.Dayawan mutanen ƙauyen da aka haife ni suna mamaki in sun ji ina labarin abubuwan da suka shuɗe tsawon shekaru,amma kuma ga ni nan dai cikin ganiyar ƙurciyata saboda ban tsufa,alƙalamin daɗuwar shekaruna ya tsaya cak tun sa'ilin da na shiga shekara ashirin da huɗu tun ƙarni biyu na baya.

Ina rayuwa ni ɗaya ,cikin wani ɗakin kara da na gina shi da hannuna a can cikin daji.Yanayin shigata ya banbanta da na mutane ,don tamkar wata mahaukaciya haka nake suturta jikina.

Ba zan manta ba wata rana,ina tsaka da cin tururuwa da ƙwari don sune abincina sai na ji an bubu min ƙofa tare da cewa " ɗari shidda da sittin da shida?"

Kawai sai na samu kaina da amsawa "na'am" ina yin wannan furicin sai na ji tamkar an yi min wankin ƙwaƙwalwa,sai a lokacin ne kuma na tuna cewa sunana shi ne Evaliya.

"Evaliya? Evaliya? Evaliya?" na ji wata murya ta kira ni har sau uku,sai dai wannan karon ban amsa ba sakamakon ƙaton buzuzu da na saka a bakina. Shiru duk muka yi ni da baƙuwar muryar da ban san ta wace ce ba,amma duk da haka ina jin tamkar tsayuwar wasu sabbin abubuwa waɗanda ba a gani.To daga wannan lokaci ne kuma na fahimci wace ce ni, sannan na gane zan iya sauya siffa hakazali zan iya yi wa wani aiki irin yadda bokaye suke yi dalilin da yasa na soma cutar da duk wani da ya biyo hanyata nake kuma kyautatawa waɗanda suke zaman lafiya da ni.

Baƙin aikina na farko ba zan manta ba,wata rana ne ina zaune bakin ƙofar ɗakina ina wasa da maciji sai kawai na ji muryar wani namiji.

"Evaliya mai ƙarfin iko,budurwa jeji,shugabar matsafa na zo nan ne domin ki taimake ni" iya muryarsa kawai na ji tukuna ban gansa ba,sai da na nutsu na duba sai na ga ashe shi ne a cikin siffar wani ƙayon ɓera.Muna haɗa ido na gane shi,domin kuwa na san iyayensa waɗanda duk suka yi mulki a ƙalla zamani kusan biyar.

"Me na zo nema?" ita ce tambayar da na yi masa wancan lokacin.

"Ina son kawar da ɗan uwana ne kafin shi ya kashe ni,saboda mun yi tarayya akan buri guda wato hawa karagar mulki a yadda kuma na fahimta yana iya yin komai akan hakan" wannan ita ce buƙatar da ya zo min da ita wacce kuma ya san ina iya yi masa maganinta.

Sai da na yi dariya mai isata,su ma maƙarabaina suka shiga taya ni wato aljanai da ruhikan da nake rayuwa da su, can kuma duk muka yi shiru.

Na ce masa "Mene ne farashin da za ka bayar?" a wancan lokacin in za a iya mutum mugun aiki ba wai kuɗi ake buƙata ba kamar yadda bokayen wannan zamani ke yi,a'a mu jini muke so jinin kuma na ƴan adam.

"Ƴata zan baki mai wata ɗaya da haihu" ya faɗa saboda ya yarda ya rasa ƴarsa akan kujerar mulki wacce duk rintsi wata rana zai sauka ko kuma mutuwa ta sauke shi.

"Ka tabbata za ka iya kawo min ita a yanzu?"

"Eh wannan ba damuwa ba ce,zan sa masu tsaron lafiyata su kawo miki ita a nan.Ai babu abin da ya fi muhimmanci kamar sadaukar da rai domin samun muƙami da ƙarfin iko"

"Je ka kawo min ƴar taka" na basa umarni,ina gama faɗa sai ya nufi hanyar da za ta mayar da shi can cikin gari.Ni kuma haka na ci gaba da zama tare da ƙaguwa na ga babyn wacce nake ji a raina za ta iya yi min wani amfani domin kyautata gobena.

Daga ƙarshe dai ɗaya daga cikin masu yi masa hidima ya kawo min babyn,saura ƙiris na mutu don daɗi saboda yadda na ga taurarinta na da mugun haske . Cikin ƙwarewa da iya aikin siddabaru sai na soma bincike akan rayuwarta ta gobe,sai na gano cewa ita ce sarauniyar zamaninsu muddin ta rayu har zuwa lokacin.Sannan za ta yi farin jinin samari,daga cikinsu akwai sarakuna da kuma masu muƙamin mulkin gwamnati,ba kamar ni ba da babu wanda ya taɓa cewa yana sona saboda ni ɗin banda kyawun gani sannan kuma na banbanta da mutane. Wani tambari na yi na matsafa na yi zanen ido,da ƙwarangwal da niyyar canja gangar jikina daga nawa zuwa na ƴar ƙaramar babyn haka na soma yin baƙin tsafin duk da na san aiki ne mai matuƙar haɗari amma na gaji da gangar jikina.Cike da ƙwarewa na kammala aikina,ruhina ya shiga cikin gangar jikin babyn,yayin da na mayar da na babyn cikin nawa.A wannan lokacin abin da ya rage min shi ne samun ahali,wannan yasa na bazama yawo a cikin doron duniya a haka na haɗu da wasu mata da miji waɗanda sun shekara wajen goma sha biyar amma ba su taɓa haihuwa ba. Ni ce nan na ɗauke jinin period ɗinta wanda yayi silar zuwanta asibiti aka tabbatar mata tana ɗauke da juna biyu,a ranar ita da mijinta kamar su yi hauka tsabar murna ba tare da sanin ni ce nan zan zama ƴarsu ba.Kamar da wasa haka na saka cikin matar yana ta girma cikin ƙanƙanan lokaci har ta shiga watan haihuwa,kamar yadda na tsara haka komai ya tafi a gida ta haifo ni wanda a ƙiyasi watana goma sha ɗaya a duniya amma a wurinta yau ne ta haife ni.Sosai na shiga canyara kukan jarirai wanda hakan ne ya jawo hankalin maƙwabta suka san ta haihu.Bayan ta yi min wanka ta kimtsa ni cikin wani tatausan tawel sai ta soma yi min hoto ,yadda fitila ke dalle min ido sai na ji duk na tsani haka a ranar na tarwatsa wayarta ta ci screen kafin ma ta kai ga turawa mutane hotunana.

Bayan mijinta ya zo shi ma sai hau murna,tuni kuma maƙwabta suka soma shigowa duk wacce tsakani har da Allah ta yi murnar haihuwata haka zan yi mata abin alkhairi ta hanya buɗe mata business ɗinta,ƴan baƙin ciki masu hassadar uwar riƙona kuma haka na bi duk na cutar da su don ba zan manta ba wata mata uwar ƴan surutu sai cewa ta yi "Fannah wannan baby taki ƙatuwa da ita dube ta kamar ba jaririya ba" sosai na ji haushin furucinta,amma kuma don iya ƙwanƙwanto haka ta tsure ni da shegun idonta tana kallo.Ni kuma don in nuna mata ba duka komai ne in an gani ake tankawa ba kawai sai na ɗaga mata gira tare da murguɗa mata baki a tsorace ta ajiye ni tare da fita tana waiwayena nan ɗin ma gwalo na yi mata wanda yayi sanadin faɗuwarta to tun daga lokacin ta zama mai shanyewar ɓaren jiki kuma ta kasa yin magana.

Sai mace ta biyu wacce bakinta yake kamar na aku ga kuma shegen tambaya kama ma'ila'ika.Ba zan manta ba bayan ta sha kunun barka kawai ta soma yi wa Mamana tambayoyi har ta so kan haihu,"Fannah kika ce je ɗaya kika haihu babu ungozoma to wa ya yanke miki cibiyar jaririya? Ko kin iya? Har mahaifar ke kika rufe ta? Na ce duk uban jinin nan na haihuwa ke ce kika wanke shi alhalin kin haihu?" ji na yi kamar na kama da wuta,saboda a cikin abin da ta zano babu ko ɗaya da ya samu Fannah wacce take sabuwar uwa a gare ni sam ban bata wahala ba haka ta haifo ni kamar wacce ta zo yin kashi,sannan babu wani jinin haihuwa,ita kuwa mahaifa da cibiya duk babu su saboda tun ranar haihuwar wacce nake cikin gangar jikinta aka yanke su.A lokacin Mamana wato Fannah shiru ta yi ta kasa cewa komai,ita kuwa ƴar jarida ta je za ta sake jego wata tambayar na yi amfani da ƙarfin ikona na dantse mata harshe tun lokacin ba ta sake yin magana ba.Ba kuma shikenan iya abin da na yi mata ba,a'a haka duk dare nake zuwa can gidanta na shiga cikinta ina juyi tare da bata azaba irin ta naƙuda haka za ta haifo ni na faɗo jini na yi mata zuba sannan in ta zo yanke cibiya sai na mayar da ita maciji a ƙarshe dai tun hankalinta na iya ɗaukar dramar har ta kai ta rasa hankalinta.

Bayan sati guda da haihuwa ta sai aka zo zaɓen suna,ni ce nan na juya kwanyar wanda yake sabon mahaifi a gare ni ya zaɓar min sunan Evaliya.Sosai na yi murna ganin yadda suke nuna min so,na ji daɗi ni ma na samu asali sai dai fa babu wani abu da ya canza dangane da ruhina iya gangar jikin ce ke sabuwa.Ban farga cewa har izuwa yanzu aikin banza ba ne nake ,domin ba a canzawa tuwo suna sai da na soma yin wayo aka saka ni makaranta haka yara za su dinga yin wasa suna ware ni ba su so na shiga cikinsu,wasu ma da zarar sun ganni guduwa suke sai daga baya ne na gane cewa idon yaro na ganin sharrin abin da mayafi ya luluɓe.Wato idona uku haka ya bayyana a sabuwar gangar jikina,babu mai iya ganinta duk duniyar nan sai yara ƙanana ko kuma aljanai.

Wannan yanayi da na samu kaina na rashin karɓuwa a wurin ƴan uwana ƙawayena sai ya soma jefa ni cikin damuwa.Kullum in Mama ta bani abinci sai na ƙi ci haka komai ta yi min wanka sai na sake mayar da dattin jikina,in kuma Baba ya dawo sai yayi ta yi wa Mama faɗa sai kuma hakan yake yi min ciwo.Don ba zan manta ba akwai ranar da ya mari Mama,ni kuma na saukar masa da ciwon hannu wanda kuma shi ne farkon binciko matsalar gidan.Don kuwa ana ta neman magani amma hannu ya ƙi warkewa,da aka soma yin na gida ne wani boka ya ce "ai wannan sihiri aka yi masa,ba zai warke ba dole sai ya nemi gafarar wanda ya cutar" Baba na jin haka sai ya nemi Mama gafara ni kuma na cire ciwon da na saka masa.Na yi tunanin duk komai ya ida, kwatsam Baba ya fito da zancen aure wanda hakan ya tayar da hankalin Mamana amma duk ƙoƙarina na ganin an fasa auren abu ya cuttura,sai ranar da aka kawo amarya na fahimci cewa wata shararriyar matsafiya ce ya auro na saki murmushin mugunta don na san ai duk iya ƙwarewarta da tsafi ba za kai ni ba ƙila rabon a yi ne yasa ta auri Babana.Tun daren farko na caza mata kai yadda na jefa wa Baba wani laƙanin tsafi ya shatata mata fitsarin kwance,sai takaicin nata ya zama biyu ga shi bai kusance ba ga kuma yayi mata fitsari kan sabuwar katifa.Tun asubah ta fito tana masifa,ni kuma ina gefe kusa da Mamana macen da ke mugun sona duk da yadda ta soma lura ba normal mutum ba ce ni.

Da rana ƙawayen amarya suka zo,ana ta yi wa Mamana habaici daga cikinsu ma akwai wacce tsatsauyi yasa ta dungure min kai tare da shammata ta wai mai idon kifi,a zuci na ce ' za kuwa ki ga idon kifi'

Gefe na koma daga can bakin ƙofa ina kallon yadda suka ɗoran manyan tukane kan wuta wai al'adarsu ce washegari garin aure amarya za ta yi girki a rarrabawa mutane. Ina zaune hankali kwance har lokacin motsa miya yayi,ita wannan wacce ta dungure min kai ita ce ta je don motsa miyar tana buɗe tukunya muka haɗa ido huɗu da ita .Don a maimakon naman kaji a'a kaina ne kwance cikin tukunyar ina yi mata wani makirin murmushi,ta haɗiye yawun tsoro kafin ta waigo inda nake zaune nan ɗin ma ƙure ta na yi da ido.Ƴan magana na cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne,to haka take ita ma ƙawar amarya matsafiya ce amma ko a cikin matsafan ita jaririya ce.Murmushi na sakar mata mai nuni da ba ta ma ga komai ba ,tun da ta yi karanbanin taɓo ni har na bayyana ɓoyayyar fuskata a gare ta to ta shiga uku.Cike da mugunta na sa ta tsoma hannunta cikin tukunyar da ke kan wuta tana tafasa,ta ƙurma uban ihun da ya jawo hankalin dukkan sauran duk suka yi kanta sai a lokacin kuma na shige ɗaki......

[5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

23

Har suka gama tsiyar guminsu suka gama Mama ba ta fita ba haka ta jawo ni ta shimfiɗe kusa da ita tana dadaɓa ni irin in ana so yaro yayi bacci.A lokacin shekaruna biyar ne a cikin sabuwar gangar jikina,ido na lumshe amma hakan bai hana ni ganin Mamana tana hawaye ba. Ban san cewa na yi mata ƙuri da ɗayan idona na tsakiyar goshi ba sai da na ji hannunta na shafar idon kafin ta ce "ban so kina buɗe idon nan Aliya" saboda ita haka take kirana a cewarta wancan sunan kiristoci ne,na saki murmushi na ce "Mama kenan kina ganinta?"

"Ina gani mana Aliya ,tun ranar da na haifo ki na ganta"

"Amma me yasa ba ki nuna alamun tsoro ba?"

Sai da wasu hawayen suka zubo mata kafin ta ce "saboda ita uwa tana son ɗanta a duk yadda yake,sannan duk abubuwan da suka gudana wurin haihuwarki na fahimci ke ƴar baiwa ce ƙila shi yasa na haife ki haka nan"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull