Bakin ruhi complete - Chapter 19
Bakin ruhi complete Chapter 19: Bakin ruhi complete Chapter 19. Shiru na yi tare da buɗe idona biyu sai na ƙure ta da dukkan ukun,wato abin da na fahimta…
3,340 words
Shiru na yi tare da buɗe idona biyu sai na ƙure ta da dukkan ukun,wato abin da na fahimta matar nan tana mugun sona duk da ta ga alamomin da zai sa ta ji tsorona ko kuma ta yi wa kanta tambayoyi amma ta yi shiru ta ƙyale saboda ta jima tana roƙon Allah ya bata haihuwa gani take in ta nuna ba ta sona kamar ta yi wa Allah butulci ne.Na rungume ta ƙam,a wannan ranar ce na ji a raina ina iya canza BAƘIN RUHIna izuwa fari,komai niyya ce hatta shaɗan da yake hatsabibi farko ba haka yake ba shine ya mayar da kansa sheɗaniya.Sai na yi ta tunanin ta ya kenan zan canza? Amma ban samo amsar ba muryar Baba ta ratso ɗakin da muke kwance.
"Ki warware baƙin sihirin da kika yi wa ƙawar matata ko kuma na lakaɗa miki shegen duka" shi ne abin da ya faɗa cikin kumfar baki. Da idona na tsakiya na kafe shi,amma da dukkan alamu shi bai iya ganin haka.
Cike da ladabi Mama ta ce "to babu matsala" tana gama faɗar haka sai ta dube ni tare da sakar min murmushi wanda tuni na fahimci abin da take nufi,na saki ruhin abokiyar amarya sai dai fa hannunta na nan a ƙone.
Da suka yi girki sai suka hana mana ni da Mamana ,ni kuma na lalata dukkan abincin amma idonsu bai iya ganin haka ba wannan yasa duk suka ci cikinsu ya kumbure suka yi ta yin amai da guduwa.Ni kuwa da Mamana ɗan abin da ba a rasa ba ta nemo muka ci, da dare muna jin yadda Baba da amaryasa suke saffa da marwar shiga banɗaki a taƙaice dai wannan daren ma babu wani zancen raya sunnah.
Tsawon kwanakin da Baba yayi a ɗakinta haka na yi ta ƙirƙiro musu matsala iri-iri wacce ta hana su kasancewa abu ɗaya.A cikin ranakun akwai wanda na haifar mata da zubar jini,wani daren kuma na mayar da Babana shi da mace babu banbanci,yayin da wani dare kuma na fesa musu dafin cuta duk ƙuraje suka fito musu suka kwana dare soshe-soshe.
A ranar da Babana ya dawo ɗakin Mama na warkar da shi garas,sai kuma na yi balaguron ruhi don ba zan so na ji ko na ga yadda suke mu'amala ba tun da ni dai ba yarinya ba ce.A cikin balaguron ruhin da na yi ne na haɗu da wata mata mai ɗauke da farin ruhi ana ce mata Yabobo.Ban san me ta gani a tattare da ni ba wanda yasa ta rage min ƙarfin mugunta sai kuma ta bani wata power mai tsabta.A cikin wannan daren kuma ta zaga da ni duniyoyi biyu mabanbanta da ke can ɓoyayyar duniya.Ta koya min karatu da kuma bani labarinku kai da Haule,sannan ta sanar da ni mission ɗina wato kula da duk wani lamarin Haule da nuna mata hanyar da ya dace.Yadda muka shagala sosai ni da ita yasa ba mu farga gari ya waye ba a duniyar bil'adama,sai da na ji ana kukan makoki wai na mutu a lokacin ne kuma na dawo da esprit da RUHIna a gangar jikina.Sosai Mamana ta yi murnar haka,ta zubar da hawayen farin ciki tare da rungume ni ƙam a ƙirjinta.
Kasa ɓoye mata abin da na je na yi,amma da mamakina sam ba ta ji tsoro ba kuma ta ci gaba da zama da ni a haka ƙila don ba ta taɓa haihuwa ne ba.
Kwana biyu Baba yayi a ɗakin Mama kafin ya koma na amarya,a wannan gaɓar so nake na kawo ƙarshen komai wannan yasa na shiga tunanin Baba na soma controling ƙwaƙwalwarsa.Sosai na saka ya ɗirkawa amarya shegen duka ya yi mata rauni sosai don sai da ta samu kariya a ƙafa ,hannunta guda kuma ya goce.Ban tsaya a nan ba haka na sa Baba ya dinga yin Yare ya fi kala goma na mutanen ƙarnin da suka wuce,sannan sauyawa idonsa fasali sannan na sa yayi ta aman ɓoyayyen sirrin amarya da take tunanin babu wanda ya sani.
Washegari tun da safe danginta,dangin matsafa suka zo suka tafi da ƴarsu da Baba ya je biko kuma suka hana masa duk a tunaninsu manyan aljanai ne a kansa ba su san ni ce sheɗaniyar ba.
Tun daga wannan lokaci zaman lafiya ya wanzu a gidanmu,sosai iyayena suke nuna min so da ƙauna.A lokacin da na shiga shekara ta goma ce Mamana ta kwanta ciwo,jinyar da ba ta tashi ba ta yi sanadin mutuwarta.Rashin Mama a gare ni shine ya koyar da ni yadda ake jin ƙunci da damuwa,sai duk na bi na ɗaga hankalina da na Babana don kusan kullum sai na tashi tsakar dare ina nemanta.
Tsawon watanni uku muna cikin jimamin rashi kawai sai guɗa muka ji wai Kaka mahaifiyar Baba ta yi masa sabon aure.Tun da idona ya sauka kan amaryar na ji wata irin muguwar tsanarta a raina,sai dai kuma babu yadda zan yi da ita saboda mace ce mai son addini da kuma yawan yin sallar dare.Ina ji ina gani Baba ya tare shi da amarya,wacce ba ta rage ni da komai ba tun daga wankin kayana,abinci breakfast da duk wani abu da ya shafe ni baiwar Allah haka take yi min komai sai dai fa ba su sa na so ta ba.Saboda ina taya Mamana kishi,akwai ranar da na yi niyyar cutar da ɗan cikinta amma ban samu nasara ba saboda yadda duk bayan sallah asubah take yin Azkhar ta shafe dukkan jikinta sannan hatta cikin ma tana yi masa addu'o'in tsari.
Da na rasa hanyar da zan bi na kore ta kawai sai na tsiro da sabon iskanci na bar cin abinci kwata-kwata.Juyin duniya ta yi-ta yi na ci abinci amma na ƙiya,in Babana ya zo sai yayi ta yi mata faɗa ni kuma ina jin daɗi.Da na fahimci in an taɓa ni Baba na yin fushi,sai na dinga ƙirƙiro ƙananun matsaloli a tsakaninsu.In ta wanke kayana sai na furza musu datti su koma kamar ba a wanke ba,sai na ta yin kuka ina cewa Baba an bar kayana da dauɗa don an ga mahaifiyata ba ta da rai.Haka shi kuma zai tsare ta yayi ta balbalin bala'i,wani sa'in har marinta yake yi sannan sai su fi sati guda ba su yi magana ba wanda hakan ya fi komai yi min citta don in suna gaba nan ɗakin Mamana Baba ke zuwa ni kuma na ta yi masa hirarta.
Ban taɓa sanin addu'a makamin mummuni ba ce,kuma duk wanda ya riƙe ta ya riƙi hanyar tsira sai da matar Baba tsiro da wani sabon salo.Haka za ta yi ruwan addu'a ta feshe duk katangun gidanmu da na dakuna,turare Habbatu sauda da kuma zuba ta a cikin abinci sai ya zama ɗabi'arta.Babban abin da ta toje akai shine sallar dare,haka take kwana kan dadduma tana yin addu'a Allah ya tunkuɗe fitinar da ke sa suna samun saɓani ita da mijinta.Sosai addu'arta ke ƙona min ruhi tana raunata ni,so nake na bar gidan sai dai ban san ta yaya ba.
Wata rana ina kwance kan shimfiɗa dukkan jikina yayi ja sai raɗaɗi yake yi min saboda yadda take neman tsari daga sharrina ba tare da ita kanta ta san cewa ni ce matsalarta ba.Kawai sai ga Yabobo ta bayyana a ɗakina,"lokacin barin gidan nan yayi Evaliya zan nuna musu kamar kin mutu in sun rufe ki zan je na tono ku amma ki yi haƙuri ki bar Babanki na aro ya huta yayi rayuwar farin ciki,na san in kin yi haka mahaifiyarki ta aro ita ma za ta ji daɗin haka" shine abin da Yabobo ta ce min,banda wani zaɓi kuma da ya wuce na yarda da haka ɗin.
Washegari suna tashi suka ga gangar jikina ta sandare,aka kai ni asibiti likitoci suka tabbatar musu da na mutu.Baba ya kuka sosai na rashina ba tare da ya san cewa ni ba ƴarsa ba ce,haka aka yi min wanka aka je aka haƙa kabari aka binne ni.
Ina nan kwance ina jiran Yabobo ta zo ta tono ni,sai ga kuma wata gawa da aka kawo ba tare da ita ma ta mutu ba.Haka nake kallon komai har suka ida binne ta,a daidai lokacin ne kuma Yabobo ta zo ta ciro ni daga cikin kabarin sai kuma muka zuba ma na wannan baiwar Allah ido yadda take motsi take shirin yin mutuwar gasken.
Mu muka taimaka mata muka fitar da ita,sai kuma ta bamu labarin cewa ita Yayar Haule ce sunanta Aliya ga kuma silar zuwanta maƙabarta ba tare da ta mutu ba.Tun daga ranar ne kuma na ɗauki sunan Aliya matsayin nawa dama can haka Mamana ke kirana,sai kuma na shigo wannan ƙasar don nemo Haule ban kuma sha wahala ba aka kawo ni gidan da take aiki" Aliya na gama feso tarihinta Maheer ya ce "ita kuma Aliyar tana ina kin ce tana da rai?"
"Eh tana can dajin ceto,tun lokacin ta rasa hankalinta za ka ga ta yi maganar masu hankali bayan minti biyu kuma ta koma ruwa biyu.Na ɓoyewa Haule tarihina ne gudun kar ta shiga damuwa ta kasa ajiye hankali ta fuskanci babban ƙalubalen da ke tunkaro ta"
"Me yasa kika karɓa gayyatar Dr David ?"
"Ƙaddara ce da kuma neman ƙwaƙwaf na bin didigin abin da bai shafe ni ba,haka ba zai amfana min komai ba.Ina son sanin cikakken labarin Lubna ne shi yasa nake kula Dr David ashe shi da tasa manufar"
"Yanzu ai kin samu sai ki tashi ki koma gida,gobe ma ki je ki nemo gulmar" Maheer ya faɗa cike da takaici yana tunanin ina Haule ta shiga? Suna nan tsaye mahaifiyar Dr David ta shigo tana kuka,da aka nuna mata gawarsa kuwa sai da aka bata gado tsabar yadda ta shiga shock amma hakan bai hana aka soma shagalin bikin rufe shi ba. Tuni kafafen watsa labarai sun samu labarin mutuwarsa.Duk yadda Dr Maheer ya so kwantar da hankalinsa da ture lamarin Haule amma zuciyarsa ta kasa ɗauka,haka ya je ya buɗe ofis yayi zaune abin tausayi.Mutane dubi suke mutuwar Dr David ce ta jefa shi wannan halin ba su san cewa tunanin abincin ruhinsa yake yi ba.
Lokacin da Aliya ta koma gida ta tarar da Yasmine ta farka da dogon baccin da take ta ɗora wata sabuwar drama a gidan Hajiya . A falo ta tarar da Lubna da kuma ita kanta mai gidan,yayin da Yasmine ta jera kiras ɗin ƙwai ya fi ashirin tana ta ɗaukar ɗaya bayan ɗaya tana haɗiyewa ido a rufe. Aliya ta yi tsaye tana kallonta,tuni ta fahimci MACIJIN CIKI(MRS SADAUKI) ne cinye ɗanyen ƙwan ba wai ita Yasmine ɗin ba.
"Ki taimaki ki hana ta cinye min ƙwayaƙwayi,kaf abincin da aka yi na gobe ta cinye shi yanzu kuma ta koma da ƙwai.A ƙalla ta cinye kiras ya fi biyar" Hajiya ta faɗa tana hawaye,Aliya ta ce "hajiya ki koma ciki zan sa ta amayo duk wanda ta haɗiye" ai kuwa Hajiya sai ta ɗauki shawarar Aliya ta shige ɗakinta sai a lokacin kuma ita Aliyar ta yi amfani da powerta don dakatar da Yasmine sai ta fahimci cewa macijin jikinta ana ciyar da shi da jinin mutane yau kuma da aka killace ta babu yadda ya iya shi ne yake cin abinci don gusar da yunwarsa sai dai abu ya cuttura don abinci ba zai yi masa maganin yunwa ba.
Aliya ta dubi Lubna kafin ta ce "matso ki gani" ba ta musa ba ta matsa,sai Aliya ta kama yatsan Lubnar ta tsaga shi nan take jini ya soma zuba.Yasmine wacce idonta ke rufe tana jin ƙarnin jini kawai ta buɗe idonta waɗanda suke sak na maciji,tana ganin jini sai ta kama yatsan Lubna ta soma tsotsa na tsawon lokaci kafin ta saki ta ɓingire bacci.
Cike da tsoro Lubna ta ce "me hakan ke nufi?"
Kai tsaye Aliya ta bata amsa da "saboda a kullum ɗaya daga cikin member ɗin family yana shayar da ita ɗigon jininsa,shi yasa na bata naki "
Murya na rawa Lubna ta ce "amma ai ni na fita daga cikinsu"
Aliya ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo kafin ta ce "har yanzu sunanki yana rubuce cikin fayil ɗinsu,ba zai taɓa gogewa ba sai ranar da kika yarda kika bada ainahin labarinki sai a yi miki magani" tana gama faɗar haka ta yi gaba.
★JAPAN
Bayan mun gama waya da Innarmu sai na soma jiyo wani irin kuka kamar na doki kamar na jaki.Ban tsaurara bincike akan sai na san na mene ne ba kuma daga ina ya fito,kawai na samu wuri na kwanta.Bacci nake son yi amma tunanin halin da Maheer yake a wannan lokaci sai ya tsaya min a rai,a hankali na lumshe idona tare da lalubo tunaninsa cikin ikon Allah kuwa na same shi a zaune a ofis duk ya hargitsa kashin kansa,idonsa sun yi ja jawur kamar wanda yayi kuka. Muna haɗa ido,ya jefo min tambayar"ina ne nan kuma kika je? Da izinin wa kika fita?" ban kuma kai ga basa amsa ba sai ya juye dubansa kan system ɗin da na gama hira ni da Innarmu.Wani furici yayi nan take ta tarwatse ta zama gari liƙis,yadda ƙarar fashewarta ya fita sosai har sai da na zabura amma ban buɗe idona ba.
Hannnsa ya tsaga tare da yin amfani da jininsa yayi min wani rubutu a ƙasan marata,ban san mene ne ya rubuta ba saboda ba da Yaren Hausa ko turanci ba ne harufan ma ban san su ba.
"Haule?" na ji muryar Yaya Aliyu,da sauri na buɗe ido ina mai amsawa "na'am!"
"Karar mece ce na ji?" ina jin tambayar da yayi sai na dubi system ɗinsa sai kuma na ganta ras babu abin da ya same ta.Ban sani ba ko don ya ga na kalli saitinta ne yasa shi zuwa ya soma dubata,can kuma ya ɗago ya dube ni ya ce "Haule me kuke ɓoye min ke da Innarmu? Mene ne ba ku so na sani? Ko kina tunanin zan iya cutar da ke ne?"
Cike da mamaki na ce "don me yasa kake faɗar haka Ya Aliyu? Ni ban ɓoye ma komai,kawai dai Innarmu ta ce na koma can inda nake aiki lokacin karɓar muƙamina bai yi ba" na faɗi haka ba tare da na san dalilin yi masa ƙaryar ba.
Ya ce "amma me yasa kika goge duk hirar da kuka yi ke da Innarmu? Sannan ba ma iya ita kaɗai ba har da wasu bayanaina masu muhimmanci.Tun yaushe kika fara sarrafa ƙarfin ikonki? Kuma ma da kike cewa ba yanzu za ki karɓi kujerarki ba kenan sai yaushe alhalin hatta sarƙar juya ruhaniya ga ta nan a wuyanki?"
Na kai hannu na taɓa sarƙar da na ɗauko a dajin sirri,shiru na yi na kasa ce masa komai .Ya furzar da huci ya ci gaba da cewa "me yasa ba ku so iyayenmu maza su san da bayyanarki?"
"Saboda lokacin bai yi ba Ya Aliyu,ka sani shi fa komai yana da tsari ba haka ba ne ake yinsa kara zube .Ko ita sarƙar wuyana ban soma yin aiki da ita ba"
"A'a kin soma mana Haule,tun da har kika iya gane duk members Family wannan yasa kika raba ni da Yasmine.Faɗa min son ta kike yi ko me?"
Sai da zuciyata ta buga jin wani zance da Yaya Aliyu ke yi min,amma sai na kawar da kai ban ce komai ba.Ya ce "na ji na bar miki amma ki mayar da ita gidansu lokacin amfani da ita bai cika ba sai ta kai 18 years"
Zuciyata na luguden tashin hankali na ce masa "okay!" kawai sai ya fice ya bar ni nan,sam kasa bacci na yi haka na tashi na yi alwala sai dai babu hijabin da zan yi sallah kawai sai na hau yin zikiri.
Washega haka na haddace lambar Innarmu kafin Yaya Aliyu ya kai ni ɗakin sirrinsa wanda ta hanyarsa ne yake yin balaguro ya kuma zaga duniya.Sam ban yi mamaki ba ganin ta madubin tsafi ne zan bi na koma can Kamaru,da jininsa yayi amfani ƙofa ta buɗe muna kallon juna cike da soyayyar ƴan uwantaka muka rabu na ratsa madubin ina ayyana wa a raina inda zan sauka.Gidan Hajiya na ce ,sai dai ban faɗi a wane wuri ba hakan yasa na faɗo a cikin ɗakin Maheer a kuma bisa gadonsa.....
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻
*Ko kinsan Maman Yusuf Dr mata kuwa ?? Hmmm akace in bakasan gari ba to ka saurari daka*,💃🏻💃🏻 *Namu na dabanne kamar yadda salonmu yake daban ingantattun kaya ne da basuda wata illa ajiki sannan ba boka ba malam zaki mallaki mijinki da dandanonki sai yadda kikayi dashi*
Duk abunda kk so a bangaren kayan mata zaki samu hajiyata daga gyaran ciki harma Dana waje
Munada ingantaccen maganin sanyi na maza Dana mata hakama maganin Basir
Maganin nono Dana hips Maganin kiba dakuma maganin rage tumbi da kibar, Maganin gashi
Sabulun wanka na gyaran jiki Sabulun dilka na amare Dilkar amare
Kwallin mallaka (daga ni sai kai) Maltinar mata Bobintan mata Set na lalata gindin kiahiya Set na ukku bala'i Set na rantse bakida kishiya,
Kalolin gumba Kalolin gari Kalolin matsi Kalolin sabulan tsarki Zumar mata Zumar ridi Zumar goron tula Tsumin mallaka Tsumin jaraba Tsumin sabon budurci Tsumin kankana Tsumin tabaje Tsumin makalemata Shayin mata Sirrikan mallaka Dan goshi da mahadinshi Dan goshi na Mara Kyallen al'ajabu Rakumi da akala Bita zai zai Dahuwar kalolin kaza zabo zakara Dahuwar zuciya Dahuwar ciccibi Dahuwar zuciya Dambun nama Dahuwar yan shila Yajin mata Yajin maza domin Karin karfi
*Hmmmmmm in nace sai na lissafamuku zafafan kayan nan sai in wuni ina typing shawara daya zan baki uwargida in har baki jaraba kayan mmn Yusuf ba to ki garzaya ki saya da kanki zakizo kina godiya , 😉😉😉😉😉😍 wadan da suka San ya kayan suke kuwa. Basa bukatar wani Karin bayani , Domin Neman Karin bayani kokuma ganin kayan da nake dasu Ku tuntubeni ta wannan number 07069711327 call or WhatsApp mmn Yusuf mai kayan mata🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
Ina bada sari ina sokoto ina aikawa kowane gari cikin aminci da yardar Allah , Don Allah in baki shirya siyaba to kibari sai kin shirya sai muyi magana🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
24
🌻🌟🌻🌟🌻⭐🌻⭐🌻⭐🌻🌟🌻🌟
*_GYARA SHINE MACE_*
*_shahararriyar Mai Saida kayan Matan nan maman Yusuf likitar mata sokoto kuma CEO ta SOKOTO TOP 3 KAYAN MATA SOKOTO mai gyaran mata ciki da waje ta sake zo maku da zafafan Kayan masu kyau da inganci don farincinku a kullum shine burinmu* 💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻
*Ina uwargida da Amarya ina masu shirin yin aure budare da zawarawa , ina masu son su zama taurari ✨🌟ababen alfaharin mazajensu , ina mata masu kishiyoyi da ake ci masu zarafi ake wulakantasu akan kishiyoyin su ina wacce keshan wulakancin namiji , ina matan da sukeson burge mazajensu da zallan ni'ima da dandano ??? Ina matan fake fama da rashin ni'ima , budewar gaba wadan da suka faru sanadin ciyon sanyi kokuma haihuwa , ko wadda Ke fama da k'arancin ni'ima da karancin sha'awa , ?? To saurara kiji*✋🏻✋🏻✋🏻