Kenza eBookz

Bakin ruhi complete - Chapter 22

Bakin ruhi complete - Chapter 22

Bakin ruhi complete Chapter 22: Bakin ruhi complete Chapter 22. Da yake ni ma ina fatan ace abin da na gani ɗin ba gaske ba ne kawai sai na sa a raina eh…

3,355 words

Da yake ni ma ina fatan ace abin da na gani ɗin ba gaske ba ne kawai sai na sa a raina eh hakan ne shi yayi girkin.Da ya ga na yarda ɗin sai ya ja ni muka zauna muka ci abinci,bayan nan sai kuma ya bijiro min da buƙatarsa ta hanyar aika min saƙonni masu taɓa ruhi,tuni kuma na ɗau caji sai dai a wannan karon ɗakinsa ya ja ni wanda ya sha banban da yadda aka tsara nawa komai na cikinsa ja ne Haule.Kan gadonsa yayi min masauki wanda yake facing madubi,tun da muka hau bed ɗin sai na ji salon yadda yake yi min komai ya canza tamkar dai hannu bibbiyu ne ke shafata,tsoron zafin da zan ji yasa na buɗe idona na kasa rufe su a daidai lokacin da Mr Sahil ya soma nemana ta haramtacciyar hanya a daidai lokacin ne kuma idona yayi mugun gani Haule.Wata irin siffa ce a cikin madubi tana tsaye tana kallonmu,wannan tashin hankalin shi ya mantar da ni bala'in da ya soma faruwa da ni har sai bayan komai ya kammala na ji tamkar an tsaka ni gida biyu.

Na ci kuka sosai a waccan ranar,sai dai kuma na kasa yi wa Mr Sahil ƙorafin yin amfani da yayi ta haramtacciyar hanya.

Cikin ƙirjinsa ya rungume ni tare da yi min furicin da har in koma da Allah ba zan manta da shi ba,"na gode sosai Hijja na matakin ikon da kika sa aka bani,na ji daɗi sosai da na same ki a daidai ba ki taɓa baiwa wani bayanki ba..." yadda yayi murnar alfasha shi ya fi min ciwo,a jiya sam bai yi min godiyar kyautar budurci ba amma ga shi yana godiya akan luɗu da yayi da ni.A ranar nan ne na fahimci mugu bai da kama,sannan gaggawa aikin sheɗan ne yana kuma daga cikin babban kuskuren da na tabka a rayuwata da ban tsananta yin bincike a kansa ba kawai na aure shi na jefa rayuwata a garari..." anty Bahijja na kawowa nan da bani labarinta sai ta dakata tana mai ci gaba da yin kukanta.

Sosai na ji ta bani tausayi sai na soma bata haƙuri,na tayar da Yasmine sannan ta haɗo kayansu muka fito.A wannan karon kuma ban samu matsalar komai ba,sai bayan mun shiga taxi ne nake ta tunanin abin da kuma zan cewa Hajiya a wannan karon in na je. A daidai lokacin da taxi ɗinmu ta tsaya a ƙofar gidan Hajiya a wannan lokacin ne kuma Dr Maheer da Mahmud suka shigo layin gidan .Sai na yi tsaye har suka iso,a motar Dr Muhamud ɗin ce suke.Wani irin kallo na ga Maheer na yi min tare da jefo min maganar ido,"a ina za ki sauke su? Ko an faɗa miki nan ɗin asibitin jinnu ce da za ki dinga kwaso shara da tarkace kina kawo min a gida?"

"Ka yi haƙuri don Allah Alhaji , za ta dinga yin aiki ne ita ma kuma tana buƙatar taimakonmu " na basa amsa ni ma ta ido.

"Taimakonku ke da wa? "

Duk da na ga tambayar kamar cikin salon wulaƙanci amma haka na daure na ce "taimakonka nake nufi"

Sai yayi wani murmushin gefen baki kafin ya kawar da kai,ya ce "Dr Mahmud mu je daga ciki"

Sai a lokacin ne kuma na gaishe shi,sai na taimakawa anty Bahijja ta shigo da kayanta.A ɗakina na yi mata masauki kafin na ce "nan ɗin gidan da nake aiki ne,in Hajiyar ta zo ki ce mata Alhaji ne ya kawo ki za ki dinga yi mata aikin tuwo-tuwo.Na san hakan zai yi miki wuya duba daga gidan da kika fito amma..." da sauri ta katse ni "a'a wallahi zan yi kar ki damu na gode sosai "

Sai na saki murmushi na ce "jira na dawo" sai na fita zuwa kitchen,ruwa na zuba a tukunya ina shirin kunna gas ɗin na ji tsayuwar mutum a bayana,hannunsa ya ɗora kan nawa da ke kan makunni.Tuni ƙamshinsa ya yi wa ruhina dabaibayi,kasa motsi na yi na soma takurewa wuri guda don babu ta hanyar da zan bi na gudu sosai ya manna ƙirjinsa da bayana.

Cikin bazata na ji hannunsa ya zagaye cikina kafin ya ɗora haɓarsa kan kafaɗata ya soma magana a hankali cikin wani salo kamar tsohon kwarto. Duk illahirin jikina ne ya soma yin rawa,ya busa min iska a kunne yana mai sake tambaya ta "kawai don kina son Maheer sai ki ta yin ƙarya da shi ? Me yasa ba za ki ce su dinga cewa ke ce kika kawo su ba uhum? Kina tsoron Hajiya ta kore ku ke da su ne ? Me yaya Aliyu ya miki? Ya shaida miki wani abu ne da ya shafi gidanku?"

"Ka sakar min ciki tun da ni ba ƴar iska ba ce!" na faɗa da sauri ina jin zuciyata na tafasa,sai yayi baya kaɗan hakan ya bani damar juyowa.Yatsunsa biyu yasa ya matse laɓana yana mai cewa "duk ranar da kuka sake furta kalmar iskanci a gare ni sai na nuna muku yadda ake iskanci" yana gama faɗa ya sake su.

Na banka masa harara ina mai cewa "don ina gidanku sai aka ce maka ba zan iya faɗar gaskiya ba,in ba ɗan iska ba wane ne zai taɓa jikin wacce ba matars..." ban kai ƙarshe ba saboda wata irin fizgowa da yayi min da ƙarfi har sai da kaina ya bugu da ƙirjinsa.Da wani irin mamaki na waro ido jin a inda ya sauke min hannunsa,ban kai ga cewa komai ba na ji saukar laɓansa kan nawa.Irin abin nan da anty Bahijja ta gama bani labari ta ce ana ji shi ne ya soma dirar min ba tare da na shirya ba,na yi tunanin mugunta ce zai yi min amma sai na ji yana shan leɓana na ƙasa a hankali yana kuma sauke min numfashinsa kafin kuma ya soma yi min ainahin sumbar wacce ban san dalili ba na ji idona na fitar da ruwan hawaye..... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via

2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank

DM +22795045822.

🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.

__________________________________________________ *PAID PAGE*

26

Wata irin kasala ce ta saukar mini,duk wata lakkar jikina ta mutu murus.Banda wani ƙarfi ko izzar ture shi,hasali ma jikina rawa ya ci gaba da yi yayin da shi kuma Maheer yake kissing ɗina kamar wanda ya samu alawa haka yake yi wa lips ɗina da kuma harshena. Sai da ya gaji don kansa kafin na ji ya zare bakinsa daga cikin nawa yana mai sakar min numfashinsa a fuska,a hankali kuma na buɗe idona da ke ta tsiyayar da hawaye na zuba su cikin nasa da suka yi ja suke kuma fallasa min muradinsa.Duk da uwar masifar da na gani cikinsu bai sa na sunne kaina ba ko kuma na kawar da dubana ,haka muka ci gaba da kallon juna cikin ido kafin a hankali na ji hannunsa da ke bayana tun ɗazu ya soma ɗan janye shi a hankali har ya cire gaba ɗaya ya maido shi kan fuskata da take shaɓe-shaɓe da hawaye.

Da sauri na ƙara jan ido na kulle,ina jin yadda bayan hannunsa ke yawo kan fuskata yana goge hawayen amma kamar ma sake tunzura ni haka na ci gaba da yin wasu sabbi. Iskan bakinsa na soma jin yana hura min ,na san don na buɗe ido ne amma na ƙi. "Queen?" na ji ya furta can ƙasan maƙoshi kafin kuma na sake jin lips ɗinsa kan nawa,sai a lokacin na motsa da niyyar ture shi amma ya riƙe min dukkan hannuwan nawa tare kuma da yi min mugunta ya cije min leɓena na ƙasa sai kuma ya ɗan ture ni da sauri na buɗe ido, ya watso min wani kallo cike da shaƙiyanci ya ce "ita maitar taki har da ta sarrafa tunanin mutum kike da? Wato kambu Maita ne kika jefa min don na sumbace ki,to ai shikenan tun da kin samu abin da kike so sai ki je ki yi wanka" yana gama faɗar haka ya fice ya bar ni ƙumshe da takaici.

Da na rasa abin da zan yi kawai na yi zaune dirshen na fasa kuka,wato ni ce ma ke son haka? Shi bai ma ga rashin dacewar abin da yayi min ba tuhumata ma yake akan zunubin da shi ne ya aikata.

Sai da na ci kuka na gaji kafin na tashi na koma can ɗaki,cikin ikon Allah sai na tarar da anty Bahijja da kuma Yasmine duk sun samu bacci.Toilet na shiga,sosai na ji takaicin ganin abin da ban saba gani ba in ba a cikin mafarki na samu dalilin fitar da shi ba .Nan ɗin ma kuka na yi kafin na yi wanka na fito,ina tsaka da saka kaya Aliya ta shigo da dukkan alamu kuma cikin murna take.

Ba ta yi ƙasa da gwiwa ba ta soma surutunta da ta saba"kin ga gwamna ya saki challenge ɗin nuna gasar restaurant ɗin da suka fi iya girki,sannan kuma za a duba iya adadin mutanen da suka saya don a bai wa shugaba kyaututtuka na musamman ita da ma'aikatanta " tana maganar ne tana kallon wata takardar tana murmushi.

Duk da ban cikin yanayi haka na karɓi takardar ina dubawa,Aliya ta ci gaba da cewa "Hajiya ma ta shiga tsarin,kin ga za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe domin lashe wannan gasar mu fito da ƙimar Hajiya kin ga ta silar haka za ta ƙara mana albashi "

"Haka ne! Amma fa akwai jan aiki don akwai manyan restaurant fa " na faɗa .

"Ya na ji muryarki wani iri?" Aliya ta jefo min tambayar,sai a lokacin na ɗago kai muka haɗa ido ta saki ɗan murmushi tare da ƙumshe dariyarta sai kuma ta ce "za mu yi ƙoƙari don ganin mun ci gasar,kin ga har da fa babbar restaurant yayi alƙawarin zai buɗe ga gwarzuwa "

"To Allah bamu sa'a,me ya maido da ke gida?"

"Mun tashi mana! Hajiya ta wuce can kasuwa,ni ma na tawo gida kuma wallahi ban ida wanke sauran kwanuka ba kin ga karɓi key ki je ki ƙarasa" ta faɗa tare da bani key ɗin gidan abincinmu,sai kuma ta kalli anty Bahijja ta kuma maido dubanta gare ni.Na kawar da kai kawai sannan na ɗauki hijabina na fice,a ƙafa na tafi ina tafe ina tunani har na isa. Da na buɗe haka na shiga gyaran ko ina na wanke kuma kwanuka sai na zo nan inda ake cin abinci na ja kujera na zauna,abin da Maheer ne yayi min ya dinga dawo min a kwanya sai kuma na ji hakan ɗin ma na sake saka ni ni cikin wani yanayi,duk yadda na so na ture tunanin kuma na kasa.

"Almajira na yi muku bara" na ji muryar wata tsohuwa daga can bakin ƙofa,ba tare da na juyo ba na ce "ki yi haƙuri!" ban sake jin ta ce komai ba,na yi tunanin ta tafi ne sai zuwa can kuma na ji muryarta.

"Rashin sanin darajar mutane bai kamace ki ba jikata " da sauri na juyo muka haɗa ido ina kallonta sake da baki jin wani zance sai ka ce na zage ta .

"Me yasa za ki cewa na yi haƙuri alhalin kina da abin da za ki bayar da shi sadaka?" ta jefo mini tambaya tare da kafe ni da ido .

Cikin sanyi murya bayan na sauke ajiyar zuciya na ce "banda komai Kaka,ki yi haƙuri duk abinci ya ida"

Sai ta saki murmushi ta ce "a'a kina da shi,wannan ƙuncin da damuwar da ke ƙumshe a zuciyarki ita nake so ki bani"

Da na ji abin da ta ce sai na ɗan saki murmushi,ita ma ta mayar mini da martani kafin ta ce "ko ke fa! Dubi yadda fuskarki take da kyawu in kina fara'a .Faɗa mini kina sonsa irin sosai ne?"

Ƙuri na yi mata ina kallo,sai na fahimci ita fa wannan ba mutum ba ce kamar kowa.Kujera ta jawo ta zauna da kanta ba tare da na bata damar yin haka ba,sai ta tallabo fuskata da dukkan tafukan hannunta waɗanda suke da datti kafin ta ce "shi so wani abu ne da ba ya ɓoyuwa jikata,ki sani zuciyoyi suna kamu da ƙaunar junansu tun kafin masu mallakarsu su san da haka.Soyayyar mace ba ta ɓoyuwa rauni da ita kamar yadda ita ma ɗin take da rauni,yayin da shi kuma namiji yake da dakiya da ƙarfin halin ɓoye sirrin zuciyarsa sai dai kuma yake da rauni ta ɓangaren saurin bayyanar da kishinsa.Ina baki shawara,ki tsayar da zuciyarki wuri guda amma kuma ki yi abin da zai sa shi ya tunzura har ki raunata wannan ƙarfin nasa da dakiya da izza.A wannan gaɓar zai furta miki kalmar so"

Na kai hannuwana na ɗora kan nata kafin na ce "amma Kaka ban fahimci abin da kike son faɗa mini ba"

Da sauri ta janye hannuwanta kafin ta ce "je ki kawo min ruwa na sha "sai ta soma yin tari,da sauri na tashi na shiga ciki na samu kofi mai kyau na zubo mata ruwa sai dai ina fitowa wayam ban ganta ba.

Na leƙa waje ko inuwarta ban hango ba ballantana mai kama da ita,kuma ba ta isa yin nisa ba.Ni ma rufe gurin na yi na kama hanyar komawa gida.

★ A ɓangaren Maheer kuwa tun bayan da ya je bikin jana'izar Dr David ya kamu da ciwon kai mai tsanani saboda kiɗe-kiɗen manyan ganguna da kuma waƙoƙin kiristoci da ake a wurin.Wannan dalilin yasa ya ji bai iya driving kawai ya ce wa Dr Muhamud ya zo ya sauke shi gida,motarsa ma a can ya bar ta.Tun da suka shiga ciki ya lura kamar Dr Muhamud ya ji haushin yadda suka ƙure juna da ido shi da Haule amma ya basar,har ya kwanta kan kujera sai kuma ya sauko ƙasa don haɗa tea sai kuma ya ci karo da Haulen.

Sai da ya ƙarewa bayanta kallo na wani ɗan daƙiƙu kafin ya shiga ya rungume ta har ya sumbace ta,a duniya a jikin mace yana son ƙugu yana bala'in tayar masa da hankali.Sai kuma yau ne ya lura sosai Queen ɗinsa nada su sosai wannan yasa ya dire hannunsa a can .

Tun da ya ɗanɗanin zaƙin yawunta,ya ji ƙusoshin kansa sun kwance.Yau ne karon farko da ya soma yin kiss,ya so a ce kalaman ƙauna ne ya feso mata amma baƙar aƙidarsa ita ke ƙaran fankama ego ɗinsa wurin cewa bai son Haule kawai dai abokiyar cika aikinsa na duniyar Ruhaniya ce ita.Dakyar ya maida kansa sama,yana zuwa ya zube kan kujera yana jan numfashi.Dr Mahmud kuwa kallo ɗaya ya yi wa Maheer kafin ya fice ransa na masa ƙuna.

Maheer ya bi bayansa da muguwar harara kafin ya danne cikinsa da ke yi masa ciwo.Ya ja dogon tsuki a bayyane yana jin tamkar ya ɗauko Haule ya sauke girman abin da yake ji na shekara da shekaru.

In ya tuna kuma yadda ya ga duk jikinta yayi sanyi liƙis akan sumbata kawai sai ya shiga yi mata dariya yana jin cewa to ina ya gama da romance da kuma yi mata mai kankat? Dariyar shaƙiyanci yayi a fili kuma ya furta " suma za ta yi don daɗi" sai kuma ya yamutsa fuska ya miƙe a dadafe ya shiga toilet yayi wanka.

Bayan ya fito ya buɗe drower yana kallon dutsen sirrinsu wanda ke ɗauke da ɓoyayyen abu a ciki,kuma iya shi da ita ne kawai za su iya tarwatsa dutsen ya buɗe har su ga mene ne a ciki.

Rufewa yayi,ya kuma buɗe wani ɓangare ya ciro kayansa ya shirya cikin jallabiya H color.Bayan ya fesa turare sai yayi kwanciyarsa kan bed,ido ya lumshe yana son lalubo tunanin Haule duk da bai yi nasara ba amma yana jin motsin Yabobo a kusa da ita.Da sauri ya ware idonsa yana mai cewa "Uwa Yabobo a wannan duniyar ? To me ta zo yi? Kar dai a ce ta shaidawa Haule da aurena kanta in shiga uku" sai kuma ya miƙe da mugun sauri ya fito,direba yasa ya tuƙa shi zuwa can gidansu Dr David bayan ya ɗauki motarsa sai ya wuce can rijiyar sirri.

Yana kallon ruwan da ke ciki ya ja ajiyar zuciya kafin ya soma yin formula na kiranta zuwa gare shi.Ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba Yabobo ta fito fuskarta ɗauke da murmushi,Maheer ya kafe ta da ido kafin ya ce "na ji kin kai mata ziyara"

"Wace ce ?"

Ya ɗan turo baki gaba ya ce "wannan yarinyar mana"

Uwa Yabobo ta kawar da kai gefe kafin ta ce,"ni ban taɓa zuwa duniyar bil'adama ba akan yara"

Ya saki murmushi mai sauti kafin ya ce "ina nufi Queen H"

"Ita ta faɗa ma na je?"

"A'a ni na gano da kaina"

"Eh haka ne"

"To amma mene ne kika ce mata?" Maheer yayi tambayar cikin sauri ,hakan ya saka Uwa Yabobo juyowa tana kallonsa tana mai cewa "tsoron me kake ji?"

Ya ɗan yamutsa fuska ya ce "ni me zan ji wa tsoro?"

"To mene ne abun damuwa?"

"Kawai ni dai ban so ta sani"

"Tsoronta kake kenan?"

"A'a kin san halinta da rawar kai , wallahi har fyaɗe tana iya yi min muddin ta san sirrin cikar ƙarfin ikonmu ya ta'allaka ne da zama abu ɗaya ni da ita"

Sai da uwa Yabobo ta ci dariya kafin ta ce "kuma fa tsaf za ta iya in dai Queen Haulat ce,amma to kai me yasa ba ka son ku zama abu ɗaya?"

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce "dalilan nada yawa Uwa Yabobo ".Da sauri ta ce "bani guda uku"

Ya yi ƙasa da idonsa sannan ya ce "na farko dai har yanzu yarinya ce ita,sannan magana ba ta kwana bakinta shegen surutu ne da ita kamar Aku,a ƙarshe kuma ni dai ba zan iya bayyanar da jikina a gare ta ba"

"Shirmen banza! Babu ƙwaƙwaran dalili ko ɗaya a nan,kawai ka ce shegen taurin kanka ne ba zai bar ka wurin gudanar da abin da ke naƙarƙasar zuciyarka ba ne.Sannan ina mai baka shawara ka yi tattara don in ka cika sanyi hali da yi yuwar a canzawa Queen jarumi ɗan jagora" wani irin kallo yake bin uwa Yabobo da shi yana jin zuciyarsa na zafi,dakyar ya haɗiye yawun takaici "a canza mata wani yayi mata me?"

"Abin da ka kasa yi mata mana"

"Amma uwa Yabobo ba ki ganin ta yi ƙanƙanta,ko murfin shekara ashirin da biyar fa ba ta rufe ba.Kuma na faɗa miki tsorona take,na san ba ta shirya zuwana gare ta ba"

"Yanzu dai sai an jima akwai aikin da zan yi,ka tabbatar kuma ka tsaya tsayin daka har komai ya tafi daidai.Ita kuma Yasmine da ka yi biris ka ƙi kula da ita sai yaushe ne za ka yi mata maganin?"

Ya ja wani dogon numfashi kafin ya ce "to ai mutumniyarki ma ta sake komawa ta jajiɓo uwar Yasmine ɗin.Kin fi kowa sanin kuma macijin ciki ne babbar matsarta,na kashe shi ma bata kariya na cikinta kuma da buƙatar a fasa cikin"

"A'a bai kai ku fasa cikin ba,ka zauna ku tattauna da Queen ita ce za ta sanar da kai yadda za ku yi .Kar a kashe macijin a barsa da ransa don zai yi amfani a gaba" tana gama faɗar haka ta yi ƙasa ta koma can ƙasan rijiya.Da sauri Maheer ya bar wurin tare da zuwa ya shiga motarsa ya nufi can asibiti.

Ko da na isa gida na tarar da Lubna ma ta zo,suna zaune suna cin abinci ita da Aliya da kuma anty Bahijja wacce na ga babu wani laifi ta ɗan saki jikinta. Bayan mun gaisa na zauna ni ma na saka hannuna kafin na dubi inda Yasmine ke kwance tana ta bacci abinta,na ce "har yanzu ba ta farka ba? Kun ajiye mata abincin ne?"

Aliya ta ce "kin san fa ita cin abincinta ba wani ba ne,kawai dai shegen macijinta ne ke da matsala dole sai ya sha jini sannan a zauna ƙalau ba"

Readers Also Read

More by Bilyn Abdull