Bakin ruhi complete - Chapter 23
Bakin ruhi complete Chapter 23: Bakin ruhi complete Chapter 23. Shiru na ɗan yi kafin na ce "kar a sake bata shi,kawai ta ci abinci daidai wanda zai ishe…
3,368 words
Shiru na ɗan yi kafin na ce "kar a sake bata shi,kawai ta ci abinci daidai wanda zai ishe ta ita ɗaya"
"Wai kin ga abin da ta yi kuwa?Amma kuma ban san dalilinki na faɗar haka ba" cewar Aliya ,ban sake yin magana ba har muka ida na fita don kawo ruwan sanyi sai na yi kiciɓis da Hajiya wacce dawowarta kenan .
A mutumce na gaishe ta amma ba ta amsa ba ta jefo min tambaya" a ina kika tafi jiya? Wato yawon gantali za ki fara Haule don kin ga na kasa ɗaukar mataki a kanki? "
"Ki yi haƙuri Hajiya " na furta cikin sanyin murya amma tamkar na watsa mata ruwan zafi haka ta soma yi min masifa tana rantse-rantse akan ba za a yi yawon ta zubar ba a gidanta.Su Aliya duk sai suka fito,sai kuma Hajiya ta koma kan anty Bahijja "ita kuma wannan wace ce? A ina kuka jajiɓo ta?"
"Ina wuni Hajiya ? Dama Maheer ne ya ce na zo sai na dinga yi miki aikin tuwo-tuwo" anty Bahijja ta faɗa murya na ɗan rawa. Hajiya ba ta sake cewa komai ba ta yi gaba,yayin da mu kuma muka je muka taya masu aikin gidanta kwaso kayan da ta sayo.
Aliya ta matso dab da ni tana mai rage murya kafin ta ce "ina ga in kuka yi auren sirri ke da Maheer akwai babbar matsala,yo in ciki ya ɓullo jikinki Haule ba ke ba hatta mu muna cikin matsala"
Na dube ta da mamaki na ce "ni kam me zai sa na aure shi? Allah kiyaye min" a nan take kuma abin da yayi min ya faɗo min a rai har sai da na ji wani yanayi ya ratsa ni.
Aliya ta yi murmushi mai sauti kawai ba tare da ta ƙara cewa komai ba,bayan mun gama kwasar kaya muka yi sallah sai Lubna ta ɗebo tafarnuwa muka fara gyarawa a nan cikin ɗakinmu.
Aliya uwar surutu ta ce "Haule ni kam ki ci gaba da bamu labarinki,ya aka yi har kika zo nan gidan Hajiya?"
Na ce "tun ranar da na samu wannan ɓoyayyen sirrin na faɗa muku ban ƙara samun sukunin ruhi ba,duk kuma wata hanya ko alama wacce za ta nunawa iyayenmu maza na san sirrinsu Innarmu ta toshe ta.A kullum cikin yi min turare take sannan tana karanta min wasu abubuwa na cikin littafinta.Sai dai duk da hakan wannan halittar ta ɓoye a ɗakin sirri ba ta bar ni shaƙat ba haka duk dare zan dinga jin tana kirana tana cewa " Haule ki zo zuwa gare ni,Haule ke ce magajiyar wannan gidan " ban ƙara gigin ƙara komawa ba a bisa tsaron Innarmu wacce ta koma yin bacci da ido ɗaya.Ban san cewa ƙin zuwan nan da nake yi babbar illa ba ce sai da ƙuraje suka fara feso min a jiki masu mugun ƙaiƙayi,ba na yin bacci haka ma mutanen gida .Ana ta nema mini magana amma shiru kamar mai cutar kuturta haka abu ke ta yin gaba,ban warke ba kuma wata cutar ta sake bayyana a gare ni ita ce ta rashin yin baccin dare .Ko angaje ban yi ,sai in an kira sallar asubah kawai.Haka nake gadin dare wanda banda abubuwan ban tsoro babu abin da ake nuna min,a wani yammaci ne aka fara yin ruwa kamar da bakin ƙwarya yayin da mutane ke nema mafaka don su ɓuya a daidai wannan lokacin ne Innarmu ta samu zane ta goya ni tare da yafa wani ƙaton bargo wanda ban taɓa ganinsa ba sai ranar.Haka ta fito da mu ,ta yi tafiyar ƙasa mai nisa kafin ta tsaya ta sauke ni sai a lokacin kuma na ga cikin jeji ne ta kawo mu.
Tamkar yadda ake wankan jego haka Innarmu ta yi min wanka da wasu ruwa tana furta wasu harufa,cikin abin da bai fi minti goma ba sai ga dukkan ciwukan jikina sun warke.
Da mamaki na ce "Inna ya aka yi kika yi haka? Duba duk na warke "
"Kar ki sake yin tambaya Haule,ina so ki buɗe kunnuwanki da kyau ki saurare ni.Lokacin barin gida a wurinki yayi,za ki je wani gun ki ci gaba da rayuwa.Zamanki a gida babbar illa ce a gare ki da kuma sauran al'umma,na ɗaukarwa Yayana alƙawarin cewa zan ci gaba da gadin muƙamin nan har zuwa lokacin da zan damƙa shi gare ki,Haule ke ce hasken da zai haskawa duniya wane ne BAƘIN RUHI don haka ki zama jaruma kar ki saka tsoro a tafiyarki" bayan ta gama yin wannan furicin ba ta bani damar yin magana ba ta hura min wata hoda a fuska,ban sake sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na ganni a kwance kusan wata makarantar allo.Ban san a ina ne nake ba,wacce ƙasa ce? Shi ma ban sani ba.Haka na tashi zaune ina kallon yadda almajirai ke ta yin karatu,na jima sosai a haka kafin malaminsu ya zo gare ni.
"Baiwar Allah wace ce ke?" ita ce tambayar da ya yi min bayan yayi mini sallama. Na ɗago na dube shi babban malami ne,muna haɗa ido sai na ga yayi murmushi tare da cewa "tashi ki shiga ciki kin ga gidana nan" haka na miƙe na shiga kamar yadda ya ce ɗin,sai dai a bakin ƙofa na tsaya cak ina kallon ikon Allah. Wata mata ce a zaune dirshen kan tabarma tana ciyar da ƙadangare abinci tamkar wani ɗanta.
"Ke lafiya? Wace ce ke?" ta yi min magana cikin ruɓaɓiyar hausarta da dukkan alamu ba bahaushiya ba ce.Ban kai ga amsawa ba malamin ya shigo yana cewa "Agwe ki bata abinci baƙuwarmu ce,ta ɓata ne ba ta san kowa ba"
Ta yamutsa fuska kafin ta yi min alama da hannu,dakyar na cira ƙafata na isa gare ta sai ta nuna min gefenta na zauna sai kuma a lokacin wannan ƙadangaren da na gani a kallon farko na ga ya koma ɗan ƙaramin yaro kyakkyawa da shi kuwa.
Ko da ganin haka sai na fahimci cewa to na ƙara shiga hannun wasu matsafan."Ungo ci gaba da basa abincin kafin na kawo miki ruwa" ta faɗa tare da turo min kwanon abinci,yaron na kalla sai na ga yayi min ƙuri yana kallo.Ƙwayar idonsa sam ba ta yi kama da ta yaro ɗan shekara biyu ba,ta fi kama da ta babban mutum amma haka na daure na ɗebo abinci na kai bakinsa amma sai ya ƙi ci sai dai aukin kallona har sai da na tsargu.
Mamarsa ta dawo ta kawo min ruwa na karɓa na sha,bayan nan ta bani abinci na ci sannan na yi wanka na mayar da kayana.A wuni guda na fahimci Agwe,mace ce mai kirki sannan Kirista ce ita akwai addini da tawakali.Na gano haka ne a bisa labarinta da ta bani cewa tun aurensu da malam take neman haihuwa ba ta samu ba sai shekaru biyun da suka gabata ta samu Jafet shi ma da taimakon shugaban Cocinsu,ni dai saurarenta kawai nake amma ni na san gaskiyar da ba ta sani ba wannan yaro ba mutum ba ne .
A hankali na ɗan juya ɓangaren da yake a shimfiɗe yana bacci,sai na ga yana kallona kamar mai son tantance wani abu ni kuwa sai na mayar da kaina doluwa na shafi kansa na ce "kyakkyawa da shi kuwa anty,kin ga ashe hatta kiristoci ma kuna yin addu'a kenan ta neman biyan buƙata?"
Ta washe baki ta ce "eh sosai gobe in zan tafi in kana so sai mu je tare"
Na ce "zan je mana"
Ni na taya ta yin girkin dare,bayan an gama muka ci sai bayan sallar isha'i kawai malam ya zauna da mu ya binciki karatuna da kuma addinina kafin ya koyar da ni abin da ba a rasa ba.
Da dare yayi sosai duk muka yi shirin kwanciya,idona a rufe suke amma ba bacci nake ba.Ji na yi ana kallona irin kallon ƙurillar nan amma ko da wasa ban buɗe idona ba don kuwa na fi tunanin aljanin yaron nan ne,ai kuwa shi ne.A hankali na ɗaga fatun idona ina satar kallonsa ta ƙasan ido,sai na ga idonsa suna bado haske tamkar na mage ban kula shi ba haka ban nuna na gane wane ne shi ba haka na soma yin tunanin gida har bacci ya ɗauke ni.
Washegari malam ya tashe ni na yi sallar asubah,sai Anty ta bani zanenta na yi ɗaurin ƙirji sai na wanke kayana ko da gari yayi haske kuwa sun bushe na yi wanka na mayar da abina.Bayan mun ci ɗumame sai muka fita zuwa Coci,sosai na yi mamakin ganin yadda Cocin ta cika maƙil da mutane.
Cikin ƙanƙanen lokaci na ƙarewa cocin kallo,komai na cikinta ja ne tun daga kujerun da mutane ke zama har wani dogo capet da ke shimfiɗe haka ma inda Fasto ɗin ke tsaye yana yi musu huɗuba shi ma ja ne,idona na sauka kan wata ƙatuwar Cross sai na ji gabana ya faɗi saboda wani tambari da na gani a tsakiya mai zanen ido.Ina shirin kawar da kai sai na ga idon na ƙyaftawa daidai kuma wannan lokacin ne Fasto ya ce "duk kowa ya lumshe ido za mu fara yin addu'a " haka kowa ya rufe ido,amma ni nawa na bar su a buɗe akwai mutane sosai amma hakan bai hana Fasto sanin cewa akwai wanda bai rufe idon ba sosai na yi mamakin haka da na ji yana cewa "kowa ya rufe ido na ce" amma na ƙi rufewar sai da na gansa a tsaye a gabana tsudum,na zabura ina kallonsa tare da mamakin ta ya aka yi duk ya ƙetare mutane har ya zo gabana? Ba ma wannan ba wurin na da girma sosai in ma zai tawo ai zan ji sawun takunsa ba da sauri na rufe ido.
Addu'o'insa waɗanda ba na komai ba ne sai na tsafi ya soma yi nan wasu suka fara faɗuwa suna ihun iskokai ,a gaban idona ƙatti majiya ƙarfi suke ɗaukar duk wanda ya faɗi suna shigar da shi wani gurin.
Cikin muryarsa ta mayaudara yake cewa "mala'iku za su sauko yanzu ,kowa yayi addu'ar da yake so"muryar Anty Agwe na ji tana addu'ar tana so ɗanta ya fara magana kamar kowanne yaro,a hankali na buɗe ido na kalli Jafet wanda ke goye a bayanta ,shi ma kallona yayi yana wani ƙanƙance ido.Muryar Fasto ta daki kunnena inda yake cewa "akwai waɗanda ba namu ba ne a wurin nan,akwai kura da fatar akuya a cikinmu" yana gama faɗar haka sai ƙamshin wani turare ya cika wurin,yayin da kuma Fasto ya soma zagayen ko ina yana magana cikin wata irin murya wacce ta saukar min da kasala nan take jikina ya ɗau kyarma kafin na farga na zube ƙasa,da sauri ƙattin nan suka zo suka ciciɓe ni suka shigar da ni inda na ga sun kai sauran a can ne na yi arba da wani sabon tashin hankali,na fahimci cewa har yanzu dai tamkar ina cikin komar iyayenmu maza...... [5/18, 07:33] Buhainat: My book is only 500 via
2670215530 ZULFAU YAHAYA Ecobank
DM +22795045822.
🔞In kin san ba ki biya ba kar ki karanta min book,yin haka babban kuskure ne don cin haƙin da ba naki ba ne.Kuma Allah ba yafe haƙin wani akan na wani,don haka kar ki raina girman haƙi komai ƙanƙantarsa.
__________________________________________________ *PAID PAGE*
27
Ɗakin da suka kai ni wani keɓaɓen wuri ne mai kamar matattarar sheɗanu,an yi zane iri-iri na fatale da doddani sannan ga wani abu da suka da farin alli a ƙasa mai kamar da'ira.A cikinsa suka jefa ni suka yi tafiyarsu,da na gwada fita sai na ji tamkar an hura wuta a wajen da'irar da nake ciki dole na zauna babu jimawa kuma shi Fasto ɗin ya shigo da maƙarabansa.Wasu suna waƙar nan ta kiristoci yayin da wata mata kuma ke kwance tana jan ciki tamkar yadda tsutsa ke yi,sai kuma na ji muryar Fasto yana amton sunana "Haule kin jima a wannan duniyar,amma ba ki ga komai ba.Yau esprit da ruhinki za su yi balaguro su zaga duniyarmu " yana gama faɗar haka sai biyu daga cikin maƙarabansa suka zo suka kamo hannuwana,ina son ƙwacewa na gudu amma tamkar wata gawa haka nake a sandare ban iya wani motsi.
Fasto ya matso kusa da ni hannunsa riƙe da wani plate mai cike da jini baƙi ƙirin,sai kuma alƙalami."Wannan gangar jikin da kuma ruhin da ke cikinsa namu ne,a yau za mu ƙaddamar da ke ki san amfanin zuwanki duniya.Za ki yi hidima ga shugaba,kafin ya dawo mamallakinki ya shiga gangar jikinki " yayi magana tare da ɗaukar alƙalamin yana dangwalo wannan baƙin jinin yana mai yi min zane a tsakiyar goshi da kuma hannuna na hagu .Yana gamawa na soma ganin wasu irin baƙaƙen inuwoyi na saukowa tamkar doddani,na yi ƙara sai dai muryata ba ta fita ba.Tuni suka fara ɗalasiman tsafi ta hanyar fasa ƙwai da kuma kunna jan kyandir,tamkar an hasa wuta a cikina haka nake jin duk illahirin jikina ya ɗau zafi,ɗaya daga cikin inuwar da ke faman saukowa ta matso dab da fuskata ta ce " bamu abin da kike da na farin ruhin da ya hana mu ƙarasa aikinmu" tana gama wannan furucin sai na soma kakarin amai tamkar ina son fitar da wani abu,ƙila abin da suke so ne.
Ina cikin wannan hali ne kwatsam sai ga wata tsohuwa ta shigo ɗakin hannunta riƙe da wani tsohon Bible tana mai karanta shi cikin muryata ta tsofi,nan take Fasto ya faɗi ƙasa yana nishin azaba haka ma maƙarabansa.
Ban ƙara sanin abin da ya faru ba sai tashi na yi na ganni a ɗakin tsohuwar nan. "Kin tashi?" ta furta,na jinjina mata kai kawai ita kuma ta ci gaba da cewa "ban san dalilinki na zuwa Cocin BAƘIN RUHI ba alhalin kina ɗauke da baiwar fararen taurari.Amma ki sani da ace ban zo ba da ƙila sun juya alƙiblarki"
Na ce "amma Kaka na ji kina karatun Bible hakan na nufin ke ma Kirista ce? Kuma dama Bible nada muhimmancin haka?"
Ta yi wani murmushi kafin ta ce "Annabin Allah ne ya zo mana da shi fa kin ga ba za a ce bai da amfani ba,sosai ake yin ruƙiya da shi a ƙasashen kiristoci"
"Amma ai musulunci ne addinin gaskiya"
"Shi ma wanda aka bai wa littafin Bible ai musulmi ne,sai dai kuskuren da aka samu shine yadda mabiyan Bible suka bin son zuciya na ci gaba da amfani da shi alhalin hatta Bible ɗin ya faɗa musu cewa akwai Manzo na ƙarshe da zai zo shi za su bi,sannan littafin da ya zo shine za su ci gaba da karantawa su kuma yi aiki da shi"
Na ce "Kaka duk kin san wannan amma kike ci gaba da rayuwa a haka? Kawai ki musulunta hakan shine daidai"
Ta ce "gani na yi na tsufa sosai"
"Shi addini ai babu ruwansa da tsufa kawai ki tuba ki koma turbar gaskiya"
Ta jinjina kai tare da yi min alƙawarin za ta musulunta sai kuma ta tambaye ni,"ina ne gidanku?"
Shiru na yi kafin na ce "gidan malam mijin Agwe "
"To tashi mu je na yi miki rakiya" ta faɗa sai duk muka fito,ashe babu ma wani nisa .A ƙofar gida muka ga malam,shi ne kuma ya baiwa Kaka kalmar shahada ta biya ta a gabana kafin na shiga ciki.
Wanki na tarar anty Agwe na yi,muna haɗa ido ta kawar da kai bayan ta yi min kallon banza .Jikina ne yayi sanyi ganin canjin da aka samu, ina shirin gaishe ta idona ya sauka ga Jafet wanda ke wasa da ruwan da aka yi masa wanka .Muna haɗa ido ya sakar min murmushi irin na nasarar nan ,wato abin da na fahimta zuwa yanzu ya tabbatar wa kansa ina ganin ɓoyayyar siffarsa.
"Kar ki sake kallon yarona,kuma yau sai kin bar gidan nan bari malam ya shigo " Agwe ta faɗa tana zuwa ta ɗauke shi ta goye a baya shi kuwa munafiki har da yi min gwalo yana wani lafewa a bayan wacce in bai yi jika da ita ba to ya haifi sa'anta.
Sallamar malam ce tasa na juya,tare suka shigo da Kaka wacce na bari yana biya mata karatu.Cikin ikon Allah kuwa idonta ya sauka kan Jafet wanda shi ma na lura har sai da ya firgita .
"Ke kam lafiya kika goya shi a baya kina aiki? Kawo shi nan na riƙe miki " Kaka ta faɗa tana matsawa kusa da Agwe,Jafet ya fashe da kuka saboda bai so a sauko shi Kaka ta riƙe shi amma duk da haka munafikin sai da aka sauko shi.
Kaka ta samu wuri a tabarma ta zauna tare da rungume shi tana mai cewa "malam yi ruwan addu'a ka miƙo na basa ka ga yadda maɗagarsa ke motsi alamun ciwon kai ne"
Malam kuwa abin nema ya samu ya kuwa cika kofi da ruwa yana ta zuba addu'o'i, murmushi kawai nake yi ina kallon Jafet da ya soma yin maganar ido.
"Ya za ku yi min haka? Ai ita Agwe ɗin ce ta damu Fasto kan sai yayi mata addu'a ta samu haihuwa yanzu kuma don ta haife ni shine kuke baƙin ciki?"
"Dukkan ku munafukai ne kai da shi,da ta ce tana son haihuwa ta ce muku tsoho take so irinka? Kuma ma mene ne amfanin cutar da Haule?"
"Ita ɗin tamu ce ,ina so ki sani duk inda za ta shiga daga ƙarshe dai dole ta dawo tsagenmu saboda ita jika ce da Nalado " shine abin da ya faɗa ,da sauri na ga Kaka ta juyo tana kallona kafin ta jefo min tambayar "dama ke tsatson Nalado ce?"
Jikina ne yayi sanyi dakyar na iya motsa idona na bata amsa da " eh shi ɗin Kakana ne"
Ba ta ƙara cewa komai ba,ta jira sai da malam ya miƙo kofi sannan ta dinga taɓe bakin Jafet tana ɗura masa ruwan wanɗanda suke ƙona baƙin ruhinsa mai cike da mugunta.Cikin nishin azaba ya buɗe baki ya ce "ku bar ni zan fita"
Malam da Agwe duk suka maido hankalinsu wurinmu ƙila jin muryar tsoho a bakin ɗansu. Kaka ta yi murmushi ta ce "zan tara mutane ka faɗa musu mugun ayyukan da kuke yi a Coci sannan ya zama dole a rufe ta ma"
Haka Jafet ya dinga kuka saboda babu abin da Mayu da matsafa suka tsana irin tonon asiri,amma kafin ka ce me tuni an tara jama'a a ƙofar gidan malam kafin dugunzuma gidan mai gari.A can ne Jafet yayi bayanin cewa shi ne Jatau wani tsoho da yayi zamani kusan ma akwai jikokinsa har yanzu cikin garin.Tsohon maroƙi ne shi,sannan kuma maye ya jima yana cinye jariran mutane sannan kuma suna haddasa husuma a cikin gari tare da ingiza mutane cikin ɓata suna yaɗa da'awar ƙarya tare da yin tsafin da zai sa mutane su yarda Cocinsu tana da wani ƙarfin iko wanda littafin Bible ya basu.A ranar ya shaida mafarin da ke sa wasu daga cikin mutane ke faɗuwa in Fasto na huɗuba,masu ragowar imanin gaskiya ne ko kuma waɗanda tsafin bai kama ba sai idonsu ya ga abin da bai kamata a ce sun gani ba wannan yasa suke ɗauke su domin shayar da jininsu ga abin bautarsu. Sai da Jafet ya sha azabar ayoyin Alkur'ani sannan ya buɗe bakinsa wani baƙin abu yayi ta fita can kuma Jafet ya tsanyara kuka saboda zuwa yanzu iya shi ɗaya ne ke da iko da gangar jikinsa. A wannan ranar aka rufe Coci,yayin da kuma malam ya ɗauki darasin amfanin yi wa ƴaƴa addu'a a kowacce safiya.
Bayan komai ya lafa Kaka ta ja ni gefe tana mai cewa "rayuwarki na cikin haɗari ya zama dole ki bar garin nan tun yanzu ba wai sai gobe ba,mu je na yi miki rakiya" ta faɗa tare da jana muka je gidanta,ko sallama ban yi wa su malam ba Kaka ta busa min irin hodar nan wacce Innarmu ta yi amfani da ita.
A wannan karon ji na yi kamar numfashina ya tsaya na wuccin gadi kafin kuma na bayyana daidai ƙofar wani kamfani. Shiru na yi ina nazari,' to yanzu kuma wace masifar zan haɗu da ita ni Haule ?' na tambayi kaina a zuci,kafin na samo amsa na ji muryar wani babban mutum a kaina .